Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ya ce'' mummy zamu tafi masallaci ai mana addu'a"..

Shafa kan shi tai tare da faɗin my lovely son Allah Ubangiji yasa adawo lafiya' ina mai roƙon Allah da ya shirya min kai Allah yasa a hanyar ku tadawowa ko zuwa a ga matar aure ai min surika; a mota ma shine yake driver ɗin dady na gefen zaman banza shima nan dady ɗin ɗaura mashi ya yi daga inda mummy ta tsaya ya ce'' wai dady kungaji dani ne da kuke ta faman nai aure?"

Kallon shi dady ya yi ya ce'' a'a abdul jalal shi ana gane mutumin kirki ne ta hanyar aure idan ya kai Lokacin sai dai idan babu halin yin auren ne shine mutum zai hakura amma kaifa son mai karasa a ciki? Kana da kuɗi kana da sana'a ga gidan ka da ka gina mai kake jira yanzu to sai aure ai!!!"

Uhmm dady in sha Allah na kusa kamar yadda kuke so inyi zanyi in sha Allah "dady fatana ku tayani addu'a" haka dai suka isa ana firar uba ɗa gwanin sha'awa har suka dawo gida, inda dady ya raba ma mabukata kuɗi saboda duk ranar Friday yake ranar laraba yake dawowa ya koma Lahadi duk lokacin da zai dawo zai raba masu kudine su ta samai albarka...

............... bayan kwana biyu da zuwan Waheed gidan su jannat, tana ta jiran shi ranar amma bai zoba saboda ya ƙara bata lokaci tai tunani mai zurfi hakan ko a kai mama ta bata shawara mai ƙyau ta ce'' jannat idan kin amince da shi to kada ki bata mai lokaci ki faɗa mai in kuma kina san shi sai ki faɗa mai shima, jannat da taji mama ta ce wai in tana San shi duk abin sai ya bata kunya ta sun ne kai mama ta ce ja'ira ashe kina so da baki fita ba ai da naga yadda zaki kifara san nashi"

Da sauri tafito ta cigaba da aikin ta na mai tuna maganganun shi tana jin wani sanyi cikin ranta ji take daman tai tsuntsuwa taganshi a gabanta don ita macece wacce bata iya san abu ba idan tana san abu tsakani da Allah yake san wannnan abu, ko habaicin da suke yaɓa mata tana jin su sai dai ta share kawai ba wai don bata jin haushi ba a'a bata nuna masu ne!

Washe gari tunda ta dawo makarantar yamma ma take jin gabanta na faduwa, gashi kwana biyu tunda Waheed ya san gidan su ya daina zuwa ƙofar islamiyar tasu, ƙarfe 6:00 ta fidda warar ta duka a waya ɗaya take tadawo gida saboda sun gyara warar su ga yajin tafarnuwa mai daɗi wanda yaji magi: samun wata kula tai ta zuba warar ɗari biyu ta aje cikin ɗakin su ita dai mama bata ce komi ba illa idanu.......karfe 8:30 dai-dai akai sallama wai ana kiran jannat, wannan karon bata jira maganar mana ba tai gaba don ganin ko Waheed din ne tana zuwa kuwa taganshi kan dakalin ƙofar gidan nasu ta gaida shi ta ce bari indawo......tana shiga ta ce mama shine kular da ta aje wara ta ɗauka Hadi da ruwa a kofi sai dadduma tafito


Shin wacece jannat?
Wanene Abdul Jalal?
Wanene Waheed?

Amsa duk tana cikin Uncle j KUDAI ku biya naku ku sha labari ₦300 kacal account number 3040725456 Imrana Dauda first bank sai shedar biya ta wannan layin 08108353370

Masu turo da kati MTN ko aitel ta wannan number 08138012334


*UNCLE J*

#romantic
Caring#.
#hot love

Littafi na kudine na kusa gama free page sister ki han zarta ku sai na ku kada ki jira na Sata🤏. ₦500 kacal account number 8108353370 maryam Ahmad opoy ko


Page 7&8

Abduljalal samir shine cikakken sunan shi ɗana ga Alhaji samir wani babban attajiri ne wanda yake har kan gidan man fetur na garuruwa da dama ciki harda Legos, inda ya fi zama kenan sai da sukai shekara 15 sannan Allah ya kawo masu ciki farin ciki da murna kamar mai don har azumin godiya sukai ma Allah inda laulayi ya tasa rabi sai dai ƙarin ruwa da ake sa mata domin ta samu ƙarfin jikin ta cikin ta na shiga wata tara yazo gari ya tafi da ita Legos saboda ya fi sana'ar shi a can ƴan uwanta since a bari ta haihu anan amma ya ce gwanda ta haihu kusa da shi domin ya rinƙa ganin ta.....

Kwana a tashi ba wuya gun Allah gashi har ciki yana cikin wata na tara har ya gota ma, ita dai rabi addu'a take Allah ya sauke ta Lafiya ana haka ne ya fita aiki marar ta ta damai ta da ciwo tun tana daure wa har ta kasa ta ciro wayarta ta kira shi da ƙyar ta faɗa mai halin da take ciki, duka minti 30 sai gashi kuwa kai tsaye asibiti suka nufa....... Tafi awa biyu tana abu ɗaya an yi tunanin na kawai ai mata c.s sai Allah ya taimake ta ta sulɓo yaron ta mai kyau ga hanci kamar ubanshi ya yi tubarakallah, farin ciki da murna kamar mai ana ta hidimar suna ƴan uwa kuwa sai dai akai masu bizar zuwa ta jirgi domin gano abduljalal sha tara ta arziki ta samu ga haihuwar nan haka ta cigaba da renon ɗan ta cikin kwanciyar hankali da annusha abduljalal yana da shekaru goma ne suka dawo Kano unguwar j.r.a gida ne plat house har ya gaji da tsaruwa part dayane sai dakuna hudu dakin mummy sai wani daki an zuba kayan wasan yara ɗakin wasan Jalal sai ɗakin Daddy sai ɗakin barcin jalal, iya tarbiyya Jalal na samu gun mummy idan dady yadawo sai ya rinƙa mai abinda yake so idan mummy tai magana ya ce yaro ne, babbar makarantar yasa shi inda ya hadu da abokan banza suka sa shi hanyar neman mata tun bai iya ba, idan za ai wasa da matan agaban shi tun yana jin kunyar a yi a gaban shi har takai ga bai jin komi, wata yarinya zarah ta na ce ala dole sai ya rinƙa wasa da ita ya nuna a'a bai son wannan ta ce ya kulla soyayya da ita hakan shine dalilin tabarbarewar tarbiyyar Jalal ranar da mummy ta gano ta sha kuka har ta mai duka ta jimai tar gaɗe a kafa dady yai ta faɗa ita bata san yaro ba ne da zata mai dukan nan, kuma wannan wasan ai yara na yin shi shine fa tadage da addu'a ta daina magana ranar da yaso ya kwana gida randa bai so ba ya kwana gidan abokai wannan shine tarihin Jalal

Back to story

Tana fita ta shimfida mai daddumar hadi da aje kular agaban shi wani daɗi ne ya kama shi daganin wannan shima yasan ta amince tunda yaga wannan karramawar da tama shi, ta katse shiru ta hanyar ƙara gaida shi ta ce'' ina wuni"?

Kallon ta ya yi da murmushi a fuskar shi ya ce'' lafiya lau haske na ina fatan kema haka kike?"

Ehhhhhhhhhh lafiya lau yadda taja ehhhhhhhhhh din sai ya bashi nishaɗi a ranshi cikin zuciyar shi yake fadin yarinyar nan tana da daɗin Murya walllahi sai tasani suma, a fili kuwa ya ce'' Masha Allah!''

Shiru ne ya biyo baya kusan minti 10 sannan ya ce'' ƙanwata nazo ne domin naji shawarar da kika yanke, abinda ya hanani zuwa saboda aikin shago ne da yamin yawa shine dalilin amma ina tuba gareki gimbiyata"

Murmushi tai duk kunya ma ta kamata' ta buɗe baki kamar zatai magana sai ta fasa.....ya lura da hakan ya ce'' mainene abin jin kunya ta ƙanwata ki faɗa min abinda ke ranki game dani kada kiji kunya please na roƙe ki Madam jannatlove!!!!!

Ita abin har mamaki ya ke bata saboda sunayen da yake canza mata kamar a bakin shi a ka rada sunan saboda yadda ya iya faɗa.... Ta ce na amince Allah ya zaɓa mana abinda yafi Zama alheri ta faɗa tare da rufe fuska!

Murna ce ta cika cika shi kamar zai yi rawa haka yake ji, suka ci-gaba da firar su har ƙarfe 9:00 sannan ya ce ta shiga cikin gida dare ya yi.... miƙe wa tai a kunya ce ta wuce ciki hadi da aiki yaro ya ɗauko mata kayan da tafita da su, ko da ta shiga cikin gidan ta faɗa "mama yadda sukai da Waheed fatan alheri tai mata hadi da bata shawara" Bangaran matan gidan kuwa sai habaici su ke saki wai an kaita gun boka shine har ta samo wannan sudai basu damu ba tunda ba can suka je ba!


Dady fa ya tafi sai tsula tsiya yadawo kamar kullum yau ma da ya tashi sai ya biyo ta kofar baya shi da budurwa shi, inda mummy tana can palorn ta kofar gaba tana jiran taga dawowarsa sai da ya ma baƙuwar shi ma sauƙi cikin dakin shi sannan ya canza shiga izuwa jallabiya fara ya fito palorn ganin ta ya yi zaune ya ce'' mummy Lafiya baki kwanta ba har Yanzu dare fa ya yi"

Ta ce'' son Kai nake ta jira nan shine ka gan Ni nan zaune"

Murmushi ya yi tare da faɗin "mummy ni fa tun 8:39 ina cikin gida barci nai yanzu ma yinwa ce ta fito dani na zo dafa indomi naci, ya ida sa maganar tare da wuce wa kitchen yana shiga ko ya zuba ruwan zafin da ke cikin plast ya yi sauri ya gama duk da haka tana nan palorn ta yi tunanin fita zai yine har sai da tayagama ya fito ya ce mummy ga indomi din ki ci kema, ta ce a'a son good night ya mata tare da shigewa ɗakin shi"



Tobe contuie


UNCLE J
Real matar dear ce👌

Free page

Page 9&10

Yana shiga cikin ɗakin ya saki dariyar shaƙiyanci cikin zuciyar shi kuwa ya ke faɗin haba "mummy kin kasa kin tsare gashi ɗan cikin ki ya maki wayo, a fili kuwa ya ce beb tashi na dafo Maki indomi ɗin"

Da sauri kuwa ta tashi ta ce'' baby j naga ka yi sauri haka gaskiya kai din gwarzon maza ne na gaske, ta ida faɗin maganar da manne mashi ido"!



Tana gama cin abincin ta taso ta matso gare shi, ya ɗan ture ta hadi da cewa please ki je kiyi wanka mana sannan ki brush kin san dai ƙa'ida ta ko...........taji haushin abinda ya mata amma hala ta basar ta miƙe zuwa bayi, wow ta furta a fili aljannar duniya kenan wannan bayi ko dakin da take kwana bai kai bayin nan ba ta shiga ruwa ta haɗa tare da shige wa ciki ta wanke lungu da sako na jikinta, tana gama wankan ne ta sa turaren wanka mai ƙamshi a normal wura ta watsa bayin kuwa ya dumame da ƙamshi ta ɗauro ta wul tafito shima tashi ya yi domin yin wankan!!!!!!!!!!


Zaria

Tunda ga ranar da "Waheed yaji ya yake cikin zuciyar jannat hankalin shi ya kwanta, sai dai aikin shago ya mashi yawa ba halin zuwa gareta idanun shi na yinwar ganin ta suke kamar me"

Haka bangaren jannatlove 😘. duk tabi ta damu kodai daman ba da santa yake da gaske ba shine ya ƙi dawowa, gaskiya idan ko haka ne bai kyauta mata ba.....wayar mama ce tai ƙara alamun ana kira dubawa tai sai taga baƙuwar number ce bata ɗauka ba har sai da akai kira biyu sannan ta ɗauka a na uku ' da Muryar ta so silent ta yi sallama har cikin zuciyar shi wannan sallama ta ratsa ilahirin jikin shi ya ce'' jannatlove sai anjamin aji sannan za a dauki kiran nawa....

Wata ajiyar zuciya ta sauke mai daɗi' har shi da ke can yaji wannan ya ce'' jannatlove Allah yasa dai ba nine nasaki wannan ajiyar zuciyar ba?''

Ɗan dafe kanta tai alamun taji Kunya tai shiru na second 4 sannan ta ce'' yayana yanzu dai ina wuni"

Lafiya lau ƙanwata ya furta, dashi shi ma yana murmushin haka suka ci-gaba da fira cikin kwanciyar hankali kamar ba zasu rabu ba ita mama har mamakin yadda "Waheed ya sa ce zuciyar ta da wuri haka" duk saboda jannat ta samu mijin aure ƴan gidan nasu sai haibece habaice suke masu ita dai jannat ba abinda ya dame ta tunda ta saba da habaicin da suke mata kamar kullum yau ya kama asabar da wuri ta shirya saboda zuwa islamiyya kada ta makara, wanka tai ta sa kayan makarantar ta fito zuwa kitchen tana dafa warar yamma yanzu jannat ta daina tuya waje sai a gidan su a juya a kula duk wanda ya shigo ya siya da zafin ta haka suke kullum


WACECE JANNAT

Jannat ƴa ce ga malam Imrana mai caji wanda ita kaɗai ce gun mamanta, gidan su mata uku ne maman su samira ita uwar gida sai maman su Hadiza sai su din su jannat dakin su samira su uku ne hamida sai na'im sai ita kanta samirar "hamida tai aure amma bata da yara, na'im kuma neman kuɗi yake zuwa Kaduna sai uwar gaiyar samira"

Dakin su Hadiza kuwa su biyu ne daga zuhaira, tai aure a Lagos ba ko wane lokaci take zuwa ba, sai anty Hadiza tana da yara uku mace biyu namiji ɗaya.........ta tashi ne tana da shekaru 5 mahaifin ta ya rasu su kadaine a gidan sai kannen baban su da yayye da suke taimaka masu da abinci da kudin kashewa, suke da yara makarantar islamiyya da boka har su kammala karatun su!!!!!!! Wannan shine taƙaitatten tarihin jannatlove 😘

Back to story

Tana shiga cikin makarantar ne aka fara tarar latti Allah ya taimake ta baza taci dukan malam Nura ba domin bai iya duka ba, tashiga cikin ajin na su domin yanzu hadda suke saboda saura wata uku su kammala suyi sauka.......karatu suka ci-gaba da yi Cikin kwanciyar hankali malam Aminu ne ya shigo an sar hadda, jannat ita ce ta farko haka ta mike tafara raira karatu cikin Muryar ta mai daɗin gaske tana karatun suratul anfal a haka har kowa ya biya shafi biyu daman masu saukar mutum 15 ne matan sai maza mutum biyar, ana ta shi bata tsaya wasa ba ta tafi gida inda ta iske kiran Waheed har uku tare da text biyu shiga tai cikin text taga ansa..

Jannatlove nasan kin tafi islamiya don Allah ki karatu da kyau duk da nasan baki da wasa, na biyun kuwa i love you kawai ne a jiki..
Murmushi tai tare da mai da mai nagode sosai

_________________ sai da yarinyar Jalal tai kwana biyu a gidan sannan ta tafi, duk wannan lokacin da take gidan j Yana gida bai fita kwata_ kwata idan ya yi sallar isha'i to yana tare da mummy har zuwa ƙarfe 9:30 sannan zai tafi da indomi ya ba ta taci haka har kwana biyu ita mummy har ta fara murna yaron ta ya shiryo har ƙara sadaka tai domin jin daɗi' a kwana a tashi ba wuya gun Allah gashi har dady ya yi wata biyu da tafiyar sa, sai dai waya da suke tashi tare da video Call da suke yi kullum yana kallon iyalan nashi cikin farin ciki............ Kamar kullum yau ya kama juma'a sun yi abincin sadaka da suke duk ranar Alhamis da juma'a ya dawo masallaci ne ya ke faɗa ma mummy zai je Zaria gun wani abokin shi zai yi aure, ta ce Allah ya kai ka Lafiya kaima daga can kai mana surika!!!

Murmushi ya yi tare da rufe baki ya ce" mummy kuma sai na rasa mata duk nan garin har sai naje can Zaria? Ni gaskiya yaro ne ban isa aure ba ya faɗa tare da ɗan rugawa part ɗin shi"..

Mummy ta tsaya kallon shi ta ɗan daga murya yadda zai jita ta ce" shekarar kafa 27 shi ne kai yaro ne to ka bari na maka mata da kai na ka ji Yaro"

Ɗan juyowa ya yi ya ce'' noooooooooooo mummy, yana shiga wanka ya faɗa tare da shiryawa cikin farar shadda tare da sa hula baƙi hakama takalmi wani farin glass ya sa wow na furta ganin j ɗin ya fito a abduljalal din shi ya fesa turare tare da ɗaukar wayar shi ya fito palorn, mummy ta kalle shi ta ce wannan wanka abduljalal ai dole ma ka yi min surika ta yau"!!

Shi dai sallama ya mata ya fita motar shi kai tsaye ya ɗauki hanya cikin kwanciyar hankali ya ke tukin shi, kusan awa uku sanan ne ya iso garin Zaria kai tsaye tundun Wada ya nufa inda ake ɗaura auren abokin na shi...

Idan naga Comment da yawa zan ƙara maku yawan typing 🤣🤣🤣🤣🤣. In sha Allah

Kada ku manta littattafin UNCLE J yadawo ₦200 nan da kafin azumi account number 8108353370 Maryam Ahmad opoy sai naji ku


UNCLE J

Real matar dear ce 👌


Last free page

Idan kina san ci-gaba da karanta *Uncle j* to zaki turo ₦200 kacal ta account number 8108353370 Maryam Ahmad opoy masu turo da kati ta wannan number 08138012334 sai na jiku fan's 🤗.

12/13

Yana isa kuwa har an fara shirin ɗaura auren ko minti biyar bai da zuwa ba aka ɗaura auren NURA DA ALIYA, wasu daga cikin mutanen ne suka fara watsewa sai ƴan uwan ango da abokan shine suke gun ana ƙara ta ya juna murna, hotel ango ya kama ma abokai domin ai shagali a can saboda anjima da daddare za ai dina suna isa Jalal ya samu gado ya haye domin ya gaji sosai barci ya ɗan samu ya na tashi ya watsa ruwa ya canza kaya izuwa pink din shadda wanda ango ne ya dinke abokan shi saboda ita ce ankon dina dim su tai matuƙar amsar jikin shi kamar shine ango sai tsokanar shi ake saura shi haka suka tafi a motar shine aka ɗauki amarya zuwa hol din da aka kama!!

________________

Jannatlove ce zaune kan tabarma tana tsifa sai ga "samira ta taso da saurin ta tana kumburi kamar zata bugi jannatlove ɗin ta ce ke wato saboda ina san Waheed shine kika zagaye kika same shi ko?? To walllahi bari kiji ko bajima ko ba daɗe sai na samu Waheed ke kuma kin rasa wannan alkawari ne"!

Mama ce da taji kamar hayaniya ta leƙo tare da faɗin "samira Lafiya dai nake jin wannan hayaniyar ne?"

Ta ce'' ina fa Lafiya ƴar zata min ƙwacemin saurayina saboda ta zama nusara ta samu nata mijin ta zo zata min kwace Allah sai ta barmin Waheed"

Babbar magana inji jannat ta miƙe ta ce'' ke samira shiru_ shiru ba tsoro bane Malama bariki ji Ni basan kina san Waheed ba saboda baki nuna min ba, kuma shi kan shi wanda kike magana akai bai san kina wannan haukar taki ba, ta ɗauki botikin wankan ta ta shige bayi daman saura uku ta gama sifar wanke kan tafara yi ga gashi kamar zai ci kan shi saboda yawan gashin ta bata san kitso mai yawa bai fi ai mata 10 ko takwas ba shima kuma mama ce ke mata"

Nan dai aka bar "samira mama tana jin jannat na wannan maganar ta koma cikin ɗakin daman gyaran shinkafa take, ta wuce fuuuuu tana magana kasa kasa"

Ko da jannat ta fito bayi mama ta ce" jannat daman kin san tana San shi??? Ko daman ita ya ke so yadawo kanki??? Tai wannan tambayar Lokaci ɗaya"

Ƙwalla ce ta kawo idon ta ta ce'' walllahi Mama ba sanya yake ba hasali ma jiya da yazo fira ne tagan shi, har suka gaisa amma ai kin san layin su anty Hadiza ya ke shine mai ɗinkin nan kin san kuma yana ma mutanen gidan nan aiki ina tunanin anan ta san shi har take wannan maganar"!!!!!!!!

Ita dai mama shiru tai don bata san tashin hankali ko kaɗan, saboda hankanin ta tashi ya ke tashiga a damuwa sosai shiyasa bata shiga hidimar kowa sai wanda ya sa ta cikin hidimar shi, mama ta ce'' to Yanzu dai ki shirya zan baki sako gun "gwaggonki" ( matar ƙanin baban ta) can wajan tundun Wada ta ce mama ki bar aiken ki sai zuwa gobe Kinga yamma tayi...........ta yi mata daƙuwa tare da cewa uwaki don gidan ku ba yau Alhamis ba sai ki dawo gobe juma'a ai ki kwana ɗaya dai saboda Kinga asabar islamiyya!

Ɗan bata fuska tai Kamar zatai kuka ta ce'' to mama bari nasa kala ɗaya cikin leda ko?"
Ehh kisa nima bari na zuba masu wara atafin masu da ita...

*Samira*

Zaune take gaban boka mai aiki kamar yan kan wuƙa ta ce'' ina so ai masu far raƙu ne yaji ya tsane ta sai ni bana san ya aure ta saboda Ni ina san shi, so nake arabasu kamar yadda yaro yake barin nonon uwar shi........

ɗaga murya ya yi tare da faɗin angama amma ki sani sai kin kawo antar jaki da idon raƙumi mai jikin fari!!!!

Zaro ido "samira tai ta ce na shiga uku ina zan samu waɗannan kaya ni?"

Ɗaure fuska ya yi ya ce'' daman kin shiga uku daga nan har duniya ta naɗe,
Zaki bada kuɗi ne aba aljani suɗi su suyi maki kuɗi ₦20000000 ne idan kina san aiki kamar yan kan wuƙa kuwa"

Zaro ido tai ita ina zata samu wannan kuɗi, ta ce'' boka banda kuɗi amma mai zai hana ai abinda aka saba ne?"

Murmushi ya mata tare da cewa shiga ciki ina zuwa....... miƙewa tai ta shiga shima kulle kofar ya yi ya bi bayanta zuwa ciki..

_________________
Masha Allah wajan dina an ci an sha, masu rawa na yi wasu dai suna zaune suna kallon masu yi tare da dan na wayar shi, shi dai Jalal ganin ba garin su bane ya kama kan shi domin wannan ƴan matan da yake can nan ya nuna ba ruwan shi saboda yaga duk yarane ƴan matan amaryar, duba agogon wayar shi ya yi yaga ƙarfe 6:30pm ya miƙe tare da ce ma ango kaina na ciwo sai kun iso.....
Ango bai ji dadin haka ba haka dai ya mai sallama ya fito motar shi ya shiga tare da kunna ta ya miƙo domin dawowa ma sauƙin su, wayar sa ce tai ruri alamun ana kira ɗagawa ya yi tare da faɗin "hello mummy wallahi na yi missing ɗin ki over"

Daga can bangaren ne ta ce" don idan da kayi kewa ta ai da ka kirani saboda an shiga hidima ka manta dani ko ai shi kenan"

Ya buɗe baki zai magana ne sai ji yake kiiiiiiiiiiiiii ya buge mutum wanda bai san wanene ya buge ba, da sauri ya fito don ganin aikin da ya yi jiki na rawa ya sami mutane aka sa mai ita a mota ya nufi asibiti mafi kusa..


Sister na wannan shi ƙarshen free page din mu idan kina san cigaba da karanta wa sai kisa ₦200 ki 8108353370 Maryam Ahmad opoy sai naji ku peopleeeeeeeeeeeeeeeee

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment