Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kona bata lokaci na akansa ba d'an gidan alhaji Jameel ne fa taya iyayensa zasu yarda".

"To indai kinsan haka ne ki daina kula shi".


"Allah baba ba nice nake kula shiba shine kullum yake zuwa gurin suyar awara ta yana takura min".

"Awarar ma ki hakura da soyawa ki daina daga yau".

"Amma baba idan na daina dame zamu rika biyan kudin haya sabuli wanki ya zamuyi kenan"?.

"Babu komai Husnah Allah zai kawo mana wata hanyar".

",$hikenan baba bari nai sallah na fito na dora muku abinci" wucewa tai yayin da tabar su baba da jimami.


Badiyat ce zaune ita da 'kawar ta a gurin shakatawa ta zubawa guri daya ido tayi zurfi Cikin tunani.


Kallonta dayar tai tana cewa "ke Badiyat kina lafiya kuwa meya faru irin wannan zubawa guri daya ido ki rufawa kanki asiri kar cutar ciwon zuciya ta kama ki".

Sauke numfashi Badiyat tai cikin damuwa tace " meye ma bai faru ba zeey taya damuwa zata rabu dani bayan kullum abinda nake hari nake so nake mafarkin samu yana kara nisa dani".

"Kaii da alama keda Aliyu ne ko"?.

"Da shine man zeey gabadaya yabi ya zafafa min kai ya burkita min tunani gashi ya'ki bani aron lokacin sa baya saurara ta ko kadan Taya zan samu kusanci dashi harya karbi soyayya ta ya gane ina azabtuwa akan sa"?.

Tsaki zeey tai "kema duk dake kamar ba mace ba harki xaune namiji yana miki yau'ki yana dage miki kai maimakon kece zaki masa kallon me kika tsaya yi harya gano lagon ki"?.

"Humm zeey kenan bakisan waye ya Aliyu ba shiyasa kike ganin gazawa ta kwata kwata baya bani fuska baya kula ni baya saurara ta taya zan samu sauki"?.

Dariya zeey tai "a kwarai kuwa kice kece kika fara nuna masa yadda zai wulakanta ki idan ba haka ba kefa mace ce kece ya kamata kija masa aji Amma shine me miki gaskiya kawata kin fado ko zakiji haushi saina fada kin rako mata tunda har kika tsaya me hula yaga gurin kwanan ki".

Amma gaskiya ya mayar dake gariya" zeey ta fada tana shekewa da dariya.

Cikin jin haushi Badiyat ta mike zata bar gurin da sauri zeey ta riko mata hannu tana cewa.

"Sorry sorry kawata meye abun fushi zauna muyi magana ta nutsuwa".

Zama Badiyat tai badan taso ba zeey ta dora da cewa "yanzu ya kike gani me kike so"?.

Kai tsaye Badiyat tace "kawai ni bukata ta shine na samu soyayyar Haidar ya zama ni kadai yake iya gani kuma ya aure ni ya zama ya kasance a karkashin iko na".

Rausayar da kai zeey tai "kin samu 'kawar zanyi miki hanya wata Rana sai Haidar yai kneel down a gaban ki ya roki soyayyar ki kuma nina fada miki wannan".

"Aiko zeey da naji dadi domin bani da buri ko fatan daya wuce auren ya Haidar na zaune tare dashi mu kasance guri daya".

Zeey zatai magana sukaji ance Zainab ashe kina nan ni ina ta neman ki"?.

Duk dagowa sukai ganin Saminu yasa zeey hade rai tana cewa.

"Wai Saminu wannan wacce irin jaraba ce duk inda nai kana bina kamar tare aka haife mu wallahi ka shiga hankalin ka".

Kamar yana gaban mahaifan sa haka ya durkusa a gaban ta cikin muryar tausayi yace.

"Haba Zainab ni inacan ina damuwa da rashin ganin ki kuma daga zuwa saiki kama ni da fad'a Amnah na tambaya tace min kina nan taya zan samu nutsuwa bayan kece farin ciki na bana jin dad'i idan har ban ganki ba".

Tabe baki zeey tai cikin rashin nuna kulawa tace "Amma saina ci uwar amnah bari na koma gidan zatai bayani".

Saminu yace "karki mata komai dan Allah ba laifin ta bane nawa ne😔".

"Wannan kuma kai ya dama tunda tsautsayi yasa kazo saika kaimu Shan ice cream".

Cikin yanayin jin tsoro yace ban fito da kudi ba".

"Oh ina ATM dinka"?.

"Yana mota".

"Kuturun uba kasan da ATM din a mota zaka ce baka fito da kudi ba saboda ni sa'ar wasan kace ko"?.

"Kiyi hakur...........

Bai karasa ba ta katse shi rike hakurin ka bana bukata malam ka wani tsuguna a gaban mutane sai kace kyanwa🐈😂".

Kamar soja haka ya mike yana 'kamewa guri daya Saida ta wuce Badiyat tabi bayanta sannan da gudu ya je ta bude musu motar Saida suka shigw ya rufe shima ya zagaya yana shiga driver seat ya tashi motar suka wuce.

Badiyat da tsananin mamakin dake neman sheke mata numfashi ganin yadda zeey kewa Saminu son ranta tace.

"Ke zeey meye sirrin duk haduwar wannan gayan kike iya juya shi"?.

Dariya zeey tai " karki damu kin kusa taka wannan matsayin idan kina so"?.

"Tab ina so man please ki taimaka min".

"Ok yayi kinga yanzu babu lokaci zan sameki daga baya sai muyi maganar ki tabbata kin samu kan Aliyu kin aure shi".

Cikin tsananin jin dad'i da farin ciki Badiyat tace "na gode zeey gaskiya ke 'kawa ce".


Zaune Husnah take ita da Fatima a palon su suna Hira Husnah da hankalin ta yai gida ta mike tana cewa.

"Fatee Bari na tafi na baro baba su kadai a gidan a Rana ta fara nisa".

Ok yayi muje na miki rakiya" daidai maman Fatima ta fito ganin su a tsaye yasa tace a'a Husnah badai har tafiya zaki ba"?.

"Eh mama gida zanje domin na baro su baba ban Dora musu abinci ba".

"A'a yi zaman ki indai abinci ne ba matsala bari ya karasa ki tafi musu dashi".

Shiru Husnah tai domin bazata iya mata musu ba tana matukar daraja mama saboda ta mata komai a rayuwa itace ta dau har nauyin karatun ta bata da baki magana saidai tace Allah ya biya ta.

Dole komawa tai ta zauna Saida mai aikin mama ta gama sannan ta karba tayi musu sallama ta wuce gida.

Gaban ta ne ya fadi tun daga kofar gida ganin mota tasan waye shiyasa ta karasa ciki jikinta a sanyaye.

Kamar yadda Tai zato tana shiga ta hango alhajin da suke hayar gida a gurinsa yana tsaye suna magana dasu baba.


'Daki ta shiga tana dauko kud'i ta Mika masa bai karba ba yace "nawa ne naga baikai adadin yadda kuke biya ba"?.


"Eh alhaji dubu talatin ne zan cika maka daga baya kafin watan ya cika".

"A'a nifa gaskiya nafi son kud'i ful lokaci guda banason zuwa gaba a dawo baya saboda naga baku da karfi shiyasa nace ku rika bada dubu talatin amma naga ashirin"?.

"Zan cika maka zuwa watan ya kare dan Allah alhaji kayi hakuri" Husnah tai maganar cikin damuwa.

Juyawa yai zai fita yace "shikenan naji amma ku 'kokarta ki hada sauran kafin na sake zuwa".

Batai magana ba ta dai bishi da kallo har ya fita kafin ta sauke ajiyar xuciya tana kallon Innah data zuba mata ido sai kawai ta mike tana shiga kitchen ta dauko plate ta zuba musu abinci.


"Asma'u a ina kika samu abinci"?.

"Am baba naje gurin Fatima ne shine mama tace na taho muku dashi".

Shiru ne ya biyo baya suna cin abincin ita kuma tayi tagumi tana kallon su zuwa wani lokaci tace.

"Baba dama na fada maka idan na daina awarar nan akwai matsala gashi tun ba'a je ko'ina ba mun fara fuskantar 'kalubale".

Daina cin abincin baba yai yana kallon inda Husnan take kamar mai kallonta yace.

"Husnah karki shiga damuwa komai ya zafi maganin sa Allah zamu samu wata hanyar duk wanda ya dogara ga Allah zai isar masa wanda ya tsaya a kofar shi zai karbe shi wanda ya nufo shi zai cika masa burin sa wanda ya ro'ke shi xai kar'ba masa ya fitar shi daga wahala Wanda yabi rayuwa a hankali sai tazo masa da sauki dan haka kada haka ya daga miki hankali kafin cikar wata zamu samu".

Kai Husnah ta daga "shikenan baba Allah ya mana maganin abun".

"Ameen Asma'u".

Sai lokacin baba ya koma cin abincin sa yayin da Husnah ta mike tana shiga daki kamar mara lafiya".



Shigowar Fatima kenan zata shige taji ance "wato kema kinyi graduate shine kika fara kawo kawayen ki ko"?.

Da sauri ta juya ganin yayanta Jabeer yasa tadan bata fuska tana cewa "kai ya Jabeer Husnah ce fa yar gidan baba Ibrahim".

"Kin tabbata itace"?.

"Allah da gaske nake".

"Ok yayi kije".

Wucewa Tai tana tunani har zata shiga part dinta ta tsaya ta juyo tana kallonsa tace "yaya Jabeer kodai kodai"?.

" 'dagowa yai "kodai-kodai me"?.

Shiru tai tana kallonsa sai kuma tayi dariya tace " da cewa zanyi kodai ka fad'a ne"?.

"Ina na fad'a wato yarinyar nan kin raina ni ko? Ya fada rai a hade.

Rufe baki tai tana girgiza kai dariya na cinta da gudu ta shige ciki jin yace tazo.


Zaune yake a wadataccen palon gidan su ya zubawa guri daya ido babu ko kiftawa fitowar wata farar mata ganin yadda ya shiga yanayi yasa tace "Sadiq".

Ganin yai shiru alamar baiji ba ta kara Kiran sa da karfi "SADIQQ".

Da sauri ya dago ganin momyn shi yasa ya sauke ajiyar zuciya yana goge gumin dake goshin shi.

Momy data zuba masa ido cikin mamaki tace "Sadiq wai lafiyan ka kuwa kwanakin nan duk ka mayar da kanka wani iri meke damun ka ne"?.

"Momy ina cikin matsala kuma bansan ya zan magance taba damuwa ta ciwo ne kuma baida magani".

"Tofa wannan wacce irin cuta ce Sadiq? Kasan fa cuta bata sauka ba Saida aka saukar da maganin ta, to kai kuma wacce kala ce taka"?.

Kai tsaye yace "ciwon so ne".

"Son wa"?.

"Husnah".

Baki bude momy tace "Husnah"? yaushe ka fara son mace Sadiq ashe zanga wannan ranar? a ina take wacce ita"?.

"Anan anguwar take".

"To 'yar gidan waye"?.

"Ibrahim".

"Ai ka sake shigar dani duhu wanne Ibrahim din domin suna da yawa a anguwar nan".

Saida ya sauke numfashi sannan yace "ibrahim na bayan layin mu Wanda ake cewa baba makaho".


"Ok na gano shi Amma tun yaushe kake sonta"?.

"Da dadewa momy kawai na kasa fada muku ne saboda tunanin yadda zaku dau maganar ina jin tsoron ku hana ni auren ta domin itace za'bi na".

Gyara tsaiwa momy Tai "a'a ni bazan hana kaba kuma mahaifin ka ma mutum ne mai fahimta idan ita ce alkairi a gare ka Allah ya baka ita".

Cikin farin ciki Sadiq yace "Amin mom na gode sosai da kika fahimce ni kimin addu'a itama ta karbe ni sosai a zuciyarta".

"Babu komai karka damu ya kamata ka fara shirye shirye akan tafiyar ka".

Tana fadin haka ta wuce shima mikewa yai jinsa garau kamar Wanda ya tashi a ciwo".


Zeey na shiga gida ganin Amnah a palor yasa ta ajiye ledar hannunta tana karasawa ta tuma mata duka a baya cikin masifa ta soma magana.

"Yaushe raini ya shiga tsakanin mu Amnah saboda ke shegiya ce shine wato Saminu ya tambayi inda nake kika fada masa saboda kin gaji munafinci kika sa yaje ya dame ni ko"?.

Bacin rai ne sosai a fuskar Amnah tace "wai dan Allah aunty Zainab me nai miki"?.

Kan ta zeey tayo "uban ki kika min jimin yar iska, oh wato nan tsare ni kikai na fada miki abinda kika min ko? To zo ki matse ni saina fada".

Amnah zatai magana ummi ta fito tana kallon zeey cikin takaici tace "sai yaushe zaki hankali ne Zainab? Wai ace kamar ki da girman ki kinyi asara ba islamiyya sannan bazaki zauna a gida ba kullum kina waje kina yawo a titi kina zubar mana da mutunci uban me Amnan tai miki"?.

Daukar ledarta zeey tai cikin fushi tana cewa "ai ummi duk laifin kine dole ta raina ni take ganin kafadata daidai take da tata a gurin ki ta samu lasisi saidai wallahi bazan dau wannan iskancin ba zanyi maganin kowa aikin banza kawai".


Wani irin abu ummi taji ya tsirga mata bayan zeey tabi da kallo tana cewa "bazan miki baki ba domin ni mahaifiyar kice saidai nace Allah ya shirye ki".

Maida hankalinta tai kan amnah cikin jin nauyin yadda zeey din ke zubar mata mutunci a gaban yar kishiyar ta Dan ma yarinyar me nisan tunani ce.

"Kiyi hakuri kinji Amnah tunda kinsan bata so ki daina fada masa inda take idan ya tambaye ki".

Kai Amnah ta girgiza tace "nifa ba nice na fada masa ba ni a yau ma banga Saminu ba sharri ya min".

"Shikenan ko kin shiga part din naku karki kula ta kinji na sani kin fita hankali".

Mikewa Amnah tai tana daukar Jakarta tace "yau gurin Mami na zanje acan zan kwana".

"To ki gaida ita" fita Amnah tai yayin da ummi ta girgiza kai tana kallon zeey data fito tana nufar dinning table zauna sai wa'ke-wak'e take.

Ummi taso share ta Amma taji baza ta iya ba karasawa tai inda take tace.

"Yanzu ke Zainab a haka zaki ci gaba da tafiyar da rayuwar ki sakaka babu control Amnah 'kanwar kice Amma ta fiki hankali gaskiya ki gyara kafin lokaci ya kure miki".


Daina cin abincin zeey tai ta dago ta naiwa ummi wani kallo tace "wai ummi meye damuwar ki da ni ne duk kinbi kin takura min nifa bansan irin wannan sa idon ya isa haka".

"Zainab ni kike cewa na sa miki ido"?.

"Au wace ke da bazan fad'a ba jimin mace Dan Allah yadda kika zo kikai min wani tserere akai kamar wata escort dina*.

Shiru ummi tai ta kasa magana sai juya abubuwan da zeey din ta fada mata take.

"Nayi karya ne"?.

Ganin har lokacin bata tanka mata ba taci gaba "nace nayi karya ne?.

"Ai ummi tun ba yauba nasan cewa kinfi son Amnah a kaina nida nake yarki ganin ba kauna ta kike ba yasa nima nai watsi dake na bada ajiyar ki domin haihuwa ta kawai kikai bayan haka baki da wani amfani a gurina".


Hawaye ne ya cikawa ummi ido ganin yadda zeey ta mayar da kanta yar bariki.

Zatai magana jin zuciyar ta na tafasa yasa ta juya tabar gurin dariya zeey tana bin bayanta da kallo tace "tafi a hankali karki fadi ki karya kafa" .

Share ta ummi tai ta wuce ita kuma taci gaba da cin abincin ta cikin nishadi🤔.


"Salamu alaikum wai Husnah tazo inji wani" yaro ya fada yana kokarin juyawa.

"Bata nan tayi tafiya" Husnah tai maganar cikin jin haushi daidai ta fito daga kitchen.

"Amma Asma'u bakisan waye ba zaifi kyau kije ki gano ko".

"Baba bazai wuce Sadiq ba".

"Ba lallai kije dai ki gani kafin ki yanke hukunci".

Batasan yiwa baban musu don haka tadau hijab dinta tana fita kuma sai gashi abun da tai zaton ya zama gaskiya.

Tana sallama ko bari ya amsa batai ba ta d'ora "wai dan Allah Sadiq na tambaye ka tare aka haife mune"?.

Murmushi maganar ta bawa Sadiq fuskar sa a sake yace.

"a'a".

"To meyasa baza ka barni na huta ba"?.

"Saboda ina son ki amma yanzu zan baki guri ki huta sosai domin zanje gurin dad dina yana Malaysia sai nayi wata uku please Husnah kice kina Sona".

"A'a Sadiq na roke ka nima ka 'kyale ni domin Kona amince maka saidai na batawa kaina lokaci kai ba sa'an aure na bane d'an mai kud'i Saida 'yar mai kud'i haka rayuwar ta zama shiyasa bazan yarda na kamu da ciwon sonka ba".

"Zaki soni Husnah ni na fada miki wata rana".

Kaita girgiza "kada ka soma wannan tunanin domin so baya shiga lokaci guda sai kawai Wanda zuciya ta amincewa".

Kallonta Sadiq yai "to Amma ni ta amince min"?.

" A'a hakan bazai samu ba kayi hakuri".

"Husnah sonki yanzu nasa d'amba banajin akwai wani abu dazai shiga tsakani na dake sai mutuwa".

"Humm Sadiq kenan wata rana daidai ka rika tuna wannan zancen namu domin abun zai zama kamar tatsuniya".

Murmushi yai yana kallon ta yace "shikenan na yarda da ke amma kisa a ranki ina sonki ni masoyin kine".

Sauke ajiyar zuciya tai Wanda tasa Saida ya sake kallonta zatai magana ya katse ta.

"Sauri nake kinga harna so wuce lokaci na Ina kallon ki ban sani ba Nina wuce".

Kasa cewa komai tai wata babbar leda dake kusa dashi yace "ga wannan na tafi ki kula".

Juyawa yai yana tafiya tana kallonsa har ya 'bacewa ganinta daukar ledar tai tana shiga gida kan tabarmar dake shifide kusa dasu baba ta zauna tana fitar da kayan dake ciki.

Dogayen riguna ne guda biyu da kayan kwalliya da kudi dubu hamsim sai kwalin karamar waya tecno.

Innah dake kallon yadda yadda ta ya sauya tace "Husnahn kayan haka daga ina"?.

Muryarta har dan rawa take tuna yadda zasu dau maganar tace "Sadiq ne".

"Sadiq ne kamar ya"?.

Sauke numfashin kokarin hana ta magana tai tana dan kallon Innah tace.

"Shine ya ajiye ya tafi".

"Amma Husnah ya mukai dake kwanan baya ba cewa kikai bakya son shi ba"?.

"Eh baba kuma har yau ban canza ba wannan kayan ma ba ni ya baiwa ba domin zan mayar masa da abinsa gidansu".

"Karki soma zuwa gidan su ki kiyayi kanki".

"Aiko tafiyar dayai ko shekara goma zaiyi zan jirashi ya dawo ya karbi kayan shi bana bukata".

"Eh ki aje din Amma ban yarda ki mayar gidan su ba ko kije bana son a wulakanta min ke".

Mikewa Husnah tai tana daukar kayan ta shiga dakin ta dasu.


Zarah! Zarah!! umma ce ke kwalla Kira Amma babu Zarah babu alamar ta daina aikin ta tana fitowa daga kitchen ganin babu kowa a palon yasa ta kwankwasa kofar shiga part din Haidar jin nan ma shiru yasa tace.

"Tofa ina Zarah tayi yanzun nan daga fakar ido na"?.

Tunani ta tsaya yi zuwa wani lokaci ta shiga part din Badiyat har bedroom ganin Badiyat tsaye jikin window ta d'aga labule tana kallon waje tace.

"Badi'ah ina Zarah bata shigo nan"?.

Juyawa Badiyat tai fuskarta shakaf da hawaye tana kallon umma cikin mamaki sosai umma tace.

"Lafiya meke damunki kukan me kike fad'a min"?.

Kasa magana Badiyat tai sai saman gado data fad'a tana fashewa da kukan da take rikewa a yan kwanakin.

Umma dake tsaye 'kame guri guda a ranta tace kodai yarinyar nan ta fara kewar gida ne tunda tazo bata ta'ba zuwa ba shekara guda kenan"?.

"Inko haka ne zan fadawa daddy Zarah ya mayar da ita tunda ta nuna da kanta tana son gida ai dai baxa ace nice na kore taba".

Juyawa tai ta fice bata sake magana ba Badiyat data mike tana komawa jikin windon ganin basa nan a inda suke yasa tace.

"Wallahi dukkan ku biyun bashi kuke dauka ku jira ranar da zaku shigo hannu na bazan raga muku ba zwkuyi bayani ace Dan masifa kullum kuna tare ni kuma taya zan samu ya rika kula ni lallai Zarah sai na 'batar dake".


Fuuuuu tai waje da niyyar take garden din inda suke ganin su a palor ga umma a gurin yasa taja burki ta tsaya tare da Dan hararar dukkan su ukun.

"Ki karaso man kika tsaya anan" umma tai maganar suna ci gaba da tattaunawa".

Ko kula iskar ta batai ba ta juya tana komawa part dinta cikin bacin rai Wanda batasan dalilinsa ba.


Washe gari ranar weekend ne Badiyat ta sani kuma tayi alkawarin ko ta yaya sai Haidar ya kulata tun wuri tai wanka da kwalliya ta kashe dauri tare da fesa turare ta fito palor ta zauna.


Kusan awa biyu baby alamar kowa tsaki tai tana kallon agogon hannunta tace.

"Ina nan zaku fito daya bayan daya ku same ni yau koni koku a gidan nan".

Fitowar Zarah kenan ganin irin wankan da Badiyat ta dauka yasa tace.

"A'a ta yaya na doctor Aliyu Haidar irin wannan kwalliyar kure maki haka? Gaskiya da yaya ya fito zai miki kyauta domin kin dau wankan ala tsine uwar mai 'karya na gaida ke aunty badi'ah na😜".

Harara ta sakar mata daidai Haidar ya fito tace "kinsan Allah Zarah ki shiga hankalin ki niba sa'ar ki bace".

'Yar dariya Zarah tai tana kallon Haidar tare da rike masa hannu tace.

"Barka da safiyar ranar asabar yaya doctor".

"Ya kike fatan kina lafiya kuma babu wata matsala"?.

"Eh yaya babu komai kawai yau ina so mu fita tunda ranar hutu ce saidai dad yana gida idan ya fito zan tambaye shi".

Bai zauna ba yana tsaye a inda yake yace "xaki fita yanzu ma kuwa 'kanwata abinda kike so shine za ayi".

Kallon Badiyat yai wacce ta zuba musu ido yace.

"Ya kike"?.

Zaro ido waje tai sosai kamar zasu fad'o kasa tare da murje idonta dakyau Dan ta tabbatar ba mafarki take you back a zahiri ne yau Haidar ya budi baki ya mata magana da kansa kodai aikin da zeey tace zatai mata ne aka fara? Ta tambayi zuciyar ta.

Sake fito da dukkan girman idonta tai tana kara kallon sa tace "ya Aliyu kaine kayi min magana yanzu ko ina mafarki ne"?.

Bai kalli inda take ba a hankali yace "no you are not".

Dakyar taji abinda yake cewa Wanda yasa ta mike a zabure tana karasowa inda yake tsaye.

Ta kasa cewa komai sai kallon 'kurulla da take masa kamar bata ta'ba ganinsa ba sai ranar.

Zarah dake can kan dinning tana breakfast dariya take musu domin abin nayi ne.

Saida ta gama ta dawo tana cewa "yaya mu tafi na gama".

Sun fara tafiya ya tsaya batare daya juyo ba yace muna jiran ki a mota, a wannan lokacin ba Badiyat ba hatta Zarah Saida mamaki ya kama ta.

Balle uwar gayya a guje ta juya part din ta tana dauko wani dan mayafi ta fito kamar zata kifa dan sauri ta shiga motar jikinta har rawa yake.

Ga wata murna data baibaye ta harta kasa cewa komai abun ne ya bata mamaki ganin ya tsaya ya mata sayayya kuma ita kadai banda Zarah Saida lokaci guda taji faduwar gaba ganin ya nufi anguwar su.

Kasa magana tai Saida sukaje har harabar gidansu yace "fita".

Muryarta na rawa sosai tace "naje ina ya Haidar"?.

"Ki shiga gidanku ba kuka kike ba acan kina son dawowa gida shiyasa na taimaka miki".

"Ni wallahi ya Haidar bance ina son na dawo gida ba".

"To me kike nufi? kinsan dai baki isa na sake dakon ki zuwa gida ba".

"Nikam saina koma acan nake son zama" ta karasa maganar tana goge hawaye.

"Out".

Taji yace cikin hade rai 'kin fita tai zatai magana ya daka mata tsawa domin ya tsani musu dashi.

Da gudu ta bude motar ta fita tana fashewa da kuka tai cikin gidan su.

Zarah dake kallon Haidar tace "Amma yaya meyasa ka dawo da ita"?.

"Daddy ne yace haka".

"Oh shikenan kace mun yada mangoro mun huta da 'kuda" tada motar yai suka bar gidan.


Badiyat na shiga gida ganin maman ta a palor yasa taje ta fad'a kanta tana kuka.

"Ke lafiyar ki daga ina haka sassafe meyasa kike kuka"?.

Dagowa Badiyat tai tana kallon mamanta tace "mama an wulakanta miki ni".

"Waye ya wulakanta ki fad'a min"?.

"Waye zai wulakanta ni mama bayan ahlin gidan daddy kamar ni ba jinin suba haka suke nuna min bambanci komai nai cikin hantara da tsangwama nake".

Cikin bacin rai mama tace "ke dama kinsan ga irin zaman da kike a gidan shine bazaki dawo gida ba sai yanzu da kikaga zasu kashe ki to shi Yusuf din yana ina suke miki hakan bai dau mataki ba"?.

"Yana office mama ai bazai San abinda yake faruwa ba tunda ko yana gida basayi a gaban sa saiya fita".

"Kaji shegu dama ai na fada miki karkije kika 'ki ko ba komai kin zubar da ajinki a gunsu yanzu bazasu kalle ki da daraja ba gani zasuyi kamar zaman maula kike a gidan su dama dangin uba haka suke da tonawa mutum asiri shiyasa tun farko nace kije gurin yayana ubaliyo ko kije gidan kamisu tunda zaman cikin dangi kike so Amma kika 'ki sai yanzu zaki zo ki dame ni".

"Ai ni mama ba dangi na ne suka koro niba matar daddy Yusuf dince wai na tafi tunda gidan bana uba na bane".

"Inji ubanwa gidan bana ubanki bane itace ma za acewa gidan bana ubanta ba tunda ko yanzu ya d'aga mata Jan kati dole tabar gidan".

Mikewa Badiyat tai tana sharbar hawaye tace "ai ba hakura nai da zaman gidan ba saina koma".

"Bazan hana kiba kuma duk Wanda ya kawo miki rashin da'a a cikinsu kada ki 'kyale kowanne Dan iska kici min uban su" mama ta karasa maganar harda dunkule hannu.

Karshe ma ta mike tana dauko hijab da key din mota tace "muje na mayar dake".

Fita sukai ba kunya haka mama taje ta rika baza rashin arziki a gidan kuma dama tun daga harabar gida ta tambayi masu gadi suka ce mata daddy ya fita.

"Wato Aisha saboda diban albarka akan baki gaji arziki ba shine kina kallo fitsararrun 'ya'yanki suke wulakanta min 'yata harda wani wai ba gidan ubanta bane, to ai Masha Allah domin shima mutum ba gidan ubansa bane gara ita wan mahaifinta ne amma kefa ko yanzu ya baki red card dole ki ware gidan tsoho"🙊.


Kallon ta sosai umma keyi da kuma mamakin maganar data fad'a Wanda tasan wace Khubrah wajen iya rashin mutunci".

"Aisha kallo na kike kamar yau kika ta'ba

Please Login or Register in order to submit comment