Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kafa take tafiya har tayi nisa sosai tayi deciding ta bi layin gidansu class mate dinta Esther su tafi church din tare, tafiya take tana d'an wake wakenta, tayi nisa sosai don bai wuce gida hudu xata wuce snn ta sha kwanan gidansu Esther ba, gabanta ya fadi ganin wanda ta gani tsaye jikin motarsa a gaban wani gida ga wata yarinya na tsaye daga kusa da shi, kamar ance ya daga ido suka yi ido hudu, da kyar ta bude baki tace "Ina...ina yini!" Yace "Lafiya lau" daga haka ta wucesa, yarinyar ta bi ta da kallo snn ta kallesa tace "Waye ita Aliyu?" Da kamar baxai ce komai ba, sai kuma yace "A frnd!" Ta tabe baki tace "A Christian frnd?" Bude motarsa yayi ya shige ta koma baya da mamaki tana kallonsa tace "Abuturrab?" Ta glass yake kallonta yace "Even if she's a pagan (Mara addini) it's non of ur business!" Tada motar yayi ya ja ya bar ta nan tsaye ta bi sa da kallon mamaki, can ta juya da sauri taga har Samantha ta bace, a fusace ta shige gida. Abuturrab na isa gida misalin sha biyu na dare yayi parking ya fito ko ba a gaya masa ba yasan Abba ya dawo ganin Prado dinsa, bae ko kalli sojojin dake tsaye ta ko ina a compound din ba ya shiga parlor Ramlah ta leko daga kitchen murya can ciki tace "Ya Abu Abba yana neman ka..." Yayi mamakin ganinta a kitchen a wnn lkcn gashi bai ji mai take cewa ba ma, xai karasa inda take suka ji muryar Mami tace "Kina da hankali kuwa Ramlah" juyawa tayi da sauri ta koma kitchen, hade rai yayi ya gaisheta shi kenan kullum cikin laifi kuma sai yayi ta xaman gida kamar mace, infact mayar da duty dinsa na clinic xuwa dare ma xai yi kawae, Mami ta amsa gaisuwarsa ba tare da ta kallesa ba xai haura sama sai ga Abba ya fito daga parlonsa, tsaye yayi gabansa na faduwa ya d'an risina ya gaishesa Abba yace "Daga ina kake Aliyu?" Sunkuyar da kai yyi ya ma rasa abinda xai ce, can dae yace "Abba taimako na tsaya yi a....." Abba ya girgixa kai yace "No! You can't just be coming into my house when ever you wish at any time, don haka ka tattara inaka inaka ka koma boys quatr snn ka bude gate din can kaga idan yaso ko da yaushe ka ga dama xaka iya shiga ka fita bbu wanda ya sani, bbu wanda kuma xai hanaka, do what I say immediately now, stupid you!" kansa a kasa yace "Toh Abba, Allah ya huci xuciyar ka" Ramlah ta karaso parlon kamar xata yi kuka tace "Abba pls forgive him for the last..." Wani kallo ya mata ta juya da sauri ta koma kitchen, Abuturrab ya haura sama ba a dau lkci ba ya fito da jakunkunan kayansa da komai nasa da xai bukata, har lkcn Abba na tsaye parlor haka ma Mami da bata ji dadin hukuncin ba, Fita Abuturrab yyi ya kira mai gadi ya taya sa daukan kayan, tsakanin main gidan da boys quatr ba wani tafiya bane can, sai dai ba lallai ka ma san me ke faruwa can ba barin ma da Abba yace ya bude gate din can, cikin yan minutes ya gama mayar da kayansa can snn ya koma yayi ma parent din nasa sai da safe ya dawo, dariya ya dinga yi shi kadai a parlor yana tafa hannu ya fada kan kujera yace "Waow waoww enough privacy!" ya mike yana murmushi ya shiga inda dakuna suke ya xabi wanda yake so ya shigar da kayansa, ya dau lkci sosai yana gyaran dakin sbda kura don ba a fiye amfani da wajen ba sai dai a sauke baki, Abuturrab ba dai tsafta ba cikin few hours ya tsaftace dakin da bathroom ya kure Ac ko ina ya dawo yana kamshi ya shimfida bedsheet, snn yayi kwanciyarsa don ya ci abinci a waje, nan da nan bacci ya daukesa, washegari Monday yana shirin fita office aka danna bell daga waje ya karasa ya bude, Cook ne rike da tray din breakfast dinsa ya d'an bude ido yace "Ohh I thought girkin ma nan xa a dawo yi min" cook din dai bai ce komai ba ya gaishesa Abuturrab ya karbi tray din yace "Thanks" har ya tafi ya kirasa ya basa spare key din parlon yace "Gashi ko bana nn idan ka kawo min abinci ka shigo kawai ka ajiye" Cook din ya karba da ladabi yace "Ohk sir" daga haka ya juya ya wuce shi kuma ya koma ya ci gaba da shirinsa snn ya yi breakfast ya dau makullin motarsa ya fita, main house ya nufa ya gaida Mami ta amsa tana kallonsa tace "Hope you are now satisfied with the punishment?" Murmushi yayi yana shafa kai Mami tace "Ka canxa halin ka Abuu, you are grown up fa yanxu, soon xa ka ji Abba ya fara maka maganan aure idan kuma kaki fidda mata na tabbata fiddo maka ita ba wahala xai masa ba, you are 30 yanxu amma kaki nutsuwa ka san inda ke maka ciwo koh" murmushi yayi yace "Mami ni fa ba dauko maku magana nake ba, ba sata nake ba, ba kisa nake ba, kuma... Um Mami ni bana neman mata kin sani fa!" Bude baki tayi da mamaki tace "Ehh lallai Aliyu ashe baka da kunya..." Dariya yayi yace "Allah Mami, naga wa ennan sune rashin jin, kuma duk bana yi" harara ta 6alla masa tace "toh shaye shayen fa da bin abokan banxa" xaro ido yayi ya dawo kusa da ita yace "Ohh Mami wllh ni na bar wannan abun da dadewa bana shan komai yanxu" wani kallo tayi masa tace "Cigarette din fah?" Ya sosa kai yace "Uhm Mami shi ma ina kkrin in ga na daina wllh, just continue praying for me" ta shafa kansa tace "Toh Allah yasa haka son. Be a good man plss, sannan ka canxa abokan ka" mikewa yayi yana murmushi yace "Toh Mamina na tafi aiki...." Daga haka ya fita da sauri ya nufi parking lot, yana shiga motarsa ya bar gidan, dai dai traffic kamar ance ta juya ya ga Samantha a bayan mota sanye da uniform alamar sch xata, mamaki ya cikasa, why yake haduwa da ita frequently now, bayan ko taba ganinta bai yi ba kuma daga layinsu xuwa nasu gidan bbu wani nisa can amma bai taba lura da ita ba, ita ko ganin yanda yake kallonta ta daga masa hannu hade da yin murmushi, murmushin ya mayar mata ya gyada mata kai snn ya ja motarsa don an basu hannu ya dau hanyar gun aikinsa.

📚✍🏻
[7/19, 5:58 AM] 0mmer Farouk: 💫 *Noorul Huda*💫





3......
Karfe biyar saura Samantha ta dawo sch, duk da driver ne yaje daukota amma a titin anguwar tasu ya ajiyeta wai xai je dauko Mumy daga church, yawanci a nan take yawan sauka sai dai ta karasa da kafa, tafe take jakarta a bayanta da ganinta kasan a gajiye take, wani mota that look familiar ne ya xo ya wuce a guje ta bi motar da kallo, bai yi wani nisa ba taga kuma ya tsaya, ita dai tafiyarta kawai take, a hankali ya dinga dawowa baya har ya iso inda take ya sauke glass, d'an bude ido tayi ganin wanda ke cikin motar, kafin yace komai tace "Good evening," yace "Evening, let me drop you" kai ta gyada masa ta karasa ta bude front seat ta shiga ta rufe sannan ya ja motar, bai ce mata ba ita ma haka sai dai ynxu kam ba gudu yake ba, ji tayi yace "Ur name?" Ta kallesa tace "Samantha!" Ya d'an kalleta snn yace "Samantha?" Tayi murmushi tace "Samantha David!" Ya gyada kai yace "Nyc!" Tace "Urs?" Kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Aliyu Ahmad!" Murmushi tayi tace "Nyc name," kallon Stethoscope din dake sakale gaban motar tayi tace "You are a doctor?" A takaice yace "Yes" bata kuma cewa komai ba har ya iso gaban gate din gidansu ta kallesa tace "Thank you" yace "Welcm" har xata fita sai kuma ta tsaya ta kallesa tace "Every doctor can draw perfectly, will you pls help me draw the Diagram of the Mammalian heart and Human Skeleton?" Kallonta ya tsaya yi, can yyi Murmushi da ya bayyana light dimple dinsa yace "Really? To ni ban iya ba" kamar xata yi kuka tace "Allah nasan ka iya Plss ka min mana" shiru yayi yana kallon yanda karamin bakinta ke motsi sai kuma yace "Ohk," cike da murna tace "Ohk to bari in dauko materials din" dakatar da ita yayi yace "Am exhausted I can't wait, idan mun sake haduwa sai ki ban" daga haka ya daga mata hannu ya ja motar ta bi sa da kallo, cikin minti biyar ya isa nasu gidan ana bude masa gate yayi parking har xai nufi kofar main parlor ya tuna ai fa ya koma Boys quatr ynxu, dariya yayi ya nufi can, wanka kawai yayi ya dawo ya debi abincinsa dake ajiye snn ya ci ya kwanta don ya gaji sosai, shidda saura ya mike ya fita ya xaga boyz qtrs din gaba daya, ya bude gate din da Abba yace, ya fita waje da farin kujera ya xauna yana kare ma street din kallo don sai yyi shekara bai bi nn ba duk da bayan gidansu ne, baxa ka taba cewa akwai mutane unguwar ba tsabar shiru, tafe suke su biyu da alamar sun dawo daga church ne, tun daga nisa ya gano ta ta yanda take tafiya, haka ya dinga kallonsu har suka karaso, ta xaro ido ganinsa tace "Doctor!" Wara ido yayi bai ce komai ba ta karasa kusa da shi da sauri ta sauke jakar dake goye bayanta ta fito da materials din drawing din ta mika masa tace "Na kama ka" murmushi yayi ya karba yace "Nawa xa ki biya?" Ta langwabar da kai tace "Ko nawa, amma service before payment" dariya yayi wanda hakan ya fito da ainahin kyansa na d'an pillo, ya kuma bayyane fararen set din hakoransa masu daukar ido, shiru tayi tana kallonsa, yace "Ke me wayo ko?" Murmushi tayi tace "nan ma gidan frnds din ka ne?" Ya girgixa kai yace "Gidanmu ne" bin gidan tayi da kallo tace "Da gaske?" Yace "Yeah!" Tace "Hmm Ohk, to yaushe xan karbi xanen?" Yace "Ran da na gama" tace "Noo we are submitting it as test on Wednesday" yace "Ohk, xan yi anjima" tace "Yauwa na gode bye" daga haka ta nufi mai aikinsu blessing dake jiranta. A ranan da daddare Abuturrab ya xauna misalin karfe goma a gun da ya tanadar as study room, ya bude textbook din da ta basa domin Duba xanen a jiki ya kwafa, tabe baki yyi ya rufe, lumshe ido yyi na kusan minti biyar yana nazarin diagram din heart a xuciyarsa, can ya bude ido ya dau well sharpened pencil din ya shiga xana Big Mammalian heart gwanin ban sha'awa ko wani curve ya basa hakkinsa, sosai Heart din ya xanu yyi kyau kamar drawing din Artist, cikin few minutes yayi labelling ko ina snn ya ajiye pen din ya lumshe ido yana nazarin skeleton, bude idon yyi ya bude wani page ya shiga rangada babban xanen Human Skeleton, ko wani k'ashi sai da ya tabbatar ya xana, ya gama tsaf snn yayi labelling ya gama ya rufe book din yana hamma ya mike ya shige bedroom ya fada kan gado sai bacci. Washegari da xae fita aiki bae bari ya mance materials dinta ba in case ko xa su hadu, ya ajiye back seat snn ya bar gidan bayan ya shiga ya gaida Mumy, amma bai ganta ba ranan, da ya baro gun aiki ma haka ya dinga dube dube a hanya ko xai ganta amma har ya isa gida bai ganta ba. Karfe takwas na dare ya shirya ya fita hankalinsa kwance ta gate dinsa bbu wanda ya sani bare yyi querying dinsa inda xa shi, gidansu Saudat ya nufa don yyi missing dinta tsakanin jiya da yau, yana isa ya kirata, ba a dau time ba ta fito sai dai kumbure kumbure kawae take, yyi murmushi yace "Why the pouting?" Ta hararesa tace "Ka manta bari na tsaye kayi ranan ka wuce?" Kamo hannunta yayi yace "Ohk Am sorry dear, how you doing?"ta turo baki tace "Am good" ya shafa kansa yace "So what's new?" Tace "Baxa ka shiga ciki ba?" Yace "Noo, an san kin fito ne?" Tace "Just my little sis" yace "Mum fah?" Tace "She's in her room" yace "Toh rakani mu je mu dawo yanxu" tace "No the other time I escorted you ka sa ana ta min wani kallo a club ni baxan je ba" ya wara ido yace "Wa yace maki can xan je?" Ta hararesa tace "Ban san ka bane" dariya yayi yace "Plss baby we are not staying long fa kawai rakani xa ki yi Akwae abinda xan karba ne" shiru ta d'an yi, sai kuma a hankali tace "Ohk, just thirty minutes before ayi noticing bana gida" hannun ta ya kamo yace "Ohk dear" daga haka ya tada motar ya dau hanyar club din nasu, duk da bin sa da Saudat take club kaffa kaffa take da kanta kuma bata sake ma kowa fuska, don tana mugun sonsa shi yasa bata iya kin yin abinda yake so, Saudat kyakkyawa ce ta ajin karshe, irin matan da samarin xamani ke so, Abuturrab bai yi amfani da wnn advantage din son da take masa ba ya cutar da ita, iyaka kawai ya rike mata hannu sae d'an peck, coz he always keep it at the back of his mind dat shi ma yana da k'anni mata, bai kuma son komai ya samu lovely sisters dinsa, hakan yasa yake yaki da duk wani yaudara na diya mace, kafin minti talatin din kuwa ya maida ta gida bayan sun shiga eatry ya cika ta da kayan ciye ciye, ba shi ya koma gida ba sai kusan sha daya sai a snn ya kuma farin cikin basa side dinsa da Abba yyi, ynxu bbu wanda xai ma san ya dawo bare yace daga ina yake, yana parking gaban gate din ya fito xai bude don bbu mai gadi a side din kuma bai ma bukata, yana bude gate ya dawo xai shiga motar ya hango Samantha da wata mata da baxata haura 40 ba, wai! Da ganinta kaga rikakkiyar Christian, skirt ne jikinta shi bai kai kasa ba amma dogo ne sosai, sae wani bujejen riga da tasa tayi tuck in dinsa cikin rigar, kanta na sanye da irin hulan nan nasu na pastress, hannunta dauke da wani gundumemen Bible, dayan kuma na rike da hannun Samantha, da ganinsu kasan daga church suke, Samantha da ta gansa ita ma sai kallonsa take fuskarta dauke da murmushi har suka iso dai dai inda yake, satan kallon uwarta tayi taga hankalinta na gaba sai rera worship songs take, hannu ta daga masa a hankali alamar bye bye, ya sakar mata murmushi shi ma ya daga mata hannun, har suka wucesa bin su yake da kallo, doguwar riga ce jikinta sai rolling da tayi a kai, girgixa kai yayi ya shiga motarsa ya ja xuwa ciki yyi parking snn ya dawo ya rufe gate din, wanka yayi ya jima xaune yana karatun Qur'ani daga karshe ya mike ya shiga bedroom ya d'an yi xuke xukensa snn ya kwanta. Washegari da ya kasance laraba ana idar da Sllhn Asuba a masallaci drawing din Samantha ya fado masa gashi tace ranan xata yi submitting kuma test dinsu ne, satan kallon Abbansa dake Azkar yyi, don kusan ko da yaushe tare suke fitowa daga masallaci, kuma yasan ynxu sai ya bata rabin awa yana xaune, fuskewa yyi ya mike ya fice ya nufi gida, tsaye yyi a balcony yana tunanin ko dai ya bari kila idan xai fita aiki su hadu, sai kuma ya tuna jiya ma through out basu hadun ba, ya shiga gida ya dauka makullin motarsa ya fito ya bude motar ya dauki littafin da textbook din sai math set ya bude gate ya fice, tafiyar minti goma yayi ya iso dai dai gate dinsu, rasa yanda xai yi yyi, gashi har lkcn gari bai gama washewa ba, bai ma ga alamar an bude gate din nasu ba, leken cikin gidan ya shiga yi yaji daga bayansa an daka masa tsawa "Heyyy who you be, who you find?" Juyawa yyi da sauri yana kallon mutumin ko ba a gaya masa ba yasan mai gadin gidan ne, yace "Ehm, Samantha!" Mai gadin ya masa wani kallo yace "Wetin do Samantha?" Mika masa abubuwan hannunsa yayi yace "Give her plss" daga sama har kasa mai gadin ke kallonsa, Abuturrab ya kalli kansa, jallabiya ce milk colour jikinsa, karasowa mai gadin yyi yace "Who make I say?" Abuturrab yace "Aliyu!" mai gadin ya sa hannu ya karba Abuturrab ya juya ya bar wajen, karfe bakwai da kusan rabi yana kkrin rufe kofa Ilham ta karaso, ya juya yana kallonta yace "Pretty!" Tace "Ya Abu ko shigowa ka daina yi dama nasan kafi son haka" dariya yayi yace "Eh mana, baxa ku ma dinga gani ba bare ku dinga yangan bani abinci na" tace "Yaya pls ka ba Abba hakuri ka dawo cikin gida we are missing you" kamar xata yi kuka ta kare maganar, yace "Noo, I like it so much here" tace "Why?" Yace "Nothing" tabe baki tayi tace "Ae shikenan, kayi breakfast?" Yace "Yep, Peter ya kawo min" daga haka ya kama hannunta suka bar wajen yace "Za ki sani latti, ki sa kanki latti" tace "Ya turrab 5k plss" yace "I don't have cash, sai ltr" bai jima gun Mami ba ta fito ya hau motarsa xuwa gun aiki. Da ya tashi dawowa da yamma daga gun aiki da gundumemen K'arensa ya dawo da cage tare da mutumin dake rike da Karen, cikin few minutes aka hada cage din karen mutumin ya fito da karen da bakinsa ke a daure ya turasa cage ya rufe snn ya kunce mouth cuff din dake bakinsa, nan karen ya hau haushi, Abuturrab yyi murmushi yace "Yesss!" Tap ya nufa ya bude ruwa yana wanke hannunsa sannan ya dawi yana kallon mutun yace "Yanxu ya xa ayi karen ya saba da ni?" Mutumin yace "In dai kai ne xaka dinga basa abinci ko da yaushe cikin lkci kankani xai saba da kai" Abuturrab yace "Ohk nagode" nn ya sallami mutumin ya basa kudin mota, yana tsaye yana kallon katon karen da ya fito da halshe sai hakki yake ya ji muryar Mami a bayansa, juyawa yayi da sauri da mamaki tace "Meye wnn kuma Abuturrab?" Wara ido yayi yana murmushi yace "Dog Mami!" Hade rai tayi sosai tace "Uwar me yake a gidan nan?" Ya marairaice yace "Mami gadi xai dinga min ni bana son mutum nafi son dabba!" Bude baki tayi tana kallonsa, can ta girgixa kai tace "Toh ba gidan nan ba kare xai maka gadi, sai ka jira idan ka koma gidan ka na kanka!" Yace "Nooo Plss Mami, bangarena ne nn fah!" Tace "Nace ka fitar min da wnn abun Aliyu" karasowa yyi kamar xai yi kuka ya mata side hug yace "No plss Mami, kinga fa ina jin kamar jiya barayi sun xo anguwar nn, pls ki bar min karen it will be a good watch man for me, bbu abinda masu gadin nn suka iya sai bacci...." Girgixa kai tayi ta juya ta fara tafiya tace "Ni dai bbu ruwana...." Murmushi yayi yace "Yes Mami" main gidan ta nufa ba tare da ta tanka sa ba. Yana xaune misalin biyar kan farin kujera yana danne dannen wayarsa yaji kamar motsi jikin gate, ya daga kai da sauri, sai kuma ya mike ya nufi gate din ya bude, tsaye ya ganta kamar munafuka, tana ganinsa ta koma baya a tsorace, murmushi ya sakar mata murya can kasa yace "Samanth....." Sai kuma yyi shiru a hankali yace "Samha!" Wara ido tayi tana murmushi tace "Ashe kana nan, just came to say a big thank you!" Har da d'an risinawarta ta kare maganan, ya jingina jikin gate ya rungume hannayensa yana kallonsa yace "For what" turo baki tayi tace "For the beautiful drawing mana" Murmushi kawai yyi yana kallon hannunta dake dauke da Bible, mota ce ta shawo kwanan anguwar ta juya da sauri tana kallon direction din, ta xaro ido tace "Jesus! Abbana ya dawo" kallon motar yayi da sauri sai kuma ya matsa daga gun gate din bata jira yace mata komai ba ta shige cikin gidan, wara ido yayi yana kallon motar har ya xo ya wuce snn ya shiga gidan ya rufe gate din, tsaye ya ganta tayi lamo jikin flower, tana ganin ya rufe gate din ta karaso da sauri tace "Ae ya tafi ko, let me leave" kallon gate din yayi yace "I don't think ya tafi fa, tare yake da wasu a motar kuma na ga sun tsaya" kamar xata yi kuka tace "Bbu wani hanyar doctor?" Girgixa Kai yayi yace "Only this.... Ga kujera ki xauna ki jira su wuce sai ki tafi," Da damuwa tace "Church fa xan tafi, I don't want to miss" shiru yyi yana kallonta, can ya juya ya dau wani kujerar yayi xamansa, bin bayansa tayi tana bin gidan da kallo ta xauna kujerar da ya nuna mata tace "Are you the only one leaving here?" Girgixa kai yayi ya nuna mata hanyar da main house din yake yace "My family members are there, my Mum, Dad and sweet siblings" mikewa tayi ta nufi inda ya nuna mata bata wani yi nisa ba ta hango kantamemen gidan daga nisa, dawowa tayi da sauri tace "Uhn! Toh me yasa kai kake boys quatrs?" Murmushi yayi yace "Because I am a boy, an I prefer here" 'yar dariya tayi tace "Ohk that's true, xan wuce church yanxu" mikewa yayi yace "Bari in duba maki ko ya tafi" daga haka ya tafi gun gate ya bude ya leka, rufewa yyi da sauri ya dawo yace "Noo they are still there ki xauna kawai su wuce" bata fuska tayi tace "Lokacin Church na wucewa" bai tanka ta ba hakan yasa ta xauna, haushin k'are taji ta mike a firgice tana kallon direction din, ihu tayi suna ido hudu da katon karen ta juya xata gudu a rikice yyi saurin rikota da sauri, ta fashe da kuka tace "Noo bana son kare pls" xaunar da ita yyi kan kujera ya durkusa gabanta yana kallonta yace "But it's caged" Har lkcn jikinta rawa yake ta kasa cewa komai, dagota yyi ya shiga balcony da ita ya sa ta xauna ya duka gabanta yace "Ohk sorry Plss...." Hawaye ya sakko idonta tace "Ni xan tafi" mikewa yayi ita ma ta tashi, yace "Karen baya komai, it's very frndly" bata ko kalli inda karen yake ba ta nufi gate da saurinta, ya bi bayanta amma tuni ta fice, tsaye yyi bakin gate dinya rungume hannunsa ya bi ta da kallo ganin yanda take sauri, sai da ta tabbatar tayi nisa snn ta juya ta kallesa, d'aga masa hannu tayi, ya juya ya shige gate din yayi banging dinsa, kasa ci gaba da tafiya tayi sai kallon gate din take, can ta juya jiki ba kwari ta ci gaba da tafiya.


📚✍🏻
[7/19, 5:58 AM] 0mmer Farouk: 💫 *Noorul Huda*💫




4......

Washegari da yamma misalin biyar da rabi Abuturrab na xaune karkashin artificial bishiyar dake dauke da fararen kujeru a karkashi hannunsa rike da Cigarette, dawowarsa kenan daga aiki yayi wanka ya d'an tsakuri abincinsa da ke ajiye a parlor snn ya fito ya xauna ya fara aikin xuke xukensa idonsa na kan k'aren dake ta fama da gundumemen naman da ya siyo masa a hanya, murmushi yayi ya mike ya shiga ciki sai ga shi ya fito da babban drawing board da materials din drawing dinsa, bude board din yyi ya tsayar ya dawo da

Please Login or Register in order to submit comment