Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wata hanyar daban ya dauka har suka iso main road ya tsayar da adai daita suka hau, mai adai daitan ya tambayesa inda xa su yace "Mu je gaba kawai" samantha ta kallesa tace "Ina xa mu je" kasa ce mata komai yayi ganin yanda idonta ya fada, ya kamo hannunta a hankali yace "Am sorry for everything samha" bata ce komai ba, ya kalli mai adai daitan yace "Jan bulo xaka kai mu." Suna isa mai adai daitan yayi parking dai dai inda Abuturrab yace yayi, yana sauka ita ma ta fito, ya mika masa dubu dayan hannunsa ya basa canji ya kalleta yace "Mu je" bin bayansa tayi ya kwankwasa gate mai gadi ya bude, suna gaisawa ya shiga gidan ita ma haka, sai a snn a hankali tace "Doctor ina ne nan?" Ya kalleta yace "Gidansu frnd dina ne nan, bbu wayar da xan kirasa shi yasa mu ka xo" Farida kanwar Mujaheed na xaune karkashin umbrella tree da alamar assignment take, tana ganinsu ta mike tace "Lahh ya Aliyu daga ina?" Yace "Mujaheed na nan?" Tace "Ehh yana nan" yace "Kice ina jiransa" tace "Toh" snn ta kalli Samantha tace "Sannu da xuwa" Samantha ta sakar mata murmushi tace "Nagode" daga haka yarinyar ta wuce ciki, ya kalli samantha yace "Mu je ki xauna" bin bayansa tayi suka xauna karkashin bishiyar, ba a dau lkci ba Mujaheed ya fito, ya xaro ido yana kallon Abuturrab yace "Daga ina haka?" Abuturrab bai tanka sa ba har ya karaso ya ja kujera ya xauna yana kallon Samantha murmushi dauke fuskarsa yace "Sannu yan mata!" Samantha ta sunkuyar da kai tace "Ina yini" ya amsa da fara'arsa, Abuturrab yace "Kira farida su shiga ciki, xa mu d'an fita da kai ne yanxu" Mujaheed yace "Ohk" ya ciro waya ya kira kanwarsa ta fito, Abuturrab ya kalli Samantha yace "Samha ku shiga ciki am coming back soon" kallonsa kawae take lkci daya idonta ya kada, mikewa yayi da sauri yace "yanxu fa xan dawo Samha" dago ta yayi suka bar gun daga Mujaheed har kanwarsa suka bi su da kallo, jikin flowers ya tsaya ya daga kanta yana kallon kwayar idonta yace "Ko baki son nan din ne?" Ta girgixa kai bata ce komai ba, a hankali ya kai lips dinsa forehead dinta murya can kasa yace "am coming back soon dear" Daga haka ya kama hannunta suka dawo inda suke ya hada ta da farida suka shiga cikin gidan, A motar Mujaheed suka bar gidan, sun dan yi nisa Mujaheed yace "Kai malam wai ina xa mu" Abuturrab yace "Yi parking muyi magana" Mujaheed yayi yanda yace snn yace "Wnn ba yarinyar nan da ka taba kawowa clinic bace? Dama budurwarka ce?" Abuturrab yace "Ni dai ka saurareni ina son pls ka min wani favour" Mujaheed yace "Na me?" Abuturrab yace "Laifi na yi ma Abba, pls so nake kayi pretending baka san komai ba kaje can gidanmu da sunan kaje daukan ajiyar ka, sai ka duba briefcase a bedroom dina ka dauko min gaba daya Credentials dina, snn akwai atm cards dina har biyu a gaban mirror ka dauko min plss frnd" tun da ya fara magana Mujaheed ya bude baki yana kallonsa, can ya fashe da dariya yace "Me kayi kuma again?" Abuturrab ya tabe baki yace "Oho dai, kawai ni dai nasan tun safe ake cin xalina.... Kaje yanxu plss" mujaheed yace "Abban na gida ne?" Abuturrab yace "May be" Mujaheed ya girgixa kai yace "In dai yana nan baxan iya ba wllh" Abuturrab yace "Oh haka xaka min?" Mujaheed yace "No gaskiya kenan fa, to ita kuma yarinyar nan da kake yawo da fa?" Abuturrab ya shafa kansa yace "Kaga it's a long story yanxu kayi abinda nace idan ka dawo sai in baka labarin," Mujaheed yyi shiru snn yace "Ka fa san halin Dad dinka, xae iya gano hada baki muka yi, why not ka bari da daddare...." Abuturrab yayi tsaki yace "Kai dai kaje ynxu kawai, you have to pretend, sai kace kana ta kiran lines dina basa xuwa, but bani wayar ka daya in case of anything sai ka kira ni" Mujaheed yace "No gaskiya ka bari da daddare?" Abuturrab yyi shiru sai kuma yace "Toh shknn" Mujaheed yace "Da motata xan je?" Abuturrab yace "A'a kawai ka dau tricycle kaga bbu wanda xae xargi komai, kana xuwa kuma ni xaka fara tambaya" Mujaheed yace "Ohk" gidan wani abokinsu suka tafi, suka tsaya har bayan magrib, Abuturrab dai gaba daya hankalinsa na kan Samantha duk da sun yi waya ya fi sau goma ta wayar farida, Bakwai da kusan rabi Abuturrab yace "Toh kaga kar dare yayi kuma Mujaheed ka tashi ka je" Mujaheed yace "Ni dai anya xan je kuwa..." Abuturrab ya marairaice masa, da kyar ya kuma lallaba sa har ya amince daga karshe yace "Toh ina xan sameka?" Abuturrab yace "Ina nan xan jira ka har ka dawo" daga haka Mujaheed ya fita ya dau adai daita ya wuce, Mujaheed na isa yaji gate a kulle wato sai ya xaga ta daya gate din bbu yanda ya iya haka ya xaga, yana shiga ya gaida sojojin dake wajen, sae da gabansa ya fadi ganin Abba a compound suna magana da wani sanye da khaki da alamar abokinsa ne, don compound din akwae haske sosai, yana ganinsu yayi kasa da kai har ya isa gabansu ya risina ya gaidasu, duk suka amsa, Abba yace "Daga ina haka?" Mujaheed yace "Daga gida nake Abba, gun Abuturrab na xo..." Abba yace "Ohk!" Abokin Abba yace "Abuturrab din bai nan ai" Mujaheed yace "Ohk kuma ina ta kiran wayarsa tun rana baya shiga, dama akwai ajiyar da na basa xan karba ne bari in duba ko kofar a bude yake" Abba yace "Ohk" Mujaheed ya sauke ajiyar xuciya ya nufi part din Abuturrab, a bude ya tadda gun ya shiga ya dauko duk abinda Abuturrab yace masa snn ya fito, yayi mamakin ganin sojoji biyu tsaye kusa da balcony sai dai bai ce masu komai ba ya wuce su, yana isa tsakiyar compound ya samu su Abba yanda ya bar su a tsaye ya karasa yace "Abba na dauka xan wuce" Abba na gyada kai yace "Ohk...." Ko rufe baki Abba bai yi ba, Mujaheed ya ji an cafkesa ta baya ya juya da sauri ya ga wani soja ne, sojan ya karbe envelope din hannunsa ya ajiye sa kasa sannan ya fara cajin aljuhun wandonsa ya ciro atm cards din ciki da wayarsa ya jefar kan envelope din, Abokin Abba ya durkusa ya dau Envelope din ya bude ya fiddo abubuwan ciki, banda xare ido babu abinda Mujaheed yake, Abba ya karbi takardun ya kalla snn ya maida dubansa kan Mujaheed, Gyada kai yayi yana wani murmushi ya jefar da takardun kan Envelope din yace "That's a brave play, yeah kun yi kokari daga kai har shi" dukawa yayi ya dau wayar Mujaheed yace "Akwai waya hannunsa ko babu? Kuma kana min karya in sa a kai min kai barrack yanxun nan" Mujaheed da banda xufa bbu abinda ke karyo masa cikin dakiya yace "Ehh Abba akwae daya wayata a gun sa" Abokin Abba na gyada kai yace "Good, kirasa kasa a hands free kace ku hadu a filin polo yanxun nn ya karbi sakon" Da kyar Mujaheed yace "Toh" nn ya shiga kiran daya wayarsa dake gun Abuturrab, Abuturrab da ya fita yana jiransa a mota ya daga kiran da sauri yace "Yane Mujaheed ka dauko?" Mujaheed ya kalli Abba, Abba ya watsa masa wani firgitattcen kallo, da sauri yace "Ehh ehh wllh na dauko! Emm kana ji na mu hadu a filin polo yanxun nn ka karba" Abuturrab yyi shiru, murya can kasa yace "F**k you, ka bari an gano mu knn!" daga haka ya katse wayar ya jefar.

*Haske writers asso*📚✍🏻
💫 *Noorul Huda*💫

28.....

Tada motar yyi da sauri tunawa da Samantha da yayi, yasan in dai mujaheed yaga haza to fa xae iya cewa tana gidansu ma, cikin kankanin lokaci ya isa gidansu Mujaheed gabansa na faduwa, kusan a tare suka shiga compound din da kanwar Mujaheed Aysha ta dawo daga makaranta, ya amsa gaisuwarta yace "Kice ma bakuwar da ke ciki ina jiran ta pls hurry" tare samantha suka fito da Farida ta raka su har gun mota ya sosa kai yace "Kice Umma tayi hakuri ina nan xuwa gaida ta, kunya nake ji shi sa ban shigo ba" dariya kawae Farida tayi tace "Ya Jaheed fa?" Abuturrab yace "Ehh yana nan dawowa..." Daga haka ya sa samantha ta shiga mota shi ma ya shiga da sauri, farida ta d'aga masu hannu ya ja motar ya bar layin, yana fita layin motar sojoji na shiga, xaro ido yyi don bai san ko sun gansa ba ya kara gudun tukinsa, sae da suka dan yi nisa ya kalli samantha yaga idonta na waje, wani tausayinta yaji sosai ya kamo hannunta a hankali yace "Samha!" Kallonsa tayi bata ce komai ba, yace "Kin ci abinci?" Kai kawae ta gyada masa, cikin sanyayyen murya yace "Ki kwantar da hankalin ki kar ki sa ma kanki damuwa plss am with you now and forever..." Hawaye ya ga idonta, yayi parking da damuwa yace "Baki yarda da ni ba kenan Samha..." Ta fashe da kuka tace "My parent...." Ya rike hannayenta duk biyun yace "Ni ma na bijire masu duk sbda ke, kinsan irin neman da ake min yanxu? A guardroom Abba na yasa aka kulle ni da safen nan amma sae da nasan yanda na fito, na tura Mujaheed can gidan ya dauko mun Atm cards dina shima yana can nasan an kullesa yanxu kuma nasan xae iya cewa kina gidansu shi yasa na dauke ki, am at risk Samha but i don't care in har ina tare da ke, i love you... I can do anything for your love" hannu yasa ya share hawayen da ke idonta yace "Kar ki damu Allah yana tare da mu!" Sunkuyar da kai tayi bata ce komai ba, ya ci gaba da tukin, a wani atm ya tsaya yace yana xuwa snn ya fita, sae da ya fara duba nawa ne a account din Small Mum din tasa snn yayi withdraw din dubu hamsin, kamar ance ya waiga yaga motar sojoji na kokarin shan cornern gun bank din, da sauri ya koma ya labe jikin Atm din, ta gefen ido yake kallon motan gabansa yayi mugun faduwa ganin abokin Abbansa da ya fito daga gaban motar, sojoji hudu ma suka sauka daga baya, kamar kiftawan ido ya taho a 160 ya shige cikin mota yayi wani reverse bae damu da harbin da suka fara ba, ko kallon titi bai yi ba ko mota na xuwa ya hau titin ya ja motar a guje, Samantha da duk ta gama rikicewa ta dinga kwala ihu a cikin motor, ta madubi ya ga sojojin sun biyo sa a tasu motar da gudu, ya yo waje da ido yace "Kan bala'i" sae ka rantse tashi sama xae yi tsabar yanda yake gudu don ma titin bbu wasu motoci, samantha dake ta rusa kuka sae cewa take don Allah doctor ka tsaya, don Allah ka tsaya, Bai ko kalleta ba bare ya san me take cewa, hankalinsa ya gama tashi ganin sun kusa tadda su a lokacin kuma suna wajajen court road, bai damu da traffic da ya nuna masa green ba ya wani sha kwana da gudu har ya kusa karo da wata mota ya kauce mata ya ci gaba da gudunsa, traffic din nan ne ya taimaka suka samu distance tsakaninsa da soldiers din, sosai ya ga karfin halin samantha don yasan da wata ce da tuni ta suma, har ya hau titin unguwa Uku bai sassauta gudun da yake ba, a can baya sosai yake hango motar soldiers din, bai son ya shiga wani layi su tadda traffic shi yasa ya gwammace yayi ta gudu a express, hankalinsa ya tashi ganin man motan yayi kasa sosai, yana fara fita outskirt din kano yaga da nisa fa sosai tsakaninsu ya ja ya tsaya ya cire makullin motar ya fito da sauri, har lkcn kudin da yayi withdraw da atm card na aljihunsa, ya xaga ya bude inda take ya fito da ita, wani hanya kamar gona ya ja ta suka bi da gudu, daji ya dinga gani sosai a gaba amma hakan bae sa ya dakata ba, ita ko sai kuka take tana cewa "Baxan iya ba Doctor ka tsaya plss" a haka ya ja ta suka shiga dajin, bai damu da thorns din ciki da dogayen ciyayi ba ga uban duhu suka dinga ratsawa a haka, tafiya sosai suka yi a ciki ya ga kamar numfashinta na neman daukewa tsabar gajiya don jan ta kawae yake, rikota yayi da sauri ya nemi karkashin wani bishiya ya xaunar da ita yana kallonta bnda kyallin idonta bbu wani haske da yake gani a dajin, ta rike duk hannunsa biyu da kyar tace "Ruwa xan sha doctor!" Maida numfashi ya dinga yi yana kallonta, can ya runtse ido ya dinga maimaita innalillahi wa inna ilaihi raji'un a xuciyarsa, bude idon yyi ya dafe kansa, ta xame hannunta daga nasa ta fashe da kuka, mikewa yayi yana dube duben inda xai samo mata ruwa yaji ya yi kick din abu, da sauri ya duk'a yana laluba meye wnn yaga kettle ne, da ruwa amma ba da yawa ba a ciki, dagawa yayi duk da bai san ruwan meye ba ya kai baki ya sha yaji dai ruwa ne sai dai da jin sa a baki kasan ba wani mai kyau bane, ya hadiya da kyar snn ya kai mata baki, karba tayi ta sha gaba daya, ya ajiye butan, ta rike hannunsa gam cikin rawan Murya tace "Am afraid doctor, tsoro nake ji" xaunawa yyi gefenta ya jawota jikinsa murya can kasa yace "Don't be, am here to protect you, am with you" shiru tayi tayi lamo a jikinsa wanda hakan yasa ya dinga jin bugun xuciyarta, sun kusan minti talatin a haka taji ya kankameta, ta d'ago da sauri, taga idonsa a runtse, a hankali ya bude yana kallon kasa murya can kasa taji yace "Ant, i think it's an ant" kalle kallen kasan ita ma take, xaro ido tayi tayi wani uban ihu da sai da ko ina ya amsa, sai a snn ya ga me ta gani, wato kunama shi ba babba ba shi ba karami ba, ya toshe bakinta ya sa kafa yayi smashing dinsa, ko ina na jikinta rawa yake ta dinga cewa it's a scorpion, ya kai bakinsa kunnenta yace "Shhhh na fa kashe shi..." Jin baxata yi shiru ba ya lumshe ido ya rungumeta gam, tayi lamo jikinsa, a hankali ya xame dankwalin kanta ya daura a gun da kunaman ya harbesa, ba a dau lkci ba bacci ya dauketa.

*Haske writers assoasso*📚✍🏻
💫 *Noorul Huda*💫

29.....

Daren ranan Abuturrab bai rintsa ba, har asuba yana rungume da ita, gari na fara haske ya kare ma dajin kallo, sai yaga ashe gona ce gun gaba daya, bishiyoyin mangoes da lemo ne yasa gun ya xama kamar daji da daddare, ya kalli wani tabarma dake can nesa da su a shimfide da wani sanda, da alamar dae mutane na xuwa gun, butoci har biyu ya gani bayan wanda ya samu ruwa a ciki jiya, kwance dankwalinta dake daure kafarsa yayi ya shimfida nan kasa snn ya kwantar da ita a hankali ya mike, wani mugun ciwon kai ya dinga ji ya taka a hankali har ya isa inda butan yake ya ga cike yake da ruwa ya dauka ya xaga ya daura alwala snn ya dawo, ya kalli gabas ya tada sllh, bai idar ba samantha ta farka, mikewa xaune tayi da sauri tana kare ma gun kallo, a hankali ta mike ta karasa gun butan da ya ajiye ta dauka, kallonta kawae yake bayan ya idar, ta juyo ya sakar mata murmushi cikin sanyin murya tace "I want to ease my self" yace "In raka ki?" Da sauri ta girgixa masa kai yana murmushi yace "Ohk" ya nuna mata inda xata tafi, ta juya ta wuce, ko da ta dawo bata gansa ba, ta fara kalle kalle da manyan idonta, muryarta na rawa tace "Doctorrr" tim taji fadowar mango a sama, ta koma baya a tsorace tana kallon sama ta gansa samar bishiyar yana tsinkar nunannun mangoes, ya kashe mata ido yace "Breakfast...." Daga haka ya ci gaba da tsinkar mangoes din masu kyau har ya tsinko fiye da ashirin, ji tayi ya diro kasa, ya karasa ya dauko dankwalinta ya dawo ya durkusa ya kwashesu, ta karasa inda yake ta durkusa gabansa a hankali ta shiga taya sa kwashewa, ya sakar mata murmushi yace "Bari toh in kara plucking din pawpaw ae kina so" bata ce komai ba ya mike ya isa inda sanda ke ajiye ya tafi gun bishiyoyin gwandan, can ya koma baya ita dae kallonsa kawae take, taku daya biyu yayi ya buga uban tsalle ya doki ripe pawpaw guda daya da sandar hannunsa ya fado, murmushi tayi ta dauke kanta ya dawo rike da pawpaw din yana murmushi ya ajiye mata, xaunawa yayi yace "Tunda bbu ruwa haka xa mu sha mangoes din..." Daga haka ya dau mango daya ya kai baki, dauka ita ma tayi ta kai baki a hankali, biyu kawae ta sha tace ta koshi, yace "Efizzy xa ki min" murmushi tayi ta girgixa kai kawai, duk yanda yayi da ita tasha kin sha tayi wai ta koshi, pawpaw din ma shi kadae ya sha kayansa wai bata sha, yana gamawa yace "We will leave yanxu...." Mikewa yayi ya dau sauran mangoes din da sanda yana rike da hannunta suka fara tafiya can gaba, da sandar ya dinga clearing masu daji don duk a tsorace take duk da kana ganin hanyar ma kasan ana bi sae dai ba sosai ba, tafiya kawae suke har kusan karfe tara ganin ta gaji sosai ya langwabar da kai yace "Ko in goya ki baby" kamar xata yi kuka tace "Doctor wae ina xa mu...." Yace "In da Allah ya kai mu" bata kuma cewa komai ba suna ta tafiya ga uban rana me xafin gaske har sha daya tayi, ta durkusa tana haki tace "Wayyo doctor i can't go futher am very thirsty" durkusawa shi ma yayi cike da tausayinta, ta fada kansa hawaye cike idonta tace "Na gaji, yunwa nake ji" ya rungume ta yace "Kiyi hakuri plss, so nake mu fita dajin nan ne so i will find you something to eat..." murya suka ji bayansu, ta kankamesa a tsorace ya juya yaga wani tsohon bafullatani sanye da katon hat wanda hakan yasa ba sosai yake yake hango fuskarsa ba, hannunsa rike da sanda cikin hausan sa da bai fitowa irin ta fulani yace ma Abuturrab "yarinya me ya kawo ku nan" Abuturrab da yaji sanyi sosai a ransa yace "Mun yi 6atan hanya ne Baffa!" Bafulatanin yace "Subhanallahi.... Ina ne xa ku?" Abuturrab ya sake samantha ya mike yana kallon dattijon cikin harshen fillanci yace "Daga kano muke xa mu kaduna barayi suka biyo mu tun jiya da daddare shine muka yo dajin nan" tsohon ya washe hakoronsa da goro yayi masa destroying da fillanci yace "Dama ina ganin ka nasan kai namu ne, ashe d'an uwana ne, barka da arxiki da barayin basu cutar da ku ba" Abuturrab murmushi kawae yake yana gyada kai, dattijon ya kalli Samantha da yaren yace "Sannu yarinya ta barka da arxiki" Kanta a kasa tace masa sun gode da harshen fillanci ita ma wanda hakan yayi mugun daure ma Abuturrab kai ya tsaya kallonta kamar idanuwansa xasu fito, dattijon yace "Rigar mu na nan kusa ku taso mu je ku huta, tafiyar minti talatin ne xae kai mu can, na fito kiwo ne dama na hango ku nayi xaton barayin daji ne, ga can inda na boye shanaye na" dariya Abuturrab yayi tsohon ma yayi dariya yace "Toh muje..." Abuturrab ya kalli samantha ya kama hannunta suka bi bayansa, ya matsa hannunta a hankali yace "Dama kina jin fulfulde shine ko sau daya baki taba gaya min ba" ta d'an yi murmushi bata ce komai ba, haka suka dinga bin dattijon da shanayensa kusan ashirin, su sha wancan kwanan su fito ta wani su kuma shan wata kai hanyar dai gashi nan gashi nan, Abuturrab yasan ko kashe sa xa ayi kila baxae iya gane hanyar ba. Suna isa Rigar dattijon ya juya yana kallonsu da fulfulde yace "Ga 'yar rigar mu nan, da fatan xaku ji dadin xama a ciki na yau dai" murmushi kawai Abuturrab yayi, tafiyar minti goma suka yi suka iso wani gida dake xagaye da kara, Dattijon ya shiga hade da sallama suka bi bayansa, bukkoki hudu ne a xagaye a d'an karamin tsakar gidan, wata mata dake daka tsakar gidan tayi masa sannu da xuwa da yare tana kallonsu Abuturrab, ya amsa yace "Kin ganni da baki 'yan uwanmu koh?" Mikewa tayi ta dauko tabarma ta shimfida tana masu lale, Yace "debo masu nono kafin ki xauna Hansai" wani bukka ta shiga sae ga ta ta fito da kwarya cike da nono ta ajiye masu, Dattijon da ake kira da Alto yace "Ina yarinyar nan ta shiga?" Hansai tace "Taje kai fura gidan tuwaru nasan duk inda take ta kusa gida yanxu" Malam Alto yace "Toh akwae ruwa gidan koh? Allah ne yayi masu katanga da barayi suka afko daji shine fa muka hadu da su...." Girgixa kai Hansai ta dinga yi tana cewa "Allah yayi mana tsari" Wata yarinya da baxa wuce Samantha ba ta shigo gidan kanta dauke da icce, ta karaso ta durkusa ta sauke tace "Inna bak'i muka yi" Malam Alto yace "Ehh wllh gasu nan daga birni suke" ta kalli Samantha tace "Sannu da xuwa..." Hansai tace "Tashi ki shiga da ita ciki ki bata zani ta daura tayi wanka" Mikewa tayi samantha ta tashi ita ma suka shiga wani bukka, bbu komai ciki sae yar katifa da xani a kai, sae jakar gari yayi xafi guda biyu, cement din dakin duk ya farfashe, Samantha ta xauna kasa yarinyar da hausarta na fulani tace "Ki xauna kan katifa" samantha tayi yanda tace, yarinyar ta bude jaka ta fito da wani xanin kayan fulani a linke ta ajiye mata tace "Gashi ki daura" Samantha ta kalleta a hankali tace "ina son in huta ne" yarinyar tace "Toh ki huta" daga haka ta fita, Hansai tace "Kin bata xanin Binta?" Binta tace "Eh ta kwanta wai tana son ta huta" Hansai tace "Toh shknn, maxa ki xo ki hura wuta in daura sanwa tunda mun yi bak'i" Wani sabulu babba me kamshi Alto ya dauko a dakinsa ya mika ma Abuturrab yace "Aminina Hammadu ne da yaje birni ya kawo mun sabulun nn har uku... Gashi ka shiga wanka da shi xaka fi jin dadinsa" Abuturrab ya mike yana murmushi ya karba yace "Toh nagode Baffa" daga haka ya nufi 'yar kewayan dake tsakar gidan don Baffa ya kai masa ruwa Binta ta bi sa da kallo, ko da ya fito Baffa ya kai sa Bukkarsa ya dauko masa wani tsaftatattcen rigarsa irin ta fulani ya basa, Abuturrab ya karba hade da godiya Alto ya juya ya fita, yana gama shiryawa ya fada d'an gadon dake bukkar lkci daya bacci ya daukesa. Burabisko da miyar taushe da k'ashi Hansae tayi ta ajiye masu cikin langar tuwo da miya, Baffa dake xaune da yar radio a hannunsa yace "Bayin Allah da alama sun wahala, a dajin ma suka kwana" ana kiran Azahar Baffa ya tada Abuturrab yayi sllh, Hansae tace "Tafi ki tada ta ita ma tayi wanka tayi sllh" binta ta shiga ta tada Samantha tace "Ki tashi kiyi wanka sai kiyi sllh, Azahar yayi" Samantha ta mike xaune tana mitsika ido, can ta mike ta cire kayan jikinta ta daura xanin, ta kalli binta tace "ki ban mayafi don Allah" Binta ta nemo mata wani dankwali ta bata tace "Mu je in raka ki kewayen na kai maki ruwa"

Please Login or Register in order to submit comment