Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dashi ta hanyar aikin asibiti da ta soma zuwa.

Dawo dashi a tunani umma tai "ba magana nake maka bane baka amsa min ba"?.

Sauke numfashi yai yana kallon ta yace "babu komai".

"Babu komai kawai ka canza yanayin ka yanzu ko Zara ba sosai kake janta jikin ka ba meyasa"๐Ÿค”.

"Ki yarda umma babu komai kawai aiyuka ne sukai min yawa".

"Shikenan Haidar tunda baza ka fad'a min ba Saidai na maka addu'a Allah ya yaye maka koma menene ke cin ranka".

"Amin umma" yace cikin gaggawa domin addu'ar iyaye akan d'an su karbabbiya ce zaiso ace Husnah ta bar gidan nan tabar zuwa hospital shine matsalar sa shine damuwar sa.


Washe gari weekend ne Haidar tun asuba ya tafi ziyarar dole gurin Habib dan kada ma yaga Husnah gara a wuni acan da dare ya dawo.

Tunda asuba Husnah ta gamawa su Innah komai da zasu bukata sannan ta shirya tana cewa.

"Na tafi saina dawo".

"Asma'u tsaya" baba ne yai maganar.

Cak ta tsaya tare da juyowa tana kallon sa mikewa yai yana cewa "yau na yanke shawara muje gurin mutanen nan muyi musu godiya kullum lokaci kara wucewa yake kar abun ya huce da haka".

Farin ciki ne sosai ya kama Husnah harda sauke ajiyar xuciya daidai Innah ta fito daga d'aki tana saka hijab baba ya mike suka fita.

Adaidaita ta tara musu suka wuce da yake mai gadin gidan ya santa kuma tace da iyayen ta tazo sai bai hana taba.

Tana shiga duk suna falor Zarah da umma a zaune ganin su yasa umma ta fahimci sune iyayen ta.

Karba sosai umma ta musu babu nuna 'kyama ko wani abu sa'banin hankali sannan taje tawo musu magana da old Man din Zarah.

Babban mutum ne mai karamci da girmama na gaba gareshi ya fito abinda zai baka mamaki shine maimakon ya zauna a kujera ganin suna kai yasa ya zauna a 'kasan carpet ๐Ÿ‘.

Ya kuma basu girman su ta hanyar gaida su sunji dadi kuwa sai sannan suka saki jikin su ba kamar yadda suka zo a d'arare ba.

Babu yace "muna godiya fa sosai da abin arzikin da kukaiwa yarinya Allah ya saka da alkhairi Allah ya biya ku ya kara arziki munji dad'i mun gode".

Daddy yace "babu komai baba yiwa kaine abinda ka bayar shine rabonka da ita da Zarah duk 'ya'ya ne a gurina".

Innah tace "Allah ya saka da alkhairi mun gode mun gode ubangiji ya kara girma".

"Amin iya na gode".

Mikewa baba yai yana cewa Innah "taso mu tafi".

Kafin umma tai magana daddy yace "tun yanzu baba ku bari idan kuka wuni mana sai a mayar daku".

Basu iya musa masa ba tilas suka amince saidai addu'ar su Allah yasa harsu tafi Haidar bai dawo ba".

Sosai umma suka take jansu a jiki har suka ware suka fara hira Husnah kam na kitchen ita da Zarah suna aiki.

Janta part din Haidar Zarah tai tana cewa "muje part din yaya mudan huta.

Dakatawa Husnah tai "wanne yayan amma dai ba Haidar ba"?.

Zarah dake kokarin bude kofa tace "shi man ina da wani yayan bayan shine"?.

"Gaskiya baza niba ina dai jiran ki duk girman gidan nan ki rasa inda zamu huta sai gurin kalan magana ๐Ÿคจ".

Dariya Zarah tai domin taga kamar ba jituwa tsakanin ta da Haidar tace.

"Ai baya nan ya tafi wani wuri ba lallai zai dawo akan lokaci ba muje kada ki damu ko ya dawo ba gani ba sai mu had'u muyi masa taron dangi mu caskale shi"๐Ÿ˜‚.

Ba shiri Husnah ta kama dariya tana kallon Zarah tace "Allah ya shirye ki taya zamu iya dukan sa yana namiji saidai shi ya nad'e mu".

Zarah data bude kofa suka shiga tace "kai baki ji ance sarki yawa yafi sarki karfi ba yasin casa shi zamuyi dan ni akan ki zamu iya batawa da yaya".

"Hummm" kawai Husnah tace batai magana ba har suka zauna haka Zarah ta bude fridge dinsa ta debo musu kwakwa su dabino ayaba gwanda kawai suka hau gwangwajewa๐Ÿ™Š๐Ÿ™‰๐Ÿ™ˆ๐Ÿ˜‚.


Sai dare bayan sallar isha Haidar ya dawo yana shigowa ya tsaya tsam yana binsu da kallon rashin sani a ransa yace.

"Wadannan kuma daga ina na gansu duk da sanduna kamar fulani"?.

Dawowa daga tunani yai ganin umma sun fito da Husnah da Zarah tana cewa suje tasa driver ya kaisu gida.

Husnah taga yadda Haidar ke aiko mata da wani ba'kin kallo amma ta share shi suka fita hannun Zarah ya riko tana shirin binsu yace.

"Ke wadannan fa"?.

Zarah da bata lura da yanayin saba tace "iyayen sister ne suka zo gurin Daddy godiya".

Bai sake magana ba ya saki hannunta yana wucewa ciki ransa a mugun 'bace haka nan yaji ya tsani gidan kamar ya juya inda ya fito๐Ÿ™„.

Ranar su baba bacci sukai harda munshari kamar sun biya bashin banki saboda godiyar nan da sukayo da safe har so sukai su makara.

Ranar Monday Badiyat kin tafiya makaranta tai domin data dawo taji labari iyayen Husnah sunzo tayi zagi tayi tsinuwa da masifa harta gaji.

Fitowar Daddy kenan Badiyat ta tare shi kamar gaske da ladabin kura ga mai akuya ๐Ÿ tace.

"Daddy ina kwana".

Da fara'a ya amsa "lafiya Badi'ah makaranta zakije ne naga kin fito da wuri haka".

'Dan komawa kalar tausayi tai "eh Daddy school zanje".

"to Allah ya taimaka".

"Amin" tace amma saita kasa fad'a masa abinda take son fad'a kawai tai shiru tana raba ido ga Wanda yaiwa sarki karya.

Har zai wuce saiya tsaya ganin kamar tana da damuwa yace "Badi'ah kina lafiya kuwa".

Da sauri tace "a'a Daddy".

"Meke damun ki"?.

Karya wuya tai tana sakin murya Dan a tausaya mata tace "Daddy nima aikin asibiti nake so ka bani".


"Aikin asibiti kuma Badi'ah? To amma ai kin fad'i a jarrabawa taya zan baki doctor bafa bacci bane da zakice kin iya dole sai kinsan komai ki rika nutsuwa a makaranta kina lura idan kin samu wata shekarar sai na baki".

Idonta fal da hawaye tace "dan Allah Daddy ka bani ka bawa bare ma balle ni da nake matsayin 'ya a gurin ka".

Da mamaki Daddy yace "waye bare"?.

Goge hawaye Badiyat keyi cikin shashsheka tace "Husnah wacce take zuwa aiki gidan nan".

"Ok dama zaki hada kanki da ita ne ai basirar tace ta bata aiki bani bane kema ki dage kici jarrabawar ki zan baki amma idan har baki yi kokari ba saidai kiga wasu da farar riga ba keba".


"Amma ai Daddy nasan na fita a gurin ka".

",Eh Badi'ah kin fita amma hakan bazai sa ki samu yadda kike so ba bana abu da rashin tunani don haka sai ki dage kici jarrabawa idan kina son zama doctor".

Durkusawa a gaban sa tai tace.

"Daddy ka saurari hanzari na".

"A'a Badi'ah ba bukatar hakan kiyi abinda nace"โ˜น๏ธ.

Ganin ya wuce yasa ta Kira sunan sa da karfi.

"DADDY".

"Keep quiet ๐Ÿคญ๐Ÿ™Š" tsawar daya daka mata ne yasa tai shiru kawai sai hawaye dake zuba.

Yace "idan kika sake magana saina sa'ba miki".

Juyawa yai yana fita a palon yayin da itama Badiyat ta mike tana daukar Jakarta tai waje ranta a mugun'bace.


Bayan wucewar wata daya๐ŸŒ• sosai Husnah ta dage ta kara himma da bawa aikin ta muhimmanci.

Haidar ne zaune gaban Daddy tare da mika masa takarda yace.

"Daddy a kaf asibitin nan babu wanda yakai wadannan likitocin sanin aikin su kuma suna zuwa akan lokaci ya kamata a kara musu salary nasu".

Kar'ba Daddy yai yana dubawa yace "ok baby damuwa insha Allahu za'a kara musu sannan naga sunan mace ita kadai ce tai zakara a cikin likitoci matan"?.

"Eh Daddy ita kadai ce don gaskiya patient najin dad'in aikin ta da yadda take kula dasu".

"Yayi kyau dama tun farko ina da kyakkyawan zato akan yarinyar domin tana da hankali".

Cikin alamun tambaya Haidar yace "wacce yarinyar Daddy"?.

"Ita Husnah Ibrahim".

"Dama ka Santa ne Daddy"?.

"Ah ji Haidar da wata tambaya yarinyar da take aiki a gidan nan"๐Ÿ˜ฒ.

"Whatttt dama itace Husnah Ibrahim".

"Eh itace au kaida bakasan sunanta ba"?.

Shiru Haidar yai yana sauraron bugun da zuciyar sa keyi da karfin gaske saboda takaici da bacin ran daya rufeshi lokaci guda da yasan yarinyar nan ce wallahi saiya soke sunant.............

Katse masa tunanin da yake Daddy ya ta hanyar cewa "kayi shiru ko da akwai matsala ne"?.

Da sauri ya saita kansa "a'a Daddy".

"Amma kayi Shiru? Akwai abinda yake faruwa"?.

"A'a Daddy babu komai ka yarda".

"Shikenan na yarda".

Mikewa Haidar yai yana ma Daddy sallama ya fita cikin bacin rai Haidar ya kira Habib yana dagawa ya soma masifa.

"Amma wallahi Habib ka Raina min hankali wato saboda kasan tsakin mu da tsakuwa akan wannan banzar yarinyar shine ka saka sunan ta a cikin list din nan ko"?.

Dariya ce ta kama habib cikin dakewa yace "wacce yarinyar kake magana a kanta"?.

Haidar na huci yace "banzan yarinyar nan Husnah Ibrahim".

Tabe baki habib yai "ok a kanta kake min bala'i ai ban santa ba".

Numfashi mai zafi Haidar ya sauke yana cewa habib bansan rainin wayo ya isa haka saurara ka santa kake min yawo da hankali".

Habib yace "ok ban kwantancen ta".

Siffata ta Haidar yai tsaf tunda ya fara Habib ke dariya har yakai aya ransa a bace yace.

"Malam ina magana kana dariya kaban amsa"?.


"To ai Haidar har yanzu ban gane kwatancen ka ba wai wannan farar yarinyar kake nufi"?.

"Eh ko ma wacce kala ce bai dame ni ba itan nake nufi".

Cikin son kara tunzura shi Habib yace "ban santa ba saidai kamar kwanan baya naga photon ta akan screen din wayar ka kodai kana sonta ne๐Ÿ˜‚"?.


A mugun hasale Haidar ya danno masa wata ba'kar danyar ashar wacce tasa Habib cire wayar yana cewa.

"Haba Daddyn Ahmad bafa ni nakar zomon ba rataya aka bani kawai dan na fad'i gaskiya shine kake min ashar salon kasa kunne na ya kama da wuta" tsaki Haidar yaja yana kashe Kiran da yasan haka habib zai sake kunsa masa bakin ciki daya 'kyale bai kira shiba.


Kasa nutsuwa ranar Haidar yai ya rasa inda zaisa kansa har zazzabi ne ya haushi ji yake kamar ya jawo gobe dan kawai ya had'u da habib ko zai huce.

Washe gari Husnah haka ta tashi garin babu dad'i gashi babbar ranar ce wato juma'a ji take kamar ta hakura da zuwa asibitin amma tasha magani kawai ta wuce.


Haidar na zaune a office nashi ya zubawa takardun gabansa ido Habib daya le'ko ganin sa haka yasa cikin tsokana yace.

"Na shigo ko na tsaya"?.

Harara ya samu maimakon amsa dan haka ya karaso yana zama yace.

"Aliyu Haidar baban soyayya ๐Ÿ˜‚wato dan na gano abinda kake boyewa shine kake wani dauke min kai".

"Look Habib kai shiru ban san shirme".

"Oh ni nake maka shirmen Haidar"?.

"Bakai bane kasan Allah Habib ka kiyaye ni".

"Sorry na daina amma meye hadin ka da yarinyar nan ne Sam baka ra'ayin ta"?.

"Babu ruwanka ka rasa dawa zaka hada ni kaf yan matan duniya sai wannan abar Allah ya tsari gatari da saran shuka da na auri wannan yarinyar gara na mutu banyi aure ba har abada".

"Kai Haidar umm umm fa".

Wani kallo Haidar yai masa "me kake nufi".

"Babu kada gaba labari ya canza tasha fa".

"A'a ka manta airport ne zai canza ba tasha ba".

Habib zaiyi magana ya katse shi "malam ka hada min kan likitoci a hall ina son magana dasu yanzu".

"Ok baka da matsala" Habib ya fada yana mikewa ya fita kai Haidar ya jinjina yana murmushi sannan ya soma duba takardun.

Kaf likitocin dake asibitin manya da 'kanana sun hallara guri ya cika dam kowa da farar riga sunyi kyau sosai.

Husnah dake zaune hankalin ta yana kan wayar dake hannunta pop2 tana duba sakon da Zarah ta turo mata jin an zauna kusa da ita yasa ta dago.

Had'a ido sukai da wata budurwa dake aiko mata da wani irin kallo mai ma'anoni tace.

"Hummm! Husnah ko? Haka sunan ki yake idan na canka daidai right"?.

Da mamaki Husnah ta kalle ta kafin tai magana taji taci gaba "nasan baki sanni ba amma daga yau zaki sanni.

"Suna na Fauziyyah kuma na kasance a hospital din nan shekaru shida da suka wuce nasan zaki tambayi zuciyar ki meyasa nazo ina gabatar miki da kaina ba gabatarwa bace gargadi ne madam naji 'kishin 'kishin din kuna mu'amala da Haidar to ki cire idanuwanki daga kansa idan ba haka ba saina mayar dake abar tausayi a asibitin nan".


Ran Husnah a hade tace "da'ki'kiya ke kuma wacce bolar ce ta kwaso ki uban waye Haidar ko kin samu ta'bin kwakwalwa ne shin bacci kike to ki farka kisan wace Husnah babu shashanci a raina ki iya bakin ki".

"Kan uba jimin yarinya da 'karfin hali ni kike kad'a ma warning wallahi bazan 'kyale kiba zakisan ko ni wace".

"Zancen banza Kenan ke wace bayan bulkuma shashasha me zaki iya yi min".

Mikewa Fauziyyah tai tana cewa "bari kiga abinda zan miki harni zaki kalla kina fadawa magana..............

Jin guri ya kaure da tafi yasa duk suka mayar da hankalin su gurin Haidar ne tsaye Habib na kusa dashi ta yadda kowa zai jishi ya soma magana.

"Barkan ku da zuwa gurin wannan taro nawa na musamman dana shirya ba akan aiki ba kuma bai shafi hospital ba".

"Wannan wanne aiki ne doctor" gabadaya guri ya tambaye shi.

Murmushi Haidar yai yana cewa "kada ku damu yanzu zaku sani dama batu nake so nayi akan wata likita wacce batasan aikin ta bataje makaranta ba da'ki'kiya jahila amma ina mamakin daya take kula da patient ta iya allura ko kawai 'bula jikinsu take fanko ce ita batasan komai ba hatta sunanta bazata iya rubutawa ba bulkuma ce ita shashasha ina mamakin da yadda ta samu aikin gashi tana cikin asibitin nan".

Rudewa guri yai kowa yana cewa "wacece ita doctor ka fad'a mana"?.

"Kuna so ku ganta"?.

"Ehhh wallahi muna so a nuna mana ita".

Cikin wulakanci Haidar ya saici Husnah da yatsa kowa gurin ya kalla wata irin dariyar murna Fauziyyah keyi tana kallon yadda idon kowa ke kan Husnah lallai gayen nan ya iya rashin mutunci.

Ci gaba Haidar yai "doctors wannan da kuke gani sunan ta Husnah Ibrahim ita ba yar kowa ba ce amma ta dauki duniya da fad'i baban ta makaho ne amma kamar 'yar gwamna haka take jin kanta kuma kunsan meye sana'ar su".

"A'a saika fad'a doctor" duk hall din suka hada baki.

"Bara ๐Ÿ˜” shine sana'ar tsohonta bata ta'ba shiga aji da sunan karatu ba amma yau itace a doctor da'ki'kiyar mace ce kuma daga yau kusan kallon da zaku rika yi mata domin kunji asalinta ita din fa'kiriya ce amma bata da aiki sai bin gidajen manyan mutane ita da iyayen ta suna maula dan son xuciya ku kalle ta dakyau gata nan kamar 'kanzo a dafe babu romo a gashe ba maiko".

Dariya gabadaya aka sa ana kallonta kowa da abinda yake fad'a sai 'kus 'kus ake ana kallonta mata masu son Haidar sai farin ciki suke domin kowa yai tunanin ko sun san juna ne a da.

Dafe kafadar sa habib yai ransa a bace yace "amma wallahi Haidar baka da mutunci baka kyauta ba da nasan yarinyar zaka wulakanta ka tozarta bazan yi Kiran kowa ba haka ake rayuwa mai tai maka da zakai mata irin wannan abin gashi kasa sai kallon ta ake kamar wacce tai abun kunya sai nuna ta ake".

Shima Haidar hade ran yai yana kallon shi yace "kaine sila uban wa yasa kasa ta cikin list din nan"?.

"Cancanta ce ta bata".

"To yanzu ai taga cancanta ganin idonta nasan daga yau bazata sake zuwa hospital din nan ba ni kuma dama abinda nake so kenan".

"Haidar danai maka magana bakaji nadamar abinda kai mata ba"?.

"Nadama dai? akan me zanyi nadama ai yanzu aka fara wasan indai bata daina zuwa hospital din nan ba zanyi mata abinda yafi haka wannan somin ta'bi ne".

Juyawa yai yana kallon kowa yace "ina dai fatan kun ganta kun shaidata ko a ina kuka ganta".

"Eh mun sheda ta doctor".

"Abinda nake so kenan kuma buri na ya cika shikenan kuna iya tafiya" mikewa sukai da yake juma'a ce lokacin tashi yayi kowa gida ya nufa.

Husnah zata fita Haidar ya dakatar da ita "ai ban gama dake ba".

Tsayawa Husnah tai tana kallon sa taya zata manta da wannan gayen a rayuwar ta ya munana mata ya bakanta mata a gaban dubban jama'a.

"Ya kikaji yanzu nasan kinsha kunya kuma wannan hospital din ya zama haramiyar ki domin bana 'ya'yan talakawa bane kada ki kuskura ki sake zuwa gidan mu da sunan aikin maula dan yafi karfin 'kazama irin ki zaki iya tafiya".


Dakyar Husnah ta iya daga kafarta daga hall din ta fita hawaye na zuba a idonta haka ta nufi gida da zazzafan zazzabi daya rufe ta lokaci guda.

Ranar Haidar bai tafi gida da wuri ba saida ya gama komai sannan ya wuce iya Zarah ya samu a palor tana ganin sa.

Tace "yauwa yaya dama dan kai nake ta zaune tun dazu Daddy yace idan ka shigo nace kaje yana neman ka".

"Ok" part dinsa ya shiga yayin da Zarah itama ta mike tana komawa gurin umma.

Saida yai wanka sannan ya fito yana shiga part din Daddy Badiyat dake la'be a kofar part din ta tunda taji sanda Daddy ya shigo yana cewa Zarah ta jira Haidar yazo tace yana neman sa itama take tsaye taga mezai faru.

Fitowa tai tana waige-waige ganin babu kowa yasa da sauri ta bude kofar part din Daddy tana shiga itama tare da kara kunnen ta a jikin kofar taji mai za'a ce.


Da sallama Haidar ya shiga ya samu Daddy a palon bayan ya gaisar dashi ya zauna a kasan carpet cikin girmamawa yace.

"Daddy Zarah tace kana nema na"?.

"Eh Aliyu ina neman ka yaya aiki yana tafiya daidai ko da matsala"?.

"Eh Daddy aiki yana tafiya yadda ya kamata babu wata damuwa".

"Dakyau alhamdulillahi naji dad'i sannun ka da kokari".

"Daddy dama inaso na fada maka akwai likitocin daya kamata a dakatar dasu basu san aikin suba da kuma wadanda ya kamata a basu lokaci su karo karatu".

"To babu matsala kayi duk abinda ya dace dan ci gaban asibitin".

"Ammm ALIYU dama tambayar ka nake son yi".

'Dan kallon Daddy yai haka nan yaji hankalin sa bai kwanta ba kodai Habib ya Kira shi a waya ya fad'a masa abinda ya faru yau a hospital amma daya kad'e saidai kuma yasan waye Daddy wajen zafin rai da ace Habib din ya fad'a masa da yasan yana zuwa zai falle shi da mari๐Ÿ™„.................

Katse masa tunani Daddy yai da cewa "batu ne akan aure Aliyu ka samu wacce kake so ne ko har yanzu dai"?.

"Eh Daddy har yanzu ban samu ba".

"To amma ka shirya yin aure a kwana kusa"?.

"A'a Daddy ban shirya ba domin har yanzu banga wacce ta dace dani ba".

"Ni na gano maka wacce ta dace dakai Haidar" gabansa ne ya fad'i ya dago yana kallon Daddy yace

"Wacece"?.

"Cikin biyu zaka za'bi daya wacce kake ra'ayi".

"Su waye"๐Ÿค”?.

"HUSNAH KO BADI'AH ๐Ÿ˜ฎ๐Ÿ˜ฒ๐Ÿ™Š.

Zaro ido yai baisan lokacin da yace "DADDY HUSNAH KO BADI'AH โœŒ๏ธ kuma"?.

"Eh a cikin su ka za'bi daya wacce tai maka".

"Daddy babu ko daya ka kara min lokaci".

"A'a Haidar na gaji da wannan abin kullum da am maka magana saidai kace a kara maka lokaci a ciki xaka zaba ko ni na za'ba maka"?.

"Daddy da dai ka bari na samo wata".

"Ban bari ba Haidar bana son bata lokaci ka fad'a min amsa nake jira kafin na yanke maka nawa hukuncin๐Ÿ˜ก..


Shiru Haidar yai yana tunani ga koshi ga kwanan yunwa".

"Kayi Shiru kai nake saurara"?.

Sauke d'ad'd'atan numfashi yai dakyar muryar shi bai fita sosai yace.

"Daddy na za'bi Badi'ah ๐Ÿ˜ฒ๐Ÿ™„".

Badiyat najin haka wani irin suman tsaye tai cikin wani irin yanayi na shauki ta ruga da gudu cikin murna tabar part din tana zuwa bedroom dinta ta daka tsalle tana fadawa kan gado tare da dauko wayar ta ta soma neman number hajiya Khubrah da ta zeey tai musu albishir.


Kallon mamaki Daddy ke masa yace "Badi'ah ce za'bin ka"?.

Shiru Haidar yai domin babu yadda ya iya ko kadan Badi'ah batai masa ba bata cikin tsarin yan matan da yake so saidai gara ya za'be ta daya za'bi Husnah.

Cigaba Daddy yai da cewa "ni kuma ban za'be taba ba ita nake maka ra'ayi ba ni Husnah na za'ba maka itace wacce ta dace dakai da tsarin rayuwar ka domin kadau duniya a hagunce itace zata maida ka dama ta gyara maka halinka lamarin ka akwai sa'bani".

Zabura haidar yai cikin tashin hankali yace "Daddy Husnah kuma"?.


"Eh ita Haidar yarinyar nada hankali tun ba yanzu ba nake maka sha'awar auren mace mai tarbiyya irin ta domin ta gyara ka har yanzu bakasan meye daidai ba".

Yaji d'acin yadda Daddy ke fad'a masa akan Husnah amma saiya had'iye bai nuna ba yace.

"Daddy indai Husnah ce gara na auri Badi'ah".

"Meyasa ๐Ÿค”"? Akan wanne dalili๐Ÿคจ"? kaga fa bansan shaahanci ๐Ÿ˜ก na gama yanke magana zaka iya tafiya ka kasance cikin shiri domin a kowanne lokaci zan iya yi maka magana akan batun aurenka".

Haidar zaiyi magana Daddy ya katse shi "bansan jin komai 'bace min da gani" ran Haidar inyai million a ranar ya baci ko gaban sa baya gani ya juya ya fita a part din.

Yana fita ya Kira Habib a waya yana dagawa cikin masifa ya soma magana.

"Kai munafiki Allah ya toni asirin ka wato saida ka fad'a wa Daddy abinda ya faru a hospital gashi yanzu ka jawo min bala'i yace saina auri wannan 'yar talakawan๐Ÿ™„".

Dariya Habib ya fara yana cewa "uban waye ya fada nine na Kira Daddy na fada masa, da Husnan zai daura muku aure? kaiii Haidar bakaji daidai ba kodai baka ci abinci ba yunwa kake ji๐Ÿ˜‚"?.


"Uban yunwa nakeji habib magana fa nake fad'a maka akan tashin hankali na amma kake karanta min hauka".

"Kai wallahi Haidar bansan komai ba"?.

"Kamar ya bakasan komai ba kana nufin zakace min ba kaine ka fad'a masa ba kome"?.

"Kaga bari nazo gidan yanzu naji ka rude sosai duk abinda zance maka a waya bazaka yarda ba" aje waya Haidar yai yana zama akan kujera kawai yama rasa abun yi babu abinda yake tunawa kamar abubuwan dayai mata d'azu a hospital taya zai fuskanci likitocin sa bayan ya gama muzanta ta a gurin su yanzu kuma suji labari ya canza ta zama matar shi, inaaa impossible har abada.


Haka Husnah ta koma gida jikin ta sanyi kalau amma bata fad'a wa su baba komai ba tayi kokari ta danne dukkan damuwar ta da son manta abubuwan da suka faru a dakin hall din.

Washe gari kamar ta fasa zuwa aiki gidan su amma ganin ba sune sukai mata laifi ba basune suka ce kada ta sake zuwa gidan su ba shine yasa kawai ta shirya ta tafi.

Tana shiga Zarah ta tare ta da murna "oyoyo sister na wata sabon gani kwana biyar din nan da ban ganki ba sai naji duk babu dad'i anya nima bazan koma karantar likitan nan ba".

Dariya Husnah tai "to ko zaki koma kinga mun samu 'kari"?.

"Ai dan Daddy bazai yarda bane".

"Gaskiya ne ba yarda ne bazai ba Zarah bazai yiwu bane domin bangaren lawyer ๐Ÿ‘ฉโ€๐ŸŽ“ kike karanta".

"Haka ne sister kawai dake ne bana son rabuwa".

"Hum Zarah kenan ai baza mu rabu ba muna tare".

"To sister in kikai aure fa"?.

'Dan zaro ido Husnah tai "aure dai? Tab waya fada miki ni bazan yi aure ba saboda nike kula da mahaifana".

Zarah zatai magana sukaji muryar umma na cewa "Asma'u kinzo dama"?.

Cikin ladabi Husnah ta gaida ita tana cewa "eh umma yanzu na shigo".

"Ok yayi idan zaki tafi gida ki neme ni ina son magana dake".

"To umma".

Zarah dake rike da hannun Husnah tace "muje sister mu karbi aikin baba Rabi nima daga yau na zama duniya ba hutu".

Hararar ta umma tai tana cewa "ji kamar gaske bayan kuna shiga yanzun nan zaki gudo".

Dariya Zarah tai "Allah umma yau zan dage saimun gama duka muje sister".

Wucewa sukai umma data bisu da kallo tuna maganar da Daddy ya fad'a mata jiya yasa ta sauke ajiyar xuciya tana addu'ar Allah yasa Husnan ta yarda.

Ita kanta Zarah batasan da maganar ba kuma umman bata sanar mata ba.

Bayan sun gama aikin part din Zarah suka shiga kafin yamma saida akai sallar la'asar sannan suka koma kitchen dora dinner.

"Umma mun gama zan tafi" Husnah tai maganar tana aje sauran kayan hannunta akan dinning.

"Ok zonan".

Karasawa inda umman take Husnah tai Zarah kuma na zaune akan kujerar dinning din tana testing abincin da sukai.

Bata jin mai suke cewa kawai jin umma na cewa "HUSNAH HUSNAH" yasa ta dago daidai Husnah ta fita da gudu a palon.

Tasowa tai da sauri tana cewa "umma meya faru naga tana gudu mai akai mata? ko dakatar da ita zuwa aiki kikai"?.

Kai umma ta girgiza "a'a Zarah ba dakatar da ita nai ba na fad'a mata ne cewa Daddy nason ta auri haidar shine

Please Login or Register in order to submit comment