Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mamaki Ita soyayya ai bakarya bace dakike jinta nasan kisha jin labarin soyayya kala kala masu ban mamaki da al ajab amma kisani baxaki taba jin irin tamuba domin kuwa xanbaki mamaki xankuma tabbatar miki da duk yadda nakeji akirji na fujjilat meyasa meyasa kikeson karya min xuciya? meyasa kike son dawo da hannun agogo baya
Ok ok nagane wlh tallahi koda babu xuciyarki, tawa kadai xata dauki dikkan nauyin mu nafada miki wannan kije ki aje wannan maganar tawa akundin tarihinki koda xanxama gawa saina tabbata mijinki duniya ta shaida ba xankaraya ba fujjilat ba xankaraya ba nafadamiki,
Yajuya da sauri hawaye nasauko wa aidaninsa yafara tafiya domin futa agidan duka
Itama hawayen takeyi tausayinsa yagama illata mata xuciya yarufe mata kofofin iska ta ko ina
Dasauri tasha gabansa tana xubewa kasa
Karkafita a yanayin dakake ciki Haisam dan Allah kashare hawayenka,
Aa kibarni kawai domin kuwa inason duniya ma tashaida daga yau nima xankasance ayadda kikaxaba mana kullum kuma koda yaushe kunyar wa xanji hummm fujjilat kenan kokadan babu wasa acikin duk abin daya tabamin ke
Tamike tana kakalo murmushi
Tohm kayi hakuri insha Allahu nadaina taba maka kaina domin kuwa nice silar
Yayi murmushi
Aa bake bace ke ai nasan bakya komi sai da dalili mikarfi gayamin me yafaru dama shuru nake miki kwana biyu duk kinfa rame sosai inason intambayeki amma saiki basar daxarar nafara maganar
Hum bakomi kawai ramar aure nake
Dariya suduka suka kyakyace da ita kaikace ba yanxu suka gama kuka ba
Umma dake sama tana kallonsu ta window tayi kwafa tare da sakin wani murmushi maidauke da ma anoni daban daban
Kikasance tare dani acikin xuciyar ki koda yaushe fujjilat xakirinka jina tamkar gani akusa dake tagefen dama, ni haka nake yi shiyasa kullum xakiganni acikin farinciki hannun damata daf da kafadata sbda ina mai tabbacin kece kusa dani baxan wasa da damarki ba xan xama mai dafa kafadonki koda amafarkine,
Ta lumshe ido
Hummm iya kalamanka sin isa su ishekeni atsaye haisam lallai girman soyayya yafi yadda na kirgashi daga yanxu xanyi wani kokari tunda tattali da lallashi ne banruwanta xan yunkura domin natabbata dana fi mafi yawan manoma samun amfanin bana kai har dana kowacce shekara kaidai Allah ya albarkace mu
Amiiiiin amin kinsani aduhu fa maganarki tafi kama da munshiga nikadai nasan kofar futa
Tai dariya
Hhh ai xanfuto dakai haske a aikace
Allah ko
Ta daga kai
Kwarai kuwa
Toh ai shikenan bari naxo nakoma ni
Ahh haba tun yanxu bakama shiga ciki kungaisa da umma ba
Eh ai xandawo da dare shiyasa
TOHM shikenan
Ya hura mata love kiss 💋 da hannu
Hannu bibbiyu tasa ta amshe tare da yimasa byebye,
Sanye yake acikin wani blu in shadda gixina saidaukar ido take da walwali wayane akunnensa yana amsa kira tare da gyara sa hularsa
Inajinka ishaq bakomi nasan xaka kula da komi koda bana nan kacigabada da kulawa dan Allah
Kubrah dake fitowa daga part in umma takaraso wurinsa tare datsayawa domin jiransa yakarasa wayar bayan yagama yakalleta
Kubrah ya akayine naga kinxo kintsaya da alaman kinason yin magana danine ko?
Tasaki murmushi ganin tasamu fuska lallai wannan ce damarta
Tamatsa kusa dashi tana dan sin sinke kai
Dama dama yaya muneeb magana nikeso miyi dakai idan ba matsala
Yana duba agogon dake manne ahannunsa yace
Ok badamuwa inajinki
Takara kasa dakai tana wasa da yatson hannunta cike da nuna kunya tafara magana
Yah muneeb dan Allah karkayiwa maganata wani kallo daban kadauketa gaskiya kakuma alkinta ni
Yayi murmushi
Ok
Dama sonake yi nafadama ka yadda nikeji akanka yah muneeb inasonka wlh tun ina yarinya nakesonka tunkafin kafita waje karatu ban.............
Yadaga mata hannu
Ke kanwata ce banayi miki wani daban sama dana matsayin kanwata donhaka karki kawo wani magana tsakanin mu inada wadda nakeso kuma ina jiran lokacin daxan mata maganane dan Allah kiyi hakuri kinji
Yana kare maganar yagyara hular sa yafuce aikuwa kubrah Kara tasaki hade dakuka tana kiran umma
Ke da Allah wai maye zaki ishe ni dakira kibarni mada abindayake damuna wlh yarinyar nan saina dagula mata lissafi sannan xanhuta kuma wannan auren sai anfasa koda ta tsiya tsiya ne shegu dangin mayu kekuma bakida aiki sai raki bakya ma duba halin da wannan 'yar iskar ke kokarin sani saifaman kashe kudi nake inakaiwa malamai da bokaye amma taki mutuwa ai wlh bata isa tashiga ahalinmu ba yaudin nan xankoma wurin boka insunsan wata aibasu san wataba
Kubrah tafada jikin umman tanasakin wani sabon kukan
Umma yah muneeb yace baya sona umma wlh idan bai aureni ba mutuwa xanyi
Wata uwar ashariya umma tasaki tana fada
Shidin banxa shidin wofe wadanda suka fisa taurin kaima anjuyasu kinga kikwantar da hankalinki indai muneeb ne tamkar kunyi aure kuma dukiyar sa saimunchi saikin wadaka agidansa da arxiki wannan tilin dukiyar da ubansa yabar masa ubanme xai da ita dole saimin fadaciki minyi faca faca da komi donhaka kiyi shiru ai iya hawayen dayasa kika xubar wlh ni sufira u nai alkawarin seiya biya diyyarsu damakudan kudi.
Murmushi kubrah tayi tana cewa
Allah umma na koda yake ainasan ki xaki iya
Humm yadda nake sonki baxan juri ganin kukanki ba duk kuma abinkike muradi xan tsaya miki kai da fata deejata
Suka kyalkyale da dariya.

,😥😥'YAR HANNU😥😥 2021
SHAMSIYYA ADAM MATAR YAYA ❤️

Wasa take masa shikuwa sai bangala dariya yake tare darirriketa sabda yadda take cillasa sama mami kuwa nagefe tanakallonsu sai fara ah take
Nu'uman ne yashigo dai dai lokacin da jaleel yakusa subucewa daga hannun muhsana taisauri ta cabesa tana rumgumesa
Ransa abace yakarasa inda suke yana fada
Bana hanaki yiwa yaron nan irin wannan wasan ba? Kebakyajin magana ko toh wallahi duk lokacin dakikasake yasubuce yafadi yaji ciwo saikin raina kanki ya amshesa itakuma tana xumbura baki tatashi tabar falon maman jaleel yagaisar tadaga masa hannu cike da fara ah dakin mama yanufa da jaleel akafadarsa,
Assalam mama yagida?
Xaune take bisa sallaya tana wuridi shafawa tayi sannan tadubesa
Allahamdulillah Nu'uman ya office din
Mungode Allah
Takallesa
Yaron nan yanxu fa yafara ganeka kaduba fa yadda yake wani daddafemaka haka jiya kana ajesa yasaka kuka alhaji ma ya sha dariya sabonka da jaleel kam yayi nisa yanxu wannan idan akasamu inda mamansa take aka kaimusu ita yaxakayi
Yayi murmushi yana sakar ma jaleel kiss alips
Mama aibaxan iya rabuwa da kanina ba sainacewa mamansa tabarmin
Kai lallai bakada hankli tayaya xata iyabar maka danta
Shikenan saina bisu inda take nima natare acan niko mama wai menene yake damuna yaya aliyu ne kinga mafa jiya kamar abige yadawo gida kuma karshe shabiyu na dare
Mama tarike haba
Toh niyanxu yayaxanyi yaxanyi da aliyu tunda dai wannan rayuwar yaxabarma kansa yanxu kaga bama xargi ake ba antabbatar min yafara shaye shaye kaga mafa yadda yafara sawar wari da maganar aurensa da luba da abvanku yamasa magana ca yay akara sheka ra
Mama ki kwantar da hankalinki nibanason hankalinki yatashi mucigaba da addu ah insha Allahu xaidaina aida bahaka yakeba abokanan banxa ne sike son batashi kuma dama inayawan yimasa magana akan su amma yaki ji saiya dau maganar yawatsar ashara amma yanxu kam xantsaya naga nayi iya yina don ganin yadawo kamar da
Allah yayi maka albarka Nu'uman ina alfahari dakasance warka dah na
Nagode mama samun uwa kamar ki yanxu ai nemane amma Allah yadauka yabani lallai Allah shine abin godiya
Ta mika hannu xatadauki jaleel yamake kafada yana kara rirrike Nu'uman gam
Suka sheke da dariya tana lakuce masa hanci
Kaji dashi yaro nanfa muke yini dakai amma daya dawo munkoma baya ko ai shikenan
Nu'uman yamike dashi yana dariya
Bari muje shopping naga kayansa sunyi kasa mama kinada wani sautin ne
Eh to rigunan sanyi ne dama na muhsana duk sunmata kadan tabayar saika sawo mata wasu nikuma hijabi xaka sawon fari na idi tunda kaga axuminma gaba daya watan gobe ne
Eh anyi haka shikenan bari tohm nadauki muhsana muje tare muntafi
Tamasa adawo lafiya yafice.
Muhsana xaune maman jaleel kan kujera tana matsa mata kafa yashigo dakin kusa da maman jaleel din yaxauna yanadaga mata hannu cikin girmamawa
Tayi murmushi tare da hada hannayenta aranta tace
Wannan yaron dan albarka ne Allah yayimaka albarka
Musahna tashi kisa hijabinki muje botq xansaya ma jaleel kaya kema daganan kinxabo st in naki
Dasauri ta mike tana cewa
Laa yah Nu'uman yayi wlh bari nafadama maman jaleel
Tafara kwatanta mata da hannu harta gane
Jaleel ne yafara kuka yana mikawa mamansa hannu itakuwa sabda tana jin nauyin Nu'uman taki ko kallonsa
Kinga mikama mamashi ina falo kufito har maman muje itama koxataga abindatake so acan din
Shikenan yaya musahna tace tana amsar jaleel dake ta banbankarewa ahannunsa ta dorawa mama shi acinya ganin taki miko hannu ta amshesa
jaleel naganin sa hannun mamansa yasa dariya yana wangale wawulonsa dabakomi adasashin sai tudu,

Littafin Shamsiyya Adam yumnah
Karku manta munan dai cikin wannan littafi maisuna ''YAR HANNU

Fujjilat ne sanye da doguwan riga na shadda pik colu taja daurin dankwali maikyau fuskarta kam ta amshi wannan kalar shadda ga mayafinta blu black takalminta ma haka hakanan takejin dadin gayyatar tata da Haisam yayi yau xuwa shopp in wasu kayan daga cikin lefenta taji dadi sbda tana son lifaya kuma tafison tadauki wacce takeso dakanta lallai tafara jin wani abu akan Haisam yana mata so wanda kokadan bata kokwanto akanshi
Wayanta ne yayi kara tana dubawa taga yah Muneeb
Dankaramin tsaki taja kafin tashare kiran taci gaba da fesa turarenta tana kallon kanta acikin faffadan mudubin dake manne da bango
Saidata gama kimtsawa sannan tafuto akofar dakin sukayi kacibus da Muneeb yaxo dubawa yaga lfy taki daga wayarsa yanacikin wani hali agurinta ne kadai xai iyasamun amsar tambayarsa baiyadda cewa ankusa aurenta da Haisam ba idan hakane miyasa da bai saniba yana gidan sai abakin wasu awaje
Sin sinke kai tafarayi sbda tasan laifinta
Yaya barka da yamma
Yakara daure fuska
Nayinin ai shiyasa kikaganni miyasa nakira ki bakidaga min wayaba fujji?
Tana kame kame dakyar tacafko kalmar daxata iya amfani da ita wajen kare kanta
Ina wanka ne
Yaharareta
Inaxaki tohm naga kinyi shirin fita
Xamuje shopp da Haisam ne
Gabansa yafadi kardai gaske ne yarinyar nan abadata afili kwa ca yay
Yaushe kika xama haka bansa niba dawakikayi xaki bi Haisam siyayya? Baxaki ja mutumci kiba kefa 'ya macace donme xakibi wani kato daba kowan kowanki ba kufita yawo look kinajina fujji yakamata kifadamin idan akwai wani abu yanxu atsakaninki da Haisam intayaki murna don a iya sanina bakison shi dakanki kike fadar wannan
Muryar ta can kasa tafara magana
Yah Muneeb hala Abba baifada maka ba ai yanxu saura wata biyu bikinmu da Haisam
Tamkar wanda aka dokama guduma haka yasandare yakai wurin minti shabiyar kafin yadawo daidai saidube dube yake amma babu fujjilat hannunsa yasa yadaki bango tare dasakin wani xaxxafan ajiyan xuciya yanxu yanaji yanagani abin dayaso tuntana xanin goyo xata kufce masa lallai dasake yau din nan basai gobe ba xai sami abba damaganar saidai awar ware maganar Haisam akulla dashi domin kuwa yasan fujjilat bason Haisam takeba shi takeso kawai tanada kunya ne take boyewa. Ransa abace yabar falon yanufi masallaci domin acan xai sallah xuwa isha i sutaho tare da Abba tare.

Maman jaleel da muhsana tare da Nu'uman dake sabe da jaleel akafadarsa wani babban shagon saidakaya ne suka shigo babba yakunshi nau in nau in kalolin sitturu kamadaga namu nan kasa nigeria dakuma nakasashen waje irin su india, chaina, phakistan, e. t. c. Tsayawa lissafa muku yadda wurin yakai da haduwa abin badan kadan bane muhsana ce ta daga kanta saman tsaunin gurin indayake futar dawani haske anrubuta WELCOME TO XAHRA SAGEER BEUTY BOTEC
Hasken yakashe mata ido amma sunan yamata dadi takalli Nu'uman
Yah gaskiya wurin nan yahadu fa sosai
Yayi murmushi
Kefa 'yar kauye ce dadina dake karfa mushiga ciki kirude kumaduka kikasa daukar komi
Taidariya harda dan dafa maman jaleel dake ta kalle kallenta sosai ita ma gurin ya burgeta Yakuma dau hankalin ta lallai wannan ko wacece tasamu gata kuma tana jindadin rayuwar ta
Mama da muhsana suka nufi wurin kayan mata suna dubbawa yayin da Nu'uman ke dauke da jaleel akafadar sa yana tura wani babban keken dakwando ke jikinsa yana jidarwa jaleel kana nan kaya masukyau datsada
Dai dai lokacin da Nu'uman ya xagayo wurin hulina sukayi karo da ita
Wash
Yace sannu
Tadago
Yawwa
Xai dauke mata abindata yar taisauri tadauka tana kokarin tafiya yace
Dan Allah baiwar Allah kiyi hakuri bansani ba nabigeki
Tana dan taba goshin nata tace
Aa bakomi
Xata juya saikuma takalli jaleel kamar kuwa yaron jira yake takallesa yafara mika mata hannu yana dariya
Dandanan taji yaron yashiga ranta takai hannu tadaukesa tana cewa
Hey boy menene sunan sa
Jaleel
Nu'uman yafada yana kallonta yadda take komi cikin nutsuwa da hankali tanadakyau ga ta baxatayi girman kaiba so cool yarinyar mai yanayin sanyin rai da magana yaji wani abu yadan taba xuciyar sa akanta kuma itace sak irin mace dayake tajira tafado rayuwar sa Allah yasa baxata kasance masa yarasa taba
Sunan ki
Fujjilat
Yasaki murmushi
Nikuma Nu'uman shafi U
Yayi kyau ga yaron naka mekyau
tamika masa yaron tana kokarin juyawa
Dasauri yasha gabanta yana son kuma kallonta kwata kwata bata da isar gani da ji
Tun yanxu kuma dakin taimaka min da rakiya mana kitayani duba kayan
Kallon barin da Haisam yashiga daxu tayi sabda tasan halin kishi irin nasa yanxu xai iya tawa dakowa hankali baruwansa daxaran yaganta da shi
Aa ina sauri domin munatare da maigidana
Wani abu Nu'uman yaji badadi badai matar aure bace tab kai bama matar aure bace wannan
Shikenan nagode amma dan Allah.................
Amma me?
yaji anfada daga bayan sa
Duka suka juya suna kallon Haisam daya taho tabayan fujjilat hannayensa duka xube cikin alhunan rigarsa
Daf dayakaraso yatsaya gaban Nu'uman yana masa wani kai kaitaccen kallo
Haba malm tace maka tana tare da mijinta toh namaye kuma saika sake titsiyeta da tambayoyi kaga dan Allah kakula wannan matatace kuma inafatan kagane ko akiyaye
Murmushin daya xama jiki wa Nu'uman shiya yi tare da cewa
Wannan maganar dakayi kadai ta isa ta tabbatar dacewa ita din ba matar ka bace donhaka karka xake kadan daga ikon Allah yanuna maka iyakarka akanta akaramin lokaci yatabbatar maka dani amijinta domin kuwa naga iri inakuma so kaga inkanwar kace kayi min hanya
Ran Haisam abace yayo kan Nu'uman afasace abindaka damai xuciya ma aikatan gurin sukayo kansu tare da shiga tsakaninsu wasu suka rike Haisam shiko dama Nu'uman baiko motsa daga inda yake ba yajuya yana sakarwa fujjilat murmushi wanda tajisa har tsakar tafin kafarta komiyasa oho
Jin hayaniya yasa muhsana da maman jaleel suka yo kwanar taku biyu yarage Mama takaryo nu'uman yabillo rike da jaleel
Ayanayin tsoro muhsana tafara magana
Yaya hayaniya muke ji kamar dakai kuma lfy
Lfy klau muje kawai bani bane
Yarike hannun maman suka juya tare da cigaba da saye sayensu musalin karfe takwas sungama sunfita
Game da fujjilat kuwa lokacin da Nu'uman yajuya binsa tayi da kallo tana kallon lokacin daya rike wata mata yana magana dawata matashiyar budurwa baxatafita ba amma matar tajuya baya bakidaya tarasa maye damuwar ta dashi tanajin kamar tabisa tanason yaron hannun sa lallai wannan akwai wani abu na sirri tattare dashi
Funcikar hannun ta Haisam yayi suka bar gurin sbda bakinciki ba abin daya bari suka saya haka yacillata mota yaja da mogun gudu Allah ne kadai yakare su badan haka ba irin mugun gudun daya rinka makawa dasu yafice tunani kuka tasaki sosai tana rokonsa ya tsaya yadaina wannan gudun amma inaa aikamar tana kara kunnasa jikinsa tafada tana rokonsa amma ya tureta gefe daga karshe sumewa tayi sbda ba abinda fujjilat tafi tsoro aduniyar ta irin gudu amota ko Ahankali ma ake tafiya ita bata yarda da motaba saitaga kamar xa akife,
Sam baisan data sume ba dai dai kofar get din gidan Abba ya ja wani mugun birki keeeeeet kakeji yatsaya tare da kifar dakansa asikiyarin motar
Sama da minti taalatin bai motsaba balle yasan halin da take ciki
Abba ne da Muneeb sundawo daga masallaci kowanne da charbi ahanninsa Muneeb yafara magana
Abba dama inaso nayi wata magana dakai saidai kuma inaganin kamar baidace ba natare ka da ita haka kai tsaye
Aa karka damu Muneeb kaidin fa tamkar dancikina nadaukeka karkaji komi daxaran wani abu yanadamunka kasameni kafadamin xan iya kokarina don ganin kafita ahalin kaji
Shikenan Abba dama fujjilat nakeso kuma naji labari acikin gida cewa kabada ita har bikin yakarato Abba wlh nafi duk wanda xai auri fujji sonta Abba tun tana xanen raino nike sonta kuma harkawo yanxu dan Allah ab........
Yadaga masa hannu
Muneeb
Dasauri yakalli Abba kamar xaikuka
Fujjilat ba tsaranka bace baxantaba baka aurenta ba koda banbadataba sbda kai kintsasttsene kuma amana awurina donhaka banaso nakarajin wannan maganar abaknka kaji ko idan auren katashi yi ga kubrah nan intayima inbatama ba kanemo yarinya ko 'yar waye xan nemo maka auren ta
Abba
Muneeb yabude baki xai magana
Abba yadaga masa hannu
Kayi shuru dabakinka domin kuwa nariga dana yanke hukunci kuma dole kabi inkanason kwanciyar hankali na danaka
Yakara gaba yabar Muneeb xuciyar sa achakude yarasa wannan yarinyar menene tayiwa Abba tsanar tayi yawa shifa yanasonta komin bakin halinta kuma shida Haisam saidai su xuba donkwa baxai taba bari ya aure taba

Shurun yaji nata yayi yawa yafara jijjiga ta amma shuru afirgice ya cacumota jikinsa yana kiran sunanta amma shuru kakeji dasauri yaballe murfin motar yafito tare da kokarin sakai cikin gidan Muneeb da Abba suka karaso Muneeb naganin halin datake ciki ya sureta kafin Haisam yadawo daga ciki dauko ruwa kaitsaye falo sukayi kacibos da Haisam wani mugun kallo yabisa dashi yayinda Muneeb kotakansa bai biba yakwantar da ita akan doguwar kujera ya nufi furij yadauko gorar ruwa yafara shafa mata afuska Ahankali yana hura mata iska akunne ran Haisam in yakai dubu yabaci cilli yayi da gorar ruwan daya dauko yana barin falon afasace yaxama dole yatakamata birki kuma lallai yafara xarginta da kula maxa kowanne namiji kokarinsa yataba jikinta ga yadda wannan garan yadaukota tamkar wata matarsa saubiyu kenan xandau mataki saina nunamasa kurensa shima saiyasan yana tabamin mata,
Abba ma bai bi takanta ba ya wuce dakinsa kubrah da umma kuwa dama suna ciki part din umma basu san wainar da ake toyawa ba
Ahankali tafara sauke ajiyar xuciya tare da kankame hannun Muneeb dake rike danata yanamata sannu dasauri tatashi tana kiran
Haisam kadaina gudu dan Allah xan............
Idaninta suka sauka afuskar Muneeb dake xaune saman kanta yana rike da hannunta idaninsa cike da kwallah yana tausayawa rayuwarta bakidaya babu kwanciyar hankali aciki
Sannu fujji kinji menene yafaru kika suma
Kuka ne yakwace mata yayin data janye hannunta daga cikin nasa tana kokarin mikewa
Magana nake miki yanxu haka kike so ki auresa kixo ki ta kuka Haisam yafiye xuciya da hasala baya sauraron kowa saikansa yaya kike tsammanin xaigwada miki adalci kinga xuciyata bata dakwari fujji idan har mutanen dake cikin duniyar nan baxa sudaina saki kuka ba nima xandauwwa ina kuka ina tausayin yadda kike fuskantar rayuwa inakuma tir da masu cusguna miki xan fansar dakomi domin farincikinki amma baxan iya shuru yayin danake ganin hawayenki ba banso abin yaci karfina harkikasani ba amma dole namike nakwatar miki 'yancinki kidaina kuka fujji I'm wth u.
Aa aa yah Muneeb ai babu wani sauran abu daya rage auren Haisam kam shine mafutata karike komi daxakamin koka nunamin duk yadda nake da tabbaina ahaka yakeso na yamin abinda bantaba tsamman xansamu daga wani ba
Tafuta tana kuka
Kinaga tsaya
Cak tatsaya tana sharar hawaye
Idan manufar kike so kiji abude shine ina sonki kuma baxaki auri Haisam ba mutkar ina raye nine nake miki so tunkina yarinya donhka kije ki naxari Haisam baxai miki yadda nake so ba donhaka baxan sakar masa ba.
Wani suman takusa yi agun kafin ta juyo yabar falon duka ranar batai bacci ba saiwajen sha biyun dare.

Takunce dai Shamsiyya Adam MATAR YAYA ❤️ nasan masu karatu sunan xuciyoyinsu cike da tambayar shin wacece ''YAR HANNU tohm amsar ku takusa xuwa xaku fahimta asannu kudai muje xuwa cikin labarin.

Umma naji shuru fa har yanxu yah Muneeb baisaurarona
Wani shegen kallo umma tajefi kubrah dashi tare da neman guri taxauna
Kinga nifa bana kaunar gajen hakuri arayuwata shin kinganni axaune ne? Ko kinga gwiwa na tayi sanyi toh bari kiji ni yanxu babban abindake gabana shine naga natarwatsa wannan maganar auren ta Haisam da fujjilat idan naga komi ya kammala saikuma mufara takan Muneeb kekinsan baxantaba bari wannan dukiyar ta subuce mana ba
Kubrah tayi dariya
Hakane fa umma bakidaya nima naji hakuri na yafara karewa ne akansa shiyasa kikaji kamar na xaku
Humm banaso kimatsa ko ki tirsasa akansa yanxu kibarsa dakansa xaikawo kansa gunki nan badadewa ba
Wayar kubrah yashiga kuka kallon umma tayi tana katse wayar
Wayake kiranki naga kindatse kiran?
Tana kame kame tamike
Aa ummy ce wlh bari naje sai anjima
Tafita tana mai hararar wayar kamar itace taimata laifi
Kiran numban data kiratan takashe tayi
Hello kaga gaskiya Alhaji mamman wannan ba yi bane ainasha fadamaka cewa karka rinka kirana harsai kaga plash ina amma bakaji ba gashi nan kakusa sa umma tagane
Bayan daga bangaren Alhaji mamman yayi magana ta numfasa
Humm saina huce tukunna xuwa jibi xamu hadu
Takatse wayar tana jantsaki
Game Muneeb kuwa dik yadda yadauki abin ashe yafi haka domin kuwa yau sati biyu kenan baya ganin fujjilat koda afalo yakira wayanta kuma akashe
Itakam tunranar da abin yafaru tahada kayan ta tagudu gidan baba harkawo sati biyun nan Haisam baine metaba abinya dameta donhaka yau tashirya xata gidansu tadubasa taga ko lfy yake
Hajia lami na falo tana kallon tashare arewa 24,tayi sallama tashigo
Kafin tagaidata tamike tare da daga mata hannu
Haisam ko shikikaxo nema sbda bakida kunya ko? Tsawon sati biyu kenan anemeki anrasa kinacan yawon dandin dakikasaba anafada amma bama yarda sai yanxu nagama fahimta toh kisani aure fa tsakanin ki da Haisam babu kuma wlh narabaki da dahna karki sake nakarajin wani abu yahadaki dashi futa kibar min gida
Kuka yakubcema fujjilat
Wlh mama ba inda nije inagidan bahba dan Allah kiyi hakuri karki rabani dashi
Hajia lami tamkar tashake fujjilat tamutu takeji sbda bayadda xa aitayadda da ita bayan ga xahiri yau sati biyu kenan bata gida
Kinga kifita kibarmin gida wlh konasa awulakanta ki kuma kayan aure tun shekaran jiya aka amso mana kayanmu
Turata tayi tarufe kofar falon ganin taki futa sai gursheken kuka take
Dagudu tafara fita agidan bakin get suka hado da Haisam yadawo motar sa yake kokarin yashigo da ita
Dan Allah kafadamin menayi menayi ne wa mutane kowa bakina yake gani babu wanda naimishi dai dai abinda mama take fada shin yafaru
Afasace yayo kanta tamkar xaidaketa
Gaske gaske wai tambaya kikeyi ko dagaske ne yafaru toh bari ki ji yafaru kuma aure nafasa baxan aure ki ba banxa karuwa ''YAR HANNU wulakancciya wlh nayi nadamar yin soyayya dake kuma wlh mutkar baki futa asabgana ba saina tattakaki banxa kawai
Kanta ne yafara juyawa tafara gani uku uku hudu hudu kafin tace
Me kace nikake muxantawa haka Haisam hai...........
Taga yashige da motarsa cikin gidan yabarta bayadda ta iya face tajuya ta koma gida
Kafin ta tsallaka titi tafadi yiiiiiif sbda bakinciki da bacin rai lallai kafarta baxata taba iyadaukarta ba,
Har yawuce yadawo dabaya tare da tsayan da motan yaklli abokinsa
Kamar macace ce ma fa haidar
Haidar dake bangaren mai xaman banxa yace
Subhanallahi gadai gwanin tausayi kowa sai wuce ta yake duniyar nan yanxu taimako yayi karanchi
Ubaid ya yi saurin sauka dagakwalta yakashe motar kai tsaye inda fujjilat take ayashe yamatsa tare dayin bismilla yaciccibeta gidan baya yakwantar da ita sannan yakoma yaja motar kaitsaye hospital in da babban aminin sa yake aiki ya nufa da ita kafin yakarasa yakira sa awaya tare dasanar masa gasunan dauke da psion

Subhanallahi inna inna
Usman dayafado gidan dagudu kenan yana nishi
Inna habi takallesa
Kai da Allah can dabaka sama kanka nutsuwa ji yadda kafado min gida agigice kana kiran sunana menene yafaru? nasan dai bakalau ba

Please Login or Register in order to submit comment