Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shaa Allah shi ma xai dawo hanya madaidaiciya, uwar ta kam dama ba a magana tayi nisa sosai" Ummi dake ta kallonsa ta gyada kai cike da gamsuwa tace "Haka ne boy, na kuma lura abinda yasa ta fara loosing interest sbda nisanta ku da juna da nayi ne, buh i have no other alternative kada in xamo uwar banxa, abinda baxan bar d'a na yayi ba to d'an wani ma baxan bari yayi ba.... Kuma xancen xaka aureta ynxu bai taso ba boy, ka bari sai ta amshi islam don kanta ba don auren ka ba... Xaka aureta amma not so soon, ynxu dai ka dinga yawan shigowa a kai a kai ta daina jin kadai cin da take ji, komawanta can ne dai baxae taba yiwuwa ba, kai da Yusuf kuyi xaman ku a can tunda xai jima sosai a nan, one more thing boy pls pls ka daure kaje gida ko don mahaifiyar ka..." Kallonta yayi da sauri yace "Sai ince Samha tana ina, baxa ki gane ba Mami ai ina kai kaina gida yanxu ni nasan kano yayi ma Abbana kadan yyi min hukunci sae dai Abuja, xan je gida amma ba yanxu ba" kallonsa kawai Ummi take, can ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh shknn boy, kai ma ka rage ma kanka damuwa bana son kana raman nn, Samha dai ba rabaka nayi da ita ba, duk lkcn da kake son ganinta sai ka shiga har hira ma kuyi, i won't stop that" ya d'an yi shiru sai kuma yace "Toh Mami nagode, amma plss let this continue to be a secret btwn us bana son a san she's nt my wife" da damuwa ya kare maganar, Ummi ta gyada kai tace "Alryt boy" a hankali cikin sanyin murya yace "Mami... mami ko yusuf ma fa kar ki ce masa ba matata bace...." Shiru Ummi tayi tana kallonsa, Gabansa ne ya fadi sosai ganin kallon da take masa, sai kuma tayi saurin gyada kai tana murmushi tace "Aiit, u can leave now boy.... I will let no one know" Mikewa yayi ya mata sallama ya fita, for the 1st time tun bayan faruwan incident din ranan yaji hankalinsa ya kwanta sosai. Fatima ce xauna balcony da kawayenta biyu handouts a gabansu Khadija da Samha suka fito, Khadija tace "Sister xa mu je siyo airtime..." Fatima tace "Ohk" Bin su da kallo fatima tayi suna yin nisa billy tace "Kin ki gaya min dalilin dawowar yarinyar nn part din ku..." Fatima tace "How many times do i have to tell you nima ban sani ba kuma ban san ta yanda xan sani ba Billy, I've snooped, I've put an eye all to no avail.. Ummi ba gaya min xata yi ba, that silly khadijah of a being ma ko da tasan abu she won't tell me" farida tace "Buh guy din ya fara sake maki kuwa?" Fatima bata ce komai ba ta dau handout din gabanta, Billy tace "i have a plan for you teemah..." Yusuf na xaune karkashin artificial tree dake compound din gidan yana waya amma idonsa da hankalinsa na kan Samha da khadijah dake tahowa, Samha ta saci kallonsa suka hada ido ta dauke nata da sauri, khadija tace "Yaya xa mu je siyo card..." Yace "Card?" Tace "Eh, airtime" yace "Ohk, taho in maki transfer" Tace "Toh yayana thank you..." Daga haka ta kama hannun samha suka nufi inda yake, kujera ta ja ta xauna tana kallon Samha ta dauko mata wani kujerar tace "Sit" Samha ta kirkiri murmushi ta girgixa kai tace "Thank you" Yusuf dake kallonta yace "Why?" Bata ce komai ba kuma bata kallesa ba, yace "Ki xauna" bbu yanda ta iya haka ta xauna kan kujerar, yana danna waya yace "1000 ya maki yawa koh?" Ta xaro ido tace "Noo yaya, ya isa fah" yayi murmushi yace "Tohm! Waec bai fito ba har ynxu koh" tace "Ehh muna ta jira..." Samha dai kallonsa kawai take, height dinsu xae xo daya da Abuturrab haka ma haskensu, tana kkrin tantance wanda ya fi kyau cikinsu ya dago kai ya ga tana kallonsa, mikewa tayi da sauri tana kallon khadija tace "Amm, xan... bari in shiga ciki in taya usaina..." Daga haka ta bar wajen kmr warce aka kora ya bi ta da ido yana murmushi, Khadija tayi tagumi tana kallonsa, can dai tace "Big bro.... She's someone's else property fah?" Kallonta yayi da sauri yace "Whose?" Ta hade rai tace "Ba na gaya maka ba Dr Aliyun nn mana...." Yusuf yace "Hmm yeah... Amma yaushe suka xo gidan nan?" Khadija tace "Xa su kusa 5 weeks fa" yace "Ohk, but why is she staying a part dinmu?" Ta bude ido tace "Nima ban sani ba wllh, at 1st nayi tunanin ko bata da lafiya ne ma" yace "Ohk, a ina Aliyun yake aiki?" Khadija tace "A clinic din Ummi..." Kallonta kawai yake can yace "Ohk, da suka xo garin nn baya aiki ne?" Khadija tace "Toh, nima dai bn sani ba amma Ummi dae ta basa aiki a clinic" Yusuf na gyada kai yace "Ohkk, daga wani gari suke?" Tace "Kano wai..." Yace "Ohk, amma bata gaya maki komai a kan ita da Aliyun ba, i mean ko a hira bata gaya maki san da suka yi auren ba...." Khadija da ta fara isa da tambayoyin tace "A'a ni fa ban taba tambayarta komai ba" Yace "Ohk, but is dis their 1st time in Gombe?" Mikewa khadija tayi don tasan in ta ci gaba da basa amsa sae su kai dare a gun, ta turo baki tace "Kai yaya, sai kace ka samu case.... Wnn ko a court sai haka ae ta ya ni xan yi in san ko sun taba xuwa gombe, ni dai tnx for d airtime xan je mu ci gaba da girki..." Daga haka ta kara gaba ya bi ta da kallo yana murmushi.

*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫

By khaleesat Haiydar📚✍🏻

46....

Karfe shidda saura Abuturrab ya dawo daga gun aiki, yana gama parking ya fito yana kallon Yusuf dake compound din har lkcn, karasawa yyi ya basa hannu suka gaisa, Yusuf yace "Welcome back..." Abuturrab yace "Thank you, iska kke sha knn" Yusuf ya shafa kai yace "Not really am making a call...." Abuturrab yace "Aiit" daga haka ya wuce part dinsa, har aka kira Magrib Yusuf na xaune waje, sai da ya ga fitan Abuturrab masallaci snn ya tashi ya karasa tap din dake compound din yyi alwala ya bi bayansa. Kusan a tare suka shigo da Ummi compound din hakan yasa suka karasa can part din gaba daya don gaisheta, Abuturrab bai jima parlon ba ya koma part dinsa don tun da ya shiga bai ga Samha ba, yana kwance idonsa kan news da ake a tv aka bude kofa hade da sallama, Khadija ce ta shigo tare da Samha rike da abinci hannunta, har suka karaso inda yake idonsa na kan Samha, khadija ta ajiye abincin hannunta tace "Ina yini Uncle" ya kalleta ya amsa yace "Lafiya dija, sannu da aiki" tayi murmushi bata ce komai ba, Samha da kanta ke kasa tace "Ina yini?" Ya kalleta yace "Lafiya lau..." Sai a snn ta daga ido ta kallesa, murmushi tayi ganin yanda yake kallonta, tace "Ya aiki?" Yace "Alhmdllh...." Mikewa khadija tayi tace "Bari in dauko plate...." Daga haka ta wuce kitchen, saukowa kasa Abuturrab yyi yana kallonta har lkcn, cikin sanyin murya yace "Kin guje ni Heart beat...." Murmushi take ta girgixa kai tace "A'a" Dago kanta yyi ya kamo hannunta yana kallon kwayar idonta yace "I love you Samha...." Murya can kasa tace "I... i love you more" rungumeta yayi kan idon yusuf da ya shigo parlon a lkcn, Khadija kuma ta fito daga kitchen rike da plate, a hankali Samha ta xame jikinta, Yusuf kuma pretends he saw nothing yana danna waya, mikewa Samha tayi tana kallon Khadija da ta ajiye abun hannunta tace "Ba mu kai ma Ummi abinci ba" Daga haka ta nufi kofa Khadija ta bi bayanta. Ummi na xaune bedroom dinta Yusuf ya shigo, kallonsa take har ya nemi waje ya xauna, ta kalli agogo ganin goma ya wuce tace "Baka tafi can ba?" Yace "Yanxu xan wuce" Bata kuma cewa komai ba ta ci gaba da shan fruit din gabanta, Yana kallonta yace "Ummi...." Kallonsa tayi tace "Ya aka yi?" Ya shafa kai yace "Ummi ya Aliyu suke da yarinyar nn ne..." Wani kallo tayi masa tace "What's ur problem with that Yusuf, if am nt mistaken you've asked me that before, fine... Matar sa ce are you okay by that?" Yar dariya yyi yace "Buh few days ago ce min kika yi ba matarsa bace Ummi, how's this? Hmmm?" Hararansa tayi tace "Yea sun rabu ne then buh ynxu everything is normal" kallonta yake ko kiftawa bbu kmr me son gano abu, ta ci gaba da cin fruits dinta ba tare da ta kuma kallonsa ba, can ya dai yace "Toh mai take xama yi nan har yanxu?" Cike da masifa tace "Lemme rest pls Yusuf, i want him to know her value shi yasa har yanxu bata koma ba, kuma baxa ta koma ba..." Shiru yayi yana kallonta, can yace "Amma within dis short period din xamansu a gidan nn har kuka saba haka kika gano suna da prob... buh em fatima told me sabon aure ne, sabon aure shine har aka fara samun matsala, from my investigation na gano abu Ummi...." Mikewa tayi a fusace tace "Enough! Leave right away" mikewa yayi yana shafa kai fuskarsa dauke da murmushi ya nufi kofa ya fita, Ummi ta xauna hade da sauke ajiyar xuciya underneath her breathe tace "Damn it! Shi wai Barrister, Ya Allah kar ka bari ya gano komai kar in xama mara alkawari, i spoilt everything at d beginning" Yusuf na fita har xai nufi kofa yaji motsi kitchen a tunaninsa Khadija ne ya karasa kitchen din, Samha ya gani tana wanke wanke, suna hada ido ta dauke kai ta ci gaba da abinda take, shiga kitchen din yyi ya rufe kofa yace "Sannu da aiki" tace "Na gode" yana gyada kai yace "Ohk, ya ma sunan naki?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Samha" yace "Nyc.... Ain't you missing home" da sauri ta kallesa sai dai bata ce komai ba, ya mata murmushi yace "You re nt tunda ga Aliyu koh" dauke kai tayi, dai dai nn aka bude kofar kitchen din, juyawa yyi da sauri, Ummi ta shigo, kallon Mamaki take masa tace "Me kke nn kuma Yusuf?" Yace "Ummi ruwa na xo sha, just came to take a glass of water...." Hade rai tayi sosai tana kallonsa, ya kalli Samha yace "Good nyt" a hankali tace "Thank you" daga haka yace ma Ummi ma sai da safe, ya fita ba tare da Ummi ta tanka sa ba. Ummi ta ajiye bowl din hannunta duk jikinta yyi sanyi ta juya ta fita. Ko kadan Abuturrab bai rintsa ba cikin dare, he was just planning on what to do next, yasan Ummi is truly good to him but bai jin xai iya ci gaba da xama garin when yusuf is around, May be some other time xai dawo gun ta don baxai taba mance irin halaccin nn da tayi masa ba, But he can't stay in gombe with his Samha any longer, kafin assalatu ya gama concluding next step din da xai dauka, and he was relieved.

*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫

By Khaleesat Haiydar📚✍🏻

47.....

Washegari Yusuf na bacci Abuturrab ya gama shirinsa, atm cards dinsa kawai ya dauka snn ya fita tun bakwai da rabi bai yi ba, bai fita da mota ba don kar ma Ummi ta ji fitarsa, clinic ya tafi, sai da ya tabbatar Ummi ta iso asibitin kusan karfe goma snn ya fita, gida ya nufa direct, khadija ce da Samha kadai gidan da yake ranan alhamis ne Khadijar bata je islamiyya ba, Gaishesa khadija tayi ya amsa yace "Samha fah?" Tace "Tana daki" daga haka ta wuce dakin sai ga su sun fito tare, kallonta yake har suka karaso, ya kirkiri murmushi yana kallon khadija yace "We will be back soon khadija, Cafe xamu" daga haka ya juya Samha da ta bi sa da ido ta ji yace "Ki dauko Hijab" juyawa tayi ta koma ta sako hijab dinta ta fito ta samesa yana jiranta waje, idonsa na kanta har ta karaso kusa da shi, yace "Mu je..." Tace "Ummi ta sani" yace "Yeah" daga haka ya kama hannunta suka fice. Mamaki ne ya cika ta ganin inda suka nufo, ya sauka ya ba mai adaidaita kudi, fitowa tayi ita ma tace "Doctor..." Hannunta ya rike ya nufi cikin park din, direct inda ake kiran passenger din Kaduna ya nufa, lkci daya hawaye ya cika idonta cikin sanyin murya tace "Doctor Ummi fa bata sani ba" bai ko kalleta ba bare ya kulata, bbu bata lkci ya biya masu kudin mota, ya nemi bench yyi xamansa kafin motar ta gama cika, can ya kalleta yace "Yea we will be back some other day..." Hawaye sosai take, bata xauna ba har mota ya cika ya mike ya shiga motar, sai da wata mata tayi mata maganar baxa ta shiga mota bane, snn ta shiga ta xauna kusa da matar. Throughout Journey din Abuturrab hirarsa da mutumin da ke kusa da shi yake don mutumin ba dai surutu ba, Samha kam duk jikinta a sanyaye yake, to ina kuma xa su, ganin bata da amsan ba kanta ta hakura kawai, lkci daya bacci ya dauketa. Kusan la'asar suka shigo kd, tana fita mota ta je ta tsaya wani gefe ta rungume hannayenta, shi kuma ya tsaya sallama da sabon abokin da yayi, har suka yi exchanging number da xumar xa su hadu wani lkci idan Allah ya yrda, Mutumin da yace sunansa Bashir yayi ma samha sallama don Abuturrab ce masa yyi matarsa ce, Abuturrab ya karasa yana kallonta yace "Kin gaji koh baby?" Dauke kai tayi bata ce komai ba, yace "Don't worry Sweet baxa mu taba mance Ummi ba, wataran xa mu kai mata xiyara amma as husband and wife, may be with our kid ma then.... Yanxu ina muka nufa?" Sai a snn ta kallesa kmr xata yi kuka tace "Da baka san inda xa mu ba muka taho nan?" Yace "Noo mana baby, yanxu dai mu fara xuwa gun aunt da kika ce tana nan garin koh..." Kallonsa tayi da sauri tace "Da gaske?" Yace "Yea mana, a wani anguwa take?" Tace "Familyn mijinta na can mararraba, lkcn can Abbana ke kai ni, amma wani lkcn suna xama Makera" yace "But mun wuce mararraba ai" shiru tayi bata ce komai ba, can yace "Toh mu je makeran ne ynxu?" Kai ta gyada masa, ya tsayar masu da Napep suka wuce Makera, amma cikin rashin sa'a yan gidan suka ce ai sun ma saki gidan sun koma can maraba, bbu yanda suka iya haka suka fito, Abuturrab na kallonta yace "ki xauna dakalin can dear, xan yi sllh in sama maki abinda xa ki ci sai mu tafi can maraban" xama tayi ta jira yyi sllh masallacin dake layin, ya fito ya nemi shago ya siya mata soft drink da snacks shi ya siya Malt, kallon mutumin dake xaune bakin shagon yana ta xukar taba yake, tunani ya shiga yi me ma yasa ya daina shan abun nn, sai yaji kmr ana tempting dinsa ya siya ya juya kawai ya bar wajen da sauri, taxi ya samu drop da xai kai su har maraban, ba su suka isa ba sai kusan biyar da wani abu, tana gaba yana biye da ita a baya yana kare ma garin da baxa a kira da kauye gaba daya ba kallo, Ita ce ta fara shiga d'an gate din gidan da Sallama ganin ya ki shigowa ta juyo tana kallonsa tace "Come in mana" Murmushi yyi ya bi bayanta, tsakar gida ne madaidaici me dauke da dakuna hudu a jere sai bandaki da kewaye a gefe daya, bbu kowa tsakar gidan sai murhu me dauke da tukunyar shinkafa a kai, kallonsa tayi ya wara mata ido a hankali yace "Shiga mana baby" kallon bangaren bayi tayi jin kmr akwai mutum a ciki sai kuma ta karasa bakin kofar daya daga dakunan dake a matsayin parlor ta bude labulen xaune taga Anty Maryam tana yankan alaiyahu sai wata mata dake kwance tana bacci ta juya baya, sake wukan hannunta tayi ta bude baki tana kallonta, can ta kalli matar dake kwance da Samha ma ke kallo ganin kamar Anty Sarah, mikewa Anty maryam tayi da hanxari ta karasa bakin kofar kawai ta kama hannunta suka fito, turus tayi ganin Abuturrab, ae yana ganin reaction dinta ya gane ba lafiya, murya kasa kasa tace "Ku taho...." Bude wani kofa tayi, dai dai lkcn da Samha taji muryar Mahaifiyarta daga cikin bandaki tana kwalo ma Anty Maryam kira wai ta miko mata zani, ai samha bata jira ta gama bude kofar ba ta shige a mugun tsorace, shi kansa Abuturrab ya rikice ba kadan ba, xae fito da ita daga dakin tun kan ta karasa shiga Anty Maryam da ita kanta a gigice take murya can kasa tace "Ku shiga i will close the door now" hakan yasa Abuturrab ya shiga dakin Anty Maryam ta garkame da makulli ta juya da sauri ta koma parlor tana amsa kiranta. Kuka Samha ta dinga yi tana cewa Abuturrab kashe ta mumy xata yi, bbu irin lallashin da bai yi ba amma kamar yana da da tunxurata duk tayi mugun tsorata gani take kmr Mumy xata fado dakin, shi kansa Abuturrab kansa ya daure ae da kawai Anty Maryam ta bari su fita kawai. Kin koma parlor Anty Maryam tayi don gani take kmr Rachael mahaifiyar Samantha xata ce xata shiga dakin da ta rufe, ai ko tana fitowa tace "Ki duba min kaya a jaka ki kawo min dakin can..." Daga haka ta nufi dakin da su Samha suke, Anty Maryam da gabanta yayi mugun faduwa tace "Anty dakin a kulle yake ai, baban su Asiya ne... Ina jin ajiya yyi" Rachael ta juyo tana kallonta sai kuma tace "Ina ce a bude naga dakin daxu kuma ai Aminu bai dawo gidan nn ba" Tabe baki tayi tace "Toh muje nan din, nagansa very untidy ne" Xaune tayi parlon tana shafa mai tace "Ai Maryam tunda pastor din nan na celestial church jiya yace min ina xaune xan ga Rebecca da musulmin nan very soon hankalina ya kwanta, idan kin kula jiya baccin da nayi har da minshari, rabona da bacci haka fa tun daren da Rebecca ta gudu..." Ta girgixa kai tana wani murmushi tace "Yesu ka ga irin tarbiyar da nayi ma yarinyar nn, yesu nasan baxa ka kamani da laifi ba, Toh kayi gaggawan bayyana min ita!" Ita dai Anty Maryam cukuikuye Alaiyahu kawai take duk hankalinta bai gun, Rachael tace "Ya kina ma alaiyahun haka, tunanin me kike" Da sauri Anty Maryam ta xubar a cikin farantin gabanta tace "Babu komai Anty...." Rachael ta gama xura rigarta ta dau Bible ta fita, Anty Maryam ta bi ta da ido xuciyarta na bugawa.

*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫

By khaleesat Haiydar📚✍🏻

48.....

Xama tayi tsakar gidan ta bude Bible din hannunta tana dubawa, Anty Maryam ta mike da kyar ta fita tsakar gidan, ta ja kujerar tsugunno ta xauna tana ci gaba da aikin da take, can ta sace kallon Mumy tace "Hayakin nn bai damun ki Anty?" Rachael ta kalleta snn ta kalli Murhun tace "Yo ba gwara ya dame ni ba da xafi ya kasheni a d'an akurkin parlon nn naki Mary.... Ai dai kinga ribar musulunci da auren Musulmi" Anty Maryam ta hade rai tace "Don't start that again aunt, shi da ma Christianityn forcing mutane ake yi su yi?" Tsaki Rachael tayi tace "Mu dama bama bukatar irin ku, ku kare rayuwar ku a musulunci don yesu bai so ku da rahama ba" Tsaki Anty Maryam tayi ta mike ta bar gun ta koma can gaban murhu, Rachael ta tabe baki tace "What a pity" Tunani Maryam ta dinga yi abinda xata ma Mumy taji haushi ta bar gidan ko ma ta wuce church kawai, can dai tace "Ga ku abun tausayi amma ku wani ce kuna tausayin mutum, Astagfirullah... shi Annabi Isan da ku ke bautawa ku ke kiransa da d'an Allah ance maki......" Tsam Mumy ta mike a fusace tana huci tace "Kee Maryam kar ki kai aya, maxa ki tofe yawun bakin ki kan fushin Jehovah ya sakko ya same ki ynzun nn, shi d'an nasa kike xancensa cike da izgilanci??" Maryam ta tabe baki tace "Ni na isa in ma Annabin Allah, ma'aikin Allah izgilanci, ni dai nasan Allahu bai haifa ba ba'a haifesa ba, Annabi Isa kuma messenger dinsa ne haka zalika Annabi Muhammad...." A mugun fusace Mumy ta katse tana hakki tace "Toh kuwa Allah ya tsine maki da wnn furucin, a kan ke musulma ce xa ki dinga fadin wa ennan maganganu, waye kuma Muhammad?" Mikewa Maryam tayi "Annabin Allah ne shi ma, kuma comforter din da Annabi Isa A.S ya gaya maku xai xo, if am nt mistaken bible ne a hannunki, idan kuma baki mance ba nima fa kusan nasan komai a Christianity din nn naku, Anty ki bude john 16:5-8....." Ganin Mumy ba budewa zata yi ba sai kumfar baki take ita a dole an tabo Yesu ta karasa ta karbe bible din ta bude, sai da ta duba tas snn ta rufe bible din tace "Let me make it short, the verse goes thus 'For if i go not away, the comforter will not come unto you, but if i depart, i will send him unto you, and when he comes, he will reprove d world of sin, and approve righteousness nd Judgement..." Murmushi tayi tana kallon Mumy tace "And who is Isa A.S referring to you all as a comforter?? That's prophet Muhammad S.A.W, he is the comforter" Mumy tace "Jehovah ya dawwamar dake cikin duhu, kada ya taba baki ikon gane gaskiya, sha sha sha kawai, talauci kadai ma da ya bar ku da shi ai ya ishe ku" Mai Abuturrab xai yi bnda dariya, sosai Mumy ta basa dariya, ya rike kai ya dinga yi, Samha ta rikesa a tsorace tace "Noo Doctor xa ta ji plss ka dainaaa" hadiye dariyar yayi ya rike baki, Maryam ta tabe baki tace "Ae ba don Allah bai sonmu bane ya bar mu a haka, sai ki ga mu samu in the world here after" Mumy tace "Inaaa ai kwalelanku ku da arziki, baku yrda da d'an sa ba ku ke zaton xai maku arxiki... Baki ganin ynda ubanku ya mutu ko tinkiya daya ba shi da..." Sai kuma ta fashe da kuka tace "Da yau xan ga Rebecca gwara in kasheta in yi layyarta" Anty Maryam tace "Sai kuma ki ga kafin ta dawo ta musulunta, kila har ma ya aureta da ciki jikinta" wani kara da ya firgita sarah dake bacci ta fito da gudu Mumy tayi, Ta isa gun Maryam da gudu ta shakota tace "Jehovah ya isa tsakanina dake, Jehovah ya kona bakin ki da ya furta haka, Jehovah ya hanaki farin ciki da shegen talakan musulmin mijin ki...." Sai kuma ta fashe da kuka tace "Sarah dauko min jakar kayana in wuce hotel, Idan na ci gaba da xaman gidan nn nasan xan shiga fushin ubangijina...." Sarah tace "Haba sis Rachael me ya hadaku haka duk makwabta na ji?" Tura Maryam Mumy tayi ta shige daki sai ga ta ta fito da jakarta tace "Idan kin ga dama ki fito da taki jakar in kuma so kike mu kone a gobarar da xa a aiko masu yau ne sai kiyi ta xama" Daga haka ta fice fuuuu daga gidan, Sarah tace "Maryam me ya faru haka ne" Maryam ta koma kujera ta xauna hade da sauke ajiyar xuciya tace "Toh ma ina na sani magana kawai muke sai naga kuma kmr warce aka ma allura" Sarah ta sa takalmi ta bi bayanta da sauri, murmushi

Please Login or Register in order to submit comment