Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

auren su faruk da prince.

Iyayen biyu, mum da mami, kullum suna busy.

Zuby da zarah kuwa, lokacin suna semester exams, suma basa da wani time sosai.

Yanzu kuwa neena ta kara wayewa, dan zama da zuby dole mutum ya goge.

Duk kayansu idan sun matse su, ko sun gama yayi, sai ku tarkata su bata, dama neena akwai body, dan jikin ta yafi shekarunta.


Yau ake sa ran zuwan prince, dan sai da dad da abba, suka masa fada sosai, dan cewa yayi, shifa bazai samu zuwa va, suna da aiki a bayalsa.


Amarya ikram, sai shiri akeyi, ta shirya events sunfi biyar.ita kuwa amaryar faruk, Deeja, dama yan maiduguri ne, acan zasuyi komai,sai dai a kawo amarya kawai.



Neena tare da amir a garden, suna wasan buya, yanzu amir a dauke a matsayin uwa, idan bata nan ba mai iya shawo kansa, shi yasa yanzu sai wata wata take samun zuwa wurin umma, kuma ta wayar zuby take samun gaisawa da yaya habu, dan har chat suke da zuby din (toh fa)


Amir yace, aunt neena, yau papa dina zai dawo, neena na shirin bude baki, zarah ta kwala mata kira ta kofar kicin.

Da sauri ta karaso wurinta, zarah dake zuba abinci a plate tace, kije inji mum.

Neena na zuwa, ta samu mun da mami a daki, sun baje kaya a tsakiyar dakin, dama yau kwanan su biyu da dawowa daga Egypt.

Neena ta gaishe su tace mum gani, mum ta mika mata wasu kayan a dinke suke, kala har biyar, tace ga kayan biki kema, neena tayi murmushi, sannan ta musu godiya.
Tazo zata fita, mum tayi saurin cewa, yauwa neena, neena ta juyo, tace kidan shiga dakin Na'im ki gyara masa, suzy na min aiki a BQ, neena tadan ware ido, dakin papa!!!!! Mum tace eh jeki pls, ya kusan isowa....



By→☆sultana
[8/8, 4:04 PM] .: 🌳🌳 🌳🌳
🎃 *YAR TALAKAWA* 🎃




By→ _afrah_


Episode →4⃣4⃣→4⃣5⃣








Neena ta fito, kamar waddda kwai ya fashewa a ciki.
Dakin ta, ta shiga ta ajiye kayan ta, sannan ta fito ta nufi dakin prince.
Tana cikin tafiya suka hadu da zuby, dauke da kedar kayan data amso musu daga wurin tela.
Neena takai hannunta zata taimaka mata, tace barshi neena na kai, kinsan anjima zamu, family dinner, yanzu saloon zamuje, mami tace muje dake, dan haka idan kin gama aikin ki, ki hau taxi kizo, kinsan ai wurin?? Neena tayi murmushi tace ehh na gane wurin, a wuse 2 ko, zuby dake tafiya tace eh nan ne kiyi sauri pls.


Neena ta shiga dakin prince, ta zo wurin gadon sa, ta tsaya, take ta tuna lokacin daya jawo ta jikinsa, ta runtse idon ta, ta bude a hankali, sannan tazo ta fara gyara gadon, kamshin bed sheet din, tamkar shine a wurin , haka nan ta samu kanta da rungume zanin gadon, ta shaki kamshin, ta tuna lokacin daya dauketa, haka jikinsa keta kamshi, tayi saurin ajiye wa, taci gaba da aikin ta, da taga zata fara tunane tunane, sai tace a'uzubillahi minal shaidanil rajim, Allah ka raba ni da tunanin mijin wata, ni duka shekaruna nawa, ni inshaAllah karatuna zanyi nima, na zama kamar mum, tayi murmushin ta taji gaba da aikin gaban ta.


Ta gama kimtsa dakin, ta shiga toilet, woow ta furta, katon toilet ne sosai, gashi shima sai kamshin freshener yake yi.

Ta shiga wanke wa, tana gama wanke na farko ta shiga wurin shower, din, dan daban daban ne, amma duka a cikin toilet dinne.

Ta shiga ta gama wanke wa, tahau kalle kallen wurin, duk glasses ne, ga kuma remote, neena ta shafa'a da kalle kallen ta.

Sai jin bude kofar toilet din tayi, ware ido tayi, waye ya shigo kuma????

Tayi sauri tadan leko, Prince ta gama a tsale gaban mirror, shaving din kasumbar sa yakeyi, daga shi sai, rigar towel fara.

Da sauri neena ta koma cikin shower din, ta dafe kirjin ta, yanzu ya zanyi, nasan ya prince ya gabe ina nan ciki, zan shiga 6 ne bama 3 ba.

Ta rasa ya zatayi, sai wiki wiki take yi da idanunta.

Shi kuwa prince, yana kammala shaving dinshi, ya wanke fuskar sa, ya juyo yana kallon shower din , da gani nan yake shirin shiga , ya watsa ruwa.

Neena tension dinta ya lunku, dan wanda ke ciki yana iya ganin na waje, shi dake waje bazai ganta ba.

Take wata idea tazo mata, tayi saurin lalubar, aljihun pakistani wandonta, tana tabo wayar dake ciki, ta sauke lumfashin ta.

Wayar amir ce daya bata ajiya, lokacin suna wata a garden, tayi saurin lalubar numbar papa, aikuwa ta gani, Allah ya sota ta iya karatun ta.

Da sauri hannun ta na kyarma ta danna kiran numbar...........



Kuyi hakuri da wannan bana da caji wlh



By→☆sultana
[8/8, 4:12 PM] .: 🌳🌳 🌳🌳
🎃 *YAR TALAKAWA* 🎃




By→ _afrah_


Episode →4⃣6⃣→4⃣7⃣





Prince ya mika hannun sa zai bude kofar ya shiga, yaji karar ringing din wayar sa daga daki.

Mtsww, yayi tsaki, zuwa fa wurin nan ba dole bane, ya bude kofar toilet din ya koma daki.

Neeena tayi saurin sauke ajiyar zuciya, wai Allah na gode.

Fitowa tayi da sauri, tazo ta lekasa ta kofar, ganin shi tayi zai dauki wayar, tayi saurin rakubewa, ta fito tana bin bango, tana sando, kamar wata munafuka.

Prince ya dauki wayar, hello dear, am busy nw, zan neme ka anjima kaji, prince bai jira jin komai ba ya kashe wayar, ita kuwa neena hankalinta na, wurin kawai taga ta fice daga dakin.

Sai lallabawa take yi tana bin bango, prince na ajiye wayar ya juyo zai koma toilet, sai ganin neena yayi ta lallabawa zata fice, ya saki baki, ita wannan kuma fa?! Kaman ya make ta yake ji, ya daka mata tsawa, kee!! Mai ya kawo ki nan?!!

Neena ba karamin tsorata tayi ba, ta jingine da hango tana kallon shi a tsoracen.

Prince ya karaso wurin da take a tsaye, ya nuna ta da yatsa sa👉🏼😳😁, mai ya kawo nan?, neena ta kasa motsa harshen ta, dan nauyin da yayi mata, prince ya sake cewa da tsawa, ba da ke nake ba??!! Neena tayi saurin runtse idon ta, dan tsawar da yayi mata kamar zai hadiye ta.

Tayi kokarin motsa lips dinta, tace , ni ni uhm ni dama ni uhm, mum ce , uhm tace wai, nazo na gyara maka dakin, prince ya wani wurga mata harara, ya juya yace, get out!!!! Da sauri neena tayi gaba harda su tuntube.


Sunje salon, an musu gyaran gashi, su zuby sai yaba tsayin gashin neena suke, zarah kuwa na nan zaune sai waya take da mates dinta, wai ance mata zasuyi paper da yamma, shine take ta kira dan taji koda gaske ne.


Sun dawo gida karfe hudu na yamma, neena tayi dakin amir, a kwance ta iske shi tare da faruk, suna game da ipad.

Neena na shigowa tayi sallama, amir yayi saurin saukowa daga saman gadon, ya rungume ta, neena tayi murmushi, my little master, muje nayi maka wanka, amir yayi tsalle zanje naga fuad yau inji uncle faruk, neena tayi murmushi, sanna ta kalli uncle faruk, ina wuni ya faruk? Faruk ya juyo ya kalle ta, yayi murmushi, lafiya neena, har kun dawo ne? Neena tace eh yanzun nan muka dawo, faruk ya mike, bari na shiga wurin ya prince, ya fice.


A zaune ya iske prince, yasha wankan shi, cikin wasu tsadaddun kaya, farare, faruk ya samu wuri ya zauna, yace ya prince , su dad sunce idan mun kammala mu same su a can family house, prince ya tabe baki, faruk yayi dariya ya mike, haba yaya kadan saki fuska, kada ka bawa amaryar mu tsoro, prince yaja tsaki ya jefe shi da remote din da ke kusa dashi, faruk ya fita yana masa dariya.


Neena zaune ta gama shirya amir, yayi kyau shima sosai, ta shafa fuskar sa, little master kayi kyau abunka, amir ya shafa fuskar ta itama yace, u r pretty like a barbie aunt neena, neena tayi dariya, nagode, oya maza je wurin su antu zarah su tafi dakai, amir ya make kafada, ni sai dake zan je, neena zatai magana, mum ta shigo tare da zarah da zuby.

Mum ta kalli neena , ya baki shirya ba neena, oya tashi tashi, kije ki shirya, dan dole sai ke amir dinnan. Amir ya rike hannun mum yace, grany da aunt neena zamu ko? Mum tace eh da ita zamu, sannan ta kalli neena tashi kije ki shirya.


Neena ta saka, riga da skirt dinta, dinki zamani, sun zauna mata sosai, kamar ba ita ba, sai juyi take tana kallon kanta, wai dama umma na na nan, ta ganni cikin kayan nan, tayi murmushi.

Zuby ce ta shigo dakin, neena kiyi sauri muje, tsayawa tayi tana kallon yarinyar, baki a bude, tace kin ganki neena, neena tayi murmushi tace kinyi kyau kema anty, zuby ta karaso ciki tace, sai dai bakiyi make up ba, kuma dankwalin ki, zuby ta sa hannu ta cire jakwalkwalon daurin da neena tayi, tace zauna na gyara miki.
Neena na murna ta zauna.



By→☆sultana
[8/8, 4:13 PM] .: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
_*YAR*_
🎃 *TALAKAWA*🎃



By→afrah




Episode→4⃣8⃣→4⃣9⃣









Zuby cikin mintuna kalilan, ta kammalawa neena simple but pretty makeup, woow zuby tace, kin ganki kuwa?, neena sai murmushi takeyi, dan tunda take ,daga powder sai mai , kawai take shafawa fuskarta, yau gashi harda su pink janbaki, tayi kyau mashaAllah, kamar ba ita ba.

Zarah ce ta shigo dakkn, cikin shiri itama, dinkin su kala daya da zuby, tace kuzo muje mana, su mum duk sun wuce fa.

Sakin baki tayi tana kallon neena, ta nuna ta da yatsa, who is dis sisi? , zuby tayi dariya, amir nanny, zarah ta matso tace, dama kyaun neena yakai haka?, neena tayi murmushi tace anty kuma ai kunyi kyau, zarah tace toh matso muyi selfie kafin mu wuce, zuby ta matso hakama neena, zarah ta daga wayarta ta dauke su, sunyi kyau kamar wasu flowers (lols).



Sun isa wurin mutane a cike, duk family dinsu ne a wurin, amarya ikram tasha gayun ta, cikin wasu tsadaddun kaya, ga makeup an mata, tayi kyau sosai abunta, ango kuma ga kyaun amma ba fara'a, fuskar nan kamar kullum, a tsoke.


Neena ganin duk ba wanda ta sani, kuma duk inda tayi sai an kalle ta, wasu a zaton suma , irin ruwa biyun nan ce, dan a gaskiya neena farace soaai.

Neman su amir ta farayi dan ta tsare su, kada suje su tafka banna, mum ta hango ta, ta kwala mata kira, neena ta karaso wurin table dinsu mum, zaune suke su hudu, mami, mum, mummy, sai wata mata, da ganin kaga su abba, dan kamannin su harya baci, neena ta gaishe su, mum ta mika mata car key, je ki dauko min, wasu kaya a mota, neena ta amsa tace toh.

Wannan matar mai kama dasu abba, tace asiya (mum) ina kika samu yarinya,? Mum tace nanny din amir ce, da sauri naga matar ta kalli mum, nanny? ? Shine taci gayu haka, bata da uniform ne ko me?, mami tace tana dasu, amma su abban faruk sunce kada ta ringa sakawa, matar nan dama da ganin ta yar masifa ce, dan fuskarta ba alamun wasa ko kadan, tace ban gane kada tasa ba, ita din yar Wacece??? Mummy dake jinsu tace yar wacece fa fashe _YAR TALAKAWA_ matar nan ta maimaita, yar talakawa, shine zasuce kada tasa uniform, wannan yar yarinyar da ba'a gama rainon taba shine zaku bata rainon wani?, gata yar talakawa, ko karatun kirki batayi ba, tazo ta koya wa yaro tabi'a irin tasu?, toh wai ina professionals nannies, dinda kuke masa hiring? .

Mum tace yaya B , wannan da kike gani duk tafi su wlh, yaya B taja tsaki, zamuyi dai maganar idan mun isa gidan.

Duk wannan maganar da yaya B keyi, neena taji, dan ta dawo daga daukar kayan taji ta tana aibata ta, a sanyaye ta kawo wa mum kayan, yaya B ta watsa mata kallon tsana, ta juya zata koma seat dinta, batasan lokacin da hawaye suka sauko daga idon taba, can baya ta samu ta zauna, ta buga uban tagumi, hawaye na fita daga idon ta, tunda tazo family duka suna sonta, amma da gani ranar tafiyarta ya kusa, wani kuka yazo mata, tayi saurin dukar da kanta, ita kam bazata iya rayuwa ba amir ba, haka takeji har zuciyarta.

Tana nan zaune gaji anyi kiran amarya da ango, ta dago kanta ta kallo su, sunyi mugun yin kyau , ta dauke kanta tace, ku kam kunji dadin ku.
Tana nan zaune har aka kammala family dinner din nan.

Su zuby suka fara neman ta dansu koma gida, sai suka hade da wasu cousins dinsu, meera da meena, nan suka fada firar yaushe gamo, ya faruk yazo yace musu suzo ya maidasu gida, nan suka bisa, suka ma manta da neena.

Amir kuwa yash neman neena bai ganta ba, su abba zasu koma suka tafi dashi.

Duk wurin an watse, neena ta mike ta shiga neman amir, amma duk wurin sai data duba bata kansa ba.

Tazo har bakin gate tayi tsaye, kowa ya tafi, ita tana can ta lula duniyar tunani, addu'ar ta daya Allah yasa amir ya bi wasu yana gida.

Can ta matso dan ta tari mai taxi, Allah ya taimake ta tana da sauran canjin dazu, data je saloon.

Wata bakar motace tayi parking a gaban ta, saurayin dake ciki ya fito, tana ganin sa, ta gane shi, Moha ne yayan ikram.

Ya fito ya nufo ta, sai wani layi yakeyi, da gani dai yayi dan shaye shayen sa.

A gaban neena ya tsaya kikam, tadan matsa kadan ta gaishe sa, ya amsa yana dariyar shakiyan ci, yace muje na kai ki gida, neena tace nagode amma kaje, zan hau taxi, moha ya sake matso ta zai kama hannunta, muje bana baby, neena tayi saurin ja baya tace da Allah malam nace kaje bazan bika ba!!

Moha ya kwashe da dariya, see dis village gal, ke harni zance kizo na baki lift kice bakyaso, who d hell r u, yar talakawa dake, bakauyiya.

Neena ta share hawayen ta, tayi gaba dan samun taxi, sai dai jin hannun moha tayi, ta cafko ta, yana neman rungume ta, ta fasa kara ta fara tura shi, dankwalin ta ya fadi, moha ya kurawa fuskar ta ido, ya yaye gyelen jikinta ya jefar , yasa hannunsa yana shafa gashin kanta, neena sai mutsu mustu take tana kuka, can taji kamar yana shirin zage mata zip, tayi kokari ta wanka masa mari, kai wane irin maye ne eyee, moha ya ciji leben sa yace yanzu zaki gane wane irin mayen ne ni, yayo kanta kadan kadan.....



Prince zaune a family house, ajiye coffee cup din hannunsa yayi, ya mike, its over tunda naji shiru.
Ya mike ya dauki, wayar sa ya fito, yasa key ya rufe gidan, sannan ya nufo gate dan a waje yayi parking din motar sa.

Tunda ya nufo gate din yake jin kukan mace, ya kara sauri, yana isa ya hango moha sai kokarin yage wa yarinya riga yakeyi, shi baima gane wacece ba.


Yana isowa moha na yage hannayen rigar neena, dan materials ne, ba wani wahalan yagewa gare shi ba.

Prince yayi saurin zuwa ya janye moha, ya wanka masa kyawawan mari kuda uku, sannan ya tsukomo rigar sa, ya nuna sa da yatsa, kada ka sake na kara maka ma moha, maza wuce jahili kawai, moha yayi saurin shigewa mota ya wuce fuu, dan yasan halin prince sosai, zai iya kai shi sell ne kawai ya rufe.


Juyowa yayi wurin yarinyar, yaga wayam sai gyelenta da 👝 da dankwali, can ya hango ta tana tafiya kamar zata fadi.

Neena duk hankalin a tashe yake, gaba daya kwakwalwarta ta tsaya cak, ko prince dinma bata gane shi bane, tafiya kawai takeyi.

Harya shiga mota zai wuce abunsa, can ya fito ya dawo ya dauki, gyelenta da jaka da dankwali, ya koma motar, yaja yakai dai dai inda take, yayi horn, yaga bata tsaya ba, yajaa tsaki , shi kawai tausayi ta basa, ganin ta yar teenager, ya fito yace kee!!! Neena taci gaba da tafiyar ta kamar zombie.

Prince yasha gaban ta, sai a sannan ta tsaya ta dago idanunta da suka rine zuwa jajaye, fuskar nan kamar tomatoe dan ja.

Prince ya kura mata ido, shikam kamar yasan wannan fuskar, take ya tuna dazun daya ganta a dakinsa, yace a fili nanny! !!! Toh mai ya kawo ta nan ? kuma ya akayi kowa ya tafi sai ita aka bari??



Aka°•○sultana
[8/8, 4:20 PM] .: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
_*YAR*_
🎃 *TALAKAWA*🎃



By→afrah




Episode→5⃣0⃣→5⃣5⃣






Ya kura mata ido, da gani hankalinta har yanzu a tashe yake, yace da silent voice dinshi, muje ya nuna mata mota, neena tayi saurin ja baya, har tana faduwa, dan gani takeyi kamar har yanzu moha dinne.

Prince ya girgiza kai, yaja tsaki, wai meyasa ma ya tsaya taimakon ta, ya bude kofar motarsa zai fice abunsa, sai kuma ya nushi motar ya dawo wurin ta, har lokacin tana nan a kasa ta zauna rashe rashe , sai kiran sunan Allah take , da yaya habu da umma.

Prince ya duka daidai fuskarta, ya kura mata ido, yace come back to ur sense, nine papa din amir, neena zata ja baya , prince ya rike ta , yace ba abunda zai faru dake, tashi mu tafi gida wurin amir, tayi saurin kallon shi, tace amir, prince ya kada mata kai, ta mike tace ka kaini wurin amir, prince ya mike shima sannan yace shiga muje toh, taki motsawa daga inda take, prince ya buga kafar sa , yace ohh darm it, ke nifa zan wuce abuna haba!
Neena ta kalle shi, prince yace nibar kallona da wani idon ki katoto, neena tayi one step dan zuwa shiga motar, duk ta takure dan sanyin da takeji, ga iska, ga kuma ba gyele a jikin ta bare dankwali, prince ya lira da hakan, sai ya biyo bayan ta dan ya bata gyelen ta rufa, aikuwa neena na juyowa, sukayi karo da prince, dago kanta tayi ta kalle sa, kamshin nan nasa yasa, tayi saurin kallon fuskarsa, tace Papa!!! A zaton ta a zuciya tayi maganar, sai dai taji yace, ke lafiyanki, dare keyi fa, neena tayi saurin shigewa motar, dan take ta dawo hankalinta, prince ya tabe baki ya jefa mata gyelen ta, ta window.


Suna ta tafiya shiru, ita duk ta takure wuri daya, sanyi takeji kamar mai, gashi ya kunna AC abunsa.

Yana lura da yadda take kyarman sanyin, amma saboda mugunta ta prince , sai ya share ta, wai dolene ma ya bata punishment, tasa ya bata time dinsa, gashi yana da abunyi gobe da safe.

Sunzo bakin gate , amma a kulle, dan dare yayi sosai, karfe, sha biyu, yayi kiran wayar mai gadi, shiru sai ringing kawai takeyi, yaja tsaki mtsw...., neena tayi saurin kallo shi, ya sake kiran faruk shima tayi ringing harta katse ba'a dauka ba.

Duk yan gidan sai daya kirasu amma, ba wanda ya dauka, sai tsaki yake take ja, neena data kagara tabar motar, sai tace, papa ni zan shiga ciki, prince ya watso mata harara, sai ki shiga ai, neena tasa hannu ta bude motar, ta fita taje bakin gate din, sai kiran mai gadin take amma shiru, ga iska sai hurata takeyi, sai da tayi minti sha bakwai, sannan ta jingina da gate din, prince ya hurar da iskan bakin shi, yayi mata horn.

Ta kallo shi ,sannan ta karasa wurin motar, shigo kawai prince yace mata, ta bude ta shiga, prince yaja motar suka bar unguwar.

Neena gaban ta yahau faduwa, ina zai kaita ne????



Toh fa nima afrah, na kunna motata nabi bayan prince, dan gano wa idanuna inda prince zai kai mana neena.



Aka°•○sultana
[8/9, 8:19 AM] .: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
_*YAR*_
🎃 *TALAKAWA*🎃



By→afrah




Episode→5⃣6⃣→5⃣8⃣






Sai sharar gudu yakeyi, ga titin ba kowa , saboda dare ya tsala sosai.

Bai zarce ko ina ba, sai family house din da suka baro.

Ya shiga yayi parking, sannan ya fito ya nufi cikin babban gidan, neena ta bishi da kallo, harya isa babban balcony din gidan ya zura key a kofar yana budewa.

Ganin zai shige, ga tsoro har yanzu bai sake ta ba, yasa tayi saurin fitowa tabi sa ciki.

Babban falone sosai, can ta hango prince yana hawa benen, tayi sallama ta karaso falon, prince bai ko juyo ba ya shige wani daki dake kusa da benen.

Neena ta samu saman carpet ta rakube tadan kwanta, Allah yaso ta ma bata sallah ranar, sanyi takeji bana wasa ba, sai kyarma takeyi, ta rufa da dankwalinta amma inaa, sanyin yaki raguwa, tun tana kalle kallen falon, tana rawar sanyi har barcin dole ya dauke ta.


Prince ya sauko dauke da blanket a hannun sa, daga shi sai singlet, shikam yana son lokacin sanyi sosai.

Yana isowa ya duka wurin da take a kwance, ya warware blanket din, ya rufa mata a jiki, yazo rufawa hannun ta, yaga karcewar akaifa, jini yadan bata mata gyelen data rufa dashi.

Mikewa yayi zai koma sama abunsa, sai kuma ya dawo, yaje ya dauko akwatin gaggawa, ya duka yasa hannu ya janye gyelen, farar soft fatar ta , ta fito, ya dauko auduga da dan spirit, ya fara goge ciwon, neena taji dan zafi, ta muskuta ta juya, juyawan da tayi, ya bayyanar da kyakkyawar fuskarta, da tayi jaa, prince ya kura mata ido, sawon hannu ya gani a jikin fuskarta, ya kai hannunsa ya shafi wurin, ya tausayawa yarinyar gaskiya, gata karama (a yadda kake gani ba ).

Ya mike ya wuce saman ya kwanta shima.

Tunda asuba, daya fita sallah, ya barta sai sharar barci takeyi.

Yana gama sallah ya nufi wani dan boutique, kusa da gidan, ya siyo riga da skirt, masu kamar suwaita, amma gaskiya sun hadu karshe.

Yana komawa ya iske ta a zaune a kasan, tayi saurin gaishe shi, ya kalle ta kawai ya mika mata ledar hannunsa, ta amsa, tace miye?, prince yayi gaba bai ko amsa mata ba.

Neena ta bude ledar taga, kayan dake ciki, ba karamin kyau suka mata ba , ta mike ta fara neman inda zata shiga ta canzo kayan, amma duka kofofin a rufe suke, sai dai ta samu bayan kujera , ta fara cire skirt dinta , ta canza, sannan ta zage zip din rigarta , ta cire, ta dauko sabuwar ta saka kanta, harta zura hannayenta....

Prince ne ya sauko cikin dan sauri, ta bayan kujerar ya biyo, baima san akwai mutum a wurin ba...
Neena na ganin yayo wurin ta, ta saki ihuuuu...
Prince yadan tsorata, dan shima bai tsammanin mutum a wurin ba, ta juyo yana kallon ta....


Please Login or Register in order to submit comment