Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tana Fadin"Tsiyata da Qawata wauta yaushe zaki bar Karamin yaro Shi kadai Cikin Falo ke ki tafi naki Sabgar..? Ga Iska ko ta ko"ina nata Kadawa Cikin Falon.."

Tafada Lokaci Daya Tana karisawa ta kashe Fankar Falon ta kuma Dauki Rimot din A.C ta kashe kana ta Sauke Jakar Hannunta da Ledan ta zauna ta Sunkuci yaron Bisa Hannunta Tana kallonsa sai Sharan Barcinsa yake Hankali kwance yaci wasu kayan Sanyi masu kyau sai Tashin kamshi yake yi Yaron sak Babanshi ne Hasken Fatan Subai kadai ya Debo.

Bata Jima Zaune ba sai ga Subai Ta Fito Daga Cikin Bedroom Dinta Tana wani Taku Daidai da Waya a Hannunta mamaki ya sandarar da ita ganin Hafsah zaune Dauke da Salim Baki ta saki Tana kallonta tama kasa karisowa Dariya ta kama Hafsah ta Bude baki Tana Fadin"Rufe baki Kuna ki Karaso sakarya Uwa kawai.."Da Sauri Subai ta karisa Gareta ta Fada gefenta Ta Rumgumeta tana Fadin"Innalillahi kai Qawas kin Bani Mamaki ne sai na ganki kamar Daga sama Wlh.."...

Tafada Cikin Wani Farinciki Daya kasa Boyuwa acikin Ranta Hafsah Ta Saki Mirmishi kafin Tace"Mamakin dama nake so na Baki Shiyasa ban Hidi miki gani Tafe ba..Sai nazo na iske kin bar yaro shi kadai Cikin Falo kuma kin kure Fanka da A.C ko..? Jego kike yi ne Subai ko kuwa Danyan Iskancin Jego ko..?

Wata Dariya Subai ta saki kafin tace"Kaji yar rainin wayau..Wai ke Hafsah kemin Fadan Yara..?Don Kaniyarki Koda kika yi Aure na Haihu so banga me zaki Fadamin ba.."Tafada tana Dariyarta Harara Hafsah ta sakarmata kafin tace"Waya gayamiki bata Daganan Wlh..banga alaman kin san komai ba Tunda kika bar Jariri Dayan Haihuwa Shi kadai kuma kika sakarmai sanyi ba zaki sani ne in sanyi ya kamashi ke zaki Dinga jelan zuwa Asibiti Allah na Tuba bama Fata.."Subai tace"Naji Zan gyara Mu bar mganar..Allah laifin Honey ne shi fa na barmawa na Shiga wanka Kinga sai ya ijiyeshi nan ya Fice abunshi.."Hafsah tace"Mun hadu dashi da zan Shigo Har muka gaisa Shima yana tamin Tsiya ke Subai kiji Tsoron Allah kin gama Barbadini  a Duniya ko..?

Wata Dariyan Iskanci Subai ta kara Saki kafin tace"Yo Uban wa yaja ma kansa..? In da kinzo ai bazakiji korafi na ba ballatana Honey  yaji Wlh ya san baki zo ba Daga ke har shi Uban gayyar wanda baki san laifinsa Yaya Abdullahi.."Hafsah tace"Kya dai ji Dashi Malama Na dai wanke Duka laifin gani nazo yau nan zan Wuni musha Fira.."Subai tace"Allah naji Dadi Sosai..Dama kamar kinsan ina nemanki.."

Hafsah tace"Lafiya kuwa..? Subai tace"Da sauki mu gaisa Tukunnah..Zamuyi Zencen Daga Baya.."Daganan suka Fara gaisawa da Tambayan gida da yara,Hafsah tace"Ina muhsin da Muhsina..? Subai tace"Suna Makaranta sai anjuma zasu Dawo..Ina su Amira Nayi ma Yaya Abdullahi mganar su zo min Weeked kuma naji Shuru.."

Hafsah tace"Ban ma sani ba Wlh...Wanchan weekend din a Tudun wada sukayi shiyasa ammh Insha Allahu zasu zo.."Subai tace"Allah ya yarda.."Daganan suka cigaba da Hiransu ta kawaye Hafsah ta bata Atamfar Data zo mata Dashi Ta karba Tana mata Godiya Cikin Fara"a Take fadin"Masha Allah matar Babban Yaya harda Wata Dawaniya Salim yayi Goshi Allah ya saka da alheri.."Hafsah Ta karba da Ameen.

Tare Sukayi Girkin Rana Suna yi Suna Hira Acikin Hirar ne Subai take gayama Hafsah wannan Shekaran Mahmud yace zata Dora karatunta,Hafsah ta kalleta Cikin Fara"a tana Fadin"Kai kai na tayaki Murna kawas wlh..Kinyi Sa"a ke mijinki ya barki zaki Dora karatunki Allah ya  Bada sa"a yasa afara Cikin Nasara.."

Subai tace"Ameen kawata kema kici gaba da naci in kinci Sa"a kila yaya Abdullahi ya barki kicigaba kinga sau mu Dora tare,kinga ma kin Fini Fita da sakamako mai kyau aji Biyu Direct zaki samu Kawata.."Hafsah tace"Hmm bari kawai Kawas..kin fa san Halin yayan naki wlh bazai bari ba.."

Subai tace"Gaskiya ne ai yaya Abdullahi sai ke kawata...Yana da Wani Budadden Hali ne da Shegen Miskilanci zama Dashi sai mai Hakuri ammh ai illimi ba laifi bane in ya barki kin Cigaba kika samu aiki yau ai Ribarsa ne.."Hafsah tace"Kul karma ki bar yaji ki kina Fadin haka wlh sai ya Saba miki Shida yace Ko Da Kwalin Digree gareni Wlh Tunda na Aureshi bazai min amfaani ba Mace bata karatu Gidansa kuma bata aiki.."Subai tace"Uhum..Gaskiya yaya Abdullahi nada Tsauttsauran Ra"ayi kamar ba Dan Boko ba.Su mariya suna Complain dinsa Takura musu yake sosai sunce kila har gwara lokacin mu ni da Anty Zannira nace ba gwara wlh muma munsha wannan Saka idon da Takuran na Yaya Abdullahi.."Hafsah tace"wannan kuma bai yi laifi ba matsayin Uba yake gareku.."Hararanta Subai Tayi Ita kuma Hafsah ta sakamata Dariya.

Sai da suka gama Abincin suka ci sukayi Salla kana suka Zauna zaman Hira Subai na Dauke da Salim tana bashi Nono tace"Honey yayi nisan zango kinga har yanzu bai Shigo ba...?Hafsah Tace"Kuma yace min gida zai je bazai Dade ba zai Dawo ba.."Subai ta tabe baki kafin tace'"Ai bazasu barshi ya Taho ba..Wannan Shegiyar yayar nashi Bazata barshi ba Dama tace na mallakeshi bayajin mganar kowa sai Tawa.."..

Hafsah tace"Subhanallah Wacce Daga Ciki kuma..? Subai tace"Anty Uwani babar yayarsu mana..Wlh kawata Matarnan ta Fara Shigarmin Hanci da Majina na Ta isheni.."Tafada Cikin Damuwa da Bacin rai Hafsah tace"Toh duk mai ya kawo haka..?

Subai tace"Ohon mata bai wuce Rainin arziki mana Dama Tana ta Fadin wai yaje ya kwaso musu Diyar Direba mai Auri saki,gidanmu gidan Takalawa kuma matsiyata ai kinsan Tana India wajen jinyar mijinta akayi mganar Aurenmu da Honey kuma tana chan akayi Auren Toh Tunda ta Dawo Shikenan Idonta ya kawo kaina Matarnan bansan me na Tsareta mata ba in da Honey zai Bi nata mganar toh da yanzu ya Rabu dani.."

Subai ta karishe Mganar Cikin Taruwar kwalla Hafsha tace"Innalillahi Abu baiyi Dadi ba wannan ai Tozarci ne..Toh in ya sakeki ta aura mai wa..? Subai tace'Kanwar mijinta mana..Samira ta Fadamin kanwar mijinta wacce take karatu a lagos ita keson Honey kamar ta mutu Ita Anty Uwani taso ta Hada Abun Shi kuma yaki ya Nuna Baya Ra"ayi sai kuma Rashin lafiyar mijinta ya taso suka Tafi India Ciwon Sugar yake Fama Dashi Chan suka Rikesa wajen Shekara koda ta komo anyi Auren mu nan fa sai Bala"i take Daga karshe tace sai ya auri yarinyar shi kuma ya kiya Kinji fa Dalili yanzu Duk inda muka Hadu ta Dinga sakarmin mgana kenan Hafsah.."Tafada Hawayen Idanuwanta suna kawowa,Matsowa Kusa da Ita Hafsah Tayi Ta Dafa kafadanta Tana Fadin"Kiyi Hakuri kawata Bai kamata ki saka wannan Abun Aranki ballatana Har ya Dameki ba Kedai Allah ya gani Mijinki na Sonki Saboda haka ki Fidda kanki Cikin mganarsu ki barshi Shida yar"uwansa ne babu Ruwanki..".

Subai ta Sauke Salim kan Cinyarta ta mika Hafsah Shi Tana Fadin"Wlh kawata in Cin Mutumcinta Baya Taba Ahalina da asalina Ko Damuwa  Banyi ammh Cim mutumcin nata ya wuce kaina ya koma kan Ubana Dayake kasa Baisan meyake Faruwa ba,Ranar sunan wannan yaron fa Ya"yanta da Surukanta suka zo Gidanan baki ji Abunda suka Dinga Hidima su mariya ba wai Babanmu Auri saki ne Bakincikinsa ma ya kashe Uwata wai kuma Dukkanmu suna da Labari ba wacce uwarta ta Haifeta Gidan Ubanta Duk Daga Baya aka maidomu Don Allah Hafsah ya Dace nayi Shuru da wannan Cin Mutumcin da Tozarcin..? Tafada Idanuwanta suna kara Zubar kwallah.

Hafsah tace"Gaskiya bai Dace ba kam..Ammh Shawarata gareki ki saka musu ido ko Mahmud din karki Fadamawa..In kika yi musu Banza kika Nuna bama kisan Sunayi ba Wlh su da kansu in suka Gaji zasu Daina.."Subai tace"Ina Wlh ban iya wannan Shegen Hakurin irin naki Hafsah..Sai da na gayama Honey Kuma ya Bisu har gida yaci musu Zarafi itama Anty Uwani sai da sukayi ba Dadi Dashi aie..Zan iya Hakuri Da komai ammh banda Zagin mu iyaye ai iyaye bai fi Iyaye kuma Ban Taba Cin Zarafin nashi iyayen ba kin ga kuwa Bai kamata na Zauna ana cin Zarafin nawa ba Har sai da Umminsa tazo Har Gidan nan tana Bani hakuri kuma tamin alkawarin Uwanin bazata kara ba.."Hafsah ta Rike baki kafin tace"Ke kawata Fitinarki nada yawa fa.."

Subai tace"Ah naki wasa ne Wlh kuka na sakamai Wiwi na Hada kaya nace ni Gidanmu zani Shine Hankalinsa ya Tashi ya Kira Ummi ta waya gayamata Shine tazo Taban Hakuri ta kuma Min alkawarin insha Allahu haka bazata Kara Faruwa ba.."Hafsah tace"Ke yanzu da ya barki da Danyen Jegon zaki komama Mama Gida..?

Subai tace"Kina wani Zence kawata..ai nasan bazai barni na Tafin bane.."Tafada tana Dariya Hafsah tace"Karyan Tsiya kike Subai Karki dai ki kuma irin Haka ba Dadi kin Dagama bawan Allah Hankali haka kurum.."Subai tace"An bari matar yaya ammh gwara da nayi ba gashi an ma Abun Tufkar Hanci ba.."Hafsah tace"Hakane..Allah ya kyauta na gaba Rayuwar ne sai Hakuri.."Da haka suka Cigaba da Hiransu Hankalinsu kwance sunayi Suna Shakiyansu da Suka saba in ka gansu zaka Fahinci ko Daman Chan suna da Shakuwa da kuma kyakyawan Fahimtar juna.

Basu Fahimci Lokaci yaja ba sai da Direbam gidansu Mahmud ya Dawo Daga Dauko su Muhsin Daga makaranta Suna Zaria acadamy ne,Tare da Yan Gidansu Mahmud din kannensa da kuma ya"yan yayyinsa Toh Duk mota Daya kai kaisu kuma ta koma ta Daukosu ta maida kowa Gidansu,Suna Dawowa suna ta murnan ganin Umma Wato Hafsah kenan suna Tsalle Tsalle abinci kadai sukaci sai kiran Sallar La"asar,sukayi salla kuma aka kwashesu Zuwa islamiya Itama Hafsah bayan ta idar da salla tace zata tafi Gidan Mama Subai Tace bata isa ba Ai Wuni tace mata zatayi Bazata tafi yanzu ba.

Hafsah ta kalleta tana Fadin"Yanzu Fisabilillahi Ban miki Wuni ba..? Tun karfe nawa nake gidanka ga..? Nafa gaya miki Su Amira na Gidan Mama kuma yayanki yace chan zai Je ya Daukomu mu koma Gida in yaje ban Dawo ba kema kin san Hali Dagani har ke Sai mun raina kanmu.."Subai ta Dauke Jakarta da Hijabinta tana Fadin"Eh din naji..Wlh Baki tahiya yanzu sai anjuma in Honey ya Shigo ya Sauke ki Gidan mama.."Hafsah Tayi tayi Subai"a ta bata Hijabinta da Jakarta taki sai ma ta kai Cikin Bedroom Dinta ta Kulle da makuli ta Fito Tana Dariya Hafsah ta Shaka Duk Ranta ba Dadi sanin Halin Gogan nata yanzu Ranta zai baci in batayi wasa ba.

Mahmud bai Dawo Gidan ba sai gabda mangariba Koda ya Dawo Hafsah ta gama Sadakarwa Kawai yau Ita da Abdullahi sai ta kauda kai kawai koda ya Shigo ya ganta nan Subai"a ke bashi labarin Abunda ta aikata Shima Biye mata yayi,sai da yayi Sallar mangariba suma sukayi Subai"a ta matsa mata sai da taci Dinner kana Ta Dauko mata Jakarta da Hijabinta tana Duba Wayarta Sai da Gabanta ya Fadi 7missed calls na Abdullahi harda Kiran Mama gabanta ya Fadi Jikinta ya kama Rawa Cikin Firgici tace"kingani ko Subai..? Yayanki sai kiran wayata yake harda Kiran Mama Wlh kila ma ya Dawo yaje chan bai ganni ba.."

Subai tace"Kwantar da Hankalinki Tare Dani zamu Rakaki har gidan mama.."Saboda Haushi ko Kulata Hafsah batayi ba ta Fice Subai ta Bita da Dariya Kaya ta Sauya ta Dauko mayafinta ta Nado Salim cikin Towel ta Fito Haraban Gidan inda Mahmud ke jiransu,Su muhsin basu Dawo ba kila suna wajen Ummi,Hafsah tana so tama Subai fadan Fita tana Jego ammh Hankalinta ba"a kwance yake ba yasa bata mata mgana ba suna ma Cikin motan sai kiran Abdullahi take yaki Daga Kiranta sai Cikinta kawai ya Kulle Zufa ya fara ketomata.

Subai"a nata Jefata Cikin Hirarsu ita da Mahmud hankalinta Baya Jikinta sai dai kawai tayi musu yake,Suna kawowa Kofar Gidan Mama da Abdullahi suka Fara Cin karo Shida Auwal suna Tsaye suna mgana Wutar motar ta Haske musu Fuska Subai tace"Hafsah mun Shige su ga Yaya Abdullahi nan wlh..."Ai Hafsah bata tsaya ma Sauraran Subai"a ba ta Balle Murfin Mota ta Fice motar ko Gama tsayawa batayi ba Subai"a ta Bita da kallo tana Girgiza kai Mahmud yace"wai duk Tsoron Fadan yayan namu ne Haka..?

Subai tace"Bama itaba nima kaina sai yanzu nake Nadamar Biyoka Har ni nan bazan Sha Daga Fadan yaya Abdullahi ba wlh.."Mahmud yayi dariya yana Kallonta Hafsah kuwa tana Fitowa Daga Motar ta nufi su Abdullahi Shi kuma Daman yana Ganin motar ya gane na Mijin Subai"a ne Ransa yabasa Cewa Hafsah suka Kawo dama Tun kafin mangariba ya taso Daga wajen aiki yana zuwa Mama tace Hafsah bata kariso ba Tukunnah Ransa ya baci ya dauki waya ya Kirata bata Daga ba gabadaya Zuciyarsa ta Fara tafasa kawai ya Fita zuwa masallaci sallar mangariba bayan sun idar ne yaga Kiranta yaki Dagawa suka Taho tare da Auwal Daya gani a masallacin suna mgana kan Shangonsa Dake Tudun wada sai gasu Hafsah.

Tunda ta Nufosu ya Hade Ransa tamau ba alamun Fara"a Auwal ne yana Hangota ya washe baki yana Fadin"la..yaya Abdullahi gama Anty Hafsah nan.."Yana jinsa kawai sai ma ya Juya ya Shiga Cikin Gida ya barsu nan Hafsah ta Bisu da kallo kafin ta kalli Auwal tana amsa gaisuwansa Cikin Firgici take Fadin"Yayanku ya Dade da Dawowa ne..?

Auwal yace"Wlh Anty Hafsah bansani a masallaci muka Hadu nima dawowata Shago kenan Dayake daga makaranta na Wuce.."Hafsah ta kada kai tana fadin"Allah sarki..ya karatun..? Yace"Alhamdulillah Anty..mun godema Allah..'Hafsah tace"Allah taimaka Bari na Shiga Ciki.."Daga haka ta Shiga Ciki Shi kuma ya karisa wajen su Subai da Mahmud Dake Tahowa ya amshi salim suna gaisuwa kafin suma su Shiga Cikin Gidan.

Hafsah tana Shiga Gidan ta Iske Abdullahi cikin Dakin Mama Su Amira najin sallamanta suka Rugo da Gudu suna mata oyoyo ta Rikesu Tana Fadin"yan Gidan mama yau kunsha ma mama wuni ko..? Tafada tana Sallama Dakin Mama wanda ke Haske da kwan Fitilan makarfi Domin Babu Wutar Nepa,Mama Dake Zaune kan Daya Daga Cikin kujerun Falon ta amsa sallaman Tana Fadin"Hafsah kin kariso..?

Tace"Eh Mama.."Tafada tana Satan kallon Abdullahi dake Zaune Akasa gefen mama kansa na kasa yana latsa wayarsa Gefensa Chan Nesa ta zauna Tana gaida mama ta amsa Tana Fadin"Ya dawo yana Tambayanki nace baki kariso ba Tukunnah...Kila Subai"atu ta Rike ki..'Hafsah tayi yake kafin tace"Eh Wlh Mama tun bayan La"asar na Shirya tahowa Subai ta Hanani Mama.."Tafada Tana kallon Abdullahi wanda ko kallo bata Isheshi ba.

Mariya ce ta Fito Daga Uwar Dakin Mama Tana Fadin"Anty Hafsah ina wuni.."Hafsah ta Dago Tana Fadin"Lafiya lau mariya ya Gida..? Ya kariniyan Su Amira..? Mariya tayi Dariya kafin tace"Mama ce tayi fama nima sai Yammah na Dawo daga makaranta.."Hafsah Zatayi mgana kenan Abdullahi yace ma Mama"Mama wai meyasa kike Barin Jidda Tana kaiwa Dare a waje ne..?

Mama tace"Wlh ba laifina bane Yayansu Kanwar mamarta ta aiko Taje yau suna Tariyan sabon Gida Tun Safe tatafi kuma har yanzu bata Dawo ba kila chan zata kwana.."Abdullahi yace"Wani irin chan zata kwana..? Banda ta Raina mutane in zata kai Dare ko kuma zata kwana Bata iya Kiran waya ta sanar..? Kuma ni wlh bana som wannan Yawom na Rashin Dalili Mama..".

Mama tace"Sai dai fa kayi Hakuri gani nayi Hassana ce ta aiko Taje Shiyasa nace ta Shirya taje Bakomai Da nan da chan Duk Dayane in ta kwana ai ba wani abu bane.."Kai Tsaye Abdullahi yace" Da abu mana Mama...Chan ai ba Gidansu bane bamai kwabamata Abunda taga dama zatayi Dama ai Jidda bata Jin mgana Ki kirata awaya Mama Kice nace mata komai Dare ta Dawo Gida wlh ko na saba mata.."Mama tace"ai Shikenan bari na kirata na gaya mata.."Daga Haka kawai ya mike Daidai Lokacin dasu Subai suka Shigo Gidan da sallama Mama ta amsa Auwal ne kan Gaba wajen Shigowa Dakin Dauke da Salim sai Subai"a da Mahmud suna Binsa a baya baki Mama tarike kafin tace"Me zan gani haka..? Subai"a da Danyen Jegom kike wayo..?

Subai"a Tayi Dariya Mariya ta Fito tana mata oyoyo kamar yadda su Amira suka Riketa suna mata oyoyo Mahmud ya Gurfana yana gaida mama ta amsa Cikin Sakin Fuska kafin ya waiga yana Fadin"Yaya Abdullahi mun wani lafiya..'?

Ya fada yana Mikewa Lokaci daya Yana Mikamai Hannu ya karba sukayi musabaha bayan sun gaisa Subai"a na Dari Dari tace"Yaya Ina wuni.? Wata uwar Harara ya Sakarmata kafin yace"Ke ashe baki da Hankali bansani ba..? Wani irin Sakarci ne zaki Fito kina jego ana mgana kina ma Mutane wannan Shashashar Dariyar nan taki koda yake ba laifin ki bane na wannan Mijin naki ne daya koma Mijin Hajiya.."

Yafada Fuskarsa ba Annuri Subai"a ta Sadda kai batayi mgana ba Mama tace"Ka yi mgana dai kila taji haka tarika wannan Fitan Lokacin haihuwar muhsina Wlh ki kya kanki da wayon nan Subai"a kina da Karamin Yaro.."Mahmud yace"Baza"a kara ba Mama yanzu ma Antynmu matar yaya muka Rako.."

Abdullahi ya kada bai kara Mgana ba ya kalli Hafsah yana Fadin"Ki Dauko su mu tafi.."Daga haka ya waiga yana cema Mama"Mama sai da safe zamu Tafi.."Mama tace"Allah tashemu lafiya.."Hafsah ta mike itama tama Mama sallama Lokaci Daya tana cema Su Amira su Dauko Unifirm dinsu da Sch bag dinsu sai kwandonsu Mariya ta Dauko musu kayan makaranta wanda ta wanke da Jakunkunansu ta basket dinsu Tabama Hafsah,Subai"a ta taso ta Biyo Hafsah har Haraban Gidan Tana Fadin"Kawas sai da safe.."Wata Uwar Harara Hafsah ta sakar mata kafin tace"Zaki sani ne.."Dariya ta mata kawai nan sukayi sallama Mariya da Auwal suka rakasu har waje Amir Shi ya zauna agaban mashin din ita kuma ta Hau Baya ita da Amira ta Rike Ledan da Sch Uniform dinsu yake Ciki da Sch Bag dinsu Basket dinsu kuma na Hannun Amira su Mariya na Daga musu Hannu Abdullahi yaja Mashin Din suka Wuce.

Tunda suka Hau Titi kala Abdullahi bai ce ma Hafsah ba itama Batacemai,sai Sharara Gudu yake Bisa mashin Daga gani Ransa yana bace ne Hafsah ta Fara tsorata da Gudun da Abdullahi yake Cikin Sanyin Murya tace"Don Allah Abban Amira kayi a hankali kada ka kadamu.."Kamar ta kara Zugashi ne ya kara sakarma Mashin din wuta sai kawai ta kame kanta ta koma tana sallami Cikin Ranta gefe Daya kuma Tana karanta Hasbunallahi wani"imal wakil.






*Shakira..*
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*

*Wattpad:JamilaUmar351*

*Dedicated To:My Habibaty💞Aisha Idris Abdullahi...*!

*006*

"Ajiyar Zuciya ta Sauke Lokacin Data ga sun kawo kofar Gida bai ce mata komai ba ya karkata mashin din ta Sauka Bayan ta Sauke Amira,harma wajen sauka ta Sarke kafarta tayi kamar zata Fadi ya saka Dayan Hannunsa ya Riketa,ammh bai kalleta ba dayaji ta Tsaya da kafafunta sai ya saketa ya Sauke Amir kasa wanda ya Fara Barci bai Jira cewar ta ba kawai ya kara Tada mashin din nasa ya juya ya koma Da kallo ta Bishi acikin Ranta kuma Duk Babu Dadi tafi kowa sanin Illar Fushin Abdullahi karshenta Itace zata sha Wahalansa.

jakarta ta lalubo ta Dauko key din Gidan wanda ke Hade Dana Sauran Dakunan,da Fitilar wayarta tayi amfani ta Haska ta Bude Gidan Bayan tabarma Amira Rikon ledan kayan makarantarsu,Suna Shiga Gidan Nepa na maido Wuta,Ta Bude Dakinta suka Shiga ta Kunna Wutar Ciki dana waje haske ya Bayyana ko"ina Amir ta kallah wanda ta Rikeshi a Jikinta Barci yaFara Daukansa.

Kumatunsa ta Shafa kafin tace"Amir kana jin yunwa.? Kai ya Girgiza mata alamun A'a Amira ce tace"Umma mun koshi Munci Tuwo agidan Mama.."Hafsah ta mike tana Fadin"Kama Hannunsa ku Shiga bayi kuyi Fitsari kuzo ku kwanta.."Batayi gaddama ba ta ijiye ledan kayansu akasa Ta kama Hannun Amir Zuwa Cikin Dakin Barcinsu hafsah inda Tailet din yake Ciki,Suka Shiga tayi Fitsari ta saka Amir yayi ta kamo Hannunsa suka Fito,Hafsah ta kamasu Zuwa Dakin Barcinsu ta kwantar dasu Tayi musu addu"an Barci ta Tofa musu Ta ja musu Bargo ta Fito Falo ta zauna kan Kujera ta zabga Tagumi ganin har Tara ta wuce Abdullahi bai Dawo ba Dakyar ta iya Tashi ta Kwashi kayansu Amira da suka Dawo dasu takai musu Ciki ta Fada Tailet tayi Alwala Bayan ta saka Ruwa a kittle sanin Abdullahi in ya Dawo zai yi wanka tazo tayi salla Ta idar kenan tana Zaune kan Sallaya taji Shigowar Abdullahi da Karan Mashin Dinsa tayi Zumbur ta mike ta Fito Tsakar Gidan ko Hijabinta bata Cire ba.

Yaga Fitowarta ammh sai yayi kamar bai ganta ba ya Bude Dayan Dakin ya saka Mashin din nasa ya Fito Hannanunsa Dauke da Ledoji Guda2,Ya Raba ta gefen Hafsah ya Shiga Dakin Tabi bayansa saman Capet nan kasa ya Zube Duka ledojin Dake Hannunsa ya kama Hanya ya Shige Bedroom Hafsah tayi sakale Tana Binshi da kallo Jiki a sanyaye ta karisa ga Ledan ta Bude,Daya maganin Sauro ne sai mayan Bicuit Guda Biyu nasu Amira ne,Dayan ledan kuma Gasashiyar kaza ce Guda Biyu sai Tiriri suke da alaman yanzu  aka gama gasasu,Dauka tayi ta matsar gefe Ta Dauki ledan mganin Sauran zuwa Ciki Sai suka ci karo ya Fito Daga Tailet Dauke da Botikin wanka na karfe Kadan ya Rage basu bangaji Juna ba Hafsah tayi Saurin Matsawa Baya Shi kuma ya Rabata ya Wuce Hafsah sai dai Tabishi da kallo kawai gefe Daya na Zuciyarta na addu"ar Allah ya saukar da wannan Fushin Data gani a Kan Fuskar Abdullahi.

Bayanshi Tabi Bayan ta Ijiye ledan maganin Sauron Abunda tagani ne ya Bata mamaki Abdullahi ya zage yana Cika Botikin Daya Fito Dashi Da Ruwa a Rijiya Cikin mamaki ta karisa Tana Fadin"Abban Amira me zakayi da Ruwa kuma..? Alhalin Duka Bombin Tailet Cike  suke da Ruwa Hakama na wajen nan.."In Iskar Dake wajen ta Tankanta toh Abdullahi ya Tankata,yayi mata Banza bai Dakata ba sai da ya Cika Botiki tsaf kana ya Dauka da Hannunsa tana Tsaye ya wucewa Zuwa Ciki da Sauri tabi Bayanshi Har Cikin Tailet din Abunda ya Bata mamaki bai Juye Ruwan Kittle ba Taga kawai ya Fara Kwabe Rigar Jikinsa alamun wanka zaiyi baki sake take Binshi da kallo Shi kuma yaki yarda ya kalli Barayinta ganin bata Niyyar Fita yasa ta Tube Duka kayansa ya Wurga Cikin kwandon tara kaya wanki ya Fara watsama Jikinsa Ruwan sanyi.

Batazata iya Juran ganinsa Haka ba Koda suka Haihu har sau Biyu Tana da kunyar ganin Tsaraicin wani kawai sai ta kada kai ta Fito Zuwa Cikin Bedroom din Hawaye sun kawo Cikin idanuwanta gefen gadon ta zauna Kawai Tana Tunanin mafita da kuma makomar wannan Shariya ta Abdullahi wanda komai nata yanzu baya Bukata,Tana nan zaune ya Fito Daure da Babban Towel  ta gabanta ya wuce zuwa Jikin Wardrope ya Bude ya Dauko Jallabiyansa Baka ya saka kana ya koma Toilet din da Towel Din Dake Hannunsa,sai chan kuma ya Fito gaban madubi ya koma ya Fesama Jikinsa Spry, Tana kallonsa ya koma Bisa gado ya kwanta Bayan ya kashe wayarsa,Har kuma ya kwanta sai kuma ya mike yaje ya Kashe Wutar Dakin ya koma ya kwanta Harda Jan Bargo kamar bai sam da zaman mutum a gefen gadon ba.

Ganin haka sai Jikin Hafsah yayi sanyi Cikim karfin Hali da Shawaran Zuciyarta ta Mike ta isa Kusa Dashi dan Dukawa tayi tana Fadin"Abban Amira.."acikin Taushin Murya da kuma Lallashi Tsit yayi kamar bai jita ba sanin yana Jinta yasa tacigaba da Fadin"Don Allah kayi hakuri kan Abunda ya Faru yau..Wlh ba laifina bane laifin Subai"a ce Zan taho Tun bayan La"asar ta Daukemin Jakata da Hijabina taki Barina natafi..Allah ba laifi bane.."Ta karishe Fada Cikin Rawar Murya kamar zatayi kuka Shurun ya sake mata sai ma kawai Taga ya gyara kwanciya ya Juya mata Baya bata Hakura ba Ta kara Bude baki tana Fadin"Kayi Hakuri...Ba..."Bata karisa ba Taga kawai yayi Zunbur ya mike Har sai da Ta Tsorata tatashi da Sauri kawai sai taga ya Dauki Filo da Blanket din kawai ya Bar mata Dakin Galala Hafsah ta Bishi da kallo kafin ta Hadiye wani miyau mai Zafi wanda ya wuce ta Cikin mangwaronta bai Shirya ba.

Bayaansa Tabi Cikin sanyin Jiki nan ta iskeshi kwance kan Doguwar kujera,yayi kwanciyar Rigingine yana kallon Celling gefe Daya kuma ya goya Hannayensa Akan Kirjinsa ya kuma Lumshe Idanuwansa kamar mai Barci Hafsah tayi kasake kafin ta karisa Tana Fadin"Ka tashi ka koma Ciki Don Allah..kasa ina jin wani iri Abban Amira.."Ko alaman yajita ma bai yi ba,Balle ta saka Ran zai amsata Ganin haka yasa ta kara marairaicewa Lokaci Daya tana Riko Blanket din Daya Rufu Dashi Tana Fadin"Kaji..Don Allah ka tashi ka koma ci..."Bata karisa ba Taji ya Daka mata wata Gigitattaciyar tsawa Wanda sai da ta sa ta afirgita ta saki Bargon ta koma Baya Cikin wani Zafin nama ya Tashi zaune yana kallonta kafin yace"Kinga malama indai bakina so na barmiki Gidannan bane ki Tafi ki bani

Please Login or Register in order to submit comment