Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙaramin kyau ya ƙara ba, yayi fresh har ɗan ƙiba yayi, da'alama babu wani abun dake damunshi ga tarin farin cikin ganinsa a tsaye ji take kamar ta ture Adda Rahma ta gurbinta a jikinshi.
Zaleeha ce wanda shigowarta falon kenan, cikin sakalci da tura baki tace.
"Wayyo Allah na, dana sani da ban amince maka akan maganan surprising ɗinnan ba, tun da dai gashi kai kaɗai kawai aketa kulawa nikam kamar ba a sanni ba an mance dani". Maganar da takeyi ne yasa gaba ɗaya hankalinsu ya dawo kanta.
Raleeyace ta rungume ta cikin farinciki tace. "Oyoyo my aunty, i miss you more".
Murmushi tayi itama ta rungume Raleeya, ahaka suka ƙaraso cikin falon, daga kan Ummi har zuwa Ameena saida duk ta bi ta rungumesu, sosai suka yaba da irin zallan kyawun da tayi, duk da cikinta ya ƙara girma, haka ma hips ɗinta sun sake cikowa, ta zama wata babbar mace, ta kara zama cikakkiya abun so ga ko wani namiji.
Anan falon suka zazzauna, suna ahaka kuwa su Ishaq da Mudassir da kuma Salisu dama su Wareesu suka ƙaraso domin lbrin isowarsu da Ahmad ya basu da workewanshi, baƙaramin murna suma sukayi da ganinsa ba, daɗi kam sunjisa alokacin da suka ga yana taka ƙafafunsa.
Hira sukayi sosai a falon Ummi da aminanshi sunyi farin ciki mai tarin yawa anan a take yake cewa Ishaq ya shirya nanda wata biyu shida Rashida zasu tafi India ganin likitan ido, nan duk akayi ta fatan Allah yasa shima a dace, daga nan suka cicci abin gwalamar da Ameena tai musu, sannan suka fito suka nufi cikin Garden ɗin dake bayan part ɗin Ummi dan su ɗan barshi ya gana da iyalansa saida suka fitan.

kafun shida Zaleeha kowa ya nufi sashinsa danyin wanka, ita part dinta ta wuce wanda Zahira da Ziyada da Raliya suka gyara matashi fes-fes.

Shi kuwa ƙiran Ameena yayi yace tazo ta haɗa masa ruwan wanka.

Suna shiga part ɗinsa ya jawota jikinsa ya rungumeta ƙam, anutse ya shiga kissing ɗinta tako ta ina, tare da ce mata.
"I miss You so much cingom ɗina".
biye masa tayi dan itama tayi missing ɗinsa sosai, wata uku cur batare dashi ba ji take kaman shekara uku ne, cikin tsananin jin daɗi tace.
"Miss You too ya Habibi". saida sukayi tsotse-tsotsen su sannan yayi wanka.

Afalon Ummi suka sake haɗuwa, nan cikin falon suka baje, anan sukayi ciye ciyensu.
Haka sukayi ta hira, sai da aka ƙira sallan magriba sannan kowa yaje yayi sallah.

Su Ishaq basu bar gidan ba sai bayan sallan Isha, haka suka dai sha hiransu, ƙarfe tara kuwa kowa ya nufi part ɗinsa, Zaleeha kam sanin cewa ba itace ke dashi ba yasa ta na kwanciya se bacci dan agajiye take jin kanta.

Shida Ameena kuwa nan cikin bedroom ɗinsa suka ƙule, cikin aminci da salama suka raya daren nasu, inda Saifuddeen ya dage ƙwarai wajen nuna mata yayi missing ɗinta, sosai ya jiyar da ita daɗin dayasa ta kuka, haka suka liƙewa juna har kusan ƙarfe 1 na dare. Saida suka gurji juna sosai kafun suka kwanta.
Washe gari kuwa Bappa Ali ne yazo ya duba Saifuddeen ɗin ya ji daɗin ganin Saifuddeen ɗin na tafiya ƙwarai, haka dai suka wuni yau ɗin cikin nishaɗi, mutane sai zuwa musu barka ake, ƴan uwa da abokan arziki su Alhaji Rabi'u dasu Baba Bellon da Alhaji Yawale da Alhaji Kabiru da dai duk manyan yan kasuwa da mutanen wajen aikinsu.
Ya Ameenu ma da Ziyada sun zo.
Hakama da daren Baba Malam da Mamy da Mama sun zo, Ya Ahmad kuwa kiranshi yayin waya ya mishi barka, Aunty Kubra ma tazo haka Rashida da Umman Ishaq hakama Jabeer da Hisham suma sunzo da matansu a daren.

Koda suka shga kuwa Saifuddeen da Ameena kamar zasu cinye juna. Adeel kuwa kam ya maƙalewa Zaleeha ranar tare suka kwana sabida Ameena tace mata yanzu baya tashi shan nonon dare.

Washe gari kan Zaleeha zata amshi miji tace a a ita kam ta yafe mishi yaje suyi sati ɗaya rak da Ameena ita zata raini cikinta ta huta da gurzan data sha a instanbul.

Randa ta cika satine.
Washe gari kuwa Zaleeha ta amshi girki, da dare haka suka shana ita da Saifuddeen dan hutun satin da suka samu duk sunyi mararin juna, sabida ita kanta soyayyar tana bukatar hutu bare kuma aurataiya.
Bayan dawowansu da kwana goma cib.
A ranar ne kuma ƙauran su Raleeya, babu yanda Zaleeha batayi da Ahmad ba akan ya bari sai bayan ta haihu sannan su ƙaura, murmushi yayi tare da cewa.
"Chab naƙi wayon, hakanan sai na bar matata kuta samin ita bauta ko yaushe tana kitchen kamar ƴar aikinku ita ba haihuwa ita ba karatuba ita ba hutun bautaba ita ba gidan mijiba ai abin ya mata yawa, gaskiya na gaji inason matata ta huta, hakanan kullum fa ita ke muku girki, amma dai namiki alƙawari idan kika haihu zamu zo muyi sati, tun da ai muna da ɗaki agidan nan".
Dariya duka falon sukayi, dan su kansu sunsan Raleeya na aikatuwa ƙwarai.

Bayan sun gama kimtsa komai ne, da yamma dukansu suka raka Raleeyan zuwa haɗaɗɗen gidansu da Ahmad ya ƙenƙesa musu, Ummi kaɗai suka bari agidan, dan har Saifuddeen saida ya raka ƴar ƙanwar tasa, sosai gidan nasu yayi kyau sashin su mai girman sai BQ da kuma Sashin Gogga Dada Baba. Wanda tuni an kwaso musu komai nasu, suma har Sule ya tafi ɗaukosu.

Anan sukayi diner sai dare suka dawo.
washegari kuma Ummi da ta raka Goggo Dada da mijinta tanayi misu tsiya wai sun zama amare.
Kana da yammacin ranar kuwa aka kawowa Ummi ƙanwarta me taimaka mata aiki gida, wanda take ƴar Baffan Ummin dake gari Hashidu ƴar iya Bukku, to kasan cewar iya bukkun ta rasu yanzu zumunci sukeyi sosa, kasancewar tana da matsalan jinnu shiyasa har yanzu batayi aure ba, tana da hankali kuma ƙwarai, uwa uba tsabta, sannan ta iya girki, duk wani abu da bata gane ba kuwa Ummi take tambaya ta ganar da ita,
Kana dama Ummi da kanta ta sayi ɗan ƙaramin gida ta dawo da Baffa nata nan ta kuna bashi kuɗin aure ya auro wata tsohuwa mai kirki, daga nan suka dawo cikin gombe da Goggonta Goggo Abu da bata taɓa haihuwa nan ba.
Yaran baffa nata kuma maza duk suna can garin Hashidun, koda ta gayawa Saifuddeen abinda tai cewa yayi ai shima dama yanada niyar dawo dasu nan dan haka ya maida mata kuɗinta, ita kuma Ummi taƙi amsa tace a a tayiwa ƙanin mahaifin ta kyauta da arziƙinta.

Zaleeha kuwa yanzu cikinta yayi girman da yake basu mamaki, hakanne yasa duk suke tattalinta.
Yanzuma zaune take akan sofa inda ta mimmiƙe ƙafafunta, kanta kuwa na kan cinyar Saifuddeen dake zaune akan kujera, hannayensa duka na cikin gashin kanta yana shafawa. Ɗago kai tayi ta dubesa tare da cewa.
"Honey wai ya batun aikina ne, har yanzu bakace komai ba, gashi kuma har yanzu baka bani motata ba, saidai idan zan fita na karɓi motan aro".
Murmushi yayi tare da sauƙowa ya zauna akusa da ita, cikin kulawa yace. "Motocinki duka biyu sunanan idan bakya sonsu ma sai nasanja miki wasu, naga motar Ummu Adeel ma taɗan tsufa inason sanja mata sabuwa, idan na tashi zan sanja muku tare, wace iri kikeso?."
Ɗan fari da idanunta tayi, cikin salon tsokana tace. "Range rover nakeso". Dariya yayi tare da cewa. "Kinaganin bazan iya saya miki ita bane?." Kai ta girgiza tare da cewa.
"Ba haka nake nufi ba, ai nasan kaiɗin babban mutum ne".
Kansa ya jinjina tare da cewa.
"Inma zugani kikesonyi to na ɗauka, saboda haka kushiryawa ganin sabbin Range Rover, maganan aikin ki kuma ki bari sai kin haihu kafun nan ƴaƴan mu sun ɗan ƙara ƙwari, sai ki koma kinji ko." Cikin jin daɗi ta rungumesa tare da manna masa kiss agoshinsa, cike da farinciki tace.
"Thank you Mijina ɗan al'janna".
Dariya yayi sannan suka ci gaba da hiransu.


Bayan dawowansu da wata biyune kuwa Ishaq da Imran da Rashida suka tafi India dan ganin likitan ido.

Kwanci tashi ba wuya rayuwa tayiwa familyn daɗi sosai, inda yanzu cikin Zaleeha ya cika wata takwas da sati biyu, sosai cikin ya ƙara girma, zama da ƙyar tashi da ƙyar, ƙafafunta kuwa sun kumbura sosai, hakanne ma yasa kusan kullum asashin Ummi take wuni, dan Ummi ce dakanta keyi mata komai, kasancewar yanzu Saifuddeen ya tsaya akan aikinsa sosai, kullum da safe sai ya fita office, idan yazo dawowa kuwa saiya cikowa Zaleehan leda dakayan ciye ciye, dangin fruits da kuma chocolates.

Anan hakanne ya biya musu zuwa umra, duka gidan baki ɗaya, harta Ahmad da Raleeya ya biya musu, haka ma Hayatuddeen da Zakariyya, sai su Sameenu da Raihana da kuma Wareesu Wasilanshi harma da Saleesu, Safiya shi sannan Mudassir da Muminai shi, sai Adda Rahma da Ya Adnan ɗin shi.
Kana can gefensu Zaleeha kuwa Ya Ahmad ya biya Mamy da kuwa Ziyada da Habu, haka yasa Ya Ameenu yace to shima zaije baza'a barshi shi ɗaya a gidaba.
duka abokansa babu wanda be biyawa ba, har ma Baba Bello da Iyya saida ya biya musu dasu Goggo dada.
yaso suje tare dasu Ishaq sai-dai zuwa lokacin shida Rashidan sa sunyi sati biyuma da tafiyarsu India, sai kuma Ameena wanda itama bazata samu zuwa ba, kasancewar awajen aikinta ba abata dama ba, sannan kuma babba ma dalilin idan suka tafi dukansu zai zamana gidan nasu ba kowa, hakanne yasa tace ta haƙura wani zuwan Insha Allah sai aje da ita. A ranta kuma tafi son taje daga ita sai mijinta.

Haka dai ranan wata jumma'a jirginsu ya ɗaga zuwa sararin samaniya.

Basu sauƙa ako ina ba kuwa sai a ƙasa me tsarki.
Suna zuwa kuwa suka fara gudanar da ibada, sosai suka nutsu sukayi ibadansu me kyau yayinda gaba ɗayansu Saifuddeen keta binsu da roƙon susa mishi Zaleeha a addu'o'in su , Allah ya sauƙeta lfy, haka kuwa akayi gaba ɗaya su suna sata a addu'o'insu.

Aranan da suka cika kwana goma da zuwa ne, Da sanyin safiya naƙuda ya tashi wa Zaleeha, abu kaman wasa sai gashi ya kan kama, domin sosai bayanta ya riƙe, tun tana daurewa tana cijewa ita ɗaya har dai ta gaza, kasan cewar masauƙinsu a jere-a jere yake,
cikin dauriya ta nufi inda Ummi da Mamy suke,
tana shiga da tasu mamy na sa kaya, Ummi kuwa tana bathroom tana wonka da alamun zasu tafi haramine.
Mamy na ganinta da yadda take tafiya tace.
"Zaleeha lafiya kuwa?".
Da sauri Mamy tayi kanta ganin yadda take ɗaga ƙafarta da ker sabida sauƙowa daga sama da tayi ya tunzuro naƙudar,
cikin rawan murya tace.
"Mamy marata bayana ƙuguna".
Cikin kaɗuwa Mamy tace.
"Hasbunallahiwani'imanwakil kodai haihuwace?".
Dai-dai lokacin kuwa Ummi ta fito cikin kaɗuwa tayi kansu,
ganin yadda gaba ɗaya taketa tsastsafo zufa ne yasa Ummi cewa.
"Haihuwane Mamyn Ahmad kira mana yaran mazan".
Sai ta kuma kamo hannu da Zaleeha ta soma yarfa hannuwanta, da cije baki, ganin hakane yasa hankalin su Ummi tashi.
Cikin gigita Ummi ta lalubi wayarta ta kira Saifuddeen wanda shi kuma lokacin suke dawowa daga harami shida Dr Adnan da kuma Salisu.
ganin sun isone yasa bai ɗaga kiran Ummi ba kawai ya nufi ɗakinsu.
Da sauri ya ƙaraso cikin ɗakin a kuɗine yace.
"Ummi meya sameta, Zaleeha meke miki ciwo?".
Da sauri Mamy ta ɗan matsa fahimtar itace ta hanashi ƙarasowa,
ai kuwa tana matsawa ya tallabo Zaleeha,
Ummi kuwa hijabi tasa bayan tasa riga cikin fargaba tace.
"Haihuwane Saifuddeen mu tafi asibiti".
Saifuddeen da kansa ya ɗagata caɗak nufi hanyar fita Ummi da Mamy na biye dashi.
Suna fitowa Ya Adnan na saukowa ganin halin da suke ciki yasa maza ya koma ɗakinsu takardun awun Zaleeha na Instanbul dana Nigeria ya kwaso wanda a hasashen duk sukaga wai yara biyune a cikin Zaleeha amman ɗayan kawunanshi biyu,
wannan dalilin ne ya tashi hankali Saifuddeen shiyasa ya biya musu Umrah baki ɗaya dan su tayashi addu'o'in samun waraka a lamarin, haka yasa daga nan F.M.C Gombe sukayi musu takardar transfer zuwa nan asibitin saudia,
Suna fitowa suka samu Samisu ya dawo, so a motar daya dawo suka tsaida.
Bayan ya sata amota, ummi ne ta rufa musu baya sai kuma su Mamy da Raleeya.
Suna kaita asibiti kuwa Doctors suka karɓeta da gaggawa ganin abinda ke kan takardunta, da sauri aka wuce da ita labour room.
Gaba ɗaya Saifuddeen rikicewa yayi, dan ya kasa control ɗin kansa, addu'a kawai yaketa yiwa Zaleehan, dan dagani tanajin wahala, sosai yakejin tausayinta bare in ya tuno zancen likitoci, in kuma ya tuna mafarkin da yayi sai yaji sanyi kaɗan a ranshi.
Haka su Ummi sukayi jigum jigum dan gaba ɗaya acikin tashin hankali suke Ya Ahmad da ya Ameenu ma da Aunty Lubna da Ziyada sun taho Zakariyya da Hayatuddeen kuwa suna can cikin gari.
Acan cikin labour room kuwa duk yanda Zaleeha ke tunanin ciwon na ƙuda ashe ya wuce tunaninta, sosai tasha wahala, gaba ɗaya jikinta ya jiƙe da gumi, addu'a take yi tare da ambaton sunan Allah.
Ta gigice sosai,
haka yasa cikin rauni tacewa ya Adnan da yake cikin doctors ɗin cewa dan Allah a kira mata Hamma Saif.
To al'barkacin Ya Adnan yasa aka barshi.
Yana shigowa ya matso gabanta cikin rawan murya dake baiyana tsantsar azabar da takeji tace.
"Hamma Saifuddeen zan mutu ka yafe min duk wani abinda nai maka na zahiri da baɗiri".
Da sauri ya ɗan sunkuyo kanta da nufin zai kissing goshinsa,
ɗai-dai lokacin kuwa yaro ya kawo kai nishi mai ƙarfi ya taho mata.
Ruggumeshi tayi gam a jikinta da ƙarfi ta saki nishe.
Cikin ƙarfin ikon Allah kuwa, ta kuma ƙara danna wani irin nishi hakanne yasa likitoti suka taimaka mata wajen zaro mata yaronta na miji, ajiyan zuciya ta sauke mai nauy,
shi kuwa Hamma Saif jin kukan jaririne da kabbarar da likitocin keyi yasashi.
Yin wani mashahurin murmushi tare da ƙoƙarin tasowa,
Ido ya zaro da ƙarfi jin wani irin ruggumeshi data kuma ruggumar da saida yaji numfashin shi zai ɗauke,
cikin sanyi murya can ƙasa yace.
"Wayyo ya Adnan ta shaƙeni".
ita kuwa Zaleeha nishi takeyi a jere a jere sabida kan yaro da ya sako kai.
wani yunƙurin tasakeyi sai kuma ga wani yaron ya sake faso kai, da sauri suka amshi ɗan.
Kabbararin da sukayi a wannan karon yafi na forko domin wannan alamace ta hasashen likitocin baiyi dai-dai ba.
A take aka yanke cibiyoyin yaran akazo da nufin za'a ɗaura mata su kan cikinta,
da sauri babban doctor ya hana tare da ce musu.ai da sauran wani a cikinta dan ga cikin yana motsawa,
tashin hankalin su kuwa yadda jini ya ɓalle mata,
madadin zafin naƙuda sai ta fara lumshe ido alamun bacci zatayi,
cikin tsoro Dr Sulaimi dake gefenta ta fara bubbuga kumatunta da ƙarfi alamun ta farka karta rufe ido.
Amman ina,
Dr Adnan kam sosai ya gigice.
Saifuddeen kuwa sai numfarfashi yake fidda jin ta sakeshi,
da sauri Babban Dr ya kalli Saifuddeen yace ya rinƙa kiranta.
A kiɗime Hamma Saif ya sunkuyo kanta tare da fara mgn da ɗan ƙarfi kamar yadda likitocin suka umarceshi.
"Zaleeha tashi buɗe idonki tashi kiga yaranmu, Zaleeha ki bude idonki".
A hankali ta fara buɗe idanun nata sabida, muryarshi da take jiyowa.
da sauri Ya Adnan yace.
"Kiyi nishi kiyi nishi da ƙarfi".
Ina bazata iyaba ga alamun Baby kuma ta sako kai,
dole Dr Sulaimi ne tazo tasa hannu da dabarun su na likitoci ta fara nemo kan yaron ita kuwa Zaleeha jin murya Hamma Saif na ce mata tayi nishine yasa ta ɗan rufe idonta, yunƙuri ta sakeyi da ƙarfi aiko da sauri suka sake zaro mata kyakkyawar ƴarta mace, amatuƙar wahalce take sakin ajiyar zuciya me ƙarfi,
cikin farinciki doctors ɗin suka kimtsa yaran sannan itama suka gyarata tsab, take suka mata alluran bacci dan tana buƙatar nutsuwa sosai.
Ganin tayi bacci yasa suka kwaso yaran suka fito dasu, rige rigen amsan yaran akayi tsakanin Ummi da kuma Mamy da Raliya dasu Ahmad, cike da matsanancin mamaki suke kallon kyawawan jariran yara uku reras Saifuddeen kuwa yama kasa magana sai kukan farin ciki da yakeyi yana ruggume da ƴarshi macen.
Ummi da Mamy kuwa suka amshi mazan masu matuƙar kyau,
cikin mamaki Ummi ta dubi nurse din, amamakance tace. "Nurse duka waƴannan kyawawan ƴaƴan yanzu Zaleeha ce ta haifesu." Kai nurse din ta jinjina alaman.
"Eh." Kabbara sukayi dukansu, yayinda Saifuddeen ya miƙawa Adda Rahma ya macen kana ya durƙusa yayiwa Allah sujjada, cikin matsanacin farinciki Ummi ta shafa fuskokin su, abayyane tace. "Alhamdulillah Allah abun godiya".
Saifuddeen ne ya bukaci daya ga Zaleehan sai-dai doctors ɗin basu bashi daman hakan ba, sunce ya bari saita farka ya Adnan kuwa daya fito dariya yayi taiwa Saifuddeen yana cewa.
"Baban yara kasha shaƙafa,
ai in mace na naƙuda kada ka yarda kana mijinta ta kiraka ka motso domin babu shakka zata shaƙeka".
Ahmad da Salisu da Mudassir da Warisu kam dariyar ƙeta suka saka.
Raihana kuwa da Iya da Baba Bellon suna harami.
Ya Ahmad ne ya matso jikin Mamy ya amshi yaron dake hannun nata,
Ya Ameenu kuwa ƴa macen ya amsa masha Allah.
Ahmad kuwa mijin Raliya ɗan dake hannun Ummin ya amsa.
Haka dai suka dinga kiran ƴan uwa suna faɗa musu, Baba Malam da Mama, ba ƙaramin farinciki sukayi ba dajin hakan.
Haka dai suka wuni a cikin asibitin, koda Zaleeha ta farka, sosai taji daɗi, saidai tasha mamakin ganin cewa wai itace ta haifi ƴan uku, sosai tayiwa Allah godiya,
Sai daren aka basu daman shiga inda take.
take kuwa suka shiga tarairayanta kaman ɗanyen kwai, ko awajen bawa yaran nono saida akasha fama da ita sosai saida taga Hamma Saif ɗinta ya ɓata rai sannan tace.
"To zan basu amman sai anjima".
Cikin fahimtar kunya takeji yasa gaba ɗaya suka fita.
Shi kuwa Saifuddeen a hankali ya matsota da kyau tare da cewa.
"Ki fara baya Mamana kinga itace karama kuma itace mace tanada rauni".
Cikin tura baki da alamun gaji tace.
"To bakaji iya tace ai wai sai an wonke bakin nonon".
Baki ya ɗan taɓe tare da cewa.
"Rabu da iya ita tana zaton ma'auranta yanzu irin na zamanin dane, da bata san nononmu fes yake,
abinda kullum sai nasha abuna na more wani datti zaiyi? Ba datti ko kaɗan kuma dama nayiwa yarana tanadɗin nipples sun fito ras".
Ya ƙarishe mgnar yana ɗaura mata yarinyar a kan cinyarta.
a hankali yasa hannunshin cikin rigarta ya kamo nonon, a hankali tace.
"Wash Hamma Saif, in na basu suna shan bazanji komai bako?".
Dariya yayi tare da cewa.
"Ke tafi daga nan, waɗannan yaranki ne na cikinki ko sau dubu sabanin zasu tsotsi nononki bazakiji komai,
sai dai in nine na tsotsesu nanne kwaɗayinki zaisa kiji kinata yoyo ki jiƙe kiyi ta min ihu".
murmushi tayi tare da kauda kanta cikin jin kunya.
Sunkuyowa tayi ta kalli yaran a take taji sonsu na ratsata,
a hankali ta sunkuyo ta sawa macen nononta,
da sauri ta rufe idonta domin kamawa da ƴar tayi zafi taji,
shi kuwa Hamma Saif ɗaya yaron ya ajiye meta a gefen cinyarta tare da bashi nono ɗayan.
Da sauri ta kalleshi tare da cewa.
"Hamma Saif yaran ƙanana basuyi ƙatti ba".
Kanta ya shafa tare da cewa.
"Zasuyi ƙatti in sha Allah shiyasa nake son ki fara shayar dasu tun yanzu".
Kai ta gyaɗa kana cikin alamun yanayin raunin masu jego tace.
"Hamma Saif tun safe basuci komaiba ne?".
Kai ya jujjuya mata kana ya ɗauki ɗayan ya ruggumeshi tare da cewa.
"A a tun da safe na basu ruwan dabino sunsha sunyi nak sannan sunsha zam-zam shisa sukayi ta baccinsu".
Kai ta gyaɗa tana mai jin wani irin daɗi a hankali tace.
"Honey ita wannan dani take kama, shi kuma wannan da kai take kama, na hannun ka kuma to da waye yake kama".
Murmushi jin daɗi yayi tare da cewa.
"Shi wannan da Autan Ummi yake kama wlh sak Hayatuddeen".
Da sauri tace.
Hayatuddeen yaga babies ɗinsu dan yasan kafin su dawo suma ɗin sun dawo.

Washegarin kuma abokan Saifuddeen suka nuna matsa zallan bajinta, inda kowannensu ya sayawa yaran kayayyaki masu kyau da tsada.
Haka rayuwarsu tayi musu dadi sosai, inda Zaleeha ta koma kamar da ɗinta, idan kaganta bazakace itace ta haihu ba, dan jikinta fresh, sannan cikinta ya zama flat, sai wani shinning take.
Ranan da yara suka cika kwana bakwai, Saifuddeen ya raɗawa kowannensu suna Babban shiyaci sunan Abba Muhammad kenan, za'ana ƙiransa da sunan (Khareem) sai me bimasa wanda aka sa masa Sunan Nurudeen, shikuma za'ana ƙiransa da (Khasim) itakuwa baby girl sunan Ummi aka sa mata wato Fateema, inda za ana ƙiranta da (Khausar) Ummi taji daɗin hakan sosai, aranan kuwa wani irin gagarumin walima suka haɗa, Raguna uku da suka yanka, haka suka kwaso masu aiki suka babbake musu naman, diner sukayi me rai da lafiya, inda Zaleeha tasha kwalliya sosai kaman wata sarauniya, duk inda ta gilma, Idanun Saifuddeen na kanta, daya kalleta kuwa zai kalli ƴarta Fateema wato Khausar, wanda take matsanancin kama da ita, komai na Zaleeha yarinyar tana dashi, sauran maza biyun kuwa Dukansu da Saifuddeen suke kama kaman antsaga kara, saidai Khareem ne idan ka zuba masa idanu sosai zaka ga yana shige da Hayatuddeen, hakanne yasa Hayatuddeen da Zakariyya bakinsu ƙin rufuwa, sosai sukeson yaran, hakan yasa kullum cikin ɗaukan hoto da yaran suke. Yau ya rage saura kwana uku su koma Nigeria, Bayan sun gama dinner ne Raleeya ta kalli Hamman nata, cikin kulawa tace.
"Yauwa Hamma dan Allah inason roƙonka wani abu."
Murmushi yayi tare da cewa.
"Inajinki Raleeya ki roƙeni kome kikeso aduniya matuƙar ina dashi zan baki Insha Allah." Idanunta ne suka ɗan kawo ƙwalla, cikin rau rau da ido murya na rawa tace.
"Dama ko Hamma Saifudddeen Aunty Zaleeha ce ta min al'khairi wai in ta haihu zata bani ɗan, to kuma gashi Allah yasa har uku muka samu,
Dan Allah Hamma kabani ɗaya daga cikin yarankan nan kaji, ka ga ni har yanzu Allah baibani haihuwa ba, kuma ina matuƙar son yaran". Idanunsa ya zuba mata, take yaji wani irin matsanancin tausayin ƙanwar tasa ya rufesa, tasowa daga inda yake yayi, tare da ƙarasowa ya zauna akusa da ita, hannunta ya kamo cikin kulawa yace.
"Kin wuce haka awajena Raleeya, komai nawa nakune, komai na mallaka aduniya, naku ne, bazan taɓa iya hanaku abun da kikeso ba, ke ƙanwatace ta jini wanda nake matuƙar so, saidai kuma kiyi haƙuri bazan iya baki Khausar ba, saboda kinsan tundaga kanki ba a sake haifa mana mace a familyn mu ba, ganan Zaleeha itace mahaifiyar yaran, nasan bazata taɓa hanaki ɗanta ba, nasan zata amince saboda haka nabaki dama daga kan Adeel, Kareem, Kasim, ki zaɓi duk wanda kikeso acikinsu na bakishi halak malak." Wani irin matsanancin farinciki ne ya rufe gaba ɗaya zuciyoyinsu, hakan yasa Raleeya

Please Login or Register in order to submit comment