Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gani na ki bani amsar da nake son ji miye dalilin ki na wulakanta min 'ya"?.

"Ni ya kamata ki tambaya ba ita ba".

Inda akai maganar suka kalla ganin Zarah tsaye yasa Khubrah ta lelayo ashar ta narka mata tana sake bude dukkan girman idonta akan Zarah.

Tace "ke kuma shegiyan Mara kunya Dan uwarki ba dake nake ba ban sako dake ba ni sa'ar tsohuwar kice ki rufe min baki kafin nazo na durza ki a gurin nan".

"Wa zaki durza? Amma dai ba dani kike ba wuce nan bazai yiwu kizo ki d'aga mata hankali kuma ina kallo nai shiru ba nan ba'a irin wannan shashancin ki sauya she'ka kisan inda dare yai miki tun wuri".

" ni kike fadawa haka dan 'kashin uban ki saidai wannan munafikar uwar taki tasan inda dare ya mata amma badi'ah ba dan iskan daya isa rabata da gidan nan saidai idan tai ra'ayin komawa da kanta".


Zarah zatai magana umma ta d'aga mata hannu alamar ta bari.

Ran Zarah a 'bace sosai tace "amma umma inaji ana fad'a miki magana saina kyale maye amfani na"?.

"Nace ki shiru haka ko wuce ki bar nan dani ya kamata tai magana".

Dariya Khubrah tai tana cewa "kin fad'i gaskiya dan wallahi ko ke baki isheni ba balle wata banza Zarah".

Ganin bazata iya jurar abinda Khubrah keyi ba yasa Zarah barin palon ta shige part din Haidar.

Juyawa umma tai tana fuskantar Khubrah tace "meyasa ke baki da tunani ne? Wato bakisan zuru ba saboda tsabar zubar da aji da 'yar cikin ki kike fad'i in fad'a wallahi kinyi asara ni kuma kinga na shareki shine zaki karanta min soko ganin gabas tana da araha yasa karuwa ta kama sallar walaha bani da lokacin ki domin ni nasan abinda nake ba irinki bace shashasha".


"Kan bala'i dani kike zancen wato nice shashashar aiko yau zan gwada miki shashancin a zahirance ki gani saina karya miki 'kafa a gidan na.........................

Bata karasa tai tsit kamar an doke bakin tsanya da ta'barya tana baza ido ga Wanda yaiwa sarki sata muryarta na rawar rashin gaskiya cikin shayi tace.

"Aliyu Haidar ashe kana gida baka fita ba"?.

"Eh ina kwana" kawai abinda yace ya shareta domin yaji komai.

Cikin son wanke kanta tace " lafiya kalau d'an albarka dama yau nake son zuwa mu gaisa na dade ban zo ba".

"Ok yayi kin kyauta".

Umma ya dan kalla yana bata wasu takardu daidai zai fita yace "am umma wannan takardun kamfani na ne ki adana su zanje can ana nema na".

"Shikenan Allah ya tsare saika dawo".

Zaro ido Khubrah tai tana kallon takardun ji take kamar ta fauce ta gudu dasu data more.

"Na dawo gare ki Khubrah muje zuwa" umma ta fad'a tana kallon ta.

'Dan sosa kai tai kamar sabuwar kamu gashi ganin dukiya yasa ta dubulbulce ta kasa cewa komai".

"Ke nake sauraro ko kin gama"?.

'yar dariya Khubrah tai cikin wayancewa tace "kai dad'i na dake Aisha maimaita abu nifa bada wani manufa nazo ba kawai nazo mu gaisa ne na kuma rako badi'ah na baki hakuri idan laifi ta miki kinsan yaran nan ba'a saidar su musamman badi'ah wani lokacin bata da kirki na sani".

Kallon mamaki umma kebin Khubrah dashi kawai tama kasa magana saboda lamarin ya bada dariya.

"Amm ina badi'an take ina son zan koma muyi sallama".

"Tana part dinta ki 'karasa".

Wuff ta shige ciki kamar wacce aka hankada ta saboda kunyar abinda tai yanzu kuma taga kud'i ta rud'e.

Da kallo ta bita kafin ta girgiza kai tana mikewa ta shiga part din ta ita ma.

A bakin gado Khubrah ta samu Badiyat da way a hannunta shiga tai har inda take tana zama kusa da ita tace.

"Wato ke dama zuwan ki gidan baida wani amfani dake da babu duk daya".

"Me kuma nayi mama"? Badiyat ta tambaya tana turo baki.

"Oh tambaya ta kike wai me kikai ubanki kikai dama da zaki taho gidan nan badan kija ra'ayin Haidar bane uwar me kike kallo yake baiwa wancar munafikar tsohuwar tasa ajiya kenan har yanzu bakija hankalinsa ya fara sonki ba"?.

Gyara zama Badiyat tai tace "to mama ya zanyi Haidar wani irin mutum ne a murde yake ko fuska baya bani balle na samu yasan dalilin zuwa na gidan su".

"To dama taya zai sani tunda baisan gaibu ba kece zaki nuna masa ai harya fahimta idan kika sure shi zamu samu kud'i sosai a jikin sa musamman zanyo ATM ๐Ÿ™Š na cirar kud'i a account dinsa๐Ÿค”๐Ÿ˜‚".

"Mama Haidar baxai fahimce niba ta sauki ba kinga dai shekara ta guda da watanni a gidan nan amma kamar baisan da zama na nida babu daya ne a gurin sa".

"Haka yace ko kece kika fad'a"?.

"Nice nace haka domin nayi kokari na harna gaji nifa wani san idan ya cusa min bakin ciki shida Zarah ji nake kamar na hakura da aurensa na dawo gida".

Da sauri kamar za'a rigata har tana kwaruwa tace "kul karki sake ki aikata wannan gangancin kome zai miki ki daure akwai ranar ramawa tana zuwa zan taya ki samu damar sa ta yarda ba shiba hatta uwarsa da ubansa sai sunji jiki".

"Taya zaki haka mama"?.

"Hummn wasa kenan badi'ah ta yadda ake yi mana kedai kawai naki ido ne ki zuba ido ki kallo kiga abin mamaki saina aje musu abin fad'a".

Kallonta Badiyat ta tsaya yi sosai tana jujjuya maganganun ta masu kama da tatsuniya.

Ganin kallon bana 'kare bane Khubrah tace "baki yarda ba"?.

Kai Badiyat ta girgiza jiki a sanyaye tace "ina tunani ne".

"Ke tunanin me kuma? Ki barmin komai a hannu na daya Rana irin ta yau karki wani damu ki 'kyale ni dasu nasan yadda zanyi".

Shiru Badiyat tai cikin masifa Khubrah tace "wai uban me kike tunawa ne sakarya kinyi wani so'ko'ko ya 'kawar bora sunga kina tsoron su dole su raina ki goge idonki zaki ki shiga cikin su duk dan iskan daya fad'a miki cuta ki fad'a masa mutuwa kar kiji shakkar kowa sawa tace kici min mutuncin su".


TOFA JAMA'A WANNAN BA UWAR ARZI"KI BACE๐Ÿค”๐Ÿ™„.

Sauke ajiyar xuciya Badiyat tai tana kallon tace "shikenan mama zanyi duk abinda Kika ce min".

"Ko kefa da ana magana kina turo baki gaba kamar ja'ba a gaban saurayin ta ni Bari na tafi kuma maganar karshe dazan fada miki kisa ido sosai kisan sirrin komai domin Haidar yana da dukiya mai yawa a boye mu kuma ita muke so karki sakaci! Kada ki tsaya wasa!! Kada ki sare dukiyar kamar ta dawo hannun mune kisa haka a ranki".

Kai Badiyat ta d'aga tana mikewa ta mata rakiya zuwa harabar gida inda motar ta take Saida taga tafiyar ta sannan ta dawo cikin'kwarin gwiwa da daukar salon da gurbatacciyar uwar tata ta bata.


Husnah na tsaye a kofar gidan su bayan sallar magriba tare da wani saurayi wanda shima kallo daya zakai masa kasan cewa dan masu shine.

Magana suke Husnah da duk tabi ta rikirrice tace "mubashshir ka fahimta bawai na'ki amincewa Sadiq bane ko ina ja masa rai ba haka ne".

"To yaya ne Husnah"?.

Numfashin ta na sarkewa sakamakon zafi daya hada mata tace "baza ka gane bane kawai mubar maganar".

"No muci gaba zan gane".

'Dan dafe kanta tai zuwa wani lokaci kafin tace " mubashshir ko kaima sheda ne Sadiq yafi karfi na ba abokins soyayya ta bane balle har yakai mu ga aure".

"Meyasa kika ce haka"?.

"Saboda shi dan masu kud'i ne ni kuma yar talace kuma a talakawan ma nakasassu".

"Haka ne abunda kika rika ya zama hujjar ki"? Ya tambaye ta.

Shiru tai yaci gaba "indai wannan ne karki damu mahaifiyar sa itace ta Kira ni ta min bayani kuma ta bani kwatancen ki mahaifan sa na sonki meyasa bazaki Amin ce masa ba"?.

"Sadiq mutumin 'kwarai ne nine mutum na farko dazan bada sheda akan kyawawan dabi'unsa da halayensa wanda kema kinsan wani abu daga ciki Husnah Sadiq na sonki mahaifan sa na sonki Dan Allah kiyi tunani akan haka kema kiso shi ki daina kawo komai a ranki".

"Shikenan zanyi tunani".

"Ok yayi yaushe zanzo na karbi amsa ta"?.

"Zuwa juma'a ta sama".

"Zaki ganni da wuri kuwa nazo ki huta lafiya" yana fadin haka sukai sallama ya wuce Husnah ta dade a gurin kamar wacce aka daure ta kafin ta shiga gida.

Kwana biyar a tsakani baba yai Kiran ta ga Innah a gefe cikin nutsuwa ya soma magana.

"Asma'u wata alfarma Hadiza tazo nema gurin mu Amma bamu da iko dole Saida amincewar ki".

Cikin tsarguwa Husnah tace "wace haka kodai mahaifiyar Sadiq"?.

"A'a ba ita ba Sadiq da bakya sonsa ina zakiga danginsa a gidan nan Hadiza maman kawar ki Fatima nake nuf.........

Tun kafin baba yakai aya ta tare shi "lafiya baba meya faru me tazo yi"? .

"To ai Husnah baki bari ba na fad'a miki kika katse ni".

Yawu ta hadiye dakyar tana kallon Innah tace "wani abu ne"?.

Kai Innah ta girgiza "ki bari ya fada miki".

Jikinta duk yai sanyi kawai tai shiru tana sauraren taji me baban zai ce.

"Asma'u dama jiya bayan tafiyar ki islamiyya Hadiza tazo mana da wata nannauyar magana mai girma kuma bazamu iya Musa mata ba sakamakon dawainiya datai dake tun kina yarinya.

"To baba wani abu tace"?.

Kai baba ya d'aga "eh cewa tai tazo cin arziki gurin mu tana nemawa d'anta Jabeer alfarma yace yana sonki idan zamu bashi"?.

Wata irin yanke gaban ta yai ya fadi Wanda Saida ta dafe saitin xuciyar ta tana maimaita kalmar innalillahi wa inna ilaihi raji'un.

"Husnah kinyi shiru ke nake saurara"?.

"Baba Toni me zance"? Ta fada muryarta na rawa.

"Kamar ya me zakice? idan kin amince saiki fad'a idan bakya so nan ma ki bani amsa"?.

Kuka Husnah ta kamayi na rashin sanin madafa baba na sauraron ta inna na kallon ta Saida ta gama baba yace.

"Kukan me kike Asma'u? karki cuci kanki idan har kinsa bakya sonsa ki fada min ni nasan yadda zanyi bullowa al'amarin".

Kaita girgiza "a'a baba ko bana son ya Jabeer bazan iya mata musu ba mama tamin komai Wanda bazan iya biyan taba har abada Dan haka ta nemi alfarma guda daya a gurina ace na'ki yi mata na zama butulu".

"Yanzun kin amince kenan"?.

"Eh baba na yard.........

Mikewa tai da gudu ta shiga daki sakamakon kuka daya sake taho mata Wanda bata so baban ya fahimci hakan.


Zaune suke su biyu a wani gidan shakatawa Badiyat tace "ke zeey nifa ban fahimta ba har yanzu ya Haidar bai sauya ba"?.

"Eh to ai bama a fara aikin ba domin yayi tafiya saiya dawo kedai ki tanadi kudi kawai shine magana".

"Ni indai zan samu biyan bukata Dan kud'i bani da matsala dashi ina da kofofin samun su".

"To yanzu naji magana zan tambaya miki shi yaushe zamuje saiki fara shiri domin kema ki shiga duniyar nishadi ๐Ÿค” nifa bari kiji tunda na asirce uwa ta bata da kata'bus a kaina zan fada mata son raina ba yadda zatai dani to wanne mai ido ba d'an cikin zan kyale"?.

Badiyat da bata kula da zancen da xeey din ke mata ba ita babban burin ta taga yadda Haidar zaiyi a kanta shine damuwarta.

Cikin zumudi tace "to amma zeey kina ganin yaushe zai dawo ina yaje ne ya makale kamar jemage nifa na matsu ya dawo"?.

"Hummn kwantar da hankalin ki madam domin matsuwar ki bata kai tawa ba nida nake so mu fita waje nida Saminu mu gano duniya da 'kasashe saidai ina tsoron daddyn mu shi aikin ya'ki kama shi sam".

"Saidai nasan yadda zanyi ko yaso ko ya'ki ko ya amince ko ya'ki amincewa bai dame niba tafiya ta zanyi".

Badiyat da xeey din ta zama abinda kallo a gurin dan murmusawa tai tana mata jinjina da hannu tace" 'kawata ina yinki sosai".

"Kamar yadda nima nake yinki" zeey ta fad'a tana cire kwalin kanta ta zauna haka suka ci gaba da tattaunawa xeey na sake zugata tana d'ora ta akan keken 'bera๐Ÿ€๐Ÿ.

Bayan wata biyu Husnah ce ta fito fito daga daki tana waya da wata yar karamar tecno ta zauna kusa da Innah tana kwanciya akan kafafun ta taci gaba.


Saida ta gama ina tace "to d'aga ni haka idan ba so kike ki karasa min dayar kafar ba".

Dariya Husnah tai "kai Innah taya zan karya miki kafa bani da nauyi fa"?.

"Haka dai kika ce, dawa kike waya naji kina yaushe zai dawo"?.

"Sadiq ne".

"Tofa Husnah kunya zakisa muji kenan? Bayan kuma kin amince wa Jabeer yanzu kuma kike kula Sadiq alhali kin bada kai"?.

Dan dafe goshi tai tana kallon Innah tace "nifa Innah jabeer kawai na amince masa ne ba dole saina aure shiba matar mutum kabarin sa".

"Kenan bakya sonsa"?.

"Eh Innah gaskiya bai min ba".

"To meyasa kika amince"?.

"Innah ina jin kunyar mamansa ne".

"Af daga baya kenan kisan yadda dai kafin Hadiza ta ritsa ki ta turo rokon arziki dan nikam babu ruwa".

Tashi zaune Husnah tai tana cewa "insha Allahu Innah baza tazo ba har Sadiq ya dawo domin shi nake so a yanzu".

"Oh tsuntsun son๐Ÿ•Š๏ธ ya gano shi kenan lallai ya taki sa'a dama ance maha'kurci mawadaci yaron nan yayi wahala shima yaci kwakwa a kanki".

"Eh yanzu kuma lokacin sane ina baba ya tafi"?.

Sauke numfashi Innah tai tace "yaje anguwa ne".

"Ok bari nayo cefane kafin ya dawo na dora muku girki" ta karasa maganar tana mikewa tsaye tare da jawo hijab dinta dake rataye a rigiyar shanya ta fita.

Kusan karo sukai da Fatima zata shigo gidan a zaure suka tsaya cikin tsokana Fatima tace.

"Aunty na Ina zuwa ne"?.

Dan hade rai Husnah tai zata wuce Fatima dake dariya ta riketa tana cewa " kai my aunt tambayar ki fa nake kika min shiru"?.

"To ya kike so nace dama haka kike kira na๐Ÿ™„"?.

Rufe baki Fatima tai da yar sauran dariyar ta tace "ayya sorry my Husy kinsan dole yanzu na Kira ki da hakan".

"To nidai ban so idan kuma ba haka ba na hada ki da yayan naki".

"Ke rufa min asiri karki sa ya cire min baki na ta'ba amaryar sa muje na raka ki".

"Wannan kuma ke kika sani Husnah ta fad'a tana yin waje yayin da Fatima tabi bayanta tana sake tsokanar ta".


Gidan su Badiyat wani babban mutum na zaune hadadde dashi a falor yana waya hajiya Khubrah ta fito tana zama Saida ya gama ya juya bangaren ta yana cewa.

"Lafiya dai"?.

Hade rai tayi sosai ta soma kukan 'karya tana cewa "yanzu alhaji yayan ka ya kyauta"?.

"Umhum miya faru yimin bayani"?.

Sake Jan mayafi tai tana rufe fuskarta dan kar ya gane taci gaba "wai kamar Yusuf yana kallo ana wulakanta maka yarka a gidan sa amma bazai magana ba wannan tunda ranka Kenan yau kuma da babu kai fa inaga saidai munafikar matarsa tasa ya kai badi'ah gidan marayu cin fuskar nasu yai yawa ya kamata ka dakatar dasu dan wallahi akan yata bazan dauki shashanc..............

'Daga mata hannuโœ‹ yai yace "dakata min malama me kike yi haka kin fara hauka ne yayan nawa uwa daya uba daya kike Shirin zagi a gaba na saboda baki data ido lallai kuma nasan irin zaman da muke da ke ba ahli nane bakya kauna ba nine bakya so".

Zaro ido tai jin ya mata wata fassarar dabam ta fada masa haka ne dan ransa ya baci yaji haushin su Amma gashi abun yana neman juyewa kanta.


Ganin yadda ya dauke mata kai ya mayar da hankalin sa kan abinda yake ya bawa iska ajiyar ta yasa tace.

"Na shiga uku ni kuma da yaushe nace haka"?.

"Oh kina nufin 'karya nai miki"?.

Nan ma da sauri tace "a'a ni bance haka ba amnma alhaji baka tsaya ka saurare niba ka fara fad'a".

"Ina jinki".

Gyara murya tai cikin tunanin abinda zata fad'a tace "kai fa alhaji dan ban taba fad'a maka bane amma badi'ah bajin dadin zaman gidan nan take ba komai tai a tsangwame take tana Shan bakaken maganganu marasa dad'i a gurin Aisha da yarta Zarah nima ranar da suka koro t naje sulhu sai da ta zageni tass".

"Gaskiya ya kamata ka dau mataki domin ita bakin cikin Aisha akan Haidar nason badi'ah ne shine tabi ta tsane ta tahana ta sakat wai ala dole sai ya auri wata yarinyar yar gidan 'kanin ta".

"Oh haka ne kin tabbata gaskiya ne abinda kika fad'a"?.

"Kwarai alhaji haka ne gaskiyar batu".

"Ok yayi zan Kira badi'an naji komai a bakin ta".

A rude cikin rashin gaskiya Khubrah tace "ai alhaji daka kyale ta domin zata taso mata da tsohon ciwo ne".

"Baki da gaskiya Khubrah"? Ya fad'a yana mata kallon tuhuma.

"Alhaji da gaskiya ta ka yarda mutanen nan saika tashi musu tsaye ko zasu bar badi'ah ta sha'ki iska mai kyau a gidan nan".

Katse ta yai "saurara da Allah ya isa haka kin ishe ni bansan shashashanci".

Shiru Khubrah tai cikin takaicin ganin bata samu goyon bayansa ba kuma tasan waye shi wajen zafin zuciya shiyasa bata yarda tayi dogon musu dashi.


Shara Husnah keyi a tsakar gidan su lokaci guda ta tsaya tana mikewa tsaye tare da cewa.

"Wash baya na ya ma'kale gaskiya shara akwai wuya".

"To Asma'u yar wannan sharar kike kira da wuya saboda lalaci idan kuma aka kaiki babban gida fa"?.

Dariya tai "ai Innah Koda babban gidan ne saidai na rika sharewa duk bayan sati biyu".

"Da kin zama 'karama".

"Allah Innah shara da wuya gashi ta 'kamar min da baya Bari na karasa nima nazo na huta".

Komawa tai taci gaba jin taku da karar takalmi yasa Husnah kallon kofar shigowa ganin budurwa tai a tsaye sai wani yau'ki take da cin chewing gum gashi tanai musu kallon 'kyama har karamin towel tasa tana toshe hanci.

"Wace ke daga ina me kike nema"? Husnah ta fad'a ranta a hade ganin kallon cin fuskar da take musu.

Saida ta karewa Husnah kallo irin na wulakanci sannan tace "ganin ki a gidan nan hakan ya Tabbatar min da kece 'yar gidan wadannan nakasassu ko"?

"Hakan yayi ba ruwa na da makantar mutum ko gurguncewar mata sai an bani abinda nazo karba ko asan inda dare yai".

"Waike wace kin fara hauka ne zaki shigowa mutane gida ba sallama kamar kin samu arna".

"Kusa da gun hajiya nazo ne ku bani kudin hayar gidan nan".

Cikin harara Husnah tace "a matsayin ki nawa"?.

"A matsayina na 'yar mai gidan domin yayi tafiya kuma yanzu komai a hannu na yake kin gane"?.

Kallon sama da kasa Husnah tai mata kafin tace "yayi 'yar masu gida saidai ina so ki sani da alhaji xai tafi baice zai turo wani ya karbi kudin haya ba".

"To kuma saiga 'yarsa tazo a bata" xeey tai maganar cikin gadara.

'Daukar tsintsiya Husnah tai tana ci gaba da shararta tace "na karfi ne ki 'kwata idan zaki iya".

Zaro ido zeey tai "Kam baban bala'i lallai dani kike zancen aiko uban kuturu yai kadan balle na makaho saina nuna miki iyarki".

Dagowa Husnah tai tace "iyakar ki dai banza kawai".

"Nice banza? Ki jira dawowa ta wallahi saikin gane ruwa ba sa'an kwando bane".

Juyawa tai zata fita Husnah data bita da harara tace "zancen banza kenan ban dan iskan daya isa na bashi kudi ba indai ba alhaji ne ya dawo ba".

Kai Innah ta girgiza dan ta kasa magana ma baba dayai shiru cikin tunanin rashin muhalli na kansu da suke dashi yace.

"Asma'u meyasa kika biye mata da hankalin ki"?.

"To baba ina gani za'a wulakanta ku saina zuba ido na kyale meye amfani kenan".

"Ai Husnah ba maganar ki kyale bane idan mai tarbiyya da marar tarbiyya suka had'u ya kamata aga bambanci shiyasa nace miki haka".

Sauke ajiyar zuciya tai tana kallon sa tace kayi hakuri baba nayi kuskure".

"Babu komai Asma'u".

"To amma baba mai zai hana na dawo dayin awara ta"?.

"A'a Asma'u inajin tsoro wacce kikai a baya Allah yasa mata albarka".

Kasa cewa komai tai kawai ta wuce zuwa zubar da sharar tana tunanin ita kuma wannan budurwar mara mutunci daga ina ta 'bullo.

Sati biyu da faduwar haka zeey ta gayyaci Badiyat suka koma gidan su Husnah da rashin arziki kwando-kwando da suka taka zasu sauke mata idan ta kawo musu raini.


Suna shiga xeey tai bol da wani karamin bokiti wanda yake cike da ruwa tare da cewa.

"Gani na sake dawowa a karo na biyu yau sai an yita ta kare ba mutunci".

Innah dake bin zee da kallon mamakin rashin tarbiyya irin nata tace.

"Wai dan Allah 'yar nan daga ina kike waye ya turo ki"?.

Wani irin kallo xeey tai mata sannan tace "daga sama na fad'o kina tambayar waye ya turo ni baron dibar ruwa ce malamai ku fito min da kudin hayar gidan nan yanzu ko kuma kuga aiki da cikawa".

Fitowa Husnah tai daga daki tana kallon zeey tace "amma wallahi kedai baki da mutunci baki samu kyakkyawar tarbiyya ba wannan jahilcin naki yai yawa bari na miki gargadi na karshe kada ki kuskura na sake ganin ki a gidan nan jikin ki zai fad'a miki idan kuma baki yarda ba kici gaba da zuwa sai kinga yadda zanyi dake wawuya kawai".

"Ke nice wawuyar dan uwar k...........

Bata kasara sakamakon buge mata baki da Husnah tai tana nuna ta da yatsa tace "ko da wasa kada ki kuskura wannan kazamin bakin naki ya zagar min mahaifana domin a kansu babu abinda bazan iya yi ba".

Kukan kura zeey tai tana nufar Husnah da sauri Badiyat tasha gabanta tana riketa tace.

"Shareta zeey kin wuce ajin fad'a da ita kada wani ma yaji zaki abinda kunya fada da d'iyar talakawa kuma nakasassu".

Ta karasa maganar tana yiwa Husnah wani banzan kallo da wani irin bacin rai Husnah ta d'aga hannu ta shararawa Badiyat mari mai zafi Wanda yasa Badiyat gigicewa ta saki zeey tana rike fuskarta da a halin yanzu bata ganin komai sai duhu.

"Banyi miki gargadi cewa kada kuskure yasa ku zagar min mahaifana ba me kuke tunani a kaina bazan iya daku bane kome"?.

"Ni kika mara"? Badiyat ta fad'a tana kallon Husnah.

Baki ta tabe "an mare ki kadau mataki idan zaki iya".

Kai Badiyat ta jinjina zeey da tun dazu bakin ta yake a bude ganin yadda Husnah kecin ubansu ba wani tsoro ko jin shakkar su yasa tace.

"Zakiga abinda dazai faru ki jira dawowar mu wallahi sai kinyi kuka da idanun ki wannan alkawari nane".

Juyawa sukai suna fita daga gidan babu abinda baba ko Innah suka ce domin sun rasa daga inda wannan tantiriyar yarinyar ta bullo tazo ta dame su da fitina.

Husnah na shiga wanka Badiyat ta dawo tare da xeey bayansu wasu garada su uku dakin xee ta nuna musu tace.

"Kayan gidan nan nake so ku debe gabadaya kuyi watsi dasu a waje kada kubar Koda tsinke ne".

To suka ce mata suna nufar dakin da gudu Husnah taje tasha gaban su tana tare kofar dakin tace.

"Karya ne kinyi kadan kice zaki fitar mana da kaya waje kinyi tsararo baki kaiba".

Dariya zeey tai "haba yarinya wuce nan kuyi abinda nace idan kuna da bukatar karin kudi ma zaku samu.

Suna Shirin sa hannu su janye ta daga kofar dakin ta make hannun dayan da ice baya yaja da sauri cikin azaba.

Tafi xeey tai tana cewa "kai da kyau lady ina son haka jarumar mace mai kamar maza na jinjina miki a bisa wannan kokari da kikai na gaida ke".

Jarkar hannun Badiyat ta kabar tana cewa "bari nayi abinda yafi sauki shikenan na gama magana".

"Duk abinda zaki ina daidai dake" Husnah ta tana jawo murfin kofar.

"A haba dai da gaske kina daidai dani" zeey tai maganar tana kallon su baba dake gefe kan tabarma.

Maida kallon nata tai gurin Husnah tace "kina daidai dani kika ce ko"?.

" 'kwarai kina tantama ne? Niba jaka bace irin ki mara tarbiyya bana shakka kiyi duk abinda zaki yi".

Bude murfin jarkar zeey tai tana cewa "oh haka kika ce? To ai shikenan.

Da gama fadin haka ta soma bulbular da fetur din a tsakar gidan tuni warin sa ya karad'e ko'ina.

A zabure cikin tashin hankali baba ya mike yana daukar sandar sa yace "Asma'u warin me nake ji kamar na fetu............

Bai karasa ba sakamakon zafin wuta daya soma ji na bugo shi da sauri Husnah ta d'aga ina tana rike sandan baba tai kofar fita daga gidan amma a kulle domin xeey na 'kyasta ashanan suka fita da gudu suna rufe gidan.

Zaro ido Husnah tai ganin kofar a kulle kitchen ta koma tana dauko ta'barya cikin tashin hankali ganin yadda wutar take tsiri kuma tafiya take ta kusa zuwa inda suke.

Dukan kofar ta farayi da karfin gaske wanda batasan tana dashi ba a sannan dakyar ta samu taji furam din ya fara rawa.

Kamashi tai tana jijjigawa ta hada gumi shir'bin zuwa wani lokaci ta sake daukar ta'baryar tana sake dukan sa sai ga kofa ta rufta waje da hanzari ta fita dasu.

Ga mutum dan'kar an taru sai ihu ake ana watsa ruwa haki sosai Husnah keyi

Please Login or Register in order to submit comment