Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Abuturrab na xaune a tabarma tare da Alto yana shan fura da nonon da Hansai ta dama masu Samantha ta fito da Binta, kallonta ya dinga yi ita ko kallo daya tayi masa ta dauke kai Binta ta rakata har bayin snn ta dawo, Samantha na fitowa daga wankan Hansai tace "Ga buta can ki dauka kiyi alwala" shiru Samantha tayi bata ce komai ba, can ta kalli Abuturrab da idonsa ke kanta, ta girgixa kai a hankali tace "Bana yi" daga haka ta shige Bukkar Binta, wata yar top da xani binta ta bata ta sa, tana gama shiryawa binta tace "Ki fito ku ci abinci wae ke yake jira" Samantha ta mike suka fita a tare, Alto ya mike yace ta taho ta xauna, ta karasa ta xauna kan tabarmar, Fura Abuturrab ya mika mata ta karba ta ajiye, bata bari sun hada ido ba duk da irin kallon da yake mata, shi ya fara sa hannu cikin langar dake dauke da Burabisko da miya yayi bismilla ya fara ci, kasa sakewa Samantha tayi taki cin abincin sai fura da take sha a hankali Hansai tace "Ko xa ku shiga daga ciki naga kamar a takure take" Kamar Abuturrab jira yake yace "Toh" Hansai tace "Binta kai masu abincin daki" Binta ta je ta dau abincin ta shiga da shi bukkarta, Abuturrab ya mike yana kallon Samantha ita ma ta mike ta bi bayansa suka shiga Bukkar, suna shiga ya nuna mata kusa da shi ta xauna, ya dau cup din furan ya mika mata ta sa hannu ta karba yace "Finish it immediately ki ban cup din" ta yi d'an murmushi ta kai baki, kadan ta sha tace "Na koshi" ya hade rai yace "Sae fa kin shanye" girgixa kai tayi ya kwace cup din hannunta ya matso kusa da ita ya rike kan ta ya kai cup din bakinta, bbu yanda ta iya haka ta dinga sha kamar xata yi kuka, sae da ya ga ya wuce rabi snn ya ajiye ya ce "oya sa hannu" lekan abinci tayi tace "What's that" Hannu yasa ya deba ya kai bakinta, ta bude bakin a hankali ya xuba mata, da kyar ta dinga taunawa tana kallonsa kmr me taunar magani, ya dake bai bari yayi dariyar dake cin sa ba, tana hadiyewa tace "Baxan iya ci ba Dr " Ya girgixa kai yace "No, but da dadi fah, there's no other food than this!" Ta fashe da kuka tace "Baxan iya ci ba..." Shiru yayi yana kallonta, can ya kamo hannunta cike da tausayi yace "Toh me xa ki ci" cikin rawar murya tace "Rice!"

*Haske writers asso*📚✍🏻
💫 *Noorul Huda*💫

30.....

Shiru yayi ya rasa abinda xai ce mata, can ya sa hannu cikin aljihinsa yaga har lkcn kudin da yayi withdraw na nan, ya rufe burabiskon ya mike yace "To taso mu je" a hankali ta mike ta bi bayansa suka fita, yana kallon Hansai da Alto da yare yace "Baffa xa mu d'an xaga rigar nn...." Alto tace "Toh har kun cinye abincin ne?" Yace "A'a idan mun dawo xa mu ci, furan ya ishe mu" Alto tace "Toh bari Binta ta xaga da ku, sai dai fa ba wani girma ne da kauyan namu ba" tana dariya ta kare maganar shi ma yayi dariya yace "Ni kuma hakan ya burgeni sosai babu hayaniya" Alto ya kwalo ma Binta kira ta fito yace tayi masu jagora xa su xagaye Rigar garki, tace "Toh" snn ta koma ciki, dama shigar fulani tayi dogon gashinta da ke kai wa har kusan gadon bayanta an tufke mata shi gida uku, ta dau sandar kiwonsu tana kallonsu Abuturrab da fillanci tace "Mu je" Samantha dai ko kallonta bata yi ba har suka fita, tana tsakiyarsu suke tafiyar ko wani Bukka suka wuce sai ta fadi masu na wanene duk da fillanci, kai kawai Abuturrab ke kada mata, can ta kalli samantha da yaren tace "Ke bakya magana, ya sunan ki" Samantha bata ce komai ba, Abuturrab yace "Sunanta Fatima amma ana kiranta da Samha" kallonsa Samantha tayi ya wara mata ido, Binta tace "Lah ashe sunan mu daya, to me yasa kanwar taka bata magana?" Ya buda hannu yace "Haka take" tace "To kai ya sunanka?" Yace "Aliyu" ta xaro ido "Suna mai girma" Hira Binta ta dinga masa tun yana amsa mata da uhm da eh da A'a har dai ya fara magana, Samantha dai tafiyarta kawai take bata ko kallesu ba, Binta tace "Ina son wataran ni ma inje birni" kamar xata yi kuka ta kare maganar, yayi yar dariya yace "Kar ki damu xamu xo mu dauke ki wataran..." Tace "To a ina xan xauna ni da ban san kowa a birni ba" Yace "Gidanmu mana" tayi murmushi tace "Allah yasa kar ku mance da ni" yana murmushin shi ma yace "In'sha Allah" kallon Samantha yayi da fillanci yace "Are you okay?" Bata ce komai ba bata kuma kallesa ba, tsayawa yayi yana kallonta Binta ma ta tsaya, ita ko ta ci gaba da tafiyarta, ya jawota da damuwa yace "Samha tell me what's wrong?" Ta mayar masa da fillanci tace "Just want to be left alone" shiru yayi yana kallonta, ta kwace hannunta ta ci gaba da tafiya, Binta ta kallesa a hankali tace "Kilan so take ku je gun Ammin ku" Murmushi ya k'irkira bai ce komai ba suka ci gaba da tafiya, can ya kalli Binta yace "Akwai inda ake sai da abubuwan ci a Rigar nan" tace "Ehh mana akwae yar kasuwa, ana tsayar da warar fulani, hura da nono, gyada kai har da nama da...." Ya katse ta yace "Shinkafa fah?" Ta ce "Akwai mana" yace "Toh muje xan siya mata shinkafa xata ci" Binta ta kalli Samantha da tayi gaba can tana tafiya tace "Bata cin Burabisko?" Kai kawai ya gyada mata, ya karasa da sauri gun Samantha ya kamo hannunta da turanci yace "What's all this dear?" Bata ce komai ba, ya ci gaba yace "Did i offend you in anyway" Binta dake kallonsu ta gefen ido ta ci gaba da tafiya, ganin baxa ta kulasa ba ya ci gaba da tafiya yana rike da hannunta, shinkafar dari uku ya siya da wani miya da ke basa kyankyani, ita kanta Samantha da ganin yanda take kallon abincin kasan bbu yanda ta iya ne, suna gama siya yace su koma gida, wnn karan su biyu ya bari suka yi gaba yana biye da su a baya. Har suka isa gida bbu wanda yace komai cikinsu, Su Alto suka yi masu sannu da xuwa, ba laifi Samantha ta ci shinkafar sbda yunwar da take ji, ya tallabi cin dinsa yana kallonta har tace ta koshi, yayi murmushi yana gyada mata kai, murya can kasa yace "Kinsan me love?" Kallonsa tayi bata ce komai ba, a hankali yace "Idan ance ki tashi kiyi sllh ki dinga cewa toh" ta kafe sa da manyan idonta, can tace "Ban gane ba" ya lumshe ido ya bude cikin sanyin murya yace "I mean idan aka ce maki ga ruwan alwala ki ce to, ki dauka...." Wani kallo take masa tace "In yi me?" Yace "Kiyi alwalan ko baki iya ba!" Da mamaki ta dinga kallonsa, can ta girgixa kai tace "No!" Shiru yayi yana kallonta, can yace "Let me ask you, what's Good about Christianity?" Ta wani hade rai tace "What's Good about Islam?" Kamar jira yake yace "A lot, it's a religion of peace.... The true religion, Christianity is not a religion, it's just a way of life.... Ki bani inda aka ambaci Christianity a bible nima kuma xan baki inda aka ambaci Islam a bible...." Wani kallo ta dinga yi masa ya gigixa kai yace "If you know ur bible too well John 14;27 Jesus said 'Peace i leave with you, My peace i give to you, not as the world gives, and do not allow ur heart to trouble you' here Jesus made mentioned of the religion he practiced and let to his disciples (Followers) as (Shalom) and did you know the meaning of Shalom?" Har lkcn kallon tara saura qtr take masa, ya matso kusa da ita ya d'ago kanta yana kallon kwayar idonta yace "In kinsan Bible din ki sosai sanin ma'anar shalom baxai maki wahala ba... Ashe kawae ke 'yar muna Christian ce" kwace fuskarta tayi tace "Shalom means Peace!" Murmushin da ya baiyyana dimples dinsa yayi yana kallonta yace "Good, And that's the meaning of Islam (peace!), Jesus ya gargadi mabiyansa (disciples) kan cewar kada su bi son xuciya, kada su bi ra'ayinsu, but unfortunately they all followed their heart desire and got their selves the name Christianity, a name not found in the bible, a name gotten from Paul the apostle, paul shine yayi naming dinsa Christianity for his selfish interest domin a da ai ba masoyin Jesus bane Paul, true or false? Jesus acted like we muslims do, he fall with his face to the ground, but never dance, clap, or beat drum as an act of worship, did he?" Ya tambaya yana kallonta, ya girgixa kai yana murmushi yace "He never, let me add a prove to this, Matthew 26:29 read thus 'Going a little further, he fell with his face to the ground and prayed......" Murmushi yayi yace "you see, ba ace he clapped his hands, beat drum or danced ba, even till date the Coptic Christians still pray the way Jesus PBUH did, the jews in the holy land still pray the same way also!" mikewa tayi ta bar masa wajen ta koma kan katifar dakin tayi kwanciyarta hade da lumshe ido, murmushi yyi ya mike ya fice waje.
Mami ce xaune parlor ta rafka uban tagumi, Hajiya Mariya ma na xaune gefen yayartata, sai Yakumbo dake tsaye kekam bakin nan uwa an taka teba a kan titi ta jefa ma Mami harara yayi sau ashirin a wajen, manyan 'ya yanta maza duk biyun na parlorn, sai Abba dake tsaye shima kamar dai the soldier he is, sojoji ne har biyu tsaye bakin kofa, ya juya ya kuma kallon Mami strictly yace "For the last time ki gaya min inda Aliyu yake...." buda baki tayi cike da bacin rai tace "Kai kana matsayin mahaifinsa baka san inda yake ba sae ni, ta ina xan san inda Aliyu ya tafi, haba a dinga adalci mana" a fusace yakumbo tace "Yo idan bai tambaye ki Aliyu ba uwar wa xae tambaya?? ba boyayyen abu bane kowa yasan bakin ku daya da d'an iskan, ni ko rantsuwa nayi baxan yi kaffara ba kinsan inda Aliyu yake...." Sae kuma ta fashe da kuka tace "Tur!! Mu dai duk xuri'ar mu daga farkonta har ixuwa yanxu bbu crista, ko tu6a66e, ban dai san a naku yanda abun yake ba...." Mariya tace "Mu ma haka, hasalima iyayen mu da kakannin mu duk malamai ne..." Yakumbo ta jefa mata wani matsiyacin kallo tace "keee kar ki min fitsara ban sako da ke ba daga tambaya?" Ko kallonta Mariya bata yi ba, Abba ya girgixa kai yana murmushin takaici yace "Hajarah duk abinda Aliyu ya xama kece sanadi, ke ce sila...". Mikewa Mami tayi tana murmushi tace "Sae yau ka sani kenan, ae tun da na nema masa karatu a Uk na biya, na kama masa gida mai tsada, na xuba masa abubuwan more rayuwa, naki sauraran shawarar kowa ni da 'yan uwana nace ae namiji ne shi ba mace ba, na rufe ido ban ji ban gani na hada masa kaya na kai sa Airport ya tafi can yayi rayuwarsa in a free way, bbu sa wa bbu hanawa shekaru d'aid'ai har takwas, What did you expect Col???" Daga haka ta nufi stairs Hajiya Mariya ta bi bayanta, kasa cewa komai Abba yayi ya bi ta da ido, yakumbo ta tafe hannu tana salati tace "Wato mu matar nan ke gaya ma magana koh?"

*Haske writers asso*📚✍🏻
💫 *Noorul Huda*💫

By Khaleesat Haiydar 📚✍🏻

31.....
Alhaji Umar ya saci kallon Abba da uwarsa bai dai ce komai ba haka d'an uwansa Alhaji Jibril, juyawa Abba yayi kamar xae tashi ya fice daga parlon, Alhaji jibril ya ce "Toh Allah ya kyauta, Allah ya kawo mafita yasa ya gane abinda yake shirin yi" Yakumbo ta fashe da wani kuka tace "Ae ni Allah ya isa tsakaninmu da Aliyu, wnn abun kunyar da me yayi kama da wani ido xa mu kalli 'yan adawan mu, me ya burgesa game da crista arniya, ni dai ina ganin jarabawa, Aliyu ya cucemu, yaro kamar shaidan, duk artabun da aka dinga yi jiya ace ba a kamasa ba har ya gudu ko ina ya tafi..." A bangaren mumy kuwa tun daga jiya har yau kuka ne ya xamto abincin ta da ruwanta, tayi kukan tayi xage xagen, tayi iface ifacen, banda bata hakuri bbu abinda yan uwa da abokan arxiki suke, har cewa tayi da ta sani tun daren shekaranjiya ta kashe samantha tasan ba ita a duniyar ne kawai da ace ta bi musulmi sun gudu, gidan nasu cike yake da members din Church dinsu, mata da maxa, pastors har daga kaduna da Abuja sae da suka xo, masu addu'a nayi, masu xirga xirga da Abban samantha xuwa gidansu Abuturrab nayi, da ace Dad din Abuturrab ba babban soldier bane da ya shiga uku don ba abu me kyau bane xae biyo bayan irin sintirin da suke fiye da su ashirin har da matasa, daga karshe tsawa yayi masu yace "Su je duk inda xa su su nemi Aliyu su kashe sa ya basu go ahead, kada wanda ya kara d'aga masa hankali tunda basa ganin kokarinsa, bbu yanda suka iya ga gida cike da sojoji, haka suka juya sumui sumui suka fita. Abuturrab na xaune tsakar gida suna labari hira da Abba bayan la'asar, Alto bata kuma cewa a ta da Samantha tayi sllh ba a tunaninta bata da tsarki ne, Binta na xaune tana sirfa gero sai dai duk motsin da idonta xae yi a kan Abuturrab yake sauka, yana lura da irin kallon da take masa, sae abun ya basa dariya ya dai ci gaba da hirarsa da Alto, Samantha ce ta fito ta nufi bandaki da sauri ta fara amai tun kan ta isa, mikewa Abuturrab yayi haka Alto da Hansae dake wanke wanke suka dings cewa subhanallahi, Abuturrab ya d'agota a rikice yace "Meya faru?" Ta fashe masa da kuka tana rike da cikinta tace "Ciwo yake min" Hansae ta kawo ruwa a buta tace "Ikon Allah to bara in jika ma sa6ara" Abuturrab ya karbi ruwan ya wanke mata fuskarta snn ta shiga da ita ciki. Kwanciya tayi ya xauna gefenta yace "It's ur period right?" Juyawa tayi bata ce komai ba, ya mike ya fita, Tsaye ya ga Hansai har ta jika maganin da tace, yayi murmushi yace "Ae baxa ta sha ba Baaba, bbu gun sayar da magani nan ne?" Alto yace "Kai da tafiya sosai, Binta ta raka ka gun da xaka samu babur ka hau, sae kayi kamar xaka shiga Gombe...." Abuturrab ya durkusa yace "ohh daga kauyen nan sae gombe?" Alto yace "A'a akwai kauyuka har uku a gaba..." Abuturrab ya mike yace "Toh shknn bari in je..." Tuni Binta ta dauraye hannunta tace "Mu tafi..." Ya kalleta yace "Ae na gane hanya yanxu, da kin yi xaman ki" Tace "Yo ae baka san inda xaka samu babur ba" Hansae tace "Gaskiya ne, bari ta rakaka gun sai ta juyo" toh kawai yace suka fita gidan, tun da suka fita Binta ke xuba bai kalleta ba bare ya tanka ta ba, tafiyarsa kawai yake, har suka isa inda babur uku suke sbda masu fita kauyen, duk machine din sun rube, Binta tace "Bako ne daga birni wae wajen kauyen nan xaku fitar da shi xae siya magani" Bata rufe baki ba ko wanne ya dinga cewa ya hau, na gabansa ya hau mutumin ya tada machine din, ya d'an kalleta yace "Sae na dawo" daga haka yace ma mai machine din su tafi. Sae kusan karfe shidda Abuturrab ya dawo rike da leda, Alto dake kade shanayensa a waje yace "Ka dawo?" Abuturrab yace "Ehh na dawo Baffa sannu da aiki" Alto yace "Ka dai samo maganin koh?" Kai Abuturrab ya gyada masa yace "Na samo" daga haka ya shiga, Binta kadae ce tsakar gida tana kwasan tuwo, ta washe baki tace "Har ka dawo Aliyu?" Kallonta yayi don sae da tasa Mami ta fado masa, ta fi kowa kiransa da Aliyu, yace "Na dawo! Bbu kowa dakin?" Tace "Ehh ita kadai ce" ya duka ya shiga Bukkar, xaune ya ganta ta hade kai da gwiwa, ya karasa a sanyaye ya ajiye ledan hannunsa ya d'agota yace "Samha!" Ta kallesa da idanuwanta da suka yi ja, cikin sanyin murya yace "Kuka kike?" Sauke idonta tayi ya kamo hannunta yace "Am making you suffer koh, i know you re not use to all this Samha.... But for the sake of my love endure it for just a while..." Ta fashe da kuka tace "Am not complaining" gefenta ya dawo ya xauna ya jawota jikinsa yace "Bance kina complain ba, but you re not use to this such of life..." Bata ce komai ba yace "Kin fara period din ne?" Ta girgixa masa kai, yace "But it's on it way koh?" Shiru tayi bata ce komai ba, ya dago kanta yace "Shareni ma kika yi" kwace kanta tayi tace "How did you know?" Yayi murmushi ya daura kansa a kafadanta yace "I know because i am a doctor...." Tayi masa wani kallo ta gefen ido tace "Ko dai sa ido, kawai don ka ga na yi amai?" Kamar xata yi kuka ta kare maganar, dariya yayi ya kai bakinsa kunnenta yace "Ni din, toh shknn in ma ya xo ya fara wahalar min da ke ko kallonku baxan yi ba, ya gama wujijjiga ki ya xuba abinsa ya wuce" murmushi tayi ta boye fuskarta a jikinsa, lkci daya Binta ta fado dakin, da sauri ya saketa ita ma ta ja baya, Binta na ganin haka ita ma da sauri ta fita, Ya kalli Samantha yaga ta wani hade rai, bai ce komai ba ya dau ledan da ya kawo ya bude, pad leda biyu sae inner wears da allurori da drugs, perfume, Toothpaste, brush soap da sponge sai gown har biyu da veil ya xube mata su gabanta, ta dauke kai bata ce komai ba, Ya bude daya ledan ya fiddo ledojin kaji biyu ya ajiye mata daya ya ajiye dayan a gefe, sae kuma Bread biyu da Blue band daya da ya siyo da kayan tea sae table water babba, mikewa yayi ya dau ledan kaza da daya bread din ya fita don kai ma su Binta. Bayan Isha Abuturrab na xaune tare da Baffa Binta ta fito tace "Aliyu ina jin fa ciwon cikin ne ya dawo sae juye juye take" Hansai dake cin tuwo tace "Subhanallahi, ka bata magungunan kuwa?" mikewa yayi ya shiga dakin Binta ta bi bayansa, ya durkusa gabanta yace "Sannu dear, but are you flowing?" Ta girgixa masa kai hawaye na sakko mata, dagota yayi ya bude ledan da magani ke ciki ya ballan mata biyu ya bata da ruwan goran ta sha, sae da yaga ta d'an nutsu snn ya mike ya fita, Hansai ce kadai a tsakar gida sai Binta da ta gaji da tsayuwa tun daxu dakin ta fito, Hansai tace "Ta samu bacci ne?" Yace "A'a ya mata sauki ne" Hansai tace "Toh Allah dai ya sauwake, dama ashe matar ka ce?" Kallon Binta yayi don yasan ta yi mata wata magana kenan, ya gyada kai kawai, tace "Allah sarki, ae ni nayi xaton kanwar ka ce, ashe mai daki ce, to shiga ciki sai ka tsaya tare da ita tunda ma bata da lafiya" yace "Toh" Hansai tace "Binta xata kawo maku bargo" juyawa yayi ya koma dakin, ba a dau lkci ba Binta tayi sallama bakin kofa ya fita ya karbi bargon ya dawo dakin, xaunawa yayi yana kallon samantha yaga har ta fara bacci, ya shimfida 'dan bargon a kasa ya rage lamp din dakin sosai ya kwanta. Can cikin dare ta kusa fadowa kansa bayan ta sauka daga kan katifa, ya mike xaune ya rikota yace "Me ya faru?" Rikesa tayi tace "Amai nake ji" ya rungumeta yace "Amma cikin ya daina?" Kai ta gyada masa, ya fara shafa mata bayanta a hankali murya can kasa yace "Aman xai koma kin ji?" Bata ce komai ba sae rufe idonta da tayi, haka ya dinga yi mata har taji aman ya koma, ta xame jikinta ta koma kan gado ta kwanta, ya jima xaune ganin kamar tayi bacci ya koma ya kwanta. Washegari da asuba tun da ya idar da sllhn asuba a dakin yayi ta tunanin inda xa su gashi bai da enough cash a hannunsa, kudin account din Hajiya Mariya ma bbu yawa, mikewa Samantha tayi xaune ya juya yana kallonta, ganin yanda ta bata fuska ya dawo kusa da ita yace "What?" Kamar xata yi kuka ta nuna masa cikinta, yace "Ya fara ne?" Ta gyada masa kai ta mike ta nufi inda ya ajiye kayan jiya ta dau pad da brush da toothpaste yana kallonta yace "In raka ki?" Wani kallo tayi masa yayi murmushi yana shafa kai yace "Ohk sorry" ko da ta dawo tilasta ta yayi ta ci bread da butter sbda alluran da xae mata, da kyar tana juye juye ta ci kadan ta sha ruwa yayi mata alluran ta kwanta, sae da gari ya fara wayewa snn ta samu bacci ya dauketa ya mike ya fita, Binta dake shara ta gaishesa da fillanci ya amsa yana tambayar ta tashi lfya, tayi murmushi ta tafi ta dauko wani flask da cooler ta dawo ta mika masa tace "Gashi karin kumallon ku" karba yayi yace "Mun gode" ya koma daki ya ajiye, tayi sallama bakin Hut din tace "Ga kofi" fitowa yayi ya karbi cup din ya koma ya ajiye, Muryan Alto ya ji da fillanci yana cewa "Ali na tafi kiwo sae na dawo" Abuturrab ya fito ya gaida sa, Alto yace "Ya mai jikin?" Abuturrab yace "Taji sauki Baffa, kilan baxa ka dawo ka same mu ba anjima xa mu dau hanya" Baffa yace "Allah mai girma, shi yasa ba a sabo da bako, baxa ku jira hat in dawo da rana ba" Abuturrab yayi murmushi yace "So nake mu isa gida da wuri ne" Baffa yace "Toh Allah ya tsare, ni bani da komai da xan baku, amma Binta xata tatsar maku nonon shanu ku tafi da shi bamu da komai baya ga wannan" Abuturrab yace "Ayya ba komai Baffa mun gode da karramawar ma" Alto yace "Toh Allah ya tsare, ku gaida mutan gida Allah ya tsare gaba" Abuturrab ya fiddo dubu goma cikin kudin jikinsa ya mika masa yace "Ga wannan ba yawa Baffa, in shaa Allah wataran xamu kawo maku ziyara" Alto ya bude ido yace "A yi haka?" Abuturrab yace "Kai dai ka karba Baffa" Alto ya karba da hannu biyu ya dinga sa masa albarka yana masu Allah ya tsare hanya har ya fita, Wanka Abuturrab ya shiga kewayen gidan yayi ya fito ya shiga Bukka, har lkcn bacci samantha take, ya shirya cikin kayansa da ya wanke jiya ya fita da na Baffa yana kallon Binta dake xaune tsakar gidan ita kadai yace "Baaba fa?" Bata kallesa ba tace "Ta je kauyen dake gaba da namu siyo gyero" yace "Ki ban sabulu xan wanke kayan nan" ta mike ta isa gabansa ta karba kayan tace "Xan wanke" yace "Noo, kar ki damu xan wanke" bata saurare sa ba ta nufi gun randar ruwansu ta diba, ya daga kafada ya juya ya koma daki ya bude flask din da ta basa ya ga kunu ne ya bude coolern ya ga kosai, diban kunun yayi ya dau kosan ya fita ya shimfida tabarma ya xauna ya shiga ci a nan, lkci lkci yake kallonta har ta gama wankin ta shanya kayan a igiyar dake tsakar gidan, ya koma inda take ta xauna,

Please Login or Register in order to submit comment