Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da xuwa Yakumbo, ba mahaukaciya bace, xuwa tayi ta tafi da yaran wai" Yakumbo ta d'an yo waje da ido tace "Ta tafi da su? Ina xata kai su" karasowa parlon tayi tana kallon Mami da ta kasa daina hawaye ta kuma kallon Hajiya Mariya tace "Ke wai me ke faruwa, Aliyun sake gudu yyi?" Bata rufe baki ba ta gansa tsaye kansa a kasa yana rungume da hannunsa, ta tafe hannu hade da kyabe baki tace "Ikon Allah, Ka gaji da guje gujen ka dawo kenan, ae dama duk wawan da ya bar gida da kafarsa to fa da kafafuwar nn xae dawo in da rai da lafiya, ni ba dan naka naka bane da na ja maka Allah ya isa a kan wahalhalun da ka saka k'anina Aliyu, uwar ka kam dama bakin ku daya da figaggiyar kanwarta...." Daga haka ta ja tsaki tace "Na xo ne dama ayi ta ta kare ina Ahmad din..." Daga haka ta dau hanyar stairs, Rachael na fita gate Mr David ya fito daga mota da sauri yana kallonta da mamaki yace "Rachael meye haka, ina xa ki kai yaran?" Wani kallo ta jefa masa tace "Ina xan kai su kamar yaya? Ba jikokina bane" bude bayan motar tayi ta shiga, ya girgixa kai yace "Kina da hankali kuwa Rachael, kan ki daya kuwa? Ina xaki da yaran mutane" fitowa tayi daga motar tace "You're wasting my time David" daga haka ta k'ara ma sayyadarta mai ta dau hanyar gida uwa xata tashi sama, ya dafe kai yace "My God!" Yakumbo na shiga parlon Col ta gansa xaune da laptop, ya mike ganinta yana murmushi yace "Sannu da xuwa yaya" tace "Sannu Ahmad, na same ku lafiya" yace "Lafiya lau, ashe kin taho baki yi waya ba" tace "Kaga ma ni na mance wayar a gida ban da yanxu da kayi magana" xaunawa tayi tace "Ya muka ji da wannan bakar masifar, wai Aliyu ya dawo da yara, anya Ahmad baka yi masa baki ba kuwa" Col ya girgixa kai yana murmushi yace "ko daya" tace "To ita kiristar tana ina?" Col yace "Tana gidan, yanxu uwarta ta xo ta kwashi yaran ma" Yakumbo tace "Wasu yaran kuma?" Col yace "Yaran dai, baki gansu tsatstsaye parlor ba" mikewa Yakumbo tayi tace "Xata ina da su? tare da uwar yaran ta tafi?" Col yace "Xata raine su mana, ba yar ta bace ta haife su, Uwar yaran na nn parlor...." Yakumbo tace "Ban gane xata raine su ba?" Col yyi yar dariya yace "Ae fa tana da gaskiya yaya, jikokinta ne ai" ta rike kugu ta saki baki tana kallonsa, can tace "Ae ni dama tun ba yau ba nasan kai mugu ne Ahmad, wllh kai mugu ne, to muguntar taka ta sojoji sai ya kare a kan mu? ta kwashe min jikoki ka bar ta ta fita? Toh Allah ya fika" Bata jira cewarsa ba ta fice parlorn ta dawo kasa, tana kallonsu Hajiya Mariya da har lkcn suka kasa xaune, Noor kuma sai rusa kuka take, a fusace tace "Amma ku dai anyi gayyar yu yu yu, yanxu duk yawan ku a parlorn nn ku ka bar figaggiyar mata ta fice da 'ya ya har biyu?" Hajiya Mariya tace "A'a Col ne yasa ta fita da su, shi ya hanamu aikata komai wllh" a mugun fusace Yakumbo tace "Yo dama sai ku kula wnn da ya baro hankalinsa gaba daya a yak'in biafra?" Hajiya Mariya ta tabe baki tace "To ina mu ina ja da shi yaya?" Yakumbo tayi wani shewa tace "xata san jikokina ta fita da yau, kin dai san gidan koh?" Hajiya Mariya tace "Na sani" Yakumbo tayi kofa da sauri tace "Mu je" Hajiya Mariya ta dau Hijab din ilham ta bi bayanta, tun da suka dau hanya Yakumbo ke bala'i uwa xata tashi sama, col kam ya sha xagi har da na sayarwa, Hajiya Mariya dai sai bin ta take don tana da assurance baxa su fito gidan ba sai tare da yan biyu, suna isa gidansu Noor yakumbo bata saurari mai gadi dake neman sanin wanda suke nema ba ta bangajesa ta shige gate tana cewa "Kaji min mai gadin gidan bala'i" Hajiya Mariya ta bi bayanta, tsaye suka ga Mr David a balcony abun duniya ya ishesa, Yakumbo ta kalli Hajiya Mariya tace "Ita ce wnn" Hajiya Mariya na kkrin danne dariyarta tace "A'a ba ita bace" Yakumbo bata kuma kallonsa ba ta shige parlorn, bbu kowa ciki, Yakumbo ta haura sama Hajiya Mariya na biye da ita, dakuna suka dinga bubbudewa har suka bude wani wanda da alamar na Rachael ne, kwance suka ga yaran duk biyu a kan gado, Rachael na tsaye a press din kayanta xata fiddo xani da xata goya daya, ta rike daya su tafi church, duk a tunaninta David ne ya shigo shi yasa ko kallon inda kofar yake bata yi, Yakumbo ta karasa a hankali ta kinkimi yaro daya tace "Toh Wllh wllh na sake ganin sheggun kafafuwan ki a gidan K'ani na sai na ari bindigarsa na harbe su" A firgice Rachael ta juyo, Hajiya Mariya ta dau daya yaron da sauri, Rachael tace "Jesus Christ me ya kawo ku gidana?" Yakumbo na nuna ta da yatsa tayi mitsi mitsi da ido tace "Abinda ya kai ki gidanmu daxu" Tuni Hajiya Mariya tayi waje da Sadeeq, Rachael ta bi ta da sauri tana cewa "Ki dawo da yaran nn kar a ji mu a police station, ki dawo ki ajiye min jika na...." Yakumbo ta bi bayanta tana cewa "Aji mu a bariki karewar station, kin yi kadan ki shigo har gida ki kwashe ma mutane yara yar banxa kawai, ke kika yi cikin da aka haifesu xaki kawo mana rainin wayo" ai tuni Hajiya Mariya ta fice parlon gidan, Rachael dake ta vibrate ta juyo tana kallon Yakumbo tace "Amma ai 'ya ta ce ta haifesu ba wani ya haifa mata su ba, i swear to God of Jacob baxa ki fitar da yaron nn gidan nn ba yau sai dai duk abinda xai faru ya faru" Yakumbo tayi shewa tace "Dambe xa mu yi knn, to tsaya" cire mayafin kanta tayi ta goya jaririn da ya fara kuka tsabar wujjigasa da take, ta daure sa tamau a baya snn tace "Toh taho" David ya shigo parlon yana kallonsu, a tsawace Yakumbo ta kuma cewa "Ki taho nace ki karbesa, ban da raini har kya je gidan mutane ki kwaso yara, yo ai yar ki ya kamata ki kwasa ba su ba, su da suke gidan Ubansu" David yace "Kiyi hakuri don Allah" wani kallo ta jefa masa tace "Da xata can baka bata hakuri ba sai ni da na xo daukansu xaka ba hakuri" daga haka tayi hanyar kofa tace "Ashe dai karamar hauka ke kanta, nayi xaton sai mun dambatu xan bar gidan" ko rufe masu kofar bata yi ba ta kara gaba abunta, Rachael ta fashe da kuka tana kallon David yace "Serves you right" daga haka shi ma ya bar mata parlorn, yakumbo ta dinga masifa ita kadai a hanya ga yaro sai tsala kuka yake a bayan ta, ta kai masa duka a baya tace "Kai don mahaifinka rufe min baki kar in ajiye ka a nan inyi wucewata, baka gode Allah naje na amso ku a hannun kafura ba, in dan ta kakan ka ne ai sai dai kayi ta xama a gidan, mata yar banxa kawai ta xo ta kwashe ku, ita Hajarah ta tsaya tana kukan makirci ta kasa kullala komai" Hajiya Mariya na shigowa parlor Hajiya Rahina tace "Alhmdllh, har naji sanyi, amma wnn fitina da me yyi kama" Ummi ta sauke ajiyar xuciya tace "Allah ya kyauta" Mami kam kasa cewa komai tayi, Hajiya Mariya na bude yaron da ta lullube da xani sbda sanyin waje sai da tayi shock ganin Rosary a wuyarsa, bakinta a leko ta cire ta ajiye a kasa, sai ga Yakumbo ta shigo goye da Abbakar dake tsala kuka, sauke sa tayi tace "Da alama yaran nn yafi son can ne, bnda munafurci muna baro gidan ya dingi tsala min ihu har na iso nn, to tsaye xa mu yi a kansa don abun kunya daya ya ishe mu ba sai an mana k'ari ba" salati ta xabga bayan ta saukesa tace "Mayya, har ta rataya masu sarkan coci a wuya" sai kuma ta fashe da kuka tace "Duk Ahmad ne ya ja maku, bbu dole sai Aliyu ya tattara ya bar gidan tunda tun yanxu ya fara nuna masa bai son 'ya yansa, to ni idan ban so 'ya yan Aliyu ba 'ya 'yan wa xan so, dubi fa yaran kyawawa da su kamar larabawa..." Mami ta mike ta bar parlon, Yakumbo ta cire Rosary din ta jefar tace "Allah ya raya min ku a tafarkin islama, yasa ku xama manyan malaman islama irinsu Isma'il Mufti Menk a can waje da kuma fantami a nan Nigeria" murmushi Ummi tayi tace "Ameen" Yakumbo ta nufi sama tana cewa "Kuma Allah ya raba ku da hali irin na Aliyu, kwakwalwarsa kawai nake son ku dauko" parlon Col ta shiga tace "Toh naje na karbo su Ahmad, gari na wayewa kuma xa su bar maka gidan ka tunda ba son su kke ba, kai da ganinsu kuma kila sai dai girmansu" tana magana ne hawaye cike idonta.

*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫

By khaleesat Haiydar📚✍🏻

97.....

Hajiya Mariya ta kwankwasa kofar dakin Abuturrab dake xaune tare da Noor a dakin yyi lallashin har ya gaji ya xauna yana kallonta shi dai yasan sai in Yakumbo bata je gidan ba amma ko da tsiya sai ta dawo tare da yaran, mikewa yyi ya bude kofar yaga Hajiya Mariya tsaye da Sadeeq hannunta ta mika masa shi tace "Bata yaron ta" d'an murmushi yyi ya karbi yaron bai dai tambayeta d'an uwansa ba ya juya ya koma dakin, ajiye ma Noor yyi a jikinta, ta kallesa tace "Dayan fa?" Yace "Yana gun su" cikin rawar murya tace "Kila baya wajen su" Dago kanta yyi yana kallon kwayar idonta, can ya langwabar da kai yace "Baby shknn yanxu duk son da kike min kin kwashe kin mayar kan twins, to ni meye tawa makomar, naga kamar ta babies kadai kike yi ynxu" dauke kanta tayi bata ce komai ba, aka bubbuga kofar dakin ya mike yace "Toh ga shi nn shima an kawo maki" bude kofar yyi yaga yakumbo ce ta shigo dakin rike da Abubakar ta kwantar da shi tace "Aliyu, toh dai a ynxu Ahmad bai da babban makiya kamar wa ennan 'ya yan naka, idan xaka ji ta nawa ka tattara ina ka ina ka, suma ka tattara masu ina su ina su ku bar masa gidan sa, ranan da Allah yasa suka girma sai su tako da kansu su xo su gaishesa, ni ba ma wnn ba, gani nake kamar bak'in cikin rahamar Allah yake masu, to banda haka ta ya xai bar mata me xuwa coci ta shigo masa har gida ta kwashe su ta tafi dasu, kasan matar har ta rataya masu sarkan coci fa a wuya Aliyu" Noor dai sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsunta, shi kam Abuturrab bai iya yace komai ba sai kallonta yake, Yakumbo ta tabe baki tace "Toh dai Allah yyi mana tsari kwashi yaran ka ka bar masa gidansa da wuri wuri, yara maa sha Allah haka" kallon Noor tayi tace "Ke kam kinyi sa'ar uwa, toh ke ma har yanxu kina xuwa cocin kenan koh?" Abuturrab yace "A'a ita musulma ce..." Ta d'an yo waje da ido tace "Tohhh ta musulunta knn, amma dai da xa ka ji ta nawa ka samu yar uwarka musulma warce xata sa ta da 'ya yanta a hanya ka aura kwanan nn..." Sai a snn Noor ta dago manyan idonta tana kallonta, Yakumbo tace "Atoh, ni bayin Allah nake ji ma kar wataran ta mayar da su ruwa, ita ma ai tasan irin musuluntar da suke yi, bari in samu Hajarah in ji ynda xa ayi" daga haka ta fice daga dakin tana cewa "Mu muka ga kaddara, mun kuma gode Allah da ya ba mu ikon daukarta a ynda ta xo mana amma dole ya kara aure don daidaituwar gidansa" Abuturrab ya d'an kirkiri murmushi ya kamo hannun Noor ganin mood dinta cikin sanyin murya yace "You are the 1st nd the last in shaa Allah wife, no amount of talks will make me change my mind" ita dai bata ce komai ba sai hawaye da ya sakko idonta, rungumeta yyi ya lumshe ido yace "Believe me mum twins" Yakumbo na fita ta bude dakin su Ramla, Khaleesat da fatima ne a dakin, Khaleesat ta taso ta rungumeta tace "Umma yaushe kika xo" Yakumbo tace "Tun daxu fa, sai na tarar an dauke yaran da na xo gani shine na tafi karbo su, wacece wancan kuma" Fatima ta ajiye wayar hannunta tace "Ina yini" Yakumbo tace "Lfya lau" Khaleesat tace "Bakuwa ce Umma" Yakumbo tace "Ayyo, sannun ki toh" daga haka ta yi gaba, dakin Mami ta shiga, ta kalli su Ummi dake xaxxaune dakin da Hajiya Mariya tace "Toh dai Hajarah mijin ki ya nuna baro baro bai son xaman Aliyu gidan nn tunda har ya fara barin kafura na kwashe yara, don haka nace Aliyu ya lallaba ya bar gidan ko ko ya kika ga?" Hajiya Mariya tace "Gaskiya ne yaya, kuma tun da har taji ddin shigowa gidan gobe ma sai ta iya xuwa tace xata dauke su" Yakumbo tace "Wayyoo Allah Mariya, ke da kika san komai...." Xaunawa Yakumbo tayi tace "Abu na biyu kuma, Hajarah cewa nayi ya kamata Aliyu ya kara aure kwanan nn, ya auri musulma yar uwarsa warce xata sa ma 'ya yansa ido, Allah na tuba tubabbiya bbu wani tarbiyar arxiki da xata iya ba ma yaran nn biyu abun tausayi" tun da ta fara Hajiya Mariya da su Ummi ke kallonta, ta ci gaba "Shine nace in fara shawara da ke kafin in koma gun Ahmad, ko ya kika ga, ita wnn din ba wai ba ma sonta bane, a'a kawai jikokinmu muke ji ma, gwara ya auro cikakkiyar musulma yar uwarsa ta xo su hadu a ba yaran tarbiya, to ni da nake son su xama manyan malamai ma...." Mami tace "Toh, idan hakan ne mafi alkhairi Allah ya tabbatar...." Mikewa Hajiya Mariya tayi a fusace tace "Amma yaya baki kyauta ba in har kika fadi hakan gaskiya" Yakumbo ta yo waje da ido tace "Bata kyauta ba? Shi addu'ar da tayi ne bata kyauta ba Mariya?" juyawa Hajiya Mariya tayi ta fice daga dakin, Yakumbo tace "Ji sha sha sha kamar ba da ita muka je muka yi cacan baki aka bamu yara ba, Mariya fa ba cikakken hankali ke gareta ba, ko don bata san xafin haihuwar bane oho, banda haka yaya ana nema ma yaro abun alkhairi ta hayyako mana haka, so take 'ya yan sa su tashi bbu addini ne ko yaya, ai ni Aliyu ya gama cutar mu" Hajiya Rahina tace "Ae kam maganar ki na kan hanya Hajiya, uwa fa ke ba yara tarbiya ba uba ba...." Ummi ta katse ta tace "Amma ita ma ba jahila bace totally a islam kakanta musulmi ne, haka kuma kanwar mahaifinta, baka taba cewa ba musulma bace ita idan ba kun xauna tare bane" Mami tace "Ae ba don a walakantata ba Yakumbo ta fadi haka" Yakumbo tace "Atoh fada masu dai, kin san idan jika ba naka bane" daga haka ta fice daga dakin tana cewa "K'arin Auren Aliyu ba fashi wllh" Hajiya Mariya da ranta ya gama baci ta sauka kitchen ta ci gaba da taya Anty Maryam gyare gyaren da take da yaran frnds din Mami. Mami tayi murmushi tace "Shknn kinga sai a hada su da fatima Hajiya" Ummi tace "Wace fatiman?" Mami tace "daughter nah mana" Ummi ta girgixa kai tace "Allah ya kiyaye, Aliyu da matarsa sun wuce haka a gu na" Mami tace "Kamar ya Allah ya kiyaye, Hajiya idan kika duba maganan da Yakumbo tayi xa ki ga gaskiya take fadi wllh, ni ba wai bana son matar nn tasa bace kawai dai makomar yaran nake jimami, kinga shi kansa Aliyun ban da yyi sllh kan lkci sai kauce ma sa6o bbu abinda yake na addininsa, Idan ba kwanan nn da naga Aliyu ya fara tsayuwar dare ba shi ba gwanin yin hakan bane, Azkar idan yyi na safe a da can toh bbu xancen na yamma, Karatun qur'aninsa ganin dama ne, to ina gida a nn don Allah, me xata gani a gunsa da har xata yi koyi da shi ita matar? Amma kinga idan ya aure wata daban sai ta sa su kan hanya gaba daya" Ummi ta tabe baki tace "Toh Allah ya basa wata daban din" Mami tayi murmushi tace "Fatima ce ba wata daban ba" Ummi tace "Ita Fatimar ca aka maki rike take da addini banda sllh da take?" Dariya Hajiya Rahina tayi, Ummi tace "Atoh, barin yaran ynxu da bnda kishin hauka da bala'i bbu abinda suka sa gaba, ke a tunaninki xa ki nemo mai addini ki hada su amma karshensa xamar kishiya xata yi da ita ayi ta kishin hauka mara amfani, am nt in support of this gaskya Mum Aliyu, ita kuma sai aka ce a haka xata yi ta xama baxa ta nemi ilimin sabon addinin nata ba, ina ce a nan su Hajiyar Shagari qtrs take gaya mana tayi converting a gun su.... Ayi mata adalci, da rashin yan uwanta xata dinga ji ko kuma da kishiyar da ake shirin laka6a mata, bata da kowa da tafi kusanci da a yanxu ban da mu, kar a canxa mata view dinta a kan islam, in her case yi mata kishiya is totally out of the point, snn kun san duk namiji idan ya kara aure irin rawan kan da yake, Aliyu won't be exceptional, ko da kuwa ya nuna baya so to fa wataran xai so ne, For the sake of her conversion a cire maganan kishiya pls, ko da xai yi ya bari sai sun dade tare idan da rai da lafiya ta cika masa gida da 'ya ya...." Hajiya Amina dake ta jin su ta sauke ajiyar xuciya tace "Haka ne Hajiya you have a point, yakumbo tayi hakuri da wnn xancen, ke Mami ki nuna baki amince ba kawai" Mami bata ce komai, Ummi ta mike ta fita daga dakin, Ko da yakumbo ta kai ma Col xancen karin auren Abuturrab shiru yyi yana saurarenta, can ya gyada kai bayan ta kai aya yace "Kina da point a nan yaya"

*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫

By khaleesat Haiydar📚✍🏻

98.....

Washegari da sassafe Ummi ta gama shirinta ta sa fatima ma ta shirya ta dau jaka tana kallon Mami tace "Toh Hajiya xa mu koma garin mu sae mun yi waya, Allah ya raya Ahmad da Abbakar" Mami tayi murmushi tace "Irin wnn sammako haka, ko duk maganar jiya ce" Ummi tace "Haba ko daya, ina son isa da wuri ne don inje clinic" Mami ta mike tace "Toh shknn Hajiya, mun gode kwarai Allah ya kara dankon xumunci" Ummi tace "Ameen" Naman suna me yawa Mami ta tula mata da drinks sai snacks tace ta kai ma su Rabi'a, A parlor Ummi tasa aka kira mata Abuturrab, ya sakko ganinta yace "Mami har xaku wuce da safe haka" tace "Eh ina son mu isa da wuri ne, sai ka turo babban mota a kwashe maku kayan ku na can ko boy" ya d'an shafa kai yace "Toh Mami, bari in kirata ku yi sallama" tace "A'a bar ta kace mata mun tafi kawai," a hankali yace "Toh ina xuwa Mami" daga haka ya tafi daki ya dauko makullin motarsa don ta taho masa da motar tasa daga can gombe, tare da Hajiya Mariya suka tafi kai su park, ya ba Fatima dubu ashirin taki karba, dole Hajiya Mariya ta tilastata ta karba tace ta gode, yana kallon Ummi yace "Nagode Mamina sai mun xo kawo maki xiyara in sha Allah, ki gayar min da kanwata khadija" tace "Toh ina xuba ido boy, ga dai Samha nan amana, idan ka ci amana kuma kai ma kasan sauran Aliyu, Allah raya maka boys dinka a tafarkin islam" cikin sanyin murya yace "Ameen Mami" tace "One more thing Aliyu, you re educated, you knw what's right from wrong... This is all i have to tell you ka xama me aiki da hankalin ka" daga haka ta shiga mota ta ce "Toh Hajiya Mariya sai mun yi waya, Allahu ya bar xumuncin mu" basu tafi ba sai da suka ga motar ya tashi snn suka dau hanyar gida, Abuturrab na driving ya kalli Hajiya Mariya da har lkcn bata da walwala yace "Mum wani abu ya faru ne, ur mood isn't encouraging" sai a snn ta kallesa tace "Tunda wnn fitinannar Uwar taka ta xo meye ma baxai faru ba, mata bata da aiki sai hada fitina, kaga xan kira Alhaji, (wato mijinta knn) in nema maka alfarma ya baka gidansa daya dake hotoro ku koma can da xama a yau Aliyu.... Yayar babanka ba da alkhairi ta xo ba gaskiya, naga kuma kamar Mami na neman biye mata ne" Abuturrab ya d'an yi shiru, sai can yace "Cewa take sai na kara aure koh?" Hajiya Mariya tace "Ta gaya maka kenan?" Gyada kai yyi yace "Eh, ta fadi hakan gaban Samha ma" Hajiya Mariya ta girgixa kai tace "Muna komawa gida ynxu ku fara shiri, dama Col ba son xamanka yake a gidan ba naga alama, ku koma hotoro kawai, but before then xaka bar su a gidana su yi arba'in" yace "Mum to gidana fa?" Tace "Aa bn san col ya san inda kake ma" Bai kuma cewa komai ba har suka isa gida, yana biye da ita a baya suka shiga parlor, xaunawa yyi a parlorn ya gaida Anty Maryam ta amsa, ya jawo Ihsan yace "Anty amma xaki bar mana ihsan koh" dariya kawai tayi tace "Lallai kam, xuwa anjima xa mu wuce" yace "Da wuri haka Anty" tace "Shekaranjiya na xo ai" yace "Toh Allah kai mu Anty" tace "Ameen" ya mike yana murmushi yace "Da gaske fa Anty xa ki bar min ihsaan" murmushi kawai tayi ya nufi stairs, bedroom dinsa ya shiga, ganin Noor bata dakin ya fito ya shiga dakin Maminsa, Yakumbo ya tarar tana ma Abubakar wanka, Mami na xaune rike da Ahmad, Ya xauna gefen gado yace "Ina kwana Umma" tace "Lafiya lau, sai yanxu?" kallon Mami yyi ita ma ya gaida ta, Ta amsa tace "Har sun wuce" Yace "Eh sun wuce" mikewa yyi ya fita daga dakin ya koma nasa, xama yyi yana tunanin maganganun Hajiya Mariya, can ya sauke ajiyar xuciya ya mike ya shiga bathroom don yin wanka, ko da ya fito daga wanka, xaune ya tadda Noor a can karshen gado a shirye cikin riga da skirt, ga breakfast da aka ajiye mata kan rug, ya ajiye karamar towel din hannunsa ya karasa kusa da ita yace "My wife" bata ce komai ba ya kalli abincin dake kasa yace "Toh sauka ki yi breakfast mana dear" nan ma tayi shiru, ya dago kanta yana kallon kwayar idonta yace "Tell me, wani abu ya faru ne" hawaye ya gani cikin idon, cikin Sanyin murya yace "Wife...." Still bata ce komai ba, a hankali yace "Ni bn san meyasa closeness din mu ya ja baya ba Samha, we were nt like this before, it's getting worst now, baki son amsa ni idan na maki magana, you derive pleasure ignoring me always.... I don't just knw what came over you" mikewa yyi ya dau towel dinsa ya koma can daya side din ya xauna, can ya tashi ya fara shiryawa har ya gama bata dago kanta ba, kofa ya nufa ya fita daga dakin, kuka ta fara a hankali, tayi me isarta snn ta sakko kasa, dai dai shigowar Yakumbo, ta kwantar da yaron hannunta tace "Ynxu 'yar nn barin abincin kika yi ya sandare" girgixa

Please Login or Register in order to submit comment