Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Maryam tayi tayi hamdala a xuciyarta, ba a dau lkci ba Sarah ta dawo ta dau dankwalinta ta daura da jakar hannunta tace "Gobe xan xo Maryam, ban san me ke damun Sis Rachael ba" daga haka ta fice daga gidan, Maryam ta mike ta sa sakata a gidan ta dawo.

*Haske writers asso*
๐Ÿ’ซ *Noorul Huda*๐Ÿ’ซ

By Khaleesat Haiydar๐Ÿ“šโœ๐Ÿป

49.....

Da sauri Anty Maryam ta karasa dakin da suke, tana bude kofar Samha ta mike da sauri ta karasa da gudu ta rungume ta, Anty Maryam kam kallon Abuturrab kawai take, Wanda hakan yasa ya mike ya gaisheta, bata iya ta amsa ba don duk jikinta yayi sanyi ganin kyansa da kwarjini amma ya gwammace yayi ta garari sbda wacce addininsu ya sha bam bam, can dai tayi karfin halin cewa "Bawan Allah don me xaka gudu da yar mutane, and what are you up to?" Sauke kansa kasa yyi kamar baxai ce komai ba sai kuma a hankali yace "Saboda ina sonta Anty, so kuma na aure snn ina son musuluntar da ita ta dawo hanya madaidaiciya" Kallonsa kawai Anty Maryam take, ya karasa gabanta yace "Ki yarda da ni Anty ina sonta sbda Allah ba don in cuce ta ba...." Anty Maryam ta girgixa kai tace "Amma kana ganin hakan shine dai dai, rayuwa fa kake da warce ba muharramar ka ba, wanda addinin mu bai yarje mana da haka ba, ka sani amma ka bi son xuciya...." Yace "Noo Anty, i tried my best na ganin ban saba ma addinina ba all through our stay together" tace "Toh me ya hanaka auren nata har ynxu yau wataninku kusan biyu da barin gida?" Kallon Samha yayi sai dai bai ce komai ba, Anty Maryam tace "Kayi shiru?" Yace "Bana son watarana tayi tunanin ina using advantage din aurenta Anty...." Juyawa Anty Maryam tayi ta bar bakin kofar, Samha ta kallesa snn ta bi bayanta, Ko minti biyar basu yi da fita ba Anty Maryam ta dawo dakin, karasawa tayi inda yake ta zauna kan darduman dakin tace "Aliyu koh?" Kai ya gyada mata, tace "Kaga mahaifiyar Samantha na gidan nn ynxu haka nasan tana within,l.. ban san ka ba, ban san daga inda kake ba, ban san halin ka ba, amma nasan kai musulmi ne d'an uwana, hakan yasa xan baka yarda ta dari bisa dari, nasan da baka son Samantha tsakani da Allah baxa ka gwammace irin wnn rayuwar ba, don haka Aliyu kafin ku bar nan ina son ya kasance Samantha matar ka ce ta sunna, if you've tried ur best abiding to the laws of ur religion wataran hakan gagararka xai yi.... In har da gaske kake ka bari a daura maku aure komai xai fi xuwa da sauki" a sanyaye yace "Nima nafi son haka Anty, ban sai san ta inda xan fara bane...." Anty Maryam tace "Dawowar Samantha musulunci ba abu bane mai wahala ni xan taimaka maka, yanxu dai it's better ka tafi ka samu hotel, ita kuma xan kai ta gidan kawata, don mahaifiyarta na iya dawowa nn a ko wanni lkci." Yace "Toh nagode" tace "Amma all this while kuna ina da ita?" Babu bata lkci ya bata labarin d'an rayuwar da suka yi a gombe da Ummi, sai dai bai gaya mata ga abinda yasa suka bar gombe ba sai ce mata yyi kawai ziyara suka xo kawo mata" Ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh shknn Aliyu Allah ya maku jagora, ni nafi kowa farin ciki da abunda ya faru Allah yasa lkcn fitowar yayana daga 6ata ne ya xo, Allah yasa ta dalilin haka ya gane gaskiya" Abuturrab yace "Ameen" mikewa tayi tace "Bari in xubo maka abinci" daga haka ta fita. Shinkafa da wake da mai da yaji sai kayan vegetables a kai ta kawo masa da ruwa a jug, yayi mata godiya ta fita. Mai gidanta ta kira ta sanar da shi komai ta kuma bukaci ya dawo don su hadu da Abuturrab, bayan yan mintuna ya shigo gidan, a tare suka shiga gun Abutturrab, ya gaida mai gidan nata da ladabi, Duk suka xauna dakin, Mijin Anty Maryam mai suna Aminu da ke ta kallon Abuturrab yace "Sannu da xuwa bawan Allah" Abuturrab yayi murmushi yace "Nagode" tambayoyi kmr yanda Anty Maryam tayi masa ya shiga yi masa shi ma, sosai mijin Anty Maryam ya jinjina karfin hali irin na Abuturrab daga karshe shi ma ya nuna gwara kawai ayi auren komai xai fi xuwa da sauki. A can Gombe kuwa tunda Ummi ta dawo Khadija ta fadi mata ai fa tun safe Abuturrab suka fita da Samha, jikinta yyi sanyi don lkci daya ta fahimci tafiya yyi da ita barin da taji wayarsa kashe tun daxu, amma bata nuna ba ta shige bedroom kawai ta kwanta tana tunanin wani rayuwar kuma xa su yi. Sun yanke akan cewa gobe Abuturrab xa su je gun mai gari da Mijin Anty Maryam daga haka kuma Anty Maryam tace ya wuce hotel kafin Mahaifiyar Samha ta dawo ita kuma xata je kai Samha gun kawarta, Sallama yayi masu ya fita, sai dai bai ji ddin rashin ganinta ba har ya bar gidan ita ko tana parlon aunt din tata bacci ya dauketa. Karfe shidda Anty Maryam ta sa ta shirya bayan tayi wanka ta bata nikab da hijabi snn suka fita a lkcn ma yaranta sun dawo daga islamiyya, bata bari sun lura da Samha ba har suka bar gidan, Addu'a Anty Maryam ta dinga yi Allah yasa Rebecca bata anguwannin don tana da kawaye yan coci kamar ta sosai a wajajen, tana rike da hannun Samha sai sauri take su isa bakin titi ta samu machine su hau, ta layin da ke gefensu taji an kwada mata kira, ta juya da sauri cike da faduwar gaba ta ga Sarah ce tsaye kofar wani gida, Anty Maryam da ke ci gaba da jan hannun Samha da ta tsorata ita ma taki tsayawa tace "nan kika xo ashe" ganin Sarah na tahowa yasa hanjin cikinta yayi mugun kadawa tace "Gani xan xo yanxu, bakuwa xan raka" Sarah da har ta kusa isowa gun su sbda saurin da take tace "Sis Rebecca nake jira tun daxu wllh, haba tun fa daxu fada take...." Tuni Samha ta janye hannunta a na Anty Maryam tayi gaba ko ina na jikinta na rawa, Sarah ta bi ta da ido, Anty Maryam na ganin haka ta tsaya gabanta ta ynda baxa ta dinga ganin Samha ba tace "Toh ko mu je in bata hakuri ni fa ban san me ya faru ba" Sarah tace "Jesus, yarinyar nan yanayin Samantha gareta, wacece ita?" Anty Maryam tayi dariyar yake cike da karfin hali tace "Samantha da Nikab kuma? yar wata uwar daki na ce... Haka take fama da rufe fuska" Sarah dake ta kkrin sake kallon Samha da tayi nisa sosai tace "Har tafiyar fa Maryam, Jesus of Nazareth" Maryam tace "Ohh don dai Samanthar ce a ranki, ynxu mu shiga in ba sister hakuri sai ta iya hada ni da yaya" Daga haka ta ja hannunta suka nufi gidan, Suna shiga Maryam tayi wani salati tace "Amma yarinyar nn Sha sha sha ce kinga kudin motar fa a hannuna bata karba ba" Sarah tace "Ayya to kiyi sauri ki isketa mana" bata rufe baki ba Maryam ta fice da sauri tace "Ina dawowa ynxu" Can bakin titi ta iske Samha ta rakube jikin wani shago, bbu wata wata ta tsayar masu da machine biyu ta fadi inda xa su suka hau suka bar gun tana hamdala a xuciyarta.

*Haske writers asso*

Plss ana min uxuri na rasa ynda xan dinga squeezing time ne, snn kuma there is shortage of power a inda nake ynxu wllh shi yasa yake taking time.
๐Ÿ’ซ *Noorul Huda*๐Ÿ’ซ

By Khaleesat Haiydar๐Ÿ“šโœ๐Ÿป

50......

Suna isa gidan Anty Maryam ta shiga Samha na biye da ita a baya, Anty Maryam suka gaisa da aminiyar tata mai suna Amina daga haka tace mata xata bar Samha nan gidan xuwa gobe ta xo ta dauketa, bbu bata lkci ta bar gidan ta koma gida. Wani hotel Abuturrab ya samu yyi lodge, da ya tuna abinda ya faru gidan Anty Maryam sai abun ya basa dariya, sai dai hankalinsa ya kasa kwanciya ya rasa dalili, yana yin magrib Coffee kadai ya iya sha ya dawo room dinsa. Karfe takwas da yan mintuna Ummi na xaune daki gaban computer sai dai gaba daya hankalinta bai kai, sosai su Abuturrab suka tsaya mata don bata san halin da xa su je su shiga ba kuma, jawo wayarta tayi for the 5th time within that period ta sake dialing numbersa amma switch off ta dafe kai, bude kofar dakinta aka yi ta dago da sauri Yusuf ya karaso ya xauna kujera yana kallonta yace "Sannu da aiki Ummi" ba tare da ta kallesa ba idonsa a kan screen din computer tace "Yauwa" Ya d'an yi murmushi yace "Ummi kar fa ki sa ma kanki damuwa, dama ni ina ganin Aliyu nasan ba shi da gaskiya, as in the way he does his things ma xaka gane hakan, baka taba gane abinda ke ransa na lura, he can be a silent killer, at the first place na tambayeki hadinsa da Samha kika ki gaya min, daga bincikena tun a jiya na gano Samha ba matarsa bace, though bance xaman banxa suke ba, amma daga duk alamu rabo ta da iyayenta yayi may be for his selfish interest, tun daga lkcn da kika ce min bai ji na fara gano wasu abubuwan.... But Ummi me yasa kika boye min kilan da hakan da ya faru ynxu bai faru ba, i would have kept an eye...." Kallonsa Ummi tayi a karo na farko tace "Bana son xancen Yusuf" mikewa yayi yace "Aiit, buh am gonna fish him out idan Allah ya yarda" daga haka ya fita. Anty Maryam na xaune tsakar gida a ranan tana wanke kwanukan da suka ci abinci amma hankalinta na ga tunanin decision din da suka yanke da mai gidanta na aura ma Aliyu Yar d'an uwanta, bude kofar soro aka yi ta juya da sauri taga Rachael ce da Sarah, Duk da ba wuta tsakar gidan sai hasken wata hakan bai hanata ganin yanda Rachael ta daure fuska ba tana tahowa kamar xata tashi sama, Anty Maryam ta dauke kai tana murmushi ta ci gaba da wanke wankenta, sarah ce kadai tayi mata sannu da gida suka shige parlor, Anty Maryam ta mike ta dau abinci ta kai masu ta fito, ko da ta gama wanke wanken xamanta tayi tsakar gida tana sake saken yanda al'amarin gobe xai kasance, can ta mike ta shiga dakin mai gidanta ta xauna tana kallonsa tace "Abbansu Asiya ya kake ganin xa ayi gobe ne wai" Yace "Gun mai gari xa mu je a daura auren sai su tafi duk inda xa su, matukar xai iya kula da ita, na kuma ga yana sonta sosai don da ganinsa kasan ba karamin mutum bane." Da damuwa tace "To fa bata amshi musulunci ba har ynxu" yayi murmushi yace "Ba yar ki bace kin san yanda xa ki bi da ita ai, sai dai kuma kada a tilastata don in har aka yi haka tana iya komawa gidan jiya tun da ba da son ranta ba.... Ko kin mance yanda muka yi da ke Maryam" ganin dariyar da yyi ta hade rai tace "A'a ni baka aureni a Christian ba ni musulma ce a lkcn ma" yace "Amma a lkcn abubuwan da kike yi meye banbancin ki da Christians din, ba fa gori nake maki ba rabin rai kawae dai magana ce" ta tabe baki tace "Ae don ina gun yayana ne lkcn Kuma mahaifiyar Samantha ce matsayin uwata...." Yace "Toh kar ki ji komai ni nasan da kanta xata yi sha'awar addininmu ba sai an mata dole ba, at the first ma da bata son musulunci baxata yarda da musulmi ba har su gudu tare ta bar iyayenta" Anty Maryam tace "Haka ne, kuma kaga lkcn da take xuwa hutu nan bata kin yi duk abinda na sa ta tun daga kan sllh har xuwa tafiya islamiyya da su Asiya" yace "Toh kin ga" Mikewa tayi tace "Bari in je can parlor" daga haka ta fita. Washegari da ya kasance friday da safe Abuturrab ya fito ya nemi d'an boutique ya siya kaya da kudin dake hannunsa, daga haka ya nufi Atm machine don cire kudi, takaici ne ya ishesa don Atm machine din da ya gani bai fi biyu ba kuma duk ba kudi, kallon agogon hannunsa yayi yaga tara bata yi ba, kawai yayi deciding ya wuce cikin kaduna kawae, sai da ya koma hotel ya shirya snn ya dau hanya, yana isa ya kunna wayarsa tunawa da yyi sun yi exchanging number da mijin Anty Maryam, yana cire kudin ya shiga tunanin me xai siya kuma kafin ya koma wayarsa ya shiga ring Sadeeq ya gani jikin Screen din, har ya fara tunanin waye kuma sadeeq kawai ya tuna gayen da suka hau mota tare tun daga gombe, dagawa yyi, nan suka gaisa da fara'a Abuturrab yace "Kasan jiya fa can maraba muka wuce amma yanxu ina cikin kaduna na xo cire kudi..." Sadeeq yace "Au haba, a ina kake yanxun?" Abuturrab ya kalli gun yace "Ina bypass" Sadeeq yace "Haba to ka karaso nan gidanmu mana kafin ka koma" Abuturrab ya kalli agogo sai dai bai son Sadeeq ya ga kamar yyi shun dinsa, yace "Funny you, ni da nake sauri" Sadeeq yace "Sai in kai ka har maraban da motata" Abuturrab yyi jim don bai son exposing secret dinsa ma kowa kuma, can dai yace "Haba don xan xo gidan ku sai ince sai ka mayar dani, bari in taho sharp sharp in koma ba sai ka yi wahalan kai ni ba" Sadeeq yace "Alryt" address ya tura ma Abuturrab da yake yasan garin xuwa gidan bai yi masa wahala ba sai dai ba dai nisa ba don sai kallon agogo yake, babban anguwa ce ta masu abun hannu, Sadeeq ya fito daga wani kantamemen gida mai dauke da gate biyu kai da ganin gidan kasan naira ya xauna, nan suka gaisa sadeeq na dariya yace "Ashe dai xaka gane..." Abuturrab yace "Haba dai ai ba wani wahala" daga haka suka shiga gidan sadeeq ya kai sa har babban parlon gidan, Abuturrab na xama ya ji gabansa na faduwa ya rasa dalili, Sadeeq na kallon kanwarsa da ta fito yace "Kiyi setting mana breakfast a bedroom dina" tace "Toh" sannan ta gaida Abuturrab ta koma kitchen, Sadeeq yace "This is our home, you feel free frnd" Abuturrab yayi murmushin karfin hali yace "Sure" Ana bude kofar parlor ya waiga da sauri kamar jira yake, bai san lkcn da ya mike tsaye yana kallon mutumin dake kallonsa shi ma a bakin kofar ba, Sadeeq ma ya mike yace "He is my Dad...." Abuturrab ya kallesa ya kirkiri murmushi yace "Ohh alryt" juyawa Mutumin yyi ya fita, nan hankalin Abuturrab yayi mugun tashi, ya dake ya koma ya xauna, Sadeeq dake ta studying dinsa yace "Any problem Aliyu?" Wara ido yayi yace "Ohh nothing Sadeeq" ba a dau lkci ba mutumin ya dawo parlor, sai a snn Abuturrab ya gaida shi kansa a kasa, mutumin ya amsa yayi wucewarsa Sama, mikewa Abuturrab yyi yana kallon Sadeeq yace "Let me answer a call in dawo" daga haka yayi waje da sauri, wani mugun faduwa gabansa yyi ganin mutanen da bai gani ba lkcn da xa su shigo tsaye bakin gate wato dai soldiers in uniform, dakewa yayi ya karasa xuciyarsa na bugawa ganin kallon da soldiers din ke masa kawai ya juya ya koma ciki da sauri yana furta innalillahi a xuciyarsa, Yana shiga parlorn ya isa gun Sadeeq da sauri, Sadeeq ya mike da sauri ganin tashin hankali bayyane fuskarsa yace "Aliyu lafiya" Abuturrab yace "Nooo, help me out now plss!! ur dad.... Abokin Abba na ne" Sadeeq dake kallonsa da mamaki yace "Then?" Abuturrab ya kamo hannunsa yace "Don Allah make a way out for me nayi ma Abbana babban laifi i left home for months, nasan kilan yanxu ya ma kirasa wllh.... Plss" tsit Abuturrab yayi ganin Col Ishaq yana saukowa stairs, da sauri sadeeq yace "Haba to meye baxa ka hau sama mu yi break ba sai a nan frnd, plss mu tafi bedroom dina, it will be more convenient there."

*Haske writers asso*

Afuwan for the delay ๐Ÿ˜Ž
๐Ÿ’ซ *Noorul Huda*๐Ÿ’ซ

By khaleesat Haiydar๐Ÿ“šโœ๐Ÿป

51.....

Abuturrab ya gyada kai yana kirkiran murmushi yace "Toh... toh mu tafi dakin" Ta gefen mahaifin Sadeeq suka wuce xuwa dakin Sadeeq din, Sadeeq ya sa ma kofar key yace "Shitt, ohh God, i caused everything" Abuturrab kam xaunawa yayi kan gado ya rike kai, Sadeeq ya nufi Balcony din dakin da sauri yana kallon kasa ya girgixa kai ganin prickled Object dake watse a kasa wanda sbda shi aka xuba su, dawowa daki yyi yana tunanin hanyar da xa su bi su bar gidan don yasan duk Abbansa ya sa an toshe hanyoyin da yake bi, can ya dafe Abuturrab yace "Chill guy sai dai idan ba sojoji suka haife mu ba, we will surely find a way out, look... bana daukar last a irin haka fa, ni nan da kake gani ko kama kafata baka yi ba gun rashin ji, don haka in sha Allah sai mun fita" Abuturrab ya kallesa sai yyi murmushi yace "Yea kuma haka ne, buh we have to be very fast frnd" Sadeeq ya isa kusa da kofarsa ya bude a hankali tsaye ya ga Dad dinsa corridor din, pretending yyi yace "Abba you are here dama" Dad dinsa bai tanka sa ba, sadeeq ya shiga bedroom din mum dinsa, Kanwarsa Sumayya ce ke dakin tana gyara, yace "Sumy Umma fah?" Sumayya tace "Tana kitchen," shiru yyi sai kuma ya bude balcony din Ummantasa yana leken kasa, can ya dawo ya fara bude drawers dinta yana bincike, Sumy ta ja ta tsaya tana kallonsa da mamaki, ya kusa minti biyar kafin ya dago ganin kallon da take masa ya jawota a hankali yace "Pls Sumy am in trouble ki taimake ni" da mamaki tace "Me kuma kayi" murya can kasa yace "Ni da frnd dina wllh. Ga Abba can yana gadi a corridor kar mu fita" tabe baki tayi tace "You again" da damuwa yace "Plss" tace "Toh me xan maka" a hankali yace "Fita xa kiyi idan kin kai parlor sai kiyi ihu sosai kamar kin fadi din nan nasan Abba xai sauka daga nan ni da shi sai mu shigo nan mu dira ta balcony that's all, idan mun fita sai mu san next action" Sumy da ta saki baki tana kallonsa tace "Tabdi, to me ku ka yi" yace "Plss mana angel" tace "Noo ni ba ruwana baxan yi ba" wayarsa ya fiddo lkci daya yayi mata transfer din dubu hamsin, Ya dau wayarta dake kan mirror ya mika mata, karba tayi ganin alert ta bude ido tace "Har da bribing" ya langwabar da kai yace "Haba sisterna dama muna haka da ke" shiru tayi sai kuma tace "Toh ni dai bbu ruwana, idan kuma aka gano karya nayi fa!" Sadeeq yace "Haba kin fa iya pretending baby, kin ga muna bata lkci plss" turo baki tayi tace "Toh" yace "Yauwa sis of life" daga haka ya fita, waya ya tarar da Abba ke yi ya shige dakinsa kawai, mikewa Abuturrab yyi yana kallonsa, yyi murmushi yyi patting shoulder dinsa yace "Chill na samo mana hanya" gaban madubi sadeeq ya nufa ya bude ya fiddo lighter daga haka ya koma ya xauna yana jiran jin ihun kanwarsa, Can dai ya kalli Abuturrab yace "Hope ka iya dirowa daga sama xuwa kasa" Dariya Abuturrab yyi yace "Sure" Dai dai nn suka ji wani uban ihun da Sumy tayi wanda sai da gidan ya amsa, sai da sadeeq ya jira har second goma snn ya bude kofa ya ga ba Abbansa ya yafito Abuturrab suka shige dakin Ummansa da sauri ya bude Balcony, Abuturrab ne ya fara Dira kasa snn shi, Ya nufi gun da ake ajiye generator din gidan da sauri ya kinkimo gallon din mai dake ajiye gun ya isa gun flowers, da mamaki Abuturrab yace "Hey! What re you trying to do" Sadeeq bai kulasa ba ya xuba fuel kadan jikin flowers din ya mayar da gallon din snn ya dawo ya yanko wani flower mara fuel ya kunna masa lighter, sai da ya kama snn ya jefa kan flowers din da ya xuba ma fuel, lkci daya wuta ya kama, kama hannun Abuturrab yyi da sauri suka xaga xuwa daya side din suka shiga bayan wasu flowers ta yanda xai iya dinga hango gate, kan kace me daya barin ya fara ci da wuta sosai wanda hakan ya ja hankalin soldiers dake bakin gate suka taho da sauri suna raising alarm, Sadeeq na ganin gate wayam ya kalli Abuturrab yace "Gudu sosai fa xa mu yi" daga haka ya mike haka ma Abuturrab, a dari da sittin suka isa gate a kan idon Abban Sadeeq da ya fito da sauri jin alarm din soldiers dinsa, sake baki yyi yana kallonsu har suka fice, kamar masu gudun relay race suka isa bakin titi suka afka Adai daita sahu, sai a snn Sadeeq ya dinga kyal kyala dariya, Abuturrab kam lumshe ido kawai yyi yana murmushi.

*Haske writers asso*
๐Ÿ’ซ *Noorul Huda*๐Ÿ’ซ

By khaleesat Haiydar๐Ÿ“šโœ๐Ÿป

52.....

Bude ido Abuturrab yyi har lkcn yana murmushi ya kalli Sadeeq yace "Kai babba ne!" Yar dariya Sadeeq yayi yace "That's the only way out ae" Abuturrab yace "Uhm amma komawar ka gida bbu rana koh?" Sadeeq yace "Haba daii ko anjima sai naje, amma da Thummun bukumun xan shiga...." Dariya Abuturrab yayi yace "Really!" Sadeeq yace "But wani laifi ne kayi haka har ka bar gida for 2months, ni fa duk abinda xanyi ban wuce 2days a waje xan samo solution in yi komawa ta gida kuma lafiya lau" Abuturrab yyi murmushi bai ce komai ba, Sadeeq yace "I might find a solution for you kar ka ji komai ka gaya min" Abuturrab yace "You know Col Ahmad ur dad's frnd?" Sadeeq ya d'an yi shiru can yace "Na kano?" Abuturrab yace "Yea kasan shi?" Sadeeq yace "Wait! Don't tell me u re his son, don't tell me kai ne wanda ka gudu da yar mutane for months?" Kallonsa kawai Abuturrab yake, Sadeeq ya kalli me Napep da sauri yace "malam malam tsaya nn" Mai adai daita ya ja ya tsaya, Sadeeq ya fita yana kallon Abuturrab dake kallonsa shi ma, can ya fashe da wani dariya yace "Kaiii.... ashe da babba nake tare da...." Dariya Abuturrab yayi ya fito daga adai daitan Sadeeq yace "Waow... kasan da naji abinda kayi na dde ina son in gan ka ko a hotone, gaskiya kai babba ne, nasan duk yaran abokan Abba na amma banda kai how comes, kai ne wanda i think 2 years back ku ka yi fada da yaron wani minister a Uk" Abuturrab ya ba mai adai daita kudinsa ya kalli Sadeeq yace "Ai ni ban taba attempting kona gidanmu ba, kaga kuwa kai ne babba" Dariya Sadeeq yayi yace "Toh wai ina yarinyar yanxu.... Kaiii don't tell me ita ce na gan ku tare jiya?" Abuturrab yace "Yea..." Sadeeq ya xaro ido yace "Bari muyi lodging hotel kayi gist dina plsss in kara course and probably in samo maka solution" Abuturrab yace "Maraba xan wuce yanxu haka it's very urgent" Sadeeq yace "Haba, bari in kira frnd dina ya kawo mana mota sai mu je i really want us to be frnds" Murmushi Abuturrab yyi kawai, cikin minti Sha biyar aka kawo masu mota suka dau hanyar maraba, Sadeeq ke driving din, Abuturrab ya kallesa yace "But pls let this be a secret between us plss, i don't trust easily sai gashi nayi trusting dinka lokaci daya don't betray that" Sadeeq yace "C'mon baka da damuwa frnd," Abuturrab yace "Amma idan ka koma gida Abba ya tambayeka inda nake me xaka ce?" Sadeeq yace "I don't know ur whereabout and that's it" Abuturrab bai kuma cewa komai ba

Please Login or Register in order to submit comment