Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Azahar ya mike ya shiga toilet dake nn parlor ya daura alwala ya fita xuwa masallaci, ko da ya dawo a kitchen ya sameta ta daura girki, ya rungume hannayensa yana kallonta yace "Weldone dear..." Murmushi kawae tayi ta ci gaba da wanke shinkafar da take yi, ya juya ya fita xuwa balcony yayi xamansa, wata dattijuwa da baxata wuce 50 ba ce ta fito daga daya flat din idonta sanye da medicated ta rike jaka ta nufi parking space dake part din nasa ta bude daya daga motocin dake wajen ta shiga ta tada, horn tayi bayan ta fito compound din, Abuturrab ya kuma kallon motar ya dauke kai don yasan lkcn da yake dawowa daga masallaci lkcn mai gadin ya tafi, tayi horn yayi sau uku, can Abuturrab ya mike ya isa gate din ya bude mata, sauke glass tayi ta karasa gate din da motar tana kallonsa murmushi dauke fuskarta tace "Nagode kwarai..." Ya dukar da kai yace "Ina yini?" Tace "Lafiya lau, kai ne new tenant din Apartment din can kenan?" Kai ya gyada mata yace "Nine..." Tace "Maa sha Allah, you re welcome, tare da mai dakin ka koh?" Ya d'an yi jim sai kuma da sauri yace "Ehhh" tace "To sannun ku da xuwa, ni ce occupant din flat din can with my 3 kidz... Hope xa mu dinga ba makwabtaka hakkin sa" murmushi yayi sosai yace "In shaa Allah" ita ma tayi murmushin tace "Maa sha Allah, it's nyc meeting you, na fita aiki sae na dawo" yace "Toh Allah ya tsare" daga haka ta ja motarta ta fita ya rufe gate din, haka kawai yaji matar ta burgesa sae yake ganinta kamar Maminsa, yana murmushi ya koma balcony yayi xaman sa. Shinkafa da miya Samha ta girka tana gamawa ta fito ta gansa har lkcn yana balcony, ta jingina jikin kofa tace "Na gama" ya kalleta ya wara ido yace "Weldone sweetheart" murmushi tayi ta juya ta koma ciki ya mike ya bi bayanta, a tare yasa ta xuba masu abincin don yana son ta ci da yawa, ai ko haka yayi ta forcing dinta har suka cinye abincin, ya tagumi yace "But wa ya koya mamaki girki haka dear?" Tace "Uhm My mum" ya lumshe ido yace "You are a very good cook" a hankali tace "Thank you..." Yace "No thanks baby, bari in je masallaci it almost time for salat" tace "Toh" ya mike ya shiga toilet ya daura alwala ya fita, ta kwashe plates din don xuwa kitchen ta wanke.Bayan magrib yana dawowa daga masallaci matar daxu na shigowa, tsayawa yyi har tayi parking ta fito kafin tace komai ya gaisheta, da fara'a ta amsa tace "Mai dakin naka na ciki in shiga mu gaisa mu san juna..." Yace "Da ki bari xamu shigo yanxu tun da daga aiki kike ai" tace "Toh shknn ina jira" daga haka ta nufi bangarenta. Abuturrab ya juya ya shiga cikin gida, bedroom ya sameta yace "Samha, taso mu gaisa da new neighbor dinmu" ta kallesa tace "Do we need to?" Yace "Yess dear!" Mikewa tayi yace "Ki sa Hijab..." Ba musu ta dau daya daga sabbin Hijabs din da ya siya mata ta saka snn suka fita yana gaba tana biye da shi a baya, kararrawa ya danna ba a dau lkci ba wata yarinya da baxata wuce Samantha ba ta bude kofar, kallonsu ta shiga yi, Abuturrab yace "Hello, mum dinku na ciki koh?" Ta basu hanya tace "Ehh, welcome" Abuturrab ya shiga parlon Samha ta bi bayansa, sosai parlon ya hadu da gani dai kasan Naira ta xauna, xama yayi kan kujera ya nuna ma Samha gefensa ta xauna, yarinyar ta wuce ciki sae ga ta tafito tare da Mum din tasu, da fara'arta ta karaso parlon tana kallon Samha tace "Sannunku da xuwa" Samha ta sauke kai kasa ta gaisheta, ta amsa mata da murmushi tace "It's nyc meeting you... Ya sunan ki?" Satan kallonsa Samha tayi, yana murmushi yace "Samha!" matar tayi murmushi ita ma tace "toh kai fa?" Yana shafa kai yace "Aliyu...." Ta buda ido tace "Maa sha Allah ashe Abbana ne, amma sabon aure kuka yi koh?" Yar dariya yayi yace "Ehh haka ne" tace "Ae naga alama, Allah ya kawo Zuri'a dayyaba, ni sunana Hajarah...." Wara ido yayi yace "Mum dita knn..." Tace "Kai haba, shknn na samu d'a kuma babana..." Yayi dariya tace "Allah kuwa, muna xaune da kidz dina uku a nan, babban son dina Muhd na Uk, sai kanwarsa Maryam da ke Cairo tana aure, snn Fatima da Khadija da autata Rabi'ah, Ba mu yi shekara a garin Gombe ba don da a Abuja muke, yanxu haka ma Mai gidan na can sae dai yaxo week ends, am running my late dad's clinic dake nan ne shi yasa...." Abuturrab ya kalleta yana murmushi yace "Maa sha Allah Mami, Allah yayi jagora" tace "Ameen, amma a gombe ku ke?" Ya girgixa kai yace "A'a kano muke..." Tace "Ikon Allah, toh Allah dai ya bada zaman lafiya, kaga bata da kowa nn dont make her feel lonely ka dinga kyautata mata a ko da yaushe Abbana" yace "In shaa Allah Mami nagode" Hajiya Hajarah ta kalli Fatima dake xaune tana dannan waya tace "Ko ruwa baxa ki kawo masu ba Teemah" Abuturrab yace "Noo Mami Alhmdllh, xamu koma ne ynxu" Hajiya Hajarah tace "Toh shknn Boy, na gode kwarai" yar dariya yyi ya mike ya kuma yi mata sallama haka ma Samha snn suka fita. Sae da suka koma part dinsu yana kallonta yace "You like her?" Murmushi tayi ta xauna bata ce komai ba, da damuwa yace "Why ba kya son magana Samha, you re just nt ur self" ta wara ido tace "Ba komai fa, is just change of environment" yace "U will like it soon dear, nt when am with you" murmushin dae tayi, ya gyada mata kai snn ya shiga daki. A parlor yyi isha sbda hadarin da ya hadu ga iska ana yi, ita dai tana xaune parlon sae kallonsa take har ya idar, yana kallonta murmushi dauke fuskarsa yace "Ko kema kina son ki iya sllhn ne?" Tace "Uhmm" yace "Yeah dear sae in koya maki it's nothing ae" yar dariya tayi yayi shiru yana kallon fararen hakoranta tace "Wa yace maka ban iya ba?" Yace "A ina kika iya?" Tace "Uhm, na xauna gun kanwar Abbana Anty Aisha a kaduna, during my jss can nake xuwa yin long holiday, idan su Mumy xa su Jerusalem can ake kai ni, tare take hada ni da yaranta mu je islamiyya, in dai xa ayi sllh nima sae nayi a gidan, har na xo na saba idan na dawo gida sai in ta yin irin abubuwan islam shknn Mumy ta hana Abba ya kai ni kaduna kuma, at that time ina jss3, har yau kuma ban sake xuwa ba" Abuturrab dake ta kallonta ko kiftawa bbu yace "Yanxu kin iya alwala knn?" Tace "Uhm har da sllh ma, kasan suran da muke lkcn a islamiyyar da muke xuwa?" Da sauri yace "A'a" tace "Mulk" ya lumshe ido yace "Kuma kin iya?" Dariya tayi tace "May be xan iya yi da qur'an because i know the arabic letters very well" kallonta kawai yake can yyi murmushi yace "Gobe xa ki min in ji" mikewa tayi tace "Xan yi bacci...." Yace "Ohk dear ki rufe windows sbda ruwa" kai ta gyada masa ta nufi daki tana adduar Allah yasa kar ayi ruwan sbda tsoron tsawa da take. Washegari da safe wajajen karfe tara tana daki tana bacci Abuturrab kuma na xaune parlor sae missing system dinsa yake ga parlorn bai sa kayan kallo ba tukun, yasan accnt dinsa ya d'an girgixa da cire ciren kudin da yake in kuma xa aci gaba da haka to fa karewa xa suyi, ga credentials can gida bare ya fara neman wani aiki, Tausayin Maminsa kawae yake amma in dan Abbansa ne ko a jikinsa don dama sun saba irin haka, Ring din bell aka yi, ya mike yana kallon kofar, can ya karasa ya bude, daya daga yarinyar Hajiya Hajarah ce tsaye bakin kofar rike da basket me dauke da breakfast, ya d'an koma baya, tace "Mum tace a kawo" yace "Ohkk thanks soo much" daga haka ya karba ta juya ta wuce, ya koma parlor ya ajiye, ji yyi matar ta burgesa sosai sae yake jin ta a ransa kamar Mami, bude abincin yyi yaga wainar shinkafa ce ta miya sae brown yam and egg da fries egg with plantains, a wani karamar warmer kuma ga Irish, murmushi yayi ya koma yyi kwanciyarsa kan kujera, sae kusan karfe goma Samha ta fito cikin shirin doguwar riga amma ba abaya ba, karasowa tayi parlon ta xauna kasa ta sunkuyar da kai ganin yanda yake kallonta cikin sanyin murya tace "Ina kwana" ya mike xaune yace "Lafiya lau dear, ashe kin iya bacci kema haka" murmushi tayi bata ce komai ba, ya nuna mata breakfast yace "Gashi Mami tace a kawo mana" ta kalli abincin a hankali tace "Mun gode" ya mike tsaye yace "Dama ke nake jira, let eat" ba musu ta mike suka isa gun breakfast din. Da rana mai aiki ne ta kawo masu lunch, Abuturrab ya karba yana kallonta yace "Hajiya na nan ne?" Ta girgixa kai tace "Ta fita aiki tun safe" yace "Alryt" Da yamma bayan la'asar yana zaune bakin gate tare da mai gadin gidan Hajiya Hajarah ta dawo, gaisheta yayi ta amsa da murmushi tace "Ya gidan?" Yace "Alhmdllh Mami ya aiki?" Tace "Alhmdllh, ina Samha?" Yace "Tana ciki" tace "Toh a gaisheta" yace "Mami mun gode for the food" tace "Ohh it's nothing Boy" daga haka ta ja motar ta ta shiga gidan.

*Haske writers asso*
๐Ÿ’ซ *Noorul Huda*๐Ÿ’ซ




By khaleesat Haiydar๐Ÿ“šโœ๐Ÿป





35....

Yau kwana goma sha hudu da xuwan su Gombe, yana xaune parlor laptop a gabansa sae dai gaba daya hankalinsa baya kan abinda yake, damuwarsa daya yanda yake cire kudi a account gashi ba shigowa wasu ke yi ba, at all shi bai iya sana'a ba bae ma san yanda ake yi ba, he don't want to run short of money, ya lumshe ido ya rike kai yana tunanin mafita, dago kai yayi bayan kusan minti goma jin fitowar Samha daga kitchen, kallonta yake har ta karaso parlor ta xauna, ya sakar mata murmushi yace "Weldone" jin bata ce komai ba yace "Dear!" Ta kallesa ya ce "An fara Reg din Jamb, gobe sae mu je ki yi koh?" Kallonsa kawai take bata ce komai ba, yace "Yeah gobe da safe in shaa Allah" daga haka ya mike ya shiga daki. Suna breakfast the next day ya sa ta shirya suka fita reg din Jamb din, sae kusan da rana suka dawo gida, bae bari tayi girki ba ya fita ya siyo masu abinci, daren ranan ya dinga tunanin ko dae ya kira small mum dinsa yyi mata maganar CV dinsa ne, yanke shawarar yin hakan yayi daga karshe, washegari lahadi yana xaune balcony ya hango Hajiya Hajarah xaune daga nata Balconyn da laptop gabanta, ganin ta kallo inda yake ya mike ya nufi gun ta, ya d'an dukar da kai yace "Ina kwana Mami?" Tana murmushi tace "Lafiya lau Boy, ya gidan?" Yace "Alhmdllh..." Tace "Ina Samha?" Yace "Tana ciki Mami" tace "Alryt wai in tambaye ka boy..." Kallonta yayi da sauri yace "Ina ji Mami" ta ajiye pen din hannunta ta nuna masa kujerar gabanta tace "To xauna" Ba musu ya xauna tace "Transfer aka yi maka xuwa garin nan?" Ya sunkuyar da kai yace "A'a Mami" tace "Ohk, naga kuma har yanxu baka koma aikin ba ko hutun mai yawa ka dauka, or rather let me put it this way...." Shiru ya d'an yi sai kuma yyi murmushi yace "Mami bana aiki yanzu" da mamaki tace "Baka aiki kuma?" Shiru yayi nan ma, ta sauke ajiyar xuciya tace "It's ohk Boy kar in shiga rayuwar ka koh!" Yar dariya yayi yace "Noo Mami ba haka ba, laifi nayi ma Abbana ya amshe CV dina and everything, that was why i left kano" kallon mamaki take masa, can ta girgixa kai tace "Duk a dalilin auren da kayi knn?" Ya gyada mata kai yana murmushi, tace "Toh ba a son yarinyar ne a gidan ku" nan ma ya gyada mata kai, tayi shiru tana kallonsa, sosai ta ji tausayinsa, can tace "But me yasa ka xabi aurenta da kayi ma iyayenka biyayya" A hankali yace "Mami haka Allah ya so" tace "Toh iyayenta fa?" Yace "Su ba ruwansu" Tace "Satin ku nawa da auren yau?" Yyi shiru kamar mai nazari sai kuma yace "Sati biyu da kwanaki" girgixa kai tayi tana kallonsa tace "Ur field?" Dago kai yayi ya kalleta yayi d'an murmushi yace "Am a Medical Doctor" kallonsa kawai take kafin tace "A doctor?" Yace "Yes Ma'am" ta cire glass din idonta tace "Where did you schl?" Yace "Uk nayi karatu Mami!" Tace "Ina matakin karatun naka?" Yace "Nayi degree, snn nayi masters duk a fannin medicine..." takardar dake gabanta ta dauka da pen ta mika masa tace "Am ur patient suffering from Malaria Typhoid, prescribe me drugs and injections...." Yar dariya yayi ya karbi takardar yace "Alryt Ma'am" ya gama rubuce rubucensa bayan kusan minti shidda sannan ya mika mata takardar ta karba ta sa glass dinta tana kallo, gyada kai ta shiga yi, sai kuma ta mika masa wani takardan tace "Prescribe for someone suffering from chronic stomach ulcer!" Karba yayi ya kuma rubuce rubucensa ya mika mata, ta karba tana dubawa tace "Um! Yayi kyau, kana theatre ne?" Yace "Ina yi Mami" ta basa wani takardan tace "Rubuta min procedure din yanda xa ayi operating din patient that's suffering from Appendix...." Karba yyi cikin yan mintuna ya gama ya mika mata ta karba tana kallo, murmushi tayi tace "Alryt Doctor, am offering you work at my clinic daga gobe, sai ka shirya da safe mu fita tare..." Ya buda ido yace "Am soo grateful Mamina" tace "My pleasure, but try to reconcile with ur parent kaji boy, kar mace ta hadaka da iyayenka" a hankali yace "In shaa Allah Mami" aikin da take yi a laptop ta juya masa gabansa tace "Idan baxan takura ka ba pls go on with this it's understandable, am already exhausted dama..." Yace "Alryt Mami" daga haka ya fara duba abinda take yi, duk abun nn da suke Fatima na lekensu don tun da taji muryarsa ta taho da sauri ta labe, tana ganin uwarta ta mike ta bar gun da sauri, Hajiyar na kallonsa tace "Xaka iya tafiya da shi boy, idan ka gama sae ka kawo min" yace "Alryt Mami," daga haka ya dau system din da takardun dake ajiye yayi mata sallama ya wuce, ita kuma ta shiga ciki, shara ya tadda samha tana yi a parlor ya girgixa kai ya xauna yace "Kin san me?" Ta kallesa ta ce "Mene?" Yace "Three things you never get tired of are, bathing, cooking and sweeping i notice" dariya ya bata sae dai bata yi ba tayi murmushi ta xauna tace "Toh sae ka tashi kayi" ya wara ido yace "Haba in tashi in yi" ta hararesa tace "Ehh" mikewa yayi ya nufi gun da ta ajiye broom din ta dauke da sauri kafin ya isa, karba yake son yi taki sake masa tace "Nooo, ka kyaleni...."

*Haske writers asso*
๐Ÿ’ซ *Noorul Huda*๐Ÿ’ซ

By khaleesat Haiydar๐Ÿ“šโœ๐Ÿป

_Hafsat Ummu Ilham, i don't dedicate pages but here is a whole page for you dear sis, Am so grateful for the visit Allah ya bar xumunci sis ya raya su Ilham da Annur, Khaleesat heart you sisto_ ๐Ÿ˜

36.....

A can kano kuwa har gobe neman Abuturrab Abba yake, har imagining irin hukuncin da xae masa yake, Sosai Mami ta damu ganin har kusan sati bbu labari, to ina Aliyu xae kai yar mutane, kullum Hajiya Mariya sai ta xo gidan yayar tata tana kwantar mata da hankali amma ko kadan bata nuna tasan idan Aliyu yake ba duk da ta lura xargin ta yayarta take, Mahaifiyar Samantha kuwa ba don mai gidanta da ya hanata ba kotu dama tayi niyar kai karan, bata da aiki sae kuka da tsine ma Abuturrab ta kuma dau kudirin ko da ya dawo da Samantha kasheta kawai xata yi kowa ya huta don bata san mugun abinda yaje yyi mata, da dai ace ta xama musulma gwara ta kasheta a cewarta, bbu bata lkci ta shiga shirin tafiya Jerusalem don yin addu'an Allah ya dawo da Samantha tayi masa sacrifice dinta, mahaifin Samantha kam mutum ne mai saukin kai da boye damuwa baxa ka taba cewa abun na damunsa ba. Ranar Asabar Samha na kitchen tana kkrin daura girki da yamma shi kuma Abuturrab na xaune balcony rike da sabon system din da ya siya don bai iya rayuwa bbu shi, d'aga kai yyi ganin shadow din mutum, ya ga fatima tsaye daga bakin balcony din tace "Mum tace matar ka ta xo" daga haka ta juya ya bi ta da ido, haushin ta ya ji har cikin ransa, ko kadan yarinyar bata yi masa ba, ya ga alamar bata dau hali irin na mahaifiyarta ba sai girman kai, ya tabe baki ya mike ya shiga ciki, kallonsa Samha tayi jin abinda yace, can tace "Toh girkin fa!" Yace "Don't worry ki sa hijab ki tafi" ba musu tayi yanda yace ta fita xuwa part din Hajiya, tana parlor da duk 'yan matan nata uku sai wata dake xaune tare da fatima alamar kawarta ce, Samha ta risina ta gaisheta ta amsa da fara'a tace "Kadaici bai damun ki Samha, ki dinga shigowa nan ku saba da su fatima mana" murmushi Samha tayi tana wasa da fingers dinta tace "Toh" Hajiya tace "yauwa ko ke fa, xama ke dayan nn bbu dadi, ki dinga shigowa cikin mutane" kai samha ta gyada mata, Hajiya tace "Kar fa ki daura girki xa a kai maku idan an gama a nan kin ji" murmushi Samha tayi bata ce komai ba, Mami tace "Gobe su fatima xa su saloon sai ki bi su ki ga gari idan mijin ki ya amince, ke ma sai kiyi gyaran gashin daga can" Samha tace "Uhm to Mami" Fatima ta mike ta dalilin wayarta da yayi kara ta kalli kawarta Bilkisu tace "Gashi sun kira Billy" daga haka suka fita balcony, a waje Billy tace "Teemah new tenant din gidan nan ne yarinyar nn?" Fatima ta kalleta sae ta fasa d'aga wayar tace "Ehh" Billy tace "Kai amma yarinyar is pretty... Amarya ce koh?" Fatima tayi wani murmushi tace "Sai ma kin ga mijin xa ki san she is nt pretty...." Billy ta wara ido tace "Haba dai??" Fatima tace "Uhn He is more than cute, kin san Allah gabana faduwa yake idan muka hada ido da shi, but sai in wani daure fuska ko gaishesa bana yi" Billy tace "Waoww xan so in gansa kuwa" Fatima xata yi magana sai ga Samha ta fito ta sa takalmanta ganin yanda suke kallonta tace "Sannun ku" Billy tace "Yauwa!" Daga haka tayi wucewarta xuwa part dinsu duk suka bi ta da ido. Abuturrab yace "Har kin dawo?" Kai ta gyada masa tace "Tace xa mu je saloon gobe da yaranta" Shiru yyi yana kallonta sai kuma yayi murmushi yace "Allah ya kai mu" ciki ta shiga tayi kwanciyarta tun da tace kar tayi girki, fatima ce ta kawo masu abinci kusan Magrib bbu sallama ta shigo parlon, Abuturrab na xaune yana kallo a system Samha na gefensa ta jinginar da kanta jikin shoulder dinsa idonta a kan system din ita ma, a tare suka daga kai suna kallonta, ko kunya taji sai kuma ta sunkuyar da kai tace "Assalamu alaikum" Samha ce kawai ta amsa ta karaso ta ajiye abincin tace "Mum tace a kawo" Samha tace "Mun gode" daga haka ta juya ta fice. D'an tsaki Abuturrab ya ja can ciki, Samha ta kallesa tayi murmushi bata ce komai ba. Washegari khadija ce ta taho Balcony tana kallon Abuturrab dake duba newspaper da ya siya daxu da ya fita karo masu kaya a boutique, gaishesa tayi ya amsa tace "Wae Ummin mu in kira Anty Samha idan ta shirya" Abuturrab yace "Toh ga ta nan xuwa, ya sunan ki?" Tayi murmushi tace "Sunana khadija" yace "Alryt xan fadi mata Khadija" juyawa tayi ta wuce ya bi ta da kallo ganin banbancinta da yayarta, baxa ta wuce shekaru sha bakwai ba amma tafi yayar hankali, yana xaune parlor samha ta fito da hijab har kasa tana kallonsa, murmushi yyi yace "Cute" murmushin ita ma tayi, yace "Sae kun dawo but kar ki bari a dinga kalle min ke fa" dariya tayi yace "Yeah nikab ma xan siyo maki" kofa ta nufa ya bi ta da ido har ta fita, jiranta ta samu su Fatima na yi, Hajiya Hajarah tace "Toh sae kun dawo, Allah ya tsare hanya" driver ne xae kai su saloon din, fatima ta shiga gaban mota, Khadija da Rabi'ah suka xauna baya tare da Samha, su kadae suke mata hira har suka iso saloon din, fatima ta bude mota ta fita su ma suka fita suka bi bayanta xuwa cikin babban saloon din, khadija na kallon fatima tace "Big sis a fara yi ma Anty Samha koh?" Fatima ta kalli Samha ganin kallonsu take bbu yabo bbu fallasa tace "Alryt" daga haka taje tayi xamanta kan daya daga kujerun Saloon din sae dae can kasar xuciyarta ji take kamar ta shake yar uwar tata, Samha da Rabia aka fara ma gyaran gashin don akwae mutane saloon din, tun da aka bude kan Samha Fatima da duk yan saloon din ke kallo, matar mai gyara mata gashin sae cewa take "Maa sha Allah you've got a very fine long hair" Samha ta kirkiri murmushi bata ce komai ba sai dai duk a takure take ganin yanda ake kallonta, cikin minti ashirin aka gama mata ta mayar da hijab dinta da sauri, aka kama kan fatima sae dai ita kitso tace xata yi, ita din ma ba baya ba gun gashi, mai saloon din na kallonta tace "Baxa kuyi lalle ba Madam?" Khadija tace "Xa muyi" wani kallo Fatima ta watsa mata tace "ke da wa, waye xae jira kuyi lalle?" Khadija tace "Ae na tambayi Ummi tace mu yi" dauke kai fatima tayi bata ce komai ba, khadija aka fara yi ma snn Samha da taki yarda da farko har sae da Khadija da Rabi'a suka tilastata, suna saloon din har aka kira azahar, Khadija ta kalli Samha tace "Mu shiga daga ciki mu yi sllh Anty Samha" shiru Samha tayi sai kuma ta mike kamar mara laka ta bi bayanta, Khadija ce ta fara alwala a toilet ta fito snn Samha ta shiga, tsura ma tap din ruwan ido tayi, lkci daya xamanta gidan kanwar Abbanta ya fado mata, a hankali ta bude ruwan ta shiga alwalan kamar yanda take yi a kaduna da yaran Aunt dinta, tana gamawa ta fito ta ga Khadija ta shimfida mata wani darduma ta saka hijab dinta ta hau kan darduman babu abinda ta mance a ynda ake sllhn sae d'an abinda baka rasa ba, har hakan ya bata mamaki, tana idarwa Khadija tace "Me xa a karbo maki?" Murmushi Samha tayi tace "Bana jin yunwa..." Khadija bata ce komai ba ta fita, samha ta mike ta bi bayanta, snacks da drinks Khadija ta sa driver ya karbo masu, bbu yanda samha ta iya haka ta karba, ba su suka bar saloon din ba sai kusan karfe uku, part din su suka tafi gaba daya, Hajiya ta yi masu sannu da xuwa tana kallon Samha tace "Har kun dawo?" Samha ta gyada mata kai, tace "Toh sannun ku daughter, bari a xubo maku abinci" Samha tace "Ae mun ci" Hajiya bata saurareta ba tasa mai aiki ta xubo masu abinci gaba daya, har aka yi la'asar tana parlon, Hajiya tace "Khadija ku shiga ciki ku yi sllh" Khadija ta kalli Samha tace "Muje daki muyi sllh" ba musu Samha ta mike ta bi

Please Login or Register in order to submit comment