Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tabarmar da Mansur ya basu.

Xama tai tana kallon dukkan su biyun ganin yadda suka d'an rame jitai wani abu ya tsirga mata bakin ciki ya mamaye ta dakyar ta hadiye abunda ya tokare mata wuyar muryarta a sanyaye tace.

"Sannun ku da gida Innah".

Murmushin dole Innah tai ganin yadda'yar tasu take cikin yanayin damuwa da bacin rai kullum tana galauniyar yawo gidan mutane domin su saboda ta samu musu abinda zasu ci.

Abincin ta aje musu tana komawa gefe ta zauna tare da tagumi kawai tana kallon su.

"Ke kuma fa baza kici abincin bane naga kin koma nan"?.

'Dan kau dakai Husnah tai dan kar Innah ta gani ta goge hawayen fuskarta tana cewa.

"Na 'koshi".

"Kin koshi kuma Asma'u me kika ci"? Baba ya tambaya yana duban inda muryarta ke tashi.

"Eh baba na koshi kullum kafin na taho muku dashi sai ta bani naci".

"Gaskiya tana da kirki kuma yaranta ma babu wani abu da suke nuna min".

Cikin jin sassauci Innah tace "Allah ya biya ta ya bada tsawon kwana a dade anayi".

Mikewa Husnah tai tana cewa "amin Innah gaskiya hajiyan nan ba laifi tana da sakin fuska bari na d'an share mana nan din.

Daukar tsintsiya tai ta share sannan ta dauki bokiti ta tafi debo musu ruwa.

Hajiya Khubrah na palor sai Kiran numbern wayar Badiyat keyi amma ta'ki tafiya ganin d'anta ya fito yasa tace.

"Mubashshir ina zakaje kaci wannan kwalliyar haka"?.

"Zance zanje".

"Zance kuma gurin wa kenan"?.

"Gurin surukar ki".

"Wace suruka ta a ina take"?.

"Zaki sani mama zan fad'a miki amma ba yanzu ba".

Sharewa Khubrah tai tana cewa "am mubashshir kaje gidan yaya Yusuf ka duba min Badiyat mai ya samu wayarta ina ta Kiran ta amma a rufe".

"Ok ba matsala".

Gudun kada a gane yasa Badiyat dawowa gida akan lokaci sakamakon Abba baya gari yasa umma tambayar ta ina taje kwana biyu bata gidan ko kallon umma take batai ba balle tasa ran zata bata amsa.


Fitowar Badiyat kenan palor ganin wanda ke zaune yasa da ihunta tai gurin sa cikin murnar ganinsa tace.

"Ya mubashshir kaine yaushe ka dawo ban sani ba kuma baka Kira ni a waya ba gaskiya nayi kewar ka yaya kuma mama bata Kira ni ta fad'a min ba".


"Ba gani yanzu kin ganni ba mama ta kira wayar ki a rufe maybe tana son ganin kine ina kika sa wayar taki"?.

'Dan sosa kai tai cikin rashin gaskiya tace "eh wayar tawa ce bata guri na".

"Ina kika kaita"?.

"Tana gurin 'kawata".

"Kawarki meye amfanin wayar taki kenan dama karya kike ba karatu zaki da ita ba ko shashancin banza zaki shiyasa tun farko nace Abban mu kada ya baki amma haka mama ta goya miki baya, me kawar taki zatai da wayan"?.

Cikin in'kina da rashin gaskiya tace "yaya assignment zatai".

"Ina wayar ta ita bata da ita sai taki".

"Fashewa tata wayar tai".

Kallonta sosai yai zuwa wani lokaci yace "Badi'aa duk ranar dana rike ki jikin ki zai fad'a miki banason iskancin banza kisa tunanin ki guri daya kafin na saita miki zama".

Tasan halinsa sarai da zafin ransa shiyasa jikinta na 'bari tace "yaya kayi hakuri da gaske nake aro na bata zuwa jimawa zata kawo min".

Bai sake mata magana ba tana dai zaune kusa dashi jin ance.

"Dear sannu da zuwa na zaunar dakai ina shiri ne sorry".

A d'ari πŸ’― Badiyat ta juya ganin Zarah tsaye ta she'ka wankan 'kure maki yasa Badiyat cewa.

"Dear kuma? A ina amma dai ba da yaya mubashshir kike ba"?.

Banza Zarah tai mta ta bawa iska ajiyar ta kallon mubashshir tai wanda ke kallon Zarah tace.

"Tab yaya kai din Zarah kake so"?.

Kai tsaye ya bata amsa "eh ita nake so kuma auren ta zanyi shirin me kikai game da hakan"?.


"Wallahi yaya bata isa ka aure taba saidai ka auri wata tunda nima ya Haidar ya'ki sona".

Kallonta mubashshir yai "to ina ruwa na wannan tsakanin kune nikam na riga na dafe tawa a hannu my Zarah 😜"..

Cikin jin haushi sosai Badiyat tace "Zarah dai wannan Zaran da nake kallo take kallo na"?.

"Aunty zaki ce mata kada na sake ji kin Kira sunan ta".

"Amma yaya ai na fita".

"Kin fita saboda ni yanzu kuma ta juye ta zama auntyn ki".

Gyara zama Badiyat tai tana cewa "wallahi bata isa ba sunan ta zan Kira Wanda aka rad'a mata zara.......... ..


Bata karasa ba ta mike a zabure sakamakon yatsa dayasa ya d'alle mata baki yana cewa.

"Dan ubanki ni zanyi magana ki Musa min mara kunya kina so yanzun nan na karya miki 'kafa".

Takaici ne ya kama Badiyat ganin saboda Zarah ne ya mata haka fuuu tabar palon tana shigewa part dinta sai gata ta fito da gyale a kafada da jaka.

Cikin tsawa yace "ina zakije dama anan din yawon banza kike fita ko"?.

Tana turo baki tace "gida zanje gurin mama".

Ficewa tai kwafa yai yana cewa " zan zo gidan ne zaki bayani".


Husnah tana son fara business dan haka ta samu baba da maganar saidai sakamakon jin ba ita kadai zatai ba wai farko zubin adashe ne yasa baba yace a'a kada tayi rigima ta shigo ciki su shiga matsala su ba wani karfi garesu ba.

Suna zaune sakamakon yau hajiyan da Husnah ke mata aiki kwanan ta takwas bata gari yasa kud'i ya yankewa Husnah ga dole Saida ta sayo musu murhu da tukunya da yan abubuwan aiki da kayan abinci.

Da yake hajiyan yar jarida ce yasa ta sake wasu kwanakin akan Wanda tace zatai komai ya kare musu ga yanzu ganin sun samu madafa Mansur ba sosai yake zuwa ba sai lokaci zuwa lokaci.

Suna zaune baba dayai shiru yace "Asma'u nasan bara πŸ˜” ba sana'a bace amma zan jarraba mu gani".

Cikin rashin jin dadi Husnah data kalli baba tace "Amma baba da barar nan mezai hana na jarraba yin awara acan bakin titi"?.

"A'a Asma'u ina ji dake kamar tsoka daya a miya bana son wani abu ya same ki mu gwada abinda nace miki ban saba ba amma haka zan daure".

Saboda ba yadda zatai yasa tace "shikenan baba Allah yasa haka ne mafi alkairi".

"Yauwa Asma'u na Amin" Innah tana gefe batai magana ba saboda batasan me zatace ba addu'ar ta asirin su ya rufu.

Da kukan bakin ciki Badiyat ta shiga gidan su kira take da karfi cikin shagwaba.

" mama! Mama!! Mama!!!!.

Da sauri Khubrah ta fito har tana tuntube tace "menene badi'ah meya faru kukan me kike"?.

Zama tai jagwaf tana kwantar da kanta akan cinyar Khubrah tace " ba ya mubashshir bane".

"Tofa daga zuwa shine ya dake ki"?.

Kai ta girgiza "a'a ba gurin Zarah yaje shira ba wai auren ta zaiyi sai nace mata aunty dan naki ya buge min baki".

Cikin masifa Khubrah tace" kan bala'i uban aunty yaci uwatar zakice wato dan bashi da hankali Zarah yake ko uban me zaiyi da ita ga Batul yar gidan yaya Shafi'u tun yaushe take son shi aiko nida shine yau zai dawo ya same ni".

Tashi zaune Badiyat tai tana kallon ta tace "ita yayan ta ya 'kini shi kuma yaje harda wani ce masa dear".

"Uban dear bari ya dawo xai min bayani ke kuma ina son magana dake akan lamarin Haidar saidai ki tsaya ki kwana anan.

"To Badiyat tace tana mikewa ta shige part dinta tabar Khubrah sai bala'i take zazzagawa kamar mubashshir din na gurin.

Bai dawo gida ba sai magriba yana zuwa Khubrah dake binsa da harara tace.

"Gwani na gwanaye zo".

Karasowa mubashshir yai yana zama kusa da ita yace "lafiya naga kamar ranki a bace".

"Au tambaya ta ma kake lafiya kaga raina a bace"?.

"To mama yi hakuri meya faru fada min".

"Ashe mubashshir da nake ganin ka haka girman wofi ne baka da hankali uwar me zakai da Zarah kana gani 'kiri 'kiri yaron nan Haidar saboda bai gaji arziki ba ya'ki 'yar uwarka kai kuma ga Wanda mutuwar zuciya ta same shi shine zugwi-zugwi ka debi kafa kaje wai kana son Zarah ko? Son uban Zarah ko kishi baka taya yar uwar ka ku taru ku yake su dole Saida su kadai zakuyi zumunci".

Mamakin tane ya kama mubashshir sosai kawai ya tsaya kallon ta nadan lokaci kafin yace "Kai mama ya kike irin wannan maganar nikwa in banyi zumunci da 'ya'yan uncle Yusuf ba dawa zanyi"?.


"Dan ubanka duk yan uwa na basuyi maka ba idan auren dangin kake nema kaje dangi na mana ga Bilkisu yar gidan Sabuwa ko a cikin 'ya'yan baba Saleh Shafa'atu ko Rahma.

Kai ya girgiza "a'a mama ai nasan dasu na tsallake basuyi min bane su ba kalar rayuwa ta bane basa cikin tsari na".

Wani kallo Khubrah tai masa na baka da hankali tana cewa "iye lallai mubashshir ka ri'ka ban ta'ba sanin cewa kai sakarai bane sai yau wato saboda ka zama sako tumaki Zarah ce za'bin ka me zakai da ita".

"So mana mama auren ta zanyi".

"Aiko baka isa ba bada yawu na ba kaji na fad'a maka ka fita hanyar ta tun wuri dan bazan bari ka aure taba zanje har gidan naci uwart...........


Kasa 'karasawa tai sakamakon muryar muryar Abban su data ji sai hararar mubashshir da take d'an murmushi yai yana mikewa ya shiga part dinsa.

Abba na shigo ko sannu bai bari tayi masa ba yana kallon yadda take huci yace.

"Ke dawa kike magana yanzu zan shigo uwar wa zaki ci"πŸ™Š.

Kasa cewa komai tai sai raba ido take tana susa kamar mai ciwon 'kazuwaπŸ˜‚.

"Magana fa nake miki".

Cikin had'a ba'ki tace "waya nake yi".

"Da wa kike wayar"? ya kuma jefo mata tambaya.

Rasa da wa zata ce tai gashi babu wayar ma a gurinta tana bedroom.

Ganin tayi wa'ki wi'ki yasa yace "nace dawa kike wayar koda Mubashshir? Domin naji muryarsa".


Jin zai harbo jirgin taπŸ›¬ cikin in'kina tace "eh shine alhaji".

"Ok yabar gari ne ban sani ba"?.

"A'a yana nan".

"Yayi kyau" yana fadin haka ya wuce binsa tai da kallo tana sauke ajiyar zuciya tace.

"Kai alhaji akwai 'kwa 'kwa wannan ko kana da gaskiya saiya jawo abinda zaka sa'ba lamba tab da lawyer neπŸ‘©β€πŸŽ“ da an shiga uku.

Shiru tai daidai mubashshir ya sauya Kaya ya fito da sauri tace tana kallon kofar part din Abban tace.

"Mubashshir karka sake ka fadawa Abban ku gaskiyar abinda ya faru ko zai tambaye ka kaji na fad'a maka".

Dariya ta bashi wato duk abinda zatai tana matukar tsoron Abba murmushi yai yana kallon ta yace.

"Shikenan mama na za'ai duk abinda kika ce".

Ganin fita zai tace "kar ka koma gurin Zarah".

Nan ma cewa yai *to mama".

"Wacce Zaran kike magana"?.

Zabura Khubrah tai jin Abban da bata so ya sani ya kama ta tana maganar.

"Abba Zaran Abba Yusuf take fad'a" Badiyat tai maganar tana nufar hanyar kitchen.

Dafe kai Khubrah tai jin ta tona mata asiri cikin ya'ke ta dago tana kallon sa jin yace.

"Meya had'a su da Zaran zaije gurin ta"?.

Kamar Khubrah zatai kuka tace "karya fa Badi'aa keyi me zai hada su da ita shi da ba magana ce ta dame shiba".

Bai yarda ba amma dai ya shareta kawai so yake sai mubashshir din ya dawo yaji komai a bakin sa.


Kamar yadda baba yace wa Husnah haka akai badan ranta yaso ba suka fita barar tana ri'ke da sandan sa suna tafiya lokaci zuwa lokaci tana goge hawaye.

Ba laifi suna samun abubuwa domin ana taimaka musu wasu suna mamakin ganin Husnah tana rakiyar bara πŸ˜” Sam hakan bai dace da ita.


Wani katafaren asibiti suka tsaya domin akwai shaguna masu yawa a gurin nan ma suyi barar sun fara d'an zagawa kenan wasu likitoci su biyu sunzo wucewa ganin yasa dayan ya tsaya yana cewa.

"Ke me kike anan fad'a miki wannan gurin bara ne dalla fita waje ko nasa a fitar min daku nan ba kamar sauran asibitoci bane bana 'kazamai bane".

Takaici ne ya kama Husnah tana kallonsa tace "kai hakuri bamu sani bane da babu abinda zai shigo damu domin mu ba'ki ne".

"Ko ku ra'ba ne kuyi waje nakasassu basa shigowa nan kin wani kwaso makahon ubanki kuun taho bara maimakon yai sana'a kuna tare da wahala".

Juyowa Husnah tai a fusace tana cewa "malam ka iya bakin ka abun naka yai yawa karka kuskura kace zaka ta'ba min mahaifi akan sa zan iya abinda baka zato wallahi bazan 'kyale ba".

Binta yake da kallo tsaurin idonta da ido yaiwa securities magana irin masu fushi da fushin wani yuu suka yo caaa akan su.

Husnah tayi zaton abun nasa wasa ne sai kawai taga securities sun cicci'bi baba shiga sandan sa suna jansa kamar zasu yaga shi suna nufar bakin gate.

"Da sauri tace "Me kai haka dani ne fadan ka kasa su sakar min uba dan yafi karfin wulakancin ka".

Kallon sauran securities din yai yana cewa "me kuka tsaya jira ita ma ku fitar da ita".

Kafin Husnah ta farga taji garada sunyi sama da ita Saida suka kaita har bakin gate sannan suka dire ta saita mike suka hankado mata baba suna komawa tare da rufe gate din.

Talau latau baba ya kwashi tuntu'be zai muguwar faduwa aguje Husnah ta tare shi ya fad'o jikinta har gefen bakinsa ya fashe ya samu kurjewa a gwiwar sa.

Wani irin 'bacin rai ne ya rufe Husnah tana kuka ta daga baba suka bar gurin ganin yana dingishi yasa ta lura da ciwon da yaji a wani chemist suka tsaya domin a duba lafiyan shi.

Kallon sa dayan doctor yai yana cewa "haba Haidar mekai haka? Kamar ba kaiba idan wannan mutumin yaji ciwo fa kaja yadda suke jansa"?.

Tsaki yaja mai karfi cikin nuna rashin damuwar sa ga abinda ya aikata yanzun yace.

"Haka ne ya dace dasu gobe ma sai su dawo nayi musu da sauki".

"Uban me kayi musu da saukin kasa anci mutuncin su wallahi Haidar kaji tsoron Allah na lura you are not so kind πŸ™„".

"Kwarai fad'i ka da d'a haka nake baka gani glass ne a fuskar sa maybe ma ba makaho bane karya suke".

"A'a Haidar ka bari fa" Habeeb ya fad'a yana girgiza masa kai alamar bai kyauta ba.

"Shikenan muje manta dasu kawai" Habeeb yasha mamakin abinda Haidar din yai sai yake gani kamar ba shiba.


Lokacin da aka gama duba baba suka koma gida haka Husnah ta hada kai da gwiwa tana ta kuka har muryarta ya dashe babu abinda take gani sai fuskar Haidar sanda yake cewa a fitar masa da baba da irin jan da securities ke masa.

Cikin lallashi baba yace "Asma'u kiyi hakuri laifi nane domin kince min kada nayi bara na'ki amma komai me wucewa ne shi kuma yaron dayai mana haka Allah ya shirye shi".

Cikin kuka Husnah tace "baba kaine abinda nake dashi bazan so a wulakanta min kaiba na tsane shi domin yaci zarafin ka kuma bazan ta'ba yafe masa ba".

Innah da tunda suka dawo itama take share hawayen damuwa tace "ya zamuyi mu kuma a haka zamu kare rayuwar mu cikin gagari da rashin kwanciyar hankalii na yau daban na gobe daban".

"Zamu samu mafita baza muci gaba da zama haka ba" baba ya fad'a muryarsa kanaji kasan yana daurewa ne kawai.

Karaf Innah tace "mafitahi daya ce shine mu koma garin mu".

Sauya fuska baba yai yana cewa "babu inda zamuje muna nan ni bani da wani gari" yana gama fadin haka ya mike ya yabar gurin.

Da kallon mamaki Husnah ta bishi kafin tace "wai Innah meyasa kwata-kwata baba baya so a masa zancen garinsu bayan ahlin sa na can"?.

"Wallahi ban sani Husnah ada ko 'ban'bara da gida baiso amma rana daya ina zaune ya shigo hankalinsa a tashe yana kwalla min kira garin zamu bari".

Husnah data kasa dauke idonta akan Innah tace "to meyasa baya son komawa alhali ni bansan kowa nawa ba"?.

Nam ma inba cewa tai "ban sani ba Husnah saidai gaskiya mahaifin ki yana da makiya a garin".

"Kin San su kenan su waye"?.

Murmushi mai nuna gano gaskiya Innah tai tana kallon Husnah tace.

"Abokinsa na hannun damansa da kuma yayan sa da suke uba daya".

Dan zaro ido Husnah tai cikin mamaki tace "me kike tunanin sunyi masa"?.

Kai Innah ta girgiza "babu abinda nake zargi Asma'u bar maganar haka".

Rike hannun ta Husnah cikin marairaicewa tace "dan Allah Innah ki fad'a min koda kadan daga ciki ina son sani"πŸ˜”.

Gyara zama Innah tai tana cewa "shikenan zan fad'a miki na kasance 'ya guda daya a gurin mahaifina kuma yana dukiyar shanu da kayan gona ga sana'ar saro kayayyaki da yake a birni yana kawowa garin mu ganin irin kudin da yake dashi yasa samari da yawa sukai caaaa a kaina kowa yana bukatar aure na cikin su harda yayan mahaifin ki Muntari.

Babu wanda yamin a cikin su badan nafi karfin auren su ba a'a saboda banga Wanda yake sona dan Allah ba kowa sai dan kudi shiyasa na'ki su.

Ana haka mahaifin ki ya dawo daga tafiya gurin dangin mahaifan sa da suka kasance a birni sai muka hadu dashi a rafi har soyayya mai karfi ta shiga tsakanin mu.

Kuma babu bata lokaci aka gama komai na maganar auren mu bayan bikin da wata daya mahaifina ya kamu da rashin lafiya sosai wacce ba'a ja kwana ba ya rasu😭.

Gashi mahaifiya basa tare da baba sai wata muguwar mace da yake da ita Asabe wacce take matukar gallaza min bani da wani jin dad'i har saida nai aure nabar gidan.

Amma duk da haka wani agolan d'an ta bai rabu dani ba yaso saina aure shi Asabe ma ta matsa min lamba sosai saina aure shi amma na'ki amince masa domin ita ma harin ta kudin ne.

Bayan rasuwar mahaifina sai komai ya dawo hannu na ni kuma na damka shi ga mahaifin ki duk gari ya dauka babanki ya min asiri ya mallake komai dama dan haka yasan siddabarun dayai ya aure ni maganganu iri iri marasa dad'i suna samun mu haka muka share.

Baban ki mutum ne na kwarai me gaskiya da rikon amana dukiya ta dana bashi bai ha'ince niba ko sau daya kuma cikin karamin lokaci dukiyar ta sake habbaka.

Wata rana da dare sosai wuta ta tashi a gidan muka rasa komai ya kone ranar muka fahimci kaf garin babu me kaunar mu da gari ya waye babu wanda ya kula mu balle yace Allah ya mayar.

Sai dariya da ake mana wai yanzu aga dame muka dogara rayuwa ce ta fara sauya mana hatta da kud'in mu idan mukaje sayan abu agarin baza a sayar mana ba.

Haka babanki yazo dangin sa na mahaifiya gurin kawunsa ya bashi jari ya koma da wannan jarin ya dora sana'a muka ci gaba da zaman hakuri.

Bazan ce miki abinda muka rasa ya dawo ba amma mun samu rabinsa nan munafikai da masu dariya sukai laushi.

Ganin da sukai muna kara samun Komai kamar kyauta ake bamu yasa wutar kiyayya da barazana ta sake kunnuwa sai baban ki ya sameni wai abokinsa ilu yace zasu fara kasuwanci tare zuwa birni saro kayayyaki kamar yadda mahaifina keyi.


Bance masa a'a ba ya sayar da kadarorin da suke aje kamar gona shanu da awakai bai bar komai ba sai tsabar kud'i ranar tafiya suka tafi sayo kayan.

Sun to sari sosai naban mamaki suka kawo kauyen nan da nan Kaya ya kare sai abokin babanki Muntari yace shi bazai koma wannan karon ba sai wani jikwan.

Shi kuma iro yayan sa yace wai mezai hana ya sayar da kadarorin sa na gado sana'ar zatafi karfi kamar wanda ya shanye shi haka ya d'aga komai ya sayar ya kara ninka kud'in akan wancan.

Ranar tafiya ya tafi shi kadai ya sayo amma me kawai yaci abincin ya fita shago ba'a dade ba sai gashi ya dawo hankali tashe yana kwalla min kira ina fitowa daga daki yace.

Wuta ta kama shagon nasa gabadaya ba'a samu koda allura ba komai ya kone dan haka na shirya kayana mubar garin na shiga bashi amma yace.

Ina bazai sake koda wuni a garin ba balle kwalla ji yake shima kamar ana hura masa wuta a jikinsa ganin dayai banda niyyar yin komai yasa shi shiga daki ya soma tattara mana kayan sawar mu nidai ina tsaye bance komai harya gama sannan ya fito da kayan waje ya dauka a kansa ya soma tafiya cikin sauri.

Ganin danai da gaske yake yasa dole nasa hijab nabi bayansa ba Wanda ya ganmu ta karamar kofar garin inda babu gidaje da yawa tanan muka bi har mukai nisa da kauyen muka isa garin wasu fulani.

Anan mukai kwana biyu kafin muka sake daukar hanya bamusan inda zamuje ba sai kace anyi mana koran maita mun kusa wani gari muka hangi wata irin ba'kar guguwa mai duhu ta taso munso shiga garin kafin ta iske mu amma ina tun a dajin ta ritsa mu

Baka ganin komai ga wasu irin maganganu da ake da wani yare ana dariya a cikin iskar bansan ya akai ba sai jina nai an d'aga ni sama ana juyawa dani har shidewa nake kamar raina zai fita zuwa wani lokaci aka sake ni na fad'o kasa a sume.

Tunda safe har magriba muna gurin babu kowa nidai dana farfad'o naga babanki kwance kamar gawa baya motsi yunkurin tashi na taimaka masa nake amma na kasa kafa ta a harde ga ciwo da take min.

Ina kallon sa ba damar zuwa inda yake haka na kwana banyi bacci da safe yadda kasan ba halitta mai motsi shiru ko'ina har rana ta dago ganin dan motsa yasa na ja kafata naje gurin da yake ina Kiran sunan sa

Ya bude ido amma sai naga kamar ba kallona yake ba sake rufe idon yai ya bude a banza yasa hannu ya murde d'if

Sai yace min baya gani cikin tashin hankali nace baya gani yace eh ga yunwa muna ji mun kwana da ita mun tashi da ita

Har wani bawan Allah yazo wucewa na roke akan ya taimake mu naimar bayani Kiran matarsa yai ta taimaka min na tashi ina jan kafa mukaje gidan mutanen nada karamci domin sun kula damu sun batar da kud'in su wajen nemo mana magani amma Abu yaki karewa


Sai hakura mukai mun zaune dasu tsawon shekara kafin sukace mana su fulanin tashi ne zasu sauya muhalli zasu 'kara gaba bamuji dadi ba domin mun ruga damun saba haka muka rabu rabuwar mutuncin zaman tare kowa yana mararin Dan uwansa

Kuma sun dau kyautar kud'i sun bawa babanki ni kuma aka bani sanda na ke jingina dashi wajen tafiya da wannan kudin muka hau mota zuwa gurin dangin babanki na uwa nan ma wanda mukaje gurin nasa ya rasu 😭 lokacin watansa tara da rasuwa sai d'an sa guda daya kuma baya gari ya tafi waje

Gidan kuma dora shi a hannun jari wato sai dashi za'ai hankalin baba yai mugun tashi ga baya gani ga d'an guzurin mu kare haka muka koma abun tausayi wani mutum ya taimaka mana da wani shago muna kwana

Ganin zaman jiran shi bata lokaci yasa muka sauya anguwa a acan muka karbi hayar wannan gidan daya kone zuwan mu da wata shida aka haife ki anan kika girma kuma bansake jin labarin komai game da garin mu ba wannan ne abinda ya faru a wancan lokacin" Innah ta karasa maganar tana sauke ajiyar zuciya da duk wani takaici da take tunawa.

Husnah wacce tunda aka fara maganar take kuka jin rayuwar da mahaifan ta suka sha a baya.

Mikewa tai tana cewa "amma umma mezai hana duk da haka mu koma zanwa baba maganar".

Katseta Innah tai "a'a Husnah karki soma fada ki kyale idan fa rabo wata rana zamu koma kamar yaune".

"Ni umma damuwa wai dama makantar sai daga baya ya samu ba tun asali ace"?.

"Eh daga baya ta same shi".

"To amma umma mezai hana mu dage masa da maganin gargajiya ko zamu dage dayi masa ko zamu dace.

"Ina muka ga kudin Husnah"?.

"Allah zai kawo hanyar samun zan sake dagewa fiye da da".

Kallon Husnah tai cikin tausayawa da kuma nuna kwazon ta bata sarewa balle ta gaji ta kosa akan abinda take musu lallai ba shakka sunyi dacen 'ya ta gari, kallonta ta kuma tana cewa.

"Shikenan Husnah Allah ya bud'a ya bada sa'a ya tsare ki".

"Amin inna na gode da addu'ar ki gare ni" mikewa tai tana cewa "Innah bari na gano ko hajiya ta dawo daga tafiyan dan lokaci yaja".

"To Asma'u saikin dawo" Innah ta fad'a tana binta da kallo yayin da Husnah ta dau hijab dinta tana ficewa daga gidan.

Badiyat tayi kusan wata daya a gidan su Khubrah tana 'kwar'kwance ta da sake tunzura ta da bata shawarwari baudaddu ranar da zata tafi haka ta bata magunguna iri iri nasha dana wanka da duk saboda Haidar ya sota.

Tun ranar data koma ta soma aiki da maganin da kuma salon rashin mutuncin Khubrah

Please Login or Register in order to submit comment