Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tajudden ya dafa kafadar sa cikin lallashi yace "ka yi hakuri ka manta, na sha gaya maka sai kayi hakuri da ita in dai kana son albarkar Alhaji. Daure ka gaya mata saboda hakkinta ne ta sani, son samu ma ku tafi tare ta zama a kusa da mahaifin ta duk sanda ya bude idon sa ya ganta don itace sanyin idaniyar sa".
Malam Tajudden ya karasa inda Amani ke kokarin fitowa daga mota yace "ran ki ya dade Malam Mukhtar na son magana da ke, a kan lafiyar Alhaji ne" Amani ta dalla masa harara tace "shi kurma ne? Ko Kai ne bakin sa? Bana son kinibibi bace min da gani".
Mukhtar ya karaso wurin yana cewa "in kika sake alaqanta ni da rashin ji sai na buge bakin ki, wannan dattijon bai haife ki ba?" Ai kuwa Amani ta fusata fiye da farko tace "ka fita hanya ta don ni ba tsarar yin ka bace, mai kama da jan kosai kawai" ya kusa ya buge bakin nata ya tuna mace ce, ya kuma yarda Amani tayi fama da juvinile deliquency a shekarun kuruciyar ta, wadanda suka mika mata har zuwa yanzu da take shekaru ashirin. Bata ganin kan kowa da gashi.
Har ta wuce shi ta tuno maganar asibitin Alhaji sai ta dawo tana sosa keya tace "for your information inaso zan kai Alhaji asibiti a Jiddah don ban yarda da kwarewar wannan asibitin da ka kai shi ba".
Mukhtar ya hadiye haushin ta yace "France zan kai shi" tace "a wane dalilin zaka kai shi inda ban sani ba?" "Saboda ni Dan sa ne idan baki sani ba, daga yau ki sa a ran ki ba ke kadai ya haifa ba uwar tutiya da uban da bata iya masa biyayya" "to ban yarda ba Jidda zamu je. Akwai asibitin da suke duba shi a can, tun ina karama can yake zuwa". Musu ya kaure tsakanin Muktar da Amani, a karshe ya ce "wait pls, wai in aka bar ki kika kai shi Jiddan zaki iya jinyar sa ne? Alhaji fa yanzu komai sai an masa har wanka da tsarkin lalura, kina mace me zaki iya kulla masa? Na fada miki ki sakar min komai kawai, don ba abinda zaki iya kullawa".
Idanun ta fal hawaye, don ta tsani a dinga nuna mata gazawa don tana mace. Shima Alhaji haka yake mata, komai tace zata yi sai yace Mukhtar zai yi don ita mace ce, shi yasa take kishin sa da cewa he snatched away her father's love from her.
Mukhtar ya ga ta rasa ta cewa a wannan gabar, sai ya juya zai tafi ya bar ta a wurin. Sai ji ya yi ta ce da siririyar muryar ta mara amo.
"To ka shirya tafiyar da ni, in ba haka ba hankali na ba zai kwanta ba in bana tare da shi, ban kuma san halin da yake ciki ba".
Mukhtar ya daga gira ya ce "alright. Yanzu kika yi magana Ma'am".

At long last. Mukhtar Diffa ya sake yin nasara a kanta.
***** ****** *****

Kasancewar Mukhtar, Alhaji da Amani duk suna da 'Schengen Visa' yasa basu sha wahalar gama shirin fita da Alhaji zuwa Birnin Paris ba. Inda tun kafin su zo Mukhtar ya gama yi musu kowanne tanadi ta yanar gizo da asibitin Hôpital Saint-Louis dake tsakiyar babban birnin kasar na Faransa wato Paris.
Ranar Lahadi suka daga zuwa Paris daga birnin tarayya tare da Alhaji wanda zuwa lokacin yana cikin hayyacin sa sai dai baya iya motsa kowacce gaba ta barin daman sa.
Tuni asibitin na Hôpital Saint-Louis sun shirya musu dakin da Alhaji zai yi jinya. Babban daki ne na alfarma ciki da falo a rukunin dakunan physiotherapy department.
Daga zuwan su kuwa bayan Mukhtar ya gama settling bill din asibitin, likitoci na musamman suka fara yi wa Alhajin dukkan kulawar data dace da masu irin lalurar sa.
Mukhtar da Amani dambe ne kawai basa yi kullum saboda sain sa, don a kan baiwa Alhaji madara ko tea ma kadai kullum sai sun yi fada. Kowanne yace shi zai yi. Mukhtar a hotel ya kama nasa dakin wanda ba shi da nisa da nan da asibitin. Amma kullum tun safe har dare yana dakin majinyacin, shi yake yiwa Alhaji alwallah, wanka, tsarki da komai. Tare da taimakon ma'aikatan jinya maza. Rannan Amani har da kukan ta, tana fadin duk ya kwashe ladan ya bar ta. Bayan ita ce da uban shi dan karo ne.
Mukhtar ba kasafai yake tanka mata ba amma a sanda ta fadi hakan sai da ya kusa yin murmushi, amma ya shanye abinsa, kada ma ta ga murmushin sa, a ran sa ya ce na ji din. Dan karo kore dan gida kenan!.
Shi ya san da ace gorin Uba na tsiro, da yanzu babu masaka tsinke a jikin sa sabida gorin Amani na Alhaji ba Uban sa bane. Wani zubin yafi gane yayi mata banza wanda hakan yafi kona mata rai, har gara ya amsa mata su yi wa juna wankin babban bargo yadda suka saba tun a gida ta fi ganewa da samun biyan bukata.
Duk fadan nan da suke yi kullum Alhaji na jin su, don wani lokacin har sai ya daga musu hannun sa mai lafiya alamar yana rokon su yi hakuri su bari. A ran sa ya rasa dalilin wannan rashin jituwa, gashi yanzu duka burin sa ya taallaka a kan mayar da su abokan rayuwar juna wato su zama maaurata karkashin inuwar aure shine kadai burin sa na karshe a duniya. Kuma abinda zai bashi kwanciyar hankali a yanzu, tunda ya yarda yanzu kam ya nakasa, ba ya jin kuma zai sake tashi a kan kafafun sa nan kusa yadda yake jin jikin nan nasa. Sannan Alhaji babu baki. A kwance yake kawai yana karbar treatment amma yana hankalce da duk wani takun sakar Mukhtar da Amani mai saka shi a damuwa, don shi ba haka yake son gani daga gare su ba, so yake ya ga Mukhtar na kula da Amani kamar yadda zai kula da kanwar sa ta jini. Ita kuma ta dinga respecting din sa tamkar Yayan ta. hakan kawai yake so daga gare su.
Kullum Alhaji na hango kujerar gwamna daga nesa a idanun sa, sai ya ji wani bakin ciki ya rufe shi. Tun farko me yasa ya jawowa kan sa maganar siyasar nan? Bayan duk daukakar da ya dade yana samu a siyasa karkashin jam'iyyar Action Congress? Watakila da bai kawo zancen ba da duk bai fada a damuwar data yi masa wannan sanadin wahalar ba. Ya dade da sanin conditions din sa na hawan jini da sugar Amma ya zo ya saka damuwar aurar da Amani a ran sa har ta kassara shi. Alhaji Sadi din bai san suna yi ba, ko irin abinda zancen auren da yayi sanadi ya janyo masa yanzu.
Bakin Alhaji ya karkace baya iya magana amma kwarai ya ke so ya gayawa Mukhy maganganu da yawa masu matukar muhimmanci ciki har da son ya kira masa Alhaji Sadi Talle a waya don ya warware yarjejeniyar su. Ya hakura da kujerar gwamnan, yanzu ta lafiyar sa yake, zai baiwa Amani dama ta koma karatun da ta ke so a Jamiar da ta ke mafarkin zuwa wato Queen Mary University of London har Allah ya bashi lafiya idan ciwon sa na tashi ne. Idan kuma ba na tashi bane zai yi kokari ya cika umarnin da zuciyar sa ke bashi akan rayuwar Amani dungurungum, wadda yake ganin shine kadai mafita ga rayuwar ta da tasa!
Wadda ba zai taba bari ta rushe ta hanyar fadawa hannun mijin da ba zai rike masa ita da so da kauna da amana ba, da kuma kiyaye mata dukiyar da ya karar da shekarun rayuwar sa yana tara mata ta hanyoyi daban daban na yaki halak da yaki haram, duk don ta ji dadi kada ta sha wahalar duniya. Wanda ta kowacce fuska ya san Alhaji Sadi Talle bai cikin wannan tsarin na rukunin mutanen da ya ke yi wa rayuwar Amani wannan tanadi.
To wa ya dace?
Zuciyar sa a take ta halarto masa da kyakkyawar amsa cewa ba wanda ya dace da zama mijin Amani wanda zai cika dukkan wadannan attributes din da yake so a tare da mijin Amani, ya zame mata garkuwa kuma mijin marainiya, ya tallafi dukiyar ta da gaskiya, ya kuma saita dabiu da tarbiyyar ta da bai samu damar yi ba sabida tasirin son da yake mata kamar Mukhy din sa. Wato yaron sa kuma mataimakin sa Mukhtar Diffa.
**** ****** ****

Kamar yadda yake ga cutar stroke saidai a ji sauki ba dai a warke sumul kalau gaba daya a lokaci guda ba, to hakan ce ta faru da Alhaji Usman Faskari da aka fi sani da Hon. Faskari. Yau satin su guda kenan a asibitin. Ya ji sauki a cikin jikin sa don yana gane duk wanda ke kan sa ya kuma fara magana amma bata fita sosai, yana zama in an jinginar da shi a jikin filo, daga baya Mukhtar ya samu hanyar da zai dinga jin abinda ke ran Alhaji, wato ta hanyar rubutu da hannun sa mai lafiya don baa iya gane abinda yake fada.
Mukhy yayi sallama ya shigo dakin asibitin da Alhaji ke jinya hannayen sa rike da ledoji na sayayyar abinci da yayo musu, a kalla likita ya ce zasu yi wata guda anan kafin a basu sallama, Amani dake zaune dai- dai kan Alhaji ko ta amsa sallamar tasa. Ta maida hankalin ta ga hirar da ya samu tana yi wa Alhaji cikin kunnen sa. Wannan abu bai yi wa Alhaji dadi ba, yayi burun-burun din maganar sa duka basu gane me ya ce ba amma Amani ta gane fada yake mata kan kin amsa sallamar Mukhtar, tayi mirsisi kamar bata gane me Alhaji ke nufi ba, sai Mukhtar ya ajiye ledojin da ya shigo da su akan bed side, daya a gaban Amani, ya karasa gaban Alhaji ya kama hannun sa yana tambayar sa kome yake son cewa?
Alhaji yayi masa alama da ya bashi biro, Mukhtar ya dauko jotar da suke magana ya bashi tare da biro, Alhaji yayi rubutu ya mikawa Amani, da ta karanta zumburo baki tayi don Alhaji cewa ya yi bai ji dadi ba da bata amsa sallamar Mukhtar ba, amsa sallama ga musulmi wajibi ne. Ta ce to Daddy in dai amsa sallamar wannan mutumin ce zan shekara ban amsa ba, tunda shima ba ya amsa tawa. Mukhtar yayi dan murmushin da ya kara masa kyau, ya matsa gaban Alhaji yace Alhaji ka ga kuma ni sayayya ma na yo mana har da ita, wai ni mai kanwa, amma ko nagode na tabbata ba zata ce ba. Amani tayi maza ta ce Daddy ka fada masa kada ma ya kara sayo komai da ni, kada ya kara alaqanta ni da shi, bamu hada jini ba bamu hada komai ba, idan ina son abu na san inda zan je na sayo ba shi kadai ya san hanya a garin nan ba.
Mukhtar ya ce a ran sa kin yi da dan halak. Amma saboda ganin damuwar da ke kan fuskar Alhaji sai bai tanka mata ba, amma ya ji haushi sosai da wannan gorin nata na basu hada jini ba basu hada komai ba, dama kullum ta tashi rashin mutuncin ta ta kance masa dan karo, ai Alhaji ba uban sa bane. Sayayyar kayan ciye-ciyen snacks din McDonalds da ya yo mata da ya lura su take son ci kullum, bata da cin abinci sai su, ya dauke ledar daga gaban ta ya kaiwa nurses din da ke kula da Alhaji, bayan duk kamshin pizza ya gama cika ta, ya tado tsohuwar yunwar cikin Amani.
Amma sabida ki-fadi irin nata tabe baki kawai tayi. A ran ta kamar tayi kuka, a kufule ta ce to da ka fita da abincin ni me zan ci? Ya ce ai na dauka kin san hanyar inda ake sayowa? Alhaji kan sa sai da ya harare ta don yana jin duk yadda aka yi. Mukhtar ya zauna yana cin shawarma yana korawa da sassanyan lemon tuffaha bai kara kula ta ba. Yadda yake taunar sa gentle-gentle ma kadai abun shaawa ne ba zaka gaji da tsayawa a gefen sa kana kallon kyakkyawan bakin Mukhtar ba.
Ta yi kwafa ta mike don ta dauro alwalar sallahr azahar, amma me? Sai ta ga bakon watan ta ya zo, ga shi bata yo guzurin kunzugu daga gida ba.
Ta rasa yadda zata yi, ta kasa fitowa daga toilet din, don ta san bada jimawa ba zata soma staining jikin ta.
Gashi yanzu ta gama cewa kada ya kara sayo mata komai ta san hanya, kuma da kunya yanzu shi ba mijin ta ba ba komai ba ta aike shi sayen kunzugun mata.
Da taga cigaba da zaman a toilet zai sa har jinin ya soma naso, cikin shagwaba irin tata sai kawai ta fashe da kukan da ta san yana rikita Alhaji.
Daga Mukhtar har Alhaji ba wanda bai jiyo kukan nata ba, Alhaji har gaban sa sai da ya fadi don ya dauka wani mummunan abun itama ya faru da ita a toilet din, tunda shima tsautsayin da ya same shi a toilet ya same shi.
Inkiya da buruntun magana ya hau yi wa Mukhtar da hannun sa mai lafiya a kan don Allah ya duba masa ita ya ga ko menene, shi Mukhtar kunya ce ta kama shi, ta yaya zai bita toilet alhalin ba matar sa ba ce ba kuma kanwar sa ba? Sai yanzu ya ga rashin dacewar tahowar su ba tare da sun lallaba Haj. Rabi an taho har da ita ba, don sau da yawa in ya shigo dakin sai dai ya koma in ya ga Amani ta baza dogon sassalkan gashin kan ta tana tajewa babu mayafi a jikin ta, wannan gashi yana matukar kidima Mukhtar, ita kuma ta kasa sabawa da barin lullubi a jikin ta, kamar yadda take yi a gida a nan ma haka take rayuwar ta babu takura saidai shi ya takura ko ya rufawa kan sa asiri ya fice in ya kasa jure kallon ta, sabida dalilai na shariah, ita kuma idan ta zauna da lullubi duk sai ta ji ta takura don bata saba ba, shi da kansa ya gaji ya yi mata magana jiya da kakkausar murya a gaban Alhaji ya ce mata ki dinga saka lullubi a kan ki idan ina nan. Me yasa ke baki san duk wani ya kamata bane? Me yasa Baki gudun fitsarin shaidanu a kan ki? A lokacin zumbura masa baki kawai ta yi bata tanka masa ba. Bata san cewa wannan zumbura bakin ba karamin kyau yake yi mata ba, ya kara fiddo zahirin kuruciyar ta a fili, ko ina ruwan Mukhtar da lullubin ta da zai nemi takura mata? Lullubi zata wuni tana yi saboda shi ko me? Shi waye dinta? Me ye gamin ta da shi baya ga kasancewar sa maaikacin Baban ta wanda ya dace a ce respect yake bata? Wannan mutum akwai wuce gona da iri in ji Amani. Ko an gaya masa don shi ta zo jinyar? Ko zaman sa ta ke yi a asibitin ba zaman jinyar mahaifin ta ba?
Abinda ta fada a ranta kenan ba tare da ta tsinka masa ba wai aka ce kulawa ma yabawa ce.
Mukhtar ya san yanzun ma in aka bibiya abinda take yiwa kukan nan bai kai ya kawo ba, sangartar ta ce kawai don bai ji alamar faduwa ko makamanciyar ta ba. Alhajin ba lafiya ma ba zata bar shi ya huta da shagwabar ta ba.
Amma yadda ya ga Alhaji ya shiga damuwa sai tausayin sa ya kama shi, wannan ya tasa ko fitinanniya, ya mike zuwa kofar toilet din ya na kwankwasawa ya ce ke lafiya? Ki fito menene? Amani ta rasa abunda zata ce masa, dole ta share hawayen ta fito tana tafiya kamar a kan dan yatsan ta ko wadda kwai ya fashewa a ciki, Mukhtar ya hau kallon wannan tafiya kamar ta mai koyon tafiya ya rasa me take ciki haka? Ita kuma bata ce masa komai ba don ta san da kunya kuma ta aike shi wannan hidimar, bayan gwaleshin data gama yi yanzunnan, sai ta dauki Jakarta ta fita da sauri don ta taimaki kanta.
Allah ya taimaketa a nan cikin asibitin ta samu akwai pharmacy, ta sayo pad ta dawo ta sake shigewa toilet wannan karon da gudu-gudu ta rufe, bata ko kula tambayar da yake yi mata ba daga inda yake tsaye harde da hannuwa a kirji. Are you okay? Tayi masa banza. Ba karamin haushi ta bashi ba da share shin nan data yi, ya kudire a ran sa bazai kara shiga shirgin ta ba har su koma gida.
Alhaji ya so a ce yana da baki, ya yi sulhun alkhairi tsakanin Mukhtar da Amani, baya son wannan rashin jituwar tasu wanda zaman su waje daya tsayin sati biyu bai saka sun shaku da juna ko sun daina kyarar juna ba, su daina hamayyar nan mara dalili da shi take sakawa a damuwa da tantamar cikar burin sa a kan su.
Shi dai kullum kunnen sa sain sar su ke tada shi daga barci, idanuwan sa basa ganin komai cikin idanun su sai tsanar juna, da rashin jin dadin zama da juna da hantara da kyarar juna. Bai taba jin sun yi maganar arziki a tsakanin su ba tun zuwan su asibitin, ko sentence daya balle a je ga batun gaida juna. Basa amsa sallamar junan su sai a cikin cikin su. Babu mai ragawa dan uwan sa. Gara shi Mukhy yana rage uzzura mata a dalilin kaifin idon Alhaji.
Data fito daga toilet ficewa ta yi ta bar musu dakin ta koma reception din asibitin ta zauna a kujera nesa da jamaa ta kira Hamida Balewa. Hamida ta ce mutuniyas ina kika shiga ne? kwana biyu ban ji complain din dan Alhaji ba Da 'yar damuwa a muryar tace tana asibiti tare da Daddy a France, Daddy na ya samu stroke Hamdy ki yi masa addua na san ke mai addua ce mai yawan sallah ce da tsayuwar dare Hamida ta shiga juyayi, a karshe ta jajantawa aminiyar ta, ta ce ke da Haj. Rabi kuke jinyar kenan?
Wani mikakken tsaki ya fito kai tsaye daga bakin Amani, tace cikin dan daga murya kema kin san ko da waye, ko baki tambaye ni ba, ni da waye kuwa banda bare ka fi dan gida, yana nan ya hana ni sakat, ya hana ni samun ladan uba na, masifar yau daban ta gobe daban, ke sai ki rantse da Allah yana da gadon Daddy ko tare Alhaji ya haife mu, tare kuma yake so mu rayu dole, ya shiga komai na gidan mu yayi kane-kane ya fi ni iko da uba na yanzu sai ta kama matsar kwallah, Hamida tana so ta yi dariya sabida wannan sakalci na Amani, amma ta san Amani bata cikin mood din da take bukatar a yi mata dariya, don tsakanin ta da Allah take sharing mata damuwar ta, don bata da inda zata je ta fada ta ji sanyi, wannan Mukhy! Ya addabi aminiyar ta, ita kuma haka nan yake burge ta, bata ganin laifin sa ko kankani, da kullum Amanin ke nanatawa, wanda duk ciki in ka saurareta zaka fahimci ba komai ke damun ta ba sai kishin son da mahaifin ta ke ma Mukhtar din.
Hamida ta nisa tace kin san Allah Amani, idan har na isa in baki shawara ki dauka to ki koma girmama Mukhtar, ki kaunace shi matsayin dan uwan dake taimakawa Daddyn ki, ki bashi gurbin Yayan da baki da shi, ku zamawa Alhaji Yaya da kanwar sa.
I'm sure duk da ban sani ba Alhaji haka yake so ya gan ku, musamman a yanzu da bashi da lafiya ku biyu ne a kans a kuke jinyar sa.
Idan ya bar miki jinyar bazaki iya ke kadai ba dole sai namiji dan uwan sa idan ana maganan stroke.
Kuma kin ga wannan fadan da kuke ta yi a kan idon Alhaji yana saka shi a damuwa musamman cikin yanayin da yake a yanzu, shi fa Daddy in na fahimta saboda Allah yake son Mukhtar din nan. Hayagagar ki bata isa tasa ya kore shi ba, da zai kore shi da tuntuni ya kora don gudun bacin ran ki.
To fadan da yafi karfin ka hausawa suka ce ka maida shi wasa, sai ka zauna lafiya.
My friend I want you to stay cool and healthy, kada Mukhy yasa jinin ki ya hau, zuciyar ki ta buga a banza ya yi wa Alhaji da kan sa asara. Ta karasa cikin dariya ta kuma yi maza ta kashe wayar ta. Amani na kururuwar sai tagaya mata me take nufi da hawan jinin ta ta ko bugawar zuciyar ta zata zamo asara ga Mukhtar. Meye manufar ta?
Hamida nata dariya ita kadai ta tura mata text. Ga abinda ta rubuta mata.
kan ki ake ji kullum a kan sa, kin hana kan ki zaman lafiya saboda shi, watch your actions over him, you care too much for him, listen to your heart and understand the actual feelings.
-Yours Hamdy.

Amani ta kusa zagin Hamida, ta kira ta back yafi sau biyar Hamida ta ki dauka, kamar ta yi hauka ita kadai wai Hamida ta zageta, zagin da baa taba yi mata irin sa ba, ta rasa wanda zata ce ta saurari zuciyar ta a kan sa sai Mukhtar? Me zata saurara din banda bugun zuciyar ta dake karuwa kullum a kan bacin ran da yake sanya ta kullum?
Hamida daga inda take sai murmushi take yi rike da wayar hannun ta, ta dubi fuskar wayar kamar Amani take kallo tana mata murmushin karfafa guiwa, haka kawai ta samu kan ta tana ma aminiyar ta shaawar auren Mukhy din nan, duk da kasancewar sa a karkashin mahaifin ta, ta shiga yi ma Amani adduar samun daidaiton raayi da fahimtar juna tsakanin ta da wanda take ganin ya shige gabanta. A ganin Hamida ba wanda zai iya da ita da halayen ta duk duniya sai wannan Mukhtar din, da tun yanzu yake juya Amani wanda hakan ke nuna zai iya jarumtakar zama da Amani da dukkan halayen ta, ta san zama da Amani sai jarumin mutum, duk kawayen su na makaranta babu wadda Amani bata yi fada da ita ba itama don ta zame mata kamar 'yar uwa ne ko sun yi fada ita da kanta Amanin

1 Comments On AMANI
avatar
nafisa-adamu

8 months ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment