Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai munje gidan Ummi zan tsaya”.
Cikin sauri M Jameel ya juyo gareshi tare da ɗan ware idonsa yace.
“Kama san ana binmu kuma shine ka ƙi tsayawa? Idan kuma wanda zasu cutar da mune fa A.J?”.
Kai Moddibo ya girgiza yana mai cigaba da tuƙinsa tare da buɗe lips inshi a sanyaye yace.
“Ai nasan wanda ke binmu fa Alhaji Bashir ne”.
Da sauri M Jameel yace. “Waye Alh Bashir?”.
Ɗan juyow Moddibo yayi tare da ɗan kallonshi kafin yace.
“Babban yaron Malam Arɗo ne”.
Cikin sauƙe Numfashi M Jameel yace.
“Ok to Meyesa ba zaka tsaya ba?”.
Ba tare da ya juyo ba yace.
“Nasan magana ce mai yawa yazo dashi, koda na tsaya ma, ba zamu gama ba kuma kaga agefen titi muke baya ga hakama na masa signal ya fahimta”.
Kai M Jameel ya gyaɗa tare da faɗin.
“Ok shikenan”.
Daga nan sukaci gaba da tafi.

Suna isa ƙofar gidan Ummi M Jameel ya buɗe ƙofa ya fita dai-dai lokacin da Alh Bashir ya ƙara so fuskarsa ɗauke da murmushi ya miƙa wa Alh Bashir hannu sukayi musabaha cikin sakin fuska Alh Bashir yace.
“M Jameel Ko?”.
Kai M Jameel ya gyaɗa mishi tare da cewa.
“Ya gida ya iyalai ya kuma Baba Arɗo?”.
Cikkn sakin fuska Alhj Bashi yace.
“Duk Suna lafiya”.
Murfin motar M Jameel ya buɗewa Alh Bashir tare da cewa.
“Bismillah kashiga”,

Sannan ya zagaya gefen da moddibo yake wanda har zuwa lokacin bai fito ba yace.
"Bari nashiga ciki sai ka shigo”.
Kai Moddibo ya gyaɗa cikin yanayin sanyin magarsa yace.
“Nima Ina Shigowa yanzu”.
“To sai ka shigo”.
Ya fadi tare da juyawa ya nufi cikin gida yashiga bakinsa ɗauke da sallama.
Ba lefi madedecin gida ne mai kyau daga farkon gidan ze iya ɗaukan motoci biyu se tank na ruwa dake can gefe tsakar gidan shimfiɗe yake da interlock sai babban sashe guda ɗaya cikin gidan zagaye yake da fulawa wi masu kyau wanda keda alaƙa da Moddibo dan duk inda yake da dama sai ya ƙawatasa da fulawowi, sabida suna samishi farin ciki.
Tsarin ginin yayi matuƙar kyau duk da cewa ba babba bane amma komai fess dashi haka zalika madedecin falon nasu da befiye girma ba yayi matuƙar kyau falon na ɗauke da manyan setin kujeru kalar ash da baƙi cai Centre table dake tsakiya da kuma ƙaton TV dake maƙale abango daga gabar da TV akwai ƙaton fanka bayan AC dake maƙale da bango daga yamma da TV zagaye yake da wasu flowes masu kyau da ɗaukar hankali sai tattausan carpet mai ɗan kare kyau dake malale a tsakiyar falon...

Cike da so kulawa ƙauna irin ta uwa Ummi ta kalli Jameel dake shigowa tare da sakar masa da murmushin da bata san ya subce mata ba,
bayan ta amsa sallama.

Cike da farin ciki Asma'u ta miƙe tare da gyara wuyan abaya ɗan baby himar dake zage da fuskarta da ɗauke da murmushi cike da jin daɗi ta rungume M Jameel da faɗin.
“Oyoyo Yaya Jameel na Ina yini”.
Kanta ya shafa cike da son yar uwar tasa yace.
“Lafiya lau my blood ya karatu?”.
Cikin murmushin ta amsa da.
“Alhamdulillah”.
kana ta zauna daga ƙasa kusa da ƙafafunsa,
Ummu kuwa miƙewa tayi tana ɗan leƙan bayansa.
Murmushi M Jameel yayi domin ya fahimci Moddibo take leƙawa ganin basu shigo tare ba.
Cikin yanayin fara'arsa yace.
“Kai Ummina ki bari mugaisa kafin ki tambayi 'yan biyun nawa??”.
Ka ta girgiza tare da cewa.
“A'a gwara in tambaya naji, domin shi yace na muku dambun couscous shiya keso kaga kuwa ai bazan ji daɗi ba in ban ganshi ba”.
Murmushi M Jameel yayi yana mai jin daɗin yadda mahaifiyarsa ke nunawa amininsa ƙauna tamkar ita ta haifeshi, yana murmushi jin dadi yace.
“To yana mota”.
Da sauri ta sake dubansa tare da cewa.
“To me yakeyi amota da bai shigo ba?”.
Ashagwaɓe yace.
“To Ummina mu gaisa mana”.
Dawowa tayi ta zauna bisa kujera 2 str,
shi kuwa M Jameel zamewa ƙasa yayi zauna daɓas bisa carpet kana ya ɗaura kansa acinyarta murya a sanyaye yace.
“Ummina daga shigowa ko gaisawa ba muyiba sannan baki samin albarka ba kika tsareni da tambayar Moddibo”.
Hannunta ta ɗauka bisa tsakiyar kasan tare da shafa kansa tana mai cewa.
“Ubangiji Allah ya Albarkanci rayuwarku! Allah ya dafa muku acikin dukkan lamuranku!!
Ubangiji ya tsareku daga sharrin abinƙi tsakanin mutum da aljan!!!
Allah ya baku 'ya'ya masu biyayya tamkar yadda kuke mana kaida Amininka”.
Cike da tsananin jin dadi da sassayan salama yace.
“Ameen thumma Ameen Yah Ummi”.
Hannunta ta ɗan janye daga kansa tare da sake tambayar sa.
“Ina Moddibo?”.
Ƴar dariya mai sauti yayi tare da miƙewa ya zauna akusa da ita kasancewa kujeran 2sitter ne.
gyara zamansa yayi yana fuskantar ta yace.
“Moddibo zai shigo amma ba yanzu ba”.
Da sauri tace.
“Meyasa?”.
Cikin saurin shima yace.
“Bari dai in miki bayani hankalinki ya kwanta.
Muna tahowa ne Alh Bashir babban yaron Malam Arɗo ya biyo mu to suna mota suna tattaunawa.
Nasan bazai wuce ƙorafi ya kawo akan mahaifinsu ba”.
Tsaresa da ido Ummi tayi kana tace.
“ƙorafi akan Babansu kuma?”.
Kai ya jinjina tare da cewa.
"Eh Ummi saboda Malam Arɗo wani irin mutum ne wanda zamuce mai dukiyar lukudi gashi dai Allah ya bashi dukiya na ban mamaki amma babu wanda ya isa yaci wannan kuɗin kamar abin masifa”.
Gyara zama Ummin tayi tare da cewa.
“Ikon Allah to sabi da me?”.
Numfashin M Jameel ya ɗan fesar tare da cewa.
“Tun bayan rasuwar mahaifinsa abubuwan suka ƙazanta.
Domin baya sauraron shawarar kowa koda kuwa ƙannensa ne domin shine babba acikinsu dan haka babu mai tanƙwarashi.
To fa saidai Allah ya ɗaura masa son Moddibo a zuciyarsa duk abinda Moddibo yace ko kuma ya kawo shawara akai to zaiyi koda kuwa ransa baya so.
Duk da wani lokaci zakiji yana yiwa Moddibon ma faɗa akan cewa zaisa shi kashe kuɗi amma koda ya gama surutun daga baya zakiga yayi abin da ya fadan.”
Gyara zama M Jameel yayu tare daci gaba da cewa.
“To fa wannan dalilin ne yasa muddin 'ya'yansa suna buƙatar wani abu saidai su biyo ta hannunsa Moddibo”.

Ka saƙe Ummi tayi tana kallon Jameel din kana cikin sanyin murya tace.
“To kada fa hakan yasa yayi baƙin jini awajen 'ya'yansa kasan ɗan adam”.
Dariya M Jameel yayi kana yace.
“Ummi me Moddibo zai buƙata awajen Malam Arɗo me zeyi da dukiyarsu? Mutumin da baiwa yayansa Bama me zai bawa Moddibo wanda baida shi".
Kai Ummi ta gyaɗa tare fesar da numfashi a sanyaye tace.
“Hakane kam al'amarin Moddibo da Innayi akwai al'ajabi, domin ko nasan baza su taɓa buƙatar wani abu awajensa ba, duk da kuwa anayi musu kallon basu da wani cikekken jigo acikin rayuwarsu.
Amma kuma yanda suke tafiyar da rayuwarsu cikin tsari da hikima da wadata yana bani makaki”.
Kai M Jameel ya gyaɗa tare da cewa.
“Kinga Koda motar da Malam Arɗo ke hawa tsohuwa ce aƙalla zata kai shekaru ashirin da biyar ko ashirin da takwas amma har zuwa yau ya kasa can zawa, anyi-anyi dashi yaƙi duk yanda akayi dashi ya sauya wata yaƙi kuma kullum ciki bashi ciwon kai takeyi.
har kyautar Mota ɗansa Alh Bashir ya bashi amma yaƙi amsa domin atunaninsa daga baya zai fanshe kuɗin sa.
Ko gidansa da kike gani yanzu ga gini dai yayi mai kyau amma ɗakunan matansa kamar zauren haka suke babu kujeru bare wani abu shi Tv.
Yanzu haka kwanan ake gyaran makarantarsa wanda da taimakon Moddibo akeyinsa kuma adalilinsa ne yake biyan Malamai albashi mai tsoka inba haka ba baki ɗaya makarantar ta koɗe sannan babu albashin kirki saboda Moddibo yanzu aka rushe makarantar ake gyarawa yanzu hutun da aka kara ma gani yake kamar za'a yi masa asara shiryasa yace adawo ko ba'a gama gininba to bayan an dawo yanzu dole aka sake komawa hutu saboda ba'a gama gyaranba yanzu ma cewa yayi dole kada a wuce wata ɗaya da ƙyar Moddibo ya lallaɓasa aka tafi hutun kafin adawo angama gini da kuma tsare tsare sa duk ya buwaye mu da cewa Moddibo na sashi kashe kudinsa”.

Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da cewa.
“Masha Allah shiko wannan wani irin mutum ne?”.
Murmushi M Jameel yayi tare da cewa.
“Ummi haka 'ya'yansa ke fama dashi, kin san ku fulani”.
Murmushi Ummi tayi tare dayi masa daƙuwa.

Aɓangaren Moddibo kuwa.
Zaune suke da Alh Bashir bayan sun gama gaisawa shiru na wasu daƙiƙu ya wanzu atsakaninsu kafin.
Cikin kulawa Moddibo ya ɗan juyo ya kalli Alh Bashir cikin kulawa yace.
“Alh ya akayi?”.
Numfashin mai nauyi Alh Bashir ya sauƙe kana a hankali yace.
“Mitsss Moddibo Agaskiya al'amarin Babanmu yana matuƙar ɗaure mana kai?”.
Lumshe idanunsa yayi kafin yace.
“Meya faru!?”.
Kai ya girgiza cikin yanayin damuwa yace.
“Modobbo wallahi Mahaifiyata bata da lafiya, ance sai anfitar da ita waje, gashi duk cikin mu babu wanda yake da halin biya afita da itan.
Kasan halin Babanmu kuma, duk iyakar iyawata yaƙi amincewa.
Ni kuma bani dashi”.
Cikin sanyi Moddibo yace.
“Alh baka dashi kuma”.
Kwaffa Alh Bashir yayi tare da cewa.
“Wallahi Allah Moddibo wasu lokuta idan akace min Alh Bashir ba ƙaramin ɓaci raina yake ba domin bafa mahaifina ne yabiya min Makka ba.
Sannan ba nine na biyawa kaina ba dukiyata bace yasa naje ba.
Dalilin Surukina naje wato mahaifin Matata fa ya biya min na samu naje duk wani abu da nake buƙata sai dai Inje wajensa wanda kuma hakan da kunya da kuma zubar da girma.
amma mahaifina Allah ya hore masa fiye dana surkina amman bazai taimaka manaba ayanzu ga jinyar mahaifiyarmu dole sai anfitar da ita waje an mata dashen ƙoda.
shi kansa yana ɓuƙatar canjin mota lokuta da dama yana tafiya Atsakiyar titi zakaga ta lalace, idan shi baya damuwa da zaginsa da akeyi a gari da rayuwarsa to mu muna buƙatarsa ba mason wani abu ya sameshi kuma bama jin dadin habaice-habaicen da akeyi mana.
Shiyasa nazo wajen ka.
Dan Allah da Manzonsa kayi masa magana ya kai mahaifiyarmu asibiti. Sannan ya canza motarsa bayan wannan akwai kannen mu mata da suka gama secondary akwai buƙatar su tafi jami'a amma yaƙi sasu domin aganinsa za'a cajesa kuɗi masu yawo dan Allah katemaka kayi masa magana akan waɗan nan abuvuwan”.
Ya dire ayar mgnar da haɗe tafin hannunsa alamun roƙo da neman al'farma.
Moddibo kuwa ajiyar zuciya ya sauƙe tare da buɗe idanunsa dake lumshe kana a hankali yace.
"Insha Allah zanyi masa magana, amma ayanzu da ƙyar zai amince domin da mun zauna zance ɗaya yake nanata min wai na sashi kashe kuɗi amakaranta wai zan talautashi”.
Murmushi mai ciwo Alh Bashir yayi tare da cewa.
“Muma ko agida haka muke shan complain Koda kudin cefene da sauran abubuwa aka tambayesa zaice Ni bani da kudi wannan yaron Moddibo duk yasa na kashe kuɗaɗenna aginin makaranta”.
Murmushin gefen baki Moddibo yayi wanda ke ƙara fitar da ainihin kyawunsa cikin sanyi yace.
“Uhufm Malam Arɗo kenan.
Ba matsala Insha Allah zanyi magana dashi duk yadda mukayi dashi zakaji”.
Ya kare mgnar yana shafa tattausan sajensa.

Godiya Alh Bashir ya masa sannan su kayi sallama Moddibo yashiga cikin gida.

Shi kuma ya juya ya tafi.

Tattausan murmushi Ummi tayi ganin Moddibo cikin kulawa tace.
“Babana na kaina sannu da zuwa”.
Kasancewar sunan mahaifinta garesa.
Cike da ladabi ya zauna yana cewa.
“Ummi fatan mun same ku lafiya ya yara?”.
Da murmushi afuskarta tace.
“Duk muna lafiya ya jikin Innayi?”.
“Alhamdulillah Ummi jiki kam da sauƙi sosai ma".
Ya kare mgnar yana mayar da kallonsa ga Asma'u data fito daga Bedroom da alama muryarsa taji ta fito, har ƙasa ta tsugunna tare da cewa.
“Yah Moddibo ina yini”.

“Lafiya Asma'u ya karatu da hadda?”.

“Alhamdulillah”.
Kai Ya jinjina tare da faɗin.
“Meyesa yau bakije hadda ba?”.
Kanta aƙasa tace.
“Yah Moddibo bani da lafiya ne zazzaɓi ke damuna”.
Kallonta yayi na daƙiƙu uku, kana yace.
“Asmau kadafa ki biyewa wannan mashiririciyar ƙawar taki, ki dena harƙa da ita sam banason alaƙarta dake tsakaninku.
Domin yarinyar bata ji kona misƙala zarratin, bana son ganinki tare da ita dan gaba ɗaya sunanta ya zagaye makarantar saboda rashinjinta sam bata da nutsuwar da za'ayi abota da ita.”
Ita dai Asma'u kai take jinjina mishi.
M Jameel kuwa ido ya zuba mishi yayinda Ummu kuwa ke murmushi.
Shi kuwa Moddibo gyara zamansa yayi tare daci gaba da cewa.
“Domin shin abota anaso ayi da na gari, bi ma'ana idan za kayi abota kayi da mutum na gari domin kamar dai misalin:
meyin abota da me saida turarene koda ba azata masa ƙamshi ba to baza azata masa wari ba, sannan misalin: mai abota dame zuga-zugi koda yana da haske to ba za'ayi masa zaton haske ba".
Ɗan kishingiɗan M Jameel yayu tare da lumshe idanunsa.
Shi kuwa Moddibo cikin nitsuwa yaci gaba da cewa.
“Manzon Allah (S.A.W) ya kwaɗaitar damu da yin abota da mutanen ƙwarai domin abokin ƙwarai yana daga cikin wanda Allah yayi alƙawarin zai sasu acikin inuwar alarshinsa ranar tashin ƙiyama, amma kuma duk abotar da ba'agina sa saboda Allah da manzo ba to ƙarshensa nadama ce sam wannan FATTANAH bata dace da zama abokiya a garekiba”.
Itade Asma'u kanta na ƙasa batare data ɗago ba tace.
“Toh Yah Moddibo”.

M Jameel dake kishin giɗe idanunsa lumshe kuwa a hankali ya miƙe tare da buɗe idanunsa akan Moddibo dake cigaba da yiwa Asma'u nasiyya akan tarabu da Khausar cikin tsareshi da ido yace.
“Wai dan Allah A.S meye haka? kana tayiwa Asma'u huɗubar watsar da aminiyarta shin ita Khausar ɗin sheɗan ka ɗauketa ko kuwa dujjal?”.
Ɗago kai Moddibo yayi tare da tsuke fuska yana kallon M Jameel yace.
“Kusan haka domin sam yarinyar bata da ɗabi'un kirki”.
Kai M Jameel ya girgizi kana yace.
“Haba Moddibo yarinyar nan tana fahimtar karatu duk wasu abubuwa da ake koyarwa tana ganewa fiye da duk yan ajinka,
kawai rawan kai da ƙuruciya ke damunta, da zaran ta mallaki hankalinta zata dena, amma ka zauna kana ƙoƙarin cusa ƙiyayyarta azuciyar Aminiyarta sam hakan ba dai-dai bane yoh ba ita cema ke taimakawa ƙanwar taka da kake zugawarba ita me take ganewa ma tana nan kai kamar na kifi”.
Itade Asma'u kanta na ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.

Wani kallo mai cike da manufofi Moddibo yayiwa M Jameel tare da taɓe baki kana yace.
“Ina ruwanka? bansa bakinka ba da Asma'u ƙanwata nake magana”
Kana ya juyo ya kalli Asma'u da har zuwa lokacin kanta ke sunkuye yace.
“Maganata kika ɗauka zakiyi amfani dashi ko nasa?”.
Da sauri tace.
“Naka Yah Moddibo”.
Murmushi yayi da faɗin.
“Ɗayyit Allah ya miki albarka”.
Ɗago kai M Jameel yayi dai-dai lokacin Asma'u ta ɗago kanta,
ido yakashe mata ita kuma murmushi ta sakar masa.
Ummi dake sauraronsu kuwa sai yanzu tace.
“Yawwa Moddibo ka cigaba da samun Ido akan yaran nan dan yaran saida sa ido”.
Moddibo kuwa ido ya lumshe tare da gyaɗa kai kana yace.
“Insha Allah Ummi na lura J da wannan fitinanniyar yarinyar kusan halinsu ɗaya shima kullum fama nake dashi ya nutsu yaƙi nitsuwa”.
Wara ido M Jameel yayi tare da cewa.
“Nine bani da nutsuwar A.S?”.
duk dariya suka sanya banda Moddibo da yayi murmushi.

Abinci Ummi ta bawa Asma'u umarnin ta kawo musu fita tayi ba daɗewa ta dawo hannunta ɗauke da warmers ta ajiye musu M Jameel ne ya buɗe murmushi Moddibo ya saki yana kallon yanda dambun yayi kyau sai tashin ƙamshi albasa da kuma ƙamshin man shanu.
Ummi da kanta ta zuba musu tare da mimmiƙa musu plate ɗin.

Bismillah sukaui kafin suka fara ci suna kammala ci sukayi wa Ummi sallama sannan suka tafi.

Washe gari. Tun wuri Khausar ta tashi amma taƙi shiryawa da wuri seda kowa ya gama shiri ya rage saura ita kaɗai, dan Allah ya sani ita ta tsani ta gama shiri ta tsaya jiran wasu.
Ahankali take shan comflakes dake hannunta kamar ba jiranta akeyi ba yayin da Raudat ke zaune gefenta, Cikin fushi Amina ta banko labulen ɗakin cikin kumfar baki tace.
“Wallahi Khausar zamu tafi in banda raini da samun waje tuntuni muke jiranki amma kin tsaya feleƙe dan kin san in mun tafi mun barki Abba zaiyi faɗa”.
Anutse ta ɗago manyan Idanunta dake lumshe ta watsawa Amina wani kallo kafin ta taɓe bakinta kamar zata ce wani abu sai kuma ta fasa ta miƙe ta riƙo hannu Raudat suka fita bayan ta gama shanye Comflakes ɗin.
Ajiyar zuciya Amina ta sauƙe cike da takaici tabi bayan Khausar da haramta, duk sanda tazo da niyyan ciwa yarinyar mutunci da zaran sun haɗa ido zata nemi duk wani karsashinta ta rasa koda suka shiga motar Amina bata tanka taba ita da Raudat keta faman surutu har suka isa cikin sa'a Moddibo beshiga ba zamansu ba daɗewa yashigo as usual cikin shigar jallabiya Onion color da yasha guga kansa sanye da hula malam taɓani kaji ruwan hadith yayin da ya naɗe da hirami jikinsa na fitar da ƙamashin daddaɗan tularensa,
cike da ladabi suka shiga gaishesa Amsawa yayi kamar ko yaushe a saman laɓɓan sa.

Taɓe baki Khausar tayi aranta tace.
“Akwi madaran ƙasaita ana mutun kamar sarki”.
Batare daya kallesu ba yace.
“Su kawo hadda wiƙiƙi da ido Amina tashiga yi kasancewar itace afarko kuma bata iya ba ya dubi Samira sani yace ta karanta hadda still itama bata iyaba kallon Abeeda Sa'idu yayi yace ta karanta wacce ƙawar Samira Sani ce da ƙyar ta karanta aya biyar aciki sumunin da zasu karanta koda yazo kan Khausar cikin nutsuwa da ƙwarewa ta karato sumuni ɗaya na farkon Suratul Taubah.
Kanshi ya jinjina tare da juyowa ya kalli Asma'u Ahmad.
Cikin yanayin tsoro ta kawo suminin amman yayi mata gyara biyu.

Da ɓacin rai Moddibo ya fitar da wanda basu karanta ba ya basu punishment.
Khausar kuwa tasa su gaba ta riƙa dariya baƙin ciki ya cika musu zuciya kamar su mutu ahaka Malam Ahmad dake malamin Tajweed ne shima ya zuwa wurin addar.
Har yayi ya gama basu dawo ba seda aka tashi kafin aka ƙyalesu akan punishment ɗin...

Da dare.
Mamy ce tsaye cikin ƙasaitacciyar shiga, tana zuwa wani irin ƙamshin kulaccar sirri da ta saya wurin Aysha Aliyu Garkuwa.
Baki ta ɗan taɓe tana kallon yada Khausar ke shishita sabida uban yajin da ta zambadawa indomei wanda yaji nama da.
Kai kawai ta jijjiga sannan tayi musu sallama ta wuce turakar mijinta.
Tanaci tana kurɓar ruwan sanyi, tana bawa Raudat har suka gama ɗaukar Raudat tayi suka shiga ɗaki kai tsaye toilet suka wuce brush tayi sannan tayiwa Raudat kana suka ɗaura alwala suka fito.
Jikin window Khausar ta nufa da niyyan rufewa Idanunta suka sauka akan Haiydar dake ɗauke da Ramadan zasu shiga sashen Hajiya Bunayya,
fasa rufe window tayi cikin ɗan ɗaga murya tace.
“Haiydar ina zakuje?”. shima cikin ɗaga murya yanda zataji yace.
“inda kika aikemu”.
Cikin takaici ta rumtse idonta kafin tace.
“Wai Haiydar meyesa karai nani ba dama in maka magana, ko in baka umarni saika riƙa bani amsa kai tsaye”.

Bakinshi ya taɓe tare sa fadin.
“Acikin gida ma saiki riƙa tambayar ina zanje! Me zanyi? Me zanci? fisabilillah ni bani da ikon da zanyi abu da kaina koda Mamy bata Matsamin irin yanda kike min gsky na gaji”.
Bai jira jin amsartaba ya wuce yashiga sashen Hajiya Bunayya,
Aseeya yayar Amina na ganinsa ta saki murmushi tace.
“Umma ga babanki yazo”.
Cikin sauri Hajiya Bunayya ta fito hannunta ɗauke da glass cup na madara tana jujjugawa fuskarta da murmushi tace.
“Gashi babana madaran shanu ne mai ɗumi”.
Amsa yayi yana murmushi saboda yanayin sanyin dake garin yace.
“Nagode Umma”.
Jujjuya Glass Cup ɗin yayi kafin ya kai bakinsa da faɗin
"Bismillahi”.

Khausar kuwa jingina bayanta da jikin bango tayi kafin ta ɗaga hannunta sama cikin raunin murya tace.
"(Ya wadud³,Ya zul'arshil makin,ya fa'alillima yurid,As'aluka bi izzatil lati la yura,wa mulki kallazi la yuda)ya Allah katsare min ɗan uwana kada Hajiya Bunayya taci galaba wajen cutar dashi”.
Kafin ta shafa ta kwanta lamo agado....

A can side din kuma cikin mugun sauri Hajiya Bunayya ta riƙe hannunsa domin bokan daya basu maganin ya tabbatar musu da zaran anyi Bismillah laƙanin maganin ya karye,ta anshi Glass Cup ɗin da faɗin.
“Bari mugani kode da zafi ne kada ka ƙone bakinka”.
Kai ya girgizi tare da faɗin.
“Ba zafi Umma”.
miƙa masa ta sake yi amsa yayi ya sake kaiwa bakinsa da faɗin.
“Bismillah”, saurin karɓa ta kuma yi tare da cewa.
“Mugani kode sugar bai jibane”.
Kai ya girgizi yace.
“Kin san ba damu da zaƙiba Umma”.
yaƙe tayi da faɗin.
“bari dai na ƙaro maka sugar”.
Ta faɗa tare da shigewa Bedroom duk aƙoƙarinta na ganin ta mantar dashi Bismillah ba jimawa ta fito ta sake miƙa masa tana jujjuyawa aranta tana addu'ar Allah yasa ya manta da Bismillah. Aseeya kuwa ikon Allah kawai take gani wajen mahaifiyarta ita kuwa Amina tasan komai domin ita ta karɓo maganin wurin boka Karƙuzu.
Karɓan Glass Cup ɗin yayi yakai bakinsa kana yayi Bismillah yasha kallon Ramadan yayi yace.
“Zaka sha?”.
Kai Ramadan ya girgiza alamar a'a...
Hajiya Bunayya kam ji tayi kamar ta haɗiye zuciya ta mutu ganin maganin data kashe maƙudan kuɗi wajen amsarsu aranta tace.
“Shegen yaro mai ta ammalli da addu'a duk uwarsu ta koya musu yin addu'a akan ko wani irin abu afili kuwa murmushi tayi tace.
“Babana sugan yayi?”.
Kai ya gyaɗa mata sannan ya shanye bayan sun sake taɓa hirane ya mata seda safe ya fice...

Washe gari da safe Ummi ta nufi gidansu Moddibo domin duba jikin Innayi bakinta ɗauke da sallama tashiga cikin gidan atsakar gida taci karo da Innayi dake faman gasa nama irin wanda ake yiwa masu jegon.
Cikin sakin fuska Innayi ta mata sannu da zuwa, Murmushi Ummi tayi tare da zama ta gaisheta cike da ladabi tare da tambayarta ya jiki kana ta kama mata aikin suka gama.
Bayan sun gama ne Moddibo da M Jameel suka dawo zama sukayi tare da gaisawa Ashagwaɓe M Jameel ya dubi Ummi yace.
“Ummi bacci nakeji”.
bai jira cewarta ba ya zame ya kwanta tare da ɗaura akansa a cinyarta
Moddibo kuwa Hararansa yayi yace.
“Kaidai ba zaka taɓa girma”.
Tura baki M Jameel yayi amma baice komaiba saboda baccin dake cinsa kwanciyarsa ba jimawa bacci ya ɗaukesa ganin lokaci na tafiya yasa Ummi tace. “Moddibo bani filo ka gani”.
miƙewa yayi ba daɗewa ya fito hannunsa riƙe da pillow Ummi ta karɓa ta ɗaura kan M Jameel akai sannan ta yiwa innayi Sallama.
Moddibo ya tafi mai data bayan sun hau kwalta Moddibo ya dubi Ummi cikin sanyin murya yace.
"Dan Allah Ummi ki riƙa yiwa Asma'u faɗa ta daina ƙawance da wannan yarinyar sam bata da nutsuwa zata ɓata Asma'u da halayyarta na rashin nutsuwa yarinya nada naci in ba da gaske mukayi ba bazamu ci nasara ba da na lura ta shiga ranta koda na yiwa Asma'u magana kan tarabu da ita.
Kuma naga kamar ba zata yiba anma idan ya zamana mu biyune muke mata faɗa zata ɗauka”.
Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
“Insha Allahu zan riƙa yi mata”.
Ahaka suka isa gida ya ajiyeta sannan ya koma...


Washe gari. Ya kama Juma'a misalin ƙarfe uku Khausar na zune kan 2sitter Raudat na gefenta tana yanke mata ƙumba yayin da Mamy ke riƙe da hisnul Muslim tana Azkhar Asma'u tashigo bakinta ɗauke da sallama miƙewa Khausar tayi tare da rungumeta tace.
"Oyoyo Ƙawar arziƙi”, Murmushi Asma'u tayi cikin sigar zolaya tace.
“Fattanah kina son karya ni ko?”.
Saketa Khausar tayi tare da tura ƙaramin bakinta tace.
“Kina so mu ɓata ko?”, Murmushi Asma'u tayi tare da tsugunnawa har ƙasa ta gaisheda Momy cikin sakin fuska Momy ta amsa tana tambayarta Umminta ta bata amsa da.
“Tana lafiya, Momy tace ma in gaidaki”.
Cikin sakin fuska Momy tace.
“Ina amsawa”.
Ita kuwa Asma'u cikin girmamawa tace.
“Ayyah Momy in ba abinda Khausar zatayi miki ta rakani mana Ummi ta aikeni kuma banason zuwa ni kaɗai”.
Sanin Asma'u yarinya ce me tarbiya da nutsuwa uwa uba kamun kai yasa Momy amincewa.
Kai ta gyada mata tare da cewa.
“Toh kada dai ku daɗe ku kuma kula da kanku banda kula maza”.
Cikin jin dadi Asma'u tace.
“In sha Allah kuwa Momy”.
Ita kuwa Khausar murmushi tayi tare da cewa.
“To ni baki nemi izinina ba”.
Ta ƙare mgnar tana
Shiga Bedroom ɗin ta, murmushin Asma'u tayi tare da bin bayanta kana ta langwaɓar da kai tace.
“Ayimin afuwa ƙawar arziƙi”.
Hira suka ɗan fara taɓa sannan Asma'u ke sanarwa mata zata raka unguwar Teku ta kai saƙo Ummi ta aiko cikin zumuɗi da son fita ta miƙe tare da ɗaukan dogon hijab maroon colour tasa akan riga da wondon dake jikinta ba tare data tambayi inda zata jeba tace su tafi dan kawai tana masifar son unguwar Teku...

Aɓangaren Moddibo kuwa bayan ya dawo daga sallar la''asar,
Side ɗinsa ya wuce,
Ruwa ya watsa tare da sauya kayan jikinsa, wani tattausan riga da wondo nevy blue mai taushi ya zira, tare da fesa turarensa oud jannah mai masifar ƙamshi,
System ɗinsa da wayarsa ya ɗauka kana ya fito, a hankali ya lumshe idanunsa jin yadda sassanyar iskar ke ratsa cikin tattausan sumar kansa da yana iya kwana biyu bai cire hulaba.
A hankali yake taka steps din yana sauƙowa ƙasa wani irin masifeffen kyau yayi

1 Comments On SAKAYYAH
avatar
fatima-8-5-3

4 months ago

Reply

Allah ya qara basira

Please Login or Register in order to submit comment