Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

data tina saitaji komi yawuce
Lokacin da abun yafaru fujjilat da musahna har sunfuto waje tarako musahna batajiba haka shima Nu'uman din

Tundaga nesa fujjilat tahango motar Ubaid gabanta yafadi
Nu'uman dake cikin mota shida jaleel yafuto kenan xaikasa ciki sbda hango su mama dayayi na futowa xasu tafi saiganin mutum yayi agabansa
Yasan hakan xatafaru shiyasa yatanaji abubuwan kare kansa donhaka shima hade rai yayi yana kallon Ubaid dake tsaye gabansa tamkar xaki.
Kafin yanuna Nu'uman da tsaya
Ban mamaki ba sbda kalar fuskar ku kenan ta xahiri irinku, amma kasani naga ragwanta ka tsagwaro da rauni atattare dakai satar amsar dama ita tadace dakai domin kuwa kaikasan axahiri fujjilat kaxo mata baxata soka ba, kuma nasan daba xakataba samun soyayyarta ba, s.......
Ya isa Nu'uman yabuga masa tsawa
Badan vaka cikin hayyacinka aidanafada maka idaninka sundade suna nunamaka gaibu sbda kaikasan waye ni mata bina suke suna kuka in soyayya dasu inaki kaiga nau ne ba jiyau ba nasara kuma nayi babukata ta kayabeni koka kusheni ba aa cikar burina sauran duk daga baya kafahimta ubaid wallahi inkunkai ku goma kuke son fujjilat xan iya dafa al kur ani mai tsarki akan ku duka nafiku sonta ko baka ganiba aidama ita nasara tana xuwa ne gawanda yafi cancanta

Karya kake wlhi idan ko har hakane bawanda yafi cancanta da ita kamar ni!
Haisam kenan dayaka rasa xuwa gaban Nu'uman
Duk dabansan kaba amma naga alamun soyayyarta acikin idaninka amma ni idan kaduba aduk jikina ma sonta ne itace waccce xan aura akasi akasamu kuma nadawo yanxu donhaka kuma bar rigima Dan banga amfaninta ba,

Hhhhhh ubaid yasa dariya yana kallonta haisam don bai taba ganinsa ba labarinsa kawai yaji abakin fujjilat
Au dama kaine Haisam din tab aiko najinjina wa rashin rabo irin naka lallai yakamata ama jaje domin kuwa katafka babbar asara wacce baxakataba maida irin taba
Yana nuna Nu'uman
Kaikuma kashiga hanklin ka tin kafin dare yayimaka karo dani Ubaidu badadi kaikasani
Yajuya inda fujjilat da musahna ke tsaye sunyi fasta kwakkwaran motsi sunkasa sbda ganin tashin hankalin dake faruwa
Nu'uman yaja tsaki
Yana shigewa mota
Haisam yajawo kafadar Ubaid dakarfi suka fuskanchi juna
Ba ashiga gonata afuta salin alin kai har ka isa kafadamin magana kaci bulis?
Wlh saika samu kwakkwarar amsar data ninka taka sau milion,
Amma bari nabari saiwani jikon ga xahiri kaidin matsora cine
Ubaid yadaga hannu xaikwashe sa damari fujjilat tarike hannunsa
Duka kallo yakoma kanta alhaji shafi u alhaji adamu inna habi mami baba h da dahda duk sun rako mama ne da Alhaji shafi u, sukayi turusss
Karka maresa kyalesa yah Ubaid kabarsa yaji ma kadai da abun dake damunsa wlh Haisam baxakataba samuna matsayin mataba idan ban da kai din bakada kunya ba ka isa kakuma nuna wai kanasona ba kamanta abun dayafaru tsakanina dakune? Humm da alama toh kajuya kaje kasake rayuwar dababu ni kakuma koyawa kanka kina domin bana kaunarka
Haisam yarike kansa dake juya masa
Fujjilat nikike gayawa haka bakya kaunata fa kikace?
Anfada ko akwai wata kalmar datafi ta xafi nayaba maka kai mekafadamin au bansan ciwon kainaba kenan kayi kuskuren fahimta
Takalli ubaid
Yah ubaid kaje gida xami magana awaya naji duk abindaya faru tsakaninku kuma nafahimta atakaice kaine kanemomin mami donhaka kai xan aura
Nu'uman dasai ganin sa akayi akasa
Ashe yabude motar afasace xafuto ne kansa yayi nauyi kirjinsa yadau xafi kafin yakuma yunkuri yafado daga mota asume
Ehu musahsana tasa tayikansa mami ma gurinsa tayi dasauri jaleel ma kuka yasa yana mika hannu dagwarancinsa
Uncle uncle
Fujjilat da ubaid har Haisam sai lokacin suka fahimci halin da ake ciki inna habi ce taruga gida tadebo ruwa tadawo akafara shafa masa
Mami ce takalli fujjilat ranta amutukar bace
Kekuma indai nice mahaifiyarki na umarceki dakibar gunnan kikoma cikin gida kuma indai xaki min biyayya toh kisani baki da wani miji bayan Nu'uman fice ki ban gu
Fujjilat kuka tasa tana fadawa gidan inna habi da gudu
Ubaid harkasa yatsuguna yaba mami hakuri sannan yashiga mota yabar gun Haisam afasace yabar gun shima bayan farfadowar Nu'uman mama da alhaji shafi u suka tafi duk da Nu'uman baigama wartsakewa ba mami sai shafa kansa take tana lallashinsa domin tadauki Nu'uman tamkar danta baxata taba bari ya cutu ba kuma fujjilat shixatabawa hankalinsa yakwanta sosai jin yadda mami ke tamasa lallashi da alkawarirrika akan auren fujjilat
Haka suka tafi mama da alhaji sunji dadin yadda mami tanuna kulawar ta akansu da dan nasu alamu yanuna xatayimusu halacci,
Babha ne bayan komi yalafi yakalli mami
Toh yanxu saiki tashi mutafi ko
Mikewa tayi tana goya jaleel
Alhaji adam yadubi inna habi
Tagane donhaka takalli su bahba
Yakuma xa ayi haka bahba
Bakomi munason 'yar mu akusa damu ne wannan karon donhaka yasaketa yanxu duk da kinga yanxu aurenma ashiri ar musulinci babu shi jamila tashi muje
Baxa ayi hakaba bahba takoma dakinta yau bayan sallar mangaruba sai a sake maida auren
Inna habi taimaganar
Aa Allah yabada lada axaman baya dasukayi naga ba kuma babu don ba xamu mukumayin sake da 'yarta mu kwara daya tak?! Ba yaje nangaba yasalwantar mama da ita don haka don Allah muduka muyi hakuri aure ne ahakura haka,
Kafin tasake magana sunbar falon mami ko ajikinta domin itama batason komawa gwara takoma gaban iyayen ta daxama ta da safara u dangin shedan
Alhaji adam yanaji yana gani bahba yasa jamila agaba suka bargidan ko kallonsa batakarayi bama balle yasa ran xata ga hawayen dake xuba a idaninsa tashare masa tadawo dakinta
Yaji ana share masa hawayen
Abba kadaina kuka dan Allah
Fujjilat kenan data fada jikinsa itama tanasa kuka
Ya rumgumeta yana magana
Dan Allah kuyafe min kiyafemin fujjilat wlh bansan komi ba duk abindake faruwa yaxama tamkar tilasi baxan iya kwatanta miki yadda bakincikin xuciya ta ke dada karuwa ba, nacutar dake da mamanki dan Allah kuyafe min
Abba kadaina kuka munyafe ma kuma mami xata dawo gidan mu nayi maka alkawari
Yana murmushi yakalleta
Dan Allah fujjilat? Xaki dawo min da mamin ki?
Kwarai abba
Tohm shikenan daxanmiki gagarumar kyau ta niko
Allah Abba
Sosai ma
Sukayi dariya inna habi ma dariyar tayi sbda yadda suke tashirar su cike da kewa na dogon lokaci

Umma umma kina ina umma?
Tafada bedroom din umman agigice
Ya akayi ne kubrah?
Umma data futo atolet kenan tana tsane kanta da twil sabda wankesa tayi
Umma wlh yanxu da idanuna naga mamin fujjilat wlh tare da bahba da dahda wlh umma!
Haki take sosai tana ba umman labari sbda gudu tayi domin taxo takawowa umma labari sbda ta taba fada mata watarana cewa mamin fujjilat baxa ataba ganinta ba,
Toh menene nima abindake damuna kenan tun safe nake shekawa kaina ruwan sanyi duk sanyin nan da ake wlh banaji xafi kaina yadauka yanxu jinake tamkar anhuramin wuta ajikina sbda xafin kiyayyar dake tsakanina da jamila kuma boka yasanar min yagama min aiki sbda ankona masa aljani kinga babu wata mafuta saita xubawa sarautar Allah ido
Kubrah taxaro ido
Au yanxu umma kawai saimu xuba musu ido mamin tadawo tab wlh kinsan Abba dai yafi sonta kuma wlh xamu gane kurenmu
Rufe min baki wacce bata iya magana mai dadi ba inji uban wa!? Au har fatama kikemin inxa ma bora hamm
Aa umma
Wuce min dagani kuma kije kidauko mahmud da ummi amakaranta yanxu
Tohm
Tafuce tana danyin dariya kasa kasa ashe umma na tsoron mami kenan tasan in aka xauna haka baxataji dadi ba ga harta furgice daga jiya dataji labarin xuwa yau
Abba ne suka shigo hannunsa rike dana fujjilat
Umma batagama hargitsewa ba saidata kula da irin mugun kallon da abba ke jifanta dashi kanta kasa tana murxa yatsun hannunta har yawuce dakinsa fujjilat kuma jakar islamiyya tadauka tayimasa sallama tatafi gidansu danufin baxatadawo ba har saita dai daita tsakanin abbanta da mami anmai da auren kodan taga yadda umma xatayi,
Safara u daxuwa yanxu tagama tsinkewa da al amarin abba don haka Dayamma tashirya tasamu talallaba tabar gidan kaitsaye gidan hajia lami ta nufa sbda taga Abba take takensa zai wahala basakinta xaiba daga yanxu xuwa dare sbda yadda yake kullaci da ita ko magana mabaya amsa mata idan tamasa game da abba kuwa so yake kawai amaida aurensa da mami yasaki umma sbda tunda inna habi tafahimtar dashi itace tamasa asirin daya manta da rayuwar 'yar sa da matarsa har batan jamila yaji yatsaneta baya kuma kaunar tacigaba da xama dashi matsayin miji.

Haisam ne zaune kanmota yamarasa wanne irin mataki xaidauka akan fujjilat sbda abindata masa yanuna cewa baxata taba dawowa taso saba kuma bayajin kotagun manya xaikuma samun nasara akaro nabiyu ba donhaka dole yasan me yayi mata baxaitaba bari wani ya aure ta salin alin ba inaaaaa tab yabuga bot in motar yana direwa kasa
Car idaninsa suka fada na umma data turo get din tashigo
Kai kuga munafukar matar nan dataxama silar komai
Yatafi gunta gadan gadan
Koma koma kibar gidan nan ko wani munafuncin ne kika kuma kullowa
Umma da take kallon Haisam da mamaki tace
Haisam yau kuma nice munafukar? Kadubeni ina matsayin uwarka kace min munafuka
Ya isa damecece duk abindayake faruwa waye sila kinga malama wallahi kijuya kikoma indakika futo tunwuri konasa dan misra yamiki kacha kacha al kur an uwa kuma uwar dai watsatstsiyar 'yarki kubrah baniba
Dafe kirji tayi hawaye nasilalowa a idaninta
Nikake xagi Haisam kake cewa kubrah warsatstsiya bayan ga watsatstsiya can dakuke haukan so!
Bata kai maganar ba yasauke mata mari
Jikake kau shima haji a lami ta wanke masa kunchi har sau biyu
Fuce min da gani mara mutumci wanda kunya takare kannan ka mika hannu safara un kake xagi abin yakai harda daga hannu ka mareta
Haisam yadafe gun
Mama
Rufe min baki nace
kabar nan ko ban isaba Haisam?
Hajia lami takira sunan sa dakarfi
Motarsa yashiga kafin yatayar hajia lami tasan halinsa kwarai da xuciya dasauri tajawo hannun safara u donkar yataka mata kafa da mota
Get man dasauri yabude masa get din yafuta aguje
Safara u dake ta gursheken kuka tajuya tabar gidan hajia lami nakiranta amma bata saurareta ba tafuce tana kuka hanikan.

AIKI DA NAXARI DOMIN FARIN CIKIN MAKARANTA (READERS) NA SHAMSIYYA ADAM MATAR YAYA ❤️

Sannu yakakejin kan naka yanxu?
Yawwa ummi dasauki don bakamar jiya ba
Tasake kallonsa ganin yadda hawaye ke santari bisa fuskar sa yana magana dakyar bakinsa duk yabushe fuskarsa ta fada dan danan yaxama wani kala daban

Dan Allah Ubaidu kayi hakuri kasawa ranka salama akan yarinyar nan haba mekake so kamaida kankane kaiyanxu ban isa nasaka kayi ba nafadamaka basan sau nawa nasha fadamaka ba idan rabonka ce xaka aureta ko bakayarda da Allah ne kadai ke yadda yaso ba?
Muryarsa wacce dakyar take futa yamotsa
Nayarda ummi kukan kuma danake bayana nufin xanja da ikon Allah bane ina kukane sbda jikina yanabani fujjilat tawani ce idan kuma haka yatabbata ummi hawayena basu da ranar tsayawa
Tagirgixa kai
Aa aa Ubaid kaidai kacigaba da yin addu ah akan wannan lamarin nima xantayaka kuma insha Allahu xaka aure ta don nima nawa jikin nabani haka haba autan maxa karkasa ni nasare mana karkamanta kaikadai ne kwarin gwiwar umminka ,
Yayi murmushi tare da damke hannunta
Ina sonki ummi na
Nasani nasani autan maxa kuma xanxamar maka abin share kukanka xan gurfana gaban ubangiji naita reramaka addu ah kaji yawwa wartsake wartsake Ubaidu autan maxa
Yasaki dariya duk dabafuta take sosai ba
Fujjilat da shamsiyya ne sukayi sallama
Tafado gabansa tana kokarin sakin kuka ganin yadda yaxama xuru xuru

Ummy fuskar ta dauke da murmushi ta amsa
Au fujjilat kune
Wlh ummy naxo naduba yah ubaid ne tunda yaki fadamin baida lfy haidar ai shi yaje yafadamun har gida

Ayya ai dasauki ne jikin nasa shiyasa
Tana kokarin share kwallar dake kokarin xubowa tace
Amma Ummy dan Allah kuma baxa afadamin ba kodai yadaina kanwar danine bansani ba?
Ummi tai dariya tana mikewa tashige falo
Tambayesa gaki gashi nan ai

Shamsiyya suka gaisa tadubasa tafuta sayen kati a unguwar
Tunda suka shigo idaninsa nakanta duk maganar datake da ummi dayadda ta nuna damuwa akansa muraran hawayen dake kokarin kuma saukowa a idaninta yasa hannu yatare
Dan Allah karki karamin ciwo akan Wanda yake damuna dan Allah ki adanamin hawayenki kibari sai farinciki yaxo ki matse domin sa pls my baby
Hannunsa dake fuskarta har yanxu tajanye tana gyara xamnta takallesa sosai
Yaya baxanyi kuka ba yah Ubaid kaga kuwa yadda kaxama duk akaina wai menene yasa meyasa kuke sona dan Allah kafada min dan.......
Yalumshe idaninsa yana budewa
Bakaramin kyansa tagani ba kyawun fuskar Ubaid yana jan hankalinta

Dalilan dayawa fujjilat baduk dah namiji bane xaiganki baiji yana sonki ba
What! To akan me
Kinga cool down dama ciwon duk akanki ne kuma naganki shikenan nikam na warke dan Allah fujjilat ki aure ni
Tayaya yah Ubaid nima fatana kenan amma xai wahala faruwan hakan mami tadage min akan Nu'uman
Bakyaso nane
Inasonka amma yaxanyi da xabin iyayena ko kanaso nabijire musu ne?
Hawaye suka xuba a idaninsa
Bance ba bakuma nafatan naxama sanadi kibijire musu donhaka xankokarin mantawa dake kamar yadda kika iya tirsasawa kanki mantawa dani
Hawayensa hartakai hannu xatashare tatina ba muharramin bane tatsaya tare da mikewa
Wlh baxan barka ba xan iya kokarina don ganin na mallake ka matsayin miji
Tajuya dagudu tabar dakin
Shamsiyya dake falo axaune taja hannunta suka futa
Waike fujjilat maye haka ko gajiya da kukan ma ke bakyayi dan Allah kinga ni sakeni akan namiji kita kuka ina mai tabbatar dacewa sukan baxasu kasance haka ba
Fujjilat nagirgixa kai tace hamm mm
Dakinsani dabaki ceba shamsiyya ko yanxu Yah Ubaid kuka yake hani an kuma kekinsani a irin soyayyar da yake yimin har yakwanta rashin lafiya saiyanxu nafara tantance wani abu ashe shiyasa dah naji banajin komi akirji na face sabo lokacin danake tare da Haisam shamsiyya wlh akan ubaid naji can ji akan wanda nakeji dah. Nagane so nakeyi nakamu dasoyayyar yah Ubaid kenan?
Eh mm mana ni nace aa tawa tai xafi nangaba aisaiki fadan magana fujji indai akan ubaid ne kece dama baki gane ba amma tunsan da kina gidansu nafahimci kema kinasonsa.
Hmm toh yaya xanyi da mami na akan tafahimchi Ubaid shine xabina?
Ummm toh kibita ahankali tunda yanxu kinga lallabata ma muke tayarda takoma gidan abbanki karkuma kikawo maganar Ubaid abu ya dada lalacewa sakarki tadawo baya donhaka dole mu lallaba awuce inda ake yanxu daga baya saiki shigo da maganar Ubaid ko?
Fujjilat tajin jinawa shamsiyya da hannu
Yayi kawata kai yau kwakwalwar nan taki tamin amfani shiyasa kike cinye gasa dadama ta ilimi ko ta hikimar xance nima nakusa baki lambar yabo amma tukunna sai shirin dakika shirya yafada wuffff sai nabaki wannan
Ta jinjina mata hannu
Shamsiyya taja tsaki
Hmm inajinsu ne kema kuma kinkusa bin layinsu
Fujjilat tadaka mata duka
Kefa bakya yadda dayabo
Humm toh ai kambamawa ce idankuma akayi nasara akanka saikanajinka wata tsiya magana ce kowa xai iya tsarata kamar yadda nakeyi kema sokwanci ne yamiki yawa shiyasa bakyama Tina komai
Sukayi dariya
Amma wlh kin cuce ni nice sokuwar
Anfada
Takuma kai mata duka caraf tarike hannun
Hayyyyy nafagaji wannan ai saiki taran jini ajika daga rakiya saiyaxama fada
Fujjilat tayi dariya ganin mutuniyar xata bata rai dayake dama shamsiyya batason wasan duka kokadan.

Abubuwa dadama sunfaru acikin sati biyun nan game da Abba daikam dakyar bahba da dahda suka amince jamila xatakoma bayan ansake daura aure haka kuwa akayi yau aka maida aurensu bayan sallar mangaruba 'yan uwansu dake katsina su biyu ne suka maida ita dakinta wanda itama kanta tasha mamakin yadda abva yagyaramata dakin ankashe kudi sosai haka falonta wasu shegen royel akaxuba saidaukar idanu suke falon mine falo ma yasha sababbin kujeru gidan har fenti akasake dakin su fujjilat ansake musu gadaje ita da kubrah mai dadi abba yayo musu oder sunci sinyi nak sannan fujjilat tayi musu sallama tafuta jaleel abba yadauke daga cinyar mami ganin yayi bacci dan karamin godansu maidaure da net abba yakasai yakwanta sannan yadawo inda yabar mami axaune tana wasa da hannunta sbda bakaramin mamakin abin takeba wai yau itace da Alhaji adaki lafya kuma kalau tab yaushe rabo tun fujjilat na shekara uku
Jamila
Abba yakira sunanta
Kanta akasa ta amsa
Na am
Jamila idan naga kina kin kallona sainaga kamar har yanxu baki yafemin ba abindaya faru kuma agunki bai wuce ba
Tadago kai ahankli tanakallon mijin nata cike daso dakauna wasu xafafan hawayen kewa suka xuba daga idaninta

Allah yayafemana bakidaya amma ni komi ya wuce aguna
Nagode jamila nagode
Bakomi Alhaji
Yadan harareta
Tohm naji indai dagaske ne anyafemin anunamin
Dariya ma yaso bata sbda tasan meyake nufi tasunne kai atafin hannayenta
Alhaji kenan kana nan da halinka
Yana kokarin banbare hannunta dake rufe da fuskar ta yace
Aaff toh dama ai bahaushe yace inkadade bakaga mutum ba tambayi halinsa shi yana nan
Suka kyakkyace da dariya,

Umma dake labe tadafe gefen xuciyarta dake mata xafi tun daxu tana labe duk abinda suke tattauna wa tanaji saidataji shuru ankashe kwan dakin sannan tabar kofar tanufi daki tana tsaki da magan ganun xuci
Shegiya yaufa ansamu miji tsohuwar jaraba ta motsa humm xaku fadane wlh duk saina kuma maganinku
Dakin su kubrah taleka amma ba kubrah sai fujjilat tana bacci hankalinta kwance
Ina kubrah taje har shabiyu bata dawo ba subhanallahi kawai take maimaitawa kafin takoma dakinta dasauri ta rarimi waya tashiga kiran layin kubrah.


Chan kuwa hotel din mai xuma daki mai lamba shida kubrah ce kwance bisa kirjin Alhaji mamman yana shafata tamkar wata jaririyar mage tayi lamo sai tsotsar sweet take da Alhaji yasamata bayan yagama tsotsa shima
Idaninta alumshe takallesa
Waikuwa alhaji karrrrfe nawa ne ummm
Tabungiri tana sakin jikinta duka ajikinsa
Dariya alhj mamman yayi sbda burinsa yacika yau xaikwana da ita ahotel din nan yasan idan tana cikin hayyacinta ne datuni tatafi baxatakai ko karfe shadaya ba shiyasa yabata kwayar maye acikin lemo tasha tum bayan sallar isha I take abuge shikam saikwasar gara yake yadda yakeso,
Karfe biyar baby yanxu
Tayi dariya
Is ok is ok kace ma yanxin garin yawaye kenan Alhaji
Eh mana
Tayi
Mika tare da shafo fuskarsa dai dai bakinsa tasa nata tana tsotsar lebensa
Ganin yadda take sarrafa sa yabiye mata kiran wayartane yashigo amma suka share yayin dasuka cigaba da aikata masha ar su
Umma batayi bacci ba ranar sbda bakinciki kubrah bata kwana agida ba ga uban kishi daya dankare mata arai

Sai wajen karfe bakwai tafarka daga nannauyan baccin daya dauketa farka war dxatayi taga alhaji mamman kwance kusa da ita sai lokacin tafahimchi kwaya yabata tasha har takwana dashi a hotel abinda bata taba yi ba kin kwana agida tab ko tolet batakalla ba tararimi jakarta tai waje tana tararrabin yadda xasu kare da umma dakuma wacce irin karya xata shiryamasa gabdaxata futa suka ci karo da mubaruka tawatsa wa kubrah mummanan kallo
Kubrah wacce hankalin ta yay gida tashare ta tana karawa gaba xata tsallaka titi kenan sukai ido hudu da haisam xai wuce amotarsa yadan tsaya anbuga masa iska kuma ta tabbatr yaga futowarta daga cikin hotel din mai xuma wannan shine gani nabiyu dama yataba ganinta da Alhaji kaseem awani gidan hutawa yana rumgume da ita, dasauri tadauke kanta tana tarar me napep tahawa yaja Haisam yaja tsaki aransa yana cewa
Watsatstsiya kawai anfada uwarki na hankoron anmiki sharri yau abin yayi abu awaje ma takwana hmm ayidai mugani donko umma ga 'yar hannu cikakkiya adakinki kinsamu
Da wannan tunani yakai gida ransa tas domin dama haushin umma yakeji.

Umma ce tai hamdala data kula lokacin da kubrah tashigo gida bawanda yatashi abacci ma balle afuto tunda akayi sallar asuba kowa yakoma barci duk da yauma alhaji baifuta masallaci ba muneeb ne da mahmud suka futa sallar asubah fujjilat ma tanayin sallar yau ko karantu bata tsaya yiba takoma bacci sbda yadda idaninta ke ciwo alamun baccin bai ishe taba, kodata ga gadon kubrah bakowa bata xargi komi ba tadauka kawai adakin ummanta ta kwana tunda abba na wajen mami.
Umma data funciko kubrah ranta abace tajata dakinta takulle tashaketa alungu karshen tolet sbda karma aji kukanta ko aji fadan ta
Don kutmar ubanki gidan uwar wa kikaje kika kwana kifadamin gaskiya khadija ko nasa wuka nayanka ki nakuma yanka banxa
Jikinta rawa kawai yake
Umma dan Allah kiyi hakuri wlh ina gidan gwaggon ki
Umma ta shara ra mata wani mugun mari wanda sbda masifar xafinsa saida numfashin kubrah yatafi hutun gajeren lokaci kannan yadawo
Dan Allah umma d..............
Ya isa nixaki munafunta nixaki toxarta ki wulakanta ashe kinfara bin maxa bansani ba abin yakai harda kwana dole Haisam ya fadamin magana ga xahiri ashe ina nan ina haddin baloko kekuma kina can tsakiyar duniya kina kwaye min baya yaushe kikafara kula maxa? Nacee yaushe?
Jikinta duk yadauki maxari ganin muguwar dorinar dake hannu umma wacce taxama murdediya gata anannde tasha mai sai kyalle take da alama umma har gishiri tasa ajikinta sbda tashirya kashe ni yau wayyo ni kubrah yau kwana na yakare kuma, Allah kajikai na
Xabga mata daya umma tayi
Tagantsare xatasaki ihu umma ta toshe mata baki da tsumma tare dasa hannu abaki
Shiiiiiiiiiiiiiii!
Munafukar Allah ta ala wlh yau saikin bawa kawayenki labari dake xanji ko da mugun ubanku daya maidani shara agidan daga dawowar kilakin matarsa jiya jiya wlh saina huce haushina akanki kuma al kur anin Allah inkinsan ma kin kwaso ciki atsinannen yawonki kanki don wlh kauye xantattara ki nakai ki can ki karata hayakin ice dana kara ma ya isheki don wlh danaji kunya gwara narasaki duka shegiyar yarinya karama dake amma kinsan namiji
Tafara xuba mata bulalar hannun ta
Tun kubrah nakuka sama sama har tafara mance sunanta
Ajigace tarike bulalar tana shartar hawaye
Xanfada xanfada wlh umma xanfada miki gaskiya,

Xaifi miki sauki don idan baki gaji ba da dukan nima dake dukan naki baxangaji ba
jikin bangon tolet din tajingina wanda ke mamaye da tayels saidaukar ido yake

Wlh umma yau shekara biyu kenan kuma natara kudi dayawa ayanxu acount ina nabanki inada miloin biyar sannan inada gidaje uku ina da napeep uku naxub da ciki sau hudu kenan

Murmushi taga umma tayi tare da cillar da bulalar taruko hannun kubrah ta tasheta sannan tarike suka futo bedroom sbda yadda jikin kubrah yay tsami ko ina ciwo yake mata mamaki yahana kubrah iya magana sai bin umman take da kallo da mamakin yadda dandanan tasauko tafara tarairayarta tana goge mata xuffar data hada

Ke dagaske kin samu wadannan kudaden da kadarorin haka duk bansani ba garin yaya basai kimin bayani ba tun afarko kafin nakaidamiki wannan mugun dukan
Kubrah adarare tace

Umma ban taba tsammanin xaki saurare ni bane shi yasa amma wlh da gaske nake dik abindana fadamiki inada su
Umma tasaki dariya

Allahamdulillahi aihakan bakaramin axanci kikayiba donhaka nasamu kudi ahannu na yanxu xanxama babbar mace nafara futa kasashe kala kala na waje xanfara harkar shigo dakaya daga dubai xuwa nigeria xan samu makamin yakar wannan kilakin datayi kuskuren sake dawowa fadata
Da mamki kubrah ke kallon ummanta sannan tace

Umma xanturo miki miloin uku da rabi acount dinki anjima sannan takardun gida kuma xanmiko su hannunki saiki yadda yadace dasu ko

Yawwa 'yar albarka hakan yayi ai sbda dakar Alhaji yayi xargin ina nasamu kudi sai nace kawatace hajia indo tabani jari ko
Eh umma
Kai amma kinfitar dani kunya naji dadin haihuwarki gashi xaki min rana.
Kubrah tai murmushi

Umma taimaka min kikai ni toleit xandan gasa jikina
Dasauri umma takamata
Ai dole dole nataimaka miki sannu.

Musalin karfe goma da rabi Alhaji Adam yatara iyalin nasa apalon gidan natsakiya umma tayi mamakin ganin yadda mami taxama yadda ta murje taikyau bata taba tsammanin xata fada kyakkyawan hannu ba tab fujjilat kusa da kubrah can kujerar dake gab da kofar futa afalon Muneeb ne yana aikin danna waya tare da breakfast wanda mami tayi Alhaji na bacci,

Tohm allahamdulillahi da Allah yasake hadamu tare daku anan kuma ina farincikin sanar da wadanda basu saniba dawowar jamila bayan rashnta damukayi nawasu shekaru san.........

Umma takatse sa

Please Login or Register in order to submit comment