Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fuskarta.
Yayin da Raudat ma ke sanye cikin irin shigar dake jikin Khausar sai dai nata ɗinkin dogon riga ne.
Haiydar kuwa sanye yake cikin wata Bugaggiyar shadda Sky blue anyi masa ɗinkin samarin zamani rigar ta tsaya iya gwiwarsa, kansa sanye da hula yalwataccen sumar irin na fulanin Usul yana kwance lib aƙeyarsa haka ma Ramadan sanye yake cikin irin shigar Haiydar Yayin da Mommy ke sanye cikin Atanfa mai Golden mai masifar kyau anyi mata ɗinkin riga da zani fuskarta ɗauke da simple make da Khausar tayi mata.
Baki ɗaya falon wani sanyayyan ƙamshi yake fitarwa wanda ya haɗu da ƙamshin jikinsu.
Cike da tsantsar farin ciki Khausar dake ɗaukar su hoto ta juya ta kalli Mommy kana tace .
“Kuce Chesss”.
Dariya suka fashe dashi kana suka ce.
“Cheeessss”, Akuma dai-dai lokacin ta ɗauki hoton.
Sosai hoton yayi kyau kallo ɗaya zaka musu ka tabbatar da cewa suna cikin tsantsar farin ciki da annushawa tare da nutsuwa.

Suna cikin hoton Hajiya Bunayya tashigo cikin shiga ta alfarma da kamala sosai tayi kyau.
Zama tayi bayan tayi Sallama Idanun ta akan Mommy tace.
“Barka da Sallah ƙanwata fatan anyi Sallah lafiya?”.
Murmushi Mommy tayi kana ta zauna kusa da ita tare da cewa.
“Ayyah Yaya ina shirin zuwa wajenki ma”.
Murmushi Hajiya Bunayya tayi kana tace.
“Ayyah babu komai nima cewa nayi bari na rigaki zuwa in samu ladan gaisuwar. Fatan munyi Sallah lafiya?”.

Jinjina Kai Mommy tayi kana tace.
“Lafiya Lau Alhamdulillah Yaya Ubangiji Allah ya amshi ibadun da ayyukanmu na Al'khairai Allah ya nuna mana na baɗin baɗaɗa da rai da lafiya”.
Kai Hajiya Bunayya ta gyaɗa kana tace.
“Ameen ya Allah Ƙanwata”.

Khausar kuwa kallo ɗaya tayi mata ta kawar da kai gefe.
Hajiya Bunayya kuwa kallonta ta mayar kan Khausar dake ɗaukar Haiydar, Ramadan, da Raudat hoto, cike da makirci tayi wani murmushi kana tace.
“Khausar Barka da Sallah”.
Anutse Khausar ta juya ta kalleta babu walwala afuskarta muryarta ta saisaita kana tace.
“Yawwa Barka dai Ummah”.

Hajiya Bunayya ta mayar da kallonta kan Haiydar dake tsaye gefenta hannunsa ta kama tare da damƙa masa key da murmushi afuskarta tace.
“Ga Barka da Sallah ka Babana”.
Zare ido Haiydar yayi tare da buɗe hannunsa ya kalli sabon key ɗin mashin dake cikin tafin hannunsa,
cike da tsananim farin ciki mara misaltuwa ya faɗa jikin Hajiya Bunayya tare da rungumeta cike happy ya saƙi ƙara kana yace.
“Wayyo Ummah na Nagode. Allah ya saka da al'khairi. Allah yaƙara miki nisan kwana mai amfani. Allah yarabaki da sharrin Mutum da Aljan, gaskiya nayi farin ciki kinyi surprise ɗina da kince sai bayan Sallah da kwana biyu.
Cike da farin ciki tayi murmushin gefen baki kana tace.
“Ameen,Ameen Babana, Eyyyy dama sunce sai bayan Sallah da kwana biyu sai kuma suka kawo jiya da daddare”.

Khausar kuwa cike da takaicin halayyar matar ta riƙa watsa mata harara wani irin haushin ta takeji, aƙasan ranta kam cewa take shegiya muguwa aniyar ki ta biki da izinin Allah babu abinda zai samesa.

Mommy kuwa kallon Khausar dake bin Hajiya Bunayya da harara tayi kai ta girgiza tare da cewa.
“Khausar jeki ɗauko mana abinci a kichen ki kawo kin tsaya kin tsare mutane da ido baza ki iya taya ɗan uwanki samun abin farin cikin da yayi ba”.
Zumɓura baki Khausar tayi tare da miƙewa batare da tace Komai ba tashiga kichen.

Haiydar kam Kallon Mommy Yayi kana yace.
“Mommy Ummah ku tashi nayi muku hoto”.
Miƙewa sukayi da murmushi afuskarsu Haiydar yashiga ɗaukar su.
Khausar kuwa fitowa tayi hannunta riƙe da Warmers dake ɗauke da soyayyun kaji ta ajiye a dining kana ta koma ta sake ɗauko wasu Warmers ta ajiye.
Dai-dai lokacin da Mommy ke cewa.
“Yaya mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi Agaskiya nayi farin ciki”.
Fuskar Khausar ta ɓata kana tace.
“Haba Mommy irin wannan godiyar sai kace wacce aka biyawa Kujeran Hajji”.
Kallonta Mommy tayi kana tace.
“Ai kujeran hajjin ne Khausar, mutumin daya so ɗan ka arayuwa har yayi masa alkhairi ai babu kamarsa ”.
Kai Khausar ta girgiza kawai aranta tace Mommy har yanzu baki san wacece wannan makirar matarba, shiyasa kike yabonta wannan matar da kike gani tafi kwalba sharri afili kuwa cewa tayi.
“Hmmmm Allah ya kyauta”.

Murmushin da be wuce saman laɓɓaba Hajiya Bunayya tayi kana ta miƙe tare da cewa.
“Nikam zan wuce”.
Miƙewa Mommy tayi tare da cewa toh mungode Yaya Allah yaƙara girma da ɗaukaka”.
Ita kuwa Hajiya Bunayya ficewa tayi Yayin da Haiydar yabi bayanta zuwa sashen Lamiɗo.
yana shiga yace.
“Abba gashi Ummah ta siya min Mashin zan hau?”.
Kai Lamiɗo ya gyaɗa kana yace.
“Babu damuwa tun da kana son hakan, amma kafin nan sai an sake koya maka mashin ɗin na tsawon wata biyu kafin ka fara hawa kai ɗaya kaga ai ka sake koya”.
Jinjina kai Haiydar yayi kana yace.
“Toh shikenan Abba babu Matsala ”.

Bayan sallah da kwana biyu jirginsu Moddibo ya sauƙa a Nigeria cike da farin ciki Moddibo, Innayi da M Jameel Ummi suka dawo gida yayin da Hajja Nana ma ta sauƙa ta Ɓadamaye cike da farin ciki da kuma murna.

**********

Ahaka rayuwa ta cigaba da tafiya komai yana tafiya dai-dai cikin ikon Allah Akwana atashi asaran mai rai, sekonni na juyawa izuwa Mintuna, Mintuna na tafiya izuwa awanni.
Yayin da awanni ke juyawa izuwa kwanaki, kwanaki na tafiya izuwa Makonni.
Yayin da Mokonni ke juyawa izuwa Watanni. A hankali kuma watanni ke tafiya Izuwa shakara ko shekaru...

Alhamdulillah su Khausar sunyi nisa kiwo aski yazo gaban goshi, yanzu suna shirye shiryen zana jarabawar Ƙarshe na kammala secondary School WEAC and NECO baki ɗaya kansu ya ɗauki zafi basu da wani lokaci saina karatu sosai suka maida hankalin su suna karatu tuƙuru domin fitowa da kyakkyawan sakamako Inda yanzu ya rage saura Exam biyar ya rage su kammala Neco.

Khausar ce tsaye gaban Dressing mirror jikinta ɗaure da towel da tsawon sa ya kai gwiwarta,
Zuwa yanzu ko ina na jikinta ya cika fam, dukkan ƙirar girma maƙerin budurci ya ƙenƙesa matashi, musamman Dukiyar fulaninta da kuma hips dinta da suka cika ƙugunta, yalwataccen sumar kanta irin na Fulanin Usul ya sake tsawo da sansti.
Manyan Idanunta sun sake girma tare da lumshewa siririn dogon hancinta ya sake tsawo yayin da madaidaicin bakinta ya sake tattarewa izuwa pich collor, yana yin ƙiranta kamar kolbar Coca cola Yayin da Tsananin kamanninta da Kajol ya sake bayyana ayanzu tana da shekara goma sha tara a duniya.
Cikin sauri ta shafa Lotion ɗin ta tare da shafa powder sama-sama sai kuma ta shafa kwalli amanyan Idanunta lipstick kaɗan ta shafa asaman laɓɓannta cikin sauri sauri ta sanya Uniform ɗin ta daya sha guga tulin sumar kanta tayi acuci dashi kana ta feshe jikinta da turarukanta masu masifar daɗin ƙamshi da sanya nutsuwa.
Cikin Sassarfa ta fito falo harara Mommy ta maka mata kana tace.
“Ke dai Khausar ba zaki canza ba kin girma amma kullum shiririta kike ƙarawa tun yaushe Ake jiranki, ga Amina ma can tanata jira amma sai ɓata musu lokaci kike”.
Langwaɓar da kai Khausar tayi tare da riƙe kunnenta kana tace.
“Sorry Mommy”.
Fuska ta tsuke tare da ce wa. “Kin dai san Amina in ta gaji da jiran ki”.
Cikin ɗan sauƙe numfashi tace.
“Uhumm ai yaseen in ta gaya min mgn ramawa zanyi in banda asarama tun tuni yaci ace ta gama, amman kullum taba cikin dakon aji har wai sai yanzu zamu gama tare”.
Mommy na juya zata fita tace.
“A'a ni bana son fitina”.
Ta ida mgnar tana fita,

Haka yasa ta biyo bayan Mommy da ɗan sauri yayin da ko wanni gaɓa na jikinta ke motsa wa baki ɗaya alamun Budurci sun bayyana ajikinta ta ko wanni fanni ta zama cikakkiyar budurwa ƴar gayu First class.
Bayan motar ta buɗe ta shiga bayan ta ƙarasa wajen gani tayi duk Amina ta wani babbaje.
Kamar ba zata ce komai ba sai kuma tace.
“Ɗan matsamin in zauna”.
Kallon banza Amina ta watsa mata cikin ya mutse Fuska ta kalli Khausar kana tace.
“Keɗin har nawa kike da wannan wajen ba zai ishe ki ba?”.
Cikin juya ido tace.
“Kinsa cikakkiyar sura ta ƙasaitattun mata Allah ya min dole wurin bazai isheni ba tunda ba irin baki bane”.
Cike da fusata Amina tace.
“Eh lallai yarinyar nan wuyanki ya kai yanka, amman dadin ta dai bada ɗuwawunki nake zamaba kuma bada ƙugunki nake ɗaura zabi ba”.
Taɓeki tayi tare da juyawa ta kalleta.
Har kamar zata yi magana sai kuma ta fasa ganin yanda lokaci ke tafiya sannan ya Exam na Geography zasuyi tasan muddin aka fara Moddibo na iya hukuntata baya ga haka ga kuma alamun yau akwai hadari a garin wanda yau kimanin kwana tara kenan ba'ayin musu ruwan saman ba.
Gefen Haiydar ne ya matsa mata ta shiga kana Driver yaja suka tafi.
Suna Isa Khausar tayi saurin ficewa tare da nufar Hall da zasu zana Exam ta nufi Hall ɗin yayin da Iska mai sanyi ya soma kaɗawa gari ya fara duhu suna cikin rubuta Exam ɗin hadari ya fara haɗa gangami sosai a hankali gari ya fara duhu.
Basu wani ja lokaci ba suka kammala rubuta Exam ɗin atare Khausar da Asma'u suka fito.
Asma'u ma ta zama cikakkiyar budurwa komai na Budurci ya bayyana ajikinta.

Juyowa Khausar tayi ta kalleta ƙirjinta rungume da Questions da suka gama rubutawa, murmushi ta ɗan yi kana tace.
“Asmeey ki gaida min Ummi dan Allah, wallahi nayi missing ɗinta, rabo na da ita fa ya kai wata biyu”.

Hararanta Asma'u liƙa mata kana tace.
“Ai baki da kirkine sannan babu saƙon ki da zan fada mata in da gaskene kizo”.
Ta ƙare mgnar tana mai ɗaga kanta ta kalli sama, ganin yadda gaba ɗaya garin ya rufa yayi duhu.
Da sauri Khausar ma ta fara juye-juye tana cewa.
“Yah Salam wannan hadari haka, ina Haiydar suzo mu tafi, kar ruwa nan ya rutsamu a nan.”
Murmushi Asma'u tayi tare da cewa.
“Allah yasa ya rutsa kin dai muga ta tsoro”.
Ta ida mgnar tare da yin murmushin mugunta dan tasan yadda Khausar ke masifar tsoron walƙiya da tsawa.
“Ba Amin ba”.
Khausar ta faɗa tare da tura baki.
Ita kuwa Asma'u dariya tayi tare da jan hannun Bashir sukayi gaba saboda yanda hadarin ke sake gangami ko ina yayi ɗib.
Murmushi Khausar tayi kana tace.
“Bashir dan Allah kagaida Ummi, dan naga yau mutuniyar Black Stomach take ji dashi”.
Asma'u na ƙoƙarin shiga mota tayi murmushi kana tace.
“Oho dai ance zuwa da kai ai yafi saƙo”.
Khausar kuwa murmushi tayi tare da bin bayansu ganin Haiydar yayi gaba.
Da ɗa sassarfa ta tashiga bayan motar ta zauna kusa da Haiydar tana ɗan kallon harabar makarantar da duk aka watse sai mutane ɗaɗɗaya har malamai da alamun sun tattafi da sauri ta juya ta kalli Haiydar kana tace.
“Ina Amina kuma?”.
hannu ya buɗe mata alamar bai sani ba, bata sake cewa komai ba,
ta lumshe idanunta tare da jingina bayanta da jikin Kujeran sassayan iskan hadarin dake bugawa na ratsata.

Acan harabar makarantar kuwa Amina ce da Samira Sani ke tafiya.
Cikin taɓe baki Samira ta kalli Amina kana tace.
“Ni wallahi tunda nake ban taɓa kallon mutum Irin Moddibo ba ace mutum kamar dutse sam baya fahimtar komai”.
Murmushi Amina tayi kana tace.
“Hmmm ke dai Samira bari M Jameel ɗin ma meyene, duk tsawon lokacin da muka ɗauka muna aiki da maganin fa yanda yake wani shan min Ƙamshi”.
Harara Samira ta watsa mata cike da takaici tace.
“Amma Wallahi Amina baki da godiyar Allah ki dubi yanda mutumin nan ya fara sake miki, yana amsa gaisuwar ki da fara'a, yana kula ki da ace nice nasamu wannan damar, awajen Moddibo ai dana godewa Allah”.
Jinjina kai Amina tayi kana tace.
“Haka ne kuma amma gaskiya har yanzu sai mun sake sabon shiri akansu domin har yanzu Malam Jameel yafi ji da wannan shegiyar yarinyar akaina”.
Da wannan hira suka isa jikin motar wani matsiyacin kallo Amina ta watsawa Khausar dake bayan mota Idanunta alumshe cike da gadara da kuma Izzah ta ya mutse fuska kana tace.
“Iyeee ƙarfin hali yau naji Agola da ƙarfin hali, motar na gidan Ubankine da zaki shiga baya kiyi kane-kane aciki, to ni kuma a ina zan zauna ji yanda kika tara ƙannenki kuka lafe abaya ku gaku ramukan kura ko daga ke sai ƙannen ki, wai ma tukunna ni akanki zan zauna ne!? Da kika wani baza masaka-masakan duwaiwaka”.

Ahankali Khausar ta buɗe Idanunta dake lumshe ta zuba mata su tana kallonta cike da mmki, amma ba tace komai ba sai gyara zamanta da tayi tare da buɗa mata inda zata zauna.

Ya mutse fuska Amina tayi cike da jaraba da kuma gadara ta dubi inda Khausar ta matsa mata kana tace.
“Wannan wani irin iskanci ne da raini ne ko kuma ni sa'ar kice ke badan kinyi sa'ar Babanki ya mutu ya bar uwarki tayi zawarci babana ya kwasa ba ai koda hanyar da nabi baki isa ki biba. Agola kawai mara galihu ƴar matsiyata”.

Cike da ɓacin rai Khausar ta ɗago kanta babu walwala afuskarta ta kalli Amina tare da cewa.
“Wai Meyesa kike son zagina ne? Baga shi na gyara niki ba wannan ɗan ɗuwawun da kamar an ɗaurawa kare zani me zai hana filin isarki, baki shigo kin zauna kinga wurin bai ishi tsamurarrun mauzanki da suke kamar an matse lemon tsamiba kawai saboda kin saba da Akuyanci da kuma karnukan ci sai kin tsaya anta masifa dake da raba hali, saboda ke Jaka ce baki san darajar mutane ba, zaki tsaya kina ta goranta min akan wani Akwalar mota! To ki sani ni dai bazan zagi iyayenku ba musamman mahaifinki da yake mumini uwarki kuwa zaginta ma asarane don ko zagi akan mai tsarki yake fatan a aikeshi”.
Harara Amina ta watsa mata kana Afusace tace.
“Eh koda Akwalar ce aiba Ubanki bane ya saya idan kuma Ubankine ya saya sai inji? koda yake nasan har matsiyacin Ubannaki ya mutu bai taɓa mallakar irin wannan na kansa ba!”.
Cike da matsanancin ɓacin rai Khausar ke kallonta idan akwai abinda tafi tsana aduniya kana yake saurin fusata ta shine zagin mahaifinta.
Azuciye ta sauƙa daga motar yayinda Haiydar da su Ramadan ma suka sauƙo,
cikin nuna Amina da yatsa tare da ƙanƙantar da idanunta kana tace.
“Kada ki sake zagin Ubana domin Ubana yafi ki daraja koda Agaban Ubangiji”.

A yatsine Amina ta watsa mata mugun kallo kana tace.
“An zage sa ƴar iskan yarinya mai hana ruwa gudu ƴar matsiyata”.
Cikin wani irin fushi Khausar ta ɗaga hannunta tare da kife Amina da wani irin azabebben mari hagu da dama cikin nunuta da yatsa tace.
“Ki sake zagar min Uba kiga abinda zan gwada miki”.
Dafe kuncin Amina tayi cike da Mamaki take kallon Khausar kana tace.
“Ni kika mara Khausar?”.
Harara Khausar ta watsa mata da manyan Idanunta kana tace.
“An mare ki”.
Ahankali Habu Driver ya leƙo kansa tare da faɗin.
“Khausar kiyi haƙuri".
Sai kuma ya kalli Amina dake huci kana yace.
“Amina kema sam baki kyauta ba taya zaki zagi Ubanta ai duk Abinda zakuyi tsakaninku ne”.
Wani shegen kallo ta watsa masa Afusace tace.
“Habu ka rufe min baki ka fita Idona na zagi Uban nata idan taji haushi tabar mana gidan mu ta tafi gidan Ubanta ƴar matsiyata ƴar jarababbu Angola ta bar nan garin ta koma can dajin nasu mana”.
Ta ida maganar tare da shiga motar taja murfin ta rufe da ƙarfi.
Sai kuma ta sauƙe glass ɗin motar tare da cewa “Haiydar, Ramadan, da Raudat ku shigo motar tunda ku dai ta Ubanmu ne”.
Cikin takaici Haiydar ya girgiza kai alamar a'a su tafi.
Ita kuwa Khausar ciki takaici ta ɗaga Raudat da Ramadan ta sakasu cikin motar tare da nunawa Haiydar ƙofar motar alamun ya shiga.
Murya a cushe yace.
“Toh kefa Adda Khausy”.
Cikin danne fushinta tace.
“Kada ka damu zan shiga Napep”.
Zai yi mgn tayi tayi saurin cewa.
“Dan Allah kada kace komai shiga kuje”.
Ta ƙare mgnar tana turashi ciki, dole ya shiga. Ita kuwa Amina tsaki taja tare da cewa.
“Dole su kam shiga ke kuma sai kije can kishiga naki na Uban”.

Kallon Habu tayi kana tace.
“Haba kaja motar mu tafi”.
Da mamaki Habu drive ya kalleta kana yace.
“Haba Amina taya zamu tafi mu barta anan dubi hadarin daya taso sannan babu kowa a haraban makarantar ya za'ayi mutafi ne”.
Harara ta galla masa kana tace.
“Mu tafi kuma wallahi idan ka ƙi na rantse da Allah saina sa Ummah tasa akoreka”.
Ahankali Haiydar ya juya ya kalli Amina wanda tun da suka fara magana bai sa baki ba yace.
“Haba Addah Amina Meyesa haka Fisabilillah ai koma menene bai kamata ki hanata shiga mota ba dubi hadari fa kuma kin san yadda take tsoron yanayin ruwan sama”.
Harara ta watsa masa kana tace.
“Rufe min baki an hanata ɗin rufe min baki ɗan Iskan yaro zaka nuna min ƴan Ubanci kenan ruwan ya cinyata, ta mutuma kawai kowa ya huta”.
Da ɓacin rai Afuskarsa ya kalleta kana yace.
“Ni dai bazan nuna miki ƴan Ubanci ba, saboda bamu tashi da shiba, kuma wallahi idan na koma gida na faɗawa Ummah ma ke kanki kinsan sai tayi miki faɗa”.
Dogon tsaki taja tare da cewa.
“Kayi sauri kada ƙuda ya rigaka”.
Jin haka yasa Haiydar yin shiru sai kuma ya kalli Amina tare da cewa. “Matsa min In ɗauki jakata bazan iya tafiya in barta anan ba”.
Girgiza kai Khausar tayi kana tace.
“A'a Haidar kada ka ɗauka ka shiga dasu Ramadan ku tafi nima yanzu zan biyo bayanku”.
Amina kuwa kallon Habu Driver tayi kana tace.
“Mu tafi”.
Jin haka yasa Khausar jan marfin motar tare da rufewa kana tace.
“Pless dan Allah Haiydar zauna ku tafi, in Sha Allah babu abinda zai sameni”.
Dole ya zauba ba don ya soba,
Shi kuwa Habu ba yanda ya iya haka yaja motar ya tafi.

*Yar uwa littafin SAKAYYAH na kuɗine daga wannan page ɗin na gama Free page, in dai kin ganshi a waje to na satane, a Groups ɗina na sakayya ne ɗai ya halatta, 1k ne biya ki karanta cikin Salamah 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA ban yafe ba a karanta min littafi ba'a biya ba in kin tura kuɗin ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276*

Khausar kuwa shiru tayi tare da bin motar da kallo har ya fice aharabar makarantar, ahankali ta juya ta kalli cikin makantar babu ɗalibi ko ɗaya duk sun watse haka zalika ma Malamai duk sun watse shiru tayi sai kuma ta ɗaga kanta sama ganin yanda hadari ya taso ga iska dake kaɗawa da ƙarfi.
Tamkar kazar da ƙwai ya fashewa aciki haka ta fara jan ƙafanta har ta fice acikin Makarantar tsayawa tayi abakin titin koda zata samu Napep amma takai minti biyar babu abin hawan da yazo ya gifta sakamakon hadari daya taso sosai a garin yasa dukkan ababe hawa tsagaita zirga-zirga tana nan tsaye har aka fara ɗan yayyafi hakan yasa ta fara tafiya ahankali a gefen titin.
Ba tayi nisa da makarantar ba taji an buɗe gate ɗin makarantar da ɗan sauri ta juya, akan motar Moddibo Idanunta suka sauƙa da sauri ta kawar da kanta gefe kana ta cigaba da tafiya.
Acikin mota kuwa Moddibo ne da M Jameel yayin da Moddibo ke Driving M Jameel na gefen me zaman banza.
Kallo ɗaya Moddibo yayiwa bayanta ya ganeta, baki ya taɓe Aransa yace yau kuma wannan wani sabon rashin kunya tayi musu suka sauƙeta, sai kuma ya ɗage kafarɗarsa alamun ita ta jiyo.
M Jameel kuwa sam bai ganeta ba saida suka gifta wajenta sannan yaga fuskarta.
Da mamaki ya furta.
“A'a Lelewal”.
Cikin sauri ya ɗaura hannunsa kan Moddibo tare da cewa.
“A.J tsaya Please dubi duk ɗalibai sun watse amma sai ita kaɗai mai ya tsayar da ita anan kuma ga hadari baƙiƙƙirin dubi fa yanda garin yayi duhu ko Babba hadarin na bashi tsoro yakeyi!”.
Juyawa Moddibo yayi tare da Kallonsa cikin yanayin nutsuwarsa yace.
“To ina ruwanka da ita!?”.
Wara Ido M Jameel yayi kana yace.
“Ban gane ina ruwana da ita ba? ɗalibarmu cefa! sannan kullum a mota ake kawo su sannan zuwa ake aɗauke su, kana mun ganta ba'a tafi da ita ba sannan ka duba ita kaɗai ce a layin nan dubi fa yanda layin babu kowa”.
Kallon gefen Ido Moddibo yayi masa kana ya taɓe baki.
Da sauri M Jameel ya cigaba da cewa.
“Haba A.J ya za'ayi kace haka?”.
Moddibo kuwa juya idanunsa yayi kana yace.
“Toh Meye haɗin mu da ita? kasan Meye Uzurin daya tsayar da ita?
Sannan kasan Meye dalilin tsayuwarta! Wata ƙil ma wani bishiyoyin anguwar takeson hawa”.

Girgiza kai M Jameel Yayi kana yace.
“Ai koma mene sai mu tsaya mu tambayeta ko?”.
Kallonsa Moddibo yayi kana yace.
“Nifa bazan tsaya ba”.
Langwaɓar da kai M Jameel yayi kana cikin sanyin murya yace.
“Dan Allah A.J da darajar Annabi Muhammad (S.A.W) mu taimaki yarinyar nan.
Yanzu idan Asma'u ce zaka iya barin ta awajen nan ne?”.
Da sauri Moddibo ya kallesa kana yace.
“Asma'u kuma mai ma zai tsayar da ita anan mai zai haɗa ta faɗa da wasu har tayi musu rashin kunya su sauƙeta amota, ai Asma'u baza ta kasance haka bama!”.
Sake Langwaɓar da kai M Jameel yayi kana yace.
“Amma kayi tunani ƴa mace ce ita ko addininmu ya koyar mana da kula dasu da kuma kula da al'amuran daya shafesu A.J bai kamata ba na roƙe ka dan Allah ba danni ba kuma badan ita ba dan Allah da kuma darajar Manzon mu kayi haƙuri ka tsaya! In ma bazaka ɗauketa ba, ni ka sauƙin bazan iya tafiya in bar Khausy cikin wannan yanayin A.J bazan iya barin ta ananba”.
Ya ƙarashe mgnar cikin wata iriyar raunatacciyar murya mai fito da sirrin dake binne cikin zuciyarsa.
Hannu Moddibo ya sanya tare da dafe goshinsa alamar ya gaji da damuwar M Jameel ahankali yasanya lallausan tafin hannunsa ya shafa sajensa ba tare da yace komai ba ya taka burki ya tsaya.
Yana mai kallon yadda M Jameel ya sauƙe numfashi.
Ganin ya tsaya ya sanya M Jameel sakin murmushi tare da buɗe motar ya fita cikin sassarfa da ɗan gudu ya nufi inda Khausar take dan sun ɗanyi mata nisa kana ga yayyafin da aka fara da ƙarfi da kuma rugugi alamar ana gaba da kecewa da ruwa mai ƙarfi.
Moddibo kuwa da kallo yabi M Jameel ta mirror motarsa.
Aransa yace Ohhh J ji yanda yake gudu kamar wani yaro ko ya gani a wannan ƴar nan har yake jinta cikin zuciyarsa.
Khausar kuwa tana ganin M Jameel ta saki nannauyan Ajiyar zuciya tare da cewa.
“Yaya Jameel”.
Cike da kulawa ya kalleta tare da cewa.
“Lelewal mai yafaru yana ganki anan ke kaɗai, bayan baki ɗaya student's sun watse”.
Ahankali ta kallesa sai kuma tayi saurin lumshe Idanunta tare da cewa.
“Wallahi Yaya Jameel Amina ce ta hanani shiga motarsu yau kam masifa take ji dashi”.
Girgiza kai yayi tare da faɗin.
“Subhanallah gaskiya bata kyauta ba, maza zo ki shigo mota mutafi”.
“Toh”,tace tare da bin bayansa cikin sassarfa yayinda ko wanne gaɓa na jikinta ke motsawa.
Ɗan guntun tsaki Modibbo yaja, tare da kauda kansa daga kan madubin, ganin yadda suka wani jero da J ɗinsa.
Suna isa wajen motar M Jameel ya buɗe mata bayan gefen da Modibbo yake tashiga, sannan shi kuma ya zagaya ya shiga a hankali Khausar ta ɗaga kanta tare da kallon gaban motar ai kuwa idanunta suka sauƙa akan Moddibo da batasan yana cikin motar Ba gashi ta zauna asaitin bayansa.
A kuma dai-dai lokaci ruwa ya kece tamkar da bakin ƙorya, key Moddibo yayi wa motar tare da figarta a dan guje suka fara tafiya.

Kallon Moddibo M Jameel yayi kana yace.
“A.J kasan zamu biya ta gida ka sauƙe ni tun safe Abba ke kirana wai Inje Yana son magana dani muje ka sauƙe ni”.
Kallon sa Moddibo yayi tare da cewa.
“Baza ka bari sai anjima ba?”.
Girgiza kai M Jameel Yayi kana yace.
“A'a muje dan Allah ka sauƙe ni saboda bansan me yake sona dashi ba yanata ne mana tun tuntuni”.
Kai Moddibo ya gyaɗa kana yace.
“Toh naji”.
Yayi mgnar tare da haharan M Jameel ɗin,
Sannan ya cigaba da Driving ɗin sa.
Shi kuwa M Jameel murmushin yayi tare da ɗan mishi alamun zunɗe.

*Littafin SAKAYYAH na kuɗine daga wannan page ɗin na gama Free page, daga gobe in dai kinga littafin SAKAYYAH a wani wuri to na satane, yar uwa ki biya 1k ne kacal ki karanta cikin Aminci ba haƙƙin kowa a kanki littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa kada ki karanta in baki biyaba 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276*

Khausar dake zaune abayan motar kuwa ƙanƙame jikinta tayi saboda yanda ɗumin motar ke ratsata sam cikin motar babu sanyi da yawa ba kamar waje da iska ke kaɗawa ba.

Sanyayyar Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da gyara Questions peper dake hannunta ta sake rungumesu aƙirji sai kuma ta gyara zaman wuyan hijabinta wanda har tattausan gashin gaban goshinta mai

1 Comments On SAKAYYAH
avatar
fatima-8-5-3

4 months ago

Reply

Allah ya qara basira

Please Login or Register in order to submit comment