Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

๏ปฟ[08/23/05 08:18pm] Yusrah Musa Abubakar.

Cikin biyu โœŒ๏ธ
* HUSNAH KO BADIYAT*


}{SHORT STORY}{

ANNURI WRITER'S ASSOCIATION
Home of hospitality and harmony

Mrs Al'ameen Ahmad ce
WHATSAPP NO: 234 905 527 3614.

YUSRAH MUSA ABUBAKAR
MAMAN FATEEMA ELHAM
(*()*) (*(*()*)*) (*()*)

In the name of Allah the most benefits and the most merciful we love our nabeey we like him and peace be upon him ameen.

Dedicated to
ANNURI'S WRITER'S ASSOCIATION GROUP MAY ALLAH ACCEPT YOUR DUAS MAY ALLAH HELP YOU AND PROTECT ANY WHERE YOU ARE AMEEEN๐Ÿ‘.


Mrs Al'ameen Ahmad ce ๐ŸŒน.

PAGE 01 to 05.
Wani 'karamin gida ne mai dakuna biyu wanda kana gani iya yanayin sa ko ba a fada ba kasan gidan haya ne duba da cewa komai a matse yake.


Zaune wani farin tsoho yake gefen sa kuma wata mata ce itama fara da sanda a kusa da ita Wanda alama ya nuna tana da ciwon kafa dashi take amfani gurin tafiya.

Hira suke sosai jin sallama yasa suka amsa baba dake kallon saitin inda akai sallamar yace.

"Sannu da gajiya kinji Asma'u ya karatu"?.

Zama wata kyakkyawar budurwa ta tana kallon su cikin nutsuwa tace "alhamdulillah baba ya gida kuyi hakuri ban dawo da wuri ba na barku da yunwa jarrabawar yau dince ta dauke mu lokaci kuma zan taho Fatima tace na tsaya idan aka zo daukar ta sai mu taho tare".


Murmushi baba yai yana cewa "kai Husnah irin wannan dogon bayani haka ai sai kisa kaina yai ciwo buri na ace kin dawo lafiya shine fata na".

"Lafiya kalau baba kallon matar tai cikin muryar shagwaba tace "innah muna ta magana kinyi shiru kin 'ki saka baki ko laifi na miki"?.

Dariya Innah tai tana cewa "oh ni Husnah rigima kin girma fa kodan baki da 'kani shiyasa kike jinki yarinya to ya makaranta fatan kin dawo lafiya".

Kaita daga "lafiya na dawo Innah ta bari na tashi na sama muku abinda zaku ci".

Hanyar kitchen ta nufa yayin da suka bita da kyakkyawar addu'ar jin dadin kula dasu da take da nuna musu kauna.

Saida ta Dora farar shinkafa sannan ta fito tana yin alwala ta shiga daki domin yin sallah.


Bayan ta idar fitowa Tai tana komawa kitchen ta duba sannan ta leko tana cewa.

"Gaskiya yau miya za ai domin shinkafar tana kyau bari naje na sayo".

" Husnah mu da muke tsofi basai kinyi mana wani 'kyale-'kyale ko fara kika mana da yaji zamu ci".


"Allah baba ta miya zata fi dadi Bari na je nasayo Dan yau harda nama zaku ci" tana fadin haka da sauri tai waje kafin baba yai magana.

Kai Innah ta girgiza tana duban baba tace "abin da take so yau din muci kenan saidai Allah ya mata albarka".

Da kamar minti biyar ta dawo tana dariya ta shige kitchen tana fara hada miyar.


Saida ta gama sannan ta xubo a babban faranti tazo tana zama a tsakiyar su tare da gaurayawa cikin so da kauna suke cin abincin.


Yayin da idwn ta debo saita bawa Innah a baki sannan ta sake debowa ta bawa baba.

Suna matukar jin dadin yadda take nuna kulawar ta a gare su suna farin ciki da samun ta matsayin d'iya a gare su.

Saida suka gama ta tabbatar sun koshi ta dau ture din tana komawa kitchen ta wanke kayan data 'bata ta fito kenan.


Yaro ya shigo yana cewa "wait wani yace Husnah tazo".

Hade rai Husnah tai tana kallon sa tace "kace bata nan".

"To yaron yace zai juya baba ya dakatar dashi yana cewa.

"Asma'u baki san waye ba kije ki duba".

Kallon baba Husnah tai tace "baba bazai wuce Sadiq ba domin na wuce shi a majalisar kofar gidan alhajin da muke hayar gidan nan a gurin sa".

"To me zaki masa yake neman ki"?.
Husnah dake hararar kofar gidan kamar shine a gurin tace "babu abinda daya taba hada mu bansan neman me take min ba".

Tana fadin haka ta shige daki shiru baba yai zuwa wani lokaci yace.

"Lamarin yaron nan yana bani mamaki to kodai sonta yake nifa bana San irin wannan abun ina zaune da yarinya ta lafiya azo a daga min hankali".

Innah ma da yawan n turowa da Sadiq din take neman Husnah tace "nikam da tun kwana baya zanyi magana kuma na fasa amma muci gaba da addu'a idan shine alkairi a gare ta Allah ya Tabbatar idan babu alkairi Allah ya raba ta cikin ruwan sanyi".

"Amin" baba yace daga haka suka dau wata hirar dabam suka manta da wannan zancen.


Mrs Al'ameen Ahmad ce ๐ŸŒน
YUSRAH MUSA ABUBAKAR GIMBA


Na gode da kulawa tnk 4 ur supports may Allah open the door of success and happiness 4 all of u Muslim Amin๐Ÿ‘๐Ÿฅ€โœจ.

ANNURI WRITER'S ASSOCIATION
Home of hospitality and harmony

Allahumma salli wa salli ala sayyidina Muhammadin sayyidil mursali na.


Mrs Al'ameen Ahmad ce ๐ŸŒน
PAGE 06 to 10

Wani 'kayataccen gida ne Wanda ya shahara wajen tsaruwa da kyau fadar kalar daular sa bata ๐Ÿ•š ne.

Zaune wani farin kyakkyawan saurayi yake cikin palon da laptop a gabansa yana aiki bayan sa wata budurwa ce ta tsaya ta bayan kujerar ta sakalo hannuwanta ta wuyan sa tana kallon abinda yake yi.

Fitowar wata mata ganin su yasa ta girgiza kai tana karasawa tace.

"Sannun ku da hutawa".

Duk su biyu dagowa sukai suna kallon ta taci gaba "wato Zarah dama da nace kije kitchen gurin Rabi ta rika koya miki yadda ake sarrafa komai shine kikayo nan kinsan dai abin kunya ne ace kamar ki ayi auren ki baki it's komai ba".

Sakin wuyan sa Zarah tai cikin shagwaba tace "Allah umma naje tun dazu gajiya nai shine shine naxo in huta ban dade da zuwa ba kuma ki tambayi ya Aliyu kiji".

"Ni bazan bata lokaci na natambaye shiba bayan bakin ku daya maza tashi ki koma bansan shirme".

Mikewa tsaye tai tana cewa "Amma umma Badiyat tana can tana bacci ita baza ta zo ayi aikin da ita ba"?.

Kai umma ta daga "eh baza tazo ba ina ruwan ki da ita ko ce miki tai bata iya girki ba"?.

Zarah zata magana umma ta katse ta "nace maza ki wuce yanzu ko".

Juyawa tai Tana nufar hanyar kitchen din umma data mayar da hankalin ta kansa tace.

"Haidar ka shagwaba yarinyar nan da yawo gashi har yanzu taki maida hankali ta koyi girki".

Shiru yai Saida ta sake magana ya dago yana kallon ta cikin muryar shi nutsatstsiya yace.

"Umma duk duniya bani da wacce zan kalla naji dadi ko nayi alfahari idan ba Zarah ba ita kadai ce sister na yar uwata jini na 'kanwa ta dukkan soyayya ta tana gurin ta da ban debe kewa da ita ba dawa zan debe"?.

Cikin tsokana umma tace "idan wacce zata debe maka kewa kake nema sai kai aure".

"Ba yanzu ba umma".

"To sai yaushe"?.

"Ba Rana bana jinsa kusa".

Juyawa umma tai zata bar gurin tace "shikenan Haidar Amma nikam ina jinsa a kusa" tana wucewa ciki.


Rufe laptop din yai yana jingina bayansa jikin kujerar tare da rufe ido alamar ya gaji hutawa zaiyi.

Da kamar minti goma wata budurwa ta shigo palon tana hamma alamar daga bacci ta tashi ganin sa shi daya yasa ta karaso tana zama kusa dashi.

Tace "good morning ya Aliyu fatan ka tashi lafiya"?.

Bai ko motsa ba balle tasa ran zai bata amsa.

Muryarta a damuwance tace "wai dan Allah ya Haidar meyasa kake min haka ne sai ka rika share ni idan na maka magana nima fa yar uwar kace kamar yadda kake ji da Zarah ya kamata ka saurari hanzari na".

Jin har lokacin ya mata banza bai tanka mata ba yasa ta kalle shi idonta na kawo hawaye.

Daidai shima ya bude idon sa sai cikin nata dauke kai yai yana bude laptop yaci gaba da aikin sa kamar baisan da wanzuwar wata halitta a gurin ba.

Cikin jin haushi ta mike tana barin gurin ta nufi dinning tana 'kwalawa yar aiki Kira".


A guje ta karaso tana durkusawa gaban ta numfashin ta kamar zai fita tace.

"Gani aunty".

Xama Badiyat tai tana cewa "yi serving dina abinda ya Aliyu yai breakfast dashi".

Shiru yar aikin tai cikin jin tsoron me zata ce tsawa Badiyat ta daka mata tace.

"Ke dabba uban me kike kallo cewa nai ki serving din".

Jikinta na rawa kamar yadda muryar ta keyi tace "kiyi hakuri yau baiyi breakfast b.............


Bata karasa ba Badiyat ta dauke ta da mari cikin bacin rai tace "bace min da gani kafin na zubar miki da hakora banza jaka yar kauye kawai akuya".

Da gudu tabar gurin rike da kunci tana kuka batasan me taiwa wannan budurwar ba tun ranar da tazo gidan nan shikenan ta hana ta jin dadi gara ta cewa baba raba ta gaji tayi magana a sallame ta ai talauci ba hauka bane.

Mikewa Badiyat Tai tana komawa cikin palon ta zauna tasan saboda ita ne Haidar ya daina cin abincin gidan Amma baby komai tara shi take.


Zarah ce ta fito tayi tumu tumu da jikinta tazo tana zama kusa da Haidar tace.

"Wash Allah gaskiya yan aikin suna kokari Allah ka zama gatan su ๐Ÿฐ din da tazo dashi ta bawa Haidar a baki tana cewa.

"Yaya kaci irin girki na kaji ko hannu na ya soma fadawa"?.

Dagowa yai yana kallon ta yace "good 'kanwa ta ki sake kokari" ya karasa maganar yana bata sauran cake din data bashi a baki.


Murmushi tai cikin jin dadi zatai magana ganin umma ta fito yasa Tasha jinin jikinta tana cewa.

"Allah umma mun gama kuma kije ki tambayi baba Rabin ita tace min na taho".

Kai umma ta girgiza batai magana ba tai hanyar kitchen da sauri Zarah ta mike tana kallon Haidar tace.

"Yaya zan buya a part dinka kafin umma ta dawo Allah na gaji".

Kallon ta yai alamar ta dauko masa laptop dinsa shima tafiyar zaiyi rufewa yai yana mikewa yai gaba yayin da Zarah ta dauka tana bin bayansa cikin dariya ganin har lokacin umma bata fito ba.

.
Da harara Badiyat ta rakata ta sani cewa Zarah kanwar Haidar ce uwa daya uba daya Amma tana matukar jin kishi zafi rad'ad'i a duk lokacin data gansu tare.

Cikin takaici tace "walkahi duk kunyi da yar halak na rantse Zarah saina mayar dake abar tausayi tunda saboda ke Haidar ya'ki saurara ta balle ya bani lokaci muyi magana indai na cika suna na Badiyat saina mayar dake abar tausayi Dan wallahi bazan zuba ido bakin cikin ku ya kashe niba saina dau fansa".

Umma data zo wucewa ne duk da bataji komai cikin abinda Badiyadin ke cewa ba ta tsaya tana kallon ta tace.
.
"lafiya kike magana ke kadai"?.

Daidaita nutsuwar ta Badiyat Tai tana cewa "eh umma lafiya kawai wani saurayi ne yake damu na a waya ya hana ni sakat".

Wucewa umma tai tana cewa "ki rika kula sosai ba kowanne kalar saurayi zaki na kulawa ba".

Tsaki Badiyat tai bayan tafiyar umma tace "ji min munafikar mata ina ruwan ki da kalar samarin da nake kulawa zaki wani dame ni zaku gane kuren ku ne a juri zuwa rafi".


Zaune Husnah take a kofar gidan su tana soya awara kamar yadda ta saba Fatima na gefen ta suna Hira Husnah tace.

"Fatima karfa yayan ki Jabeer ya koma gida ace masa bakya nan ya dake ki kinga karshe takwas tayi".

"Cabdijam waye ya fada miki aini yanzu nafi karfin haka wuce nan saidai yaiwa su Aisha".


Yar dariya Husnah tai cikin tsokana tace " umm umm fa Banda cika baki karmu jiyo ihun ki daga nan kina cewa Dan Allah yaya kayi hakuri".

"Daga baya kenan kema dan baki da yayan ne shiyasa kike cewa haka".

Husnah zatai magana sukaji ance salamu alaikum sannun ku".

Dagowa sukai ganin wanda yake tsaye yasa Husnah kara hade fuska tana dauke kai Dan bata son damuwa ko kadan.

Xama yai akan wani karamin dutsi dake gurin yana kallon ta yac "Husnah Dan Allah ki bani lokacin ai yaushe ki fada min zan iya jiran ki konan da shekara ne"?.

"Ba lokaci kawai kai hakuri".

"Haba Husnah dan Allah ki saurara kiji abinda zan fada miki".

"Ina jinka".

Gyara zama yai yana fuskantar ta sosai domin abinda kake so baka zuciya dashi.

Yace "Husnah tsakani da Allah zan fada miki gaskiya ina sonki".

Zaro ido waje Husnah tai ba arziki tana kallon shi muryarta na rawa tace "kana sona kuma"?.

" 'kwarai ina son ki kuma ba da wasa ba son aure fatan zaki amince min"?.

Kai ta soma girgizawa tace "a'a Sadiq bazan bata lokaci na ba na yaudari zuciya ta akan abinda ba tabbas bane kawai kayi hakuri bazan iya ba".

"Mene bazaki iya ba a cikin soyayya dani ko aure na"?.

Kai tsaye ba wani boye boye ba kwana kwana tace "duk biyun. babu Wanda zan iya Dan haka ka rabu dani".

A rude Sadiq yace "kar ki min haka Husnah wallahi da gaske nake ina sonki".

"Nifa ka 'kyale ni hakan bazai samu ba".

Ganin ta dauke kanta yasa ya kalle Fatima dake gefe tana sauraron su yace "ki fahimtar da 'kawar ki ta gane halin da zuciya ta take ciki ta karbe ni ta sani a sahun masoyan ta na 'kwarai".


Cikin tausayawa Fatima tace "karka damu insha Allahu zata fahimce ka zaka samu amincewar ta kamar yadda kake fata".

Mikewa Sadiq yai yana sake kallon Husnah datai bala'in dauke kai yace "shikenan na gode Fatima saida safe" juyawa yai yabar gurin.


Yayin da Fatima ke kallon Husnah tace "gaskiya kawata ba haka ake ba wannan shariyar tai yawa ya kamata ki rika sassauta masa duk Wanda yace yana sonka ya gama maka komai a rayuwa".

Kai Husnah ta girgiza tana cewa "kema kina goyon bayan sa kenan"?.

"A'a Husnah bawai batun ina goyon bayansa bane kawai dai gaskiya nake fada miki Sadiq mutumin kirki ne kuma ya cancanti a soshi ta ko'ina".


"Ni basan bata lokaci na akan saba domin shi d'an masu hali ne nikwa fa kuma koba haka ba bani da sa ran zanyi sure bazan iya nisa da mahaifana ba idan nai aure na tafi na barsu waye zai kula dasu baba ba gani yake ba Innah kafarta na ciwo ki duba lamarin".


Fatima tace "ai 'kawata duk wanda ke sonki zai iya kula da mahaifan ki musamman Sadiq wallahi gayen nan yana da hankali".

"To naji abar maganar".

Murmushi Fatima tai tana mikewa tace "shikenan Husy an barta bari na wuce gida sai gobe idan munje school zamu dora".

"Ok Saida safe Fatima" Husnah ta fada itama tana kashe sauran iccen data gama suyar ta tattare kayanta tana shiga gida.


Tunda ya fito ta tsayar da idanuwanta akansa cikin so take kallon sa dakyan dayai cikin shigarsa ta likita yana karasowa dinning din ta mike cikin kashe murya tace.


"Good morning ya Aliyu me zanyi serving dinka"?.

Banza ya mata bai tanka ba fitowar Zarah kenan daga part dinta tana sauri zata tafi school bata ma lura da suba.

Da muryarshi a hankali yace "Zarah".

Juyowa tai ganinsa yasa ta aje handbag dinta tana tahowa da murnar ta bude mata hannu yai tana zuwa ta d'ale shi tana cewa.

"Good morning BB (Big Bro๐Ÿ˜œ).

"Morning fatan kin tashi lafiya"? ya fada yana komawa ya zauna zama itama tai a kujerar kusa dashi tana hada masa tea da Irish sannan ta hada nata ta soma sha.

Rike masa hannu tai cikin shalele tace "yaya yaufa kaine zaka kaini school".


"As you wish 'kanwata da kaina zan kai ki".

Badiyat dake tsaye tserere kamar an dasa bishiyar dogon yaro cikin jin takaicin katse mata hanzari da Zaran keyi tace.

"Nima ya Haidar yau zanje school saimu tafi tare idan kai kaita nima saikai dropping dina".

Ganin bai kula taba taci gaba "ke kuma na dawo gare ki uwar shishshigi duk kin bi kin kanainaye shi ki sani dai babu aure a tsakanin ku sai wani li'ke masa kike kamar tip da taya wannan ko aure yai muddin kina gidan nan baza kibari ya bawa matarsa cikakkiyar kulawa ba kullum kina manne dashi kamar tip da taya".


Dire cup din hannunta Zarah tai tana kallon ta tace "wai dan Allah Badiyat meye damuwar ki dani ne? A kin manta ba tip da taya zaki ce ba saidai super glue wallahi ki cire idanuwanki daga cikin samun ido ina kema kina da yayan saiki koma gidan ku ki rika masa isa nai shiyasa".

"Bazan koma gidan namu ba anan nai niyyar zama kuma babu wanda ya isa ya hana ni".

Tabe baki Zarah tai "babu kam madam 'kwas'kwas Amma ina mai baki gargadin ki fita hanya ta kafin na dumama miki jiki".

"Kam bala'i nice zaki dake kike nufi wallahi da saidai ki kwanan asibiti a ranar Dan sai na kakkaya ki".

Zarah zatai magana Haidar ya rufe mata baki yana kallon cikin idon Badiyat yace.

"Zarah kina da aji baki da lokacin shirme muje".

Mikewa yai rike da hannunta suka bar gurin Zarah data tana hararar ta tace.

"Zan kama kine zaki bayani".

Cikin bacin rai Badiyat ta daga murya tace "saidai ki kama uwarki mitsiyaciya kawai".

Tashi tai daga gurin fuuu kamar iska na deban ta harda bol da Jakarta ta wuce part din ta tana zuwa ta zauna akan stool tana kife kanta akan mirror cikin kuka ta soma magana.

"Wallahi Zarah kinyi da yar halak zan nuna miki iyakar rashin kunyar ki saina mayar dake abar tausayi yadda kika sani kuka kema saikin zubar da hawaye kuma zaki gani".


Zaune suke karkashi wata ni'imtacciyar bishiya suna Hira yayin da suke kallon wadanda ke filin rawa suna cashewa.

Hamidah tace "oh kalli dai Dan Allah ji yadda saira take rawa a gaban mutane sai lankwasa jiki take kamar ta karye".

Cikin tsokana Husnah tace "murnar graduate ne kema ya kama ta kije ki d'ana".

Zaro ido tai "kee rufa min asiri so kike yaya Muzammil ya kusa kashe ni ko idan na koma gida".

"Ba wani dan yau daya kawai".

"Yau dayan ke kije ki cashe mana" Fatima ta fada tana kallon yadda wata daliba ke karye karye.

Dariya Husnah tai "ai ni kinsan bana rawa ni salihiya ce๐Ÿ˜".

Fatima tace "nikam banga abinda burgewa a rawa ba kodan ban saba bane ai Hamidah ba keba koni da ya Jabeer baida kowa cikin school din nan bazan iya rawa gaban mutane ba".

Hamidah tace " to kin gani dai kalli ga Ishat can ma tana fama".

Wata budurwa ce ta karaso gurin tana kallon su tace "wai wace Husnah Ibrahim"?.


Cikin faduwar gaba Husnah tace "nice lafiya"?.

Kai ta daga "eh ban sani ba uncle Shareef ne ke neman ki yace kije yauzu".

Tana fadin haka ta wuce dafe kirji Husnah tai "na shiga uku me zanyi masa"?.

Fatima tace "kila baki sani ba ko mistake ya gani game da jarrabawar ki kije kiji Kiran me yake miki zan jira ki anan kafin azo dauka ta".

Mikewa Husnah tai tana tafiya jikinta a matukar sanyaye har ta karasa kasa kwankwasawa tai ta tsaya kawai tana kallon kofar office din tafi minti goma kafin tai knocking".

Tana daga waje taji muryar sa yace "come in shigo man".

Saida ta sauke wani zazzafan numfashi sannan ta bude tana shiga zaune ta same shi yana duba takardu gaida shi tai hannu kawai ya daga masa anan ta sake tsinkewa.

"Have a seat ko kinfi son kita tsaiwa" zama tai cikin rashin sukuni.

Tana cikin tunanin dalilin dayasa ya Kira ta taji yace "Husnah ibrahim ko"?.

"Eh uncle nice".

"Ok kinsan meyasa na Kira ki"?.

"A'a uncle".

Kai ya jinjina yana dagowa tare da zuba mata ido yace "Husnah ina sonki tunda kika shigo makarantar nan na ganki kuma na ajiye a Raina sai kinyi graduate zan furta miki fatan zaki amince domin auren ki zanyi".

Jikin Husnah na tsananin rawa ga wani uban tsoro daya lullube tavlojaci daya jin abinda yace dakyar muryarta na kakarewa tace.

"Uncle anyi min miji".

"Whattttt? Anyi miki miji"? Ya fada cikin tsawa.

Wanda Saida ta zabura mikewa yai ya soma zagaya office din yana fitar da iska mai zafi .

Shiru Husnah tai tare da sunkuyar dakan ta hawaye na zuba taji yace.

"Tashi kije".

Tun bai karasa ba kamar wacce ake hankada ta da gudu tai waje tana sauri kamar zata tashi sama har ta karasa gurin da motar gidan su Fatima take.

Ganin yadda take a rude yasa Fatima tace "ke Husnah lafiyan ki kalau kuwa? Me kika yiwa uncle Shareef din"?.

Kuka Husnah ta fashe dashi tana cewa "na shiga uku Fati wai Sona yake".

Zaro ido Fatima tai "sonki kuma? jimin tsoho da karambani".

Goge hawaye tai tana cewa "wai harda wani tun shigowar mu school din nan yake Sona kiji fa".

Dariya Fatima tai tana kallon Husnah tace "to kema Husy kina da laifi ga samari masu jini a jiki suna sonki kin 'ki amincewa har tsofi sun fara layi".


"Su waye samarin"?.

Fatima tace "kai Sadiq man Allah 'kawata ki tsaya kiyi tunani shi din ya dace ki so shi".

"Humm Fati kenan sau nawa zan fada miki ni baby aure a tsarina bazan iya nisa da mahaifana ba".


"Shikenan Allah ya baki wanda zai hada harda su ya rike".

"Amin Dan saidai hakan".

Daidai sun karaso driver ya tsaya ta fita sannan ta mata godiya tana juyawa sukai ido biyu da Sadiq.

Dauke kai tai kamar bata ganshi ba zata wuce ya sake shan gabanta yana cewa.

"Haba Husnah dan Allah ki taimaka ki saurare ni kozan samu sauki".

Ganin yadda samarin majalisar suka zubo musu ido yasa ta ce "ba yanzu ba".

"To sai yaushe ki bani lokacin da kike so da kanki"?.

"Sai anjima" ta fada cikin son ya barta ta wuce.

"Ok nagode saina zo".

Bata tanka masa ba yana matsa mata hanya ta wuce zuwa gida cikin mamaki take kallon tulin kayan abincin dake zube a kofar dakin su.

Tace "wannan kayan kuma fa daga ina"?.

Baba ne ya bata amsa "Sadiq ne ya kawo su daxu bayan tafiyar ki makaranta".

"Amma baba meyasa kuka karba"?.

Tashi xaune baba yai daga kishingiden da yake yana kallon saitin inda Husnan ke maganar kamar yana ganin ta yac e.

"Asma'u a yanayin maganar ki kin nuna bakya ra'ayin sa"?.

"Eh baba gaskiya yafi karfi na shiyasa ma bazan wahalar dakai na

Please Login or Register in order to submit comment