Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace "Ke kin karya?" Gyada masa kai kawai tayi, yace "Yaushe Baaba xata dawo?" Tace "Kila tana hanya yanxu" yace "Bakya xuwa makaranta ne?" Ta kallesa tace "Yau alhamis" ya d'an buda ido yace "Haka fa" Bai kuma cewa komai ba, can tace "Bacci take ne?" Yace "Ehh" haka suka yi ta xama tsakar gidan shiru har Hansae ta dawo ya mike ya karbar mata kayan hannunta snn suka gaisa. Sai kusan tara da rabi Samantha ta tashi, har lkcn Abuturrab na xaune waje, ta mike ta dau sabulu da sponge ta fita, su biyu ne tsakar gidan shi da Binta dake wanke gyero, Samantha bata ko kallesu ba Abuturrab da ya bi ta da ido yace "Wanka xa ki yi?" Binta na jin haka ta mike tace "Bara in juye maki ruwan xafin ki" daga haka ta dau bokiti ta nufi gun murhu ta juye ruwan kai ta kai bokitin gun randa ta sirka ta kai kewaye tace "Bara in dauko maki sabulu" Samantha tace "Akwai sabulu a nn" Binta ta dauko kwando ta mika mata Samantha ta shiga bayin, mikewa Abuturrab yayi ya shiga daki.

*Haske writers asso*

Da fatan anyi sllh lfya Allah ya maimaita mana.
💫 *Noorul Huda*💫

By Khaleesat Haiydar📚✍🏻

32.....

Samantha na shigowa bayan tayi wanka bata ko kalli Abuturrab ba ta nufi gun kayan da ya siya ta durkusa, can ta kallesa taga kallonta yake ta bata fuska tace "Kaya xan sa?" Ya wara ido yace "Na rike ki? Ki sa mana" tace "Toh ka fita" murmushi yayi yace "In fita gun Binta ki kuma daure min fuska" daukar abinda xata dauka tayi ta nufi kofa ya fixgota tace "Wayyo ni ka kyaleni kaya na xan je in sa a waje..." Ya wara ido yace "Toh me xa ki boye min da ban sani ba jikin ki!" Ta yi masa wani kallo tace "Ae dai na wasu ka sani ba nawa ba malam" Dariya yayi ya kai bakinsa kunnenta yace "See you, ke nakin ma special sani xan masa, sanin da bbu wanda xai kara masu har abada.... Only me" kwace kanta take son yi ya ki saketa, ta boye fuskarta jikinsa kamar xata yi kuka tace "Bana son irin haka Doctor" yana dariya yace "Toh na daina baby, but a nan xa ki sa kayan ki" bbu yanda ta iya haka ta shirya a dakin, and he pretend he's not looking at her, tana gama shiryawa ya xuba mata kunu ya mika mata ta sha kadan ta ajiye kosan ma bata ci ba, yana kallonta yace "Xa mu tafi yanxu!" Kallonsa tayi bata ce komai ba, can ta mike ta fara gyaran dakin, ya taimaka mata suka gama, sha daya suka fito xa su wuce, Hansai ta fito tana masu Allah ya tsare hanya tana cewa Allah sa ba shikenan an gama xumuncin ba, Abuturrab yayi dariya yace "In shaa Allah baxa mu mance ku ba Baaba wataran xa mu xo, dubu uku ya bata ta dinga godiya har da hawayenta, Abuturrab ya kalli Binta dake xaune nesa da su yace " Babu Sallama Fatima" kallonsu tayi yaga hawaye cike idonta, Hansai tace "Kaji shashanci to tashi ki rakasu mana" Samantha tayi ma Hansai sallama sannan ta fita, Ya karasa kusa da Binta ya durkusa yace "Nace maki xamu xo wataran fa..." Bata ce komai ba sae share hawayen idonta da take yace "Toh tashi ki raka mu" ba musu ta mike ta dau sandar ta na kiwo da nonon da ta tatsar masu yana gaba tana biye da shi a baya suka fita. Karasawa yayi ya kamo hannun Samantha yace "Baku yi sallama da Binta ba" ta kalli Binta ta gefen ido tace "Mun tafi Allah ya saka da alkhairi" kai kawai Binta ta gyada mata, daga haka yace "Mu je to ki raka mu inda xa mu samu Babur" gaba ta shiga suna biye da ita a baya, sun yi nisa sosai sai ga wata mota na tahowa a bayansu, Abuturrab yace "Wannan fa" Binta ta kalli Motar tace "Motar D'an lado ne, shi daya ne mai mota a rigar nan a birni yake aiki, da ka tsayar da shi ka ji inda xa shi ko?" Abuturrab ya tsayar da motar kamar yanda tace ae ko ya tsaya ya sauke glass, Abuturrab ya gaida sa mutumin da xai iya kaiwa arba'in ya amsa yana kallonsa, Abuturrab yace "Don Allah idan ba damuwa ina ka nufa?" Mutumin yace "Gombe xa ni...." Abuturrab ya d'an yi shiru, sae kuma yace "Toh mu ma can muka yi, xa a taimaka?" Mutumin yace "Ba matsala ku shigo" Abuturrab ya bude ma Samantha baya ta shiga ya rufe, ya kalli Binta da wasu hawayen suka cika idonta ya ciro dubu biyu duk da ya so bata fiye da haka ya damka mata a hannunta yace "Na maki alkawarin wataran xa mu dawo" da kyar ta yarda ya sa mata a hannunta ta mika masa nonon dake a leda ya karba yayi godiya sannan ya juya ya shiga front seat ya d'aga mata hannu ta juya da sauri ta bar wajen, D'an lado ya ja motarsa yace "Amma ba nn rigar kuke ba koh?" Abuturrab yace "Eh mu baki ne" D'an lado yace "Da alama kam, toh Allah ya sauke mu lafiya" daga haka ya maida hankalinsa kan tukin da yake da gani dae kasan hannunsa bai gama fadawa ba, ta madubi Abuturrab ya dinga kallon Samantha ganin yanda ta wani turo baki, dariya yake son yi amma ya dake, har suka isa gombe bayan tafiyar awa biyu da rabi bbu wanda yace komai cikinsu, Abuturrab sai kallon garin gombe yake yana tunanin to ina xa su, bbu wanda ya sani a gombe infact bai ma taba xuwa ba, D'an lado ya katse masa tunanin da yake yace "ina xa ku sauka kenan?" Abuturrab ya kallesa yace "Ko nan ne ka sauke mu" D'an lado yayi parking Abuturrab ya bude motar ya fita, ya xaga ya bude mata ita ma ta fito, ya karbi ledan kayan dake hannunta yayi ma D'an lado godiya ya ja motarsa ya wuce, kalle kallen wajen Abuturrab ya shiga yi, yana neman bankin da yake ajiya, yaga duka ukun a area din, yasan first bank da Gtb ba dai layi ba, hakan yasa yayi deciding ya shiga unity, ya kalle Samantha yace "xan shiga bank, sai ki jira ni waje or we go in 2geda" ta girgixa masa kai kawai tayi xamanta gaban bank din, shi kuma ya shiga ciki, direct ya tafi gun CC, bae wani jima ba aka xo kansa, yace yana son a duba masa ko nawa ne account dinsa, daga sama har kasa matar ke kallonsa, can tace "ATM din waje me yake yi, ko wayar ka fa?" Yace "Akwai layi sosai, waya kuma bani da, idan xa ki taimaka ki taimaka...." Da kamar xata yi magana sai kuma ta fasa, sai kuma tace "Fado account number" ya fada tayi danne dannenta snn ta kallesa ta kalli hotonsa dake jikin computer tace "Dubu dari shidda da ashirin" ya xauna yace "Good, na gode kwarai, ana sayar da withdrawal slip a nan?" Ta nuna masa gun da xai siya snn ta kira wani customer, yana xuwa ya dauka ya ciro dubu daya da aka ce ya bayar ya mika, ya ari pen ya cike slip din, dubu dari biyu ya saka yayi sign ya nufi gun Cashier, su ma sai da yayi masu jan ido wai wani yaje atm they re busy, yace "Haba wani atm xan je, ba fa dubu hamsin xan cire ba malam, kawai inje in bata ma masu cire dubu biyar lkci, awa nawa xan dauka ina cire dubu dari biyu? Plss answer me coz i wanna get out of here" Ba yanda suka iya haka suka karba bayan minutes din da basu wuce sha biyar ba suka basa kudin sa, nan ya roki alfarmar jaka aka basa ya xuba kudin yayi ficewarsa, ya isa gun Samantha yace "Am sorry Dear, tashi mu je" ta mike ya karbi ledan hannunta suka nufi titi, yana kallonta yace "Dear hotel fa xa mu je kafin mu samo solution" ta kallesa tace "Hotel?" Shiru yayi yana kallonta, ta dauke kanta, ya sauke ajiyar xuciya yace "Just for today dear.... Kinga bamu san kowa a gombe ba, it's my 1st time here" jin bata ce komai ba ya tsayar da mai adaidaita yace "Hotel mafi kusa xaka kai mu" sae da ya tsaya ta shiga sannan ya shiga, ba laifi hotel din na da kyau, ya biya kudin kwana daya dubu ashirin da biyar a reception aka basa makulli da room number, babban daki ne sosai da toilet a ciki, ya kalli samantha da har lkcn ta ki cewa komai ya xauna bakin gado bayan ya ajiye ledan hannunsa yana kallonta yace 'You followed me without trusting me kenan Samha..." Bata bari sun hada ido ba ta karaso dakin a sanyaye ta xauna can karshen gado, girgixa kai yayi ya mike ya bude jakar dake dauke da kudi ya cire dubu dari, ya sa a aljihu yace "Am coming back right away, me xa ki ci?" Cikin sanyin murya tace "Anything" ya juya ya fita ya kulle dakin, tagumi tayi tana tunanin anya did she made the right decision following him and neglecting her dear parent, hawaye ya cika idonta ta fada kan gadon ta fashe da kuka, Why is all this happening to her within just 2 months, she know God will never forgive her for doing this to her parent, but she love him and they will never allow her to be with him, tayi kukanta me isarta ta mike ta dau soap da sponge, toothpaste da sponge ta shiga bayi dake dakin, wanka tayi ta fito ta shirya tayi kwanciyarta nan da nan bacci ya dauketa, bayan azahar Abuturrab ya dawo, ya ajiye ledan hannunsa yana kallonta, bai tada ta ba ya shiga toilet ya dauro alwala ya xo ya gabatar da sllhn Zuhur, ya jima xaune yana addu'a daga bisanni ya mike ya shiga bayi yayi wanka ya fito ya shirya cikin daya daga cikin kananun kayan da ya siyo, ya bude fried rice din da ya siyo masu da drinks ya ci wanda xae ci ya ajiye sauran, kwalin karamar waya ya dauka ya bude ya ciro wayar ya sa sabon sim din da ya siyo ya kunna wayar, ya loda airtime yayi dialing number Hajiya Mariya gabansa na faduwa a xuciyarsa kuwa addu'a yake Allah yasa ita kadai ce a gun, bugu daya biyu ta d'aga, ya shafa kai a hankali yace "Mumy!" Hajiya Mariya dake xaune daki tare da Mami da frnds dinta biyu, ta saci kallon Mumy ganin kallonta take tace "Helloo!" Abuturrab yace "Ina ji Mumy ina yini...." Hello... Hello... Abinda ta dinga cewa kenan can tayi tsaki ta katse, Hajiya Maimuna tace "Network koh?" Hajiya Mariya tace "Ae kuwa...." Hajiya salaha tace "Toh da ki fita waje...." Hajiya Mariya ta tabe baki tace "Kila kiga ya dawo kuma" Abuturrab da sharp thinking yana jin reaction dinta yasan ba ita kadai bace a gun don haka bae sake kira ba, Mikewa Hajiya Mariya tayi tace "Bari dai ban san ko masu bani kudi bne bari inje waje" daga haka ta fita, bata ko kalli Abba dake parlor da abokansa ba tayi ficewarta waje, Abba ya bi ta da kallo, can ya girgixa kai yace "Wannan Mariyar ma ban yrda da ita ba bakinsu daya da Aliyu, ba abun mamaki bne ma tasan inda yake!" Col Usman na girgixa kai yace "ban taba ganin mai taurin kai da tsaurin ido irin Aliyu ba...." Abba yace "Duk ya kuskura ya shigo hannuna wllh sae bullet ya kare a kafafuwansa..." Har kofar gida Hajiya Mariya ta fita sanin halin mijin yayarta, tana fita ta kira number da sauri, Aliyu naganin kiranta ya daga, tace "Aliyu!!" Ya buda ido yace "Mumy..." Tace "Kuna ina Aliyu?" Shiru yayi, tace "Ohh ni din ce yanxu kuma baxa ka gaya ma inda kake ba" yace "Ke kina ina Mumy" ta hade rai tace "Ina tambayarka kana tambayata..." Ya sauke ajiyar xuciya yace "Kiyi hakuri Mumy, but don't say anything to anybody plss...." A fusace tace "Uwarka! ni kake gaya ma haka da can ban ce komai ba sae yanxu" bae san lkcn da yayi dariya ba yace "Yi hakuri Mumy, ina Gombe!" Ta xaro ido tace "Gombe kuma Abuu, wa ka sani a can?" Ya girgixa kai yace "Ba kowa wlh..." Da damuwa tace "Yarinyar fa?" Ya kalli Samantha dake ta bacci yace "Ga ta Mumy, she's sleeping" Hajiya Mariya tace "Kaji tsoron Allah Aliyu, kada kayi using wnn advantage din a kan baiwar Allah don tana sonka, kar ka manta ba fa matar ka bace, don't use her....." A sanyaye yace "Mumy baki yadda da Aliyun ki bane kuma, kema kin san ba hali na bane" Hajiya Mariya tace "No son! Kasan sha'anin rayuwa, bbu abinda shaidan baxae iya yi ba...." Sosai jikinsa yayi sanyi yace "In'sha Allah Mumy xan kiyaye.... Mami fa?"

*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫

By khaleesat Haiydar📚✍🏻

33....

Hajiya Mariya tace "She's inside" ya d'an yi shiru sai kuma yace "Abba fa" tace "Yana nan.... But you re in trouble in har ka shigo hannunsa" Aliyu yayi murmushi yace "Na sani" da damuwa tace "Ka dai kula Aliyu tausayin yarinyar nake, tunda har ta guji iyayenta sbda kai, jan ra'ayinta xuwa musulunci baxai yi wahala ba" Yace "Hakane Mum, dama am planing of marrying her soon don ban son in cuceta, i don't want her to regret trusting me, idan nayi haka komai xae fi zuwa da sauki" Hajiya Mariya tace "Anya, naga kamar ya fi ka jira sae ta amshi musulunci, kar ta ga kamar kana using advantage din auren ne..." Bude gate ta ji anyi da sauri tace "Za mu yi waya Aliyu, don't call again xan dinga kiran ka..." Daga haka ta katse wayar, Abba ta gani bakin gate waya kare a kunnensa ya rako abokansa xa su wuce, tayi dialing din number wata da xata bata kudi suka yi magana snn ta juya ta nufi gate din ya bata hanya tayi wucewarta, bin ta yayi da kallo har ta shiga cikin gida, ya juya ya koma ciki shi ma bayan abokan sun shiga mota, ya shiga part dinsa ya kira Mami, bbu bata lkci Mami ta iso, yana tsaye bakin window rungume da hannunsa (Inda Aliyu ya gado rungume hannu knn, lol" ya juyo yana kallonta yace "Hajarah! i won't take it likely with ur sister idan naga da sa hannunta a abubuwan nan da Aliyu yake, xan ajiye cewar yar uwarki ce a hukuntata yanda ya kamata...." Mami tace "Ban yi mamaki ba... You can do more than that, yanxu kuma ka bar xargina ka koma xargin yar uwata" ya daga kafada yace "Ni dae na gaya maki" juyawa tayi ta fice daga dakin, dakin su Ramla ta shiga ta ci kukanta Ramla na lallashinta kafin ta fita ta koma dakinta, Hajiya Mariya na ganin Abba ya kira Mami dama ta yi saving din number Aliyu da wani suna daban tayi deleting dinsa daga call log, ko da Mami ta shigo dakin Hajiya Mariya na bathroom, ta dau wayarta ta fita, kiranta na karshe ta kura ma number ido, can tayi dialing taji muryar mace, ta dudduba dai bata ga alamar komai ba ta koma daki, Hajiya Mariya bata tambayeta dalilin daukan wayarta ba sae harkan gabanta take. Tunani Abuturrab ya dinga yi ko dai gida xae kama masu nan gombe ne, duk ya rasa takamaiman solution, kallonta yayi ganin tana juye juye kan gado, can ta mike xaune yace "Cikin ya fara koh?" Ta gyada masa kai, ya mike ya dauko mata abinci yace "Sauko ki ci in maki allura" ba musu ta sauko ya bude mata abincin ta fara ci, alluran ya hada ya ajiye yana jiran ta gama, bata wani ci da yawa ba ta mike yace "Sauran fa" da kyar tace "Anjima xan ci" daga haka ta kwanta ya mike ya karasa kusa da ita yayi mata alluran, Finger dinta ya kura ma ido ganin har lkcn xoben da ya sa mata na nan, ya kama hannunta a hankali yace "Samha!" Dago kai tayi ta kallesa, ya sakar mata murmushi ya kai lips dinsa kan hannun cikin sanyin murya yace "I will never let you down dear, i will be ur hero, i will be ur everything...." Hawaye ya cika idonta ya dago ta ya rungumeta, ta fara kuka a hankali, jin tayi shiru ya dago kanta a hankali ya ga idonta a lumshe, kwantar da ita yayi ya mike ya nufi window yana tunanin next action din da xae dauka, can ya dau kudi ya fita, wani me taxi ya tsayar bayan tsayuwar kusan minti sha biyar a bakin titi duk yana duba responsible cab man da xae tsayar su yi magana, yana kallon mutumin yace "Pls ina d'an tambaya ne" cab man din yace "Allah yasa na sani" Abuturrab na shafa beard dinsa yace "Kasan inda xan samu agent... I mean their office, anywhere around?" Mutumin yace "Wae na gida?" Abuturrab yace "Yes!" Mutumin yace "Wanda na sani da nisa daga nan, sae dai..." Abuturrab yace "No mu je kawai ka kai ni" daga haka ya shiga mutumin ya ja taxi din. Tafiyar kusan minti ashirin suka yi suka iso office din wasu agent, Abuturrab ya fito yayi masa godiya ya basa dari biyar ya shiga office din, ba shi ya fito ba sae kusan karfe shidda bayan an basa tabbacin nan da xuwa gobe xa a karbar masa gida. Ko da ya dawo lodge dinsu tana bathroom tana wanka, ba a dau lkci ba ta fito daure da towel, tana ganinsa ta tsaya nan bakin kofa, yace "Naga alamar ba kya gajiya da wanka yarinyar nan...." Murmushi tayi bata ce komai ba ya mike xae shiga yayi alwala ta durkusa da sauri tace "Nooo" xaro ido yayi yace "Ina ruwana da ke?" Murmushi yayi ya shiga toilet din, ta mike da sauri. Ko kafin ya fito har ta gama shiryawa, yana kallonta yace "Xan je mosque, will be right back" ta gyada masa kai ya fita, sae bayan Magrib ya dawo dakin, ya ganta xaune shiru da alamar tunani take, ya karasa kusa da ita ya durkusa ya ajiye ledan fruits din hannunsa yace "Sorry Dear, na jira anyi magrib ne" ta d'an yi murmushi bata ce komai ba, ya xauna ya bude mata ledan fruits din yana kallonta, Apple ta dauka ta kai baki a hankali, shi ma ya dauka ya kai daya baki, wayarsa dake kan gado ya fara ring, ya dauka yana kallon screen din yaga Hajiya Mariya ce, ya daga ya kai kunne yace "Hello Mum!" Tace "Aliyu where is she?" Kallon Samantha yayi ya mika mata wayar yace "My mum!" Ta sa hannu ta karba ta kai kunne, Hajiya Mariya tace "Ya kk Samha?" Samantha tace "Lafiya Mumy ina yini?" tace "Lafiya lau, kiyi hakuri kin ji, Allah na tare da ku, kar ki sama kanki damuwa...." Kai kawae Samantha ke gyada mata kamar tana ganinta.

*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫

By khaleesat Haiydar📚✍🏻

34.....

Mikewa tayi a hankali ba tare da ta kallesa ba ta dau rigar baccin ta shiga bathroom, ba a dau lkci ba ta fito, kallo daya yyi mata ya dauke kai, ta nufi kan gado a hankali ta kwanta ta juya masa baya, bayan kusan minti goma ya mike ya cire shirt din jikinsa ya shiga bayi, ko da ya fito kashe tvn dake aiki yyi ya kashe wutan dakin ya karasa gado ya kwanta, a hankali ya birgina inda take, cikin sanyin murya tace "Doctor..." Yace "Samha...." Bata ce komai ba ya juyo da ita ya kwantar da ita kan faffadan kirjinsa yace "Sleep tight love, am with you" ta lumshe ido tayi lamo jikinsa, a haka har bacci ya dauketa, a hankali ya kwantar da ita ya mike ya koma kujerar dake dakin yayi kwanciyarsa amma ya kasa bacci sae juye juye yake, can dae ya mike ya shiga bayi ya dauro alwala ya fito ya tada sllh, sae kusan karfe uku da rabi ya samu yayi bacci, da asuba a masallacin dake cikin Hotel din ya fita yyi sllh sae da gari ya waye ya shigo masu dakin da breakfast, har ta shirya ya sameta, yana kallonta da mamaki yace "Ina fita kika tashi amma koh?" Kai kawai ta gyada masa, yayi murmushi yace "Alryt xo kiyi break kafin in shirya" daga haka ya shiga bathroom, ko da ya fito har ta gama cin abinda xata ci, yace "Are you sure kin koshi?" Ta gyada masa kai, shiryawa yayi ya ci chip da egg din kadan ya mike yace "Bacci nake ji Samha, let me sleep small" murmushi tayi ta mike xata gyara masa gadon yace "Noo don't worry dear...." Daga haka yayi kwanciyarsa, ta koma ta xauna ta rufe sauran breakfast din, yana kwanciya bacci ya daukesa, ita dai tana xaune idonta a kan tv, sae dae ko kadan ba sanin kan film din da ake tayi ba, tayi nisa a tunanin da take, Abbanta kawai take tunani wanda hakan yasa hawaye ya cika idonta, why did she accept to leave her family because of Aliyu, hade kanta da kujera tayi hawaye na sakko mata sae a snn take jin bata kyauta ba, tayi kukanta mai isarta daga nan ita ma bacci ya dauketa don yanda bai yi wani bacci ba haka ita ma bata jiya ba daren jiya duk tana kallonsa yana sllh, sai kusan goma da wani abu Abuturrab ya tashi, ganin yanda ta kife kai ya mike da sauri ya isa gabanta ya dafa ta yace "Samha" dagowa tayi da sauri tana kallonsa, kallon idonta ya dinga yi, da damuwa yace "Kuka kika yi?" Ta sunkuyar da kanta ya dago ta yace "Samha you re regretting everything koh?" Ta fashe da kuka tana girgixa masa kai, duk ya rikice yace "No plss samha, kar ki min kuka don Allah, naji xan maida ki gida...." Da sauri ta girgixa kai cikin sanyin murya tace "Am not regretting" yace "Toh me yasa kike kuka" goge hawayenta ta shiga yi cikin sanyin murya tace "Its just.... We re in trouble" ya lumshe ido ya kamo hannunta yace "Allah na tare da mu Samha, kar ki damu kin ji" sunkuyar da kanta tayi, yace "Tashi ki raka ni!" Ba musu ta mike ya kashe kayan kallon yace "Mu je" kofa ta nufa ya bi bayanta, suka fita ya kulle dakin, gun agents din jiya ya tafi, suna isa daya daga agent din yace su je ya ga gidan ko yayi masa, a motar agent din suka tafi, gida ne babba hadadde mai flats biyu, gidan na dauke da dakuna uku manya, Abuturrab ya kalli Samha yace "You like it?" Sunkuyar da kai tayi, yayi murmushi yace "Alryt, yallabai gidan yayi, thanks much" bbu bata lkci Abuturrab ya biya komai na gidan kusan 450k, da yamma bayan sun dawo hotel din yace "Xuwa jibi sae mu koma can koh dear?" Kallonsa tayi bata ce komai ba, ya kamo hannunta yace "Kin yi shiru?" Murmushi tayi bata ce komai ba. Washegari Abuturrab shi kadae ya fita ya bar ta tana bacci don xuwa can gidan ya ga abubuwan da ya kamata ya xuba, a ranan yayi furnishing gidan gaba daya, har food stuffs sae da ya siya, ya kashe kudi ba na wasa ba, da yamma ya koma hotel, Wanka ya sameta tana yi, yyi kwanciyarsa don ya gaji, washegari da ya kasance alhamis misalin sha daya suka tafi can gidan, nan ya fara tunanin anya xae yi ynda Hajiya Mariya tace masa kuwa, bai jin xae iya xama gida daya da ita bayan ba muharramar sa bace, idan shaidan bai ci galaba kansa yanxu ba yasan ko a jima ko a dade akwai ranan da abinda yake gudu xae iya faruwa, don yanxun ma he's just fighting his self from inside, kwanciyarsa yyi a parlor yana tunanin next step din da xae dauka, ana kiran

Please Login or Register in order to submit comment