Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta sha ta mika masa, yace "No, daure ki shanye don Allah" girgixa kai tayi cikin sarkewar murya tace "Na koshi" karba yayi ya ajiye, ya mike ya nufi gaban mirror ya dauko paracetamol biyu ya dau ruwan goran da ya rage ya dawo ya mika mata, ba musu ta karba ta bude ruwan ta sha maganin ya karbi ruwan ta koma ta kwanta ta lumshe, lullubeta yayi da duvet don Ac'n dakin a kunne yake, ya kusa awa daya xaune kafin ya mike ganin sha biyu ya wuce ya dau pray mata da blanket ya fita parlor. Washegari yana dawowa daga masallaci ya hadu da Mami dake kkrin shiga parlonsa, sosai gabansa ya fadi, ta tsaya ganinsa tace "Sai yanxu ka dawo daga masallacin?" Ya risina yace "Ina kwana Mami" tace "Lafiya lau, su wa ke buga gate jiya Aliyu?" Rasa abinda xai ce mata yayi, duk hankalinsa ya tashi har ta so gano hakan, ganin irin kallon da take masa ya dake yayi ta maza yace "Kiyi hakuri Mami, a nan anguwar suke, emergency ne daya daga yaran gidan basu da lafiya!" Tabe baki tayi cikin nuna rashin gamsuwa tace "Ae tun ba yau ba dama ka iya karya" shiru yayi bai ce komai ba tace "Naga alamar your staying here is doing you more harm than before, bari dae Abban ka ya dawo...." Daga haka ta juya ta bar wajen, ya bi ta da kallo a sanyaye, cikin rashin kuzari ya shiga parlor, ya karasa bedroom ya ganta durkushe jikin gado ta hade fuskarta da gadon, karasawa yayi kusa da gadon da sauri yace "me ya faru samha?" D'ago kai tayi tana kallonsa da idonta da suka tashi da gani kasan ta ci kuka kenan da daddare, ya durkusa kusa da ita da damuwa yace "Samha!" Sauke idonta tayi kasa tace "Addu'a nake" sae a snn hankalinsa ya d'an kwanta yace "Ohk, tashi kije kiyi wanka, but you have to hurry up before daybreak, xamu fita kafin su mum dinki su dawo...." Tana jin haka kuwa ta mike ta nufi bathroom, duk tausayinta ya cikasa, yanxu duk shi fa ya ja mata everything she's going through, kuma ko k'adan bata nuna tana jin haushinsa ba, cikin kankanin lkci tayi wanka ta wanke baki da mouth wash ta fito, taga bbu shi a dakin, ta rakube gefe daya don tasan gaskiyarsa su Mumy na iya xuwa yanxu, shi kam main house ya nufa yaji alamar Mami na kitchen da mai aiki, ya haura sama da sauri ya shige dakinsu Ilham duk sun koma bacci, a hankali ya bude press dinsu yana kare ma kayayyakinsu kallo, ganin kamar samantha ta fi son Abaya ya dau wani well ironed Abaya baki da veil dinsa ya rufe gun, rasa yanda xai fita da kayan yayi kar yaje ya ci karo da Mami, bathroom ya shiga ya dauko towel dinsu ya nannade kayan a ciki ya bude window a hankali ya jefar da kayan kasa, yana juyowa yayi ido hudu da Ramla da k'aran bude window yasa ta farkawa tunda basu dade da komawa ba bayan sun yi sllh, mikewa xaune tayi tana kallonsa ya hade rai yace "Ku baku da aiki sai na bacci ne a gidan nan? Oya duk ku tashi ku fita daga dakin nn, breakfast din ma sae Mami taje tana muku?" Yanda ya buda murya yasa duk sauran suka farka, yasan Ramla na iya leka window idan ya fita don haka sai da ya tabbatar duk sun fita suna turo baki snn shi ma ya fita, da sauri ya xaga ya dau kayan ya koma part dinsa, har lkcn tana xaune ya sameta, ya sakar mata murmushi ya ajiye mata kayan ya nuna mata gaban mirror yace "Ga lotion, body spray, perfumes, ki shirya kafin in fito" daga haka ya shiga bathroom don yin wankan shi ma, ko kafin ya fito har ta gama shiryawa tana xaune tayi jigum, mikewa tayi ganinsa da towel ta fice daga dakin, bai wani dau lkci ba ya fito sanye da kananun kaya hannunsa rike da makullin mota yana kallonta yace "Tashi mu je, idan mun fita sai kiyi breakfast" bata ce komai ba ta bi bayansa, ya nufi gun da motarsa ya ke ya bude mata snn ya xaga ya bude ya shiga driver seat, ya fara warming din motar, kamar wanda ya tuno abu yace mata yana xuwa ya koma cikin gidan, kayan ta na jiya ya dauka har da dankwalin ya saka a leda snn ya fito, ya bude bayan mota ya ajiye ya rufe motar, gate ya bude ya dawo ya fitar da motar, ya kuma fitowa ya kulle gate din snn ya shiga motar ya ja suka bar layin, sai da suka hau kan main road snn ya kamo hannunta yace "Samha!" Bata iya ta amsa ba hakan yasa ya kuma kiranta, ta juyo ta kallesa, yace "Gaya min me ya faru jiya" ganin ta ki cewa yasa bae takurata ba, har sai da suka yi nisa sannan yaji cikin sanyin murya tace "I told Mumy everything" kallonta yayi da sauri yace "Me kika ce mata" tsaf ta gaya masa yanda aka yi jiya bata boye masa komai ba, duk jikinsa yayi sanyi ba kadan ba ya kasa ce mata komai, kuka take a raunane wanda yake jin hakan har cikin xuciyarsa, kasa daurewa yayi, yayi parking ya kamo hannunta biyu cikin sanyin murya yace "forgive me samha, ni na janyo komai, kuma duk hakan ya faru ne ta dalilin son da nake maki, no matter what kar ki guje ni Samha, ban taba yi ma wata diya mace irin son da nake maki ba, baya ga mahaifiyata bbu wata a xuciya ta sai ke, ina son ki son da baxan iya kwatanta maki ba, ki yarda da ni, na maki alkawarin har abada baxan barki ba komin wuya da tsanani.... Kuma kin san alkawari kaya ne, i am not using a sugar quintet mouth on you, i mean all what am saying, it's coming from the bottom of my heart" hawaye kawae take, wanda hakan yasa yaji kamar shi ma yayi kukan, ya hade hannayensu yace "But kema ki min alkawarin baxa ki bar ni ba" bata iya ta bude baki ba banda kai da take gyada masa kawai, sun kusa minti goma a haka kafin yayi karfin halin ci gaba da driving din. Karfe bakwai da kusan rabi mota guda na 'yan sanda suka yi parking kofar gidansu Abuturrab, kusan 'yan sanda shidda suka diro, bude kofar wata bakar mota da yayi ma motar 'yan sandar jagora aka yi, Mumy da su Anty Sarah suka fito da wasu maza har uku, da ganin idanuwan Mumy kasan ba tayi bacci ba daren jiya, bubbuga gate yan sandan suka dinga yi da karfi, kwata kwata Mumy bata san main gate din na ta daya bangaren ba, irin bugun da yan sandan ke yi ya ja hankalin masu gadi a can gate din, suka karaso su biyu duk da kayan sojoji jikinsu, suka bude gate din, kallon kallo suka shiga yi tsakaninsu, wani d'an sanda cikinsu ya fiddo id card dinsa yana nuna masu yace "Inspector Gbenga..." Tun kan sojojin su ce komai sae ga Mami da Ramla, duk suka bata hanya ta dinga bin 'yan sandan da su Mumy da kallo, duk da yanda gabanta ya fadi hakan bai hanata dakewa ba murmushi dauke fuskarta tace "Sannun ku da safiya, Allah dai yasa lafiya!" Mumy ta tabe baki tana girgixa kafa tace "Ae babu lafiya har sai dan ku ya fito min da 'ya ta yanxun nan wllh" da mugun mamaki Mami ke kallonta, inspector Gbenga yace "Muna son Hajiya a bamu dama xa mu shiga gidan nn yanxu...." Mami xuciyarta ke ta bugawa ta matsa da sauri tace "ohh bismillanku" daya daga sojan dake tsaye yace "Kiyi hakuri Hajiya sae mun kira Col mun sanar da shi..." Yan sandan suka ce "Sorry plss amma mu ma a bakin aikin mu muke ae" Sojan yace "Ehh gaskiya knn wnn, amma sai mun kira mai gidan" a hasale Mami tace "Toh me xae yi idan kun kirasa xae hanasu yin aikinsu ne?" Wani inspector yace "Alryt kirasa ku sanar da shi...." Cikin kankanin lkci sojojin suka kira mahaifin Abuturrab dake Port Harcourt a lkcn suka sanar da shi komai, mikewa tsaye yyi daga xaunen da yake yayi shirun kusan second talatin a xuciyarsa kuwa ya nanata Aliyu ya kai sau biyar, can ya gyada kai yace "Alryt su shiga..." Daga haka ya katse wayar yan sandan suka shiga gidan tare da su Mumy, iya bincike duk anyi a gaba daya gidan bbu samantha bbu alamar ta kuma, Mumy sae kuka take tana cewa "Yesu why me, ya gudu min da 'ya na shiga uku, wllh duk inda yake ku nemo sa ya fito min da ita, xan dauresa har sae inda karfi na ya kare, xae san da ni yake..." Mami dai na tsaye gefe duk jiki a mace, lkci daya hawaye ya cika idonta, Ramla da su ilham ma banda kuka bbu abinda suke. Dago kai Abuturrab yayi da sauri jin an dafa kafadarsa yaga Hajiya Mariya ce, da mamaki tace "Tunanin meye haka Aliyu, ga ni ga ka na kira ka ya fi sau uku amma shiru!" Ajiyar xuciya ya sauke ya lumshe ido yace "Mumy jikina na bani there is something happening at home, my heart is throbbing..." Cikin kwantar da murya Hajiya Mariya tace "Kayi addu'a Allah ya kawo komai da sauki ka ji son..." Kai kawai ya gyada mata, tun shigowarsu gidan ya kasa cin komai, samantha kuwa tilasta ta Hajiya Mariya tayi ta yi breakfast daga nan kuma ta kai ta bedroom dinta tasa ta kwanta, tana kwanciya kuwa bacci ya dauketa.

*Haske Writers asso*πŸ“šβœπŸ»
πŸ’« *Noorul Huda*πŸ’«

26.....

Karfe goma da kusan rabi Abuturrab na kofar gida zaune yana danna wayarsa kiran Abba ya shigo wayar, sosai gabansa ya fadi da kamar baxae dauka ba sae kuma ya daga ya kai kunne yyi shiru, daga daya bangaren Abba yace "Kana ji na, ka taho gida yanxun nan am waiting for you, i mean immediately!" kasa cewa komai yayi jikinsa yayi sanyi sosai, yayi karfin halin mikewa ya shiga gida, xaune ya samu Hajiya Mariya parlor hannunta rike da Hisnul muslim, ya isa gabanta ya durkusa yace "Mumy wai kin ji Abba in xo, ni nasan all is not well tunda har hankalina yaki kwanciya" ita kanta sae da taji hankalinta ya tashi, ya girgixa kai ya daura kansa a kafarta cikin sanyin murya yace "Mumy ni baxan iya rabuwa da ita, ban san irin son da nake mata ba..." Dago kansa tayi taga hawaye idonsa, wanda hakan ya bata mamaki sosai anya ma ita ta taba ganin hawayensa, ta girgixa masa kai tace "Be a man Aliyu, ko kaje yanxu just show you know nothing about her whereabout, ni kuma in'sha Allah i will take care of her a nan, baxan bari taje ko ina ba, tashi kaje tunda yace yana jiran ka" mikewa Abuturrab yayi jiki ba kwari ya fita, har ya isa gida gabansa bae daina faduwa ba, kallon motar yan sandan dake bakin gate har lkcn ya dinga yi, can ya dake ya fito ya rufe motarsa ya shiga gidan, ko kallon yan sandan dake tsaye tsakar gidan bai yi ba ya nufi inda ya hango Abbansa dake tsaye sanye da uniform da gani kasan saukansa knn, Mami na tsaye daga gefensa Ga Mumy da tawagarta da alama shi dae ake jira, yana isa kuwa Abba ya sauke masa lafiyayyen mari ya sunkuyar da kai ya kasa dagowa, cikin tsananin fushi Abba yace "Ina ka kai yar mutane?" Da sauri ya dago yace "Yar mutane kuma Abba" komawa baya yayi ganin Abba xae kuma marinsa, ya xaro ido yace "Bbu wata yarinya dake gu na Abba, gun aiki na fita, i know nothing about any girl...." Cakumosa Mumy tayi cikin tsananin fushi tace "Karya kake munafuki algungumi, gashi har ka koya ma 'ya ta karya, na rantse maku yasan inda take, don haka ya fito mun da ita idan ba haka ba a tada Nigeria, bbu ruwana da waye ubanka, ku fito min da yarinya ta....." Cikin kuka sosai ta kare maganar ta sake sa ta daura hannu a ka tace "Na shiga uku na lalace" Abba ya dinga yi ma Abuturrab wani kallo, Mami kam banda hawaye bbu abinda take, kasa kallon inda Mr David ke tsaye rungume da hannunsa Abuturrab yayi, cikin sanyin murya yace "Abba sharri ake son min, i know nothing about all this, toh ina xan kai yar mutane, xa a iya shiga ciki a duba ko tana nan..." Turasa Mumy tayi tana huci tace "Yesu! Kai baka jin kunyan karya ne, ina ce jiya birthday ka ja ta ku ka je, ina ce jiya ka bata zobe wae zaka aureta, ka mance hanyar jirgi daban ta mota daban, meye ya hada warce ta fito from a very good Christian home da musulmi, bbu hadin ku don haka ka fito min da 'ya ta idan ba haka ba in kashe ka har lahira!" Wani kallo Abuturrab yyi mata yace "Ni xa ki kashe kuma?" Girgiza kai yayi yana kallon 'yan sandan dake tsatstsaye yace "Ko da maganar nan xae kai mu kotu ku xaku xame min shaida kashe ni tace xata yi." Abba ya kalli sojoji uku dake tsaye gun yace "Ku saka min shi a guard room, ko ba shi ya dauketa ba sai ya fadi inda take, idan kuma yaki ba sae ta kashe sa ba ni xan harbe sa...." Ta gefen ido Abuturrab ya kalle sojojin kawai ya tafi kai kansa Guard room din kafin ma su nufo sa, Cikin tsawa Abba yace "Ku bi sa ku sa shi nace" Daga haka ya nufi yan sandan dake gun, Mumy ta watsa ma Mami wani kallo tana hawaye tace "Amma kin haifa ma kanki jaraba, don wnn d'an naki annoba ne a gari...." Vivian ta ja hannunta suka yi waje tana rusa kuka. Har bayan azahar Abuturrab na guardroom daga shi sae singlet da dogon wando, bai wani damu ba don sbda shi ma aka yi guard room din a gidan, don haka inda sabo yaci ace ya saba, ko d'an shekara 15 aka saka a gun sae yaji jiki tsabar k'ankantar gun ga uban zafi, ko kwakkwaran motsi bae iya yi, a takure yake waje daya kansa ma baya iya dagawa straight sae a duke, tun bai kai sha biyar ba Abba ke jefasa nn idan yayi laifi kuma sae yafi awa biyar a haka, rabonsa da guard room tun yana 27 yrs wato 3yrs back da ya dauko wani maganan, karfe uku yaji an bude kofa daga waje, ko ba a gaya masa ba yasan Mami ce don ita kadae ke xuwa idan aka kullesa, ae ko ita ce, ta durkusa ta bude karamin kofar da yake ciki da aka sa ma uban kwado, da ganinta kasan ta ci kuka, kamar jira yake tana budesa ya fito duk ya jike jagab da gumi, kasa kallon idonta yayi, ya dafa gwiwansa kansa a sunkuye don gaba daya jikinsa yayi tsami, ga wuyarsa da ya rike, muryarta yaji tace "Aliyu ina 'yar mutane" bai d'ago ba kuma bai ce komai ba, can dai ya dago da kyar jin tayi shiru, tausayinta yaji sosai shi dai yasan tun da kwakwalwarsa ta fara aiki irin na mutane rabon Mami da samun kwanciyar hankali, ko da yaushe cikin dauko magana yake ba babba ba ba karami ba kuma a kanta komai ke karewa don Abba cewa yake ita ta 6ata shi, kwanan nan ne ma abun ya lafa bayan ya fara aiki don ko lkcn yana sch hankalin iyayensa ba a kwance yake ba, kamar xae yi kuka yace "Mami ni fa ban san komai kan maganar nan ba sae xalina ake ci kawai!" Hawaye ya gani idonta ya xube nan kasa yace "Noo Mami don Allah kiyi hakuri...." Dakewa tayi tace "Ina yar mutane take Ali?" Shiru yayi kafin ya dago a hankali ya goge xufar dake fuskarsa yace "Mami...." Sai kuma yayi shiru, sauke idonsa kasa yayi yace "Tana nan!" Mami ta durkusa gabansa ta dago kansa tace "A ina?" Kallonta yayi murya can kasa yace "Mami.... Mami ita nake so and i want to convert her...." Komawa baya Mami tayi da mugun mamaki tana kallonsa kamar idanuwanta xa su fito, cikin rawar murya tace "Aliyuu!" Marairaice mata yayi yace "Mami ni idan ban aureta ba Allah xan iya mutuwa wllh, i will be nothing without her" hawaye ne ya cika idonsa, wanda rabon ta da ganin hakan tun yana d'an shekara goma, ko me xaka yi masa baxa ka taba ganin hawayensa ba sai dai idonsa yayi jajir kirjinsa yayi ta sama da kasa tsabar dacin rai da rashin ji irin nasa, ya daura kansa a jikinta muryarsa na rawa yace "First love support me plss, i love her, ni baxan iya rabuwa da ita ba, kuma Mami idan na musuluntar da ita lada xan samu fah..." Hawaye kawae Mami take duk jikinta yayi sanyi, ita kam tana ganin jarabawa tun da ta haifi Aliyu, ta saita kanta cikin sanyin murya tace "Toh tana ina?" Da kamar baxae ce komai ba sai kuma yace "Tana gidan Mumy!" Da mugun mamaki tace "Mariya?" Yayi shiru bai ce komai ba, ta sauke ajiyar xuciya a hankali, jin tayi shiru ya dago da sauri yace "Mami plss kar fa ki ce ma kowa haka, don Allah kar ki fadi Mami...." A rude ya kare maganar, cikin kwantar da murya tace "Ka gwammace kayi ta shan wahala knn, to ai shknn, shiru xan yi da baki na idan ma ya kashe ka kai ka ja ma kanka, tashi ka shiga ciki kafin a ganmu dama cewa yake ni ke supporting din ka" kallon d'an kurkukun yayi kafin ya marairaice yace "Mami k'ishi nake ji sosai wllh" mikewa tayi tace tana xuwa snn ta fita, ya fi kowa sanin halin Mami yasan wannan duk pretending take masa, ya kalli bunch of keys din da ta ajiye nan kasa bayan ta bude sa, ya dauka da sauri ya cire biyu ya tona kasa ya boye a cikin d'an room din, yana nan durkushe yana yi yana lekan sojoji biyun dake tsaye waje har ta dawo ya sunkuyar da kansa da sauri, Ruwan babban gora me sanyi ta kawo masa da Hollandia yoghurt, sae dambun nama cike a plate tace toh tashi ka shiga kafin ya yo nan, karban ruwan yayi ya sha kusan rabi, Key din dake ajiye kawae take kallo can ta dauka tana weighing dinsa ta kallesa strictly tace "Ka cire key a nan bani!" Da sauri yace "Key kuma Mami" wani kallo tayi masa tace "mike tsaye" yana tashi ta sa hannu aljihunsa ta dudduba taga babu, ta leka guard room din ma bata ga alamar key ba tace "Toh shiga ciki" ya ajiye ruwan hannunsa fuskar nan tasa kamar xae yi kuka ya durkusa ya shiga ta tura masa abubuwan da ta kawo snn ta rufe gun da kwado ta juya ta nufi kofa, ya bi ta da kallo yana murmushi har ta fita. Ko minti goma ba ayi da fitarta ba yasa key ya bude gun a hankali ya fito, ya dau shirt dinsa dake rataye gun ya kakkabe ya saka snn ya saka takalmansa ya nufi kofa da sauri, lkci daya ya banke kofar ya fice a dari da sittin kafin sojojin su ankara, ae ko suka bi sa da gudu, gudu yake kamar jirgi xae tashi sama, wani soldier ya ciro whistle a aljihunsa ya dinga hurawa, ae ko sae ga sojoji har uku sun fito, Abba ma ya fito balconynsa a sama ya rungume hannu da mugun mamaki yana kallon Abuturrab, komawa yayi don dauko bindigarsa amma kafin ya dawo tuni ya isa gate da karfi ya finciko mai gadin sojan dake bakin gate yana kkrin datse gate din ya wani wurgar da shi ya fixgo gate din ya fice, gudu kawai yake kamar xae tashi sama, wanda hakan ya tsorata mutane duk suka fara gudu su ma, ko kallonsu bai yi ba har ya iso titi ya tsayar da mai adai daita bai jira ya tsaya ba ya afka ciki yace "Mu je muje da sauri....." Mai adai daita ya ja machine dinsa da sauri don shi ma ya tsorata, Abuturrab ya sauke ajiyar xuciya ya share xufar fuskarsa ya bude button din riga.

*Haske writers asso*πŸ“šβœπŸ» It's Khaleesat HaiydarπŸ‘ŒπŸ»
πŸ’« *Noorul Huda*πŸ’«

27.....
Gani yake kamar ba tafiya mai adai daitan yake ba duk da yasan yayi escaping don baxa ma su san inda ya bi ba, yayi tsaki yace "Malam ajiye ni nan dan Allah" Mai adai daitan yayi parking Abuturrab ya fito yace "Sae dai kayi hakuri bani da kudi" daga haka ya yi gaba da sauri, mai adai daitan ya bi sa da kallo, yanxu kawae so yake ya gansa gidan Hajiya Mariya yasan tun da ya fadi ma Mami kamar an je an dauko Samantha an ba iyayenta ne, makullin motarsa dama tun da aka sa shi guardroom Abba ya karbe da wayoyinsa, wani bike ya tsayar yana kallon mutumin dake kai yace "Ehrm Don Allah malam ka goya ni xuwa Kofar Nasarawa idan ba damuwa..." Mutumin yace "Ba can nayi ba, nama kawo gida ka ga inda xan shiga..." Abuturrab yace "Toh don Allah ara min bike din... Xan dawo maka da shi" wani kallo mutumin ke ma Abuturrab daga sama har kasa baki bude, Abuturrab ya dafa sa yace "Na maka kama da barawo???" Shi dai mutumin kallonsa kawai yake, Abuturrab ya fixge key din yace "Nafi karfin satan machine, kuma i think da wuya a ga barawo Aliyu Haiydar! Sauka ka ban machine malam" kamar soko haka mutumin ya sauka, Abuturrab ya hau ya tada machine din ya figa da gudu ya hau kan titin, alarm mutumin ya saki bayan Abuturrab ya bace masa yana cewa ya hadu da d'an rufa ido. Cikin kankanin lkci Abuturrab ya iso gidan Hajiya Mariya, a sanyaye ya sameta a parlor ya karasa ya xauna yace "Mumy!" Ta kallesa tace "Me kace ma Mami" shiru yayi sae kuma ya mike da sauri yace "Tana ina Mumy?" Hajiya Mariya tace "Kaga ka hada ni da Mami sae da nace kar kace tana nan, to in'sha Allahu nasan duk inda suke sun ma kusa gidan nan yanxu" Abuturrab ya xaro ido ya nufi bedroom dinta da sauri ya samu Samantha kwance amma idonta biyu, ya karasa ya durkusa kusa da ita yace "Xa mu tafi yanxu samha!" Mikewa xaune tayi ya mike ya fita ta bi bayansa, durkusawa yayi kusa da Hajiya Mariya yace "Mumy babu kudi hannu na...." Mikewa tayi cikin harshen fullanci tace ya sameta a daki, bin bayanta yayi ta xauna tace "to yanxu ina xa ku Aliyu?" Ya shafa kai yace "Anywhere mum, kawai ki ban kudi kafin su karaso" Mikewa tayi ta dau purse dinta ta bude tace "Dubu uku kadai ke garen yanxu amma ga atm card!" Duk biyun ta hada masa ya karba, tace "Toh ta ya xan same ka, na kira wayarka duk switch off" yace "Abba ya karbe wayar, ina da number ki a kai i will call you idan na samu waya Mum," Daga haka ya juya ya fice ta bi sa da kallo, can ta fita ita ma, tana kallon Samantha tace "Toh xan kira ku kin ji daughter" Samantha ta gyada mata kai cikin sanyin murya tace "Nagode Mum" daga haka ta bi bayansa, Hajiya Mariya ta bi su da kallo cike da tausayi, suna fita Abuturrab ya kalleta ya langwabar da kai yace "Samha Bike xa mu hau fa!" Ta kalli machine din snn ta girgixa masa kai tace "Ban iya hawa ba...." Dariya ta basa yace "Toh ba sai in daura ki ba" ta koma baya da sauri tace "No ni ban taba hawa ba, bana so" gani yayi lkci xa su bata yace "Toh follow me fast..." Ta bi sa da sauri suka fita,

Please Login or Register in order to submit comment