Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fa 3month.."Tafada tana kallonsa da Mirmishi yana Tsayen ya sake Fadin"Duk da haka dai Subai"atu...yau kin zo mana Wuni ne..?

Daga ita har Hafsah Da kallo Suka Bi Juna kafin Subai ta maida kallonta kan ya Abdullahi Tana Fadin"Wuni kuma yaya..? A"a ba wuni nazo ba..Hafsah bata gayamaka ba,? Abban Muhsin ne ya bamu Direba zai kaimu Kaduna muje mu Dubo Anty Zannira kafin Ranar suna.."Kai Tsaye yace mata"Eh ta Fadamin mana.."

Cike da mamaki Subai ta kalli Hafsah kafin tace"To yaya ai yau ne zamu je din...Shiyasa na Fito da Wuri saboda mu Dawo da wuri kaga Hanya bakyau.."Mirmishi yayi kafin yace"Ok Nidai cikin Zencenta naji tana Gayamin Zaku Tafi Barka kaduna...."

Jin Haka yasa Hafsah tace"Ammh Abban Amira na gayamaka."Tafada Cikin Raunin murya kai Tsaye yace"Wa kika gayamawa..?ni...?Kika dai yi Zencenki ina jinki,na dauka kinaa mganarki ne kawai Domin wannann Zence ne na mata ban Daukesa aneman izinin ba.."Yafada yana Mikama Subai Saleem wacce tayi Jugum Tana kallon Ikon Allah.

Idanuwan Hafsah ya kawo kwallah Cikin wani Rauni tace"Na dauka danaji kace Ok ka amince naje din ne.."Karamin Tsaki yaja kafin yace"Saboda kin Rainani ko..? Haka kurum Saboda Subai"atu ke Auranki sai ta Shiryamiki tafiya ke kuma ki Hau ki zauna Batare dani mijinki kin Tuntubeni ba kuma da kike mganar kin gayamin Daga Ranar kin karamin mgana..?Kin sameni kin ce Abban Amira muna so zamuje Mu gaishe da Zanniratu kafin suna..? Kin sameni..?

Yafada yana Tsare ta da ido Jikin Hafsah yayi sanyi kawai sai ta Dukar dakai Hawayen idanuwanta suna kawowa Subai kuwa addu"a take aranta Allah sa kada Fadan ya Dawo kanta Tabe Baki yayi ya juya yana Fadin"Kinga kenan baki da Tafiya sai ki bari Ranar suna sai ki Tafi..Shima in kikamin irin wannan Tafiyar kinsan Allah bazaki ba.."Yafada kai Tsaye yana Shirin Shigewa Bedroom

Da Sauri Subai tace"Don Allah yaya kayi  Hakuri munji munyi kuskure bazamu kara ba..Ammh Don Allah yanzu kabari muje mu Dubata bazamu yi  Dare ba da yardan Allah...."Waigowa yayi Lokaci Daya yana Hararan Subai din Wacce ta sadda kai kasa gabanta na Faduwa cikin Gadara yajuyo yana kallon Subai"atu Lokaci Daya yana Fadin"Kinsan Allah.? Bafa zataje ba ayau..Sai dai in ku Rushe tafiyar yau wlh...In kuma bazaku Rusheta ba ki kama Hanya ki Tafi Tunda ke kin gayama Mijinki kuma ya barki har ma yabaki Direba kinga ke sai ki kama Hanya ita kuma Ranar data Shirya tafiyan in ta nemi izinina na barta sai tatafi taje ta gaisheta ta mata barka ta Dawo.."Daga haka bai kara komai ba ya Shige Ciki.

Hafsah Data ke Rike Hawayenta sai gasu sun Zubo Sharr,Subai ta kalleta  Tana Fadin"Wai ke baki Fadamai bane..? Hafsah ta Dago idanuwanta cike da kwallah tace"Wani irin ban gayamai ba.? Ina Ranar da mukayi waya da Daddare bayan ya Dawo muke tadin Haihuwan dani Dashi anan ne toh nake gayamai mun yi waya Yau zaki Biyomun mu tafi muyi mata barka yace min Toh kinji Dalilin Daya saka ban karamai mgana ba.."Ta fada Lokaci Daya tana Share kwallar Idonta.

Subai ta saki ajiyar Zuciya Tana Fadin"Toh yanzu ki Tashi ki Bishi ki gani ko zai yarda mu tafi gaskiya in bamu je ba bamu kyauta ba Duk da Mariya na chan Jiya Mama da Inna Abu fa sukaje suka Dubata suka komo.."Hafsah tace"Karma na batamiki Lokaci Subai ki tafi kawai kice ina mata barka Duk da daman na Kirata awaya na mata sannu..Ranar suna in yabarni sai na taho..

Subai tace"Kina ganin in kika lallasheshi bazai yarda ba.."Hafsah tayi yaken Dole lokaci Daya tana Fadin"Hmm Kema Subai da wata mgana kike ina ce kin Rigani sanin Halin yayanku kaifi Daya ne in yace Abu toh hakan take ba Chanzawa Tunda yace bazani ba Toh fa din bazani ba Sai dai wani Lokacin kawai..'Subai tace"Kai kai..Ya Abdullahi Danja ko Daru ne ma Zance.."Sai da ta Fada kana ta koma tana Rufe baki Lokaci Daya Tana kallon Hanyar Bedroom din Hafsah idanuwanta Duk suna waje

Mikewa tayi tana Saba Saleem Lokaci Daya Tana Fadin"Zan tafi Hafsah in naje zan gayamata kin so Zuwa yayanmu yayi Tsiya.."Tafada tana yar dariya Hafsah ma yaken tayi ta mike tana Fadin"Allah kaiku lafiya ya Dawo daku lafiya..ki gaishemin da ita Don Allah."Subai tace"Zataji insha Allahu sai ki lallabasa ya barki zuwa suna mu Tafi Tun ana gobe mu dawo Washegarin suna.."

Kai kawai Hafsah ta Kada kafin tace"Wa..? Lalle nema ina ma laifin Ranar suna mu kwana Daya bazai barni ba zai ce Ko Biki ne iyakarta kenan.."Subai tace"Gaskiya Qawata ina jinjina miki wajen Fama da yayanmu Wlh bazan iya ba.."Tafada tana Bata rai Hafsah batayi Mgana ba illah kada kai kawai datayi.


Tsakar gida suka Fito Subai na kara Saba Saleem Bisa kafadarta Tana Fadin"Lokacin muna gida munci Ubanmu ammh Mariya tace Har gwara kila lokacinmu yanzu basu da wani Motsi ko Fita Zakayi sai da izininsa Auwal ya Fadamin Jidda ce kecin kwal ubanta a wajensa.."Ta karishe tana yar Dariya Kada kai Hafsah Kawai Hafsah tayi tana Fadin"Ai fa..Sai ta rika kiyayewa kamar kowa.."

Har Kofar gida Hafsah ta Raka Subai Tana Dagamata Hannu,Har Motarsu ta bace ma ganinta kana ta koma Cikin Gida,Tana Shiga Suka ci karo da Abdullahi ya yo Shirinsa na zuwa Office sabe da Jakar Breifcase dinsa,Ko kallonsa batayi ba kawai ta saka kai ta Shige Dakin su Amira ta Shige ta Haye yar katifarsu kawai ta fashe da kukan Data ke ta Rikewa tun dazu Labulan Dakin ya Daga yana kallonta Cikin mamaki,sai da yadan Jima kafin ya kada kai yana Fadin"In kin gama kukan Jin Dadin ni na Fita.."Daga haka kawai ya sauke Labulen ya Fice Tana daga kwance ko Dagowa batayi ba Ballatana ta amsa mai.

Tana jinsa ya bude Dakin da Mashin Dinsa yake ya Fito Dashi ya Goggoge ta kafin ya Fice Tana Jin Tashin Mashin din nashi da kuma Tafiyarsa ammh bata Daga ba,Sai da tayi kukanta ya Isheta kana ta Share Hawayenta Tana Nan kwance Taji wayarta na Ringing Daga Falo ta Fito ta Dauki Wayar ganin Umman Sadiq yasa ta gyara muryanta ta Daga Kiran suka gaisa nan take tambayanta su Amira tace suna makaranta,ita Hafsah ke gayamata Haihuwan Zannira Umman Sadiq din tace ai mama ta Kirata ta gayamata in ta samu Dama Zatazo tayi barka Zahra ce batajin Dadi nan Hafsah ta mata ya Jiki basu Dade suna mgana ba sukayi sallama.

Agaskiya Hafsah tayi Dacen Surukan kwarai baga Mama ba baga Ummin sadiq ba wanda Duk kwannan Duniya sai ta Kirata taji ya suke..? Matar bata da matsala ne sosai,Abdullahi ma Suna yawan mgana Sosai,Duk da in ba ya Fada ba ba wanda zai ce Ba Mama bace ta Haifesa ba Saboda bai Taba nuna wani bambamci tsskanin Mama da Umman Sadiq ba,Gidan kakaninsa kuwa yana Zuwa Sosai yaje ya Wuni ya Dawo,koda bazai kwana ba Harda Nazifi sun sha Zuwa in sukaje yaBiya yaga Umman Sadiq sai dai in sun Daawo Hafsah taga sako inji mama kana zata san sun je gusai aranar.

Har yammah Hafsah bata saki ba ko Girki batayi ba,Complex ta jikama su Amira suka Sha Bayan sun Dawo Daga makaranta Subai"atu kuwa ta isa kaduna Lafiya ta samu ma an sallami Zanniratun ta koma Gida,Da taga Subai ita kadai sai da ta tambayi Hafsah Wanda daman Ita Subai din ta mata waya kan tare zasu zo nan Subai take basu labarin Abunda ya Faru baki Zanniratu ta Rike kafin tace"Na Shiga goma ni Zanniratu dama wai Har yanzu Ya Abdullahi bai chanza Halinsa ba..?

Mariya na gefe tace"Sai ma Abunda ya karu Anty...Kinsan Allah da bai amunce ba da ko ke bazan zo na zauna miki ba.."Zanniratu tace"Lalle ya Abdullahi isar nan da ikonsa Na nan Tare dashi Haka Aliyu na ke Fadin Yayan naku ya cika Fadin rai da isa ni kuma nayi ta karesa Duk da dai nasan gaskiya ya fada,nima Jiya Daya Kirani yayi min Barka Kunsan me yace min..?


Gabadayansu suka Girgiza kai Cikin Takaichi tace"Wai ina Dauka sai cemin yayi mai cikin Haihuwa..Nace kamar ya Ya Abdullahi..? Bude bakinsa sai cewa yayi Wai na cika haihuwa duka duka yaushe nayi Auran har nayi ya"ya har Biyar..?Subai da mariya suka saka Dariya kamar Cikinsu ya kulle Mariya tace"Kadan Daga aikin Ya Abdullahi kenan Anty Zanniratu..
"

Subai tace"Yau ai naga lukutar masifa..Kiri kiri yace Hausi baza je ba....Sai dai in mu sauya Ranar Tafiya.."Zanniratu tace"Allah sa ya Barta zuwa suna Toh.."Subai tace"Yace in ta nemi izini ya yarje zata zo...In kuma ta karamai irin na wannan karon yama Rantse bazataje ba...."Mariya tace"Kuma ya gama mgana Wlh..Kaifi Daya nan ba"a sauyata.."

Zanniratu tace"Ni wlh na zata ya sauya..ashe Hali na nan..Don ma Hafsah mai hakuri ne da yanzu anji kansu.."Mariya tace"In batayi Hakuri ba ya zatayi Anty..? Ya Abdullahi ya wuce Duk Tunaninki kan Ra"ayinsa da Jin kansa da isarsa uwa uba kuma Masifarsa kowa neman Tsari yake da Ita Har ya Auwal kuwa.."

Zanniratu tace"Allah ya kyauta..ni Lokacina Abunsa bai kai Haka ba Ko domin ina kiyaye masa ne,Ammh nifa Lokacin kan Samari munsha Fama dashi Sosai Sai da nayi Aure kuma Komai ya kare.."Mariya tace"Yanzu ai Jidda ce ke shan Wahalarsa.."Nan ta Shiga Basu labarin Abunda ya Faru Ranar har Yaya Nazifi ya kwaceta.

Subai tace"Wai ni Nazifin ya suka kare da wannan yar Jinkan matar nashi..? Tanan tana aikin nata a Abujan kenan..? Mariya tace"Eh gaskiya tana Abujan..kwanaki naji inna Abu tazo suna mganar da Mama kan cewa Tana Abuja sai dai in Yaya Nazifin ya samu Lokaci yaje mata Weekend.."


Zanniratu tace"Tabdijam...wannan wani irin Aure ne anyi ba'ayi ba kenam.."Subai tace"Ke Duk Abunda ya Faru shi yajama kansa...Auran jari yayi sai kuma yaga karshensa.."Mariya tace"Haka ake ta Fadi ma a anguwa..mudai shuru muke aminin ya Abdullahi ne karka Tofa mgana takai mai Shima irin ya Abdullahi ne akwai son Girma.."Gabadayansu suka Sheke Da Dariyan Nishadi da ka gansu kaga yan"uwa Da suke tsananin Son Junansu Jaririyar na Hannun Subai Shi kuma Saleem na Hannun Mariya sun kule Cikin Bedroom Falo kuma Kanwar mijinta ne sai wata yar Dattijuwa da uwar mijinta ta Turo mata ta zauna mata na sati Tunda aiki aka mata.

Bangaren Hafsah kuwa Har Abdullahi ya Dawo ya Isketa batayi Girki ba kuma ko wanka bata sake ba Tun kayan Shirin Zuwa kaduna barka ne ajikinta.

Bayan Sallar Isha"i ya Dawo koda ya Shigo Amir yayi barci sai Amira ta Rugo tana mai oyoyo ya Tarbeta ya Dauketa yana Tambayanta Amir tace yayi barci Sun kariso Tsakiyar Falon inda Hafsah ke zaune tana latsa wayarta Amira tace"Abba ina jin yunwa..".

Kai Tsaye Abdullahi ya kalli Hafsah Cikin mamaki yana Fadin"Baki yi girki bane..? Amira ke kukan yunwa fa kina jinta ."Batare da ta Dago ba tace"Ban girka ba.."Galala yayi yana kallonta kafin yace"Saboda mene..?kai Tsaye Hafsah tace"Bakomai kawai Ra"ayi.."Shi yama manta Abunda ya Faru da safe Cikin kulawa yace"Baki lafiya ne..?

Kai ta girgizamai kafin tace"lafiyata kalau..."Jin haka yasa ya gane Rainin Wayau ne kawai, kawai sai ya kada kai ya Sauke Amira yana Fadin"Kinga Mamata bari na fita na siyo miki abinci ban Riko muku komai ba na manta.."Sauketa yayi Lokaci Daya yana Barin Falon tana jinsa yakara Fita Da mashin din nasa batare daya ma kara kallon Barayin Datake ba.










*Shakira...*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*

*Wattpad:JamilaUmar351*
*Janafty*❤️

*Dedicated To:My Habibaty💞Aisha Idris Abdullahi..*!

*Godiya Tare da Jinjina mai Hade da Fatan alheri zuwa gareku Dimbim Masoyana na Nesa Dana kusa,Hakika naga Salon Soyayyarku ga wannan D'an karamin Labarin nawa mai Taken MASIFAFFAN MIJIN HAFSATU...❤️,Ina godiya Sosai ga Sharhinku da kuma Kayattacen Sakonninku Na Soyayyah da kauna zuwa gareni Nagode Sosai Allah ya saka da alheri Godiya Gareku Masoyana na Wattpad da kuma WhatsApp,Allahu ya bar Zumunci Janaftyshakira nayi musu Son Kauna Mara iyaka...*

*012*

 
"Tana nan Zaune har ya Dawo Dauke da Ledoji Guda Biyu,Koda ya Dawo Amira tayi barci Tashinta yayi ya bata Ledan mai Dauke da gasshiyar kaza,sai Take away din Jalop din Shinfaka sai Fura.

Sai da yaba Amira taci ta Koshi kana yaci Sauran ya Tada ita yakaita Tailet tayi Fitsari ta wanke Hannunta da Bakinta Da kanshi yakaita Dakinsu ita da Amir Daya Rigata yin Barci Hafsah na Zaune yazo ya wuceta ko kallo Bata ishesa ba itama Haka Bata kara Bi ta kansa ba sai ma ta Kishingide kamar mai Barci Saboda Bacin Ran Abunda ya mata Haka kurum Taji bazata iya Controling Din Fushinta akan karfin Ikon da Abdullahi ke nuna mata Lokaci Bayan Lokaci ba.

Sai wajen 12am na Dare kana ta mike ta Tattara Lodojin da suka barsu nan Tsakar Dakin ko Kazar basu Cinye ba da Shinkafar,Ta kwashe komai ta Kai Kicthen ta saka Cikin Fridge din Kana Ta Rufe Kitchen ta Dawo Daki ta kashe Wutar waje ta kashe na Falon Lokaci Daya ta Kulle kofar Falon Dakinsu Amira ta Shiga ta gyaramusu kwanciya Hade da yi musu addu"a,kana ta Fito ta Shiga Bedroom dinsu ta iske Tuni Abdullahi ya Dade da yin Barcinsa mamaki ya kamata wato Ita ke kidanta Tana Rawanta bai ma Damu ba kyafci tayi ta Shiga Taiolet Tayi wanka Lokaci Daya ta Dauro alwala tazo Tayi Shafa"i da wuturi Ta Dauki Filo ta Jefa kasa ta kwanta Bayan Ta Dauki Blanket ta Rufu Dashi.

Da asuba da Abdullahi ya tashi yaga Hafsah a kasan Cafet Tana Barci Mirmishin Takaichi yayi acikin Ransa kuma yana Fadin zan koya miki Hankali Hafsah ko Kallonta baiyi ba ya Shiga Toilet yayi wanka Tare da Dauro alwala yazo ya saka Jallabiya ya tsallake Hafsah zuwa masallaci sai bayan ya Fita ne Hafsah tatashi itama ta Shiga tayi wanka tazo ta Tada salla,Ganin har wasu masallatan sun Tada sallah.

Bai Dawo masallaci da wuri ba Sai da Haske ya bayyana koda ya Dawo Tagama komai hatta su Amira sun Shirya Jiransa kadai suke shima Sama sama ya Shirya ya kwashesu zuwa makaranta Dagachan ya wuce wajen aiki,Haka Zamansu ya kasance Hafsah ita ta Dauko Tsiyan sai Abdullahi ya nuna mata yafi ta sanin kan Tsiya Shima kawai ya Fita Batunta yayi Banza da ita bai ma Nuna yasan me take ma Fushi ba.

Dole kanwar naki Hafsah ta watsar da Tsiyan nata ganin Uban gayyar dai bazai Kalleta ba Ballatama ya bata Hakuri Ranar data Fara gaisheshi da safe kafin ya amsa sai da ya murmusa Lokaci Daya yana Fadin"Lafiya lau Hausi...Kin gama Gaban dani..? Shagwabe mai kawai tayi Lokaci Daya da Hararansa Batace komai ba Shima kawai sai ya Biyemata Kamar Babu Abunda ya Faru,Ganin yasa Hafsah ta Sakankace cewa Abdullahi zai barta Zuwa Suna.

Ana Gobe Suna Subai"a ta Kirata awaya Tana gayama ta Gobe ne zasu Tafi sunan Saboda Mama tace su Tsaya su Tafinma da Anty Zanniratun Sako Zuwa Gobe,Tace mata Su Hadu gidan mama Gobe da Misalin karfe 8am na safe Nan Sukayi sallama,nan take Hafsah ta Kira Ammi tana Fadamata itama kuma Tace zata Turo Direba da sako ya kawomata ta kaima Zanniratun In ta samu Lokaci ko Bayan suna Hafsah zata Rakata Taje ta mata barka.

Zuwa Yammah Ammi ta aiko Da sakon Atamfofi Guda Biyu masu kyau da Tsada sai Babban pampers mai Guda 50,Da Rigan yarinya mai kyau itama Hafsah tayi ta Jin Dadi,tace ta Huta Siyan wani abu sai tace ita Da Ammi kuma Daman ta sani Harda natan Ammi ta Hado sanin ba wata sana"a takeyi ba Duk da Babu Abunda ta nema ta rasa Abdullahi ya Tare mata gaba da baya Sai dai Abunda Ba"a Rasa ba.

Abdullahi na Dawowa ta kwaso kayan Tana nunamai Ya amsa ya gani yayi Godiya nan yake gayamata ya bama Mama 15k ta hada ta siyan ma Zanniran wani Abu sai a aikamata Dashi,Danashi dana Hafsah nan tayimai Godiya Bata gayamai Zuwa Zencen Sunan gobe ba sai da zasu kwanta kana ta gayamai bai ce mata komai ba yace Allah ya kaimu Sai da safe Bayan ta gama Shiryawa Ranar ma bashi ya Kai su Amira makaranta ba Mai mashin dinsu ya kaisu Yana kallon Hafsah tana ta Shiryawa sai da Tagama Shirya kayanta Cikin Karamin akwatinta na Kayanta kala Daya da Hijabi wanda zata Sauya na gobe sai sakon Ammi.

Abdullahi ma Shirin Fitan yake Domin ya gayamata Za"a Fara Ginin Gidanshi na Gra,Domin har an kawo Siminti da Bulo,da kasa Tun Shekaran jiya zai Fara Biyawa Yayi mgana da ma"aikatan kafin ya wuce wajen aiki,Subai"atu sai kira take tana Fadin Hafsah tayi Sauri Gata Gidan Mama.

Sai da ya Bari ta saka Hijabi kana ya kalleta yana Fadin"Wai ina zaki ne naga kina saka Hijabi..?Cikin Dariya Hafsah tace"Kaima da wata mgana..Yau ne fa Sunan Zannira baka ga Subai ma Sai Kirana take ba Suna Gidan Mama suna Jirana."Kai Tsaye yace mata"Au kin gama Fushin Dani ne..? Yafada yana kallonta kai Tsaye jin haka yasa Jikinta yayi sanyi tayi galala tana kallonsa yana Saka Takalminsa Sawu Ciki yake Fadin"Babu inda zaki...Tunda har ni nan zan Hanaki Abunda iko na ne ammh ki Nuna min ban yi Daidai ba ki Dauki gabadani na kwanaki Kidaina Dafa abinci kina ma ya"yanmu Horo da yunwa Saboda Ni na Haifesu ko..?

Yafada Lokaci Daya yana mikewa Ido ya sakarmata ganin Har Hawayen Idanuwanta sun Fara Zubowa Cikin Bacin Rai ya Cigaba da Fadin"Kyaleki nayi naga iya Gudun Ruwanki...naga inda karshen Tsiyanki zai kai ashe Babu inda zai kai...Na bari ne dama sai kin gama naki ni kuma na Fara nawa..Suna ne Bazaki ba..Sai na gani Tsakanin Hafsah da Abdullahi wanene ke Auran wani.."Yana gama Fadin Haka ya kwashi Jakarsa da Key din Mashin sa ya Fice yana Fadin"Yau ma ki Dauki Gaban dani..Karki Dafa komai ki bar yaran da yunwa kinji ko.."

Daga haka ya fice ya barta nan Taaye tana Tsiyayan Hawaye,Tana Jinsa ya Fito da mashinsa ya Fice Bata san sadda wani kukan bakinciki ya Turniketa ba,Ta Fada kan gado kawai ta sakeshi wiwi kamar karamar yarinya wani Bakinciki da Takaichi na cin Ranta da Zuciyarta Tana Cikin kukan ne Taji karar wayarta Ta Dago kanta Shabe Shabe da Hawaye ta Jawo Jakarta Inda tasaka Wayarta ta Bude ta Dauko sai taga Ammi ne ke Kiranta da Sauri Ta Daga Kiran Lokaci Daya Ammi na Fadin"Hafsah kun tafi ne..?

Jin Haka yasa wani kukan ya kara Zuwarma Hafsah kawai sai ta sakarma Ammi kuka Cikin Firgici da tashin Hankali Ammi ke Fadin"Innalillahi...Hafsah meya faru..? Ina Abdullahin..?ko wani Abu ne ya Faru daku..?

Duk atare Ammi ta Jero mata wadanan Tambayoyi,Ammh Hafsah ta kasa mgana Saboda kuka Cikin Tsawa Ammi tace"Dallah kiyi mgana lafiya kike ma mutane kuka..?
Jin haka yasa Hafsah tace"Ammi..Ya hanani zuwa Sunan ne..."Tafada Cikin Shesshekan kuka Wani Karamin Tsaki Ammi Taja Lokaci Daya tana Fadin"To Shine kuma Abun kuka..? Nifa har kin saka gabana ya Fadi Allah yasa Daddynku yana Barci kila da kin saka Jininsa ya Hau in yaji wannan Shirmen naki.."Cikin kuka Hafsah ta kara Fadin"Ammi Ranar fa Haka ya hanani zuwa barka yauma har na Shirya yace bazani ba.."Ammi tace"Sai me.
? Sai me in ya Hanaki..? Inace ba kanwarsa bace da suke Uba Daya..? Yafi ki son kije wajen yar"uwansa kuma yahanaki sai kiyi Hakuri ki zauna Ranar daya Lamunce miki sai KiTafi Hafsah.."Cikin Takaichi Hafsah tace"Ammi Su Subai na chan gidan Mama suna Jirana kuma kowa zai je Ammi sai ni kadai sai ya Hanani.."

Ammi tace"Tsiyana Dake sakarci Maman Hamzana,Suna yafi Mijinki ne..? Kuma na Tabbata wani Laifin kikemai Shiyasa ya Hanaki Zuwa Sunar ko...?

Shuru Hafsah tayi taki mgana Jin Haka yasa Ammi tace"Hmm ni na sani..Meyasa Hafsah wani Lokacin kin cika Wauta ne..! Karfa ki manta ke matar aure ce wacce ke karkashin mijinta akullum ina gaya miki Aljannarki Tana karkashin Kafar mijinki ne,sai ya Daga Zaki Shiga,kuma Aure Bautar Allah ne,Kuma Shi Aure dan Hakuri ne kinga in kikace bazaki yi Hakuri ba Wlh zaki Sha Wahala ne kawai Hafsah.."

Tura baki Hafsah tayi kafin tace"Toh ni Ammi me nake mai..Iya Biyayyah Wlh ina yi da Hakurin da kikace.."Ammi tace"Toh in kinayi me ye na kuka Saboda yace bazaki suna ba..? In kina yi sai kiyi Hakuri  ki Share Hawaye dama ai Aure ya gaji Haka.."Cikin Marairaicewa Hafsah tace"To Don Allah Ammi ki Kirashi ki Rokeshi Da Allah da Annabi ya barni naje.."Ammi ta Rike Baki Tana Fadin"Ni Jikar Hadiza..? Rufamin asiri Abdullahi na ganina da kima Ina Ruwana da Shiga Hurumin da ba nawa ba..? Yanzu bamu da iko akanki Hausi Kin bar karkashin ikonmu Tun Ranar da igiya uku ta Hau kanki kikabar Karkashinmu Zuwa karkashin Mijinki,Saboda haka yafimu iko Dake.."Bakin Hafsah kamar ya Fado Tace,"Kai Ammi yanzu dai baki Kiransa ko..?

Ammi tace"A"a wlh karya da Ciwo..Na kirasa nace mai me..? Haka kurum Jama kai Raini da lalacewa sai na Kirashi nayi mai mgana kan Abunda yake da iko akansa..?ko Babanki yaji labari sai ya batamin rai bakisan kwanciyar Hankalinsa da nawa Ba Yana da Nasaba da Kowaccenku tana zaune lafiya Gidan Mijinta ba  kuma Dukkanku kun yi sa"an Mazaje na gari ya"yan albarka Da Dangin Mijin na gari nan Shekaran jiya Abdullahi yazo yana gayama Babanki Ya siya Fili a Gra har zai Fara Gini Dukkanmu muka sakamai albarka kinsan anyi..?

Ta karishe Fada da Sigan Tambaya Hafsah tace"Bansani ba Ammi..'Ammi tace"Toh Ina laifinsa...kiyi maza ki Share hawayenki ki kirasu kice su tafi Baxaki samu zuwa ba In Ya dawo kin Lallabasa in ya barki bayan suna sai Ki rakani muje mu mata wuni mu Dawo.."Hafsah tace"Shikenan Ammi nagode..Ki gaida Daddy in ya tashi..Anty Hadiza Shuru bata Haihu ba..?

Ammi na Dariya tace"Sai ki kirata kice mata taki Haihuwa..inaga Cikinta da Sauransa bai wuce wata Takwas bafa Girman ciki ne da ita irin na Walid ne..'"Hafsah tace"Na kosa ta Haihu naje Kano na Rabu da Zuwa Kano Ammi Tun sanda Anty Hadiza ta Dawo Daga Saudiya.."Ammi tace"Toh shine me..? baku na waya da juna ba..?

Hafsah tace"Eh Ammi.."Ammi tace"Toh banga Abun Damuwa ba..Kowa ya zauna agidan Auransa yaci gaba da Bautar Aure.."Baki kawai Hafsah ta Tura Ammi Kuma ta Fara Fadin"Umm.Auta..Autan Zinariya Autan Hamza kuma Maman Hamza..Kuma kanwar Hadiza Ko Hausi.."Jin Kirarin Ammi yasa Hafsah ta manta bacin Ranta ta Shiga Dariya Ammi bata kashe wayarta ba sai da ta tabbatar da Hafsah ta saki Ranta.

Suna gama Waya da Ammi Hafsah taci karo da Kiran Subai"atu wajen Guda Biyar Lokacin tana waya,Da sauri ta Kirata Tana Daga Kiran Subai tace"Wai Gimbiya matar Ya Abdullahi ko kin Fasa zuwa ne..? Kefa muke ta Jira Har yanzu baki kariso ba..?
Cikin sanyin Murya Hafsah tace"Ku tafi kawai Subai...Bazan samu zuwa ba..'Cikin mamaki Subai tace"Bangane mu tafi ba kawai..? Ko Ya Abdullahin ya hanaki ne..?

Hafsah tace"Eh yace bazani ba..Ku tafi kawai in kunje ku gaisheta,Kuyi Hakuri da bata muku Lokacin danayi Kuma Don Allah in zaku iya ku Biyo ku karbi sakon Ammi ku kaima Zanniran.."Subai tayi karamin Tsaki kafin tace"Bansan Meyasa Ya Abdullahi ke haka ba sam..."Hafsah dai Shuru tayi batayi mgana ba Subai tace"Shikenan in da yuyuwa zamu Biyo..Baya dai kyautawa.."Tana jin Mama na Tambayan me yafaru Subai na Fadamata yadda Hafsah ta Fadamata bata tsaya Jin me Mama ke Cewa ba ta kashe wayarta kawai.

Tana nan Zaune Har su Subai"a suka kariso basu wani Tsaya ba Ta basu sakon Ammi da 3k cikin kudinta Data ke dashi tace su kaima Zanniran,Har waje ta karasu Ita da Direban Mahmud ne,sai Jidda,Da inna Abu sai Inna Talatu wata kanwar Mama ce,Tana Daga musu Hannu suka kule ma ganinta kana ta koma Cikin Gida ta Shiga Falonta kenan Wayarta ta sake neman agaji,Tana Dubawa taga Umman Sadiq ce ta Daga suka gaisa Kana Umman Sadiq ke Tambayan Hafsah ya Suna..?

Hafsah tace"Bata je ba tana gida..? Cikin mamaki Umman Sadiq ke fadin"Kina gida?toh saboda mene baki je sunan ba..? Ko ba yau bane Sunan Zanniratun..?

Hafsah tace"Yau ne Umman..Har na Shirya sai yace bai yarda naje ba..Su Subai"atun ma sun wuce yanzu.."Umman Sadiq bata Jira cewar Hafsah ba kawai ta yanke Kiran ta Kira Abdullahi Lokacin yana Office yana Tsaka da aiki yaga Kiran Umman Sadiq bayan ya Daga sun gaisa kai Tsaye tace'"Meyasa kake Tauye Yarinyarnan ne Abdullahi..?

Jin Tambayar nata yayi ta mishi bambarakwai cikin mamaki yace"Wata yarinya kuma Umma..? Cikin Takaichi tace"Kaniyarka nace..Kaji ko..? Nace kaci Gidanku Abdullahi.."Jin Haka yasa ya natsu yana Sosa kansa Cikin Lallashi yace"Umma kiyi Hakuri Don Allah bangane inda mganarki ta Dosa bane.."Umman Sadiq tace"Miye Dalilinka na Hana Hafsah zuwa Wajen sunan Zannira Kowa ya tafi sai ita kadai..?

Jin haka yasa ya gane bakin Zarensa Ransa ya baci wato Kararsa Hafsah takai kenan lalle Cikin Saukar da kai yace"Umma ki kyaleta Hafsah

Please Login or Register in order to submit comment