Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ledar da Abuturrab ke mika ma Samha sannan tayi masu sallama Sadeeq ya kashe mata ido yace "Mu yi waya" tayi yar dariya suka wuce ciki tare da Samha. Bbu bata lkci su Abuturrab suka juya, Throughout journey din Abuturrab labarinsa da Samha yake ba Sadeeq dake ta hail dinsa kace abun arxiki yayi, jin a ranan ma xa a daura auren nasu yace "Bravo jare, toh amma shine bbu gayyata gun daurin auren?" Abuturrab yace "Naji kace min kana da aiki a government house" Sadeeq ya sosa kai yace "Yea xa mu je taro governor ne" Abuturrab yace "Are you a soldier also?" Sadeeq ya yamutsa fuska yace "I dodge that!" Abuturrab yace "That funny, you re related to d governor knn?" Sadeeq yace "Inaaa karere fa kawai, son dinsa is my best frnd shine xan rakasa dauko Abban nasa....." Abuturrab yyi dariya yace "Buh what did you study in schl?" Sadeeq ya gyara xama yace "Chemical Engineering, ina aiki a port Harcourt, na dau transfer na koma lagos naga duk shirme ne lagos din, kawai na dawo kd ynxu... Gombe daurin auren wani abokin frnd dina naje suka bata min rai kawai na biyo motar haya ko sani basu yi ba...." Abuturrab da ya saki baki yana kallonsa yace "Uhm that's nyc, where did you schl?" Sadeeq ya d'an yi shiru yana shafa sajensa, sai kuma yace "I always never want to talk about this because i schl in Abuja when my mate are schooling abroad!!!" dariya ssai Abuturrab yyi yace "Why is that" Sadeeq ya buda ido yace "Wai kar in xama terror in ji Abba" Abuturrab bai kuma cewa komai ba sae dai danne dariyarsa kawai yake, can dai yace "Toh ynxu xa ku je taro governor din ne?" Sadeeq yace "A'a bari kawai inje in shaida daurin auren new frnd" Abuturrab yyi murmushi yace "Alryt am grateful" Sadeeq yace "Yanxu dai ni bari in karasa kd sai in samo mana fararen shaddodi ko ya kaga" Dariya Abuturrab yyi bai ce komai ba, Sadeeq yace "Rubuta min number ka xan kira idan na taho, coz kunna waya ba tawa bace ynxu, i will get a frnds phone" gun driver suka karbi pen Abuturrab ya rubuta masa number snn ya basa Atm dinsa yace "Sai ka ciro min 100k sadakin da xan bada" daga haka ya rubuta masa pin din a bayan numbersa, Sadeeq ya karbi takardar yace "Don't worry gudunmawata knn, xan biya maka bride price din" Abuturrab ya buda ido sai kuma yyi dariya yyi patting shoulder dinsa yace "Allah bar mu" Sadeeq ya sosa kai yace "Kuma ya shirye mu" Abuturrab na dariya yace "Yeah, yeah" daga haka ya sauka a maraba mai motar ya wuce da Sadeeq. Abuturrab na sauka ya kalli agogonsa yaga daya saura hakan yasa ya nufi masallaci don yi azahar, wani gun me shago ya zauna bayan ya fito yana jiran Sadeeq, sai kusan biyu sadeeq ya kirasa yace Yana bakin titi shi yana ina, fitowa Abuturrab yyi suka hadu, Sadeeq yace "We need to get a hotel don ka shirya" hotel dake nan kusa suka nufa, Abuturrab na gama shiryawa ya kira Mijin Anty Maryam ya sanar da shi xae taho snn suka dau machine xuwa gidan mai gari.

*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫

By khaleesat Haiydar📚✍🏻

56.....

Suna isa gidan mai gari suka sauka a dai dai kofar gida Abuturrab na kare ma gun kallo ya fiddo dari biyar dake aljihunsa ya mika ma masu machine din, tuni Sadeeq ya nufi tabarmar dake shimfide kofar gidan da mutane a kai, Abuturrab ya bi bayansa, sai a sannan ya ga mijin Anty Maryam xaune cikin mutanen, kallo daya yyi masu ya gano waye mai garin ganin irin shigar da yayi, Sadeeq ya xauna kan tabarmar ya gaida su gaba daya, Abuturrab ma ya xauna duk ya gaishesu, mai gari ne yayi gyaran murya yace "Toh da wa xa a daura auren cikinsu?" Mijin Anty Maryam ya nuna masa Abuturrab, Mai gari yace "Ya sunansa?" Nan ma mijin Anty Maryam ne ya bada amsa, mai gari yace "Maa sha Allah, Malam Aminu yyi min bayanin komai Aliyu, na kuma ji tausayin ku ainun, amma ina son ka sani in har aka daura auren nn ka cuce yarinyar nn ko ka ci amanarta ko da so daya ne tamkar ka ci amanar musulunci ne, albarkacin islama kayi kkrin ganin ka rike ta da amana Aliyu, abu na biyu kada ka tilastata kace sae tayi addinin ka, ka bari tayi hakan don kanta, kai dai yi iyakar kkrin ka wajen nuna mata shi fa musulunci addini ne mai sauki, halayyanka gareta da irin xamantakewar da xaka yi da ita shi xae nuna mata hakan ba sai ka fito baro baro ka dinga fada mata ba, duk da addinin ku ya sha bam bam ta yrda ta baro iyayenta ta biyo ka don haka in dai ka cuceta ko dai dai da rana daya to Allah xae mata sakayya, ita kuma Allah ya mata rahama ta gane menene musulunci har tayi sha'awar dawowa cikinmu, ni xan xama waliyyinka in shaa Allah, shi kuma Malam Aminu xae xama nata, mun kuma yanke sadakinta a kan dubu hamsin....." Duk jikin Abuturrab yyi sanyi hakan yasa bai iya dagowa ya kallesu ba, Maminsa ce ta fado masa, to haka xa a daura masa aure mahaifiyarsa bata sani ba bare ta sa masa albarka, irin ynda mami ta ci buri kan aurensa ace xa ayi sa ynxu bata sani ba, tunanin hakan ya sakko masa da mugun sanyin jiki duk yaga gaba daya bai kyauta mata ba, Sadeeq ne ya kirgo dubu Hamsin kmr jira yake ya ajiye masu, nan take aka daura auren Aliyu da Samha akan sadakin da aka bayar, har lkcn Abuturrab bai iya ya dago kansa da yaji yyi masa nauyi ba, Malam Aminu ya jawo ledan goronsa da alawa ya bude ya shiga rarrabawa mutanen dake xaune gun ana ta sa ma auren albarka, ganin Shirun Abuturrab yyi yawa Sadeeq ya tabo sa sai a snn ya dago da sauri, Murmushi ya kirkira cikin sanyin murya yace "Allah ya ba ni ikon riketa a bisa koyarwar addinina ya kuma taya ni fahimtar da ita gaskiya da wuri..." Duk aka amsa masa da Ameeen, basu wani jima ba suka mike gaba daya har da Malam Aminu suka yi ma mai gari da sauran mutanen gun godiya snn suka wuce, Malam Aminu yace "Yanxu xa ku je can gun Antyn tata tana son ganinku wai, amma ba gida xa ku sameta ba, sae mu je in raka ku inda xa ku sameta" har suka isa gidan Malam Aminu nasiha yake ma Abuturrab kan kada ya bari Samha tayi da ta sanin amincewa da shi, ya dinga nuna masa kada ya manta ita kadai ke gare iyayenta bbu irin jin ddin da ba a shayar da ita ba a rayuwa bbu gatan da bata samu ba tun daga kan iyayen nata har kan yan uwa, amma lkci daya ta yrda ta amince da shi ta guji kowa nata ta biyosa, kada ya bari wataran maganganun da mahaifiyarta ke yawan yi na cewa ae musulmai basu da alkawari basu da amana ya xamto gaskiya ya nuna karya take bbu abinda ya kai musulunci gaskiya da rikon amana, ya nuna mata musulunci Rahama ne, Abuturrab bai iya yace masa komai ba kansa a kasa, sae Sadeeq dake ta cewa wnn gaskiya ne, xaune suka tadda Anty Maryam tsakar gidan uwar dakinta bayan an masu ixinin shigowa, nn dai malam Aminu yyi masu sallama don xae koma gun harkokinsa ya bar su daga su sai Anty Maryam da uwar dakinta Hajiya Salamatu, cikin sanyin murya Anty Maryam tace "Aliyu kai musulmi ne ni musulma ce, mun san Do's and don't din addininmu, don't let my daughter regret trusting a musulim, make her fall for it plss, show her it's teaching and aim, Samantha ita kadae ke gare yayana don't ruin her life, idan ka ci amanarta tamkar ka ci amanar addininmu ne...." Tana magana ne hawaye cike idonta, Abuturrab ya kasa kallonta, Hajiya Salamatu tace "Ina jin ta fada maka duk abinda ya kamata D'an nan, kar ka ba mu kunya ka rike amana, Allah kuma ya kawo sassauci cikin lamarin ya huci xuciyar iyayenku, sae kaga ta dalilin hakan Allahu ya dawo da iyayenta hanya madaidaiciya, ita kuma ina mata fatan amsan kalmar Shahada nan ba da ddewa ba, sae dai hakan xae faru ne idan ka rike a bisa koyarwar Musulunci sae kaga don kanta hakan ya burgeta..." A hankali Abuturrab yace "In shaa Allah" Anty Maryam tace "To yanxu kuma ina ku ka nufa?" Abuturrab ya d'an shiru sai kuma yace "Kila mu koma Gombe can ya fi kwanciyar hankali Anty" Cikin sanyin murya Anty Maryam tace "Toh Allah yasa hakan da alkhairi, idan Babansu Asiya ya yrda sae in bi ku in ga inda ku ke...." Ya d'an yi murnushi yace "Toh Allah yasa ya yrda Anty" Hajiya Salamatu tace "Toh yanxu ina ita Rebeccan take?" Abuturrab yace "Zaria muka kai ta da abokina" Anty Maryam tace "Gun wa a Zaria?" Abuturrab yace "Gidansu yarinyar da xae aura yasa muka kai ta" Murmushi kawai Sadeeq yyi, Hajiya Salamatu tace "Toh dama ina son ita ma mu xauna da ita ne, sae dai kuma dawowanta nn da hatsari sosai, kanwata na Zaria ko gobe sae mu je can da Maryam ku kai mana ita gidan kanwar tawa" Abuturrab yace "Toh Allah ya kai mu" Anty Maryam tace "Shknn Aliyu Allah ubangiji ya hada kan ku ya baka ikon rikon amana, xa ku iya tafiya" Sadeeq ne yyi masu godiya snn Abuturrab, duk suka mike Sadeeq ya ciro sauran dubu hamsin din ya ajiye gabansu yace "Ga wannan bbu yawa Anty..." Bbu ynda Anty Maryam da Hajiya Salamatu basu yi ba kan su tafi da kudinsu amma basu dauka ba suka fita, samun Machine bai masu wahala ba a kofar gidan, suna isa titi Sadeeq yace "Ya ne frnd na ga mood dinka ya canxa, you ought to be happy ta xama mallakin ka yanxu ae" Cikin sanyin Murya Abuturrab yace "Sadeeq my mum knew nothing about this, kaga bn fita hakkinta ba, bn mata adalci ba, am just restless" daga haka ya nemi gu ya xauna ya rike kansa, Sadeeq ya durkusa gabansa yace "And that's very through, kana bukatar addu'anta, kana bukatar ta sa maka albarka" Dago kai Abuturrab yyi lkci daya idonsa ya kada ya kasa cewa komai, Sadeeq yace "Here is an advice, why not ka je kano, you do all you can ku hadu da ita secretly sae kayi mata bayanin komai, uwa ce xata fahimce ka...." Shiru Abuturrab yyi sae kuma ya gyada kai yace "Yea, gaskiya hakan xan yi frnd, xan je gidan sister dinta, sae mu hadu a can in shaa Allah, buh if you're less busy plss mu je tare" Sadeeq ya shafa kansa bai ce komai ba, sae kuma can yace "Alryt ba damuwa mu je frnd..." Abuturrab ya mike yace "That's kind of you" Sadeeq yace "Za mu fara xuwa Zaria kenan?" Abuturrab yace "Noo, mu tafi kanon kawai, but before then i need to change" Boutique suka nufa suka siya kananun kaya da P cap snn suka koma hotel din da suka yi lodge, suna gama shiryawa suka fito suka samu mota xuwa kano. Sai kusan karfe uku da rabi suka shigo kano, suna fitowa daga park Abuturrab yasa p cap dinsa yanda in dai ba durkusawa kayi ba to ba lallai ka ga fuskarsa ba, Sadeeq yyi dariya yace "Saboda tsaro ba don tsoro ba koh?" Dariya Abuturrab yyi shi ma yace "Sure kai ma daura naka" Sadeeq ya daura cap din shi ma, adai daita sahu suka dauka da xae kai su har Nasarrawa, basu suka isa gidan Hajiya Mariya ba sae kusan Hudu da rabi, suka sauka a sahun suka basa kudinsa, lkci daya gaban Abuturrab ya shiga faduwa, daga cikin p cap din ya dinga surveying anguwar kafin ya kwankwasa gate mai gadi ya bude masu, ya daga hular kansa suka gaisa ya mayar snn suka shiga gidan da Sadeeq. Babban parlon Small Mum din tasa ya nufa mai aiki ta bude masu kofa bayan sun danna bell suka shiga parlon suka xauna, ta wuce sama don kiran Hajiya Mariya, Abuturrab ya kalli Sadeeq yace "Kasan me?" Sadeeq ya girgixa masa kai, a hankali yace "I'm just restless" Sadeeq yace "Chill, bbu abinda xae faru in shaa Allah, mu da muka san Allah na tare da mu...." Saukowar Hajiya Mariya yasa yyi shiru, ta karaso parlon tana kallonsu gaba daya duk da ba ganin fuskarsa take ba amma ta gane Abuturrab ne, shi kam ya ki kallon inda take har sae da ta iso gabansa, a hankali tace "Aliyuuu" dago kai yyi ya cire cap din kansa, kasa boye farin cikinta tayi, ya mike ya rungumeta yana murmushi yace "Sweeet Mum" dago kansa tayi lkci daya farin cikin yyi fading ganin yanda ya rame ba kadan ba sai haskensa dake nn kawae, shafa kansa tayi cikin sanyin murya tace "Daga ina kake Aliyu!" Komawa baya yyi ya nuna mata Sadeeq yace "Meet my frnd, a brother!"

*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫

By khaleesat Haiydar📚✍🏻

57.....

Kallon Sadeeq Hajiya Mariya tayi, can tayi murmushi ta nufesa shi ma tace "Welcome Son! Kai ne d'an wajen Col Ishaq koh?" Sadeeq yayi kasa da kai ya gaisheta ta amsa har lkcn murmushi dauke fuskarta, can ta kalli Abuturrab tace "Aliyu daga ina ku ke?" Ya d'an shafa kai a hankali yace "Kaduna Mum" dawowa tayi kusa da shi ta xauna da damuwa tace "Aliyu ina yarinyar take?" Yace "Mum tana kaduna" Shiru tayi tana kallonsa, can ta mike ta nufi fridge ta dauko masu ruwa da drink ta ajiye masu, kamar Abuturrab jira yake ya dau exotic drink din ya bude ya kai baki ya sha iya wanda xai sha ya ajiye sauran, Hajiya Mariya sai kallonsa take, jingina yyi jikinta cikin sanyin murya yace "Mum Mamina fa?" Hajiya Mariya ltayi shiru har sai da ya kalleta snn tace "Tana gida Aliyu, fushi take da kai..." da sauri yace "Plss ki kirata ta xo nan momma, i came because of her...." Ta girgixa kai tace "I don't think xata yrda ta xo, beside i guess Abban ka na gida yanxu haka" da damuwa yace "Plss Mum ki lallaba min ita ta xo in ganta ko xan ji dadi" Hajiya Mariya bata ce komai ba, can tace "Toh ita yarinyar gun wa ka bar ta?" Yace "Sun hadu da aunt dinta" Hajiya Mariya ta buda ido tace "Haba, sai aka yi ya kenan?" Ya langwabar da kai yace "Musulma ce aunt din, Mijinta kuma ya bani shawarar aurenta kawai, daxu aka daura auren ma..." mikewa Hajiya Mariya tayi tana kallonsa da mamaki tace "Aliyuu" A sanyaye yace "I have no option mum, and... I love her, shi yasa na taho gun mami i shud ask for forgiveness, i know i wronged you all, but ba laifina bane Mumy" rike kansa yyi ya lumshe ido, Hajiya Mariya bata kuma cewa komai ba ya sakko kasa a hankali on his kneels yace "Pls ki kira min ita mum..." Hajiya Mariya ta xauna gefen kujera tayi tagumi bata ce komai ba, Sadeeq ya lumshe ido ya bude yace "Mumy plsss ayi hakuri for the sake of islam..." Bata kuma cewa komai ba ta mike ta nufi daki, Sadeeq ya kallesa yace "Chill Guy xata kira mana ita in shaa Allah" Hajiya Mariya na isa bedroom dinta ta dau wayarta ta xauna gefen gado tayi dialing number yayarta ta kai wayar kunne, Mami dake dakin Abban Abuturrab tana gyara masa press dinsa shi kuma yana xaune dakin kan resting chair idonsa sanye da glass yana duba newspaper din ranan da bai samu ya duba ba, kallon wayarta dake ajiye gefen gado tayi jin yana ring, ta isa gun wayar ta dauka, ganin Mariya ce ta daga ta kai kunne hadde da sallama, daga daya bangaren Hajiya Mariya tace "Ina yini yaya?" Mami tace "Lafiya Mariya ya gidan?" Hajiya Mariya tace "Alhmdllh, ya su Ramla?" Mami tace "Lafiya lau su ke, sun je Saloon" Hajiya Mariya ta d'an yi shiru har sai da Mami tace "Hello!" Snn a hankali tace "Yaya Aliyu na nan gida na, idan Col bai gida ki daure ki taho don Allah" Mami bata san lkcn da ta xauna gefen gado ba lkci daya duk tayi sanyi ta kasa cewa komai, Abba dai kallonta kawai yake ta gefen idonsa dake cikin glass yana lura da ita, Jin shirun da Mami tayi yasa cikin sanyin murya Hajiya Mariya tace "Kinyi shiru yaya" Mami ta saci kallon Abba da yayi saurin dauke idonsa ya mayar kan newspaper din hannunsa, Katse wayar tayi ta ajiye, a hankali tace "Ba jin ki nake ba Mariya" mikewa tayi ta ci gaba da abinda take sai dai da ganinta kasan hankalinta bai ma kan abinda take, kallonta kawai Abba yake ta glass, Hajiya Mariya ta kalli wayarta jin yayarta ta katse, duk jikinta yyi sanyi ta kuma dialing number, juyowa Mami tayi da sauri jin karan wayar kuma, suka hada ido da Abba ta karasa ta dauka ta kai kunne tace "Mariya ba jin ki nake ba ki bari anjima ki kira, the network is fluctuating" daga haka ta katse wayar ta ci gaba da abinda take, tana gamawa ta dau wayarta tace "Yallabai bari in je a fara shirin girkin Dinner!" Ba tare da ya kalleta ba yace "Ok" daga haka ta nufi kofa ya bi ta da ido har ta fita. Mami na isa dakinta ta kulle kofa ta shiga kiran kanwar tata, Hajiya Mariya dake xuba ma su Aliyu abinci ta mike ta dau wayarta jin ringing, tana ganin yayarta ce ta daga da sauri ta nufi daki, Mami tace "Mariya kika ce Aliyu na gidan ki?" Tace "Ehh yaya, ki daure ki taho don Allah...." Mami tayi shiru, sai kuma cikin sanyin murya tace "Col na gida" Hajiya Mariya ta buda ido tace "Toh to ki bari kar ki xo yaya, ko xuwa gobe sai ki samu inda kika ce masa xa ki, nasan xa su kwana ne ma" Mami da taji kamar ko yanxu Aliyu na iya disappear kuma ta girgixa kai da sauri tace "Xan san yanda na fito Mariya..." Daga haka ta katse wayar, rasa abun yi tayi, ta kusa minti biyar a tsaye kafin ta fita, dakin mai gidan nata ta nufa ta gansa tsaye kusa da window waya kare kunnensa,
Bai cire wayar ba sae dai ba magana yake ba har ta karaso tace "Yallabai na mance ban gaya maka nama ya kare ba balle a kawo wani, ynxu ko wanda xa ayi amfani da ma bbu" Ya katse wayar kunnensa yace "Toh yanxu ya xa ayi?" Tace "Fita xan yi da mota kawai in siyo wanda xa ayi amfani da, tunda yaran basa nan kuma driver na can tare da su" Abba ya daga kafada yace "If that's ok by you, ga Atm can, sai ki siyo har na amfanin gobe, idan ya so xuwa jibi sae a kawo maku" Tace "Toh shknn, ko xa mu je tare?" Girgixa kai yyi yace "Xan yi bak'i, ki dai siyo min Ginger powder for tea" tace "Alryt" daga haka ta nufi kofa, yace "Atm card din fah" ba tare da ta kallesa ba tace "Akwai cash hannuna" bin ta yyi da ido har ta fita dakin, Makullin mota kawai ta dauka a dakin ta bayan ta saka hijab ta fita ta dau mota ta bar gidan, ta window Abba ke kallonta har ta kure masa, d'an murmushi Abba yyi ya sake curtain din.

*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫

By Khaleesat Haiydar📚✍🏻

58.....

A hankali Mami ke driving din, gaba daya ta rasa dalilin da yasa hankalinta ya ki kwanciya tun da ta bar gida, parking tayi ta kafa ma steering ido kamar me naxari, but it's very unusual tace ma Col xata fita lkci daya ya bar ta, sannan shi mutum ne da bai son sae abu ya kare a gaya masa sae gashi yau ko canza fuska bai yi ba, girgixa kai tayi ta dau wayarta ta shiga kiran Hajiya Mariya, tana dauka cikin sanyin murya tace "Mariya, ina tunanin Col ya gano ni, tun da na fito gida hankalina ya ki kwanciya kuma yasan kin kira ni, Aliyu ya bar gidan ki, but make him promise baxai tafi ba, don Allah kar ya tafi" Hajiya Mariya da hankalinta ya tashi ita ma tace "Toh yaya nasan baxae tafi ba baku hadu ba...." Daga haka ta katse wayar ta fito parlor da sauri tana kallon Abuturrab tace "Aliyu, Mami ta kira yanxu, it seems Abba ya gano kiran da nayi mata, you two have to leave now immediately...." Ko rufe baki bata yi ba Abuturrab ya mike kamar wanda aka tsikara haka ma Sadeeq, Hajiya Mariya tace "Amma don Allah don Annabi Aliyu kar ku wuce, make that promise to me son!" Cap dinsa ya dauka yace "Baxan tafi ban ga Mami ba ae, xa mu yi waya mum" daga haka ya ja hannun Sadeeq suka fice, ta bi su da ido a sanyaye, Abuturrab bai yrda sun bi main road ba suka canxa hanya daga shi har Sadeeq din a dar suke, basu xarce ko ina ba sae wani local hotel. Mami na kiran Hajiya Mariya dama kasuwa kawai ta wuce ta siya abinda xata siya, bata yi mamakin rashin ganin mai gidan nata a gida ba, da yake su Ramla sun dawo su ta hada da girkin tunda masu girkin basa nan ta wuce dakinta kawai. Ko minti sha biyar ba ayi da fitansu Aliyu ba mai gadi ya xo yana bubbuga kofa, Hajiya Mariya da ta xauna ta rafka tagumi a parlon ta mike da sauri ta dau hijab ta sa ta isa kofar ta bude, ganin yanayin mai gadin tace "Lafiya Sulaiman?" Yace "Hajiya ba lafiya ba, sojoji ne birjik bakin gate wai kuma gidan nan suka xo xa su shiga...." Nan da nan Hajiya Mariya ta hade rai tace "Sai kace masu me?" Yace "Ban samu damar magana ba ni dai na yo nan a guje...." Tsit yyi ganin Sojojin sun shigo suna tahowa Balcony, wasu kuma sun xaga baya, wasu na tsaye daga gate, Hajiya Mariya ta wani murtuke fuska ganin Abban Abuturrab don shi ne ma gaba, gabanta ya isa yace "Ki ban number mai gidan ki mun shigo masa gida ba izini..." Tace "Ko me ya janyo hakan?" Yace "Za ki sani nan ba da dadewa ba, basu hanya su shiga...." Ta girgixa kai tace "Babu wannan xancen Abban Ramla, ya xa ku
shigo min gida haka ina matsayin matar aure mai gidana bai nan, wannan ko ni nace Aliyu ya bar gida da yar mutane sai haka ai, ni wllh ina ganin mutuncin ka a matsayin ka na mijin yayata banda haka bbu abinda xai sa na ci gaba da daukan wnn cin fuskar haka...." Wayarta ta latsa a fusace ta kira Mami, Mami na dagawa tace "Yaya kiyi hakuri, amma gaskiya bana son wnn abinda Abbansu Ramla ke min, duk fadin kano ya rasa warce xae dinga xargi kan barin Aliyu gida sae ni, a kan wani dalili xae kwaso min bariki guda na soldiers ya shigo min gida ko mai gidana bai sani ba...." Mami dai na sauraranta bata ce komai ba sai dai ita ma gaba daya ranta yyi mugun baci, katse wayar tayi tace "Toh sai ku shiga ku fiddo Aliyu...." Daga haka ta fice fuu ta bar masu gidan gaba daya. Hakan bai hana Abba yasa an duba masa gidan ciki da bai ba amma bbu Aliyu bbu alamarsa. Sae bayan Magrib ya koma gida, har lkcn kuma xuciyarsa ta kasa yrda cewar Aliyu bai je gidan Hajiya Mariya ba, har karfe tara Mami bata je part dinsa ba, abinci ma su Ramla tasa suka kai masa, tun da suke bata taba yi masa irin haka ba, da yaso sharewa amma kawai ya tashi ya tafi can dakin

Please Login or Register in order to submit comment