Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta sake koya mata kowa a banza take ganin sa.


Kamar yadda Husnah take yi kullum zuwa aiki gidan hajiya yauma haka tai tayi mamaki da take gidan ko'ina a hargitse.

Hajiya na ganinta tai murmushi tana cewa "Asma'u karaso mana kika tsaya anan".

Karasawa Husnah tana gaida ita haka nan taji jikinta yai sanyi domin yanayin yadda taga gidan hanata aikin hajiya tai tace ta zauna tukuna.

Ita dai ta zauna ne kawai amma maganar gaskiya hankalin ta ya tashi da komai suna haka wasu samari sukai sallama bayan sun gaisar da hajiya suka fara debe kujerun suna fita dasu.

Ganin haka yasa Husnah tai tunanin ko sauya wasu zatai kallon ta tai daidai itama hajiyan ta dago suka hada ido murmushi tai tana cewa.

"Asma'u gobe jirgin mu zai tashi zuwa Spain kuma gaskiya zan jima ban dawo ba domin nayi waya da mijina yace nabishi bercelona aikinsa da waya bashi da ranar dawowa Nigeria".

Wani mugun faduwar gaba Husnah ta tsinci kanta dashi jin zasu fito rana bayan samu inuwar fakewa idanta na tara hawaye tace.

"Hajiya Allah ya kiyaye saikin dawo".

"Amin Asma'u ga sauran kayan abinci nan zansa akai muku shi a bayan mota sannan ga wannan ki gaida min mahaifan ki".

Naira dubu ashirin ta bata sannan tasa mai tuka mata mota ya debe dukkan kayan abincin dake kitchen dinta yakai mota.

Sallama Husnah tai wa hajiya ta mike tana kuka zata fice daga palon hajiya tasan kukan sabon da sukai ne itama lokaci guda taji ta sauya yanayi na rashin jin dadi.

Dakatar da ita tai da cewa "Asma'u kukan me kike? Zo nan".

Dawowa tai tana durkusawa a gabanta rike hannun ta hajiya tai tana cewa.

"Kukan me kike"?.

Share hawaye Husnah tai tace "hajiya ina kukan rabuwar mune nasan ba lallai mu sake haduwa ba har abada tuna hakan ne yasa nake kuka".

Sauke ajiyar xuciya hajiya tana kallon ta tace "shikenan karki damu zan hada ki da kawata kici gaba da mata aiki kamar yadda kike min idan kina so kinga inna dawo saiki dawo guri na".

"Murmushin da bata shirya ba tai dan batasan ya fito ba a fili ta nuna murnar ta farin ciki da kuma jin dadi.

Kai hajiya ta jinjina "shikenan Asma'u ba damuwa gobe kizo da wuri sosai zan hada ki da ita".

Mikewa Husnah tai tana cewa "to hajiya nagode sai anjima Allah ya kara arziki".

"Amin ki gaida su baba".

Husnah na zuwa gida baba ya tare ta da tambaya "Asma'u wannan kayan fa daga ina wani yazo ya ajiye kawai yace mana inji hajiya ina ce ba abin cutarwa bane"?.

Zama Husnah kusa dashi tana cewa "eh baba hajiyan da nakewa aiki ce ta bani domin gobe zata bar kasar zata bi mijinta zuwa Spain aiki ya rike shi".

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Husnah taji sun fad'a a tare shi da Inna cikin mamaki take kallon su.

"Lafiya naji kuna salati"?.

"Asma'u ba lafiya ba Allah shike ri'ke damu amma hajiya ya bamu ta zama garkuwar mu yanzu ya zamuyi yaushe zata dawo"?.

"Gaskiya baba ba rana".

Wani salatin suka kuma saki wanda ya kusa bawa Husnah dariya tana kallon su tace.

"Amma tace min gobe naje da wuri zata hada ni da kawarta naci gaba da mata aiki kafin ta dawo".

Sai sannan suka sauke numfashi nutsuwa tazo musu Innah tace "indai haka ne to alhamdulillah".

Kamar yadda hajiya tace washe gari da asuba Husnah tai wanka taje gurin ta daga nan duka wuce duk da dama already ta sanar da zuwan nasu.

Matar itama ta kasance mai Kirki kamar dai hajiya tana da sakin fuska kuma ta karbi Husnah hannu biyu kuma tace zatai mata aiki kamar yadda take yi a baya.

Husnah na komawa gida da farin cikin ta tai turus ta ja burki sakamakon ganin dalleniyar bakar motar na sha'ki a kofar mashiga kangon da suke.

Tuna mahaifan ta na ciki yasa da sauri ta karasa bayansa ta fara gani yana tsaye cikin shigar tsadaddun kaya da agogo mai kyau.

Lokaci guda jikinta yai sanyi tun bata kalle shiba sallama tai wanda yasa shi juyowa yana kallon ta itama shi take kallo cikin mamaki zuciyar ta na harbawa a ranta tace.

"Wannan ai gayen nan dayai mana rashin mutunci nida baba a asibiti ne me yake anan kodai gidan san.................

Katse mata tunani yai da cewa "don't look ๐Ÿ‘€ me like that, what are you doing here"?.


Kasa magana Husnah tai sai kallon sa data tsaya yi cikin tsawa yace "i said don't look me like that what are you doing here"?.

Ba Husnah ba hatta su baba Saida suka tsorata a zabure baba ya mike yana cewa "kayi hakuri yaro 'yarmu muke jira tazo mu fita".

"Ai dama da 'yar taku nake me kukeyi anan waye ya baku iznin zama ko sai nasa an fara cilli daku zuwa waje daku gane yaren da nake muku magana dashi wannan gidan yayi kama da wanda irinku zasu zauna"?.

"A'a amma kayi hakuri yanzu zamu fita" baba ya fad'a yana lalumar sandan sa.

Hawayen daya zubowa Husnah akan idonsa ya dage gira yana dauke kai.

Gogewa tai cikin takaici tana karasawa ta dauko sanadan tana baiwa baba daidai ya fita a gidan tace.

"Da nasan gidansa ne wallahi ko zafin rana ruwa sanyi zai kashe mu a layi baza mu shigo ba".

Da mamaki baba yace "Asma'u kin sanshi ne"?.

"Eh mana baba shine fa wanda yasa aka koro mu daga cikin asibiti ranar dana raka ka bara har yasa aka ji maka ciwo".

Jin tafiya yasa Husnah kallon gurin ganin Mansur tai ya shigo hankalinsa a tashe yana cewa.

"Ku fito daga gidan nan bansan zai zo ba dan Allah kuyi hakuri".

Daidai ya fara tattara musu kaya wasu mutum biyar suka shigo suna debe kayan gidan suna watsawa waje cikin tsawa dayan yace .

"Zaku fita ne ko sai mun hada daku mun kai wajen banzayen mutane".

Jiki na rawa sukai hanyar fita tuntu'be baba ya kwasa sai gashi ya fad'i kasa da gudu Mansur ya d'aga shi wanda Husnah batasan lokacin data fara kuka a fili ba.

Yana jingine a jikin motarsa suka fita ga watsin daya sa akai musu duk an tarwatsa musu kayan abinci shinkafar su duk ta zube a kasa da mai wani ma ya bata musu kayan sawa.

Kofar shagonsa Mansur ya kaisu sannan ya dawo ya tattara musu komai yakai musu.

Sannan ya basu hakuri "dan Allah baba kuyi hakuri abinda ya faru laifi nane da nace ku zauna a cikin gidan ni ya kamata yaiwa ba kuba".

Mikewa Husnah tai tana cewa "mun gode Mansur karka damu komai yai farko wata rana zaiyi karshe Koda kai ko bakai dole a rubuce yake sai mun zauna a gidan yaci mana mutunci".

Kai Mansur ya girgiza "amma dai nine sila ni na jawo komai".

"A'a ba kai bane dama ya taba mana wulakanci a asibiti".

Da alamar tambaya Mansur yace "wanne asibiti AAH Aliyu Ahmad Hospital me kukaje yi".

Boye masa Husnah tai "babu kawai dai na raka baba ne, yanzu dan Allah kana ganin zamu samu gidan hayar da zamu kama nan kusa"?.

"Eh akwai ko nima zan iya baku domin wani alhaji ya bani gidajen hayarsa na nan anguwar ni nake kula masa da komai d'aki biyu da kitchen da toilet dubu casa'in a shekara".

Shiru Husnah tai kamar zata ce ya barshi sai ta tuna sai shekara kuma gashi aikin da zata rikayi duk wata dubu hamsim sai tace.

"Eh zamu kama muje ka kaimu".

Wucewa yai suna binsa a baya har suka shiga layin kusa dasu gidaje ne iya ganinta zasu kai ashirin a jere iri daya kowanne da lambarsa manne a kofar gidan.

Key yasa ya bude musu gidan dake kusa dana biyu suka shiga sannan yaje ya kwaso musu kayansu ya kawo musu kayan wanke toilet da komai godiya da albarka baba ya rika jera masa.

Cire hijab Husnah tai tadau tsintsiya ta fara share ko'ina lungu da sa'ko ta wanke harsai da taga gidan yayi fesss sannan ta fara tunanin ya zatai tayi musu girki domin ba murhu ga gida ko'ina a lelaye saidai ta sayo gas.

Fita tai zuwa shagon nasa ta masa bayani ya raka ta tasayi gas din sannan tayo wasu cefanen suka dawo.


Khubrah da kanta tasa Badiyat a mota ta mayar da ita gidansu Haidar bayan ta kare zage zage wai Allah ya rufa asiri me mubashshir zaiyi da Zarah wuce nan.

Da wuri Husnah taiwa su baba abun karyawa tai musu abincin rana dama ta sayo cooler ta zuba musu a ciki takai kusa dasu da duk wani abinda zasu bukata kafin ta musu sallama tana wucewa gurin aiki suka bita da kyakkyawar addu'a.

Lokacin da taje dama babu sanya ta shiga kofar da aka nuna mata tsaye ta tarar da yar tsohuwar tana kokarin kunna gas da sauri ta karasa tana cewa.

"Sannu iya miko na kunna miki".

Juyowa baba Rabi tai tana kallon ta da fara'a tace " 'yarnan ashe kece har kinzo, ko ba nisa anguwar taku daga nan"?.

Murmushi Husnah tai "a'a akwai nisa kawai dai na zo da wuri saboda kada ace daga fara aiki na fara makara".

"Haka ne gaskiyar ki Allah ya taimaka".

"Amin" Husnah tace tana mamaki ganin irin ababen da ake hadawa kamar ba iya breakfast ba an dafa wannan an soya wannan.

Bayan sun gama hadawa baba Rabi tace "to dauko ki biyo ni".

Dauka Husnah tai tana bin bayan baba Rabi har dinning suka ajiye suna dawowa sunyi yakai sau biyar Husnah har ta gaji domin ba irin wannan aikin take a gidan hajiya ba.

"To yanzu sai muje ki serving nasu ki jira kuma zuwa karfe daya mu sake shigowa kitchen mu dora na rana".

Ajiyar xuciya Husnah ta sauke batai magana ba suka fito a kitchen din suna shiga part din baba Rabi daidai umma ta fito Zarah dake zaune a palon tace.

"Umma ba'kuwa kikai ne"?.

"Ba'kuwa kuma a ina"?.

"Naga wata lady tare da baba Rabi sun shiga part dinta yanzu".

"Ok sabuwar yar aiki ce na samu".

"Wannan din"?.

A yadda tai maganar saida umma ta kalle ta tana cewa "to meye"?.

Kai Zarah ta girgiza "ba komai kawai dai bata dace ba".

"To ya za'ai Zarah babu ce tasa nima farkon ganinta nayi mamaki da hajiya tace min wait aiki take mata na dauka wasa take min".

Shiru Zarah tai tana kallon kofar part din baba Rabin kamar ta shiga ta sake kallon wannan baiwar Allah sai kuma ta fasa tana mikewa ta nufi dinning tare da danne bell๐Ÿ””.

Fitowa Husnah tai haka nan taji jikinta yai sanyi Zarah dake kallon ta tace.

"Mene sunan ki"?.

Husnah data sauke numfashi a hankali jin tambayar datai mata tace "Asma'u".

"Husnah kenen"?.

"Eh haka ake ce min".

"Yayi kina karatu"?.

"A'a da nayi amma yanzu na daina".

"Meyasa kika daina"?.

"Saboda bamu da halin da zanci gaba".

"Ok kinyi secondary School ne"?.

"Eh nayi har jami'a ma".

"Waye ya biya miki jami'ar"?.

Kallon mamaki Husnah taiwa Zarah jin tambayar ta fara yawa amma sai tace.

"Wani alhaji ne a anguwar da muka fara zama yadau nauyin karatu na".

"Am zaki iya kawo min takardun ki na gani"?.

Shiru Husnah tai zatai magana taji Zarah tace "sorry idan na takura miki na saba domin lawyer nake karanta shiyasa kika ga ina ta jero miki tambaya ba kwama ba wa'kafi".

'Dan murmushi Husnah tai "a'a ba komai zan kawo miki".

"Shikenan to yi serving dina".

Zama umma tai duk da taji zancen da suke bata nuna ba har tai serving tabar gurin".


Umma dake kallon Zarah tace "sannu lawyer ๐Ÿ‘ฉโ€๐ŸŽ“ kin tsare yarinyar mutane sai loya mata tambaya kikeyi".

Dariya Zarah tai "Allah umma abun ne yake tsuma ni".

"To idan ta kawo miki takardun nata me zaki"?.

"Zan taimake tane".

Kai umma ta jinjina "yayi kyau Allah ya taimaka".

"Amin umma".

Ba weekend bane Haidar ya tafi hospital sai kusan karfe daya Badiyat ta fito wai a hakan makaranta zataje.

Bude dukkan girman idonta tai tana karasawa ganin wacce batai zato ba tace "keeeee".

Da sauri Husnah ta juyo dan harta tsorata Badiyat dake mata wani kallo zagaya ta tafara yi tana tafi tace.

"Hummn yaro baisan wuta ba saiya taka Koda naji yau kuma maular nan ta kawo ki? Da kyau maraba gashashshe ina miki barka da zuwa ashe kece yar aikin da aka dauko nayi murna yanzu aka fara wasan zaki gane kuren ki".

Yadda take kallon Husnah kai kace rufeta zatai da duka sannan tabar zagaya ta kawai ta samu guri ta zauna tana dariya tace.

"To sabuwar Kitchener yi serving dina idan kuma kallon nawa sha'awa yake baki sai kici gaba".

Tabe baki Husnah tai tana kallon ta tace "ke din banza har maye a jikin naki daya zama abin kallo to bari na fada miki gaskiya idan har baki duba mudubi ba kika fito ki koma ki duba fuskarki kamar biri๐Ÿ™Š yasha lemon tsami๐Ÿ™‰๐Ÿ˜‚".

A masife Badiyat tace "kee nice nake kama da birin da uwark................

I
Rufe mata baki Husnah tai tana cewa "kada ki kuskura wannan kazamin bakin naki ya zagar min uwa wallahi bar ganin gidan kune saina gurje miki baki babu ruwa na idan kina cin kasa ki zauna lafiya to ki kiyaye ni don ni shuri ce na wuce gaban tunanin ki".

Bige mata hannu Badiyat tai tana cewa "kan uba lallai ma yarinyar nan harni kike kad'awa warning saboda kin raina min hankali yar uban waye ke a garin nan"?.

Juyawa Husnah tai tana aikin ta tace "a'a kada kiso sanin ubana domin yafi naki daraja da matsayi kuma ya bani tarbiyyar da naki bai baki ba".

"Kee dalla ya ishe ki" Badiyat ta fad'a tare da buga dinning din tana mikewa tsaye.

"Bai ishe niba ina so ki gane bambancin abinda yake fari da wanda ya kasance ba'ki me kike tunani a kaina zan zura miki ido kina fada min magana na kyale ki saboda ga wacce ta rako mata ko? To kinyi kadan ki sake shiri".


Kai Badiyat ta jinjina "wallahi zaki bayani saina kuntata miki da kafafun ki zaki bar gidan nan".

"Ai dama da kafafu na nazo kuma da kafafu na zan bar gidan bake kika kawo niba banza 'yar iya kawai๐Ÿ™ˆ".

Cizon yatsa Badiyat tai tare da dauko wayar ta tana dubo number wayar Zainab daidai umma ta karaso tace.

"Maganganun me nake ji ne anan lafiya Husnah naga kin tsaya"?.

Cikin ladabi Husnah tace ba komai hajiya aiki nake karasawa baba Rabi na jira na".

"Ok yayi".

Kallon Badiyat da ranta ke mugun hade tai tana cewa " Badiyat ke baza ki makaranta bane daya da rabi ta wuce"?.

"Eh baza niba" tana fadin haka tabar gurin fuuuu.

"Allah ya shirya ki umma tace itama tana barin gurin cikin alamun tambaya Husnah a ranta tace "tofa akwai abu a kasa kila ba yarta bace tunda naga tana mata raini ko 'yar kishiya ce.

Kitchen ta koma ta samu baba Rabi suka dora abincin rana tana yanka ganye suna d'an hira kadan kadan tunda basu saba ba.



Da wuri suka gama komai Husnah tai musu sallama ta koma gida kamar yadda Zarah ta bukata washe gari ta kawo mata takardun makarantar ta ita kuma takaiwa daddyn su.

Sannan ta fad'a masa komai ya amince ya kira Husnah sakamakon shima babban likita ne ya jarraba ta ya mata tambayoyi ta bashi amsa ba kurkure ba'ki dan haka yace kawai practical zata fara idan ta kware zai samar mata aiki likita da kansa.

Taji dadi sosai tayi masa godiya da kwarin gwiwa ta koma gida ta fadawa baba a ranar saboda farin ciki dakyar sukai bacci.


Saidai practical din da take bai hana ta yin aikin da takewa hajiya ba domin tayi alkawarin bazata barsu ba sune silar daukakkar ta zataci gaba da musu aiki.

Badiyat na zaune a palon babu kowa tana duba waya batai zato ba taji saukar bulala a jikin ta.

'Kara ta saki tana dagowa ganin wanda ke tsaye kuma tasan me tayi yasa ta mike tsaye a gigice cikin kid'ima zata gudu.

Riketa yai yana sake zura mata cikin fad'a ya soma magana "dan ubanki me kike kallo kika samu carry over? Wato dama shashancin banza kike yi a school da kula 'kawaye ko yau saina ci ubanki".

Kuka Badiyat keyi lokacin daya sake zuga mata duk jikin ta na rad'ad'i tace.

"Dan Allah ya mubashshir kayi hakuri wallahi ba 'kawaye nake kulawa ba malamin ne ya cuce ni".

Cikin tsawa yace "rufa min baki ko na karya ki a gurin nan".

Shiru Badiyat tai amma hawaye bai daina ambaliya a idonta ba sakamakon jin muryar umma yasa ya d'aga belt din ya sake zuzzura mata sannan ya fice a palon.

Kuka Badiyat ta kifa kanta akan kujera tana yi Zarah na kallon su amma batai magana ba tasan waye mubashshir idan haryai fushi shiyasa babu ruwanta.

"Lafiya Zarah me akaiwa Badi'ah take irin wannan kukan haka harda shid'ewa"?.

Rufe littafin hannun ta Zarah tai tana kallon umma tace "ita da yayan tane wai to samu carry over a exams dinta shine yazo ya gyara mata zama".

Umma bata sake cewa komai ba ta wuce tana cewa "Allah ya rufa asiri".

Zarah data zubawa Badiyat ido ganin yadda belt din ta shata a jikinta tace.

"Sorry sis ki kula nan gaba".

Wata ba'kar harara Badiyat ta sakar mata tana mikewa ta nufi part dinta tana cewa.

"To munafika ina ruwan ki".

Dariya Zarah tai "babu ruwa na kam madam 'kwas-'kwas saidai dole na baki hakuri tunda dear dina ne ya buge ki".

Tsaki Badiyat tai tana shigewa harda toshe kunnen ta saboda kar taji abinda Zaran zata ce.

Mikewa Zarah tai daidai Husnah ta shigo palon da sallama tace "oyoyo sister Husy dama yanzu nake Shirin tashi na samu umma na dauka ko kin daina zuwa".

Murmushi Husnah tai tana kallon Zarah da ganin rashin girman kanta tace.

"Ni na isa ai nida daina aiki a gidan nan mutu ka raba".


Kallonta Zarah tai cikin wasa tace "um um fa kada sai mun saki baki ki kawo mana invitation card๐Ÿค—".

Kai Husnah ta girgiza "da gaske nake ki yarda bazan yi aure ba ina tare da mahaifana".

Zarah tayi mamaki amma bata nemi dalilin da yasa tace baza tai auren ba saboda kar ta takura mata.

"Ok Sister muje kitchen yau zanga yadda zaki hada abinda mukai magana dake ranar" Zarah ta fad'a tana mikewa.

Shigowar Haidar cikin kayan likitanci ne yasa suna hada ido da Husnah gabanta ya fad'i zuciyar ta na harbawa da karfin gaske har dan rufe ido tai ta sake budewa ganin ba gizo yake mata ba yasa ta gane a zahiri ta ganshi.

"Dama wannan saurayin da yai mana wulakanci a gidan su nake aiki wadannan ahlin sane lallai akwai matsala.

Ganin irin musayar kallon da suke tsakanin su yasa Zarah tai gyaran murya da mamakin ko sun san juna tace.

"Ya Aliyu ka Santa ne"?.

Cikin basarwa yace "wa na sani"?.

Zarah tace "Husnah nake nufi".

Tabe baki yai cikin halin ko in kula yace "ban taba ganin taba me kika gani".

Kai Zarah ta girgiza "babu yaya a kallon da kukewa juna naga kamar da wani abu".

Wani irin kallo yaiwa Zarah wanda tai saurin kama bakinta cikin sauri tace.

"Yi hakuri yaya ba in nufin na bata maka raiba".

Bai tanka ba ya wuce zuwa part dinsa dan sauke ajiyar xuciya Zarah tai.

"Humm ji dan Allah daga tambaya harda wani hade rai muje sister".

Shiru Husnah tai duk jikin ta yayi sanyi bataso ace yadda su umma suke da son mutane ace Haidar a gidan yake ba.

Kitchen suka wuce yayin da Badiyat ta shigo ita da zeey da alama daga yawon banza suke a palor suka yada zango.

Gyale zeey ta cire ta cire kwalin kanta tana jawo jakarta ta dauko waya ta soma duba sa'ko 'kara ta saki tana kallon Badiyat tace.

"Zama bai same muba my 'kawar tashi muje yanzu".

A gajiye Badiyat tace "ina kuma daga dawowar mu"?.

Mikewa zeey tai tana cewa "a'a nifa matsala dake kenan hotel zamu tafi kedai ki taso kawai abin nema ne ya samu" badan ta so ba ta mike suka fita ashe gurin star zata kaita domin ya dawo daga tafiyan dayai.

Har Husnah ta gama abinda zatai ta koma gida bata saki jikinta taba kamar mara lafiya Innah data lura da ita ne ta tambaye ta.

"Asma'u lafiya meke damun ki naga kamar kina cikin damuwa babu walwala tare dake"?.


Kai Husnah ta girgiza tana sauke nannuyan numfashin daya tokare mata kofar shan iska muryarta a damuwance tace.

"Innah akwai matsala gidan nan da nake aiki ashe gidan su Wanda ya mana wulakancin nan ne dan mun shiga gidan sa.

"Subahanallahi da gaske Asma'u yanzu ya zamuyi shikenan yasa an kore ki ko" Innah ta fad'a har tana 'kwaruwa.

"A'a bai ma nuna ya sanni ba balle yamin silar aikin".

"To amma Asma'u ina jin tsoron haka yaron nan ba mutunci gare shi ba tunda ya nuna mana kawai kibar aikin".

Shiru Husnah tai zuwa wani lokaci tace "Innah na riga nai musu alkawari cewa zanci gaba da musu aiki kuma mutanen nan sun taimaki rayuwa ta idan nace na daina aiki a gidan su zasuyi wani tunanin dabam kuma banyi halacci ba".

"Shikenan to Asma'u Allah ya tsare fitina amma yaron nan ya nuna mana matsayin mu a gurinsa balle nace zamuje gurin alhajin muyi masa godiya".

Kai Husnah tai jinjina tana cewa "ai yanzu ma baku fasa ba domin gai da mai gaishe ka ko bazai amsa ba balle nasan zasu amsa basu da girman kai sam".

"To zamuje Allah yasa lokacin yana gida".

"Amin Husnah tace domin ita ma zata fi son ace baya gidan gudun ya wulakanta su.


Fatima na zaune a palon gidan su yayin da hajiya Hadiza ke kusa da ita shigowar Jabeer yasa ta kalle shi tana cewa.

"Wai yaya har yanzu babu wani labari game da 'batan su Husnah".

Kai kawai ya d'aga mata baiyi magana ba ya wuce sauke ajiyar zuciya tai tana kallon mamanta tace.

"Tsakani da Allah ace an rasa su kodai subar garin ne gabadaya wannan lamari yana bani tsoro mama kiga yau kusan wata nawa Allah yasa dai ba mutuwa sukai ba".

"Amin Fati bamu da ta cewa domin ni lokacin da wutar ta kama gidan nasu ban sani ba Saida aka gama komai nayi tunanin ko suna ciki sun 'kone wasu suka sun fito saidai suma basu san inda sukai ba".

Ran Fatima a bace tace "wallahi mama wutar ba'a banza ba akwai shiri a cikin ta tunda wasu sunce ai yan mata biyu ne suka shiga gidan a mota sai gasu sun fito da gudu suna rufe gidan daga nan akaga wuta na tsiri ta sama".

Kai Hadiza ta girgiza "Allah ne yasan yadda komai ya faru idan cutar su sukai zai saka musu tun a duniya ban bazasu taba yafe musu ba".

"Haka ne mama akwai ranar sakamako amma zamu dage da addu'a Allah ya bayyana su a duk inda suke".

"Amin kawai Hadiza tace daga haka sukai shiru babu bai cewa komai.


Bayan wata biyu kullum su baba nasa lokacin zuwa godiya amma tsoro ya hana su zuwa Husnah ta gaji harta hakura saidai tana matukar jin kunya ganin harta fara zuwa aiki asibiti basuje ba saidai ba yadda ta iya tasan gudun wulakanci suke shiyasa itama bata takura musu ba ta 'kyale su".

Da wuri ta baro asibiti ta hau adaidaita zuwa gida dayake juma'a ce babu dogon lokaci bayan tayi wanka da sallah ta huta tace zataje aiki sukai mata addu'a.

Tana shiga Zarah dake kusa da Haidar ta mike da murna ta tare ta "oyoyo sister ai na dauka baza ki zo ba yau".

Dan hade rai Husnah tai "me yasa Kika ce haka"?.

Zarah dake dariya cikin wasa tace "da naga yanzu kin zama doctor shiyasa nayi zaton haka".

Kai Husnah ta girgiza tana cewa "ai Zarah duk rintsi bazan bar muku aiki ba bazan manta daku ba domin kuna da karamci ko ba 'kashin yadawa bane".

"Kai sister kina da abin dariya me mukai miki dan d'an wannan abin ai ba komai bane".

Daidai umma ta fito Husnah ta duka tana cewa "barka da gida umma ina yini".

"Lafiya kalau Husnah ya iyayen naki suna lafiya".

Cikin jin kunyar rashin zuwa godiyar da basuyi ba yasa Husnah dakyar tace.

"Lafiyan su kalau umma sunce ma na gaida dake".

"Ayya ina amsawa".

Haidar ta kalla Wanda yai bala'in dauke kansa daga saitin su tace.

"Aliyu lafiya"?.

Kai ya d'aga mata kawai umma data mayar da hankalin ta wajen Zarah tace.

"Zarah ku shiga kitchen keda Husnah sai baba Rabi ta fito taxo ta huta itama".

"To umma muje sister" Zarah ta fad'a tana rike hannun Husnah suka wuce.

Tsaki Haidar yai ba zato Wanda yasa umma tai masa kallon mamaki domin indai ba mantawa taiba bata ta'ba jin yai tsaki ba sai yau tace.

"Wai kai 'kalau kuwa kake a kwanakin nan ka zama kamar mara lafiya meke damunka"?.

Kasa magana yai domin bazai ce mata akan Husnah ya damu ba bashi da hujjar dazai hana ta zuwa gidan su amma ko kadan baya son ganin ta gashi ta sake samun kusanci

Please Login or Register in order to submit comment