Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake bbu wani kura cikin few minutes ta gama gyaran ta mayar da komai inda yake ta dawo ta kalli agogo ta ga sha daya ya kusa, one sitter ta xauna ta canxa station xuwa Bollywood, bata yi minti goma tana kallon ba ta jinginar da kanta jikin kujera sai bacci, bude ido Abuturrab yayi ta dalilin wayarsa da ya ji yana ring a bedroom ya mike xaune yana kallonta ganin yanda ta takure kan kujeran tana bacci, mikewa yayi ya karasa kusa da ita ya durkusa, long lashes dinta kawai yake kallo ko kiftawa bbu can ya sauka idonsa kan dogon hancinta kafin d'an karamin bakinta, hannunsa ya daura kan fingers dinta ta bude ido da sauri, ya mike yace "You are not comfortable xo ki kwanta a can" xata yi magana ya kama hannunta ta mike ya nufi kan kujeran da ya tashi daga yasa ta kwanta snn ya wuce bedroom, missed call din Abokinsa Mujaheed ya gani ya shiga kiransa back, bugu uku Jaheed ya daga, daga daya bangaren yace "Ina ka shiga man?" Abuturrab yace "Was having a Nap at the parlor, ya aka yi?" Jaheed yace "Alryt gani tahowa....." Da sauri Abuturrab ya katse sa ta hanyar cewa "Yanxu fa xan fito office ku hadu a can" Jaheed yace "It's urgent....." Abuturrab ya kalli agogo yace "Ni na ma shirya fa, fitowa kawai xan yi" Jaheed ya d'an yi tsaki ya katse wayar, Tabe baki Abuturrab yayi xai shiga toilet ya ji ana danna bell, fitowa yayi da sauri, ga mamakinsa ko motsi Samantha bata yi ba, baccinta kawai take, kofa ya nufa a leka waje yaga Mami tsaye, xaro ido yyi ya juya da sauri ya isa gun Samantha tashinta ya shiga yi ta bude ido a hankali tana kallonsa, sai kuma ta mike xaune tana kalle kalle dai dai lkcn da Mami ta kuma danne bell tace "Abuu?" Mikewa Samantha tayi a tsorace tana kallonsa da kyar tace "Ur Mum?" Bai ce komai ba ya kama hannunta ya wuce bedroom dinsa da ita tana shiga ya rufe kofar snn ya fito ya koma gun Kofar ya bude, sai ka rantse daga bacci ya tashi yanda yyi da fuska, Mami tace "Bacci kake?" Gyada Kai kawai yayi, tace "Ohk sorry, ka xo ku gaisa da Yakumbo ta xo" shiru yyi yana kallonta sai kuma ya hade rai yace "Mami maimakon kice na fita aiki?" Mami tace "Go and freshen up ka fito ku gaisa nace, bana son magana" daga haka ta juya ta bar gun tana kallon karen dake cage abinsa, girgixa kai tayi tayi gaba. Abuturrab yayi tsaki ya juya ya koma bedroom dinsa, durkushe ya ganta bakin kofa ya buda ido yace "Me kike a nan kuma?" Kallonsa tayi bata ce komai ba, yayi murmushi ya nuna mata gefen gado yace "Kiyi xaman ki, or are you afraid, she's gone already?" Mikewa tsaye tayi ta girgixa kai tace "A'a xan wuce gida karfe sha biyu muke dawowa daga lesson din" kallon agogo yayi sai kuma yace "Alryt, me xaki yi a gida yanxu idan kika koma?" Tace "Idan Mumy bata nan xan yi girki, that's all, da yamma kuma in tafi catechism" ya rungume hannayensa yace "Uhn ashe kin iya girki" xaro ido tayi tace "Kai!" Sai kuma tayi murmushi ta dauke kai, yace "Ohk idan ke kika yi girkin ki xubo min xan ci" ta kallesa da sauri tace "Da gaske?" Ya gyada mata Kai, tace "Ohk xan kawo maka" daga haka ta juya tace "Bye na tafi" yace "in raka ki?" Girgixa Kai tayi tace "Noo, thank very much" daga masa hannu tayi ya bi ta da ido har ta fita daga dakin, murmushi yayi ya sauke hannayensa ya shiga toilet, wanka ya kuma yi ya fito ya shirya cikin kananun kaya ya fito xuwa main House, da sallama ya shiga parlon, Yakumbo dake xaune tare da Mami ta bi sa da ido har ya karaso parlon, xaunawa yayi a kasan lallausan carpet din dake malale tsakar parlon ya gaisheta, ta tabe baki tace "Lafiya lau, ya aiki?" Ya shafa kai yace "Alhmdllh" Tace "Wato dai har gobe baxa kayi xumunci ba ko Aliyu, nan nan yayanka ya dawo daga Germany bayan shekaru masu yawa amma ka kasa xuwa inda yake ka gaishesa" Abuturrab ya d'an hade rai yace "Umma na kirasa fa...." Tace "Rufen baki, kira nace ko xuwa can" dauke kai yyi, Mami dai bata ce komai ba, Yakumbo tace "Ba dai ka da kamarsu a duniya wllh, idan ka so ka rike su da mutunci su ne iyayenka gobe" Mikewa Abuturrab yayi ya nufi kofa, ta bude baki tace "Ohh ga shegiya na magana koh?" Ko juyowa bai yi ba har ya fice, ta kalli Mami tace "Hajarah anya tarbiyar arxiki kika ma Aliyu kuwa, yo ashe idan Ahmad na masa magana xai iya tashi ya wuce" Mami bata ce komai ba ta mike ta bi bayansa, har ya kusa part dinsa ta gansa tace "Aliyu" juyowa yayi yana kallonta ta karasa tace "Are you stupid ake maka magana xaka tashi ka wuce" yace "Haba Mami ni me yasa matar nn baxata kyaleni bane a rayuwar nn, komai nayi tace bai yi ba, ni gaskiya darajar Abba yasa nake daga mata kafa....." Tsawa Mami tayi masa tace "Koma dai meye yayar Mahaifin ka ce, and you have to respect her the way you will respect ur father...." Bai kuma cewa komai ba ya dauke Kai, tace "Maxa ka koma ka bata hakuri kar in saba maka" da kyar yace "Ohk Mami, amma sallah xanje yi masallaci yanxu" bata ce komai ba ya nufi gate, ta girgixa Kai ta juya ta koma gidan, ko da Abuturrab ya dawo daga masallaci sai da ya ga dama ya shiga gidan bbu yabo bbu fallasa ya bata hakuri ya fice daga parlon, karfe hudu yana shirin fita gun aiki aka danna bell a parlor.

Haske writers asso📚✍🏻
💫 *Noorul Huda*💫

6.....
Fitowa yyi ya bude kofar parlon ya ganta tsaye rike da basket din abinci, wara ido yayi yana kallonta, tace "Um na kawo maka abincin" rungume hannayensa yayi yana murmushi yace "Da gaske?" Ta gyada masa kai ya bata hanya ta shiga parlon ya juya ya bi bayanta, tsakar parlon ta ajiye abincin ta kallesa ya sakar mata murmushi yace "Thanks Samha!" Mikewa tayi ta dau jakarta tace "Uhm am going to church!" Shiru yayi yana kallonta, ta wara masa ido tace "Bye" daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo, can ya bi bayanta da sauri yace "Church kuma?" Ta kallesa tace "Eh Catechism xan je" rasa abinda zai ce mata yyi, ganin har ta fita ya bi ta yace "Which means baxa ki rakani ba knn, ke fa nake jira....." Ta juya tace "Ina xan rakaka?" Ya langwabar da kai yace "Clinic xan je duba patients dina" tayi shiru tana kallonsa, can tace "Toh church din fa, it's being a long time bn je church ba fa" yace "Ehh to daga can sai inyi dropping din ki a church din" bai jira cewarta ba ya juya ya dau car key a daki ya dawo yace "Mu je" yana gaba tana biye da shi suka isa gun motarsa ya bude mata snn ya tafi ya bude gate yana fita da motar ya fito ya rufe gate din snn ya shiga ya dau hanyar Clinic din da yake aiki, Ba tare da ya kalleta ba yace "Tell me about ur self!" Ta d'an kallesa sai kuma tayi murmushi tace "Ohk" jinginar da kanta tayi jikin kujera a hankali tace "Sunana Samantha David, but my baptism name is Rebecca, I am an only child, ni kadai parent dina suka haifa, I was born and brought up into a devoted Christian home, My maternal grandfather is a pastor, and my Mum Rachael took over him my mum is a Ghanian....." Shiru tayi tana kallonsa, duk da ba kallonta yake ba idonsa na kan titi amma gaba daya hankalinsa na kan abinda take cewa, still ba tare da ya kalleta ba yace "Ur Dad?" Ta wara ido tace "Sunan Abbana Aliyu Umar, but he's baptism name is David, my paternal grandfather is a Muslim, a Fulani from Adamawa, he married my paternal grand mum that was a Christian after he converted her to Islam, my father was the 1st child daga shi sai kanninsa mata biyu, duk suna kanana babansu ya rasu, shine Mum dinsu ta daukesu ta koma Ghana sbda akwai yayanta Christian a can, and that was where she re- converted to Christianity, then Abbana was still practicing the Islamic religion but when he met my mum at Sikkim Manipal University SMU sai ya koma Christian shi ma, buy he's younger sis Khadija is still a muslim she's in kaduna....." Driving kawae Abuturrab yake amma da ganin yanayinsa kasan takaici ne karara a tattare da shi, Ta langwabar da kai tace "My dad is a politician, he's a true devoted Christian also like my Mum...." Gyada kai yayi don bai ma son ci gaban labarin yace "That's nyc...." ta kallesa tace "Toh ni baka fadi min about ur self ba" shiru yayi na d'an lkcin kafin yace "Am Aliyu Ahmad, an only son with three siblings, My mum was a lecturer then, My dad a soldier.... I think that's all" Kallonsa kawai take ya kure wakar da ke tashi a motar don bai son magana kuma, har ya isa asibiti bbu wanda yace komai, yana gama parking ya kalleta ya bude motar ya fito ita ma ta fito tana kare ma asibitin kallo, tana biye da shi a baya suka shige reception, nurses din sai gaishesa suke sai dai ya gyada masu kai, ita kuma su bi ta da kallo har suka haura sama ya bude office dinsa, sai da yasa ta fara shiga snn shi ma ya shiga ya bude curtains ya kunna A.c ya xauna, tana kallonsa a hankali tace "I will like to be a doctor like you also" d'an murmushi yayi ya mike ya nufi fridge ya fiddo coke biyu ya mika mata daya ta karba ya bude dayan ya fara sha, kallonsa kawai take ko kiftawa bbu, ji tayi komai yayi burgeta yake, bai ajiye can din ba sai da ya shanye ya juya yana kallonta yace "If you study hard you will be a medical doctor also" wara ido tayi tace "Ohk I will by the grace of God" Wani d'an wardrobe ya nufa ya bude ya fito da pure white laboratory Coat dinsa ya saka ya dau stethoscope ya nufi kofa yace "taso mu je mu duba patients dina" mikewa tayi ta bi bayansa suka fita, haka ya dinga bin ward ward tana biye da shi duk jikinta a sanyaye ganin marasu lafiya abun tausayi a kwance, second to the last ward din da ya shiga ya juya bayan ya gama duba patients din ciki ya ga bbu ita, juyawa yyi da sauri ya fita ya ganta durkushe jikin bango hawaye a idonta, da mamaki yace "What happened?" Ta fashe da kuka ta mike tace "Doctor bana son gani kuma....." Rungume hannayensa yayi ya bude ido yace "is that why you are crying?" Bata ce komai ba sai hawaye, yyi murmushi yace "Alryt, tafi office ki jira ni" ba musu ta dau hanyar office din ya bi ta da kallo. Ko da ya koma office xaune ya ganta ta kife kanta da table, ya karasa yana kallonta ya duka gabanta, bak'in gashin kanta dake kyalli yake kallo ta dalilin xamewa da dankwalin kanta yyi, a hankali ya sa hannu ya karasa xame dankwalin don a rayuwar sa bbu abinda yake so kamar yaga gashin kan mace da tsayi, sai da ya rike breathe ganin gashinta din dogo ne ba na wasa ba ga tsantsi ga baki, kana ganinta kasan ta hada jini da Fulani, hannu ya daura a Hankali kan gashin yaji uban laushinsa, bude ido tayi ya koma baya da sauri ta mike xaune tana kallonsa tace "Doctor" wara ido yayi ya fara kame kame yace "Oh! you've... You've got a beautiful hair..... It's... It's very fine" mayar da dankwalin kanta tayi bata ce komai ba ya mike yana shafa kansa yace "har na gama duba patients din...." tace "Toh xan wuce church" kallon agogo yayi yaga biyar ya gota yace "Ohk...." Bude kofar office din aka yi, wani guy da baxai wuce Abuturrab ba ya shigo yace "Kai fa dan rainin wayo ne Aliyu, ina ta jiran....." Shiru yayi ganin Samantha, barin da ya ganta xaune kan office chair, Abuturrab yace "Yanxu fa da xan kira ka, to muje in ji urgent call din...." Daga haka ya nufi kofa, Jaheed dake ta kallon Samantha yace "Bakuwa kayi ne?" Abuturrab yace "Yea!" Snn ya fita, Mujaheed ya kalleta kafin yace komai tace "Ina yini" yyi murmushi yace "Lafiya lau, ykk" ta sunkuyar da kai tace "Lafiya lau" juyawa yyi ya fita, ba a wani dau lkci ba Abuturrab ya dawo yace "Ohk let get going" ta mike daga zaunen da take suka fita. Hanyar da yasan xa su hadu da traffic sosai ya bi da su, duk ta damu ita church, ko kallonta bai yi ba har sai da yaga shidda yayi yace "Wai karfe nawa ake tashi daga church din naku ne?" Kamar xata yi kuka tace "Six mana" ya dauke kai yace "Ashe ma an tashi kenan...." Bata kuma kulasa ba amma da gani xaka gane ranta ya baci, bai damu ba har ya isa kofar gidansu yyi parking xata fita ya riko hannunta, juyawa tayi tana kallonsa ya ga hawaye idonta, da mamaki yace "Kuka kuma?" Share idon tayi bata ce komai ba, yace "Toh Allah baki hakuri, but you can still go the church...." bata ce komai ba ta bude motar ta fita bai yi wata wata ba ya ja motarsa yyi reverse ya nufi gida ta bi motar da kallo, a sanyaye ta bude gate dinsu ta shiga. Abuturrab na dawowa daga masallaci ya bude abincin da ta kawo masa, Shinkafa ce da miya sai fried cow meat a wani gun daban da kayan vegetables da aka yanka, kallon abincin kawai yake duk da ya burgesa a ido amma bai jin xai iya ci, ya tabe baki ya mike ya dau naman ya kai ma karensa da ya fara sabawa da ya ajiye masa a cage, abincin kuma ya dauka ya kai ma masu gadi ya dawo ya xuba abincin da Ramla ta kawo masa ya ci kadan ya tafi masallaci, yana dawowa ya ganta da Mum dinta suna tahowa da kafa ko ina xa su, ido hudu suka yi da Mum din tata, tayi masa wani matsiyacin kallo da alamar ta tuno tare masu titi da yyi ranan ne, haka kawai yaji gabansa ya fadi, ya dauke kai ya ci gaba da tafiyarsa, Samantha sai kallonsa take har ya shiga gate. Washegari Sunday throughout bai ganta ba har yamma, duk sai yaji bbu dadi ganin har karfe shidda bai ganta ba, mikewa yyi daga karshe ya fita ya dau hanyar gidansu kamar me strolling har ya gama tafiyarsa bai ganta ba ya juya kawai ya dawo gida, har ranan laraba Abuturrab bai hadu da Samantha ba duk yaji sa bbu ddi har abun ya dinga basa mamaki, wai d'an sabon nn da suka yi har xai damu don bai ganta ba, yana xaune parlor tare da su Mami da yammacin ranan alhamis, Mami tace "Abuu!" D'agowa yyi da Sauri yana kallonta, tace "What's wrong with you?" Buda ido yyi yace "Nothing Mami...." Ta girgixa kai tace "Noo, ni fa na haifeka daga jiya xuwa yau naga you are not ur self....." Khaleesat tace "Mami baki yi noticing da kyau ba, for the past two weeks yanxu ya Turab ya canxa, he no longer talk to us, idan ma muka je part dinsa koran mu yake, he no longer treat us well...." Ilham tace "And he's alwayz closing his door don ma kar mu shiga" Ramlah tace "I think his dog is now his everything...." Abuturrab dai sai bin su da kallo yake, Khaleesat tace "or may be yana jin haushin Abba ya maida sa BQ ne, but it's not too late ya Abuu you can still beg him ya bar ka ka dawo nan" Abuturrab ya tabe baki ya ci gaba da kallonsa, Mami tace "Aliyu!" Kallonta yayi tace "Meye matsalar ka?" Ya girgixa kai yace "Bbu komai Mami, am just occupied with work ne yanxu" Mami tace "Toh shknn Allah ya mana jagora..." Mikewa yyi yana kallon khaleesat yace "Ke kuma kika sake ce min Turab sai na gurje bakin ki" daga haka ya kalli wayarsa dake ring yace "Jaheed ya xo Mami... Later xa mu shigo" Mami tace "Ohk Allah ya kai mu" daga haka ya fita xuwa bangaren sa Khaleesat ta bi sa da harara, Xaune ya ga Mujaheed yana ta kallon k'aren dake xaune cage, Abuturrab yace "Welcome!" Mujaheed ya mike yace "Yanxu pls meye ma'anar Dog din nn maimakon mai gadi" Abuturrab ya wara ido yace "Ya fi su iya gadi...." Mujaheed yayi dariya daga haka suka shiga parlor, Abuturrab ya dauko masu can coke a fridge, Jaheed yace "Kaga maganan serious nake son muyi Man kada kuma ka raina min hankali" Abuturrab bai ce komai ba sai da ya ajiye empty can din coke din hannunsa snn yace "Ina jin ka" Jaheed yace "Old man dina ne ya takura ni maganan aure this dayz wllh, am just confused donno what to do..." Abuturrab ya buda ido sai kuma yyi murmushi yace "Salima fah?" Harara Jaheed ya watsa masa yace "Salima har macen aure ce?" Abuturrab ya d'aga kafada yace "Ohk, nima of recent Dad dina ke min xancen aure...." Jaheed yace "Ae gwara kai kana da Saudat" Shiru Abuturrab yayi, Jaheed ya shafa kai yace "Gaskiya ka sama min solution, just few months ya ban if not ya hada ni da koma wacece ta xo masa a kai" Abuturrab yyi yar dariya yace "Amma kuma duk yan matan ka Mujaheed" Jaheed yayi tsaki yace "Kaga if you don't have anything good to say in tashi in kara ma motata mai" Abuturrab yayi murmushi yace "Kawai ka fara neman mata yanxu...." Jaheed yace "Wacece wnn yarinyar da ka taho office da ita ranan" wani kallo Abuturrab ke yi masa, wanda hakan Mujaheed yace "Ohk sorry ban san budurwar ka bace" Abuturrab yace "Ba budurwa ta bace" Jaheed yace "Then why the frowning of face?" Abuturrab ya tabe baki, sai kuma yyi murmushi yace "She's a Christian" xato ido Jaheed yyi yace "Christian kuma?" Abuturrab ya gyada Kai, shiru jaheed yyi yana kallonsa, can ya girgixa kai yace "That's sad, amma a ina ka san ta?" Abuturrab yace "Ga gidansu can few houses from ours" Jaheed yace "Lallai, babban magana kenan" Mikewa Abuturrab yayi jin kamar motsi a gate ya fita da sauri jaheed ya bi sa da kallo, bai ga kowa gate din ba da kuma alamar iska ce don a bude Jaheed ya bar sa, juyowa yyi ya koma parlon. Washegari friday Abuturrab na dawowa daga masallaci misalin biyu da rabi ya dau faran kujerar roba ta xauna waje jikin flower yana dannar wayarsa kunnensa sakale da earpiece, tun daga nesa ya hangota tana tahowa, ya kasa dauke idonsa a kanta ko kiftawan kirki bai yi har ta iso inda yake, ga mamakinsa sai ya ga taki kallon gun har ta wuce sa, bai san lkcn da yace frnd ba, ta juyo tana kallonsa.

*Haske writers Asso*📚✍🏻
💫 *Noorul Huda*💫

7......

Sunkuyar da kanta tayi ta dawowa cikin sarkewar murya tace "Ina yini" kallonta kawai yake ganin yanayinta yace "Baki da lafiya ne?" Kin cewa komai tayi kuma taki d'agowa ya mike yace "Talk to me mana, what's wrong?" hawaye ya cika idonta ta gyada masa kai, kalle kallen anguwar yayi, kawai ya kama hannunta suka shiga gida ya kulle gate din, parlor ya nufa da ita bayan yasa ta shiga da takalmanta ya rufe kofar yana kallonta yace "Since when?" xaunawa tayi kan kujera ta kwantar da kanta jiki ya durkusa gabanta yace "ina ke maki ciwo?" Xamowa kasa tayi ta hade kanta da gwiwa ta fashe da kuka bata ce komai ba, jin kukan nata ya dinga yi har xuciyarsa ya dago kanta ya dafa shoulders dinta da damuwa yace "Talk to me mana, ina ke maki ciwo" kalle kalle ta shiga yi can ta mike da sauri ya rikota xai yi magana ta toshe bakinta tana kkrin kwace hannunta, da sauri ya saketa ya mike ya kama hannunta suka nufi toilet dake parlon da ita, amai ta dinga kwararawa yana kallonta har ta gama tana mayar da numfashi ya debo mata ruwa ta wanke bakinta ya gyara wajen ya fito da ita, kwanciya tayi nan tsakiyar parlon tana juye juye, sai kuma ta fashe da kuka, ya hade rai yace "Kinga idan baxa ki min magana ba ki tashi kiyi tafiyar ki, leave now" mikewa tayi da kyar xata fita ba tare da ta kallesa ba ya bi bayanta da sauri ya jawota ta fado jikinsa, rufe fuskarta tayi jikinsa tana kuka a hankali, sun kusa minti uku a haka ya dago kanta a hankali yana kallonta yace "You are on ur period?" Sauke idonta tayi bata ce komai ba sai hawaye, komar da ita yayi ya xaunar kan kujera ya shiga bedroom dinsa, da yake baya rasa magunguna da allurori na Dysmenorrhea sbda kanninsa daukowa kawai yayi ya fito parlor, kwance ya ganta kasa, ya fara hada alluran yana gamawa ya dawo kusa da ita yace "Kin ci abinci koh?" Cikin kuka tace "Na sha tea" yace "Ohk, let me inject you, xa ki samu relief kin ji" bai jira cewarta ba ya fara daga doguwar gown din jikinta, ta rike da sauri don dama ita ba gwanar sa dogon wando bace, muryarta na rawa tace "Doctor ban sa komai ba...." shiru yayi yana kallonta sai kuma ya mike ya shiga daki ya dauko towel dinsa ya fito ya bata yace "to tashi ki daura," ta mike ta karba ya dauke kai ta daga gown din ta daura, kujera ta tafi tayi rub da ciki ta runtse ido ya bi bayanta, a hankali ya sauke towel din yayi mata alluran, yana gamawa ta fashe da kuka ya dagota xuwa jikinsa yace "It's okay xae daina maki yanxu" Kai kawai take gyada masa, sai da yaga ta nutsu snn ya saketa, ta xamo k'asa ta kwanta ta rufe ido, durkusawa yyi yana kallonta, ba a wani dau lkci ba bacci ya dauketa, ya mike yayi disposing syringe da kwalban alluran ya dawo parlon ya taimaka mata ta koma kan kujera. Yana bedroom aka danna bell ya fito da sauri ya nufi kofar, ganin Ramla ce yace "What again?" Tace "Ohh ya Abuu Mami ce fa ta aiko ni ka bude kofar plss...." ya hade rai yace "Pls go am busy yanxu, or you say it out there" murguda baki tayi don bata san yana kallonta ba tace "Ni fa....." Yace "Leave immediately idan ba haka ba xan sa ki kuka if I shud open this door" juyawa tayi fuu ta wuce. Sai kusan karfe shidda Samantha ta tashi daga baccin, yana parlor har lkcn yana danna laptop, ta mike xaune da sauri tana kallon agogo tace "Wayyo my mum is at home...." ya kalleta snn ya kalli agogo ta mike da sauri xata sauke gown dinta ta cire towel dinsa taga towel din yyi stain, still tayi tana kallon wajen, ya mike yace "What" girgixa masa kai tayi ta nufi toilet dake parlon da sauri, ya bi ta da kallo, cire towel din tayi xata wanke taji yace "Don't worry xan wanke....." Kasa juyowa tayi ta girgixa kai tace "No, xan wanke" juyo da ita yyi yace "Nace xan wanke" ta sauke idonta kasa bata ce komai ba, murmushi yayi yace "Yess" ajiye masa tayi ta nufi kofa ta fice daga toilet din sannan ta bar gidan gaba daya, tana isa gida gabanta ya fara faduwa, daga taje chemist a bata

Please Login or Register in order to submit comment