Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da son's of God su ma, why? How's that??? Ashe kenan ba Jesus kadai ne son of God din ba ma," Kallonsa take ko kiftawa babu, ya tabe baki yace "Ci gaba" Sauke idonta tayi a hankali tace "Am going home" daga haka ta fara kokarin mikewa yace "Baki isa ba you are not leaving here until u finish ur forged story" wani kallo tayi masa sai kuma ta fashe da kuka tace "It's not forged" tabe baki yayi yace "Then ki ci gaba since you didn't defend my question" ta goge hawayen idonta a hankali tace "Three wise men ne suka yi announcing haihuwar Jesus the Messiah..... Snn comet from the sky ne yayi leading dinsu har manger inda aka haifi Christ....." Dakatar da ita yyi yace "Yeah yeah... jump all this...." Cikin sanyin murya tace "Allah ya ba ma Christ baiwa da dama yana kuma da disciples 12 wato mabiya har sha biyu, first miracle din da jesus yayi on earth shine na tada matattace, Lazarus ya mutu yan uwansa na ta koke koke Jesus ya je tomb dinsa ya tado sa ya fara rayuwa kuma, ya warkar da mutane dayawa don ya kasance mutum me tausayi, akwai wani biki da suka je da mahaifiyarsa Mary, wine ya kare gun bikin, nan Mary ta nemosa tana tambayarsa ya xa ayi, nan yasa aka ciccika masa ruwa a pots ya maida su wine gaba daya, shine kadai mutum da ya taba tafiya a kan ruwa da kafafuwansa, ya taba ciyar da dubban mutane da bread guda biyar da kifi biyar yayi miracle suka cika baskets fiye da dari.... John the Baptist shi yyi baptizing Jesus....." Jin ana kiran sllh la'asar ya dakatar da ita yace "Alryt xan je sllh idan na dawo sae ki karasa, nima kuma sai in baki nawa tarihin islamically then you compare and contrast" a hankali tace "Ohk...." Rufe sauran abincin da ya rage yayi, tace "Ka koshi?" Bai tanka ta ba bai kuma kalleta ba, bayan yan mintuna ta mike xata wuce ya mayar da ita ya zaunar, hade rai tayi tace "Wucewa xan yi" bai ce komai ba kuma bai saketa ba, bayan wasu minutes din ya saketa yana kallonta yace "Idan ana kiran sllh ba a magana" buda ido tayi tace "da gaske?" Mikewa yayi yace "Yesss" mikewa tayi ita ma yace "Baxa ki jira in dawo ba kuma?" Hade rai tayi tace "Kai xaka sllh, ni kuma baxan je church ba, me yasa kai ma baka fasa xuwa sllhn ba" kallonta kawai yake, can ya juya yayi ficewarsa, kamar xata yi kuka ta bi sa da kallo, samun kanta tayi da kasa fita, a hankali ta koma ta xauna. Sosai yayi mamakin ganinta da ya dawo daga masallaci amma bai nuna ba, ya xauna kusa da ita yace "Oya karasa in fara nawa!" Ta sauke idonta ta ci gaba da basa tarihin, tun daga kalubalen da jesus ya fara samu gun nonbelievers, da encounter dinsa da paul the apostle, da yanda paul ya dawo Christianity, irin sharrin da nonbelievers suka yi masa, da last dinner dinsa da disciples dinsa, da yanda soldiers suka xo suka yi arresting dinsa, aka saka masa crown din k'aya a kai, aka ja sa tare da cross dinsa xuwa Golgotha ana cin xarafinsa, da yanda aka saka shi tsakanin barayi biyu, yanda aka daura sa cross din aka buga masa kutsoshi a hannu kallonta Abuturrab yake da mamaki ganin hawaye idonta, ya danne dariyarsa yana kallonta da tausayin rashin sani wanda aka ce ya fi dare duhu, cikin sanyin murya tace "Jesus Wept!!! And his last words where; Ohh father, forgive them because they don't know what they are doing!" and that was how jesus Christ died for our sins, he was crucified on the cross in Calvary, he was slain" ta karashe tana goge hawayen idonta, yana mata wani kallo yace "Ohh da gaske ya mutu ashe? Kuma sbda xunuban mu? he died on the cross for all our sins?" Ta kallesa tace "Yess! But he rose up after 3 dayz and his father took him to heaven...." Da mamaki yace "But.... But Why then do we still have to go to hell and pay for them again, don me wasun mu xa su je wuta bayan sbda xunuban mu ya mutu? Wato sau biyu kenan xa ayi judge dinmu.... Toh sacrifice din da jesus yayi sbda xunuban mu bai isa ba knn har sae an sake mana hukunci? Ina ce don xunuban mu ya yarda ya mutu, to in haka ne kenan he did not die for our sins tunda har hukunci pa na jiranmu ranan gobe kiyama, idan kuma ba haka ba ki fahimtar da ni yanda xan gane, kuma ni dai nasan it wasn't Jesus Pbuh that was Crucified or slain.... Another error from your Bible" yana kai wa nan ya wani hade rai wanda hakan yasa ta kasa cewa komai tana kallonsa ko kiftawa bbu, ya wara ido yace "Kinyi shiru?" Ta dauke kanta, ya kamo hannunta yace "Ki ganar da ni mana Samha" ta xame hannunta a hankali tace "I don't know too, all my Bible told me was that he died on the cross and rose from his tomb after 3 dayz and was taken to heaven bayan wannan ban san komai ba" innocently tayi maganan, murmushi yayi yace "Toh shknn, are you ready in fara baki nawa tarihin?" Bata ce komai ba ta sauke idonta kasa, ya lumshe ido yace "Alryt, His mother is Maryam Bint Imran, the daughter of Hannah......" Shiru yayi yana kallonta, ta d'ago a hankali jin shirun, murya can kasa tace "Ci gaba" yayi murmushi yace "Ohk...."

*Haske Writers asso*📚✍🏻

Astaghfirullaahal Adheemal lathee la ilaaha illaa huwal hayyul qayyumu, wa atoobu ilayhi!! Allah knows best.
💫 *Noorul Huda*💫

17.....

Maryam bint Imran shi ne sunanta, mahaifiyarta kuma Hannah, an san Maryam a mace mai son ibada da tsoron Allah a Jerusalem, Mala'ika Jibril shi ya xo mata da wahayin haihuwar Isa Pbuh, da farko taji tsoron ganinsa ta kuma nemi tsarin Allah daga gare shi, and he told her he was only a messenger from Allah, yana kuma yi mata albishir da kyautar A righteous son from Allah, Maryam tayi mamaki da jin hakan don tasan bata da aure kuma ita budurwa ce, a nan tace "Amma taya hakan xae yiwu..." Nan mala'ika jibril yace mata hakan xa'ayi domin Allah yana halittan abinda yaga dama, when he decrees a matter he only says to it 'Be' and it is. (Qur'an 3:47) and that was how Maryam (As) submitted to the will of Allah SWT and secluded her self from society and gave birth to Isa (AS) right under a Date palm tree (Bishiyar dabino) which serve as her source of Nourishment during labour not in a manger as said in your Bible." Murmushi Samantha tayi bata ce komai ba, Yayi murmushin shi ma ya ci gaba, "Maryam ta koma gun 'yan uwanta da Isa pbuh a hannunta, wanda hakan yasa aka fara condemning nata a garin a cewarsu ta aikata sa6o, ko kadan Maryam bata girgixa da surutansu ba tana rike da Annabi isa a cot dinsa, Allah SWT bai barta a haka ba don a nan take isa AS ya bude baki yace "Lallai ni bawan Allah ne...." Shiru yayi ganin yanda ta bude idanuwa tana kallonsa, yace "Ya?" A hankali tace "Uhm ci gaba..." Murmushi yayi ya langwabar da kai yace "He continued saying, Allah has made him blessed wheresoever he be, he has enjoined on him prayer and alms as long as he live, and to be dutiful to his mother, and Allah has made him not arrogant, unblest, and peace be upon him the day he was born, and the day he will die, and the day he shall be raised.... Qur'an 19:30-34." A tare suka kalli kofa da sauri jin an bude, Ilham tayi tsaye bakin kofar tana kallonsu, mikewa yayi fuska daure yace "You re very stupid, baki da hankali xa ki shigo min parlor haka??" Fita tayi kamar xata yi kuka tace "Kayi hakuri yaya Mami ce tace in kira ka..." Yace "Get out!" Rufe kofar tayi ta wuce, Samantha da duk jikinta yayi sanyi ta kallesa tace "Saboda ni kayi mata haka?" Xaunawa yayi kan kujera fuska daure yace "No" ta mike cikin sanyin murya tace "Ohk xan tafi" tashi yayi da sauri yace "No but ae ba mu gama ba Samha" tace "Xa mu ci gaba next time, kaga ur mum is calling" d'an murmushi yayi yace "Alryt... Thanks for the food dear" murmushin ta mayar masa ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, komawa yayi ya xauna ya jinginar da kansa jikin kujera hade da lumshe ido, yafi minti goma a haka can ya mike jiki a sanyaye ya fita xuwa main house, sosai gabansa ya fadi ganin yakumbo, sae dae ya fuske ya xauna ya gaisheta tace "Sae yanxu ka ga dama kenan" ya shafa kai yace "A'a" Mami dae sae kallonsa take, Yakumbo tace "Toh ya maganar mu ta ranan, kasan dae kai ake jira ko?" Ta gefen ido ya kalleta yace "Ni ake jira kuma?" Yakumbo ta kalli Mami a fusace tace "Ki fa gaya masa don ya raina ku ni bai isa ba ne... Ni xae dinga ma tambayar walakanci?" Abuturrab yace "No ban gane xancen bane yakumbo." Buda baki tayi tana kallonsa, ita dai Mami uffan bata ce ba, Can ya mike yace "Kar ki damu Yakumbo xan kawo maki ita har gida ta gaishe ki, shknn dai koh?"
Washegari lahadi da yamma Abuturrab ya shirya don wucewa gun aiki, Yana rufe gate ya dawo xai shiga motarsa ya hangota tana tahowa, tsayawa yayi har ta karaso sanye take da Abayarta dake ta sheki tsabar iron, tayi Islam is peace da veil din abayar, bbu make up fuskarta sai eye pencil dake idonta da lip balm da ta shafa a pink lips dinta, amma ba karamin kyau tayi ba, tayi murmushi tace "Ina yini?" Yana kallonta yace "Lafiya! Ina xa ki?" Tace "Catechism yau Sunday!" Yace "Ohk shigo in yi dropping din ki" tace "Thought clinic xaka?" Yace "Yeah" ta langwabar da kai tace "Toh ae ba hanyar bane" yace "Idan xa ki shigo malama ki shigo" a hankali ta karasa ta bude motar ta shiga, shi ma ya shiga ya ja motar suka dau hanyar titi, ganin hanyar da ya dauka ta kallesa sai dai bata ce komai ba, tafiyar kusan minti ashirin suka yi ganin har sun wuce hanyar asibitin ta kallesa tace "Ina xaka kai ni Doctor?" Ba tare da ya dauke idonsa daga kan titi ba yace "Sayar da ki xan je in yi" bata ce komai ba, haka ya dinga tafiyarsa, ji yayi ta fashe da kuka, ya d'an saci kallonta yayi murmushi yace "Toh ae ba kuka ya kamata kiyi ba, you are supposed to be reciting ur last prayer...." Cikin muryar kuka tace "Ni dai ba wasa nake ba ka ajiye ni in koma gidanmu" yace "Ke da gidan ku kuma har abada..." Ta kuma fashewa da kuka, wani anguwa suka shigo basu wani shiga ciki ba yayi horn a bakin wani gate ba a dau lkci ba mai gadi ya leko ya bude gate din snn ya shigar da motar compound din, yana gama parking, ya kamo hannunta ta fixge, yayi murmushi yace "Yanxu kin yadda xan sayar da ki" hararansa tayi tace "Baka yi kama da wanda xai iya saida Bird ba bare ka saida mutum just that you didn't tell me you are taking me this far nayi xaton asibiti xa mu je" sai kuma ta fashe da kuka sosai, jawota yayi jikinsa yace "Ohk am sorry plsss, ba jimawa xa muyi ba, gidan mum dita ne nan...." Turasa tayi da mamaki tana kallonsa tace "Mum?" Yace "Yeah, my mum sister" ta fashe da wani sabon kukan tace "Ni dai ba ruwana ka kai ni titi in hau tricycle in koma gida" yace "Ohh she's nyc, and she will love seeing you, bata da matsala" bai jira cewarta ba ya ciro handki ya fara share mata hawayen idonta, daga haka ya bude motar ya fita ya xaga ya bude mata kofar ya fito da ita. Bbu kowa parlorn ya sa ta xauna kan kujera snn ya tafi dakin Mum, Hajiya Mariya dake gyaran kayanta a closet tana kallonsa da mamaki tace "Aliyu, daga ina haka?" Yace "Gida Mum" tace "Ikon Allah, sannu da xuwa ya hanya?" Yace "Alhmdllh, da bakuwa muke" bai jira cewarta ba ya fita, sai ga ta ta biyosa, tun bata iso parlon ba take kallon Samantha har ta iso, Samantha ta sunkuyar da kanta gabanta na faduwa, Murmushi dauke fuskar Hajiya Mariya tace "Sannu da xuwa bakuwa" Samantha bata iya ta kalleta ba ta xamo kasa a hankali tace "Ina yini Mumy" Hajiya Mariya tace "Lafiya lau, ya hanya?" Kasa cewa komai Samantha tayi, Hajiya Mariya ta xauna tana kallonta tace "To koma kan kujeran mana" bata dago ba bata kuma ce komai ba, Abuturrab yayi murmushi yace "Mum meet Samantha.... But I do call her Samha.." Hajiya Mariya tace "Ohh maa sha Allah, but this Samha is too shy, taki xama kan kujera" Yace "No she's comfortable there" Hajiya Mariya tace "A'a ni ba ruwana ta koma kan kujera" daga nan ta mike ta nufi fridge don dauko masu drink, kallonta yayi yace "tashi koma kan kujera" bata kallesa ba bata kuma tashi ba, ya mike yace "Toh bari in daga ki" da sauri ta koma baya tace "No bana so ka bari plss" kamar xata yi kuka tayi maganan, ya wara ido yace "Toh kuka xa ki min?" Kin cewa komai tayi, Hajiya Mariya ta dawo parlon da ruwa da lemo ta karasa kusa da ita ta ajiye tana kallonta tace "Yanxu baxa ki hau kujera ba bakuwata" girgixa kai kawai tayi, Haka kawai Hajiya Mariya taji ta burgeta a xuciyarta kuwa tunani take wnn din ce Christian din da Abuturrab ke fadi mata, kitchen ta koma ta xubo masu fried rice din da tayi, ganin ynda Samantha taki sakin jiki ta bar masu parlon, tana wucewa ta dago kamar xata yi kuka tace "Doctor plss mu wuce" ya hade rai yace "Gidan Mum dita ne nn fa" tayi shiru bata ce komai ba, ba karamin takurata yayi ba ta ci abincin shi ma kadan, hade rai yayi ya sauko kasa ya karbi spoon din ya debi abincin ya kai bakinta, kamar xata yi kuka tace "Doctor ka bari plss" dafa forehead dinta yayi ta bude bakin da sauri ya xuba mata ya kai sauran baki, sunkuyar da kanta tayi tana taunar abincin a hankali, can ta kallesa a hankali tace "Doctor wllh na koshi" yace "Me kika ci?" Tace "Pounded yam and vegetable" yace "Shine baki kawo min ba?" Ta wara ido tace "Kana so?" Yace "Ehh mana" ta langwabar da kai tace "Toh xan maka" mikewa tayi tace "Kitchen fah?" Ya nuna mata hanyar kitchen ta dau tray din abincin ta nufi can, mikewa yyi ya shiga bedroom din Hajiya Mariya. Tana shiga kitchen taga kayan wanke wanke a hade cikin sink, liquid soap ta dauka da sponge ta hada ruwan kumfa ta fara wanke su, cikin kankanin lkci ta gama don bai da wani yawa, ta tsaftace kitchen din ta goge har Gas snn ta dau sweeper ta fito parlor, Abuturrab ya xauna gefen Mum din sa dake waya har ta kare wayar snn ta kallesa tace "Ita ce yarinyar Aliyu?" Kai ya gyada mata, ta girgixa kai tace "She's cool and pretty, kuma bata yi shige da yare ba kamar bafulatana, and kamar ba Christian ba" murmushi yayi yace "Abbanta bafulatani ne ae...." Shiru Hajiya Mariya tayi, can tace "Allah sarki.... Toh yanxu ta yarda xata yi converting din ne?" Xaro ido yayi yace "Mumy ni fa bamu taba magana irin wanda nake maki da ita ba...." Da mamaki tace "Kana nufin bata san kana sonta ba?" Shiru yyi sai kuma ya girgixa kai a hankali yace "Ko ma ta sani bata taba nuna ta sani ba" Hajiya Mariya tace "Toh fah, then it's better ka fadi mata soon as possible kaji ra'ayinta" ya lumshe ido yace "Ohk mum" 'yan shawarwari ta basa sannan tace ya tafi parlor ya bar ta ita kadai, mikewa yayi ya fita, xaune ya sameta idonta na kan tv, ya karaso ya xauna kusa da ita yana kallonta yace "Sae bayan magrib xa mu tafi koh?" Ta dago da sauri ta kallesa xata yi magana sai ga Hajiya Mariya wanda hakan yasa tayi shiru, Hajiya Mariya tace "Sannu my daughter, mun bar ki ke daya koh?" Murmushi Samantha tayi bata ce komai ba, ya kalli agogo yace "Mumy xa mu wuce...." Tace "So early?" Yace "Mun dade fa Mumy" tace "A'a ba wani dadewa" daki ta koma ba a dau lkci ba ta fito rike da leda ta mika ma Samantha tace "kiyi hakuri bbu yawa kin ji...." Da sauri ta girgixa kai tace "A'a nagode Mumy" Mumy ta mika ma Abuturrab tace "Toh gashi ka bata tunda kunya ta take" har mota ta rakasu sai da suka fita sannan ta koma ciki, a hankali yake driving din, can ya juya ya kalleta, idonta na waje tana kallon titi, kamo hannunta yayi ta juyo tana kallonsa, ya murza fingers dinta yace "Kin san me?" Janye hannunta take son yi ya ki saketa, murya can kasa yace "My mum.... Kinsan me tace?" Kallonsa ta sake yi snn tace "A'a" murmushi yayi murya can kasa tace "Wai tana son ki, she likes you, how she wish you were a Muslim sai ki xama in-law dinta" murmushi tayi ta kwace hannunta bata ce komai ba, yace "Kin yi shiru" wara ido tayi tace "Uhm and unfortunately am not a Muslim"

*Haske Writers Asso*📚✍🏻 sorry for the delay!
💫 *Noorul Huda*💫

18.....

Murya can kasa yace "And you can't become one koh?" Wani kallo tayi masa ta gefen ido tace "as in?" Shiru yayi bai ce komai ba, can yayi murmushi yace "Gaya min me ya burge ki a Christianity!" Ta girgixa kai tace "I don't want to talk about that now!" Bai sake ce mata komai ba har suka iso layinsu, tace "Kayi dropping dina kawai in karasa da kafa" bai tanka ta ba ya isa har gate dinsu ya tsaya snn ya juya yana kallonta, ta bude motar ta fita hade da daga masa hannu, dauke idonsa yyi ya ja motor ya bar wajen, ta bi sa da kallo har yayi nisa snn ta juya ta shiga cikin gida. Mumy ce xaune parlor da wata bakuwa, ta durkusa ta gaishesu xa ta wuce Mumy tace "Ina bible din naki?" Shiru tayi tana kallonta, lkci daya ta tuna ta bar shi a motar Abuturrab, rasa abinda xata ce tayi, uwar ta watsa mata wani kallo tace "Ba kya ji ne?" Wayar Mumyn ne ya dau kara ta dau wayar tare da dagawa, Bakuwarta da ke xaune ta kalli Samantha tace "Tashi kije" mikewa Samantha tayi da sauri ta bar wajen don in har Mumy ta ci gaba da tambayar xata iya fadi mata gaskiyar daga inda take. Karfe tara saura tana xaune da Mathematics gabanta tana solving don Tuesday suke da maths, gaba daya ta kasa ci gaba don ta manta calculation din, bude kofar dakin aka yi Mumy ta shigo tace "Daughter xan tafi church yanxu akwai prayer da muke yi ma wata...." Da sauri Samantha tace "Yaushe xa ki dawo Mumy" Mumy tace "At dawn, Blessing na nan ai, take care of ur self" daga haka ta juya ta fita, Samantha tayi tagumi, it's always church ta fadi a xuciyarta, shi kuma Abba alwayz politics..... Tabe baki tayi ta ci gaba da kallon math din gabanta, Abuturrab ne ya fado mata ta Kalli agogo, dai dai nn ta ji fitar motar Mumy, mikewa tayi sai kuma ta kalli jikinta ta ga 'yar rigar bacci ne iya gwiwa, ta bude press ta fiddo da kimono mai d'an kauri ta daura kan kayan ta dau veil ta rufe kanta snn ta dau textbook dinta da note book tare da pen sai calc, a hankali ta bude kofar ta ta fita ta leka dakin da mai aikinsu take taga har ta kwanta, a hankali ta sauka kasa ta nufi kofa taga a rufe, ta bude ta fita, sai da ta ganta kofar gida gabanta ya shiga faduwa, tafiya take da sauri da sauri har ta iso kofar gidansu Abuturrab, ta tsaya kusa da gate kamar munafuka, tura gate din tayi ta ji a bude ma yake, ta tura a hankali ta shiga sannan ta rufe, da sauri ta nufi balcony tana lekan parlon ta gansa xaune a kan carpet yana danna laptop yyi backing kofar, cikin dubara ta murda kofar yanda baxai ji ba sbda k'aran Tv, tana shiga parlorn bata rufe kofar ba cikin sanda ta nufesa, ta durkushe bayansa tayi wani k'ara, juyowa yayi da sauri lkci daya ya jawota jikinsa ya matse ta, xaro ido tayi, ya buga goshinsa da nata yana wani murmushi yace "See you! Tun da kika bude gate naji shigowar ki malama" boye fuskarta tayi tace "Ohhh," ya dago kanta yace "yan gidanku sun tafi church kenan" kwace kanta take son yi yaki saketa kamar xata yi kuka tace "Pls ka sake ni mana" kallon kafarta yayi don kimonon ya d'age daga kasa yace "Baki sa kaya ba knn.." Bai kai karshe ba ya dage kimonon, sai ga long legs dinta a waje, ta wani hade rai tana kkrin kwace kanta tace "What's this" ya buda ido yace "Ohh sorry, i never knew you were naked" wani kallo ta watsa masa tace "Am not naked" ya fashe da dariya, ta samu ta kwace kanta ta mike ta dau litattafenta ta nufi kofa, ya tashi da sauri ya isa gun kofar ya rufe, kallonsa take kamar xata yi kuka, ya langwabar da kai yace "Wasa fa nake" tace "Yeah na sani, bude min kofa in wuce" yace "Nooo baby i was only joking" bata ankara ba sai ji tayi ya wani sureta ta runtse ido tace "Doctor....." Kan kujera ya direta yace "Ki hakura plss" da sauri tace "Nayiii" ya ja hancinta yace "Troublesome girl" kallonsa kawai take, ya hura mata iska ta rufe idon da sauri yana murmushi yace "Irin wnn kallo" turo baki tayi tace "I brought my mathematics, put me through pls" daga haka ta bude textbook din tana nuna masa ya karba, k'asa ya sauka ta bi sa, nan ya shiga nuna mata solution din question din, sai kusan goma suka gama, mikewa tayi tace "Ka raka ni plss dare yayi" yace "Spend the night here tunda dare yayi" ta hade rai tace "No, why shud i??" kamo hannunta yayi ya tsare ta da ido yace "Cinye ki xan yi idan kin kwana?" Kallon manyan idanuwan nasa take, murya can ciki yace "Plss dear" a hankali kamar xata yi kuka tace "but it's not decent, it's not proper....." Da sauri yace "Naga dare yayi ne fa..." Xata yi magana yayi mata wani kallo ta kasa cewa komai tana kallonsa, sake hannunta yayi ya nufi kofa ya bude yace "Alryt, you can go sai da safe" ta sauke idonta kasa, ya karasa kujera ya xauna, kallonsa tayi snn ta nufi inda yake ta durkusa tace "Ohk am sorry, i will spend the nyt here sai in tafi da sassafe kamin mumy ta dawo" yace "No, am not forcing, kar ki fara wani tunani fah, you can go...." Hade rai tayi tace "Toh am not going" ya shafa beard dinsa hade da tabe baki yace "Da wani katon idonta a wajen, i guess her thought will be like what is this guy up to da yake son in kwana yau" xaro ido tayi ya fixgota kusa da shi yana murmushi yana kallon kwayar idonta yace "ko ba
Haka ba? Babu abinda xan maki har sai ran da Allah ya mallaka min ke a matsayin matata" buda ido tayi tana

Please Login or Register in order to submit comment