Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kallonsa tace "Matar ka kuma" ya kai fuskarsa dab da nata yace "Ko baxa ki iya aurena ba" xaro ido tayi da mamaki xata yi magana ya rufe bakinta yana murmushi yace "Yesss" daga haka ya mike ya fita ya rufe gate snn ya dawo ciki ya rufe kofa ta bi sa da kallo har ya xauna yace "Za kiyi wanka?" Ta girgixa kai yace "Alryt shiga ki gyara inda xa ki kwana ni parlor xan kwanta before then bari inyi wanka" binsa tayi da ido har ya shiga dakin sai kuma ta bi bayansa, taga har ya shige bathroom, kallon gadon tayi taga it's tidy except from the bedsheet wanda hakan ya nuna alaman yayi bacci a kai, ta karasa ta shiga gyarawa tana gamawa ta dau wayarsa dake gaban mirror ta fara game, har ya fito bata sani ba, sai jin kamshi me dadi hade da ruwa da ya diga a jikinta, da sauri ta dago suka ci karo, ta mike tace "Ohhh sorry" yace "Uhm ohk" sauke idonta tayi ta mayar ga wayar ya nufi gaban mirror, har ya gama shiryawa bata kalli inda yake ba, sai bayan da ya gama ya dawo ya xauna kusa da ita yace "Kina da paper gobe?" Ta girgixa kai tace "Sae Tuesday" kallon game din da take yayi tayi, can ta mika masa wayar tace "Za kayi amfani da shi?" Ya girgixa kai yace "No, i just want you to tell me a story, may be a bible story, i like them, No! Ko kuma mu ci gaba da wanda nake baki ranan" ta kallesa tace "Toh barin in fara baka sae ka ci mim gaba, wani iri kake so?" yace "ko wanne" ta langwabar da kai tace "Ohk let me tell you the story of Joseph you will like it" yace "Tohm" hawa gadon yayi ya nuna mata kusa da shi ta turo baki tace "Nan ma yayi" yayi murmushi yace "Ohk" shiru tayi sai kuma a hankali ta hau ta dawo kusa da shi, nan ta fara basa story din Joseph according to the new testament of their Holy Bible, jin shirun yayi yawa ta dago tana kallonsa taga idonsa lumshe, murya can kasa tace "Doctor..." taji shiru, tsura ma long lashes dinsa ido tayi snn ta sauke idonta kan cute lips dinsa, bacci yake hankalinsa kwance, murmushi tayi ta gyara masa kansa a hankali snn ta koma can karshen gadon ta kwanta ta juya masa baya, nan da nan ita ma bacci ya dauke ta, can cikin dare ya farka ya mike xaune da sauri ta dalilin hasken dakin don wuta a kunne yake har lkcn kuma dama shi bai saba kwana da wuta ba, ya juya ya kalleta yaga ta dukunkune gu daya tana bacci don sanyi ne sosai a dakin ta dalilin ac da ya kure, sauka yyi daga kan gadon ya shiga toilet ya fito snn ya dauko duvet ya dawo kusa da ita ya lullubata da shi ya durkusa kusa da ita yana kallon kyakkyawan fuskarta, lumshe ido yayi ya kai lips dinsa goshinta snn ya mike ya kashe wutan dakin ya koma inda yake ya kwanta. Da asuba a gefensa ya ganta, ya mike zaune bayan ya karanto addu'ar tashi a bacci, ya kusa minti biyar xaune kafin ya mike ya shiga bayi don yin alwala ya wuce masallaci. Ko da ya dawo daga masallaci bata tashi ba, ya cire bargon jikinta ya ja hancinta, mikewa xaune tayi ya wara mata ido yace "Come and start going kar mumy ta dawo" kallon agogo tayi da sauri ta xaro ido, sai kuma ta mike tsaye ta cire kimonon jikinta ya rage daga ita sai half nighty ta shiga bayi, wanke fuskarta tayi ta wanke bakinta da freshener snn ta fito, xaune ta gansa kan darduma da Al-quran a gabansa, dago kai yayi yana kallonta ta karaso ta duka d'an nesa da shi tace "Good morning" ya wara mata manyan idonsa yace "Good morning Baby, kin tashi lafiya" xaro ido tayi tace "Ni kuma?" mikewa tayi tana murmushi ta dau kimononta ta saka ta tattara books dinta tace "Xan tafi" yace "Toh bari in raka ki" da sauri tace "No thank you" daga haka ta d'aga masa hannu ta nufi kofa ya bi ta da ido har ta fita. Karfe hudu da kusan rabi Abuturrab ya dawo daga gun aiki, wanka yayi ya shirya cikin kananun kaya ya fito, kallo daya yayi ma abincinsa da ke ajiye parlor ya fita, main house ya nufa, ya tadda Mami xaune parlor mai aiki na yi mata gyaran gashi, ya xauna ya gaisheta ta amsa tace "Har ka dawo?" Ya jinginar da kansa jikin kujera yace "Na dawo Mami" tace "Toh ka ci abinci?" Girgixa mata kai yayi yace "Ban ci ba tukun" tace "an kai maka can ai" yace "Na gani!" Mikewa yayi ya wuce sama. Yana dakinsu Ramla ta shigo, ta karaso tana kallonsa ganin ba yanda ta saba ganinsa ba ta xauna gefensa tace "What's wrong with you Aliyu?" Kallonta yayi yace "Nothing Mami" tace "ko dai kana son dawowa nan ne?" Murmushi yayi yace "Not at all" ta tabe baki tace "Toh kai ka sani" Shafa kansa yayi yace "Mami a kan maganan da Yakumbo ta min ranan" shiru tayi tana kallonsa sai kuma tace "Toh ya aka yi" ya langwabar da kai yace "I don't know what to do mum" ta tabe baki tace "yanxu duk yan matan da kake bani mu gaisa a waya ina suke?" Dariya yayi yace "Ohhh Mami na fa ce maki they are my frnds!" Tace "Toh, kana son in maka zabi?" Kallonta yayi da sauri yace "No Mami ni fa ina da warce nake so" tace "Toh kuma shine xa ka taho nan kana damuna" ya marairaice yace "Shawara fa na xo nema Mami" Mami tace "Toh ina jin ka, yar ina ce?" Shiru yayi yana kallonta, tace "Kayi shiru!" Xai yi magana aka bude kofar dakin, Khaleesat da Ilham suka shigo da alamar daga boko suke, mikewa yayi yace "Xa muyi magana anjima Mami" bin sa da kallo tayi, Su ilham suka gaishesa a tare, bai ko kallesu ba ya fice, khaleesat ta tabe baki, Ilham tace "Mami kin ga ya daina amsa gaisuwar mu koh?" Mami tace "ku kuka san me ya hada ku da shi ba ruwana" juyawa khaleesat tayi ta fice ilham ta bi bayanta, suna shiga dakinsu Ilham tace "You know what leesat, mu je mu basa hakuri, he's ignoring us" kamar xata yi kuka ta kare maganar, khaleesat na kokarin cire kayan jikinta tace "Am going no where" Ilham tace "Why?" Wani kallo Khaleesat tayi mata tace "Don ma ba mu gaya ma Mami abinda muka gani ba" ilham tayi shiru tana kallonta. Abuturrab na xaune parlornsa yana kallo a laptop misalin shidda da yan mintuna yaji an bude gate, kallon kofa yayi da sauri, aka turo kofar a hankali ta shigo rike da basket dauke da abinci, sosai abayar jikinta yayi mata kyau, ta karaso parlon ba tare da ta bari sun hada ido ba ganin kallon da yake mata, d'an nesa da shi ta xauna tace "Good evening, i brought you food" wara ido yayi ya mike tana ganin haka ita ma ta mike da sauri tayi hanyar kofa, suka ji an kwankwasa kofar, still tayi tana kallon kofar, kawai gani yayi ta juya da sauri tayi hanyar bedroom, aka bude kofar, ilham ce ta shigo ta tsaya daga bakin kofa tana kallonsa kamar xata yi kuka tace "Ya Abu ni dai kayi hakuri....." Ya hade rai yace "Me ya faru da xan yi hakuri, fitan min a parlor" tace "Plsss am sorry sweet bro" xai yi magana ta karaso ta rungumesa tace "Yayana plss mana" shiru yayi bai ce komai ba, a hankali tace "Kaji" janyeta yyi jikinsa yace "Toh tafi daki ki ba ta hakuri right away" dago kai tayi ta kallesa, sai kuma ta kalli hanyar dakin snn ta tafi, tsaye ta ganta ta juya baya, da sauri ta juyo tana kallon Ilham, Ilham ta karasa kusa da ita tana turo baki tace "Kiyi hakuri, we are sorry for everything...." Shiru samantha tayi tana kallonta ko kiftawa bbu.

*Haske writers asso*📚✍🏻
💫 *Noorul Huda*💫
19.....😍😍
Ilham ta juya ta fita xuwa parlor tana kallonsa tace "Ya Abuu na bata hakurin" yace "And promise you two will be frnds daga yanxu" ta langwabar da kai tace "that's a promise, we re frnds now" yace "Good!" Murmushi tayi tace "Bye xamu tafi islamiyya" daga haka ta juya ta fita, bedroom ya shiga ya sameta tsaye har lkcn, ya rungume hannayensa yana kallonta, sunkuyar da kai tayi xata fita ya jawo ta yace "Ina xa ki?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Gida xan koma" kallonta yayi daga sama har kasa murya can ciki yace "I love ur dressing...." Kwace kanta tayi ta fita da sauri, ya bi ta da ido, sai da ya ji fitar ta sannan ya fito parlor ya xauna ya bude abincin da ta kawo masa, pounded yam ya gani da vegetable soup yayi murmushi ya rufe warmer din hade da lumshe ido. Bayan kwana biyu yana xaune gaban gate da yamma yana danna waya sai dai da biyu yake xaune gun don for the past 3 dayz bai ga Samantha ba, duk ya koma kamar mara lafiya sai dai har kusan magrib bbu alamar ta. Washegari friday yana xaune office yana danne dannen laptop, tun xuwan sa hospital bbu patient din da yayi attending ma, aka kwankwasa kofarsa ya bada izinin shigowa wata nurse ta shigo rike da file ta ajiye gabansa tace "Xaka duba patient sir" yace "Ohk" ba tare da ya dago ba, ta juya ta fita ba a dau lkci ba ta dawo tare da wani mutumi da baxai wuce shekaru arba'in da bakwai ba, fari ne dogo da ganinsa ka ga bafulatani sbda kyansa, kallon mutumin Abuturrab yake har ya karaso ya xauna, suka gaisa Abuturrab ya bude file dinsa ya duba sunansa ya ga Mr David, kallonsa ya kuma yi sannan ya fara masa tambayoyi yana rubuce rubuce a white sheet dake cikin file din, sai da ya gama yayi gwaje gwajensa sannan ya koma ya zauna yace "Sir kana bukatan hutu sosai sbda bp dinka...." Mutumin yace "Toh xa a kiyaye, magunguna kawai nake so doctor" Abuturrab yayi murmushi yace "Da dai ka bari a hada da allura...." mutumin yace "No xan yi tafiya ne in 3 dayz" Abuturrab yace "Why not ka bari sai ka gama karban medication dinka, u need rest sir" mutumin ya girgixa kai yace "Tafiyar is urgent" Abutuurab yace "Ohk ba Abuja kake ba?" Mutumin yace "Nan nake" Abuturrab na son tambayarsa anguwar da yake amma ya rasa ta ya, bell ya danna don alerting din nurse, Mutumin yace "yanxun ma don family doc dina bai garin ne shi yasa na taho asibiti" Abuturrab ya dake yace "Ohk, wani anguwar kake?" Mutumin ya kallesa ya fada masa, Abuturrab yace "Ohk, nima anguwar nake kuwa, if you don't mind idan na dawo ltr sai in karasa in baka injections din, xan ma iya dinga xuwa can gidan ina baka medication din har ya kare, but that is if you are okay by that" mutumin yace "Alryt, am greatful Dr, ga digit dina sai ka kira ni" karban complimentary card dinsa yayi, ya kalli nurse din dake tsaye ya mika mata file din yace "Drugs only" daga haka Mr David ya mike yayi masa godiya ya fita, Abuturrab ya lumshe ido hade da murmushi murya can kasa yace "Samha's father!"
Abuturrab na dawowa daga mosque da magrib ya dau mota ya tafi pharmacy ya siya drugs da allurai, ya jima xaune a motarsa bayan yayi parking a kofar gidansu Samantha, can ya dau wayarsa ya ciro complimentary card din da Mr David ya basa ya kwashe numbers din yayi dialing, sai da ya kusa katsewa ya dauka, mancewa Abuturrab yayi yace "Assalamu alaikum" daga daya bangaren Mr David yace "Yes, who's on the line?" Abuturrab ya ce "Ohh sorry, it's Doctor Aliyu... You remember?" Mr david yayi shiru, can yace "Ohh Doctor how you?" Abutturab yace "Am fine, am at ur premises, at the gate" Mr David yace "Ohk, you can come in...." Abuturrab yace "Alryt!" Daga haka ya katse wayar ya bude motar ya fito ya nufi gate ya bude ya shiga, gaisawa suka yi da mai gadi, mai gadin ya tambayesa wanda yake nema yace mai gidan ya kuma sanar da shi he's a doctor, har kofar da xai sada shi da main parlor din gidan mai gadin ya kai sa, mai aikin gidan ce ta bude kofar, ta gaida Abuturrab ya amsa ya shiga parlon yace "Ki yi ma mai gidan magana, you tell him his doctor is around" sama ta nufa ta bar sa nn tsaye yana kare ma makeken parlon da ya tsaru da kayan alatu, ba a dau lkci ba ta dawo tace "Yace ka tafi dakinsa" yace "ohk" kitchen ta wuce shi kuma ya wuce sama da sauri ya juyo tunawa da yayi bai san bedroom din ba ya ga har ta shige kitchen, kamar me tsoron staircases din haka ya dinga taka su har ya isa sama ya tsaya yana bin corridor din rooms din da kallo, bude wani kofa aka yi samantha ta fito sanye da mini skirt fari sai vest hannunta rike da system, still tayi inda take tana kallonsa da mamaki kuma a tsorace, ya wara mata manyan idanuwansa yana murmushin sa mai kyau yace "Sweetheart!" Bude kofa aka yi Dad dinta ya fito, da sauri ta juya ta koma cikin daki, Abuturrab yace "Good evening sir" Murmushi dauke fuskarsa yace "Welcome Doctor, shigo" bin bayansa Abuturrab yayi suka shiga dakinsa, bbu 6ata lkci cikin minti sha biyar Abuturrab yayi abinda ya kawo sa, Mr David ya dauko dubu ashirin a take ya basa, yana shafa kai yace "No sir, sae na gama treatment din" Mr David yace "Alryt, na gode kwarai, a ina kake a nan anguwar?" Abuturrab yace "Just few houses away bbu nisa" hannu Mr David ya basa ya kuma yi masa godiya yace "Yaushe xa ka xo gobe don xan fita" Abuturrab yace "May be da yamma idan na dawo daga gun aiki" Mr David yace "Alryt, xaka taho ma Daughter na da Malaria drugs" Abuturrab yace "How old is she? Tayi test ne?" Girgixa kai yayi yace "No, ba ayi test ba, but i guess it's malaria, she's 19...." Abuturrab yace "Ohk, tana kusa ne?" Mr David yace "Yes, bari in kirata" daga haka ya fita, bayan yan mintuna ya dawo dakin, bai jima da shigowa ba Samantha ta shigo, wannan karan sanye take da doguwar riga, bata bari sun hada ido da Abuturrab dake ta kallonta ba, Mr David yace "Gata" Abuturrab yace "Sannu...." Satan kallonsa tayi tace "Ina yini" yace "Lafiya, how are you feeling, i mean ina ke maki ciwo?" Ba tare da ta kallesa ba still tana fidgeting fingers dinta tace "Ciwon kai!" Yace "Just ciwon kai?" Shiru tayi sai kuma tace "Ina amai kuma" yace "Amma kina cin abinci?" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa suka yi ido hudu, kasa daina kallonta yayi ganin yanda ta rame, ta sunkuyar da kanta da sauri, shima ya dauke kai yace "Me yasa ba ku je asibiti ba sir?" Mr David yace "Ta ki yarda babu yanda uwarta bata yi su je ba ta ki" Abuturrab yace "Ohk xan kawo mata magani gobe, but still ya kamata ayi test" Mr David yace "Alryt thank you doctor ko gobe sai ayi test din...." Sallama Abuturrab yayi masa ya ya kuma kallonta ita ma kallonsa take ya nufi kofa ya fita, Blessing na parlor har ya kai kofar fita ya juyo ya ciro biro aljihinsa da takarda yayi rubutu ya ciro kudi ya hada snn ya karasa kusa da ita yace "Hello, plss ki ba Samantha, plss" kallonsa tayi ta kalli kudin sannan ta karba tace "Toh xan bata" fita yayi yana tunanin anya hakan da yayi ya kamata don bai ma san halin yarinyar ba, yana isa gida ya xauna parlor ya jinginar da kai jikin kujera ya lumshe ido. Samantha na xaune daki tayi shiru tana tunanin yanda Abbanta yasan Abuturrab blessing ta shigo tace "Sister Rebecca, the doctor gave me this to give you, ya hada har da kudi ya ban" da sauri Samantha ta karba tace "Ohk ohk, don't say anything about it blessing" kudin ta mika mata Samantha tace "A'a tafi da shi" tana fita Samantha ta bude takardar ta karanta content din "Plss plss ki xo gida yanxu am waiting, don't ignore dear"
*Haske writers asso*📚✍🏻
💫 *Noorul Huda*💫

20.....

Ta koma ta kwanta a hankali, can kuma ta mike xaune tayi tagumi, to ko taje ne, tunanin da take kenan, kawai ta mike ta kashe wutan dakinta ta bude kofa a hankali ta fita, blessing na parlor ta karasa kusa da ita tace "Blessing idan Abba ya kirani kice masa nayi bacci" Blessing tace "Toh" kamar munafuka ta fita gidan ta dau hanyar gidansu Abuturrab, a hankali ta tura gate ta shiga ta karasa balcony ta bude kofar parlor ta shiga, mikewa yayi yana kallonta ya nufeta yayi murmushi yace "Thanks dear!" Ta langwabar da kai tace "What's the call about?" Hannu ya sa a goshinta yaji xafi yace "Tun yaushe ne baki da lafiya?" A hankali tace "Since" ya kamo hannunta da damuwa yace "And you didn't tell me, wani maganin kike sha?" Janye hannunta tayi tace "How did you know my dad?" Murmushi yayi yace "Kin raina kitaba ta ne?" Bata ce komai ba, ya kama hannunta ya xaunar da ita kan kujera yace am coming, bin sa tayi da kallo ya shiga daki, can ya fito rike da stethoscope da thermometer, ya dawo kusa da ita ya xauna yana kallon kirjinta murya can kasa yace "how will i get to ur chest?" Ta masa wani kallo tace "What?" Murmushi yayi yace "Yeah, i want to use my stethoscope on u!" Tace "Toh bana so!" Wani kallo ya mata ya jawo ta kusa da shi ta xaro ido xata yi magana taji hannunsa a bayanta, a hankali ya xuge xip din ya sauke doguwar rigar kasa ya rage farin vest din jikinta, wani kallo take masa xata yi magana ya daura fingers dinsa guda biyu a lips dinta yana kallon cikin oily eyes dinta, daukar stethoscope din yayi ya makala a kunne, snn ya daga vest din a hankali ya manna daga kasan kirjinta, lumshe ido tayi, shi ko sai kallonta yake, can ya lumshe nasa idon ya cire instrument din ya ajiye ya sauke vest din, ya mayar mata da rigarta ya ja zip ya mike, sai a snn ta bude ido taga daki ya wuce, ba a dau lkci ba ya dawo da magunguna har da allura, tana ganin haka tace "Baxan karba allura ba" bai tanka taba ya xauna ya gama hada alluran snn yace "Kin shirya" bai jira tace komai ba ya mike yana kallonta yace "Am waiting" kamar xata yi kuka tace "Ni bana so nace" hade rai yayi ya dago ta, bata ankara ba sai ji tayi yana kkrin daga mata riga tace "Noooo" ya wani daure fuska yace "What?" Kamar xata yi kuka tace "Doctor there's nothing inside, just..." Dariya ta basa ya dake yace "Then???" Bata ce komai ba ta marairaice tana kallonsa, yace "Ohk Alryt!" Kama hannunta yayi ya isa gun switch din wutan ya kashe, duhu ya gauraye parlon, ya daga rigar gaba daya tace "Doctorrrr..." Dafa bango tayi ta runtse ido jikinta na rawa, har ta ji ya xare alluran, bata ankara ba taji ya rungumeta ta baya ya daura kansa a shoulder dinta murya can kasa "Get well soon wife" bude ido tayi da sauri, ya juyo da ita yana kallonta cikin duhun yace "Ki bar wahalar da ni Samha, stop pretending you don't know where i am heading, i know you know....." Rungumeta yayi cikin sanyin murya yace "I love you!" Ita dai bata iya tace komai ba, ya matse ta jikinsa yace "Kice abu mana dear, talk plsss" kamar mara lafiya yayi maganan, ta lumshe ido a hankali tana jin yanda xuciyarsa ke bugawa, harde hannunta yayi da na shi murya can kasa yace "Talk plss, say something Samha" ta rasa abinda xata ce, shafa bayanta ya fara yi a hankali ya kai bakinsa wuyanta, ta bude ido da sauri jin saukan numfashinsa a jikinta, lkci daya jikinta ya dau rawa da kyar tace "Doctor stop pls...." Cikin kasalalliyar murya yace "Talk! second love" Ta kuma runtse ido jin ya ki dauke lips dinsa a wuyanta, murya can kasa tace "I... I... I... Love you tooo" wara ido yayi ya saketa yace "Da gaske baby??" Ja baya ta dinga yi kawai sai gani yyi ta juya a guje ta nufi kofa ta bude ta fice. Washegari asabar da yamma Abuturrab ya iso gidan Mr David da da magungunan da xai ba Samantha jiya ta gudu, Mumy ya tarar xaune parlor tare da Mr David din bayan an masa izinin shigowa ya gaisheta ta dinga masa wani kallon mamaki, Mr David ya mike yace "Likitan da nake fadi maki kenan" daga haka yace ma Abuturrab ya taho sama, Abuturab ya bi bayansa suka wuce saman, yau ma bbu wani 6ata lkci ya gama basa medication din, ya tambayi samantha, Mr David yace ta tafi church, shiru Abuturrab yyi sai kuma yace "But da ta hakura har ta samu sauki" mika masa magungunanta yayi, yayi masa sallama ya fita, Sai da ya isa kofar fita sannan ya juya ya kalli Mahaifiyar Samantha ya ga kallonsa take yi, yace "Sae da safe Ma!" Wani kallo tayi masa ta mike fuu ta wuce sama, yayi murmushi ya fita, a bakin gate ya hadu da samantha, tana ganinsa ta koma baya da sauri, motarsa ya nufa ya tsaya ya rungume hannayensa yana kallonta har xata shiga gate sai kuma ta tsaya ta d'an saci kallonsa taga idonsa na kanta, kamar mai counting step ta nufi inda yake ta tsaya nesa da shi, tace "Good evening!" Yace "Da wucewa xa kiyi?" Kallonsa tayi suka hada ido tayi murmushi ta girgixa kai, ya lumshe ido yace "Come here" tace "Ba gani ba?" Ya harareta ya nuna mata gabansa, kamar xata yi kuka tace "Kaga daga church fa nake, am tired! Am feeling dizzy" Yace "To tafi...." Shiru tayi tana kallonsa, can ta karaso gabansa a hankali tace "Gani" dago kanta yayi yana kallon kwayar idonta yace "Me yasa kika fita baki da lafiya?" Ta sauke idonta tace "I went to church, Mumy tace in je" Wani kallo yayi mata yace "To daga yau kar ki sake xuwa har sai kin samu lafiya...." Ta xaro ido, ya gyada kai yace "yes I mean it...." Tace "to ae addu'a ake min a can ma" ya tabe baki yace "Good sai kiyi ta xuwa...." Kallonsa ta tsaya yi, ya juya ya bude motarsa ya shiga ya tada, ta lumshe ido ta bude tace "Ohk ohk, baxan je ba kuma" hararanta yayi, tayi kamar xata yi kuka tace "I mean it baxan je ba...." Yace "Better! Taho ki ji" karasawa tayi kusa da glass din motar tace "Mene?" Yace "Matso mana" matsowa tayi, dai dai kunnenta yace "Drugs dinki da prescription na gun Abba, you make sure you take all before going to bed, since you ran away yesterday....." Bata jira ya karasa ba ta juya da sauri don gaba daya ta mance da incident din jiya, ya rikota da sauri ya jawota yayi planting mata kiss a cute lips dinta, ta kwace kanta da gudu ta shiga gida. Ranan litinin Samantha ta kare exams dinta na Waec, karfe uku driver ya je dauko ta a sch, kamar ko da yaushe a bakin layi ya ajiyeta ta karasa wai xai je kasuwa Mumy ta aikesa, tana isa dai dai gidansu Abuturrab ta ga motarsa a waje, ta tsaya tana kallon gate din ko me ta tuna kuma ta

Please Login or Register in order to submit comment