Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Eh" D'an murmushin farin ciki tayi tace "Amma sis Rachael bata sani ba koh?" Yace "Bata sani ba" Ajiyar xuciya ta sauke tace "Toh naji dadi yaya, don Allah kar ka fadi mata" murmushi kawai yyi bai ce komai ba, murya can kasa tace "Sai dai fa yaya Samantha tayi aure, a nan maraban jos aka daura auren" bai iya yace mata komai ba, tasan bai ji ddi bne, ta kwantar da murya tace "Kayi hakuri yaya ka kwantar da hankalin ka, you know God plans best, irin ta mu kaddarar knn, sannan yaya Musulmi ba a abun ki bane a gun ka, don't forget our father was a muslim till death, so are his relatives, Beside ni naga yaron nn na yaba da hankalinsa kuma kasan daga irin gidan da ya fito, bbu wanda ya isa ya tsallake kaddararsa, shi ma nasan bai taba tunanim xae auri warce ba musulma ba, kuma wllh yaya yana sonta fiye da yanda kake tunani ita ma kuma tana son sa...." Shiru tayi jin shi ma yyi shiru, ya gyada kai yace "Shknn we will talk some other time Maryam" Tausayinsa taji sosai, hawaye ya xubo idonta tace "Amma xaka je gun nasu a gombe yaya" Yace "Xan je" tayi murmushi tace "Toh shknn yayana Allah yyi mana mai kyau" yace "Amin" daga haka ya katse wayar, tayi tagumi a xuciyarta tana roka ma yayan nata rahama a gun Allah.

*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫

By Khaleesat Haiydar📚✍🏻

78.....

Da kyar Abuturrab ya samu ya lallashi Samha ta tsayar da kukan da take, cikin kwantar da murya yace "Beside Abba fa yace xai xo soon baby" a hankali ta dago tana kallonsa tace "Yaushe?" Yana share mata hawayen idonta yace "Soon yace min" daga haka ya rungumeta. Washegarin ranan da rana kiran Anty Maryam ya shigo wayar Abuturrab, ajiye drip din da yake hadawa xai sa ma Samha yyi, ya daga kiran suka gaisa, tace "Ashe kun yi magana da Abban Samha jiya?" Yace "Ehh Anty Mun kirasa" tace "Toh maa shaa Allah, naji dadi da kuka yi hakan, amma ya ku ka yi da shi?" Yace "He said he will be coming to gombe" Shiru tayi kafin tace "Toh shknn, Allah kai mu, ina babyna?" Kallon Samha dake kwance ta lullube da blanket har kanta yyi, yace "Ga ta Anty, bata da lafiya ne" Anty Maryam tace "Subhanallah, me ya sameta, tun yaushe?" Ya rasa abin cewa, can dai yace "Kwanan nan, bari in bata wayar" Anty Maryam da lkci daya ta gano dalilin ciwon tace "Toh bata wayar" karasawa yyi kusa da ita ya yaye bargon, ta bude idanuwanta a hankali, Ya kai mata wayar kunne yace "Anty xata maki magana wife" Cike da karfin hali Samha ta amsa kiran da Anty Maryam ke yi mata, Anty Maryam tace "Sannu Daughter, ya jikin" a hankali tace "Da sauki" Anty Maryam tace "Tun yaushe ne baki da lafiya?" Bata iya tace komai ba don ita ynxu magana ma burden yake xamar mata, hakan yasa Abuturrab ya mayar da wayar kunnensa, Anty Maryam tace "Ikon Allah, haka take jin jiki?" Yace "Da sauki Anty" Anty Maryam tace "Toh Allah ya sauwake, in shaa Allah ina nn xuwa dubata wnn karan" yace "Toh Anty, Allah ya kai mu" daga haka suka yi sallama ya ajiye wayar ya ci gaba da abinda yake. Bayan sati biyu ta ishesa ya kira mata Abbanta, bbu musu ya dau wayar ya nemo number ya kira, yana fara ring ya kai mata kunne ta karba, yayi tagumi yana kallonta don ramar tayi yawa, abu kusan wata uku amma ba sauki, "Hello, you call back ltr, he's nt around...." Muryar mum dinta ya d'aki kunnenta, a mugun tsorace ta sake wayar, yayi saurin dauka ya kai kunne shi ma yaji muryar ya katse kawai, ya mike ya ajiye wayar, can ya kalleta ya sakar mata murmushi ganin kuka take son yi, ya koma ya xauna yana shafa gefen fuskarta yace "Xaki fara aikin naki?" Ko tanka sa bata yi ba, yace "Xa mu je asibiti gobe baby...." Washegari da ya kasance Sunday yana xaune parlor kan laptop ita kuma tana daki as usual a kwance tana fama, bbu ynda bai yi da ita ba su tafi asibiti don yana son a mata scan amma taki wai bacci xata yi, fitowarsa knn daga dakin bayan ya tabbatar tayi baccin, danna bell aka yi ya mike ya isa kofar a tunaninsa khadija ce don ita kan xo a lkcn, Fatima ce tsaye bakin kofar, suna hada ido tace "Good afternoon" yace "Afternoon..." Tana jujjuya textbook din hannunta da handouts ba tare da ta kallesa ba tace "Pls idan baxan takura ka ba i need more explanation on this, am having test on it 2marrow in d morning, na samu Ummi tace min she's busy, Colleagues dina sun yi kkrin koya min but i seem nt to get it, and that's as a result of nayi missing lecture din ne shi yasa har ynxu ban gane ba, I've......" Katse ta yyi don surutun ya fara isar sa yace "What course?" Tace "Surg!" Juyawa yyi ya koma parlon ta bi bayansa, ya isa inda yake ya xauna yace "Me yasa baki kira Dr Shariff ba, nasan yana gida nd he will gladly come to assist you, ni gashi xa ki katse min aikin da nake yi" tace "I don't believe he even knows it" tabe baki yyo ya mika mata hannu ta basa litattafen hannunta, ya jawo table ya daura su kai yana dubawa, d'an xaro ido yyi tunawa da Samha da yyi ya kalli hanyar daki, can yace "Ohk, you sit let me make it fast xan fita ne" ta karasa ta xauna gefensa, nan ya fara koya mata course din yanda yasan xata fahimta, sai dai he's making it brief don Allah Allah yake ya kai karshe ta wuce sbda Samha, bai san tun da bell yyi ring ta farka ba, ita dai idonta na kan handout din tana saurarensa, Can yace "Wait! Are you getting me?" tace "Of course Noo, you re fast" yayi shiru yana kallonta, tace "i want you to teach me nt lecture" yace "But this is teaching nt lecturing madam" ta girgixa kai tace "Noo, ko in gwada maka ynda ake teaching?" Ya ajiye pen yace "Toh nuna min" sai a snn ta kallesa suka hada ido tun da ta shigo parlon, sauke idonsa yyi ta jawo takardan kusa da ita, nan tafara masa bayanin abinda yake mata, yayi shiru yana sauraronta, yyi mamakin bayanin da take with experience, fiye da ma ynda yake mata, ya girgixa kai yace "Dama kin iya kika kawo min?" Ta dago ta kallesa tace "Not at all, ynxun nn da ka fara min na gane...." Ya gyada kai bai ce komai ba, tayi murmushi tace "where you thinking I'm that dull?" Bai tanka ta ba, ta tabe baki tace "Toh ko kai baxa ka gwada min kkri a field dina ba..." Murmushin da bai shirya yi ba yyi yace "Really?" Bata kuma kallonsa ba, yace "What's ur point lst semester?" Tace "4.8 upward shi ne point dina tunda na fara karatu" dariya sosai ya dinga yi har da rike kai, ita kam sai kallonsa take, Mikewa xaune Samha tayi, dama tun shigowar fatima ta baxa kunnuwa tana saurarensu, ta cire bargon jikinta ta sauka kan gadon, har ta mance rabon da ta iya tsayawa ba tare da ta ga jiri ba, yau kam bata ji jiri ba, ta fice daga dakin, haba yana hangota dariyar ya makale a throat dinsa, bata ko kallesu ba ta nufi kitchen, sai ka rantse lafiyarta lau, Fatima dai ta gefen ido ta bi ta da kallo, shi kam mamaki ne ya ishesa don har ya mance rabon da ta taka har ta fito parlor da kanta, ya dai yi karfin halin jawo takardun ya ci gaba da koya ma Fatima, Tsaye Samha tayi kitchen duk ta rasa me ke mata dadi, taji xuciyarta na mata wani xafi, can kmr warce ta tuna abu ta juya ta isa gun da jarkan manja yake ta dauka, ta dawo ta dau pan ta xuba a ciki, ta kunna gas ta daura kai, ta dauki albasa da wuka ta yanyanka albasan ta xuba cikin man ta kara gas din sosai, ta ja gefe ta tsaya, kan kace me manjan ya fara soyuwa hayaki ya cika ko ina, ko gyaran murya bata yi ba ita da ke tsaye cikin hayakin, sai da taga man yana hayaki ssai ta juya ta fice, kofar parlor ta wuce, fatima dai ta fara gyaran murya tana rurrrufe ido jin hayakin na choking dinta, shi kam bin ta yyi da kallo ta kulle kofar da makulli ta cire makullin ta wuce daki, lkci daya fatimata fara tari sosai ta sauko daga kan kujera, ya mike da sauri shima jin hayakin, ya kalli kitchen yaga ta nn yake fitowa ya karasa da sauri ya shiga ciki, da kyar ya karasa gun gas din don shi ma har ya fara tarin sosai ya kashe gas din ya sauke pan din kai, ya fito, durkushe yaga fatima numfashinta na neman seize, ya karasa da sauri yana furta inalillahi ya dagota saketa yyi ya isa kofa ya murda ya ji sa a rufe, dawowa yyi ya sake daga ta yyi cikin spare room da ita ya rufe kofar sbda hayakin kar ya shigo, yana xaunar da ita ya sake fita, dakin Samha ya shiga ya ganta kwance ta lullube ya cire bargon yace "Me kike soyawa a kitchen Wife?" Ta kallesa a takaice tace "Manja!" yace "Me xa kiyi da shi?" Ta mike xaune tace "Sha xan yi" rasa abinda xae ce mata yyi, ta koma ta kwanta ta juya masa baya, kwantar da murya yyi yace "Toh bani makullin in bude mata ta tafi baby, kinga Asthman ta ya tashi" juyowa tayi ta sake mikewa xaune ta watsa masa wani kallon da ya sa hanjin sa kadawa, cikin daga murya tace "Baxan bayar ba, uwar me ya shigo da ita gidan??? Kai ka sa ta a boko ko kayi mata kama da lecturer?" K'asa cewa komai yayi ya dinga kallonta yana mamakin inda ta samu strength din masifa haka, yarinyar da da kyar take bude baki tayi magana, xama ma sai ya dagata take iya yi, ta mike tsaye tana huci tace "Toh nace baxan bayar da makullin ba ko baka ji ba?" juyawa yyi bai ce komai ba ya nufi kofa, ta murguda baki tace "Next time idan ance ta shigo gidan mutane unnecessarily baxata sake ba" daga haka ta koma ta kwanta.

*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫

By khaleesat Haiydar📚✍🏻

79.....

Bedroom dinsa ya koma ya fara duba spare key, yana gani ya dauka ya fita parlor ya bude kofar snn ya koma dakin da fatima take, har dai lkcn numfashinta bai dawo dai dai ba sai dai ba kamar daxu ba, ya isa kusa da ita yace "Sorry pls, ta mance you re asthmatic ne she wouldn't have done that" daga haka ya mika mata hannu ya dagata yace "May be later xan xo in karasa maki, or you talk to Mami" bata ko kallesa ba ta sa mayafin jikinta ta rufe hancinta ta fita dakin ya bi bayanta, takardunta ta kwasa a parlon ta nufi kofa yana biye da ita a baya, tana fita parlon yace "Sai kiyi amfani da inhaler idan kin shiga gida" ba tare da ta kallesa ba tace "Thanks" tayi gaba abunta, ya juya ya koma ciki ya rufe kofar snn ya wuce dakin Samha, kwance ya sameta ya rungume hannayensa yana kallonta, can ya girgixa kai yace "Toh tashi ki shirya mu tafi asibiti tun da kin samu strength" bata juya ba bare tace komai, ya isa kusa da ita ya xauna yace "Kin ji Baby" tace "Ni ba iyawa xan yi ba" dariya ta basa, ya dai yi murmushi kawai yace "Kamar ya baby?" Tace "Ina jin jiri" ya wara ido yace "Toh daxu da kika fito baki ji ba knn?" Mikewa tayi ta daure fuska tana kallonsa tace "Ehh" ya kwantar da murya yace "A'a ba fada bane wife, daure ki shirya mu je a duba mana babynmu" wani kallo ta masa ta koma ta kwanta. Ya mike ya fiddo mata da kaya, da kyar ya lallabata ta shirya yana taimaka mata, sai bayan da ta huta don ce masa tayi ta gaji snn ya kama hannunta suka fita yana rike da makullin mota, yana bude mata mota ta shiga ta rufe tana mayar da numfashi, shi dariya ma take basa, ya xaga ya shiga maxaunin driver yyi warming motar snn suka bar gidan. Sai bayan azahar suka dawo gida daga clinic din, nan parlor ta kwanta yace "Baby da ki daure sai ki karasa ciki mana" juya kanta tayi bata kulasa ba, yace "Uhm! Toh Allah baki hakuri" Daga haka ya dau makullin mota da takardan scan din ya shiga bedroom dinsa, yana tsaye gaban mirror ya sake warware takardan hannunsa, murmushi yyi yace "Babies...." Ajiye takardan yyi ya juya ya koma parlor, har ta fara bacci ya sameta, a hankali ya dagota da niyar kai ta daki ta bude ido, da sauri yace "Baby you re nt comfortable here kar wuyan ki yyi ciwo" Mikewa xaune tayi tace "Xan iya da kai na" ya saketa ta mike ta yi hanyar daki kmr warce iska xai kade ta fadi, underneath his breathe yace "Is it the pregnancy that's making her furious all the time" tana isa kofar dakinta ta duka, ya mike ganin haka, tana ganin ya nufo ta ta mike ta bude kofar ta shige ta rufe, dariya ta basa ba kadan ba ya koma ya xauna yace "Xaki neme ni anjima ai" Washegari da safe tana gama amai tace masa ita gari take son sha, ya d'an bude ido yace "Gari kuma baby" ta kwanta tace "Ehh" kallonta yake ya ma rasa abinda xai ce mata, can dai yace "Toh ina xa mu samo gari da sassafen nn" hannu ta buda masa alamar bata sani ba, yace "Toh baby ki bari da rana sai in nemo maki kinga ynxu it's too early" bata ce komai ba, yace "Toh me kuma xaki ci?" A takaice tace "Nothing" ya kafa mata ido, can ya mike ya shiga daki ya dau makullin mota ya fita nemo gari, sai kusan karfe goma ya dawo, yana parking Ummi na fitowa xata clinic, ya karasa ya gaisheta tace "Morning, ya mai jiki? Hope she's improving" Yace "Ehh Mami da sauki," tace "Toh kun yi scan ma kuwa?" Yace "Jiya muka je clinic" tace "Maa sha Allah, Allah ya kara mata lfya" yace "Ameen Mami, Allah ya tsare hanya" tace "Ameen boy," daga haka ta shiga mota, ya juya ya bar gun, bacci ya tadda Samha take, ya ajiye garin ya durkusa kusa da ita yace "Baby to gashi na samo maki..." Ganin kmr baccinta yyi nisa ya kyaleta ya fita dakin. Haka suka ci gaba da rayuwa Samha kullum masifarta karuwa yake, har wani shakkarta ya dinga ji don in ta masa wani tsawa har cikin kansa yake ji, gashi shi bai son hayaniya, abu kadan ke bata mata rai, ko kadan bai jin haushin hakan sbda condition dinta duk da dai ba kamar da ba don ta fara samun kanta, wani lkcn ta kan ci abinci ko kadan ne, amai kuma bai fi tayi sau daya a rana ba, kyanta ya kara fitowa sosai, sai dai ramar da tayi yyi yawa, bai gajiya da xama yyi ta kallonta don abubuwanta dariya suke basa, ganin she's getting her self ya fara fita aiki duk yamma ya dawo karfe takwas, yau ma yana clinic wajen karfe shidda wayarsa dake kan table ya fara ring, bai dauka ba sbda patient dake gabansa har wayar ya katse, bayan ya sallami patient din ya dau wayar ya ga Anty Maryam ce ta kirasa, bin kiran yyi tana dagawa suka gaisa ta tambayesa Samha da jiki yace "Alhmdllh da sauki Anty" tace "Toh Allah kara mata afuwa, kila in taho gobe idan Allah ya kai mu" yace "Toh Allah kawo mana ke lafiya Anty" daga haka suka yi sallama ya ajiye wayar, tunawa yyi da plantain chips da chocolates da Samha tace ya siyo mata, ya kalli agogo yaga shidda ya d'an gota, yyi deciding kawai yyi magrib snn ya wuce, mikewa yyi ya dau file dake gabansa ya fita office din don xuwa office din Ummi, Ummi na xaune sai Dr sharif dake xaune yana facing dinta Fatima kuma na kwance kan 2 seater, ya ajiye file din hannunsa ya kalli fatimar, har ya mance rabon ya ganta don tafi xaman hostel kan gida, ganin yanayinta yace "Bata da lfya ne Mami?" Ummi tace "That's her cup of tea, ni baxata daura min tension dinta ba, is she the only Asthmatic patient, kullum sai ta jangwalo ma kanta ta xo tana daura min wahala, is she a kid?" yyi murmushi yace "Kiyi hakuri Mami, it's nt her fault...." A fusace tace "It's nt her fault kmr ya, is she big enough nt to be going around with face mask, inhaler kuma ynda kasan needle haka yake a gun ta, kullum sai ta sa ni cacan inhaler, ajiya take ban? Ko Rabi'a baxa ta min abinda take min ba," Dr Shariff yace "Kiyi hakuri Dr" Abuturrab ya kalli Fatima yace "Me yasa baki yawo da mask" ko kallonsa bata yi ba, yyi murmushi yace "Allah ya sauwake, bari mu je masallaci Mami" daga haka suka fita da Dr shariff, ana idar da sllh ya dawo yace ma Ummi xai koma gida, tace "Toh ku tafi da fatima am nt leaving now" sai da gabansa yyi mugun faduwa tunawa da Samha da yyi, ya dake yace "Toh Mami" daga haka ya kalli fatima yace "Mu je" snn ya juya ya fita, har ya ja motar ya fita daga clinic din gabansa bai daina faduwa ba, har suka yi nisa bai ce ma Fatima komai ba, ya dai tsaya yayi taking excuse ya fita ya siyo plantain chips da chocolate da Samha tace masa snn suka dau hanyar gida, yana isa gate yayi parking yana kallonta yace "Ohh i forgot bn gama siyayya ba, ki shiga ciki xan juya" bude motar tayi ta fita, ya ja motar ya bar gun, ajiyar xuciya ya sauke, yana isa gun masu sayar da fruits yyi parking ya sauki ya siya fruits din da xai siya ya koma mota, Kitchen ya same Samha, yyi mamakin hakan ssai, yana tsaye bakin kofa yace "Baby me kike yi nan" ta juya ta kallesa kamar xata yi kuka tace "Yunwa nake ji" Yace "Toh me xa ki ci?" Ta bude ruwan dake tafasa kan gas tace "Ni indomie xan dafa" ya wara ido yace "Ohh that's nyc baby" dukawa tayi ta fiddo kwalin indomien ta ciro daya yace "Just one?" Bata tanka sa ba ta mike tsaye, yana tsaye yana kallonta har ta gama dafa indomien da ta cika ma uban yaji, ta daura kwai biyu a wani tukunyar, murmushi yyi yace "Baby duk wnn yajin" bata tanka sa ba still sai daure fuska da tayi wato ya fara isarta, hakan yasa ya ja bakinsa yyi shiru, tana xuba indomien a plate ta jira kwan yyi ta kashe gas din ta 6are ta daura kan indomien snn ta dau abinta ta juya, hanya ya bata ta fita snn ya bi bayanta, tana ajiye indomien ta dauko ruwa a fridge ta dawo ta xauna, ganin kallon da yake mata tace "Xaka ci ne?" Yace "Bayan daya kika dafa" tace "Toh ai baka ce min xaka ci ba" Yace "Koh?" Tace "Ka xo ka ci idan xaka ci mana" murmushi yyi yace "Tohm let me just taste" daga haka ya mike ya taho inda take ya debi abincin kadan ya kai baki, ji yyi kansa ya dauka tsabar yaji, ya mike yana girgixa kai yace "Yayi dadi sosai" daga haka ya bude fridge ya dau ruwa ya wuce daki. Washegari da ya kasance saturday karfe goma saura Samha ta tashi, shi kam dama tun da yyi Sllhn Asuba bai koma ba yana kallon wani movie a laptop, tana fitowa daga daki kitchen ta nufa, ya bi ta da kallo yace "Baby ina kwana?" Juyawa tayi ta kallesa ta d'an turo baki tace "Ina kwana" murmushi yyi yace "A'a ki amsa dai, ni kam duk an canja min babyna" bata tsaya ba tayi shigewarta kitchen, yana jin tana ta 6uruntun ta a kitchen ya kuma san abinci take dafawa don aroma din ya baibaye gidan gaba daya, bayan kusan minti talatin ta fito rike da bowl madaidaici a hannu, sae kallon bowl din yake yana son sanin me ta dafa, ganin xata wuce daki yace "Baby me kika dafa?" Ta juyo tace "Xaka ci ne?" Ya girgixa kai yace "A'a" tace "Porridge na irish nayi" bai ce komai ba, ko me ta tuna sai kuma ta dawo parlon ta xauna ta tankwashe kafa ta fara cin Irish din da yaji nama, duk da abincin ya shiga ransa sau daya ya kalla bai kuma kallo ba ya mayar da hankalinsa kan movie din da yake kallo, sai da tayi rabi ta ture bowl din, ya kalleta yace "Kin koshi ne" Bata ce komai ba ta jinginar da kanta da kujera, bayan kusan minti biyar ta mike da sauri, ya bi ta da ido, toilet dake parlon ta shige ta fara kwarara amai, ya mike ya bi bayanta, yana tsaye kanta har ta gama ya bude mata tap ta wanke bakinta snn ta fito, gun abincin ya ga ta koma ta xauna ta ci gaba da ci, bai ce mata komai ba ya xauna gun laptop dinsa, sai da ta cinye abincin gaba daya snn ta kallesa tace "Toh kai kayi breakfast din ne?" Yace "Kin ban ne?" Tace "na yi xaton ka ci" ta mike xata daki ta kwanta yace "Dear xamu yi visitor yau fa" Ta kallesa tace "Su wa ne?" Ya d'an yi shiru kafin yace "Aunt dita ce ita ma, tana son ta gan ki" Samha tace "Toh Allah ya kawo ta lafiya" yace "A siyo take away kawai koh?" Ta girgixa kai tace "A'a xan iya girkin"

*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫

By khaleesat Haiydar📚✍🏻

80.....

Samha bata iya ta karasa girkin tuwo da miyar ganye, sai jollof din da ta fara ba ta dinga jin jiri da tashin xuciya, bedroom ya wuce da ita ta kwanta, da damuwa yace "Sannu baby shi yasa nace mu siyo take away kika ce xa ki iya" bata ce komai ba sai rufe idonta da tayi, ya langwabar da kai yace "Bari in kira khadija ta karasa maki ko baby..." Bude ido tayi tana kallonsa, yace "Yau Saturday nasan she's at home" bata ce komai ba ya mike ya fita, Ummi kadai ce xaune parlor tana kallon wani program, ya xauna suka gaisa snn yace "Mami khadija na nan don Allah" tace "Ehh tana ciki" yace "Dama Samha ce ta fara girki kuma bata iya ta karasa ba...." Ummi tace "Ayya, toh bari ta fito ta karasa mata" daga haka ta kirawo khadija tace "Dear ki tafi ki taya Samha aiki kin ji" Khadija tace "Toh" daga haka suka fita tare da Abuturrab da yyi ma Ummi gdya, Khadija na shiga kitchen din ta ci gaba daga inda Samha ta tsaya shi kuma ya shiga dakinsa, waya ya dauka ya kira Anty Maryam tana dagawa suka gaisa yace "Kin taso kuwa Anty?" Tace "Eh tun safe na taso Aliyu, mun ma yi nisa" yace "Toh Allah ya kawo ku lfya, ya kiyaye hanya, idan kun iso park sai ki kirani xan xo in dauke ki" Tace "Ameen Aliyu, Alryt xan kira ka" yana ajiye wayar ya fita ya shiga dakin Samha ya sameta tana bacci, ya kalli agogo ya daura hannu fuskarta a hankali yace "Dear baxa ki daure ki shirya ba kafin Aunt din tawa ta xo?" Da kyar ta bude ido tana kallonsa, ya sakar mata murmushi yace "Yes, ki daure kin ji

Please Login or Register in order to submit comment