Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

waima kin sakejin labarin Balkeesu kuwa?". Murmushi Rasheeda tayi tare da cewa.
"Bansake jin labarinta ba kwata-kwata, gaskiya ƙarshen Balkeesu baiyi kyauba, da kanta ta ɓata rayuwarta, Allah dai yayi mana me kyau."
Da. "Ameen". Zaleeha ta amsa, dan itakan tabbas Balkeesu ta cutar da ita arayuwa, guduwan da tayi tabar ɗakin aurenta, akwai sa hannun Balkeesu aciki dumu dumu, amma gashi tun aduniya Allah ya mata sakayya.
Hira suka ci gaba dayi da Rasheedan, wanda duk bayan mintuna kaɗan saitaje ta zubar da yawu a sink, ita kuma haka nata salon cikin yazo, bata rabuwa da yawu abakinta, da ta gaji datashi ne, Zaleeha ta bata sweet ta jefa abakinta, bayan Zaleeha ta kawo mata kayan ciye ciye taci ne, tayiwa Zaleehan zanen lalle me kyau.
Har yammaci Rasheeda takai agidan, saida sukayi sallan magriba kafun Ishaq yazo ɗaukanta, Ummine ta sashi agaba saida yaci abinci ya ƙoshi sannan ya ɗauki Rasheedan suka tafi.
Zaleeha kuwa koda aka idar da sallan isha, sabon wanka tayi tare da tsantsarawa kanta ado, sosai tayi kyau cikin shigar sleeping gown ɗin da ta sanya. Sai ƙamshi take bazawa haka ta nufi sashin Saifuddeen.
Inda su Khareem da Khausar kuwa suke wajen Inna Shatu, kasancewar sun ƙara wayo hakan yasa, basu da wani yawan ƙiriniya, sosai suka saba da Inna Shatu shiyasa idan zasu wuni su kwana awajenta, matuƙar sunsha nono to bazasu taɓa yi mata kuka ba, ga kuma Baffan su Hayatuddeen wanda shima ya ɗauki nauyin kula da yaran akansa, dan da zaran ya dawo school yana gama karatunsa, zaizo ya ɗaukesu dukansu haka zai kwanta acikinsu yana Musu wasa. Da sallama ɗauke abakinta ta shiga cikin ɗakin nasa, fitowarsa daga wanka kenan dagashi sai towel ɗaure a ƙugunsa.
Murmushi suka sakarwa juna, atare suka kashewa juna ido, giransa ɗaya ya ɗaga mata alaman. "Babe ya?." ƙarasowa gaban dressing mirror'n tayi, ɗan ƙaramin towel ta ɗauka ta shiga goge masa jikinsa, yanayin yanda take goge masa nasa jikin da salo ne, yasa duk yaji jikinsa ya sake, Saif ɗinsa na ƙoƙarin miƙewa, ganin haka yasa ta ware towel ɗin dake jikinsa, ahankali takai hannu ta shafo Saif dinsa, wanda take ta tsaya cak, cikin wani irin salo ta soma shafasa tana ɗan murzawa ahankali, ganin yanda tsikar jikinsa suka mimmiƙe ya kuma wani lumshe ido, yasa takai bakinta kan Saif ɗin, take ya saki wani irin nishi da kuma gurnani, hakanne yasa ta soma yi masa sucking tana lashewa da harshenta, sosai ta zautar dashi, har ƙafafunsa suka garara ɗaukarsa.
Ahaka yajata suka karasa kan gado, light off ɗin wutan ɗakin ya musu, azafafe ya rabata da kayan jikinta.
Wani irin romancing suka shiga yiwa juna, wanda yasa duk jikinsu ya ɗauki rawa, lokacin da suka samu kansu ajikin juna, wani irin nishaɗi ne ya ziyarcesu, haka suka dinga sambatu da gurnani kala-kala, sun raya daren nasu cike da soyayyar juna, yayinda Saifuddeen ya more zuman Zaleeha son ransa, bayan sun dawo cikin nutsuwarsu ne sukaje sukayi wanka, koda suka kwanta maƙale da juna haka sukayi bacci.

***

Lokuta da dama rayuwa tana tafiya, kwanaki suna gushewa, abubuwa kuma da yawa na faruwa, to hakanne yakasance arayuwar su Saifuddeen dan yanzu Shekaran Zaleeha Ɗaya cib da haihuwan su Khareem, acikin Shekara ɗayan nan kuma da ta wuce abubuwa da yawa sun faru, ciki kuwa harda haihuwan Ameena inda ta sake haifo ɗanta Namiji, mai kama da ita sak, saidai farin Babansa ya ɗauko, anyi shagali asunan nata masha Allah, Saifuddeen yayi bajinta, ankuma sakawa yaron sunan Babanta, taji daɗin hakan kuwa sosai suna kiranshi Abbi.
Yaran Zaleeha kuwa masha Allah sun ƙara girma sosai, sun zama gwanin ban sha'awa, dan har sun soma takawa da kafafunsu, duk dama tafiyan beyi ƙwari sosai ba, saidai wani abun mamaki yaran sun taso da wani irin kyawun daya zarce na iyayensu, hakanne yasa kowa ke so da ƙaunarsu, babuma kaman Babansu, Adeel ma yasake girma sosai dan har ansashi a makaranta, sosai ya ƙarayin wayo, ɓangaren shaƙuwansu da Zaleeha kuwa sai abun da yayi gaba, dan hatta kayan sawanshi yanzu a sashin Zaleehan yake, bashi da wani magana saina Amminsa, komai nasa na Amminsa ne, soyayyace me zafi atsakaninsa da Zaleeha.

Ziyada ma ta haifi ƴarta mace, wanda akayiwa Adda Maryam takwara, za'ana ƙiran yarinyar da sunan IMAN, tasha gata kuwa awajen ƴan uwa da mijinta, dan hidima sosai suka mata.

Haka Rasheedan Ishaq ma ta haihu, ta samu ɗanta namiji, wanda aka mawa Saifuddeen takwara, ranan da Saifuddeen yaji cewa ɗan Ishaq ɗin takwaransa ne baƙaramin daɗi yaji ba, haka ma su Ummi sun tayasa murna.

Aɓangaren Hayatuddeen dasu Zakariyya kuwa karatunsu ya miƙa, kuma Alhamdulillah suna samun nasarori acikin karatun nasu sosai, dama shi Hayatuddeen ɓangaren Accounting yake karanta, dan bashi da wani buri da ya wuce zama cikakken ma'aikacin banki, shikuwa Zakariyya Low yake karanta, dan burinsa ne zama babban lowyer me zaman kansa, Khamis kam aɓangaren Doctors yake, wanda kowa acikinsu yanason burinsa yakai ga ci. Alhamdulillah kuma suna samun nasara, dan kowanne sakamakonsa yana fitowa da kyau, dan ko a exam ɗin da sukayi, Hayatuddeen shi yazo second class offer, sosai sukayi farinciki, hakanne ma yasa Saifuddeen ya basa mota, wanda zaina ɗan zirga zirgansa aciki, yaji daɗin hakan kuwa, dan dama Ya Ahmad ya sayawa Zakariyya mota me kyau, Khamis ma kuma dama yana da nasa motar.
Yau dai kam Hayatuddeen ya ƙudurta aransa cewa zai sanar da Hammansa game da maganan Zahrah, dan zuwa yanzu sunyi wani irin sabo da Zahrah'n duk dama tanajin kunya da nauyinsa, bata wani sakewa dashi, amma tabbas ya hango zallan ƙaunarsa acikin idanunta, sannan kuma akullum yanajin kansa abuƙace da mace, dan zuwa yanzu yana da kusan shekaru 24 kenan, duk dama bayanzu yakeson auren ba, ya fiso sai ya kammala school ɗinsa zuwa lokacin yasan yana da 26 years. Koda ya samu Hamman nasa da maganan Zarah, sosai Saifuddeen ɗin yasha mamaki, saidai bai nunawa Hayatuddeen ɗin ba, murmushi ne ya fafaɗa akan fuskar Saifuddeen ɗin, cikin kulawa yace.
"A ina yarinyar take? sannan kuma a ina kuka haɗu da ita? a ina kuma iyayenta suke?." Duka waƴannan tambayoyin yayiwa Hayatuddeen su, bayan ya zuba masa tsumammun idanunsa. Ɗan sosa ƙeya Hayatuddeen yayi cike da kunya, cikin ɗan basarwa yace.
"Sunanta Zarah Hamma, kuma agidan Baba Bello take, ƴar ƙanwar Baba Bello ne, mun haɗu da ita tun wani zuwa da nayi, lokacin kuna Instanbull, ka aikeni nakai masa kuɗi shine muka haɗu da ita, Allah Hamma saif yarinyar tanada hankali sosai, kuma a layin gomnan Yobe gidansu yake".
Murmushin jin daɗi Saifuddeen ɗin yayi, cikin gamsuwa da kalaman Hayatuddeen ɗin ya jinjina kansa, tabbas yaji daɗin hakan, Insha Allah kuma bazai ƙi nemowa Hayatuddeen ɗin auren Zarah'n ba, duk da yasan cewar Hayatuddeen ɗin nada rikici, amma kuma bazai yiwa kansa zaɓin dabai dace dashi ba. Gyara zamansa yayi, cikin nutsuwa yace. "Naji daɗin hakan.ƙwarai, na kuma yi farinciki jin cewar ɗiyar Baba Bello ce, dan babu wani wanda zaiso ƙin haɗa zuri'a da jinin Baba Bello, tabbas Baba Bello mutumin kirkine Insha Allahu kuma, nasan zaiyi mana jagora wajen zuwa tambayo maka auren Zarah awajen iyayenta, saboda haka ka kwantar da hankalinka, Insha Allah ko zuwa gobe zanyiwa Baffa Ali magana, duk abuk dayace shikenan." Cikin jin daɗi Hayatuddeen ya rungumi Hamman nasa, cike da zumuɗi yace.
"Nagode sosai Hammana, yanzu zanje na faɗawa Ummi komai." Murmushi kawai Saifuddeen yayi, Hayatuddeen kuwa da sassarfansa ya nufi sashin Ummi.
Ummi ne kaɗai afalon sai kuma Zaleeha wanda take kwance asaman doguwar kujera, su Kareem da Khasim dama suna can wajen Inna Shatu. Ƙarasowa cikin falon yayi yana ta sakin murmushi, jin zuciyarsa yake fara ƙal, ganin yanda yake ta sakin fari'a yasa Ummi cewa.
"Hayatuddeen wannan fara'ar taka kuma ta mecece, duk yanda akayi dai akwai abunda kasamu na al'khairi." Murmushi yayi tare da zama akusa da Ummi'n nasu.
Hannayenta ya kamo ya riƙe cikin nuna tsantsar ƙaunar da yakewa Zarah yace.
"Ummi kin tuna lokacin dana kaiwa Baba Bello aika, lokacin su Hamma suna Instanbull?". Ɗan jim Ummi tayi, tunowa da ranan yasa ta jinjina kai alaman. "Eh" Murmushi ya kumayi tare da cewa.
"Yauwa to Ummina, arananne na haɗu da wata ƴar ƙanwar Baba Bello, Wallahi Ummi yarinyar tana da hankali ga nutsuwa, kuma sunanta Zahrah, ummmm to shine fa dama tun alokacin naji..." Shiru yayi yana wani ɗan sunne kai alaman kunya. Dariya Ummi tayi tare da cewa.
"Ikon Allah wai yau kuma ni Hayatuddeen kejin kunya, lallai akwai wata aƙasa, faɗamin kaji autana inajinka."
Jin haka ne yasa shi sake nutsuwa, duban kansa yayi, tare da cewa. "Ummi ranan ina cewa kikayi na girma ko." Kai Ummin ta jinjina masa tana murmushi tace.
"Ai yanzuma kafi ranan girma, yanzu fa kai saurayine bakaji na daina ce maka Autana ba, saboda ka girma ne ai." Jin kalaman Ummin yasashi jin sanyi aransa, tare da sabon ƙwarin guiwa.
Cikin zumuɗi yace. "Yauwa to Ummi, dama tun aranan naji inason Zarah'n, kuma naje gidansu gaishe da Mamanta ma yafi sau uku, kuma itama nafahimta tana sona, tun alokacin muka fara soyayya, saidai banason faɗawa Hamma karyace nayi ƙarami, shiyasa na bari sai yanzu na faɗa masa, kuma yayi na'am yace zai faɗawa Baffa Ali sai su samu Baba Bello, Inason abani ita agidansu Ummi, kinga yanzu next month zan fara bautan ƙasa, dana gama kuma shikenan nasan zan samu aiki, daganan kuma ai Ummi kinga zan iya aure ko?". Wani irin farinciki ne ya cika zuciyar Ummi, tabbas taji dadin hakan, musamman ma jin cewa ita yarinyar kamar ƴa take awajen Baba Bello, tsohon arziki.
Kansa Ummi ta shafa cike da gamsuwa tace. "Masha Allah Autana ya girma, na kuma ji daɗin wannan zancen saboda haka Allah Ya sanya al'khairi ya kuma sa itaɗin rabonka ce."
Da. "Ameen" ya amsa yanata wani jin daɗi. Idanunsa yakai kan Zaleeha dake bacci, hannunsa yasa yaja Khausar dake jikinta, cikin zumuɗi yace. "Adda Zaleeha wakeup please, nazo da labari me dadi."
Zaleeha da baccinta baiyi wani nisaba ta buɗe idanunta, ganin Hayatuddeen ne yasa ta tashi ta zauna tare da kontar da Khausar. Hayatuddeen kam zumuɗi yakasa barinsa yayi sakat, hannu yasa yana shafa kan Khausar kaman yanda yayiwa Ummi haka ya shiga bata labarin Zarah.
Sosai Zaleeha taji daɗin hakan, take ma taji baccin nata ya gudu, nan ta biye masa suka shiga hiran Zarah, ita da kanta take tsara irin yanda bikin na Hayatuddeen zai kasance.
Dubansa tayi cike da farinciki tace.
"Lallai lokaci yayi Hayatuddeen, tabbas kowa sai yashaida auren Autan Ummi, zamuyi ɓarin daloli zakuma mushiga mu fita, insha Allah bikinka sai ya zama abun kwatance agarin Gombe, zamu nuna maka gata sosai, wani abun saima awajen diner party, ni dakaina zan fitar mana da ankon tsalelen lace."
Murmushin jin daɗi Hayatuddeen yayi, tare da cewa.
"Yauwa Adda Zaleeha shiyasa nake sonki ai." Hira suka cigaba da ɗan taɓawa, kafun daga bisani ya ciro wayarsa ya ƙira Raleeya, tundaga kan farkon haɗuwarsa da Zarah har zuwa yanzu saida ya labarta mata, sosai taji daɗi take itama tasoma juyi da imagine yanda zasu tsara bikin. Hira suka ɗan taɓa shida Raleeyan kafun daga bisani sukayi sallama.

Haka dai Hayatudeen ya ƙare wunin ranan na yau, cikin farinciki da zumuɗi. Ɓangaren Saifuddeen kuwa, tun ayau ɗin ya ƙira Baffa Ali ya sanar masa abun da Hayatuddeen ɗin yazo dashi, sosai kuwa Baffa Ali yaji daɗin hakan, yayi farinciki matuƙa, nan yake cewa Saifuddeen ɗin.
"Insha Allah gobe zaizo idan yaso sai suje can wajen Baba Bello'n dan ya sama musu iso wajen iyayen Zarah'n."
to ahaka dai suka tsaida magana.

Koda dare yayi bayana an idar da sallan Isha, Saifuddeen sashin Zaleehansa ya wuce, kasancewar yau itace dashi, dan Ameena ma batanan yau tana da Night duty, kuma awannan karon bata barin yaron nata agida, dashi take tafiya, dan yana da yawan kuka, shi bakamar Adeel bane da yake babu ruwansa, gashi yaron yana da yawan tsotso.

Koda ya shiga ɗakin Zaleehan tsab ya sameta, ta kimtsa kanta cikin wani body hug masu kyaun gaske, wanda suka bayyana zallan suran jikinta. tana ganinsa taje ta faɗa jikinsa, tare da saka masa sakalci wai ita dole ice cream zata sha, wanda yake cikin fridge ɗinta kuwa ya ƙare. Hannunta ya kama suka nufu side ɗinsa, shida kansa ya ɗauko ice cream acikin fridge ɗinsa, zaunar da ita yayi akan cinyoyinsa. Ahankali yake bata ice cream ɗin abaki, tana sha tana lumshe masa fitinannun sexy eyes ɗinta, wanda yasa yaji gaba ɗaya ya fara rasa nutsuwarsa.
Ganin irin kallon da yake binta dashi, yasa ta haɗe bakinsu waje ɗaya, tana me bashi wani irin lafiyayyen kiss, sanyi da daɗin bakinta daya ratsashi ne yasashi sakin wani zazzafan nishi. Haka suka dinga kissing juna cikin salo, daga nanne kuma labari ya sanja salo, inda suka nutsar da kansu cikin wata daddaɗan duniya na musamman wanda yasasu zaucewa da sambatu.

Bayan sun nutsune suka maƙale juna, ahankali yake shafa bayanta har tayi bacci, tashi yayi ya ƙarasa aikinsa daya fara tunda yamma amma baiƙarasa ba, da yakeyi, yana kammalawa yazo ya kwanta ajikinta shima haka yayi bacci.

Washegari Kamar yanda Baffa Ali ya faɗa cewar zaizo, bayan anyi sallan Azahar kuwa sai gashi yazo.
Basuje gidan Baba bellon ba kuwa saida sukayi sallan La'asar, bayan sun idar da sallan ne suka tafi. Aƙofar gida suka samu Baba Bello, ganinsu yasa yaji daɗi, ya kuma yi musu tarba ta musamman, anan cikin ɗakinsa dake zaure ya musu masauƙi. Iya ne ta kawo musu ruwa me sanyi da kuma fura, duk da cewar Saifuddeen aƙoshe yake, amma saida yasha sosai, dan baya taɓa iya tsallake tayin gidan Baba Bello, dan ko ba komai nan ɗin ji yake kaman gidansu ne, haka ma Baba Bellon matsayin Baba yake agaresa. Gashi kuma yasan Iya ta ƙware sosai wajen dama fura kindirmo.
Bayan sun gama shan furanne, Baffa Ali yayiwa Baba Bellon bayanin komai.
Jin abun daya kawosu yasa zuciyar Baba Bello tayi fari, take ya cika da murna, dan kusan shi ya mafi kowa jin daɗin hakan, dan tabbas yasan Hayatuddeen yaro ne me hankali, gashi kuma yana da tsatso da kuma nasaba me kyau, saboda haka wa zaiƙi haɗa jini dasu.
Cikin son ƙarafafa musu guiwa da kuma amincewa yace. "Tabbas naji daɗin wannan maganan na kuma yi farinciki, saboda haka insha Allah yau basai gobe ba, zan nema muku izinin ganawa da iyayen Zara'u, nakumasan mahaifinta bazai ƙiba, dan me biyayyane agareni." Godiya sukayiwa Baba Bellon, take kuwa ya ciro waya ya ƙira Alhaji Ibrahim wato Baban Zarah'n kenan.
Shaida masa yayi cewa. "Anjima idan ya basu lokaci zaizo shida baƙi, zasu zo roƙon iri awajensa."
Babu wani kwana kwana ko jan lokaci Alh. Ibrahim ɗin yace.
"Su zo koda yaushe yana maraba dasu." sunji daɗin hakan ƙwarai sun kuma saida lokaci cewa, idan suka idar da sallan Isha zasu zo sai su ɗauki Baba Bellon zuwa can gidan. Hakan kuwa akayi koda sukayi sallan Isha, gidan Baba Bello suka sake komawa, bayan sun ɗaukeshi ne kuma suka nufi unguwar su Zahran. Koda suka ƙarasa gidan, tarba me kyau suka samu daga wajen Alh.Ibrahim mutumin arziki wanda ya iya karrama baƙi, dan anan cikin babban falonsa ya sauƙesu, yaji daɗin ganinsu ƙwarai, koda yaji abun da yake tafe dasu kuwa, farincikin nasa ƙara ninkuwa yayi, dan suɗin mutanene masu mutumci, bakuma wanda zaiƙi jininsu, dan yasan Saifuddeen yana kuma jin labarinsa awajen Baba Bello, harma dasu Alhaji Ishaq, dan Alhaji Ishaq da Alhaji Kabiru abokan sana'ansa ne, suna ɗan taɓa harkan saya da sayarwa ga junansu, dan shima ɗan kasuwane me cikakken rufin asirin Allah, dan sam bazaka ƙirasa da talaka ba, bakuma zaka ƙirasa da irin masu kuɗin haukan nan ba, saidai kuma akomai nasa babu ƙaranta. Kasancewar shida ƙaninsa me bi masa ne, suka tarbi su Saifuddeen ɗin, hakan yasa basuyi wani dogon zanceba, sukace sun bawa Hayatuddeen Zarah, insha Allah idan da rabo zata zama matarsa,dan dama yarinyar karatu take bata kuma kula kowa, bata ma taɓa tsayuwa da kowa da sunn hira ba, amma sun bawa Hayatuddeen daman yana zuwa zance, saidai kuma sun roƙi alfarmar cewa, abari saita ƙarasa karatunta kafun akawo maganar aure gadan gadan dan yanzu saura mata shekara biyu na ne ta gama secondary school. Sosai su Saifuddeen sukayi na'am da hakan, dan suma sun fison hakan, ko ba komai zuwa lokacin Hayatuddeen ya kammala bautar kasan sa, sannan kuma harma ya kama aiki Insha Allah. To ahaka dai suka tsayar sun kuma yi magana ta fahimtar juna masha Allah kuma, zuciyar kowa fari tas take, sun rabu da juna cikin aminci da mutuntawa. Koda suka dawo gida, basu ɓoye komai ba suka sanar da Ummi, sosai taji dadin hakan, ta kuma ƙara godewa Allah, da nasarorin rayuwa da yake basu. Hayatuddeen ma dake laɓe duk yaji komai, haka ya dinga tsalle da rawan murna, har yanaji ajikinsa cewa shikenan ya gama mallakan Zarah, Insha Allah Zarah tasa ce. Haka su Saifuddeen suka ƙirasa suka sanar masa komai da Baban Zarah'n yace.
Yayi na'am da hakan shima, saboda yasan hakan al'khairi ne agaresu, domin shima bayaso ya ɗauko maganan aure batare daya fara aiki ba, so yake shima ya tsaya akan kafafunsa, kaman yanda Hammansa ya jajirce wajen samarwa kansa dukiya ta halak, haka shima yake fata, bayason ya dogara da kowa da kansa yakeson tsayawa akan ƙafafunsa, duk da yasan cewa shiɗin me gata ne gaba da baya, amma hakan bazai sa ya kashe zuciyarsa ba, amatsayinsa na Namiji dole ne agaresa ya nemi na kansa.

Alhamdulillahi yau tsawon sati guda kenan da nemawa Hayatuddeen izinin fara zuwa zance gidansu zarah, kuma ayaune jumma'a yakeson zuwa gidan su Zarah'n. Yau gaba ɗaya abokan nasa suna nan cike agidan su, anan falon Ummi suka baje sai ciye ciye suke, sun girma amma sam wani lokaci halin nasu na yarinta na nan, yanzu ma Zaleeha ne tayi musu farfesun kaji suke ci, sai zuba santi suke, wasu daga cikinsu kuwa tsokanan Hayatudeen suke, acewarsu waidan zai fara zuwa zance yau shiyasa gaba ɗaya yakasa koda zamane, abinci ma ya kasa ci na kirki.
Khamis ne ya dubesa, cikin salon tsokana yace. "Hayatuddeen ango." Murmushi Hayatuddeen ɗin yayi tare da cewa. "Maganarka haka take soon insha Allah". Dariya sukayi dukansu, Imran ne yace.
"Nima dai Insha Allah zan biyo bayanka Hayatuddeen, dan wallahi nima inason aure".
Khamis ne yace.
"Kuji Imran fa, to waye bayason aure? ai kasha kuruminka wata ƙila ma ni na riga Hayatuddeen aure, dan dama ni suke jira".
Dariya sukayi dukansu, Zakariyya dake tauna tsokan kaza abakinsa ne yace.
"Dukan ku kallon ku nake dan duk saina rigaku aure, nima ba zama zanyi ba, dole zan faɗawa Baba Malam cewa aje anemamin aure". Dariya Hayatuddeen yayi tare da cewa.
"Lalle ma guys ɗinnan wato duk kishi kuke dani, dan kawai kunji anbani babe shikenan sai kuka tashi hankalinku, kai Zakariyya kana maganan aure bayan ko budurwa baka dashi." Murmushi Zakariyya yayi tare da shafa tarin sumar kanshi, cikin jin kai yace. "Kuna wasa dani guys ɗinnan, tun yaushe kuma

Please Login or Register in order to submit comment