Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zata zo ta nemo ta su shirya. A ganin Hamida babu mai iya auren Amani ya juya ta sai jarumin namiji saboda izzar ta. Ta kuma yabawa Mukhtar wajen jure rayuwa kusa da Amani alhali kullum tana kyarar sa da gori kala-kala. To amma Alhaji ya riga ya karbi maganar abokin sa ta kuma ce mata ta yi masa biyayya a kan maganar Alhaji Sadi, yanzu kam ta fi mata shaawar auren Mukhtar yaro dan uwan ta mai halin manya.
Zata dukufa taya Amani adduar samun zabi mafi alkhairi a matsayin ta na aminiya ta kwarai. Miji wanda zai taimaka ya saita musu hankalin ta, tarbiyyar ta, addinin ta da nutsuwar ta. Wadanda duk ta rasa a dalilin rashin tashi gaban mahaifiya.
Sanda ta koma dakin maghriba ta kawo kai, Mukhtar na yima Alhaji alwallah zai yi sallah yadda yake yi daga kwance, sai ya tabbatar Alhajin ya tada sallah sannan ya shiga ya dauro tasa ya fito, sai ya tadda Amani ta ja ledar nashi abincin tana ci ba kunya ba tsoron Allah fuska tamke, an ce yunwa ba kanwar uwa bace.
Girgiza kai yayi ya shimfida dardumar da yake sallah a kai ya tada sallah a gefen gadon Alhaji.
Ko da ya idar da sallah bai ce mata don me ta ci masa abinci ba, ya san dama in yunwar cikin ta ta kama ta zata ci ne kullum haka take masa, ba don komai ba sai don kada tace ta gode a duk lokacin da ya sayo masu abinci.
A haka sauki ke ta samuwa ga Alhaji Usman, bakin sa da ake ta gasawa ya fara fidda magana sosai, likitocin sa sun ce duk bayan watanni shida zasu dinga zuwa check up, duk da tafiya da kafafu bata samu ba don haka suka ce Alhaji zai dinga amfani da wheelchair.
Watan su guda kenan suna jinyar Alhaji amma ba abinda ya canza a alaqar su. Yau suka sauka a gida Mukhtar na turo Alhaji a wheelchair inda Haj. Rabi taje ta taho dasu daga filin jirgi tareda sauran ma'aikatan kamfanin Faskari. Kowa ya zo falo ya jajantawa Alhaji yayi masa sannu da dawowa.
Malam Tajuddeen shi ya gaya musu zuwan Alhaji Sadi Talle uku bai samu Alhajin ba, yace kuma layin Alhajin da yake da shi baya tafiya, sun gaya masa Alhaji asibiti yaje babu lafiya, ya ce duk ranar da suka dawo Malam Tajuddeen ya sanar da shi.
Ba Alhaji ne kadai fuskar sa ta sauya ba har da ta Mukhtar. Amani tunda ta haura sama ta bar su bata kara saukowa ba.
**** **** ****
Washegari kuwa tunda safe Alhaji Sadi ya zo cikin rantsatstsiyar motar sa Acura, kai da ganin irin kwalliyar da ya caba cikin sassalkar shadda fara kal, zaka san ba dubiya kadai ya zo ba har da zance na saurayi ga budurwa don fara kafa gwamnatin sa.
Mukhtar baya gida yana company don gudanar da ayyukan da suke jiran sa duk da cewa yana rage ayyukan sa daga can asibiti ta kwamfuta wadanda sakataren sa ke tura masa, musamman in Alhaji na barci, zaka same shi yana aiki cikin kwamfuta yayin da zaka samu Amani na harkokin ta cikin wayar ta cikin dakin ba ya ko daga ido ya dube ta, amma a zuciyar sa ya na takaicin ace mace bata da abun yi sai shiga social media, babu lazimi sam babu karatun Alqurani, Amani fa ko addua take son yi sai dai ta roki Hamida tayi mata don a cewar ta bata iya hana idon ta barci, kuma Hamida ta fi ta juriyar tsayuwar dare. A hakan da yake yi ya samu ya rarrage ayyukan kamfani da yawa ta yadda yanzu da ya dawo ayyukan basu cude masa ba, ko da yake yanzu ayyuka sun karu masa tunda shi yake gudanar da duk wanda Alhaji ke yi da kan sa a lokacin da yake da lafiya.
Aka yi wa Alhaji Sadi iso falon Alhajin, bisa umarnin Alhajin. Yana shiga ya ga Alhaji cikin wheelchair a zaune yana kallon talabijin. Alhaji Sadi ya ce Ya salamu sallim, ashe ciwon babba ne haka? Yanzu da wadanne kafafu zaka yi takara? Kai bana jin ma jamiyya zata yarda in tsayar da mai shanyayyen barin jiki kan kujerar gwamna tunda ba ni kadai ke da jamiyyar ba.
Sannan ya zauna gefen sa ya bashi hannu yana fadin sannu, sannu yaya jikin naka? Kana iya magana dai ko?
Alhaji ya ji ciwon wadannan maganganu na Alhaji Sadi, amma ko a fuskar sa bai nuna ba, sai yayi murmushi yace ai ba sai ka gaya min na zama mara amfani ba yanzu, nima na sani, na kuma yarda duniya da dan Adam duka ba a bakin komai suke ba, yau ne kake mutum gobe zaka iya zama rabi gawa ko duka gawa, na yi kurakurai masu yawa a rayuwa ta dana ke neman yafiyar ubangiji a yanzu ba takara ce a gaba na ba, tuni na dade da janyewa.
Yanzu zan maida hankali na ne akan ibadah da neman guzurin lahira da nemawa diya ta kyakkyawan Future.
Da kyau. In ji Sadi Talle, wannan tunani ne kayi mai kyau, amma ina fatan ba zai shafi yarjejeniyar mu ba. Ka fadi duk abinda kake so daga gare ni in yi maka, koda tsayar da wannan balaraben yaron naka ne na ga alamun sa jajirtacce ne kuma namijin duniya ne ko daga takun sa, yana da leadership appearance, amma bayan ka bani auren Amani, yau da shiri na na zo don muyi ganawa ta musamman da ita.
Alhaji yayi murmushi ya ce yadda na fasa takara haka na fasa aurar da ya ta, zan bata yancin ta ne na tafiya karatu ta kuma kawo duk wanda take so da kanta na aura mata, ko da kuwa kai din ne, don haka a adalci irin nawa, na baka damar ganawa da Amani yau, ka ji raa yin ta a kan ka, ka nemi soyayyar ta, in ta amince zan fi kowa farin ciki tunda ba yau muke tare ba na san baka da matsalar da zaa hana ka aure.
Idan kuma Amani ta ce bata yarda ba sai kayi hakuri ka nemi wata. Ina Mukhtar ina tsayawa takarar gwamnan Katsina shi da ba ma dan kasar Najeriya ba? Baabzine ne fa!

Alhaji Sadi sai ya rasa abin cewa, amma tabbas ya ji dadi da Alhaji ya bashi damar ganin Amani.
Ya dauki wayar sa ya kira Amani, da kyar ta daga cikin magagin barci, ta fara korafi Daddy ka san gajiyar da ke jiki na kuwa ka tashe ni da safen nan? yi hakuri Tafisu, sauko yanzun nan amma kisa mayafi don na san ki da shirme. Kafin ta ce komai ya kashe wayar sa ya barta da mamakin ko lafiya yake fadin tasa mayafi? Saboda ya ji Mukhtar din sa na korafi shine shima yau ya koya, wato duk inda takurawa take sai Mukhy ya nemo mata ta hanyar juya kan baban ta da irin raayoyin sa na akida.
Tana mitar tana komai ta saka Abaya da mayafin ta da silifas din bakin gado, tana saukowa suka hada steps da Haj Rabi saura kadan Hajiyar ta bangaje ta, Amani ta kauce. Haj. Rabi ta ce ji mana? Amani ta dan dakata da sauka daga steps din ba tare da ta juyo ba. Haj. Rabi ta tako ta iso bayan ta ta soma magana cikin zafin murya.
Jiya na nemi saki a gun Baban ki don na fi karfin yi wa mai shanyayyen jiki takaba ko jinya, ni ba gado ba ba komai ba, ya ce magana tana hannun ki, ke kika hana shi sallama ta da tuni ya sallame ni. To don uwar ki ke kike aure na da zaki hana a sake ni?
Da sauri Amani ta girgiza kai don bata taba jin wanda ya zagi uwar da ko gani bata taba yi ba sai yau, wadda duk da bata san ta ba, zuciyar ta cike take da kaunarta.
Haj. Rabi ta cigaba da cewa.
idan kin haifu cikin Usman da Jalan yau ki sa ya rubuta min shika uku, idan kuwa kin ki, in kun ki ji ba kwa ki gani ba. Don wallahi sai na saka masa filo a hanci na karasa shi, ko in saka masa shinkafar bera a abinci ya ci ya karasa, kuma dole a bani tumunin takaba. Amani bata iya ta karasa jin maganganun Hajiya Rabi masu neman fasa mata kwanya ba, ta wuce falon Alhaji da sauri. Ta fado dakin cikin gigita tamkar an jefo ta.
Zata yi magana ta ga Alhaji Sadi a zaune, ai kuwa fushin ta ya kara ninkuwa, ta juya za ta koma. Alhaji ya ce Tafisu bakon ka Annabin ka.
Ba don jikin ta yayi sanyi ba ta dawo ta zauna, sai don bata son kunyata Baban ta a idon Sadi Talle. Ta daga ido tace me kake so a wajena Malam? Alhaji ya soma gurgura kujerar sa mai tayoyi ya koma cikin dakin barcin sa ya bar su a falon.
Babu kunya babu tsoron Allah fuskar sa kamar gonar auduga ya ce me kuwa na ke so ban da soyayyar ki Amani? Wadda nake fatan ta kai mu ga aure nan ba da jimawa ba?
Amani ta yi kuta, ta ce ina maka kallon Babana ba don haka ba da na ce an yi furfurar banza, ka so hada ni rigima da Babana Allah ya fi ka, yana zaman zaman sa ka sa shi a damuwar data kai shi ga faduwa, wani ya baka aure na ka bashi takara shin Katsinar taka ce? Halan bai gaya maka cewa ta lafiyar sa yake ba yanzu ba ta sayar da yar sa ba? Aikin banza aikin wofi to bana son naka, ko a kafa aka daura min kai zan kunce in zura da gudu Alhaji Sadi ya ce ke mara kunya! Ya ishe ki haka, kada kimin gorin halitta don duk muni na ban kai na uban ki ba. gara ni ina iya auren shi kuwa me yake kullawa matar sa sai dai ta je waje. Don haka kada ki sake ki zage ni yanzu in tattaka ki a wurin nan.
Sai gani suka yi an daga labulen dakin an shigo da sallama. Mukhtar ya bayyana a falon cikin bakaken shirt da wando na NEIMAN MARCUS, sumar nan nannadaddiya ta sha gyara da Argan Oil tayi lub a kan sa har ta sauka kadan a kan wuyan sa. Amani na ganin shigowar sa, bata san me yasa ba, sai taji duk wani rauni na duniya ya rufto mata, ga bakin cikin aj Haj. Rabi da tsoron kalaman ta, ga na wannan mutumin, ji tayi tamkar wani savior ya zo gabanta don ya kawo mata dauki, kawai sai ta mike ta nufi Mukhtar da azama ta rungume shi ta fashe da kuka mai karfi.
Mukhtar ya kusa suma a tsayen da yake, sai kawai ya tsaya kamar an kafe shi a bakin kofar ya rike Amani dake kara neman mafaka a kirjin sa, yana kokarin zamewa tana kara rike shi, sai ya ga abin kamar a cikin mafarki amma duk da haka ya iya saita kan sa. Tsawa ya daka mata ya ce sakar ni nace, bana son sakarci.
Cikin jin kunya ta cika shi tana kuka tana nuna Alhaji Talle. Ka roki Alhaji ya yi min iyaka da su, shi da Haj. Rabi, ka roki Alhaji kada ya kara bawa mutumin nan damar gani na, tunda ya zage shi ya ci mutuncin sa. Alhaji Sadi ya yi tsaki ya tashi ya fice daga gidan. A ran sa yana cewa ba don albarkar abota ba sai yayi wa yarinyar nan asiri ta rasa mijin aure.
Mukhtar ya zuba hannayen sa duka biyun a Aljihu, ya zuba ma Amani ido tana ta kuka, ta cigaba da cewa ka fada ma Alhaji na bashi wuka da nama ya aura min duk wanda ya ga dama amma ban da wannan mutumin kuma na yi masa lamuni ya saki Haj. Rabi. Ka rokar min shi ya gaya min inda uwata take, na yi alkawarin maido masa ita gidannan ko tana so ko bata so. Amma ban yarda ya kara auren kowa ba in dai don siyasa ne ya hakura tunda bashi da lafiya.
Tausayin ta ya tsirgawa Mukhtar har cikin ran sa, amma Mukhy da taurin rai irin nasa juyawa ya yi zai bar dakin ba tare da ya ce mata komai ba. Amani ta tsanan ta kukan ta tana cewa ka taimake ni!
Mukhtar saida ya dafa kofar ficewa ya juyo ya dube ta, da idanun sa da suka kada suka yi jazir, ba abinda yake gani sai Amani zaune da Alhaji Sadi suna zance, in the first instance ta san bata son shi me ye na saukowa kasa har ta kebe da shi? Sai don ya zage ta zata zo masa da wasu zantuka da basu shafe shi ba? A fusace ya ce me yasa sai ni? Me yasa sai ni zaki aika na gaya wa Alhaji sakon ki? Baki da baki? Baki fi ni kusa da shi ba? Ko ko ni dan aiken ki ne? Mtsw!
Yasa kai ya fice daga falon, zuciyar sa da gangar jikin sa da Amani ta makalkale suna vibrating. Kai tsaye mota ya dauka ya bar gidan zuwa nasa gidan da Alhaji ya bashi wanda babu nisa zuwa na Alhajin.
Mukhtar yayi rigingine bisa makeken gadon dakin barcin sa ya na tuhumar kan sa akan me ke faruwa da shi haka? Me ke addabar zuciyar sa? Me ke saka zuciyar shi cikin jin zafin Amani, don kawai ya gan ta kebe da Alhaji Sadi? Shin abinda yayi mata anya ya kyauta tunda yau ta zubar da makaman yakin ta ta nuna masa da gaske taimakon sa take bukata???
Why is he so harsh on her??? Duka baya da amsar ko daya, don haka ya ci gaba da tuhumar kan sa yana nemo hujjar kare kan sa daga tuhumar da ya samu zuciyar sa na yi wa kana sa da kan sa a kan Amani.
**** ***** **** ****

Amani da zazzabi mai zafi ta kwana, don bata iya ganin Daddyn ta ba sai a washegari. Shi da Mukhtar suna balcony Mukhtar na bisa fararen kujerun roba da aka zuba a wurin suna Magana, Alhaji na zaune cikin Wheelchair din sa. Da alama sensitive magana suke yi domin Alhaji har share hawaye yake yi da hannun sa mai lafiya. Abubuwan da yake gaya wa Mukhtar yau ko Amani bai taba gaya wa ba. Yana gaya masa tarihin sa ne da kauyen da ya fito wato Faskari da yadda duniya da dukiya suka rude shi yayi abondoning dangin sa ko ziyara baya kai musu balle ya taimake su, bayan dukkan su talakawa ne na gamu kashe mu masu tsananin bukatar taimako.
Yace Mukhtar ban san halin da suke ciki ba yanzu, bani da masaniyar suna raye ko sun mutu sun bar yayan su na garari cikin babu, ban tashi tuna cewa ban tafiyar da rayuwa ta dai dai ba sai yau dana nakasa, ina kuma son su yi min wani amfani wato daura wa Amani aure.
Gaban Mukhtar ne ya yi bugawar dakikai masu yawa, kan sa ya wani irin sara. Ya dauka Alhaji ya janye kudurin sa na aurar da Amani ga abokin sa? Ya tuna rokon da ta rika yi masa jiya a kan ya taimake ta ya roki Alhaji ya fasa bata so, ko cikakken sauraro bai yi mata ba sabida a wajen sa Amani ba mai cikakken hankali bace.
Shi kan sa Alhaji, sai da yayi noticing canjawar da fuskar Mukhtar tayi. Mukhtar bai ce komai ba a kan duka abubuwan da Alhaji ke fada masa, Alhaji ya cigaba da bashi labarin rayuwar sa inda ya ce.
***** ***** ****




ASALIN HON. USMAN FASKARI

Na fito daga garin Faskari ta Jihar Katsina, mu uku ne a wajen mahaifin mu, mu biyu cikin mu guda ni da Malam Idrisu. Dayar mace ce uwar ta daban wato kanwar mu Sahura.
Malam Idrisu yana da bataliyar Iyali domin kuwa matan sa uku kowacce tana da yaya maza da mata sun haura goma. Sahura an yi mata aure a garin Funtua. Ban san adadin yaran da ta haifa ba.
Asali na fito birni ne neman ilmin boko, sabanin yaya Idrisu da yafi maida hankali akan sanaar mahaifin mu wato Dukanci.
A rayuwa ta ina da burin in tara kudi, in kuma auri kyawawan mata in cika gida dasu,duk da ana yawan cewa ni mummuna ne Idrisu ya fini kyau.
Nayi makarantar koyon kanikanci a garin mu Faskari, da mahaifin mu ya rasu sai nayi wa yaya na da kanwar mu Sahura sallama na ce na tafi karatu birni. Mahaifiyar mu a lokacin bata tare da mahaifin mu tana aure ne a wani gari Kaita. Duk dai a cikin Katsina ne.
A wannan lokacin samun gurbin karatu a jamioin Najeriya ba abu ne mai wahala ba, saboda gwamnati neman masu yin karatun take yi ruwa a jallo.
Na samu gurbi a Katsina state Polytechnic inda nayi HND dina a fannin Engineering, daga nan na samu gurbi a Jamiar Bayero ta Kano, naje nayi digiri na na farko akan Architectural Engineering. Na dawo Katsina na fada harkar siyasa.
Na shga siyasa da kafar dama, amma hakan bai hana ni shaawar kasuwacin kayan gine-gine ba wanda akan sa nayi karatu na.
Alhaji Sadi Talle aminina ne tun na kuruciya a lokacin shi yana kasuwanci da kasashen Africa. Shi ya sakani cikin harkar fitar da Aluminium Ore da Iron Ore daga Sierra Leone zuwa kasar France. Kasuwanci ne wanda yayi mana sanadin samun arziki mai yawa, wanda idan zamu dawo sai in saro kayan gine-gine daga can in taho dasu kasar Najeriya.
Cikin dan lokaci Allah ya saka min albarka a cikin nema na. Na soma tunanin wasu hanyoyin kasuwancin daban-daban har na samu na kafa kanfani na na farko wato Faskari Investment, amma duk da haka ban bar siyasa ba.
Cikin irin tafiye-tafiyen da muke yi ni da Alhaji Sadi ne zuwa kasashen Africa muka shiga Freetown wato babban birnin Saliyo, wannan karon mun zo ne musamman neman matar da zamu aura, don mun jima muna shaawar auren kyawawan matan da ke wannan kasa.
Abokin kasuwancin mu da muka dade tare shi ya gaya ma na hanyoyin da ake bi a nemi aure a wannan kasa, yace yayan attajiran kasar basa auruwa ga bako sai yayan talakawa, wadanda iyayen su ke cikin yanayi. Shi ya hada mu da mahaifin Jalan wanda manomi ne a garin, kuma talaka ne sosai, tun a hoto naga Jalan kuma tayi min dari bisa dari, na cika mahaifin ta da dukiya mai yawa ba tare da yayi shawara da ita ba ya daura mana aure, ya kuma ce in dauke ta in tafi da ita. Shi kuma Alhaji Sadi ya auri wata Jenaba wadda ita ta zame masa uwar yayan sa.
In takaice maka labari Mukhtar, ban sha ta dadi ba a hannun Jalan, domin bata sona ko kankani, ni na san saboda muni na ne, don babu abin da ban mata a rayuwa ba ita da iyayen ta, amma a cikin shekaru biyu da nayi tare da ita sau daya na taba morar sadaki na. A wancan lokacin ni kuma son da nake wa Jaian mai yawa ne, don har gobe babu matar da zan so kamar ta, duk matan da na aura bayan ta don na rufa wa siyasa ta asiri ne, amma ba don so ba ko neman yaya.
Kullum gorin Jalan gare ni shi ne ba zata taba so na ba, domin tana da wanda tayi wa alkawarin aure, na yaudari iyayen ta da abin duniya. Da tura ta kai bango na daina sakar mata bakin aljihu na don na gaji da gorin da take yi min. Rana daya Allah ya bani saa a kanta kuma ranar ne muka samu rabon Amani. Koda cikin ya isa haihuwa ta tubure lallai in maida ta kasar su ta haihu a can, ni kuma da bazan iya barin ta ta koma kasarsu ba sai na dauko mata mahaifan ta suka zo nan Katsina muka basu muhalli a cikin gidan nan, nace su zauna da ita har sai ta haihu, domin kuwa Jalan tana ta min rantsuwa da barazanar ba zata haihu da mammunan mutum kama na ba.
Ranar ne na fahimci Jalan saboda muni na take kina, in banda haka dame na rage ta da iyayen ta? Har Hajji na kai su duka, in banda haka kiyayyar ta tayi yawa a kaina sai na soma kankame aljihu na nima.
San da ta shiga watan haihuwa Jalan ta ci shinkafar bera don ta kashe kanta. Allah ya so mahaifiyar ta da suke tare ta fahimta da wuri, muka kaita asibiti hankali tashe, likitoci suka yi mata tiyatar gaggawa suka cire Amani, ita kuma suka bata duk wata kulawar da ta dace.
Tun da aka bani ya ta a hannu na, yar da aka ceto da kyar, naji na tsani Jalan, yau kuma na tabbatar ba zata taba kauna ta ba. Sai kawai na rubuta mata saki na baiwa iyayen ta. Na kuma basu kudin da zai ishe su koma wa kasar su da kula da lafiyar ta. Tun a aibiti da na rabu da su ban kara bi ta kansu ba har gobe. Wanda sai yanzu nake tunanin ban kyauta ba, don ban ma tabbatar da cewa Jalan ta rayu ba ko ta zarce, ban kuma san ya suka yi suka koma kasar su ba.
Na dauki Amina wadda na sakawa sunan mahaifiyar mu na tafi Faskari da ita, garin da rabon in shige shi har na manta sai a dalilin siyasa wato lokacin da nake neman kuriar kauyen namu, Yaya na Malam Idrisu yana can da iyalin sa, har lokacin kuma da na fara karfi banyi kyan kan taimaka

1 Comments On AMANI
avatar
nafisa-adamu

8 months ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment