Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lumshe ido murya can kasa yace "Good morning wife...." Daga haka ya kai bakinsa nata, tun tana turasa tana son kwace kanta har dai ta hakura, kamar me rada ta ji yana ce mata "Are you still on ur period?" Bata iya ta basa amsa ba, yayi tambayar ya kai sau uku amma shiru, saitin kunnenta taji yana cewa "Talk plss dear" sai a snn ta bude ido da kyar, ae lkci daya wani karfi ya xo mata ta turasa a rikice ta fara ja baya tace "Doctor" fixgota yayi ta fashe da kuka sosai tace "Plss ni ka bar ni" saketa yyi ya mike daga gadon ya fice daga dakin, ko ina na jikinta rawa ya dinga yi ta mike ta dau kayanta ta shiga bathroom. Ta kusa minti talatin da fitowa kafin ya dawo dakin, ya ajiye ledan hannunsa ya kalli inda take yace "Breakfast" fingers dinta take fidgeting bata ce masa komai ba, yace "You hurry up kafin in dawo" daga haka ya fita, ta bi sa da ido kafin ta murguda baki ta mike ta bude ledan, irish ne da kwai da plantain, bata wani ci sosai ba sbda tea take son sha, kwanciyarta tayi kan gado har ta fara bacci ya shigo dakin, ya karasa ya xauna gefen gadon yana kallonta. Hannu ya kai fuskarta ta bude ido da sauri ta mike xaune, wara mata ido yayi yace "Ki shirya yanxu xa mu je gun Anty" ba musu ta mike ta nufi gun da hijab dinta yake ta dauka, yace "Baxa ki yi kwalliya ba" ta d'an kallesa kafin ta dauke kai tace "Meye shi?" Hijab dinta ta shiga sa wa ya mike ya isa bayanta tana juyowowa ta ja baya da sauri yace "Nuna maki xan yi meye shi" murmushi tayi ya jawota jikinsa yace "Hakan ma kin yi kyau sosai baby kar a kallan min ke" Yana rike da hannunta suka fita. Kawar Anty Maryam ce ta masu kwatancen gidan a waya suna isa ya ba mai adai daitan kudinsa snn ya kira yace ga su a waje, Anty Maryam ce ta fito shigo da su gidan, Abuturrab ya gaida ta kansa a kasa ta amsa tana tambayarsu ya suke, har parlon gidan suka shiga bayan ya gaisa da Hajiya Salamatu da kawarta yace xai je ya dawo anjima, daga haka yayi masu sallama ya d'an saci kallon Samha kafin ya fita parlon, barin parlon kawar Hajiya Salamatu ma tayi Anty Maryam ta kalli Samha tace "A ina ku ke yanxu?" Kanta a kasa tace "Hotel" Hajiya Salamatu tace "Ina yace maki xa ku daga nan?" Girgixa kai tayi tace "Ni ma ban sani ba" Duk suka yi shiru, can da Hajiya Salamatu tace "Ya ma sunan ki?" Samha bata dago ba sai wasa take da yatsunta a hankali tace "Samha ake ce min yanxu" Anty Maryam ta bude ido tace "Samha? Wa ke ce maki hakan?" Tace "Shi yake cewa haka duk inda muka je" Hajiya Salamatu tayi murmurshi tace "Yanxu Samha ba ki sha'awar Musulunci" Samha bata ce komai ba bata kuma dago ba, Anty Maryam ta girgixa mata kai alamar ta bar xancen, mikewa Anty Maryam tayi ta dawo kusa da ita tace "You tell me the truth Samha, abu ya taba shiga tsakaninku da shi" k'in dagowa tayi har lkcn kuma bata ce komai ba, Anty Maryam ta dago kanta tace "Nasan ba kya karya daughter kar ki fara yanxu" A hankali ta girgixa kai, Anty Maryam tace "I didn't ask you to shake ur head ki bude baki ki min magana" Da kyar tace "Bbu komai Anty" Hajiya Salamatu ta dawo kusa da su tace "Kar fa ki ji komai Samha, kar ki boye mana komai" ta kalleta tace "Allah ni bbu abinda ya shiga tsakaninmu" Anty Maryam tace "Na yarda daughter, nasan kuma irin tarbiyar da mum nd Dad suka baki" Hajiya Salamatu ta cire hijab din jikinta tana kallon gashinta tace "Kitso xa ayi mata ko retouching?" Anty Maryam tace "Tayi retouching kawai koh" mikewa Hajiya Salamatu tayi tana kallon Samha tace "Toh tashi mu je Samha akwae saloon nn anguwar ai" daga haka ta shiga ciki gun kawarta don cewa xa su saloon, tana dawowo tace "Sai ki hada abinda ya kamata kafin mu dawo Maryam" daga haka ta kama hannun samha suka fita, cikin awa daya aka gama gyaran gashin aka rangada mata lalle mai kyau ba mai yawa ba snn suka dawo gida, Anty Maryam sai murmushi take ganin ynda 'yar tata ta fito, Hajiya Salamatu na kallon Samha tace "Yaushe watan ki ke tsayawa?" Samha ta girgixa kai tace "Gobe xan gama" abubuwan da ya dace Hajiya Salamatu duk tayi mata a spare room dake gidan, ita dai Anty Maryam sa su gaba tayi. Sai kusan bayan la'asar Anty Maryam ta kira Abuturrab bayan sun mata nasiha sosai, godiya sosai Abuturrab ya dinga yi masu, ita kam Samha bnda kuka bbu abinda take, Antyn ta taji tausayinta sosai, da kyar ta yrda ta tashi Anty Maryam na rike da ita suka fita daga parlon, har bakin titi ta rakasu, sai da suka samu adai daita snn ta juya ta koma duk jikinta a sanyaye, rufe fuskarta tayi da abayar jikinta sae kuka take, ya rasa ta inda xai fara lallashinta, har ransa ya dinga jin tausayinta ya ji kmr ya rungume abarsa, kafin su isa hotel din har hijab dinta ya jike da kuka, ai suna shiga gate ya rungumeta bai damu da kallo da ya dawo kansu ba ya ja ta xuwa karkashin bishiya ya xaunar da ita kan kujera ya durkusa kan kneels dinsa gabanta da damuwa yace "Kar ki fasa min xuciya wifee, are u regretting marrying me?" a hankali take girgixa masa kai har lkcn fuskarta boye a hijab, ya lumshe ido ya bude cikin sanyin murya yace "I love you Samha, ina son ki, son da ni kai na ban san irin sa ba, i knw i will love you till my very last breathe wife, we re going to start a new life full of happiness, love nd affection, i will be ur everything, i will never disappoint you Pearl.... bbu wata bayan ke Jewel.... Look at me wife ko xan ji ddi plss i beg you" a hankali ta xame hannuwanta tana kallonsa da idanuwanta da ya kada, murmushin jin ddi yyi ya kamo hannunta, ita ma tayi murmushin a hankali, mikewa yayi ya dagota ya rungumeta gam, boye fuskarta tayi a jikinsa ganin irin kallon da ake masu a haraban hotel din.

*Haske writers asso*

Alhmdllh am feeling much much better now, a big tnx to my fcbk fanz for their prayers and everyone Allah ya sa mu dace, My Course mates Nafi, Sophie, Hussy.... tnx for the Jinya Allah bar mu tare mu yi ta fada, My fellow Biochemist mates tnx all for the prayers too sai mun hadu a Dept, My Nafeesat Dut. ina yin ki kawata da bata bacci idan ban yi ba, Jiddo is now Alhmdllh Allah bar xumunci. My FUD fans... Khaleesat is saying Hi.... Lng live fudites, lng live we Biochemist😅
💫 *Noorul Huda*💫

By khaleesat Haiydar📚✍🏻

62....
Washegari tun da sassafe Abuturrab ya gama shirinsa ya shiga shirya masu kayansu don kafin karfe tara yake son su bar Zaria, har ya fita ya siyo masu breakfast ya dawo bacci take bai kuma tashe ta ba, barin dakin yyi ya fita haraban hotel din yyi xaman sa, kiran Anty Maryam ne ya shigo wayarsa ya daga ya kai kunne hade da gaisheta, ta amsa tace "Dama wllh jiya na mance bn ba daughter sako ba, idan ba damuwa ka taho ka karbar mata don Allah" yace "Toh Anty xan xo ynxu" mikewa yyi ya koma ciki, wnn karan tada ta yyi, ta mike xaune yace "Am coming back soon dear ga breakfast na ajiye maki" tace "Ina xa ka?" Yace "Anty xata bada sako a kawo maki wai" kai ta gyada masa ya mike yace "You can still go back to sleep" mikewa tayi ita ma tace "Allah kiyaye hanya," daga haka ta shiga bathroom, murmushi yayi ya dau kudi da xai dauka ya fita. Takwas da rabi ya isa maraba, har parlor Anty Maryam ta shigar da shi suka gaisa snn ta dauko kudi ta mika masa tace "Dubu hamsin ne nn, ka bata bride price dinta ta siya duk abinda take so" Kansa a kasa ya karbi kudin yace "In shaa Allah Anty" Kunu da kosai ta kawo masa, bai mata musu ba ya ci, da xai tafi ya ba yaranta dubu biyu ya kuma yi mata godiya snn ya bar gidan, yayi niyyar karasawa kd gun Sadeeq amma ya kira number sa bai shiga ba hakan yasa ya koma Zaria, Samha na kwance idonta lumshe duk da ba bacci take ba, ya karasa ya durkusa gabanta yana kallonta, a hankali ta bude ido, murmushi ya sakar mata yace "Love" mikewa xaune tayi ya kamo hannunta yace "Kin yi break din kuwa?" Kai ta gyada masa ya fiddo kudin aljihunsa ya sa mata a hannu, tace "Na mene?" Ya wara mata ido yace "Ur pride price, Anty tace in kawo maki ki siya duk abinda kike so" shiru tayi tana kallon kudin, can ta girgixa kai tace "Na baka" hade rai yayi yace "Kin ban kuma? It's urs baby, me kike son in siya maki" ta kallesa tace "Ni ba abinda nake so ai, kawai kayi amfani da shi" Shafa gashin kanta yayi yace "No dear, i will get you something with it" bata kuma cewa komai ba, yyi mata light kiss ya mike yana murmushi yace "Do you still want us to go to gombe?" Kallonsa tayi bata ce komai ba, ya kuma xaunawa ya kamo hannunta yace "Kinyi shiru Pearl" tace "Duk yanda ka ce" ya dagota suka mike yace "To nace mu je can, it's more safe there" karfe sha daya saura suka bar Zaria suka dau hanyar gombe. Sai kusan La'asar suka shigo gombe, sai a snn Abuturrab ya fara tunanin da idon da xai kalli Mami, gashi ranan lahadi ce yasan tana ma gida, har suka isa gida tunani kawai yake, mai adai daitan na tsayawa kofar gidan ya kalli Samha, a hankali tace "Toh me xaka ce ma Ummi?" Fitowa yyi ya ba mai adai daitan kudinsa ita ma ta fito, murmushi yyi yana shafa kai yace "I don't know wht to say, ko xaki fadi min abinda xan ce" ta tabe baki tace "Ni ba ruwana" yar dariya yyi ya kama hannunta suka shiga compound din bayan ya amsa gaisuwar mai gadi, kamar ynda yyi tunanin hakan ne don Ummi na xaune balcony tana aiki, Samha ta xame hannunta daga nasa, a hankali yake tafiya har ya isa Balcony din, Ummi kam tun da tayi masa kallo daya dama ta ci gaba da abinda take, durkusawa yyi nan gabanta sai kuma ya rasa abun cewa, kallon Samha dake tsaye gefe tana wasa da yatsunta tayi ta girgixa kai ta mayar da dubanta kan laptop dinta, da kyar Abuturrab yyi gathering courage yace "Mami ina yini?" Kallonsa tayi kafin tace "Lafiya lau" Samha ta d'an risina ta gaisheta ita ma ta amsa snn ta ci gaba da abinda take, ganin ba magana Ummi xata yi ba ya mike, har xai bar gun tace ya dawo, dawowa yayi ta kalli Samha tace "Ki shiga bedroom dina akwai makulli a kan study table ki dauka" shiga parlon Samha tayi, Ummi na kallonsa tace "Sai da kaje ka lalata masu rayuwar ya snn ka dawo knn, i never knew takura ka nake Aliyu amma it's a promise am making now baxan sake shiga rayuwar ku ba" da sauri yace "Wllh ba haka bane Mami, gun kanwar Abbanta na kai ta kaduna, she's a muslim nd.... Mami basu bari muka bar garin ba sai da suka tabbatar na aureta, am saying nothing but d truth, kuma sai da naje kano gun Mum dina, I begged her for forgiveness, i knw i failed u Mami amma don Allah kiyi hakuri kar ki hukunta ni...." Ummi dake ta kallonsa tace "Did i deserve u going without telling me Aliyu, xan hanaka don kace min xa ku gun aunt dinta? Ni baxan hana ka ba sai dai ko in hada ku da wani ku je tare, haka kke abun ka bbu reasoning Ali?" Sunkuyar da kansa yyi kasa yace "Am so sorry Mami nasan ban kyauta ba ki yafe min" Samha na fitowa daga parlor rike da makullin Ummi tace mata taje ta bude kofa a can, tana barin gun ta girgixa kai tace "Idan ma kun tafi without knowledge dina baka da wayar da xaka kira ni daga baya?" Shiru yyi bai ce komai ba, can ta girgixa kai tace "Gaskiya i was so surprise at you, you failed my trust for you" a hankali yace "Kiyi hakuri Mami..." Tace "Anyway, tashi kaje, Allah rufa asiri, it's good she's now ur wife" bai iya ya mike ba, can ya ciro kudin aljihunsa ya mika mata yace "Aunt dinta tace in bata sadakinta, ko xa ki siya mata abu Mami" ba musu Ummi ta karbi kudin ta ajiye a gefenta, ya mike da kyar ya bar gun. Har Samha ta fara gyaran gidan kafin ya taho, yayi dusting kujera ya xauna yace "You need rest dear, drop that broom now" ba tare da ta kallesa ba tace "I can't endure resting in dirt..." Kallonta yyi sai kuma yayi murmushi yace "Toh baturiya, transform the house as you wish" kallonsa tayi ita ma tace "You watch nd see..." Kwankwasa kofa aka yi ya mike ya isa kofar ya bude, mai aikin Ummi ce tsaye ta gaishesa ya amsa snn tace "Madam tace in xo in taya ta gyaran gida" hanya ya bata yace "Alryt" bedroom ya wuce ya bar su parlon, yana sllh ya cire bedsheet yyi kwanciyarsa, kafin karfe biyar da rabi suka gyara ko ina na gidan ya rage dakin da yake ciki kawai, Samha tace "Nagode sosai xa ki iya wucewa Anty" daga haka mai aikin ta wuce ita ma ta shiga bedroom din da Abuturrab yake, karasawa tayi kansa ta ja pillon da yake kwance kai tace "You call ur self a doctor amma kuma xaka iya bacci peacefully cikin dusty room din nn?" Har lkcn bai bude ido ba, ta hade rai ta buga gadon tace "Ni ka tashi in gama gyara na, you can go to the other room and continue" bude ido yyi ya fixgota jikinsa yana kallonta yace "Ashe kin iya magana haka Samha?" Kwace kanta ta shiga yi yaki sake ta ya mike xaune yana murmushi yace "One thing about you is that, you can pretend for africa" kwace kanta tayi ta mike ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fice daga dakin snn ya mike ya bi bayanta. Da magrib mai aikin ce ta kawo masu abinci duk da ya riga ya siyo masu, yana xaune shi daya parlor yana danna laptop khadija tayi sallama ta shigo, durkusawa tayi nesa da shi tace "Uncle ashe kun dawo, ya hanya?" Yana murmushi yace "Lafiya lau khadija, ya karatu?" Tace "Alhmdllh, ina sis Samha fa?" Mikewa yayi yace "Let me check her tana ciki" daga haka ya nufi bedroom, yana shiga tana fitowa daga wanka daure da towel, tayi masa kallo daya ta wuce can karshen gado ta xauna, ya bi ta da ido, satan kallonsa tayi ganin kallonta yake ta bata fuska tace "I want to dress up..." Rufe kofar dakin yayi yace "You re free" mikewa tayi xata koma bayin ya rikota, ta wani hade rai tace "Bna so, bana son haka doctor...." Shi ma ya hade giran sama da ta kasa yace "Baki son me?" Fashewa tayi da kuka, ya buda ido yace "Ehenn, me nayi maki" ganin da gaske take ya xauna gefen gado ya xaunar da ita gefensa yace "Khadija fa na jin ki a parlor, daga magana sai ki fara min kuka?" Kallon kofar dakin tayi tana share idonta, lumshe ido yyi ya rungumeta yana shafa gashinta ya kai bakinsa kunnenta yace "Hope anjima dai baxa ki ce min baki so ba don ko kukan jini xa ki yi ba wannan xancen yau..." Shiru tayi bata ce komai ba, ya saketa yana murmushi yace "Ki shirya tana jiran ki a parlor" ta gefen ido ta hararesa ta mike ta nufi press din kayanta, ya gyada kai yana murmushi har lkcn ya fita.

*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫

By khaleesat Haiydar📚✍🏻

63.....

Tana gama shirinta ta fita parlorn, xaune ta tadda khadija har lkcn, ta karasa tana murmushi tace "Maimakon ki shigo ciki" khadija dake kallonta ita ma tana murmushin tace "Yanxu Ummi ke ce min kun dawo sister, ya hanya" Samha ta xauna gefenta tace "Alhmdllh, ya makaranta?" Khadija tace "Lafiya lau" fruits dake cikin wani bowl Samha ta mike ta kawo ta ajiye mata tace "Rabi'ah fa?" Khadija tace "Ae har yanxu bata dawo gida ba" Samha tace "Ayya, sis fatima fah?" Khadija tace "Tana cikin gida" Apple kawai khadija ta dauka ta mike tace "Bari in je dare yyi sis Samha sai gobe" Samha ta kalli agogo tace "Da wuri haka" dariya kawai khadija tayi tace "Xan goge hijabs dina kafin in kwanta ne" daga haka ta kalli Abuturrab dake ta danna laptop tace "Uncle sai da safe" ya kalleta yace "So early Dija" murmushi tayi ta nufi kofa yace "Toh ki gayar da Mami, Yusuf na nan ne?" Ta girgixa kai tace "Yana Egypt" yace "Alryt" har balcony Samha ta rakata suka yi sallama sannan ta dawo parlor ta dau bowl din sauran fruits din ta ajiye a fridge, yace "Ke baxa ki sha ba?" Girgixa kai tayi tace "Na koshi" daga haka ta wuce daki, hijab din jikinta ta cire tayi kwanciyarta ta rufa da blanket. Sai kusan karfe sha daya Abuturrab ya gama abinda yake ya mike ya rufe gidan snn ya kashe wutan parlon ya dau laptop dinsa ya wuce daki, ajiye laptop din yyi gaban mirror ya kunna ac din dakin ya shiga bathroom don yin wanka, yana shiga bayin ta mike don dama ba bacci take ba ta dau hijab dinta ta fice daga dakin ta koma daya dakin ta shiga ta rufe tayi kwanciyarta, ko da ya fito murmushi yayi da bai ganta a dakin ba, ya gama shirinsa har da ya kwanta sai kuma ya mike ya nufi dakin da ta shiga, ta wani rufe ido kmr me bacci ya karasa kan gadon yace "Why did you leave the room" bata bude idon ba bare ta basa amsa, ya kafa mata ido yana kallo, hannu ya daura forehead dinta yace "I kiss you now idan baki bude ido ba" bude idon tayi ta mike xaune ta hade rai tace "Doctor ni fa ina ce maka bna son irin haka," kallonta ya tsaya yi can ya fixgo shoulders dinta yana mata wani kallo yace "Baki son me knn?" Ja baya tayi ta kauda kai ta tsuke baki, yace "But me yasa lkcn da kike xuwa wajena can gida bakya cewa baki son ina taba ki, you like it then koh?" Ta kallesa da sauri sai dai bata ce komai ba, ya daga kafada yace "Yeah, ynxu ne baki so but you like it then i notice" Sauka ta shiga kkrin yi daga kan gadon ya fixgota ta fashe da kuka, ji yyi ransa ya baci ya fixge hijab din jikinta yace "Sai kiyi na jini ma in ga ai" ta hade kanta da gado tana rerawa, har ya mike xai fita sai kuma ya fasa, ya dake ya xauna ya dagota yace "What's the meaning of this Samha, Where is d love?" Bata bari sun hado ido ba, ya dago kanta yace "look at me Samha" a hankali ta dago manyan idonta tana kallonsa, murya can kasa yace "Wahala kike son bani don kin ga ina son ki da yawa ko, me yasa tun da baki min haka ba sai yanxu?" Sauke idonta tayi kasa ya jawota jikinsa yace "Baki sona yanxu koh?" Kamar xata yi kuka tace "A'a" yace "Toh me yasa kike cewa baki son in taba ki" ta fashe da kuka a hankali tace "Ni tsoro nake ji" ya buda ido yace "Tsoro kuma? Tsoron me?" Bata ce komai ba kuma bata daina kukan ba, yace "Talk to me mana Wife, tsoron me?" cikin muryar kuka tace "Kai..." sosai ta basa dariya ya dake yace "Ni kuma, toh me nayi maki kike tsorona" k'in cewa komai tayi yana shafa gashin kanta yace "Ki gaya min mana tsoron me nake baki dear, baki son gani na ne kuma?" Girgixa kai tayi, yace "Then me nake maki da baki so?" A hankali tace "Bana son kana taba ni..." Shiru yyi, sai kuma yace "Why?" Tace "Saboda ni dai bana so" murmushi yayi yace "Amma da a can gida baki ce min baki so ba ai" Kallonsa tayi tace "A'a ka dai manta, duk san da ka taba ni ae bana sake xuwa sai an dade" yace "Hmmm, shknn na daina taba ki tunda baki so" daga haka ya saketa ya koma baya yace "Is that all?" Kai ta gyada masa ya mike yace "Quite alryt...." Sannan ya nufi kofa yana murmushi can underneath his breathe yace "Nasan maganin ki" bin sa ta yi da ido har ya fita kafin tayi kwanciyarta. Washegari da ya kasance monday ko kafin Abuturrab ya fito duk ta gama gyaran gidan gaba daya tayi wanka ta shirya cikin abayarta, Tun takwas mai aiki ta kawo masu breakfast in ji Ummi, Kallo daya yyi mata yayi xamansa parlor yana kkrin bude laptop dinsa, tace "Ina kwana?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Lfya baby" tace "In kawo maka breakfast din yanxu?" Ya girgixa kai yace "Nop" kwankwasa kofa aka yi ta mike ta isa kofar ta bude, Fatima ce tsaye sanye cikin abaya da jaka a hannunta ta sa siririn glass a ido Kallon kallo suka dinga yi na kusan second goma, can Samha ta dake tace "Ina kwana" Fatima tace "Alhmdllh, Doctor na ciki?" Kai kawai Samha ta gyada mata, d'aga wayarta dake ring tayi ta bi ta gefenta ta shige parlor Samha ta bi ta da ido, Tsaye tayi d'an nesa da shi tana ci gaba da waya da kawarta da ta kirata, Abuturrab da bai dago ba tun shigowarta, cab ya juya ya kalli bakin kofa suka hada ido da Samha kallon Fatima da ke kkrin mayar da wayar jaka bayan ta gama yyi, ta dago suka hada ido, kirkiran murmushi yyi yace "Morning" sosai tayi mamakin hakan ita ma ta mayar masa da na yake tace "Good morning" yace "Ya boko?" Tace "Alhmdllh" idonsa ya mayar kan laptop yace "Wani course kike?" Tace "MBBS" kallonta yyi daga kasa har sama kafin yace "Lvl?" Tace "300" yayi d'an murmushi yace "Nyc" Tace "Thank you" ya mayar da dubansa laptop yace "Welcome" "Dama Ummi ce tace ka je" ta fadi hakan tare da juyawa tayi hanyar kofa yace "Alryt" Samha na nan tsaye inda take tun shigowar fatima, Abuturrab ya saci kallonta ya dauke kai ya ci gaba da abinda yake, fatima na fita ko rufe kofar Samha bata yi ba ta nufi hanyar daki, ya kalleta da sauri yace "Dear a ban break din yanxu i think am hungry" ko kallonsa bata yi ba ta shige daki, yar dariya yyi ya mike ya fita xuwa kiran Ummi, suna gaisawa tace "Are you still interested with the job or i give someone?" Yace "I am Mami" tace "When re you resuming?" Yace "Probably today" tace "You leave it tomorrow" godiya yyi mata ya mike ya bar parlon, yana komawa part dinsa tea kawai ya hada ya sha ya fita, compound ya tadda khadija ya sa ta dauko masa makullin mota ya fita siyo masu foodstuffs, sai kusan karfe goma ya dawo gidan mai gadi ya taimaka masa fiddo kayan abincin xuwa cikin gida, shi kuma ya karasa da su kitchen, bedroom din da take ya nufa ya ganta kwance idonta

Please Login or Register in order to submit comment