Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fasa shiga xata wuce aka bude gate, sai ga shi ya fito, wara ido yayi ganinta yace "Ina kuma xa ki?" Tace "Wucewa nake yi ai" yace "Uhm, i see yaushe xa ku gama waec din?" Tace "Mun gama" yace "Waow da gaske baby, but shine baki fada min ba?" Ta langwabar da kai tace "Gashi na gaya ma!" Yace "Alryt... Plss ki xo anjima da yamma i have a surprise for you, yanxu xan tafi gun aiki ne i forgot my office key...." Tace "Baxa a bar ni in fito ba...." Xai yi magana aka bude gate sai ga Mami ta fito, gaba daya ya mance tace xai ajiyeta a hanya, kallo daya Mami tayi ma Samantha tace "Aliyu da ban fito ba wucewar ka xaka yi knn?" Ya shafa kai yace "Ohh Mami wllh mancewa nayi...." Samantha da ko ba a gaya mata ba ta gane mum dinsa ce ganin kamar da suka yi da Hajiya Mariya ta risina tace "Ina kwana..." Mami ta kalleta murmushi dauke fuskarta tace "Lafiya lau yan mata ya makaranta" murmushi kawai samantha tayi kanta a kasa tace "Sai anjima...." Daga haka ta juya ta wuce, Mami ta bude bayan mota ta shiga Abuturrab ya shiga motar shi ma ya tada, sai da yayi reverse Mami tace "Ina ka samo wnn kuma?" Ta madubi ya kalleta yace "A anguwar take, she's.... A frnd!" Mami tace "Amma ba musulma bace?" Shiru yayi na kusan minti hudu, cikin sanyin murya yace "Me kika ga Mami?" Mami dake danna waya tace "Me na gani a ina?" Yace "Da kika ce ba musulma bace" Mami da har ta mance xancen da suke tace "Ae musulinci ba boyayyen addini bne, duk inda kaga musulmi xaka gane....." Yace "But Mami uniform ne fa jikinta with Beret!" Tace "So? 'Ya mace musulma dai da ta taso gidan tarbiya baxata bar gida xuwa makaranta ba hijab ba, ko da kuwa makarantar ba a saka hijab xata sa d'an karami idan ta isa gate ta cire..." Abuturrab da idonsa ke kan titi murya can kasa yace "But mami ae lullubi ba shine abinda xai sa ka gane mutum me addini ba, a xuci....." Tunda ya fara Mami ke masa wani kallo bata bari ya kai aya ba a tsawace tace "Meye hadin ka da yarinyar nan Aliyu, who is she?" Shiru yayi har sai da tace "Baka ji na ne?" A hankali yace "She's just a frnd Mami...." Tsaki tayi ta ci gaba da danna wayarta, bai sake cewa komai ba har ya isa inda xai ajiyeta, yayi parking ya juya yana kallonta yace "Mun kawo Mami" bude motar tayi ta fita tana kallonsa tace "Yaushe xaka koma gida?" Yace "Zan bar clinic karfe hudu" tace "Ohk...." Yace "Xan biyo in dauke ki ne?" Tace "No, kafin lkcn ni na koma gida..." Daga haka tace "Allah ya tsare" sannan ta shiga gidan, ya kusa minti uku kafin ya ja motar jiki a sanyaye ya bar wajen. Karfe biyar da wani abu yana xaune kofar gida yana danna waya blessing ta xo wucewa, mikewa yayi da sauri ganinta yace "Hello!" Ta juya tana kallonsa sannan tace "Ina yini?" Yace "lafiya lau, plss wait in baki sako ki ba Samantha!" Da sauri ya shiga gida ba a dau lkci ba ya fito rike da takarda a linke ya mika mata tare da dubu daya yace "Ki bata pls" karba tayi tace "xan bata, nagode" daga haka ta wuce, ya sauke ajiyar xuciya ya koma ya xauna. Samantha ta fito daga wanka bayan magrib blessing ta bude kofar dakinta ta karasa da sauri tace "Sister Rebecca wannan Doctor din yace in baki takardan nan..." Da sauri Samantha ta karba Blessing ta juya ta fice kafin Mumy ta fara nemanta, xaunawa tayi gaban mirror tana goge jikinta tana gamawa ta dauko lotion ta fara shafawa sannan ta dau turarruka fiye da kala biyar ta feshe jikinta da su, sai da ta gama ta dau takardan ta bude, rubutu ta gani kamar haka "ki taho don Allah am waiting for you love...." Ajiye takardar tayi hade da tabe baki ta mike ta dauko kayan baccinta ta saka snn ta tusa gashinta a net, ta kusa minti talatin xaune, can ta mike a hankali ta bude closet dinta ta dauko daya daga hijabs din da take sawa lkcn sanyi ta saka shi har kasa, ta kashe wutan dakinta ta fita, tana waige waige kamar munafuka har ta fita daga gidan. Ta jima tsaye bakin gate din gidan kafin ta tura a hankali ta shiga ta rufe, bbu kowa parlon ta tsaya bakin kofa tana kare ma ko ina kallo, fitowa yayi daga bedroom, yayi murmushi yana kallonta ya karaso yace "Woaw she came!" Rufe kofar yayi yasa key yace "Welcm love" ta hade rae tace "me yasa kace in xo?" Yace "I just want to see you" turo baki tayi tace "Bude min kofa in wuce...." Wara ido yayi yace "Noo, not until you repeat what you said yesterday...." Juyawa tayi da sauri tace "Noo, plss ka bar ni in wuce..." Murmushi yayi yace "Then ashe xa ki kwana a nan" kamar xata yi kuka tace "Plsss..." Ya daga kafada yace "Ohk let see" daga haka ya tafi three seater yayi kwanciyarsa, ji tayi kamar ta fashe da kuka, wayarsa ya dauka ya jona earpiece ya makala a kunne hade da lumshe ido, ta kusa minti talatin tsaye parlon ganin ya ki cewa komai ta juyo a hankali ta ga har lkcin idonsa a lumshe suke, can ta karasa kusa da shi ta duka tana kallonsa sae ta ga kamar bacci yake, kasa dauke idonta a fuskarsa tayi, can ta cire earpiece daya a hankali ta kai kunne taji karatun Qur'ani yake ji, mayar masa tayi, ta matsa kusa da shi har lkci tana kallonsa, a hankali tace "I... I said i... Love you!" Kallon fingers dinsa tayi ta kai hannunta tana kallon Ring din azurfan dake hannunsa har biyu, lumshe ido tayi ta daura lips dinta a hankali, rike hannunta yayi ta sake sa da sauri duk ta daburce xata mike ya ki saketa ya mike xaune.

*Haske writers asso*📚✍🏻
💫 *Noorul Huda*💫

21.....

Kin bari su hada ido tayi tana girgixa kai tace "Doctor plss ka sake ni..." Yace "Noo..." Kwankwasa kofa aka yi suka kalli kofar a tare, ta xaro ido tace "Wayyo ka sake ni..." Saketa yyi ya mike yana kallon kofar, ta tashi da sauri tayi hanyar bedroom, karasawa gun kofar yayi yace "Waye?" Muryar Ramla ya ji tace "Ni ce!" Yace "What?" Tace "Abba yana kiran ka wai..." Yace "Alryt ga ni nan xuwa" tace "Toh baxa ka bude ba yaya?" Yace "Yess" tabe baki tayi ta juya ta wuce, juyawa yayi ya shiga bedroom din ya ganta tsaye bakin kofa, tana ganinsa ta juya, ya rungume hannayensa yace "Ashe kina sa Hijab?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Ina wayar da na baki?" A hankali tace "Yana gida!" Ya juyo da ita yana kallon fuskarta yace "ki ajiye shi kusa da ke yau, i will cal you" ta sunkuyar da kanta tace "Toh" yayi murmushi yace "Mu je in raka ki" hanya ya bata ta fita sannan ya fita shi ma, har kusa da gidansu ya rakata yana kallonta yace "Kar kiyi bacci fa, i will call you..." Daga haka ya juya ya wuce ta bi sa da kallo, snn ta nufi gate kamar mara laka ta shiga. Abuturrab na isa gida ya wuce parlor din Abbansa, Abba dake waya tun shigowarsa ya ajiye bayan ya gama yace "Aliyu!" Abuturrab yace "Na'am..." "Kadai san in ka raina ni to yakumbo ta wuce raini a gun ka koh?" Cewar Abba kenan yana kallonsa, Abuturrab ya sunkuyar da kai ya kasa cewa komai, Abba yace "Tashi ka je...." Ba musu ya mike murya can kasa yace "Kayi hakuri Abba dama..." Kofa Abba ya nuna masa, hakan yasa ya fita kawai, sha biyu saura ya gama abinda xai yi ya rufe laptop snn ya dau wayarsa yayi dialing layinsa dake wayar da ya ba Samantha, tana kwance hannunta rike da hymn book tana dubawa kiran ya shigo wayar dake gefenta, langwabar da kai tayi ta dauka ta yi picking ta kai kunne, daga daya bangaren yace "Hope baki yi hacci ba?" Tace "Yanxu xan yi..." Yace "Tafi ki wanke idon..." Murmushi tayi ta make kafada kamar yana ganinta, yace "Ina son in maki wani tambaya samha..." Tace "Samantha not samha..." Yace "Noo samha not Samantha.." Tace "Uhm to ina jin ka..." Shirun kusan second ashirin yayi kafin yace "Za ki iya aurena?" Kasa cewa komai tayi sbda mamaki da ya cika ta, yace "I know you re there!" A hankali tace "Aure kuma?" Yace "Yeah.." Ta girgixa kai tace "But ae bbu aure tsakaninmu da kai, our religion differs, am a Christian, you re a muslim..." Yace "Akwai aure tsakaninmu...." Da mamaki tace "How?" Ya shafa kai yace "Sai kiyi addinin ki in yi nawa!" Wani shirun ta kuma yi words dinsa na mata yawo a kai, murya can ciki yace "Samha!" Kasa amsawa tayi, cikin sanyin murya yace "Baki so na kenan..." Jikinta yayi sanyi still ta rasa abun cewa, kiranta ya kuma yi kamar xata yi kuka tace "Ni ban san me xan ce ba..." Yace "Ki ce za ki aure ni" tace "you know that's very impossible, taya hakan xai yiwu bayan addininmu daban daban...." Lumshe ido yayi yace "Nace maki kowa addininsa xai yi, i see nothing wrong with that...." Rasa ma wani tunani xata yi a lkcn tayi, xata iya auren Abuturrab kuwa? Did she even love him? She know she so care about him.. Tunanin hakan sai da yasa gabanta faduwa sosai, to in ta yarda xata aure sa Mumy da Abba fa? Ya relative dinsu xa su dau xancen... Muryarsa taji yace "Samha!" Hawaye ne ya cika idonta ta kasa amsawa, da dadewa tasan she had alwayz like him, amma bata taba tunanin har xae shigo da xancen aure tsakaninsu ba, a hankali taji yace "Shikenan sai da safe" lkci daya hawayen idonta ya xubo cikin rawar murya tace "Doctor kasan baxai yiwu ba, My parent... My relatives, my...." Kuka ta fara masa, duk ya rikice yace "Kuka kuma... Pls stop it now" kasa daina kukan tayi, yace "OMG don nace xan aure ki shi yasa ki kuka, ok am sorry baxan sake ba..." Daga haka ya katse wayar, ya jefar gefensa ya kashe wuta yayi kwanciyarsa, hade kai tayi da gwiwa ta fara kuka, daga karshe ta gaji ta kwanta, kasa bacci tayi daren ranan, maganganun Abuturrab kadai ke mata yawo a ka, sae kusan karfe uku ta samu bacci ya dauketa, Mumy ce ta tasheta karfe takwas da minti sha biyar, ta mike xaune, Mumy tace "Baki tashi kinyi morning devotion din ki ba wnn wani irin bacci kika yi" Kallon idonta Mumy tayi tace "Me ya samu idon ki, kuka kika yi ne?" Samantha ta girgixa kai cikin sanyin murya tace "kai na ke min ciwo..." Mumy tace "Kai kuma? Toh tashi ki shirya sai kiyi breakfast ki sha magani," daga haka ta fita, da kyar Samantha ta mike tsaye don ji tayi gaba daya kanta ya mata nauyi, bathroom ta shiga ta wanke baki tayi wanka sannan ta fito, tana goge jiki Abuturrab ya fado mata wanda hakan sai da yasa gabanta ya fadi sosai, hawaye ya cika idonta, jiki a mace ta karasa shiryawa, Blessing ta shigo da tray dake dauke da breakfast ta ajiye mata ta gaisheta snn ta fita, da kyar ta iya shan tea xata kwanta sai ga Mumy ta shigo da magunguna ta bata ta sha, mumy tace "Thank God sai da ku ka gama jarabawa ciwon kan ya same ki, ki kwanta xuwa anjima mu ga" daga haka ta fita, Samantha ta kwanta hade da lumshe ido, ta kasa daina tunanin Abuturrab ta kuma rasa dalili, a da tasan yana yawan fado mata barin idan suka dade basu hadu ba, amma tun daga jiya da daddare xuwa yau sae ta ga ya fi na ko da yaushe, to fushi yayi ne yasa ya kashe wayarsa amma ai gaskiya take fada, runtse ido tayi ko bacci xae dauketa amma shiru, sae a lkcn tasan ashe fa ta damu da shi haka. Har washegari Abuturrab bai sake kiranta ba, ita dai tasan bbu wani ciwon kai but da Mumy ta tambayeta me ke damunta sai tace ciwon kai, tun da take abu bai taba tsaya mata a rai kamar yanda wannan ya tsaya mata ba, ta kasa dauke tunanin a ranta, Mumy ta kira Abba dake Lagos ta fadi masa bata da lafiya xa su je asibiti, Abba yace ba sai anje ba xae turo likita, Abuturrab na xaune office yana aikin gabansa, baka taba cewa abu na damunsa sai dai da xaka shiga xuciyarsa ka ga tulin damuwar dake tattare da gun sae ka tausaya masa, babban damuwarsa bai san yanda xae yi da Yakumbo ba don yasan shi ake ta jira, gashi ya kasa daina tunanin Samantha, yasan ba fault dinta bane that's just the fact but kawai ya shareta ya kuma dau ma kansa alkawarin ko ba yanxu ba sai ya aureta ko da kuwa threatening din kisa xa ayi masa, Tun a daren yake raya ma kansa to ko ya koma ga saudat, yana jin kuma xuciyarsa ta aminta da hakan coz he gat no option. Daren ranan ya shirya ya tafi gidansu Saudat, tun da yayi parking a kofar gidansu yake kallon motar dake parke gaba da nasa ganin kamar akwai mutane a ciki, ae ko sai ga shi an bude motar saudat ta fito, tabe baki yayi ya tada motarsa kawai yayi reverse ya bar gun, bai bar layin ba kiranta ya shigo wayarsa, ya ci gaba da tukinsa ba tare da ya sake kallon wayar ba. Washegari Wednesday yana xaune office ya hade kai da table Mujaheed ya shigo, har ya karasa gun table din Abuturrab bai dago ba, mujaheed ya bugi table din yace "Bacci kake a bakin aiki doctor?" Dagowa Abuturrab yayi yana kallonsa yace "Daga ina haka?" Mujaheed yace "Asibiti na xo bani da lafiya mana" murmushi Abuturrab yayi yace "Ohh i see" mujaheed yace "Ya na ganka haka kamar kana tare da damuwa" Abuturrab yayi yake yace "Damuwa kuma, am just tired ne, ya aiki?" Mujaheed yace "Alhmdllh"

*Haske writers asso*📚✍🏻
💫 *Noorul Huda*💫

22......

Hira suka ta yi a asibitin har bayan la'asar suna fitowa daga masallaci ko wannensu ya dau hanyar gida, yau kam Abuturrab a main house dinsu ya sauka, Mami dake parlor ta bi sa da kallo bayan ya gaisheta har ya haura sama, wanka yayi ya fiddo jallabiyarsa a daki ya sa yayi kwanciyarsa. Ringing din wayarsa ne ya tashesa kusan magrib, dai dai shigowar mami dakin tace "Lafiyan ka Aliyu, baccin yamma ana xaune kalau?" Mikewa xaune yayi ya dau wayarsa yayi picking call din, daga daya bangaren aka ce "Hello!" Abuturrab yace "Good evening" "Evening, kana gida ne doctor" cewar mutumin kenan, sae a snn Abuturrab ya dau murya yace "Yeah ina gida sir, ya aiki?" Mr David yace "We Thank God, daughter na ne bata da lafiya, i want you to check on her if it's ohk by you and you re less busy pls" Abuturrab da hankalinsa ya tashi lkci daya yace "Ohk sir, i will do that right away!" Daga haka ya katse wayar ya kalli Mami dake tsaye har lkcn tana kallonsa yace "Mami na gaji da yawa ne yau" tace "ko abincin fa baka ci ba" mikewa yayi tsaye yace "Bari in dawo daga masallaci Mami" daga haka ya fita, ana idar da magrib ya tafi gidansu Samantha, bayan sun gaisa da mai gadin ya shiga, mai aiki ce ta bude masa kofa bayan ya danna bell, ya amsa gaisuwarta ya tambayeta inda Samantha take tace tana bedroom, ita ta raka sa har sama, ya bude kofar dakin suka yi ido hudu da mahaifiyarta dake xaune dakin alamar dai likita take jira, tana ganinsa ta hade rai sosai, ya sunkuyar da kansa ya karasa dakin ya gaisheta da ladabi, da hanci ta amsa masa ta mike ta fice, Abuturrab ya durkusa kusa da gadon yana kallonta ganin yanda lips dinta yayi ja, hannu ya daura forehead dinta ya ji dumi, a hankali yace "Samha..." Bude ido tayi da sauri ta mike xaune, ya kamo hannunta yace "Ina ke maki ciwo?" Hawaye ya cika idonta ta ki cewa komai, cire bargon jikinta yayi yace "Talk plss" ta sauke idonta kasa, ya tsura ma wuyarta dake dauke da farin cross ido, a hankali ya kai hannu kai xae tsinka ta rike hannun da sauri tace "Mumy ce ta sa min" bai kulata ba ya tsinka shi ya jefar gefe daya, ta sauke hannunta tana kallonsa, kallon kwayar idonta yake shi ma, hawayen da ke makale idonta ya gangaro ta daura kanta a shoulder dinsa cikin sanyin murya tace "Ni fa ban ce komai ba doctor, and you re angry, kayi hakuri pls..." Ya harde hannunsa da nata ya lumshe ido yace "Noo, kin fa ce baxa ki iya aurena ba" ta fashe da kuka tace "Nooo ni bnce haka ba fa..." Shiru yayi yana jin saukar hawayenta a shoulder dinsa, ya shafa kanta a hankali yace "But nace kiyi addinin ki inyi nawa fa, still kika ce it's impossible" girgixa kai tayi tace "Bayan kana rabani da duk wani abu na addini na shine xaka ce min haka, yanxu fa ka tsinka min rosary dina...." Buda ido yayi jin abinda tace, ya dago kanta yace "Ohh you gat me wrong samha..." Da sauri tace "Noo i am right" yace "You re sick kuma rosary din nan is a burden....." Hade rai tayi tace "A tunanin ka ba, kayan jikina bai xame min burden ba sai rosary" yace "Alryt am sorry baxan sake ba..." Bude kofa aka yi ya koma baya da sauri blessing ta shigo da gani kasan mumy ce tace ta taho, Ya kalleta yace "Taimaka mana da cup of tea pls.." Tace "Toh" snn ta fita, ya kamo hannunta yace "Toh yanxu ina ke maki ciwo" kanta ta nuna masa, yayi shiru yana kallonta, can yace ohk yanxun nan xae daina, lumshe ido yayi ya manna bakinsa kan goshinta, turasa ta fara yi tace "Doctorrrr" ya rike kanta gam ya sauko da ba lips din har kan hancinta sannan bakinta, yayi mata light French kiss, turasa tayi ta hade rai, ya wara mata ido ya koma baya yace "Alryt am sorry wife...." Blessing ce ta shigo da cup din tea ya karba ya mika ma Samantha, ta6awa tayi tace "Akwai zafi ai" ya ajiye sa kan bedside drawer yace "Toh bari inje in dawo yanxu" da ido ta bi sa har ya fita, gida ya koma ya dauko mata drugs ba a dau lkci ba ya dawo, har lkcn blessing na dakin, yayi mata kallo daya ya karasa gun Samantha ya dau tea din da ya ajiye ya kai baki yayi sip dinsa snn ya mika mata yace "Toh ya huce" hannu tasa ta karba, aka bude kofa Mumy ta shigo, mikewa yayi ya bude ledan maganin ya gwada mata yanda xata sha ya ajiye ya d'an saci kallon mumy ya ganta tsaye fuskar nan a murtuke, dukawa yayi kamar xae dauki abu murya can ciki yace "I will call you ltr..." Daga haka ya juya, bai bari sun hada ido da Mumy ba yayi mata sallama ya fita. Kamar jiya yau ma sha biyu da wani abu ya kirata, tana kwance ta dau wayar tayi picking ta kai kunne, daga daya bangaren yace "How you feeling now?" Tace "Da sauki..." Yace "Sai kice Alhmdllh..." Ta buda ido tace "Alhmdllh kuma?" Yace "Yess" tace "Tohm Alhmdllh" yayi murmushi yace "Good, a ina muka tsaya jiya a maganar mu?" Bata ce komai ba yace "Samha..." Cikin sanyin murya tace "Na'am" yace "Baki son maganan ne?" Girgixa kai tayi kamar yana ganinta tace "A'a fah" yace "Say something now" da kyar tace "Duk yanda kace doctor" murmushi yayi yace "Ohk we'll talk about that face to face...." Cikin sanyin murya tace "Toh" "Me xa ki bani for my birthday?" Wara ido tayi tace "Woaw, it's also my birthday month, wani date ne naka?" Yace "Da gaske kema month dinki ne?" Tace "Eh mana, my birthday is on 10th june...." Da mamaki yace "Are you for real?" Tace "Yes mana" yace "Woaww what a concurrent! It's same with mine" tace "heey doctor ba wani nan..." Yace "Am serious samha, i was also born on 10th june" tace "Wow so we re birthday mates?" Yace "Yeahh and we gonna celebrate it together.... No wonder shi yasa kike da kyau kema kamar ni... Haka kuma xa mu haifi yara duk june 10" Ta xaro ido tace "Uhm?" Yace "Yess am serious baby, today is 3rd, 7 dayz to our birthday!"
Tun daga lkcn wayarsu ya xama constant don xaman gida kawai take, duk bayan awa biyu sai ya kirata, hakan kuma yasa bai damu da rashin ganinta ba tunda suna waya, a haka har ya rage kwana daya birthday din nasu, da daddare yana daki ya kirata yace "Baby plss ki daure ki fito yau mana, i want to see you" ta kalli agogo taga har tara da rabi tace "But baka kalli agogo ba koh doctor" yace "Na kalla mana ai ba dadewa xa kiyi ba" xata yi magana yace "Plssss" kamar xata yi kuka tace "Doctor....." Yace "Plss" turo baki tayi tace "Na ji" daga haka ta katse wayar, tayi tagumi, can ta mike ta dau hijab ta sa ta kashe wutan dakinta ta fita, ko blessing dake daki bata sani ba, tana isa gidan bata gansa parlor ba, ta bata fuska tana kallon kofar daki, a bayanta taji sa a tsaye ta juyo da sauri ya wara mata ido yace "Welcome..." Tace "Toh kiran meye" kama hannunta yayi ya shiga da ita kitchen yace "Am hungry kuma potato and egg nake son ci, hope Mumy baxa ta neme ki ba" shiru tayi bata ce komai ba, can a hankali tace "Ohk... Mumy ta tafi church" Yace "Good, cire hijab din" tace "No xan yi a haka" gun da potatoes suke ta nufa ta debi wanda tasan xai yi masa ta fara ferewa da peeler, cikin kankanin lkci ta gama, duk yana tsaye yana kallonta, kafin minti goma har ta gama, ta daura ruwan Lipton ta juya tana kallonsa tace "Ko baxa ka sha ba" yana rungume da hannunsa yace "Xan sha mana" kayan kamshi ta xuba ta rufe snn ta dau dankali da kwan ta fita ta kai parlor ya bi ta da kallo, tana dawowa kitchen din tace "Toh kaje ka ci kafin ruwan shayin yayi" ya girgixa kai yace "No xan taya ki jira a nn" murmushi tayi bata ce komai ba, haka suka ta tsayuwa har ruwan ya tafasa ta juye flask snn suka fito, sai da ya tilasta ta suka ci abincin a tare, nan ya sa masu film a system tun tana cewa ita gida xata wuce har ta hakura tana kallon, kamar ance ta kalli agogo taga sha biyu saura 'yan mintuna, xaro ido tayi tace "Na shiga uku, doctor kalli agogo" mikewa take son yi ya riketa yace "But it's late Samha...." Turasa tayi tace "Let me plss, ni bana son kana min irin haka, you are just letting me betray my parent, ni ka sake ni" a fusace tayi maganar ta mike ya bi ta da kallo har ta isa kofa ta dawo don daukar takalmanta dake bakin kitchen, lkci daya aka bude kofar parlon, still tayi a gun tana kallon kofar, Ramla, Khaleesat, da Ilham ne suka shigo a tare, juyawa yayi shi ma yana kallonsu sannan ya kalli agogo da mamaki, ko kadan bai lura da abinda ke hannunsu ba da mamaki yace "Lafiya?" A tare duk suka bude murfin ruwan gora me sanyi dake hannunsu suka tuttula masa gaba daya a jiki lkci daya suka ce "Happy birthday....." Bai gama

Please Login or Register in order to submit comment