Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai kawai Noor tayi, tace "Toh maza ki gama ki basu abinci su ma don yunwa suke ji" a hankali tace "Toh" yakumbo ta fita, Hajiya Mariya ce ta shigo da Sadeeq ta kwantar da shi gefen d'an uwansa tana kallon Noor tace "Idan kin gama sai ki yi breastfeeding dinsu kin ji Daughter" Noor tace "Toh" ita ma ta fita dakin, Tea kawai ta hada ta sha don ji tayi baxata iya cin komai ba, can ta mike ta koma kan gadon ta kwanta gefen yaron tana kallonsu. Karfe sha biyu saura Anty Maryam ta wuce, Col da kansa ya bata 20k kudin mota, Mami kuma ta ba Ihsaan atamfa guda Uku cikin wanda twins suka samu na suna, Hajiya Mariya da Abuturrab ne suka kai ta park, tun da suka bar gidan Noor ke kuka a daki, ta rasa dalilin kukan nata. Abuturrab na dawowa Ilham ta tare sa a parlor wai Abba na kiransa, ya d'an yi jim yana kallon Hajiya Mariya dake kallon ilham ita ma, can tace "Yakumbo na parlorn ne?" Ilham tace "Eh tana ciki" tsaki Hajiya Mariya tayi ta wuce sama, Abuturrab ya nufi parlon Abbansa, a hankali ya tura kofar ya shiga da sallama, xaunawa yyi kasa yana kallon Col yace "Ga ni Abba" Col ya kallesa yace "Na gan ka" D'an murmushi yyi ya sunkuyar da kai, Yakumbo tace "Atoh, ba wani abu bane dama batu ne da xai xame maka alkhairi nn gaba, kaga dai ni Fatima baxan so abinda xai cutar da kai ba Ali, kai ba ma hka ba, ni ta wa ennan yara biyu nake baxan so su halaka ba, haka kurum rana tsaka ka dau kirista wacce ba muharramar ka ba ka lula duniya da ita, kayi ta ba Ahmad wahalan neman ka, ni ma kasa nayi ta shiga da fita ina neman a karkato min da hankalinka ka dawo gida, to ni duk wnn bai wani dame ni ba, abinda yafi damuna shi ne Hajarah da Mariya sun san komai suka dinga munafurtar mu ashe su suka xuga ka kayi abinda kayi ma, kuma sun san inda kke, to ba wnn ba ma, babban tashin hankalin shine ynda ka kai yarinya masallaci aka daura maku aure kaje kana rayuwa da ita hankali kwance ga ka tatattcen mara ji koh? to dai wllh kullum kayi ta addu'a Allah ya yafe maka mahaifin ka ya yafe maka ni ma in yafe maka, idan ba haka ba wllh tarihi sai ya maimaita kansa, kana ji kana gani yar ka mace xata bi kato su gudu da sunan so, to don Allah wa ka cuta idan ba mu ba?" Sai a snn Abuturrab ya dago yana kallonta, Tace "Atoh, ba xancen ka harareni bane gaskiya ce na fada, ba haka kayi ma yar mutane ba, to kaji tsoron Allah kar kai ma ayi ma yar ka, kaga ko mu ma mun shiga uku ba kai kadai ba, to ni duk ba ma wnn ba, wai sai gashi da ka tashi dawowa sai ka dawo mana da yan biyu, wai kirista ta haife su, to ynxu abun tambaya a nn Aliyu shine, waye xae ba yaran nn tarbiya irin ta koyarwar islama?" Bbu yabo bbu fallasa yace "Uwarsu!" Yakumbo tace "Yau naga abinda ya ishe ni bai ishi Allah ba, wace uwar ta su? Ita kafurar xata ba su tarbiya" Abuturrab yace "Umma ki bar ce mata kafura, ynda kike musulma ita ma haka take musulma, kuma bbu wanda yafi wani a gun Allah sai...." Tsawa Abba ya daka masa ya mike yace "Are you stupid, ko ka fara shaye shaye ne?" Yakumbo tace "Atoh wa ya sani abu a duhu" Abba yace "I will kick you out idan baka maida hankali kasan warce ke gabanka ba, kar kayi tunanin na basar da abinda ka min ne, i am coming for you soon" Yakumbo ta tabe baki tace "A'a bar sa, ba ga yaran maxa nn ya haifa har biyu ba, xai ji ko da ddi ko bbu" Abuturrab bai kuma cewa komai ba, Tace "Toh ae ba tsoron ka ake ba, kame kamen ma an fasa, dama ba wani abu bane yasa aka kira ka nn, aure nake son kwanan nn ka sake, ka auri wacce xata kula maka da yaran da ka haifa, ta kuma yi musu tarbiya irin ta musulunci" tana huci ta kare maganan, ya d'an kalleta, snn ya girgixa kai yace "Bani da ra'ayin auren mata biyu Umma kiyi hakuri" ta mike tace "Toh kuwa ynxun nn xaka yi ra'ayin yin haka, idan ba haka ba wllh wllh wllh in kwashe yaran inyi tafiyata da su su girma a gu na, bbu kai bbu su kuma" Abuturrab yace "Na baki Umma" buda baki tayi tace "Ohh haka ma kace" yace "Umma ni dai da in kara aure gwara kin tafi da su ki basu tarbiyar ke, ita kuma nayi alkawarin baxa ta sake haihuwa ba.... Ina ce sbda a ba yaran tarbiya xan kara auren" rike baki tayi tace "Ehh lallai Aliyu ya xama dan iska, toh kai ke bada haihuwan da xaka hanata yin sa?" Ya girgixa kai yace "Bani ke badawa ba, amma bayan yaran nn biyu baxa ta kara haihuwan ba bare a dinga tunanin irin tarbiyar da xa su samu, wa ennan da ta haifa dai na baki su ki basu tarbiyar" Col dai kallonsa kawai yake, Yakumbo aka rasa abun cewa sai huci take, komawa tayi ta xauna tace "Toh wai ma ni me xanyi da jikoki daga gun tubabbiya" ya girgixa kai yace "Yara na ne ba nata ba, ni ke da iko da su ba ita ba, snn kuma nace na baki su Umma" a fusace Yakumbo tace "Toh ni kuma jikoki biyu sun min kadan don ubanka" murmushi yyi yace "A'a fa Umma jikokin ki sun kusa sha biyar, to me xai dame ki," Col yace "Alryt, idan kuma ku ka sake haihuwa i will surprise you Aliyu, xaka sha mamaki wllh, lastly ina son ku bar min gidana yau, enough is enough, tashi ka fita" mikewa yyi yace "Nagode Abba" daga haka ya juya ya fita parlon, ko da ya shiga bedroom din Mami, samun Hajiya Mariya yyi tana ta hada kayan babies, ya xauna gefen gado ta dawo kusa da shi tace "Me suka ce" d'an murmushi yyi ya gaya mata ynda suka yi da Yakumbo da Abba ta tabe baki tace "Toh kar ka kuskura ka cuce yar mutane, koma meye gwara kayi a kanka" Dariya yyi yace "Ni in cuce kai na kenan Mum?" Tace "Atoh ni ina ruwana, am very serious don't make her use anything but you can" yace "Uhmn to shkkn Mum" ta mike tana ci gaba da abinda take tace "Gwara da kace masu haka ai, ita kuma sai in ga nonon da xata ba yaran" dariya yyi ya nufi kofa tace "Ku shirya ynxu Aliyu" yace "Toh mum" daga haka ya fita.

*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫

By khaleesat Haiydar📚✍🏻

99___100

Bedroom dinsa ya shiga ya tadda Noor kwance, yyi mata kallo daya ya dauke kai ya nufi gun kayansa, cikin kankanin lkci ya gama hada abinda xai hada ba tare da ya kalleta ba ya nufi kofa ya fita, dakin mami ya shiga Hajiya Mariya tace "Har kun gama?" Yace "Ehh" ya kalli Mami dake kallonsa ya xauna gefenta yace "Ki yi hakuri Mami, everything will come to past by the grace of God, i knw i have made u pass through so many pains, ki yafe min Mami don Allah" bata iya tace "Komai" Hajiya Mariya tace "Allah ma albarka" a hankali yace "Ameen" har lkcn idonsa na kan Mami, cikin sanyin murya tace "It's nothing Abuu, watarana sae lbri" rungumeta yyi ya lumshe ido yace "Nagode Mami" ko da suka fito dakin Hajiya Mariya na janye da babban trolleyn da ta tula kayan yara da na Noor tace "Ce mata ta fito son, u help her with the boys" yace "Mum i dnt knw hw she will feel idan ta ji xa a raba su da yaran da ki shiga ki mata mgna" Hajiya Mariya ta tabe baki tace "Duk fa baraxana ce, ya xata yi da 'ya yan mutane har biyu" murmushi yyi yace "Toh mu ma sai mu yi baraxanan bata su mu ga ko xata karba" Hajiya Mariya ta sake trolleyn ta shiga dakin, ganin Noor kwance tace "Baki shirya ba Daughter?" Mikewa xaune tayi tana kallonta, Hajiya Mariya ta dau Ahmad ta fita da shi ta mika ma Abuturrab snn ta dawo ta dau dayan tace "Kafin in dawo ki hada abinda xa ki hada kin ji, xa mu je can gida na ne" sosai Noor taji ddin hakan a ranta don ji tayi bata son xaman gidan kwata kwata, Abuturrab na rike da duk yaran ya shiga parlon Abbansa da sallama, gun Yakumbo ya nufa ya mika mata su yace "Ga su Umma, xa mu tafi ne." Ta yo waje da ido tace "Ina?" Yace "Duk inda Allah yyi!" Tace "Guduwan xaka sake yi knn" ya girgixa kai yace "Abba ne yace mu tafi" tabe baki tayi tace "Munafuki dama can kana da niyyar yin hakan ne, bnda hka ta yaya daga magana xaka kwaso min 'ya ya kace xaku tafi, anya kana son rabuwa da mu lfya kuwa Aliyu?" Yace "Ba haka bne Umma, bna son bacin ran Abba shi yasa xa mu tafi ynxu" tace "Ka ji salu6abbe, yo bacin rai na nawa, duk wa enda ka sa shi a baya ce maka aka yi ya warke a xuciyarsa ne, to ni ba wnn ba, ynxu da ka kwaso min yara ya xan yi da su?" Yace "Umarnin ki fa na bi Umma" kallon Abba da bai ko kalli inda suke ba tayi tace "Ahmad kana jin gantalallen d'anka koh? Ka tambayar min shi ya xan yi da su, nono garen da xan basu ko yaya" Abba yace "Ki barsa ya tafi da su kawai Yaya, lkcn da xai yi auren ma ba shawara yyi da mu ba bare har a damu da 'ya yansa, sai dai idan suka xama abinda kike gujen masa bbu shegen da xai ce jikokin Col Ahmad ne" Yakumbo tace "Atoh, su je kawai, amma fa da sun shekara xan bi sa duk inda suke in kwaso su" Col bai kuma cewa komai ba, a hankali Abuturrab yace "Am... am sorry dad, forgive me plss" kofa Col ya nuna masa alamar ya fita, ya juya ba musu ya fita dakin a sanyaye. Dariya Hajiya Mariya tayi ganin ya dawo da yaran tace "Sun hakura knn" Mami ta raka su har mota, tana tsaye har sai da suka bar gidan, Abuturrab ke driving din, Hajiya Mariya da Noor na rike da yaran a baya, har suka isa gidan Hajiya Mariya bbu wanda yace komai cikinsu, yyi horn mai gadi ya bude gate ya shiga yyi parking snn ya bude motar ya fito ya bude side din Hajiya Mariya ta fito Noor ma ta fito, yaron hannun Smll mum din tasa xae karba tace "A'a karbi na hannunta" bai ce komai ba, bai kuma kalli Noor ba ya koma bayan booth ya bude ya ciro kayansu ta bi sa da kallon gefen ido, ganin Hajiya Mariya tayi hanyar shiga gidan ta bi bayanta, a parlor ta xauna tana kallon Ahmad dake hannunta, Hajiya Mariya kuma ta wuce daki, a hankali Noor ta dago kanta suka hada ido da shi don yana xaune parlorn shi ma, shi ya dauke kansa, can ya mike ya bi bayan mum dinsa, ba a dau lkci ba Hajiya Mariya ta fito ta karbi yaron hannun Noor tace "Taso mu shiga ciki" Noor ta mike ta bi ta suka shiga bedroom dinta, Kan gado Hajiya Mariya ta nuna mata tace "You feel at home kin ji daughter, ina xuwa in daura girki Hauwa bata iso ba" daga haka ta fita dakin, Abuturrab ya mike ya fita shi ma, kitchen ya bi small mum dinsa yace "Mum xan wuce can gidan ina son in huta ne" tace "Wani gidan?" Yace "Mine" tace "Kafi son can kenan" d'an murmushi yyi yace "Mum it's nothing ae" tace "Toh shknn, amma me yasa baxa ka huta nn ba sai anjima ka wuce" yace "A'a ynxu nake son wucewa" tace "Toh abinci fa?" Yace "am full mum, sai dai gobe idan na xo" tace "Kun yi sallama da ita?" Yace "Ehh mun yi" tace "Toh Allah ya tsare, kayi addu'a kafin ka fita" yace "In sha Allah mum" daga haka ya juya ya bar kitchen din yyi wucewarsa. Washegari misalin goma na safe Abuturrab ya xo gidan Hajiya Mariya, suna daki gaba daya, tana yi ma Noor kitso don ko da suna bata yrda an mata kitson ba ynxun ma lallaba ta tayi ta yrda take mata sai yatsine fuska take, Hauwa mai aikin Hajiya Mariya kuma tana rike da Ahmad tana basa ruwa a feeder d'an uwansa kuma na kwance, Hajiya Mariya ta amsa gaisuwar Abuturrab tace "Sai yanxu Son" yace "Muna tare da Mujaheed ya dawo jiya" kallon Hauwa dake gaishesa yyi ya amsa gaisuwar snn ya dau Abubakar dake kwance yace "Frnd, good morning" Hajiya Mariya tace "Lallai kam frnd, frnd me hana mutane bacci da daddare, kaga Sadeeq din nn fitinanne ne na karshe" yyi dariya yace "Abokin nawa, to Abbana fa" ta kalli Ahmad tace "Shi kuma d'an taya bera 6ari ne, da yaji ya fara shi ma sai ya cafke" kallon Noor da ta sake ma kai tuntuni tayi tace "Ba ku gaisa ba Samha" Noor ta d'an kallesa tace "Ina kwana" a takaice yace "Lafiya lau mum twins" mikewa yyi yace "Na gaishe ku mum, xan je gidan boss dina ne ynxu" tace "Wai Dr Mustapha" yace "Ehh" tace "Har ya gaji da tambayar ka ya bari, xaka ci gaba da aiki a clinic din nasa knn" yace "Sae idan akwai vacancy mum" tace "Ae ko bbu na tabbata xai bari ka ci gaba, yana sonka mutumin" d'an murmushi Abuturrab yyi, yyi mata sallama ya fita. Haka Noor ta ci gaba da rayuwa da yaranta gidan Hajiya Mariya dake basu kulawa yanda ya kamata, ba ita kadai ba har mai gidanta na mugun son Arshaq da Ashraf sunan da Hajiya Mariya take kiransu da shi daga baya, yaran suka yi girma tun kan arbai'n din, sai rigima da tayi masu yawa, gasu kamar larabawa don kyau hakan yasa duk wanda ya gansu sae ya shiga ransa, ynxu kam mai aikin Hajiya Mariya bata da aiki sae na rainon yaran tsabar yanda take sonsu, ko da yaushe suna wajenta, duk da irin nutsuwar da Noor ta samu a gidan don tayi kyau ta kara haske amma bata da kwanciyar hankali don har lkcn gaisuwa kadai ke hadata da Aliyu, kuma sau daya yake xuwa wataran ma baxae xo ba don ya fara aiki a gun aikinsa na da, ita kanta small mum dinsa na lura da take takensa sai dai bata ce masa komai ba tukun, da ya xo duk awannin da xae yi a gidan yana tare da yaransa ne, Noor kam tsakaninsu gaisuwa, abun ya fara damun Noor ssai, sae dai bata iya nunawa, ranan Hajiya Mariya ta kirasa daki ta tambayesa ma'anar behavior dinsa, yyi murmushi yana shafa kai yace "Mum haka take min ita ma" Tace "Kamar ya?" Yace "Ko da yaushe share ni take ta mayar da shi habit dinta ynxu" Hajiya Mariya tace "Haba Aliyu sae kace baka fi ta hankali ba, ynxu sai ka biye mata kamar wani mara tunani" yace "No mum, am just giving her space ne, naga kamar haushi na take ji" tace "Kasan me yasa take maka haka" kallonta yyi bai ce komai ba, tace "Gani xata yi kai ga ka tare da yan uwanka ko wanne na ji da kai, to ita fa, bata da kowa nata kusa da ita ga irin uwar da Allah ya hada ta da, she will always feel dejected idan ta tuna haka" bai ce komai ba, tace "To gaskiya bna son wnn shashancin gashi naga hakan na damunta sosai, ka dinga mata adalci Aliyu" yace "To nima ta dinga min, har ynxu idan abu bai min dai dai ba sai naji xuciyata na min xafi sosai mum, nima ba a son raina nake mata haka ba, but i have no option taki kwantar da hankalinta kuma ba komai ke damunta ba illa kishi ita bata ki kar in sake ma ko wace mace magana ba in dawo muyi ta xama bana xuwa ko ina" dariya Hajiya Mariya tayi tace "How will dat be possible kuma" Sau biyu Mami na xuwa gidan da su ilham ganin Arshaq da Ashraf, ana gobe Noor xa su yi arba'in Abuturrab na gidan tun yamma har bayan isha sbda ruwan da ake, Hajiya Mariya tace "You spend the nyt here sbda ruwa Aliyu" yace "Yea am thinking of that" Noor na daki kwance wajen karfe goma da rabi, har tayi shirin bacci Hajiya Mariya ta shigo mata da yara ta kwantar kusa da ita tace "Baxa ki sha furan ba kuma Samha" tace "Na koshi Mum" Hajiya Mariya tace "Toh shknn sai da safe" daga haka ta fita, Noor ta d'an yi mamaki don in har mai gidanta bai gidan ta kan kwana da su, Hauwa kuma ta wuce gida, ranan da yake nn kuma Hauwa ce ke tsayawa ta kwana da su, bude kofar dakin aka yi ta dago kai, tayi mamakin ganinsa don bata san yana nn ba har lkcn, ya rufe kofar ya karaso cikin dakin har xai kunna Ac ya tuna da yaran dake kwance ya rage kayan jikinsa kawai ya kashe wutan dakin ya nufi kan gadon ya kwanta, turo baki tayi ta mike xaune ta dau Arshaq ta sa shi a tsakiyarsu, ta dauko Ashraf shima ta ajiyesa duk yana kallonta ta koma can karshen gado ta juya masu baya, daukan yaran yyi gaba daya ya ajiye su can gefensa ya dawo kusa da ita, ta mike xaune tana kallonsa, tashi xaune yyi shi ma xata sauka kan gadon ya fixgota, fadawa jikinsa tayi ta fashe da kuka yace "Na rashin gaskiya koh?" A hankali take kukan bata ce komai ba, can yaji a hankali tace "Am sorry...." ya dago kanta yace "For?" Kin cewa komai tayi ta mayar da kanta kirjinsa, ya lumshe ido yana murmushi yace "Sorry for ur new habit baby, in dai kika kashe ni shknn sai kiyi ta rainan yaran ki ke kadai" kuka ta fara yi sosai, ya kai bakinsa kunnenta yace "Alryt baxan mutu ba sai kin haifa min yara shidda koh?" Abbansa ne ya fado masa ya lumshe ido, ita kam gyada masa kai tayi yace "Alryt, tel me u love me" murya can kasa tace "It's nt worth sayin....." bata rufe baki ba ya fara kissing din ta, Nan ita ma ta nuna masa tayi kewarsa fiye da yanda yyi, washegari da sassafe Abuturrab ya bar gidan tun kan Small mum dinsa ta fito, ita kanta Noor bata san ya wuce ba don tunda tayi sllh ta koma bacci, karfe sha daya Hajiya Mariya ta kirasa da yake ranan lahadi ce sai ga shi ya taho, a daki ya sameta bayan sun gaisa tace "Kaga yau suka yi 40 days son, ya kamata ku koma can gidan tare, before then kuma lefen da baka yi mata ba sai kayi xa su koma" dariya yyi yace "Kai mum" tace "Yes in raka ka kasuwan, kuma miye na wucewa da asuba" ya d'an shafa kai yace "Ba komai mum" mikewa tayi tace "Toh ni dai bari in shirya mu je kasuwan ynxu" fita yyi ya shiga dakin da Noor take ya sameta xaune tana ta wasa da yaranta, xaunawa yyi kusa da ita yace "Tom kin gama da su, it's now my time" hararansa tayi tace "Ni bn gama da su ba" rungumota yyi yace "Ashe kema kin yi missing dina baby?" Ta rufe ido bata ce komai ba tana murmushi tana shakan kamshinsa me ddi, murya can kasa yace "yesterday was great...." Bude kofar dakin Hajiya Mariya tayi, Noor ta janye jikinta da sauri, yi tayi kmr bata gansu ba tace "Ina jiranka ne Aliyu" ya mike da sauri yace "Okay mum" tana fita yayi kissing dinta a lips yace "Sai mun dawo baby" bin sa tayi da ido don ba karamin kyau kananun kayan jikinsa suka yi masa ba, yana fita Hauwa ta shigo dakin. Abuturrab ya langwabar da kansa bayan sun isa Atm yace "Mum kudin account dina is nt up to 500k fa, kuma...." Tace "Baka da damuwa sai in ranta maka idan ka samu ka mayar min da kayana" dariya yyi yace "Kai mum" tace "Ehh, xan dai bada tawa gudunmawar kayan jewelries" yace "Toh nagode mum" dubu dari biyu da hamsin kawai ya ciro a account dinsa, ita ma ta cire kudi me yawa bata dai gaya masa ko nawa bne suka shiga kasuwa, akwatuna masu kyau na xamani ta fara sa suka siya set guda, daga nn kuma suka shiga shagunan atamfofi ta siya manyan atamfa guda sha biyar snn ta siya masu d'an saukin kudi guda goma, ta siya lace masu tsada biyar, sai materials da abaya kala kala, mayafai, hijab, jakunkuna, takalma, kayan shafe shafe, turare, sabulai, kai duk abinda tasan ana xubawa a lefe har da su pray mat, alqur'an da carbi, sae jewelries da ta bata lkci wajen xabansu, Abuturrab dake xaune sai kallon ikon Allah yake yace "Mum kashe ni kike son yi kawai" kallonsa tayi tace "Wato ga yarinya ka samu a bnxa koh" dariya yyi yace "Wayyo mum a dai tausaya min, ni fa ne naki" tace "A'a mamar ka na can inda ka baro ta, wnn ce tawa a ynxu" ba su suka bar kasuwan ba sai kusan la'asar, sae da ta tabbatar bbu abinda ya rage bata siya ma Noor ba uwa ynxu xa ayi auren, sai da suka isa gida ta juya tana kallonsa tace "Kudin da xaka ban nayi lissafi 450k bnda kudin jewelries" xaro ido yyi yana kallonta, bata kuma kallon inda yake ba ta fita motar, ta kira mai gadi ya taimaka mata shiga da kaya ciki, Abuturrab ya fito motar yana murmushi a xuciyarsa yace "Lallai mum" Noor bata iya tace ma Hajiya Mariya dake ta nuna mata kayan tana jera su a akwati komai ba, duk jikinta yyi sanyi wanda hakan yasa bata san lkcn da hawaye ya shiga sakko mata ba, jin shirunta yyi yawa Hajiya Mariya ta dago tana kallonta, ganin kuka take tace "Ikon Allah, kuka kuma Samha" dawowa tayi kusa da ita tace "Kukan me kike daughter" rungumeta Noor tayi cikin muryar kuka tace "I love you mum, nagode Allah kara maki tsawon kwana" Hajiya Mariya tayi murmushi tace "Toh Amin my daughter, you take me as ur mother kin ji" karfe biyar da wani abu Hajiya Mariya tayi mata duk abinda tasan ya dace dai na gyaran jiki, ta kira mijinta ta rokesa alfarmar siya masu foodstuffs, ba a dau lkci ba driver ya shigo da buhun shinkafa biyu, carton din taliya uku, jarkan man gyada da manja manya, maggi, gishiri har da kwalayen indomie biyu, Abuturrab na shigowa tace "Toh ga gara nn Alhaji yyi mata nasan har ku bar duniya baxa ka mata gorin hakan ba wataran tunda ku din ba tabbas ne da ku ba, kayan daki kuma in shaa Allah idan kudi ya shigo min xan siya mata nata" dariya yyi sosai yace "Mum you are making me feel ashame, haba my mum" bata sauraresa ba ta kara gaba abunta, bayan magrib Hajiya Mariya ta rakasu can gidan nasu da aka yi furnishing tuni, duplex ne mai kyau da parlor sama da kasa sai dakuna huda ko wanne da bathroom, sannan babban kitchen, xa a iya cewa col ne ya gina masa gidan don kudinsa ba mai yawa bane a ginin gidan, Da yake abban nasa yasan halinsa shi yasa bai yrda ya tare gidan ba da dadewa sai masu gadi har uku dake rayuwa

Please Login or Register in order to submit comment