Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana kallon yadda wutar keci gashi basu tsira da komai ba daga suturun su na sawa zuwa sauran kayan amfani wasu hawaye ne taji suna zuba mata ba 'kakkautawa.

Jin Kiran sallar magriba yasa ta dafe kanta cikin kuka tace "yanzu baba ina zamuje waye zai taimake mu"?.

"Asma'u ni kaina ban sani ba bani da wannan amsar tambayar taki".

"To baba mezai hana mu koma garin ku inaga zaifi inda dangin ka suke".

"A'a Asma'u bazan koma wannan garin ba".

"Meyasa baba"?.

"Saboda ko sunan garin bana 'kaunar ji gara zama na anan komai rashin jin dadin da nake".

Kai Innah ta girgiza tana cewa "ya kamata mu samowa kanmu mafita".

Goge hawayen fuskarta Husnah tai tana cewa "muje ni nasan ina zamuje".

Rike sandan baba tai inna kuma tana dogarawa da nata sakamakon kafar ya soma mata sauki suka nufi wata hanya.

Sallama Husnah tai a wani wuri wanda kana gani kasan gurin saida abinci ne.

Wata mata ce ta fito ganinsu tsaye yasa tace "su waye ku lafiya"?.

Matsowa Husnah tai "lafiya aunty kilima baki gane niba"?.

Rike baki tai " na gane ki yanzu Husnah ko?.

"Eh nice".

"To me kike yi a daren nan wadannan ba mahaifan ki bane ina zakuje"?.

Sauke ajiyar zuciya Husnah tai "aunty ni kaina ban sani ba gidan mu ne ya 'kone shine nace muzo nan ki taimaka mana mu kwana zuwa wayewar gari".

"Ayya Allah sarki Husnah ku shigo kinji ba damuwa".

Shiga ciki sukai ta basu gurin zama tare da kawo musu ruwa sukai alwala da sallah sannan ta kawo musu abinci kuma ta basu gurin kwana".

Saida suka samu nutsuwa baba yace "Asma'u wannan matar a ina kika santa naji kina ce mata aunty"?.

"Gyara zama Husnah tai tana cewa "amm baba auntyn muce a school din mu ta junior kasan anan muka hadu da Fatima har muka saba inata haka".

"Gaskiya tana da kirki Allah ya biyata".

"Amin baba".

Washe gari bayan sun karya ganin Husnah iya daurin zani ne a jikin ta sai hijab yasa kilima ta bata Kaya cikin na yarta.

Sannan ta tambaye ta "Asma'u yanzu kuma ina zakuje"?.

Sauke kai Husnah tai cikin yanayin damuwa tace "wallahi aunty ban sani ba zan duba mana wani gidan hayar ne saimu kama".

"Ok yayi zan hada ki da wata 'kawata tana bada haya kuma idan na bata labarin abinda ya same ku zata rage muku kudin hayar akan yadda kowa yake biya ke kuma Husnah sai kizo kina min aiki anan Wanda zan rika biyanki duk wata kema saiki samu ki biya hayar".

Godiya sosai Husnah tai mata sannan ta tambayi su baba ganin sun amince yasa tace 'yarta ta zauna mata a gurin bari ta rakasu ta dawo.

Da gudu Fatima ta shiga gidan su day kukanta tana kwalla kiran mamanta da sauri Hadiza ta fito ganin ta haka yasa tace.

"Lafiya kukan me kike"?.

Kai Fatima ke girgizawa dakyar tace "mama Husnah".

Cikin kaduwa tace "meya samu Husnan"?.

"Mama gidansu ne ya 'kone".

"Yaushe yanzu"?.

"A'a wai tun jiya".

"To kuma suna ina a wanne wurin suka kwana"?.

Kara volume din kukan ta Fatima tana cewa "nima ban San inda suke ba mama wai tun jiya suka bar anguwar".

"innalillahi wa inna ilaihi raji'un Kenan yanzu ba Wanda yake da tabbacin inda suke ya akai bamu sani ba tun jiyan"?.

Jabeer ta kalla Wanda ke tsaye a kofar part dinsa tunda yaji abinda suke cewa ya daskare guri daya tace.

"Jabeer kaji abinda ya faru ko gashi gobe zaka koma kuma ba'a San inda sukai ba".

Kasa magana yai sakamakon ya rasa me zaice domin yanzu fitowar dayai a nasa burin gurinta zaice ya mata sallama zai koma daga hutun daya zo.

"Wai baka jini bane Jabeer" mama ta sake maimaitawa.

Sauke numfashi yai yana karasowa tsakiyar palon inda suke yace "mama bansan me zance miki bane abin ne yafi karfin hankali na".

"Jabeer dole mu nemo su ina zasuje su da basu San kowa ba gashi kayansu ya kone ina son mutanen nan domin ina matukar tausaya musu".

"Zan binciko su" Jabeer ya fad'a yana fita yayin da Fatima ta shige part dinta tana sake share hawayen dake zuba mata.

Kamar yadda kilima ta fad'a musu ta dauke su zuwa gurin kawarta kuma ta roketa alfarmar ta rage musu kudin haya sannan ta taimaka musu da d'an kayan abinci da kayan sawa kuma Husnah ta fara aiki tare da ita ta shiga islamiyan anguwar.


Suna zaune baba daya gama naxari yace "Asma'u zama haka bazai yiwu ba dole saimun tashi tsaye nikam yanzu sana'a zatai min wuya Amma zamu jarraba yin bara😔".

Zaro ido waje Husnah tai "bara kuma baba😨"?.

"Eh Asma'u bara domin kinga duk da ta rage mana kudin hayar gidan nan yafi na alhaji kuma bai kamata daga farawa mu gajiya ba sannan idan muka sake wannan damar ta kubce mana mukabar gidan nan tofa zamu shiga wani hali".

"To Amma inaga baba mu nemu wani abun yin Amma Banda bara".

"Eh Asma'u bawai dauwama zanyi ina yi ba jarrabawa zamuyi".

"Shikenan baba zamu gwada " Husnah ta fad'a badon ranta yaso ba.

Tana gurin aikin ta tare da kilima taji 'yarta tazo tana cewa wasu sunce a had'o musu abinci na dubu dari🤔.

Mamaki ne ya kama Husnah aranta tace "tofa su waye wadannan sai kace sun hada dangi dasu gara da kiciciya🙃.

Katse mata tunani kilima tai da cewa "Husnah Ibrahim a fara hada musu ga Najat nan kuyi tare".

Cikin girmamawa Husnah tace "to aunty".

Fara hada kayan sukai tare dan tsaki Najat taja tana cewa "nifa banason irin wadannan yan karya su rika zuwa nan dan wasu kudin rance ne suke zuwa suyi burga dashi kar wata rana muna zaune lafiya muga motar yan sanda ta Parker anan".

Murmushi Husnah tai tana cewa "a haba dai duk Wanda kikaga yazo cin abinci da kudin sane ba wani yan sanda da zaki gani sun xo".

Dauka sukai suna tafiya daidai sun ajiye Najat tace "yo ai yanzu ne 'yan 'karyar sunyi yawa".

Ba zato sukaji ance " kan uba dama baki mutu ba"?.

Da sauri suka juya ganin Badiyat da zeey ga wani saurayi yasa Husnah ta fahimci da ita take Amma saita basar tai kamar batasan komai ba".

Zasu wuce Badiyat ta jawo ta tana cewa "a 'kwarai lallai kam wato har nice zanyi magana kimin banza to wallahi baki isa ba kinyi kadan".

"Meye damuwar ki dani ne idan ma fadan ne ga da jakar da zaki bari muyi ba dake saki tumaki ballo jaka ba Nina wuce ajin ki".

Sha'ka Badiyat ta kawo mata zamewa Husnah tai tana kallon ta da mamaki tace.

"Waike mene matsalar ki dani kodai marin danai miki a wancan lokacin yasa kin fara hauka ne da alama kina bukatar 'kari aiko yanzu zaki samu idan kikasa wasa dan nafi karfin ki ce zaki raina ni wuce nan🙄 naga so kike jikin ki yai tsami".

Kinsan koni wace dahar kike iya fad'a min maganganu son ranki"?.

Ba tare dajin wani d'ar ba Husnah tace "to wace ke fad'a min ba haihuwar ki akai kamar kowa ba wai me kika dau kanki"?.

Xeey dake gefe tace "wa kike da suna lallai kin shiga tarkon mu zamu gani komu koke kin shiga uku. tunda har kikai jayayya damu zakigani saimun gasa miki aya a hannu".

"Ni kuma saina soya muku gyad'a aka domin nima ba 'kyale ku zanba niba 'kanwar lasa bace mu zuba zaku gane kuren ku".


"Husnah me kikeyi ba kin ajiye musu ba"?.

Juyawa tai ganin kilima yasa tace "eh aunty mun kawo musu".

"Ok yayi kuje ciki kuma ga kwastomomi suna jira".

Wucewa sukai cikin mamaki Najat tace "wadannan kuma masu zubin turmin fa daga ina meya had'a ki dasu"?.

"Humm barni dasu kawai bazan kyale suba nima yanzu aka fara kefa sune suka kone mana gida".

Zaro ido waje tai "wadannan din? Kodan ba mamaki kina ganin shu'umai ne zasu aikata fin haka ma Amma ya kamata ki rabu dasu karki biye musu".

"Eh bazan biye musu ba amma bazan kyale suba idan suka nemi raina min hankali ba ruwa da sudin su waye".

Kai Najat ta jinjina "hakan yayi amma kinsan umma bazata yarda ba kiyi a hankali kada taji ku".

Murmushi Husnah tai tana kallon Najat tace "Koda zasu zo gaba su tare ni ta siyasa zanbi kamar yadda nai yanzu domin idan na nuna inajin tsoron su shikenan sun samu damata".

"Kema kuma tanan kinyi gaskiya domin da ganin su tantirai ne na ajin 'karshe saidai ki bi a sannu duk inda kike kina hankalce dasu".


"Na yarda dake da shawarar da kika ban zanyi abinda Kika ce".

Bayan wata biyu xeey tana zaune a palon gidan su da waya a hannunta shigowar mahaifinta kenan ya karaso inda take yana cewa.

"ZAINAB!!!" da karfi har saida ta zabura tana dagowa ganin yanayin sa yasa muryarta na rawa tace.

Da,dad,dadd...............

Bata iya karasa ba ya dauketa da mari dukka kumatu biyu 'kara ta kwalla tana Kiran.

"Ummi ki zo ki taimaka min dan Allah daddy kayi hakuri".

Da sauri ummi ta karaso palon ganinsa yasa taja ta tsaya bata karasa ba tasan ruwa baya tsami banza bai cika dukan yaransa ba Saida hujja babba balle zeey data girma.

Cikin tsawa yace "ina kika kaisu dama nace kije gidaje na kice su baki kudin haya saki nai? Yau ko sai jikin ki ya fada miki".

Kuka xeey keyi sosai tana kallon ummi ko zatai magana amma taga ta juya ina ta fito".

Damkarta yai yana cewa "gidan uban wa kika kaisu bayan kin kone musu kaya wallahi saikin biya su kayan su".

"Dama dan ubanki idan bana nan rashin da'a kikewa mutanen da suke karkashi na? aiko zaki gane kuren ki".

Kasa magana xeey tai saboda azaba sai kuka da take ransa yai mugun baci ga shirun datai ya sake tunzura shi part dinsa ya shiga yana dauko bel ya dawo Saida ya zane ta tas sannan da ihun ta tace tasan inda suke zata raka shi.

Cilla ta yai a mota sukaje har gurin kilima ya tambaye ta inda su Husnah suke.

Kai kilima ta girgiza tana kallon sa tace "ai Husnah yau kwanan ta ashirin da biyar bata zuwa aiki sun sauya anguwa kuma bansan inda suka koma ba me gidan hayar ce ta zuba wasu ta fitar dasu".

Tsabar tsananin 'bacin rai baisan lokacin daya kuma fidda hannu ya tsinke xeey da sabon mari ba har Saida kilima ta tsorata da marin ganin jini na zuba a hancin xeey din.

Bai damu da yadda jinin ke zuba ya kuma kifa mata wani yana cewa "wallahi Zainab saina ci ubanki zaki gane kuren ki saikin nemo min mutanen nan idan kuma ba haka ba sai kinga yadda zanyi dake daga nan ki zarce ki nemo min su duk inda suke a fadin garin nan".

Yana gama fadin haka ya wuce yana shiga mota xeey na kallo ya tafi ya barta a gurin durkusawa tai tana kuka ga zafin da fuskarta ke mata kamar wuta.

Mikewa tai tana goge hawayen fuskarta tace "na rantse da wanda yake dani ko zan rasa rayuwa ta saina Nemo ki saina halaka ki dani kike zancen ni dake ne" adaidaita ta tare tana shiga kilima data bita da kallo tace.

"Tofa ita kuma wannan meye hadinta da Asma'u me yasa mahaifinta ya mareta gaskiya akwai abu a 'kasa".



Umma na zaune a palor Rabi data fito zata wuce kitchen durkusawa tai tana gaida umma kallonta umma tai be"Rabi'atu Kira min badi'ah a part dinta".

"To hajiya" Rabi tace tana yin hanyar da zata shiga part din.

Kwankwasa kofar tai jin shiru yasa tace "Assalamu alaikum".

Nan ma jin anyi mata shiru yasa ta bude kofar tana shiga ganin Badiyat zaune a bakin gado da waya a hannunta yasa tace.

"Badi'ah hajiya na kira".

Banza tai mata har Saida ta sake maimaitawa cikin tsawa Badiyat tace "wai banji bane kome dalla malama bar nan kinzo kin wani damu mutane bazan zo ba".

Kallonta Rabi tai da mamaki wato yarinyar nan bata da mutunci bata ganin girman ta saboda tana matsayin yar aiki amma tasan duk tsiya ta girmi uwarta.

"Me kika tsaya kallo naga kin 'kwalalo min ido ko yau kika ta'ba gani na"?.

Rabi bata tanka mata ba kawai ta juya tana ficewa daga dakin tsaki Badiyat tai tana mikewa ta dau karamin gyale tasa tana fita da 'ku'kuni.

"Itama umman ko uwar me zanyi mata oho baza abar mutum ya huta ba".

Shiga palon tai ba sallama balle gaisuwa maimakon ta zauna a kasan carpet sai ta d'are kujera tare da hade fuska tace.

"Gani".

Kallon mamaki umma tai mata daga baya ta girgiza kai wato yarinyar nan baza ta canza ba duk nusar da ita da ake dan gaba amma bata ganewa basarwa umma tana kallon hanyar kitchen inda Zarah ta fito tace.

"Dama ba wani abu bane badi'ah naga tun zuwan ki gidan nan bakya ko gwada shiga kitchen duk da ban sani ba gashi na dauko wacce zata rika koyawa Zarah girki iri iri shine nace Rabi ta min magana dake kema ki fito a koyar daku tare".

Kau dakai Badiyat tai a kaikaice take kallon umma cikin rashin nuna kulawa tace.

"Me girki dai wai nufin ki na zauna wata katuwar ta koya min girki tabb never in history wuce nan 🙄 har abada ni na iya komai saidai a koyar da Zarah din domin ita ke bukatar haka amma ba niba idan dalilin Kiran nawa kenan na tashi na tafi"? .

Cikin takaici umma tace "jeki babu komai, amma gani nai ya dace ace Koda kin iya ki sake kwarewa shekarar ki guda da watanni a gidan nan Koda wasa baki ta'ba yin hanyar kitchen ba ki rika shiga sau daya ko ranar weekend ne".

Mikewa Badiyat tai "tabb lallai wallahi bazan ba bazan iya ba".

"Kada Allah yasa ki iya waike badi'ah wacce kalar rashin tarbiyya ke damun ki na fuskanci kin fara kamuwa da ciwon hauka to wallahi nawa yafi naki zan saita miki zama a gidan nan mahaifiya ta ba abar wasan ki bace akan ta jikin ki zaiyi tsami😡" Zarah tai maganar ranta a bace.

Juyawa inda take Badiyat tai tare da tabe baki tace "ke kuma tsiga tsiyau kazar 🐥🐤🐣🐔 mutsiyata ban sako dake ba".

Zarah zatai magana sukaji an shigo palon da ihun kuka da kururuwa duk kallon ta suke zuwa tai tana rungume Badiyat data tsaya kallon ta baki bude tace.

"Xeeta lafiya meya faru kike kuka haka? Yimin bayani".

Kuka sosai xeey keyi tana cewa "daddy nane ya kore ni wai saina nemo masa yarinyar nan ko kuma na hakura da zaman gidan mu".

"Kai ji daddyn nan idan kin bar masa gidan ina zakije kuma"?.

"Oho masa shi ya sani wallahi diyat duk inda yarinyar nan take saina nemo ta na hukunta ta".

Kai Badiyat ta jinjina "kwarai xeey ki nemota ni kaina na tsane ta zan taya ki muci uwar ta da yaji kuma mu zauna lafiya".

"Indai haka ne muje mu shirya yadda zamuyi" hanyar shiga part din Badiyat sukai aguje Zarah taje tana tsayawa a bakin kofar cikin yi mata kallon kin fara hauka ne tace.

"Baki Isa kin shiga part din nan ba saidai kiyi gidan ku wato saboda samun gu akuya🐐da tukin tuwo har 'kawaye zaki rika kwaso mana ki sani nan gidan tarbiyya ne ba club ba saiki San inda dare yai miki".

Ture Zarah Badiyat tai zata shiga cikin fusata Zarah ta mata wata hankad'a sai gata ta zube kasa rim.

Nuna ta Zarah keyi tace "wai ke mai kika dau kanki? Gani kike bazan iya cin uwarki ba kome idan kika sake kawo min raini Sai nayi buju buju dake ina 'kyale kine saboda banason harkar shashanci wannan ma kadan kika gani".

Da sauri umma tazo tana cira Badiyat cikin fad'a tace "Zarah me kikeyi haka? Ina ruwan ki da ita bansan shashancin banza zan sa'ba miki ran ki wuce naki gu".

Wucewa Zarah tai tana hararar Badiyat dagota umma tai tana mata sannu ta ce.

"Kiyi hakuri badi'ah zan mata fad'a jeki".

Fusgewa Badiyat tai cikin rashin kunya tace "dalla gafara can bansan munafinci wato ni zaki mayar wacce bansan me nake ba ki kifta mata ido sannan kizo kina bani hakuri".

Kallonta umma keyi "meyasa Badiyat baki da tarbiyya ne shin ba'a koya miki girmama manya ba bakisan darajar kowa ba".

Kad'e jikinta Badiyat tai tana cewa "saiki koya min gwana uwar shishshigi aikin banza kawai xeey muje naga wanda zai hana" shigewa part din sukai yayin da suka bar umma da mamakin daya cika mata xuciya na zagin da Badiyat tai mata kamar wata sa'ar ta.


Husnah na zaune tare dasu baba a wani shago da ko murfi babu ba tabarma sai kasa domin ko filasta babu ji sukai an rafka musu sallama.

Jin muryar namiji yasa baba ya fita bayan sun gaida ya dubi baba yana cewa "am baba dama nace nine mai shagon nan sakamakon kud'i sun tsaya min ne na kasa gyarawa yanzu kuma ina so na dora aikin shine nace bari na fada muku ku samu wani gurin zaman😢".

Duk abinda suke Husnah na ji cikin faduwar gaba ta mike tana fitowa kallon sa tai murya a sanyaye tace.

"Zamu tashi amma dan Allah ka bani kwana biyu na nemo mana wani gurin da zamu zauna yanzu idan mun tafi bansan inda zamu shiga mu kwana ba bamu da kowa bamu da komai".

Kallonta yai cikin tausayawa yace "shikenan nan na baki kwana uku ki nemo".

Sauke ajiyar zuciya tai tace "nagode".

Baiyi magana ba ya juya yana barin gurin cikin damuwa Husnah data bishi da kallo tace.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un wannan wacce irin rayuwa muka tsinci kanmu a ciki baba me zai hana mu koma garin ku tagaiyarar tai yawa bani da kwanciyar hankali anan idan har kuna bacci nakan kwana a zaune ina gadin ku bana son wani abu ya cutar min daku kune kadai abinda nake dashi a duniya daku nake alfahari".

Jin shiru yasa ta juyo ganin hawaye a idon baba yasa batasan lokacin data fashe da kukan bakin ciki ba da sauri baba ya riko hannu ta yana cewa.

"Asma'u kiyi shiru jarrabawa ce kiyi hakuri komai yai zafi maganin sa Allah ki rike addu'a ita ce makamin mumini".

Kasa magana tai kawai ta tsaya kallon su da tunani iri iri na tashin hankalin ta yadda zata sama musu gurin zama.

Daga gida bayan rashin arzikin da Badiyat taiwa umma hotel xeey ta gayyace ta tare da kama musu d'aki da abincin da zasu ci na tsawon sati.

Badiyat hankalin ta kwance domin tasan daddyn Zarah baya gida dama shine barazanar ta umma kuwa da ita da babu duk daya bata mayar da ita mutum ba.


Husnah tafi sati tana yawo da binciken inda zasu zauna amma saidai tasha ranar banza ta dawo bata samu ba wani lokacin takan tafe a layi tana share hawaye masu zafi.

Kamar yadda yace musu bayan kwana goma ya dawo cikin sanyin murya wacce kana ji kasan zazzabi ke Shirin shigar ta Husnah tace.

"Bamu samu gurin zama ba amma ba matsala ga shagon ka nan kar mu takura maka ko mu shiga hakkin ka kaima sana'a zakai hakan ma mun gode domin da wani ne bazai yarda ba".

Su baba ta kalla tana cewa "baba muje rike masa sanda ta suna tafiya Innah nabin bayansu.

Da kallo mai shagon ya bisu kamar ya zubar musu da hawaye gashi ba halin taimaka musu ji yake ina ace yana da karfin rike su ya basu gurin zama da abinci.

Cikin hanzari yace "ku dakata".

Tsayawa Husnah tai ya karaso inda suke yana kallon ta yace "yanzu ina zakuje daga nan"?.

Kai Husnah ta girgiza "ni kaina ban sani ba".

'Dan shiru yai zuwa wani lokaci yace "kuzo zan nuna muku inda zaku zauna".

Wucewa gaba yai suna bin bayansa har ya kaisu wani dankareran gida da ake ganinsa amma ko rabi ba ai ba daga gani gidan na babban mutum ne mai hali.

Tsayawa yai tare da juyowa yace "anan zaku zauna kada kuji tsoro babu abinda zai same ku nan anguwar muce kuma wannan gidan ni nake kula dashi na uban gida na ne ku shiga ciki karku damu".

Godiya sosai baba yai masa da addu'a mai kyau sannan suka shiga shi kuma ya juya gidan kato ne na gaske saidai ko ina yashi ne da bulalluka dakyar Husnah ta gyara musu wani guri a cikin palon ta cire hijab dinta ta shimfida musu ita kuma ta zauna gefe a kasa tana rafka tagumi ga zazzabi dake cin jikinta.

Kafin wani lokaci tuni ta fara kwara amai kana gani kasan malaria ce ta shige ta sosai har dare tana kwance ba cin safe ba rana balle dare gashi ba yadda zatai suyi ga duhu wani bai ganin wani.

Suna cikin haka sukaga an dallo fitila mai haske an shigo gidan tare dayin sallama sun dau muryar sa mai shagon daya taimaka musu ne.

Shigowa yai yana aje fitilar sannan ya basu tabarma guda biyu da bargo ga kuma kular abinci fa pure water.

Ganin Husnah a kwance ya tambaya jin bata da lafiya yasa da sauri ya fita yaje ya sayo mata magani ya kawo.

Tun baba na masa godiya har ya koma kuka saboda jin dadin karrama su da wannan saurayin yai alhali bai san su ba.

Saida ya musu mu kwana lafiya zai tafi baba yace "yaro me nene sunan ka"?.

Dakatawa yai yana juyowa ya kalle su da d'an murmushi a fuskarsa yace.

"Suna na Mansur ni d'an nan anguwar ne amma ba tanan haka ba nan anguwar masu kud'i ce baba na sunan sa Shu'aibu shima tsoho ne ni nake kula da mahaifana domin sun kasance basu da shi ina da yaya guda daya ina da 'kanwa guda daya sunan ta Ramlat.

Kai baba ya jinjina yana cewa "mun gode Mansur Allah ya maka albarka ya baka bud'i a cikin kasuwancin ka ya baka mai kyautata maka kamar yadda ka kyautata mana".

"Amin baba nagode da addu'ar ka gare ni mu tashi lafiya".

Wucewa yai yayin da yabar su baba suna ta masa addu'o'i masu kyau cikin nuna jin dadin abinda yai musu.


Fitowar Badiyat kenan daga wanka tana goge jikinta lokaci guda ta juyo a firgice tana zaro ido waje ganin gardi sa'kwa'kwa zaune a bakin gado ya zuba mata ido.

Tace "malam lafiya meya shigo dakai nan din me kake nema kayi ajiya ne"?.

Gira ya dage yana kallonta yace "niko nai ajiya mai girma ma kuwa".

"Me ka ajiye" Badiyat ta tambaye shi cikin mamaki.

Nuna ta yai "ke na ajiye kece ajiyar tawa".

Hade rai ta tana nuna masa kofar fita tace "malam yi waje bansan ganin ka".

Mikewa yai yana yowa inda take yace "saidai kuma an samu akasi ni ina son ganin ki tun ranar da naga kun shigo hotel 🏨 din nan zuciya ta bata barni na sake samun nutsuwa ba".

Cikin haushi Badiyat tace "to miye damuwa ta malam ka bace min da gani bansan zancen banza".

Shigowa xeey tai ta 'kwama wani glass a idonta Wanda ya kusa rabin fuskarta 😎 ganin a haka tace.

"Yadai 🌟 star"?.

Tsaki yaja yana kallon ta yace "wannan bagidajiyar yarinyar man dama haka take kike kod'a ta mai dodaddiyar kwakwalwa batasan komai ba".

Dariya zeey tai tana cewa "kai star yada wulakanci kuma? 'kawata ce fa kawai dan bata sanka bane".

"A'a ni bazan iya ba gaskiya wannan wahala kawai zata ban".

Dafe kafadar ta xeey tana cewa "my diyat ki gane man wannan na gida ne so yake ya huta dake zaki samu kud'i sosai yana da sakin hannu please ki bashi hadin kai🤔".

"😲 Zaro ido Badiyat tai "wai kina nufin na amince masa na bashi kaina ya lalata min rayuwa ya zanyi da ya Haidar taya zan tunkare shi gaskiya bazan iya ba bazai yiwu ba".

Tafi xeey tai "yiwuwa kai ai bari kiji albishirin ki Haidar ba a hayyacin sa zai aure kiba saimun gusar masa da tunani ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai canza alkawari nane saikin auri Haidar kin xauna dashi kin haifa masa yara".

Shiru Badiyat tai kawai ta kasa magana ta tsaya kallon zeey ganin kallon bana 'kare bane yasa xeey tace.

"Baki yarda ba diyat"?.

Sauke numfashi tai tana cewa "zan yardan dai amma ba yanzu ba sai nayi tunani ku bani lokaci".

"Shikenan ba damuwa kiyi tunanin mu zamu fita gari ne stat muje" fitewa sukai yayin da Badiyat ta bisu da kallo tana cewa.


"Jimin shashashan mutum nice zan bashi kaina wallahi bai isa ba ko yana yawo da uwarsa bari zeey din ta dawo ita ma ayi wacce za'ai.


A yawon neman aikin da Husnah keyi a anguwar ta samu wata mata mai kirki sosai take mata shara da wanke wanke saidai duk rintsi Husnah bata ta'ba fad'a mata a inda take ba ko halin da take ciki ita da mahaifan ta.

Kamar kullum yadda ta saba bayan ta gama mata aikin komai ta dawo gida zaune ta same su akan

Please Login or Register in order to submit comment