Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

our stay with her" Ashraf yace "Ummu, Grandma came to see u, go to her" Rachael ta daga hannu da sauri tace "Noo, noo i came to see my little angel" Arshaq ya bata fuska yace "With mum also" Rachael ta kirkira murmushi tana shafa kansa tace "Yes Prince" da kyar Noor ta xauna kasan carpet tana kallon Uwar tata tace "Ina yini Mum" Ba tare da Rachael ta kalleta ba tace "Eh lafiya lau" Abuturrab ne ya sakko parlon jin muryan kids din nasa, ya karaso parlon yana kallon Mum din Noor ya dai yi karfin halin cewa "Ina yini mum" ta kallesa ta watsa masa harara tace "Lafiya lau" Mikewa Noor tayi ta tafi fridge dauko ma mum dinta ruwa, Rachael kasa barin gidan tayi sbda jikokinta, duk da taki sake ma Noor bare Abuturrab fuska, gaba daya su Arshaq na xagaye da ita da yar kanwarsu da Rachael taji kmr ta gudu da ita amma ba dama, ji tayi dama ta dauwama har abada tare da yaran sbda so, su suka tilastata ta ci lunch din jollof din Cous Cous da yaji kayan hadi wanda Noor ta yi, sai kusan karfe uku ta bar gidan, bbu ynda Abuturrab bai yi yyi dropping dinta ba amma taki yrda don tuni Mr David ya wuce, wannan ne mafarin fara kiran Abuturrab da Rachael tayi bayan ta karbi numbersa gun Mai gidanta, kusan kullum sai sun yi waya da yan jikokin nata, wani lkcn Noor kan karbi wayar ta gaisheta duk da ba wani amsawan kirki take mata ba amma tana jin dadin yanda take ji da grandchildren dinta, bayan duk sati biyu ta kan xo gidan ranan asabar amma iyakarta balcony ta ba yaran abinda xata basu tayi wucewarta, hakan yasa Noor ta fara kwadayin xuwa gida ko da kuwa da yaran ne, kilan sanadin hakan su samu masalha da mahaifiyarta, hakan kuwa aka yi ranan wata friday Noor tace da Abuturrab tana son xuwa gidansu tayi weekend da kids din nata, da kansa ya kai su gaba daya gidan, har ya shiga ya gaida mum din shi ma, Rachael tayi murnan xuwan su har ita Noor din amma a fili nuna cewa murnan xuwan yaran kadai tayi, bbu abinda ta rage su da shi, duk da fa magana me tsayi bata yrda ya hadata da 'yar tata, ranan lahadi da safe Noor na daki tana bacci Rachael ta shigo tana tafe hannu tace "Toh nonbelievers ni dai xan wuce church, ga yara can basu tashi ba ki dinga kula min da su har in dawo, idan kuma suka tashi ga breakfast na hada masu a kitchen, wankan ma ba sai kin masu ba xan masu idan na dawo" bata jira cewar Noor ba ta fita, Noor tayi murmushi ta koma ta kwanta, a yammacin ranan little Noor ke ta xaxxabi Rachael duk ta rikice nan ta samo Rosary ta rayata mata a wuya, Noor dai ta kasa cewa komai kuma bata cire ba, Arshaq na kyalla ido ya gani ya cire yana cewa "Grandma am begging you plss don't put this on our little sis again, it's a burden" Rachael da ke ta kallonsa ta kwace abarta tace "Alryt give it to me" daga haka ta bar masu parlon, Noor tayi murmushi tana kallon Arshaq da ya koma ya ci gaba da kallonsa, hka suka karashi weekend din a gidan Abuturrab ya xo da daddare ya daukesu suka koma gida. Bayan sati biyu sai ga Sadeeq ya kawo ma Abuturrab Katin aurensa, Abuturrab ya taya sa murna sosai yace "In ji dai Zainab ce?" Dariya Sadeeq yayi yana rungume da Namecy dinsa Arshaq yace "Yea ta ci sa'a ita ce" Abuturrab ma yyi dariya yace "Ka dai ci sa'a" Sadeeq yace "Assiddiq nake son ka bani yyi mata xaman daki" Abuturrab na shafa kai yace "Na baka" Sadeeq yace "Am jet serious fah, ita kuma little Noor ina nan ina jiran girmanta kishiyar Zainab ce tun yanxu ka ji" Abuturrab ya wara ido yace "Me xata yi da tsoho?" Da yammacin ranan Abuturrab yasa sadeeq ya rakasa kasuwa ya siya bike sabuwa dal, Sadeeq sai mamaki yake bai dai ce masa komai ba sai da suka bar kasuwar yace "Kai kuma me xaka yi da bike frnd?" Abuturrab yace "Mu je kai dai kaga, dama kai nake jira ka xo" a gate din wani gida Abuturrab ya tsaida bike din ya sauka Sadeeq ma ya sauka, Abuturrab dai sai kallon gidan yake, yana kkrin tura d'an gate din gidan wasu matasa biyu suka fito, Abuturrab ya kare ma wanda ke facing dinsa kallo daga sama har kasa snn yace "Ka gane ni kuwa?" Mutumin na gyada kai yace "Kwarai kuwa na gane fuskar nan" Abuturrab ya kama hannunsa ya sa masa makullin bike din yace "Ga Machine dinka na dawo maka da shi, so srry for the inconvenience" kallonsa kawai mutumin ke yi ya kasa cewa komai, har Abuturrab ya juya xai wuce mutumin yace "Nagode kwarai da gaske" Sadeeq dake ta jinjina lamarin yace "Tab ai in nine tuni na mance, sai dai in biya sa a aljanna" dariya duk suka yi mutumin yyi exchanging Number da Abuturrab ya rakasu suka hau tricycle xa su koma gida, washegari Sadeeq ya koma Uk, don can yake rayuwarsa. Noor na shirin kwanciya Abuturrab ya shigo da Huda dake bacci ya kwantar da ita kan gado, ya karasa kusa da wife din tasa ya rungumota ta baya ya lumshe ido yace "Kinsan me Ummu?" Tana kallonsa ta mirror tace "Sai ka fada Abbu" jan hancinta yyi yace "Xa mu je Convocation din fatima Gombe" Bata ce komai ba bata sake kallonsa ba kuma ta shiga kkrin daure gashinta, ya karbe ribbon din yace "Am talking Ummu" still ba tare da ta kallesa ba a takaice tace "I don't think am going, baxan je ba" yace "But why? Naga kids din na midterm break ranan" A d'an fusace tace "Toh ku je mana ni baxan je ba" murmushi yyi sosai yace "Har bikin nata knn, cos an gama convocation din da kwana biyu bikinta" sai a snn ta kallesa, can kuma tace "Toh Allah ya kai mu, wa xata aura?" dariya yyi yace "Baki ji kunya ba Samhata?" Murmushin tayi ita ma tace "Kunyar me?" Yace "Kin fini sani" ta juyo ta wara masa ido tace "Ohh baka son ina kishin ka knn?" Lumshe ido yyi yace "So kai" ta rungumesa tana murmushi tace "Yauwa Abban twins dina" shirye shiryen xuwa gomben suka dinga yi, ranan talata kuwa suka dau hanya bayan sun je sun ma iyayensu gaba daya sallama, Noor bata wani yi mamakin cewar Dr Shariff ne angon fatiman ba, suna gombe har bayan bikin da kwana biyu, Noor bata so hakan ba don kids dinta xa su yi fashin makaranta knn, ranan Monday suka sallami Ummi, Ummi tace "Anya takwarata xata kuma bin titi kuwa Son, gaskiya k'ura yyi yawa" Rabi'a dake parlon ita ma tayi dariya tace "To Ummi ki biya mata jirgi kawai" Ummi tace "Ae hakan ma xa ayi, nawa ne flight din, daga baya sai ka xo ka dau motar ka" dariya Abuturrab yyi yace "Mami ba gida xa mu direct ba ma" Tace "Ina xa ku?" Ya shafa kai yace "Xa mu biya gun wani frnd dina ne" Ummi tace "Toh shkkn, Allah ya tsare" duk ynda Ummi ta so su karbi kudin da ta ba takwararta a cewarta Abuturrab bai yrda ya karba ba, a hka suka bar gidan, Noor dai na bayan motar da yaranta dake ta game da wayar Abbun su, ganin ba hanyar Kano ya dauka ba tace "Abbu ina xa mu kuma" ta madubi yake kallonta yace "Ziyara Ummu" tace "Kai Abbu my kids r missing classes fa" yace "This the only opportunity we have wife, baxa mu dawo garin nn lkci kusa ba" tace "Buh nan da wata hudu ae bikin khadija" Yace "Duk da haka dae Ummu" bata kuma cewa komai ba, sai da suka yi tafiyar kusan minti talatin snn ta d'ago inda xa su, tace "Kai dear hw did u want this kids to cope there? Kasan ba sabawa suka yi ba" yace "Ke lkcn kin san xa ki iya copying a can? Gun da har muka samu shelter for good two days ba wajen rainawa bane madam" ta xaro ido tace "No don't misunderstand me dear, i mean they r nt familiar with place like dat" yace "Yea, experience is the best teacher, let dem go nd learn, beside tun da mum dinsu ta hakura da rice during that time su ma xa su hakura ne ynxu" murmushi kawai tayi bata ce komai ba, ya kashe mata ido yana kwaikwayon muryarta yace "Baxan iya ci ba Dr..." Hararansa tayi ta rufe fuskarta, yyi dariya sosai yace "Eh mana, then na tambaye ki to me xa ki ci wai wani *Rice* ke ga baturiya" bata san lkcn da ta fashe da dariyar ba itama tace "Wayyo bana so dear ka bari plsssss" ya wara mata ido yace "Ae sae ma yaran ki sun girma na basu lbrin" kallon kids din nata dake ta playing game tayi tana murmushi.

*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫

By khaleesat Haiydar📚✍🏻

106.....

Har mamakin ynda Abuturrab bai mance hanyar garin Noor ta dinga yi, suna isa Rugar dai dai kofar gidansu Alto Abuturrab yyi parking, ya fito daga motar yana kare ma gidan kallo, Arshaq sai damun Ummun sa yake ina ne nn Abbu ya kawo su tace "We came for visit son" Noor ta fito motar rike da little Noor, twins din suka ki fitowa motar ko wannensu ya tsuke fuska, Noor ce tayi sallama kofar gidan taji muryar Mama Hansai na amsawa daga ciki, a hankali ta sa kafa ta shiga gidan, Hansai dake sauke sanwan rana na dumamen tuwo daga kan wuta ta mike da sauri tana kallonta, murmushi Noor tayi ta isa kusa da ita ta durkusa tace "Sannu mama" Hansai ta saki salati tana tafe hannu tace "Wa xan gani haka, yar nan kuna duniya ashe, Allah mai girma sannun ki da xuwa, sannu da xuwa" da sauri ta shimfida mata tabarma tana yi mata sannu da xuwa cike da farin ciki ta karbi Noorul Huda snn Noor ta xauna tace "Mama bani daya bace yana waje" Hansai tace "Wai yayan ki? Allah sarki ce mashi ya shigo maxa maxa, Alto ma na kewaye Allah ya rufa asiri bai fita ba, ce ya shigo" Noor tace "Toh mama" ta mike ta fita waje, Abuturrab na tsaye jikin mota ya rungume hannayensa tace "Ku shigo dear" daga haka ta juya ta koma ciki, ya bude bayan motar yana kallon su Ashraf yace "Come down" Arshaq ya girgixa kai da sauri yace "Noo Abbu we will wait for you here plss" hade rai yayi yace "I will knock you both, get down immediately now" fitowa suka yi da sauri yace "It's a promise, here will be ur next place for holiday" duk kallonsa kawai suke basu ce komai ba, ya shiga gidan suka bi bayansa, Hansai ta rasa inda xa ta sa su gaba daya don farin ciki ta ciko masu kwarya da ruwa ta kawo tana ta yi masu sannu da xuwa, Alto ma ya fito bayi ya dinga masu lale marhaba yana washe baki, ya rungumo su Arshaq yana masu fillanci duk suka tsura masa ido, yayi dariya sosai yace "Ga shi dai da ganin ku an ga fulanawa amma bakwa ji" Murmushi Abuturrab yyi a xuciyarsa kuwa yace dole ma ya fara yi masu yaren, Alto yace "Toh Maa sha Allah, Allahu ya raya ku 'yan samari, ashe dai da rabon xa mu sake saduwa Ali, Allah mai girma" Abuturrab yace "Wllh kuwa Baffa, da fatan mun same ku lafiya" Baffa yace "Alhmdllh, Alhmdllh mun gode Allah, duk lfya lau muke wllh" yana son tambayar Binta amma shakkar Noor ya hana yyi hkn, yana ta jiran ita tayi tambayar amma ta ki, Hansai ta dauko kwano tana cewa "Wllh gashi ynxu na sauke dumamem tuwo da miyar kuka sai dai ko k'ashi bbu a miyar sai waran mu ta fulani da na jefa ciki, kuyi hakuri don Allah" Noor tace "Haba Mama ba komai mun ma ci abinci fa kafin mu fito" Hansai tace "A'a ni dae bara in xubo ku ci don Allah" daga haka ta xuba masu tuwon da miya a kai ta ajiye ma Noor da su Arshaq, Abuturrab ma ta xuba masa ta kai masa, murmushi yyi yace "Godiya muke mama" Wata kyakkyawar yarinya ce da baxa ta wuce shekaru 5 ba ta shigo gidan da 'yar karamar tulu a kanta, fara ce sosai gashinta har kusan gadon bayanta, ta ajiye ruwan kanta tace "Inno gashi na debo" Sai a snn Noor tace "Mama Binta fa?" Hansai ta kalleta sai dai bata ce komai ba, Alto dake xaune kusa da Abuturrab yace "Ae Binta Allah ya mata rasuwa shekaru biyar kenan" Noor taji xancen nasa har xuciyarta ta kasa cewa komai sai kallonsa take a sanyaye, Abuturrab ne yyi karfin halin cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un ta rasu Baffa, Bata da lafiya ne?" Alto yace "A'a ko daya, wajen haihuwar 'yar can dai ne Allah ya karba abarsa" ya fadi yana nuna yar yarinyar dake tsaye kusa da Hansai dake matsar kwalla, Tuni Noor ta fara hawaye lkci daya jikinta yyi sanyi sosai, shi kam Abuturrab bai iya ya kara cewa komai ba sai dai tuna irin ynda ta dinga hawaye ranan da xa su bar kauyen yasa jikinsa yin sanyi sosai, bai mance alkawarin da yyi mata na cewa xa su dawo su tafi da ita birni ba, murya Hansai ya katse masa tunaninsa cikin sanyin murya take cewa "Binta ta dde bata yi aure ba bayan tafiyar ku, kullum ba dare ba rana jira take ku dawo ku kai ta birni tayi karatu kamar yanda ta ce kayi mata alkawari, da kyar dangin mahaifinta suka yi mata auren nan, ashe ta ajali ce" ta karashe maganar tana kuka sosai, Alto yace "Ka ji ta kuma...." Cikin kuka tace "To ya kake son in ce Alto" yace "Dama can wa'adin da Allah ya debar mata kenan duniya, kiyi ta mata addu'a don shi kadai take bukata gun ki" Hansai bata kuma cewa komai ba sai share hawayen da ta dinga yi, Kallon yar yarinyar dake gefenta Abuturrab yyi, a hankali yace "Allah ya ji kanta, ya rahama mata, ya kyautata na mu" Alto yace "Amin" Noor kam kasa daina kuka tayi ta rasa dalili, da ta tuna ynda ta dinga kulawa da ita taki sake mata fuska tana basar da ita sai taji duk bata kyauta ba, kukan da take yasa su Arshaq suka fara taya ta su ma, Hansai tace "Hakuri xa mu yi 'yar nn, kiyi shiru don Allah ga shi kin sa 'yan yaran nn kuka su ma, tuni na bar ma Allah komai, Binta ita kadai ya bani kuma ya karbe kayansa ba don bai so na ba, kinga ko dole in ta gode masa, ga 'yar ta nn an maida mata sunan, muna kiranta da Fatima ita na kan gani in ji ddi" Abuturrab yace "Haka ne Baaba addu'ar mu kadai take bukata, Allah ya gafarta mata" Duk suka ce Amin, Abuturrab yace "Amma ina neman wata alfarma gun ku Baffa" Alto yace "To ina sauraren ka Ali, ta me kenan?" Yace "So nake ku koma can cikin Birni da xama don Allah, xan samar maku waje, idan ya so ko wace irin sana'a kke son yi sai in taimaka maka Baffa" Murmushi Alto yyi sosai yace "Allah sarki, ban ki ta taka ba Ali, amma gaskiya ni ko kadan ban sha'awar rayuwar birni na fi son xama a ruga" Hansai tace "Haka ne Ali, ni kai na nafi son nn baxan iya xaman birni ba" Abuturrab yace "Toh shknn, Alfarma ta biyu kuma don Allah baffa kada kace a'a, so nake ka ban Fatima in hada in rike da yarana, ina son ta samu ilimi ynda ya kamata" Hansai ta d'an yo waje da ido, Alto kam murmushi yyi yace "Wani hanxari ba gudu ba Ali, kada ka mance ba mu da iko kan yarinyar nn..." Abuturrab ya katse sa yace "Mahaifinta fa?" Alto yace "Yauwa ynxu kayi magana, bayan rasuwar binta da shekara biyu shi ma ya rasu bayan yyi fama da ciwon daji" Hansai ta tabe baki tace "Dangin sa kuwa duk gantalallu ne, tun bayan rasuwar sa bbu wanda ya tako ganin halin da fatima take ciki, basu san cin ta ba basu san shanta ba, mu kadai ne gatan ta" ta karashe maganar tana matsar kwalla, Abuturrab yace "Toh don Allah ku rabu da su Baffa ku ban yarinyar nn na maku alkawarin xan dinga kawota tana maku hutu, xa ku ji dadin ta nan gaba, kar ku manta muhimmancin ilimin muhammadiyya da boko a xamanin nn da muke ciki" Baffa yyi shiru haka Hansai da ta xuba tagumi, Hansai da wasu sabbin hawayen suka xubo idonta tace "Ita daya nake gani in ji dadi ynxu Ali, idan kuka rabani da ita ya xan yi da raina?" Abuturrab ya sauke ajiyar xuciya yace "Baaba sai ki samu ko d'an 'yan uwa ne ki rike don Allah, ni dai a gaskiya ina son in ma 'yar nn abinda ke ran uwarta har ta bar duniya ku yi hakuri don Allah, sai ma mu iya xuwa da ku ku ga inda muke don lallai duniyar nn ba abun yrda bane tunda ba wai sanin mu ku ka yi sosai ba" Alto yace "A'a ni na yadda da kai Ali, Allah ya shige mana gaba, gata nan ni dai banda abun cewa kuma" ya fadi hakan yana kallon Hansai dake share hawaye tace "Ae shknn, Allah yasa mu dace" Abuturrab yaji dadin hakan yace "Yauwa baaba, in sha Allah xata dinga xuwa maku hutu har ma da yaran gaba daya" Baffa yace "Maa sha Allah, Allah ya taya ku riko" Sai kusan la'asar suka fara shirin barin gidan bayan Abuturrab ya tabbatar su Arshaq sun cinye tuwon tas, amma fa da kyar, Hansae na kwalla ta gama hada ma fatima 'yan tsummokaranta, Dubu talatin Abuturrab ya ba Alto dake ta masa godiya yana sa masa albarka, ita kuma Noor ta ba Hansai dubu goma ta kuma cire layinta dake karamar wayar hannunta ta rubuta masu number Abuturrab a takarda ta mika mata tace "Sai Baffa ya siyo layi a sa a wayar ga Numbersa nan da kun kira xa ku samu" Har bakin mota suka rakosu sai a snn fatima ta fara kuka da Fillanci take tambayar Hansai inda xa a kai ta wanda hakan yasa Hansan kuka sosai, A haka Abuturrab ya ja motar suka bar kofar gidan Noor na daga masu hannu, rarrashin Fatima Noor ta dinga yi da fillanci, Arshaq da kukan ya ishesa yace "Ohh Goodness, Ummu why are we leaving with someone's Child for god's sake? It will look as if we kidnapped her..." Hararansa Abuturrab ya dinga yi ta madubi hakan yasa yayi shiru bai kara cewa komai ba, kafin su shiga kano har tayi bacci, suna isa gida Abuturrab yyi parking ya fito, Noor ma ta fito da little Noor a hannu, su Arshaq suka fito su ma, Abuturrab ya dau fatima dake ta bacci suka shiga cikin gida.

*Haske writers asso*
07087865788 for Comment nd corrections!!! You re welcm.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment