Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa ba ko yayan sa. Amma da yake aka ce naka sai naka, yau da bukatar taimakon su ta kama ni haka na murje kunya na kai masa Amani nace ya baiwa daya daga cikin matan sa ta shayar min da ita. Amma bawan Allahn nan bai dubi hali na ba ya karbi Amani ya baiwa amaryar sa Maryama, ta hada da Kamilu dan da take goyo ta shayar da su. Maryama ba tayi shekaru biyu cikakku tana shayar da Amani ba ta rasu. Sai Malam Idrisu ya dauke ta ya maida rikon ta hannun kanwar mu Sahura dake aure a garin Funtua.
Amma zuwa na Funtua na farko naga bazan iya barin Amani ta cigaba da rayuwa a wannan gidan ba saboda rashin tsafta da cikowa, gashi nifa bawai ina taimaka musu da komi bane kan rikon da suke yi mata amma nazo na raina kokarin Sahura. Na karbo Amani tana da shekaru uku na dawo da ita Katsina hannun matar da na sake aura, na daukar mata mai raino.
Amma hankalin Hajara na kan yar kankanuwar yarinyar nan da yadda zata cutar da ita, shi yasa da na gane na saketa babu bata lokaci.
Na sake aure, saina daina baiwa mata na hidimar Amani, na daukar mata mai raino daya kwakkwara mai suna Rakiya, na sata a makaranta mai tsada, na ke kuma kirata AMANI don boye sunan mahaifiya ta.
In takaice maka ko Mukhtar, kafin Amani tayi wadannan shekarun nata na yanzu aure na goma, babu wadda na cika shekaru biyu da ita, don sun kasa kaunatar min yar nan, wadda soyayyar da nake yiwa mahaifiyar ta ce bakidaya ta koma kanta.
Suma masu rainon kullum cikin canza mata su nake, Rakiya kawai na bari mai dafa mata abinci har gobe, har Allah ya raya ta ta isa kula da kanta. Ita ta roke ni in daina aure-aure in kuma daina korar masu aiki saboda ita, shi yasa muka dade da Haj.Rabi.
To ka ji Mukhy, wanan shine labari na da ya ta Amani, a yau ina cikin damuwar irin dabiun ta da irin tarbiyyar da nayi mata, amma yaya zanyi? Ni da mahaifiyar ta Allah yayi ba masu rayuwa tare bane na tsayin lokaci, kuma ban kyauta ba da ban kara bibiyar rayuwar Jalan ba, su kuwa dangi na na Faskari wallahi sai dai Amani tayi masu kyauta amma ba dai ni ba, bana kai ta wurin su, amma ita tana kai kanta lokaci-lokaci bama tare da na sani ba. Ba yabon nawa ba, Amani ta fini kirki, ta fini son zumunci kai dai bar ta da sangartar ta wadda rashin tashi karkashin kulawar uwa ko wata shaqiqiya mace ta jiki yayi mata sanadin sa.
Mukhtar ya jinjina kai ya shafe gumi daga goshin sa. A hankali yace Alhaji labarin ka akwai darussa mai yawa a ciki Alhaji, sannan akwai tarin kurakurai a cikin sa.
Na farko Alhaji, ban yarda da abin da ka yarda da shi bana cewa Mama Jalan na kin ka ne saboda baka da kyawun suffa wannan ba haka bane Alhaji. Hanyar da kabi wajen auren ta bata dace ba, kamar ka sayo akuya a kasuwa ka kawo kasar ka ka ajiye ne, duk da mahaifin ta shi ya aura maka ita, akwai bukatar ka nemi soyayyar ta da fahimtar juna tsakanin ku, kafin akai ga maganar aure ba duka mata ake saye ba.
Amma irin wannan auren dama baya wata kima tunda da bakin ka kace min akwai wanda take so da suka dade tare, har suka yi alkawarin aure.
Don haka ka cire maganar wai don munin kane bata son ka, kuma Alhaji da bakin ka kace kana yi mata kankamo, mata da yawa musamman na kasashen Africa suna aure ne a inda zasu samu wadata da kwanciyar hankali fiye da na kasar su ta asali.
Mu koma maganar dangin ka na Faskari, zan iya cewa kayi wa Yaya Idrisu da Sahura butulci da rashin daukar zumunci da daraja. Dukiyar ka ta rude ka ka wulakanta zumunci domin sun cancanci ace a irin wadatar da Allah yayi maka kamata yayi ace ka rungume su ka zama kaine komai nasu tunda kace basu da karfi.
Muhimmin abin da zaka yi a yanzu Alhaji shine gyara tsakanin ka da yan uwan ka, neman yafiyar su, da janyo su a jiki, ka saka su a cikin niimar da Allah yayi maka.
Alhaji yana girgiza kai yace haka ne, haka ne Mukhtar, In sha Allah zan gyara, gobe-goben nan ka shirya mana tafiya Faskari don Allah ni da kai da Amani da yardar Allah zan gyara komai.
Mukhtar yace naji dadin jin hakan Alhaji, saura iyayen Mama Jalan da ita kanta ya kamata ka neme su ka sada su da Amani.
Mahaifiyar ta na da hakki a kan ta fiye da wanda kake da shi. In ta mutu baka sada su ba sai Allah ya tambaye ka Alhaji, Amani (is desperate) ga son ganin mahaifiyar ta, har taso ta bi ta wata hanyar da baka sani ba don ta kai kan ta ga mahaifiyar ta ba don na hana ta ba, duk da togaciyar da kayi mata akan zuwa gare ta.
Kafin Alhaji yace komai suka hango Amani na tahowa inda suke da hanzari da sassarfa, suka yi shiru suka maida hankalin su gare ta. Tana isowa ta nufi Alhaji ta zauna kasan kafafun sa ta saka kuka.
Alhaji yace ni fa dadi na dake shagwaba da sakarci maras dalili, yaya zaki zo muna magana ki saka mu gaba kina kuka? Mutuwa aka yi ko dukan ki aka yi? Amani ta dago jikakkun idanun ta ta dubi Baban ta cikin ido ta ce Daddy sona ke ka saki Haj. Rabi, kuma kada ka kara auren kowa, ba zasu taba son ka saboda Allah ba, dukiyar ka kawai suke so Daddy.
Muddin kuma suka fahimci ba zasu samu ba na rantse zasu iya halaka ka ko ni su sabauta ni. Daddy don Allah ka sake ta, ni zan kula da kai, na fasa zuwa karatun, zan kare rayuwa ta gaba daya cikin kulawa da hidimar ka da lafiyar ka, in dai ka yarda zaka rabu da Haj. Rabi kuma zaka fasa aura min Alhaji Sadi.
Alhaji yace cool down Amani, duk me ya kawo wannan? Maganar auren ki da Alh. Sadi tana hannun ki yanzu, na bashi dama ne ya nemi soyayyah daga gare ki, wallahi in baki so duk amincin dake tsakanina da shi bazan miki dole ba. Haj. Rabi kuwa ai zaman ki take yi, ke kika hana ta tafiya tuntuni.
Ni da ke cikin rayuwa a wheelchair yanzu, rayuwa ta bata mata bace yanzu. Ko dama saboda siyasa nake aure-auran nan amma tun daga kan Jalan na gama auren biyan bukatar rai da kauna.
Share hawayen ki kin ji Amani? Gobe in sha Allahu zamu tafi Faskari da wuri zan maida ke cikin yan uwan ki na jini.
Amma Amani ta yaya zaki iya kula dani alhalin kina mace? Da zaki yi min alfarma irin wadda baki taba yi min ba ki amince ki auri da na Mukhtar, ya zauna tare da mu, ku cigaba da kulawa da ni tare har Allah ya bani lafiya.
Na hanga na duba duk duniya ban ga wanda zan iya baiwa auren ki ba sai MUKHTAR Amani, da shi kadai na amince in yi surukunta, kuma da shi nake son jini na ya gauraya, koda kuwa ace daga sama ya fado, wato ba yan Adam ne suka haife shi ba.
Amani da Mukhtar a lokaci guda suka daga kai suna kallon-kallo, kallon son fahimtar ko me Alhaji ke nufi? Sun shiga rudani mai yawa dukkan su, amma Amani ta fi Mukhtar gigicewa. Mikewa tsaye ta yi zumbur tana kallon Alhaji a tsorace, kafin ta soma ja da baya, da kyar ta iya cewa,
Daddy ai gara min Alhaji Sadin, da dai wannan mara mutuncin mara tausayin kuma mara jin kan mace. Gara min Alhaji Sadi bakikkirin mummuna da wannan mai kyan dan macijin. Gara min Alhaji Sadi tunda ba a karkashin uba na yake cin abinci ba, kuma yake min keta da Gadara ba.
Na rantse da Allah gara in auri Alhaji Sadi sau dubu da wannan sumumu-kasau din wanda bai san darajata a wurinka ba, saboda takamar yana da fada a wurin ka.
Tana gama fadin haka ta juya ta bar wurin da gudu-gudu, sauri-sauri babu inda ba ya kyarma a jikinta saboda dimauta.
Mukhtar kuwa komawa ya yi tamkar mutum-mutumi a wurin, ko kwakkwaran motsi bai iya ya yi ba. Haka ya kasa dago kansa da ya sunkuyar saboda kunya. Ga mamakin sa sai ya samu kansa da jin kunyar Alhaji mai tsanani. A can wani sako na zuciyar sa kuma ya samu kan sa da jin dadin wannan tayi da yayi masa. Shi ma ya san ba ya kyautatawa Amani yadda duk maaikatan Alhaji ke mata, haka ba ya bata respect din da maaikata suke bata, kullum jin kan sa yake sama da ita, ba ya yarda da subordination, shi mutum ne da ba ya yarda da raini ko kaskanci, wannan kuma a cikin jinin sa ne na iyaye da kakanni.
Maganar aure da Alhaji ya yi yanzun kuwa tsakanin sa da Amani sai ta kashe duk wani kuzarin sa, ta jefa shi a wani yanayi da bai taba shiga ba na zurfin tunani da mutuwar jiki.
Maganganun Amani wadanda suka zamo raddi ga mahaifin ta, kuma zagi a gare shi ko kadan ba su dame shi ba. Fassarar da ta dade tana yi masa a zuciyar ta ne yau Allah ya matsi bakin ta ta fada a gaban sa.
Da kyar ya iya mikewa tsaye lokacin da Alhaji ya ce ya tura shi a kujerar sa ya maida shi falo ya huta.
Har suka yi sallama da Alhaji, bayan ya bashi magungunan sa na yau ya sha, Mukhtar sanyin jikin sa da bugun zuciyar sa basu koma daidai ba. Da kyar ya iya takawa zuwa gidan sa wanda bai da nisa da gidan Alhaji. Ko motar sa a gidan ya bar ta don ya san ba zai iya tuki ba.
**** **** ****
MUKHTAR
Mukhtar ya yi kwance a tsakiyar lallausar gadon sa yana sake tariyo maganganun ubangidan sa Alhaji Usman Faskari, kauna ce zallah ya nuna masa wadda babu algus, kuma wani bare bai taba yi masa irin ta ba, kuma bai taba samun kwatankwacin ta ko daga iyayen sa da suka haife shi ba.
Ya soma laluba lungu da sako na zuciyar sa don son gano stand din da ya ajiye Amani, a zahirin gaskiya wannan yarinyar ba tun yau ta ke fizgar zuciyar sa ba, ta dade tana saka shi a faduwar gaban da bai san dalilin sa ba, sai ya bar wa ran sa a cewa kyawun halittar ta da kwarjinin ta ne yake razana shi, yake sanya shi faduwar gaban, kamar yadda duk wani lafiyayen namiji bazai iya kauda kai a kan ta ba ba tare da ya ji zuciyar sa ta motsa ba. Ya sha zama a cikin dare yana tuno wasu abubuwa da suka shafe ta a duk lokacin da wata alaka ta hada su suka fita a mota tare ya kai ta wani wuri, bisa umarnin Alhaji. A irin wadannan lokutan kwana yake da tunanin ta a ran sa. Fitsarar ta, rashin kunyar ta, hararar ta da tijarar ta duk basu bace masa. Ba don murmushi yayi kaura daga rayuwar sa ba da yace wadannan halaye nata duk da baya son su, to fa hakika suna saka shi murmushi a yawancin lokuta. Amani Faskari, tana da babban alamari a tare da shi wanda ya dade da kasa ganewa.
A yau da Alhaji da kan sa ya yi masa tayin auren ta ya shiga rudu, ya shiga dimuwa da tunani mai yawa, wanda hakan ya saka shi tono duk wasu tsofaffin feelings din da ya san yana ji a kan Amani; and he realized for himself cewa ya dade yana son Amani, in dai pleasant feelings din da yake ji a can kasan ran sa a kan ta shine SO, to ya dade yana ninkaya a cikin sa ba tare da ya ankara ba, har sai yau da tayin Alhaji da kan sa ya ankarar da shi, amma kuma halayen ta sun sa ba ta burge shi, kuma ba ya son ko daya cikin dabiun ta. Ya na son ta a kasan ransa a can wani lungu da bai taba dauka da muhimmanci ba. In ba haka ba me ya sa ko kadan ba ya son zancen auren ta da Alhaji Sadi? Me yasa ranar da Alhaji ya gaya masa ya bada auren ta ga Alhaji Sadi ya kasa barci a tsayin daren bakidayan sa?
Me ya sa yake kishin ganin ta babu lullubi (mayafi?) ta fito waje ma'aikata maza na kallon ta, don duk lokacin da ya gan ta babu lullubi a gaban maza sai ya ji zuciyar sa kamar ta tarwatse. Duka wadannan alamu ne na So, don ba a kishi sai da So, sai dai son bai zo a muhallin da ya dace ya zo ba, wato Amani ubangida ce a gare shi, sannan ba ta da tarbiyya da cikar addinin da mutum irin sa za ya so ta, har yayi fatan ta zama uwar yaran sa. Ko ya aura ya kai gaban iyayen sa su karba cikin sauki.
Ya taso a gidan da ba'a san komai ba sai mutumta Dan Adam, tsatstsaurar tarbiyyah ga 'ya'ya maza da mata, gidan rikon addini da dattaku, gidan da dan gida ba shi ne Da ba, gidan da DAN RIKO daidai yake da dan gida har wani lokaci ya fi shi sakewa.
Amani Faskari ta dade da satar wani kaso mai girma a zuciyar sa, wanda zai iya cewa daga Allah ne kawai, ban da haka in kyau ne ya baro mata ma su amsa sunan mata da suka dame ta suka shanye a kyau, dukiya, ilimi da gatan da take takama da shi. Amma babu wadda ta taba saka shi a irin situation din da yake samun kan sa a duk lokacin da ya ga Amani. Something like miracle, (abin kamar karama) tana da wannan boyayyen tasirin a kan sa.
Mukhtar ya shiga ambaton innalillahi wainna ilaihi rajiun, wannan wace irin masifa ce ke neman hawa kan sa? Ya yarda da auren Amani ya yi ya ya da ita da rashin kunya da rashin tarbiyyar ta? Wadda ba ya tunanin ko karatun sallah ta iya daidai. Above all aure a gare shi a yanzu na nufin komawar sa gida, wanda bai taba shiryawa nan kusa ba. In Alhaji ya dage a kan bakan sa na aura masa fitsararriyar yar sa wa zai karba masa auren? Tunda ya san babu kowa nasa a kasar Najeriya? Kodayake Alhaji ya dauka iyayen sa sun rasu ne, shi ya sa ba ya takura masa a kan zuwa gida, duk lokacin da ya ce ya je ya gaida dangin sa zai ce zai je ne ba ya so ya tafi ya bar masa ayyuka da yawa ya sha wahala, har Alhajin ya gaji ya daina masa maganar zuwa ganin dangin sa don ya dauka ma iyayen sa sun rasu.
Yanzu kuwa da Alhaji ya bullo masa da zancen aure sai ya ji wani sako na zuciyar sa yana missing gida, yana kewar Diffa. Sama da komai yana kewar UMMAMIn sa.
***** ***** ****
AMANI
Zamu iya cewa yau Amani dan karamin kwancewar kai ne ya same ta a dalilin furucin Alhaji gareta. Wasu notuka a cikin kan ta ta ji sun kwakkwance tsabar rudanin da mahaifin ta ya jefa ta. Ta nufi cikin gida tana tafiya tana hada hanya, saura kadan su yi karo da Hajiya Rabi da ke kokarin hawa benen Alhaji. Ai kuwa ta bangaje Hajiya sai da ta kusa kai wa kasa don ba ta zaci bangazar ba, duk da ta ga Amanin ta taho a fusace kamar kububuwa, ta ce a ranta, mai yiwuwa ita da baabzinen Alhaji ne, don ta san shi kadai ya tsaya wa Amani a makogaro ta kasa fyato shi. Don ya fi karfin ta a gun Baban ta.
Hajiya Rabi ta dafa bango kafin ta kai kasa, ta ce, Ni ki ka bangaje? Kwaya ki ka sha da ba za ki dinga lura ba kina tafiya kai a sama kamar zakanya? Ai ba ni na kar zomon ba, ko ratayar sa ba a ba ni ba, jairar yarinya tatacciya, mara kunya, goyon namiji.
Amani ta sa kafa zata hau bene kenan, jin abin da Hajiya Rabi ta fada ya kara tunzura ta, da ma ya ya lafiyar Kura? Alhaji ya gama kaskantata da cewa zai bada sadakar auren ta ga yaron sa da ta fi tsana a duniya, wannan annamimiyar kuma ta ce mata goyon namiji? Bari ta nuna mata goyon namiji.
Ta wawuri Hajiya Rabi ta maka da kasa, da ma Hajiyar ba ta da jiki sam, Hajiya ta zuba ihu amma ba wanda ya jiyo ta sai Rakiya mai aikin Amani. Ita ta zo ta rike Amani da ke huci kamar maciji ya sare ta.
Rakiya ta shiga lallashin ta tana fadin, Uwar daki na mai abun alheri, Hajiya babar ki ce, a dinga hakuri, uwar ki ce kamar kowacce uwa tunda Alhaji na auren ta. Ki yi hakuri ki wuce sama, bana so ki karasa gawar da ba taki ba. Ko ba kya ganin babu tsoka a jikin ta? Me za ki dauka in kin dake ta?
Amani ta soma hawaye, wanda ba ta san yaushe suka zubo ba, zafi biyu ne ya tarar mata, ta ce, Rakiya bar ni in zubar mata da hakora don ta fi tabbatarwa ni jaira ce, tatacciya, mara kunya, goyon namiji.
Rakiya ta yi maza ta ce, Wane mutum? Wane ita ta yi miki wannan zagin duk inda alkhairi yake ga talaka kin iya shi, zagin data yi miki ba zai rage ki da komai ba tunda ba ya fitowa a goshi. Kowa ya san albarkacin ki ta ke ci da ta yi wannan dadewar a gidan nan.
Da haka Rakiya ta samu ta lallashi Amani ta raka ta har dakin ta ta dawo sannan ta tada Hajiya da ke kuka tana fadin, yau sai Alhaji ya sake ta kafin mahaukaciyar yar sa ta karya ta a banza.
Tana tashi wurin Alhaji ta nufa, lokacin Mukhtar bai dade da shigar da shi dakin barcin sa ba, shi kuma yayi masa sallama ya tafi gidan sa. Alhaji yana kakkabe filon sa zai kwanta, Hajiya Rabi ta fado dakin tamkar an jefo ta.
Biro da takarda ta dauko ta kawo masa har kan cinyar sa ta ce, Sakar ni, na ce sakar ni, kafin in sa filo in danne ka wallahi. Ka haifi jaraba, ba tarbiyya ba ganin girman na gaba, in sha Allahu ita ce ajalin ka!
Alhaji Usman ya ce, Innalillahi wainna ilaihi rajiun. Kawai sai ya karbi takardar ya rattaba wa Hajiya Rabi saki. Ya ce, Duk abin da ke sassan ki ki kwashe ki tafi da shi na ba ki, amma tunda ki ka muzanta Amani da mugun kalami irin haka na gama auren ki, da ma ita ta ke roko na in zauna da ke.
Bakin halin ki babu wanda ban sani ba da yawon ta zubar da cin amana ta. A sauka lafiya Umma-ta-gaida-Assha.
Amani da ta shiga daki duk da lallashin da Rakiya ta yi mata amma zuciyar ta ta kasa yin sanyi, sai tafasa ta ke yi abubuwa goma da ashirin, sai kawai ta hada kai da gwiwa a tsakiyar gadon ta tana rera kuka tamkar marainiya. Ko da yake ita da marainiyar da uwar ta ta mutu ta bari tun haihuwa ai ba su da maraba, don ko hoton mahaifiyar ta Alhaji bai taba nuna mata ba.
A yau tana kewar mahaifiya ko yar uwa mace, ko dan uwan da za ta kai wa kukan ta, ko wani babba a dangi da za ta kai wa karar Daddy a kan kasksanci da tozarcin da yake shirin yi mata (a wurin ta).
Aure da Mukhy shi ne mafi kaskancin abin da Daddy zai yi mata da ba za ta taba iya yafewa ba. Kuma ko sama da kasa za ta hadu, ba za ta yarda ba, za ta gudu kawai wajen mahaifiyar ta su neme ta su rasa, za ta cire kudade anyhow ta biya mai yi mata bincike kawai ya turo mata adireshi ta koma wajen mahaifiyar ta. Ta yarda yanzu Alhaji ya fi son Mukhy tsintacce a kan ta.
To za ta bar musu gidan, gabanin bashi auren nata. In yaso Alhaji ya maido Mukhtar dakin ta na gidan sa ya zauna madadin ta karshen kaunar da zai nuna masa kenan bayan ta bashi sadakar auren ta.
Hamida ta fado mata a rai, ta share hawayen ta dauki waya tana dialling lambar Balewa. Duk da ta san maganar Hamida kullum daya ce, ta dinga yi wa Daddy biyayya, yau ta san Hamida ko za ta tsokane ta to kuwa za ta taya ta bakin cikin masifar da ta ke neman tunkaro ta.
Abokin kuka aka ce shi ake gaya wa mutuwa, duk da Hamida ba koyaushe ta ke taya ta kuka ba, wani lokacin ma laifi ta ke ba ta, ba ta iya boye mata komai da ya shafe ta saboda tsananin haduwar jinin su.
Ba jimawa Hamida ta daga waya da sallama, sai Amani ta daddage ta bude murya da karfi ta fashe da kuka mai sauti, don da can mara sauti ta ke yi.
Kafin Hamida ta ce komai, sai da ta fara toshe kunnuwan ta da yan yatsun ta, kada a fasa mata dodon kunne, sannan a hankali ta ce, MUKHY ne ko!
Ita ta san Amani ba ta da wata matsala a yanzu da ta wuce Mukhtar. Har ta saba yanzu in Amani ta kira ta, to ta san Mukhtar ya kunso mata. Ita kuma ko kadan ba ta ganin laifin sa, ina laifin mai son Baban ka? Mai taimaka masa?


1 Comments On AMANI
avatar
nafisa-adamu

8 months ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment