Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta fita tana kuka".

Dafe kirji Zarah tai idonta kamar zai fito waje da matukar mamaki tace "ta auri yaya"?.

"Eh Zarah ni kaina haka ya mun lokacin da daddyn ku ya fad'a min kuma na bada goyon baya d'ari ๐Ÿ’ฏ bisa d'ari ๐Ÿ’ฏ".

Shiru Zarah tai umma ta cigaba "naga kinyi wani iri ko bakya son hakan"?.

"A'a umma ba niba ya Haidar nake ji yasan da maganar"?.

"Ya sani tun jiya".

"Kuma ya amince".

"Ai Zarah ko bai amince ba ba yadda zaiyi ba shine da kansa ba kuma mun isa dashi".

"Dama nasan bazai amince ba yadda yake jin kansa gani zai ya wuce ajinta ya Haidar yana da fad'in rai".

"Yana da fad'in rai ko yana da sakarci farko da aka bashi za'bi Badi'ah ya za'ba".

"Badi'ah kuma๐Ÿ˜ฒ?.

"Eh ita din".

Ta'be baki Zarah tai tana cewa "tabdijam Badi'ah kenan yanzu su biyun zai aura"?.

"A'a iya Husnah Daddyn ku yace".

Tsalle Zarah tai cikin jin dadi tace "wayyo Allah umma kice zamu sha biki mu gwangwaje ๐Ÿ’ƒ".

"To kiyi a hankali kinsan ba so yake ba kar ya shigo ya kama ki ba ruwa na".

Dariya Zarah tai tana zama tace "Allah umma abun ne ya bani shau'ki Allah ya kaimu ranar da alkhairi sister zata dawo kusa dani"..............

Shigowar Haidar yasa tai shiru tana kallon yadda fuskar sa take a hade tana dariya kasa kasa tace.

"Ya Haidar dama tun safe nake neman ka ban ganka ba ina kaje ne"?.

"Ban sani ba".

A fakaice Zarah tai masa gwalo๐Ÿ˜œ tana marairaice murya tace.

"Kai yaya yau kuma me na maka"?.

Hararar data samu ne yasa ta rufe baki๐Ÿค tana cewa "sorry yaya bafa wani abu nake nufi ba".

Bai kula taba yai gaba dariya ta sake shekewa da ita tana kallon kofar part dinsa tace.

"Ji dan Allah me zazzabi dabam mai shan magani dabam ni harna fara tausayin sister na ma anya zata ji dad'in sa kuwa"?.

Mikewa umma tai tana cewa "wannan kuma ke kika sani bana son sa ido".

Umma na barin gurin Zarah d'aram ta mike da saurin ta ta shiga part din Haidar tsokana๐Ÿคญ.

Nikam baya nayo idan rabon zata sha na jaki ne๐Ÿ™‰.


Satin Husnah biyu bata zuwa hospital bata zuwa aiki tana gida kuma ko da wasa bata fadawa su baba komai ba dan bata mayar da abun seriously ba.

Kawai tayo sarin kayan kwalliya da takalma ta fara saidawa kuma ba laifi tana da kasuwa ganin da shago a jikin gidan hayar nasu yasa ta saro abubuwa da yawa da albashin ta na aikin da na hospital ta soma juyawa.

Ganin abun ya zarce har wata guda kuma gashi Husnah tai shiru sai kasuwancin ta datasa a gaba bata zancen komawa aiki yasa baba yai mata magana.

"Asma'u meyasa kika daina zuwa aiki ne kullum kina gida"?.

"Babu komai baba kawai na dau hutu ne".

"Amma ya kamata ki koma hutun ya isa haka".

"To baba insha Allahu zan koma".

"Yauwa Asma'u ko kefa haka nake son ji Allah ya miki albarka".

"Amin baba" ta fada gaban ta na faduwa zuciyar ta na bugawa da karfi tuna ya zatai in taje hospital ranar Monday.

Da yake asabar ce washe gari lahadi haka Husnah ta shirya ta wuce gidan su umma tana shiga harabar gidan suka had'a ido da Haidar yana tsaye jikin motarsa wani irin ba'kin kallo ya aiko mata wanda saida taji dama bata zo gidan ba.

'Dauke kai tayi tana shige shi ta shiga palon jikin ta a sanyaye tsaki yaja cikin bacin rai da takaici ya shiga motarsa yabar gidan.

Kamar zai bige mai gadin daya bude masa kofa da sauri ya kauce yai tsalle yana fad'awa cikin fulawoyi๐Ÿ™Š.

Saida ya fita sannan mai gadin ya fito yana kad'e jikinsa daya 'baci kafin ya rufe gate din yana shiga d'aki.

Daddy na tsaye ta saman beni yana kallon sa duk abinda yake tun kafin shigowar Husnah kai ya jinjina baiyi magana ba.

Hade rai Zarah tai tana kallon Husnah tace "gaskiya sister banji dad'i ba dan kawai ance ki auri ya Haidar shine kika dauke kafar ki da zuwa gidan nan wata guda? Look kinga idan har bakya so zanje na samu Daddy na masa bayani amma dan Allah ki rika zuwa kamar da".

Murmushin dole Husnah tai tana cewa "waye ya fada miki saboda haka na daina zuwa? ko daya banjin dad'i ne shiyasa".

"Oh ayya sorry sister ashe baki ji dad'i ba ai ban sani ba da tuni nazo dubiya".

Fitowar umma ta kalle su duk su biyun tana cewa "Husnah sannu da 'kaurace mana Daddyn Zarah na neman ki".

'Kamewa Husnah tai guri daya lokaci guda ta daina gane yanayin da take ciki jijiyoyin jikinta suka daina aiki zuciyar na harbawa da karfi ta kasa cewa komai sai.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un kadai take iya maimaitawa".

"Muje na raka ki sister" Zarah ta fad'a tana jan hannunta suka shiga part din Daddy da sallama bayan sun gaida shi Husnah ta zauna Zarah ta fito.


"Husnah kiyi hakuri da abinda ya faru nayi miki miji ba tare da neman yardar kiba amma ina da kyakkyawan zato akan ki cewa ke mai biyayya ce kuma zaki amince min fatan kinji komai daga gurin Aisha"?.

"Eh Daddy ta fad'a min".

"Amma kin amince kin yarda zaki aure shi ki zauna dashi iya rai da mutuwa domin kece kika dace da shi".

Shiru Husnah tai Daddy ya dora "bazan takura miki ba idan har kinga ba hali ki sanar dani zan fahimce ki fiye da yadda kike zato kuma haka bazai ta'ba martabar aikin kiba.

Sunkuyar dakai Husnah tai muryarta a sanyaye hawaye fal idonta dan bazata iya yiwa Daddyn musu ba shiba 'kashin yarwa bane tace.

"Na amince Daddy Allah yasa hakan shine mafificin alkhairi".

"Amin na gode miki sannan ina so ki fad'a min kwatancen gidan ku domin nazo gurin mahaifan ki"?.

Gaban tane yai mummunar faduwa ta kasa magana sai rawa da jikinta keyi lokaci guda ta shiga rud'u da tashin hankali mara musaltuwa.

Shi kanshi Daddy ya fahimci hakan amma bazai fasa ba bazai yanje ba yana son raba Haidar dajin shi wani ne da fad'in rai da girman kan da yake dashi babu kuma maganin haka sai Husnah yana so Haidar ya gane talaka ba abin wulakantawa bane ba abin a tozarta bane shima bawa ne na Allah kuma badan baya son shi ya yo shi a cikin talauci ba haka badan yana son mai kud'i ya bashi dukiya da jin dad'i ba saidan ya jarraba kowanne daga cikin su.

"Tashi kije Husnah saiki fad'awa Aisha address din naku ta fad'a min".

Mikewa Husnah tai dakyar saboda har lokacin jikinta bai daina rawa ba ta fita.

Kiran umma Daddy yai a waya yana cewa "Aisha bata fad'a min ba ki tambaye ta".

"Ok shikenan" umma na sauke waya Husnah ta fito tare da 'ka'kalo murmushi tace.

"Umma zan koma".

Kai umma ta jinjina "to Husnah baki fad'a min inda gidan naku yake ba ya sunan anguwar"?.

Hawaye na neman zubowa Husnah tace "umma zan fad'a muku idan na dawo next week".

Murmushi umma tai dan ta gano manufarta tace "ok ki gaida gida Allah ya kaimu next week din duk daya ne".


Kasa cewa komai Husnah tai kawai ta juya da sauri ta fice a ranta kuwa ta yanke alakar ta da gidan bazata sake zuwa ba har abada ta hakura da shakuwar dake tsakanin su.

Da gudu Zarah ta mike tana dauko gyalen ta tace "Umma bari nabi bayan ta naga inda zataje".

"Ok Zarah".

Fita Zarah tai da hanzari ganin bata ganta ba yasa ta sake d'aga kafa tana barin layin su ta hango ta ta kusa isa bakin titi da gudu gudu ta karasa daidai Husnah ta shiga adaidaita.

Itama Zarah ta tare wani tana shiga tace "duk inda wancar napen din tayi ka bita".

Tafiya suke har suka shigo anguwar da mamaki Zarah a ranta tace ai nan gidajen Daddy ne wanda ya barwa ya Haidar dama anan sister take".

Ganin Husnah ta sauko yasa Zarah dakatar da me adaidaitar ta tace.

"Tsaya daga nan".

bashi kud'in sa Husnah tai tana shiga gida murmushi zarah tai tana cewa mai sahun ta.

"Mayar dani inda ka dauko ni saina baka kudin ka".

Cikin 'kwa'kwa d'an sahun yace "hajiya amma baki komai kawai jin dadi yasa kizo ki koma"?.

"Eh aiki nai".

"Wanne kalar aiki ne wannan"?.

"Meye damuwar ka akai"?.

"Hajiya nike da damuwa tunda ni na rako ki".

"Dan ka rako ni saiya zama dole saika san komai"?.

"Eh man hajiya ban na sha".

Banza Zarah tai masa ya sake cewa "ko 'yar sanda ce kedin ita kuma mai lefi ce aka aiko ki leken sirri"?.

"Eh laifi tai".

"Wanne irin laifi ne wannan ta aikata dan mu guje shi hajiya"?.


Ganin zai dame ta tace "bai shafe kaba are you a journalist"?.

Dariya yai "a'a ni ba d'an jarida bane dana samu wannan gatan yaushe zaki ganni a adaidaita ina yawo a rana".

Har kofar gida tasa ya kaita ta shiga ta dauko masa kudinsa domin tana sauri ko sisi bata dauka ba ta fita.

Da gudun ta taje gurin umma tare da rungume ta tace "wayyo Allah umma albishirin ki ashe ma a gidan hayar Daddy wanda ya barwa ya Haidar suke".

Kallonta umma tai "da gaske Zarah"?.

"Wallahi umma har can na bita amma ban bari ta ganni ba".

"To alhamdulillah sai kije kiwa Daddyn ki albishir".

Da murnar ta tace "Nasan zan samu kyauta mai tsoka kila ma ya sauya min mota" ta fad'a tana fita zuwa part din Daddy da farin cikin ta.


Washe gari Husnah na baccin safe bayan tayiwa su baba abun breakfast ta koma d'aki batasan wainar da ake toyawa ba harsu Daddy suka zo.

Gaisuwar mutunci da tarba mai kyau suka samu daga gun su baba saidai sun cika da mamakin meya kawo su saida Daddy ya musu bayani sannan baba yai magana.

"To alhamdulillahi mun gode sosai da karamcin ku da martabawar ku gare mu saidai maganar gaskiya Aliyu yafi karfin auren Asma'u babu abinda zance muku saidai kuyi hakuri badan muna 'kin ku kauna ce tasa muka fad'a muku haka".

"To amma baba meyasa kace Haidar yafi karfin auren ta bayan shima mutum ne kamar ta".

Kai tsaye baba yace "Asma'u 'yar talakawa ce kuma nakasassu shi kuma d'an mai kud'i kuma kasan kowacce 'kwarya da abokiyar rufin ta".

"Eh baba haka wasu suke dauka amma idan ana batun mutane bata 'kwarya ake ba babu wanda yafi wani a gurin Allah sai wanda yafi jin tsoron sa ni na rike ka tamkar uba gare ni kuma ina da yakinin zaka share min kuka na kai mahaifi ne gare ni dan Allah baba ka amince min ka bawa Aliyu auren Husnah".

Jikin baba ne yai sanyi yana ganin girman Daddy bazai iya hana d'an sa auren Husnah ba idan yai haka yayi butulci duba da duba da halaccin da Daddy ya musu.

Kai ya kad'a yana cewa "shikenan Yusuf na amince Allah ya sanya albarka a cikin auren yasa haka ne mafi alkairi".

"Amin baba mun gode" suka fad'a cikin jin dad'i sosai sannan sukaiwa Innah ma godiya umma kuwa a take ta turawa Zarah text cewa.

"Kiyi farin ciki Zarah munyi nasara๐Ÿ‘" wani tsallen murna Zarah tai lokacin da message din ya shiga harda rawar ta.

Tashin Husnah kenan daga bacci jin surutu yasa ta d'aga labule zata fito idonta ne ya sauka a fuskar Daddy kamar a mafarki ga wani kusa dashi da bata sanshi ba ga umma itama da wata kusa da ita bata ta'ba ganinta ba.

Da sauri ta saki labulen tana komawa baya zuciyar ta na fat fat fat kamar ta fito waje dan firgici jin zancen da suke da abinda baban yace yasa wata ba'kar hajijiya ta debe ta sai jinta tai sharaf ta fad'i a kasa batasan lokacin data fashe da kukan ba'kin ciki ba tana toshe bakin ta dan kada su jiyo.

Saida taji sunyi sallama sun tafi da tashin motar su sannan ta fito da kukan ta tana kallon damin kud'in gaisuwar dake gaban baba batasan ta sake fashewa da kuka ba ta durkusa gabansa tana cewa.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un baba meyasa kuka kar'ba meyasa ka yarda? bazan iya auren wannan saurayin ba bazan iya zama dashi ba".

Kai baba ya girgiza tare da sauke ajiyar zuciya yana cewa "kiyi hakuri Asma'u nasan ban nemi shawarar kiba amma a tunani na ni mahaifin kine bazan miki abinda zai cutar dake ba bazan goyi bayan ki wahala ba bazan iya musawa yaron nan Yusufu ba".

Jin ya daure ta da jijiyoyin jikinta yasa tace "nifa baba bana son rabuwa daku shine dalili na".

"Ai Asma'u rabuwa damu ya zama dole tunda ke 'ya mace ce ba kamar namiji ba dole ki tafi gidan wani abinda nake so dake indai dan ta wannan ne kisa ranki a inuwa babu komai".

Kukanta ne ya 'karu sosai ta mike tana barin gurin ta koma d'aki taci gaba dayi acan har saida ta dorawa kanta zazzabi.

Shigowar Habib kenan da shirinsa cikin manyan kaya ganin Haidar zaune yayi tagumi yasa cikin tsokana yace.

"A'a kaga ango yaufa ranar kace ya kamata kai farin ciki Koda na sakan daya ne๐Ÿ˜ maiya faru ne naga sai hade rai kake"?.

"Ban sani ba๐Ÿ˜ ".

"Kada Allah yasa ka sani d'an rainin hankali kawai tun dazu sai jiran ka muke ashe kai kana nan a zaune ko shiri bakai ba"?.

Banza yai masa Habib yaci gaba "wai meye haka Haidar ka tashi ka shirya mana lokaci fa yana kurewa".

"Naje ina"?

"Kan uba jimin d'an iska kaje ban sani ba daurin auren naka guda kake tambaya".

"Bazan jeba".

"Aiko saika je".

Ran Haidar a bace yace "saika ja ni ka kaini".

Zaro ido Habib yai "kaiii ni na isa daukar gardin saurayi kamar ka".

"A'a ka manta gardin tsoho zakace ba gardin saurayi ba".

Dariya Habib yai "kaga mubar duk wannan idan mun dawo maci gaba Daddy yace ka fito mu tafi".

"Malam karka dame ni".

"Haka kace"?.

"Eh na ce hakan ko zaka dau mataki"?.

Gira habib ya d'aga "zan dauka man".

"To bismillah".

Waya habib ya d'aga yana Kiran Daddy yace "Daddy wallahi Haidar bai shirya ba kuma na masa magana yace karna dameshi".

Daga can bangaren Daddy yace "aje wayar karka kashe ka sake yi masa magana ina ji".

"To Daddy" Habib yace yana kallon Haidar yace "Daddy yace ka tashi ka shirya mu fita yana jiran mu".

"Look Habib I don't want nonsense dan haka ka rabu dani".

"Daddy nefa ba wani ba Haidar".

Wata harara ya samu yana Jan tsaki yace "dalla malam ka rufe min baki munafiki kawai ka wani zuro min ido ya na tsohon kwarto ๐Ÿ˜‚".

Dariya ce ta kama habib Amma ya maze yasan Haidar ya shiga tension da yawa shiyasa yabar haka a matsayin so yake ya huce haushin sa a kanshi.

Suna zaune suka ji an budo kofa ganin Daddy ne ya shigo da wayar caza a hannunshi yasa Haidar ya mike da sauri yana tsallake kujera ya shiga bedroom.

Dalilin da Daddy a gurin ya hana Habib kwanciya kasan carpet yai dariya amma acting din Haidar ya bashi mamaki ashe duk iskancin shi yana tsoron Daddy dan yasan ba wasa a wurinsa har yanzu bai wuce ya zuge shiba.

Ko minti goma baiyi ba sai gashi ya fito cikin shiri kamar karamin yaro haka Daddy yaja hannunsa suka fita yayin da Habib yabi bayan su zuwa harabar gida inda motoci suke mutane a waje fal ana jira ba bata lokaci suka wuce.

Baba yasha manya kayan da d'an sandan sa a gefe yana zaune tare da wasu tsirarun mutane su Daddy suka iso.



Amm Habib dan Allah ko zakai min taimako wannan yarinyar ta'ki saurara ta Sam tunda naga kai tana ganin mutuncin ka kayi mata magana ka bata hakuri ta fahimce ni".


Mazewa Habib yai yana kallon sa yace "wacce yarinyar kake magana akai"?.

Numfashi Haidar ya sauke yana cewa "Husnah gabadaya ta caza min kwakwalwa ta rabu dani amma nasan kai zata saurare ka tunda tana ganin girman ka".

Zaro ido Habib yai kamar gaske yace "wa ni? rufa min asiri da kula matar wani so kake ace min kwarto haka kawai kake neman jefa ni cikin cakwalkwalin ku".

Cikin jin haushi Haidar yace "a ka manta uban kwarto za'a ce maka wai dan Allah Habib mai yasa kake min haka ne dan kawai na fad'a maka abinda ke damu na shine zakai min wulakanci"?.

"Ni asuwa na wulakanta Daddyn Ahmad guda kawai dai abinda ka fad'a ne bazan iya yi maka shiba".

"To me yasa Habib kana so na mutu ne"?.

"A'a ni ko kadan ina so ka fuskance ta da kanka ne zaifi akan ace wani ne ya daidaita ku ko kai ma saika fi jin dadi ace kaine ka lallashi abar ka da kanka".

Shiru Haidar yai yana kallon Habib kawai cikin yanayi na damuwa sosai ci gaba Habib yai.

"Kasan Husnah yarinya ce mai hankali na rasa wanne rudi ne yake diban ka a baya ka rika ci mata mutunci kodan Daddy ne ya hada ku aure shiyasa"?.

"Nooo Habib badan haka bane bansan meke damu na ba a wancan lokacin dan Allah Habib ina bukatar taimako".

"Ok shikenan to karka damu zanyi magana da ita amma fa saika fara zuwa kafin ni naje".

"Zanyi idan kayi min alkawarin kaima zakai mata magana".

Dariya Habib yai "kai Haidar ji yadda ka mayar da kanka lokaci guda lallai duniya da abin mamaki".

"Kaga bansan wulakanci Habib"๐Ÿ™„.

"Sorry Daddyn Ahmad ๐Ÿ˜‚ kai din da abin dariya shikenan duk mubar wannan kaje ka same ta".

"Zanje zuwa jumawa kai kuma kaje gobe da safe".

"Ahhh tab ji dan Allah da sauri haka mai lefin zuwa next week ๐Ÿ™ˆ".

Mikewa Haidar yai "Habib kana son kashe ni ne? da so same ne ace kaima kaje a yau".

"Me๐Ÿ™„ waye zaije maka a yau din? amma dai ba niba saidai wannan kujerar da kake zaune akai taje maka"๐Ÿคญ.

Shiru kawai Haidar yai yana kallon sa dan ya gama kaishi bango ya rasa ma mai zaice duk su biyu suna neman burkita masa kwakwalwa da dora masa hawan jini.

Mikewa yai yana cewa "eh ita ce zaka je min dan iska kawai" yana gama fadin haka ya fita da gudu Habib ya bishi yana dariya.


Yamma nayi daidai karfe biyar da rabi Haidar ya Parker motar sa a kofar gidan su Husnah tunanin yadda zai shiga ya fara da yadda zai fuskanci su baba tuna irin abubuwan dayai musu a baya.

Har shida ta bada baya yana cikin mota bai fita ba saida wani yaro yazo wucewa ya tsaida shi yana aikashi gidan.

Jim kadan sai ga yaron ya fito tare da baba wani irin yarrr Haidar yaji wani Abu na tsirga masa kunya ta kama shi duk da yasan baba ba ganin sa yake ba amma yaji wani irin nadama ta rufe shi tun baban baisan waye shiba taya zai iya fad'a masa wani abu.................

Katse masa tunani baba yai da cewa "waye yake nema na kai yaro"?.

Yaron dan shekara biyar dake Shirin wucewa yawon sa yace "gashi nan a cikin mota".

"A mota kuma"?.

Baba ya fad'a yana dafe kirji "eh" yaron yace masa yana yin gaba abinsa.

Fitowa Haidar yai sai kawai ya samu kansa da kasa kallon fuskar baban duk da yasan ba ganin sa yake ba da'kyar yace.

"Barka da gida baba ni nazo gurin ka".

"Yaro waye kaidin? ko mai gidan hayar ne?.

Wata kunyar ce ta sake rufe Haidar yace "a'a mijin Husnah ne"๐Ÿ™Š.

"Mijin Husnah"๐Ÿ˜ฒ.

Kasa sake cewa komai Haidar yai shiru baba yai na wani lokaci kafin yace.

"To bismillah mu shiga ciki" wucewa gaba baba yai Haidar na binsa a baya suka shiga Innah na zaune akan tabarma baba yace.

"Munyi ba'ko dauko masa tabarma".

Mikewa Innah tai da sandan ta tana dogarawa ta shiga d'aki ta dauko tana shimfida masa.

Zama yai gabadaya jikin sa yayi sanyi bai ta'ba jin nadamar abinda ya aikatawa Husnah ba kamar yau da yazo gidan su yaga a halin da suk...........
"Sannu da zuwa yaro daga ina"? Innah ta tambaya tana kallon shi.

Sauke kai Haidar yai yana gaida su muryarsa kamar mara lafiya yace.

"Daga gidan alhaji Yusuf nake".

"Ayya Allah sarki alhaji Yusuf mutumin kirki sannu da zuwa fatan duk suna lafiya".

"Lafiyan su kalau dama nazo ne d'an uwa na ya turo ni bikon aunty Husnah ๐Ÿ˜‚".

"Dama Yusufun nada wani d'an ne bayan Aliyu"? Baba ya tambaya.

'Dan dafe goshi Haidar yai jin har ya fara shirme daga zuwa cikin d'an rikicewa yace.

"Eh d'an gidan 'kanin sane".

"Oh haka akai kanin sa da suka zo tare ko? fatan dai lafiya"?.

"Eh lafiya dama yayana Aliyu ne ya aiko ni nazo na baku hakuri akan abinda ya faru kuma na roka masa gafarar ku yace gobe zaizo ya baki hakuri yana can bashi da lafiya sakamakon nisa da matar sa tai masa shi yasa ya turo ni yace ku taimakawa rayuwar sa ta koma karya mutu".

"Subahanallahi mutuwa kuma d'an nan? Insha Allahu zai warke babu komai mu mun yafe masa kuma indai batun komawar Asma'u ne zata koma kaji".

Wani sansanyan numfashi Haidar ya sauke yana cewa "mun gode sosai baba Allah ya saka da alkhairi ya kara girma".

"Amin yaro Allah ya maka albarka".

"Na gode baba".

Mikewa yai zai tafi sai kuma ya tsaya yana cewa "ya bani sako gurin ta ko tana nan"?.

"Eh tana wancan dakin" Innah ta bashi amsa dakin ya nufa hankalin sa kwance zuciyar sa na hasko masa yadda Husnah zatai in ta ganshi.


Jin an budo labule yasa Husnah cewa "Innah dama ina so zamuyi magana ni dake".

Jin anyi shiru ta dago ganin Haidar ya shigo dakin yasa ta zabura ta mike tsaye tana masa kallon mamaki tace.

"Malam lafiya me ya kawo ka gidan mu har cikin d'aki na ko anan din ma dana taho biyo ni kayi kaci min mutunci tunda naga babu wani abu๐Ÿ™„.tsakani na dakai sai shi"?.

Tunda take magana yake kallon ta har takai aya sannan yace "ni ba wurin ki nazo ba nazo gurin baba ne na karaso naga baby na".

Wani kallo tai masa da mamaki tace "kazo gurin baba? Kodan zaka kakeiya tunda ba kallon ka yake ba saidai yaji muryar ka ba kunyar sa zaka ji ba".

"Husnah"๐Ÿ™„.

"A'a ni ka daina kiran suna na dan Allah bansan ganin ka tafi kawai abunka".

"Zan tafi yanzu ma kuwa amma ki bani lokaci ko kadan ne na gyara jiya na".

"Caf taya kenan? Wazai baka lokacin nasa amma dai ba ni kake ba saidai da murfin kofar nan kake ko"๐Ÿ˜‚?.


Ransa a bace yake amma dole maganar datai yasa shi murmushi yana kallon ta yace.

"Eh kaga mai fahimta da wuri ina yinki mata ta da murfin kofa nake ba dake ba ni zan wuce".

Dauke kai tayi daga saitin sa tana tabe baki tace "ni ba matar ka bace a gaida na gaba dama na rike kane"?.

"Eh kin rike ni man, amma mai zaki bani kafin na tafi"?.

"Oh kana tunanin zaka samu wani abu ne a gurina"?.

"Eh".

"meye".

Juyowa yai yana fuskantar ta da duka karfin shi ya jawo ta jikin shi yana rungume ta tare da hada bakinsa da nata ya bata zazzafan kiss sannan ya sake ta yana cewa.

"Na zo biko ne dan haka ki fara shiri a kowanne lokaci zakiga naso daukar ki".

Yana gama fadin haka ya duka saitin fuskar boy dinsa ya masa kiss ya fita a dakin.

Hawaye ne ya zubowa Husnah lallai Haidar ya goge mata hadda wato gurin su baba yazo ya karbi bikon ta kuma suka bashi zama tai tana kife kanta kawai ta soma kuka.


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our

Please Login or Register in order to submit comment