Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da sajen sa yana murmushi yace ai kawai Hon. Ka ce ta zo gidan sauki tuwo na mai na, abu nawa maganin a kwabe ni. Ka bani auren ta ni kuma na maka alkawarin kujerar gwamnatin Katsina sau biyu, ko ana ha maza ha mata sai ka yi.
Hon. Usman a matsayin sa na uban da bai taba jin wani ya tare shi yace yana son Amani ba, saboda kowa cewa yake tafi karfin sa saboda izzar ta da irin rainon da yayi mata, sai ya ji dadin maganar kwarai, ya ga cewa tabbas Alhaji Sadi zai iya da Amani ba tare da yace tafi karfin sa ba shi, tunda in dukiya da mukamin siyasa ne da take takama yana da su ne shima Sadi a cikin su yake dumu-dumu har ya dara shi komai yanzu, in ka dauke yawan shekarun sa da suka zarta nasa, da furfurar data soma samun muhalli tsilli-tsilli a saman kansa, sai ya ga cewa zai iya bashi auren Amani muddin zai taimaka masa ya zama gwamnan jihar su.
Babban burin sa na yanzu kenan wato zama gwamnan jihar Katsina.
Alhaji Sadi bai bar gidan ba sai da suka kulla yarjejeniya a rubuce da shi da Alhaji Usman cewa zai tsaya masa a matsayin sa na shugaban jamiyyar PRC a bashi takarar kujerar gwamna shi kuma kafin nan ya aura masa yar sa Amani.
Ya so a yi maganar nan a gaban Mukhy, amma Mukhtar din tunda ya zame da sunan zai je yayi sallah ya ki dawowa.
Haka kawai ya kasa jure mayataccen kallon da Alhaji Sadi ke bin Amani da shi, kuma in zaa kashe shi bazai ce ga dalili ba. Shi kawai yana ganin ba girman Alhajin bane.
Basu kara haduwa da Alhaji ba sai washegari. Lokacin da Alhaji ya gaya masa yarjejeniyar da suka yi da Alh. Sadi washegari suna hanyar zuwa ofishin Alhajin, Mukhtar suman zaune yayi.
Ya yarda neman Mulki yana fidda wasu dattijan a hankalin su.
Ina Amani yar shekaru 20 ina tsoho dan shekaru 65 banda kwadayin Mulki da neman sa ido rufe irin na Honourable Usman? Kai bama wannan ba wani dunkulallen abu ne ya zo ya tokare shi a makogaron sa ya kasa cewa Alhajin sa komai, sai kawai ya maida hankali ga tukin da yake yi zuciyar sa na wani irin bugawa fat-fat.
Alhaji Usman yace baka ce komai ba Mukhy, ko shawarar tawa bata yi bane? Na san ka da tsinkaye, amma nima ina da amfanin da zan samu a cikin auren, ai wato komai mutum zai yi a rayuwa yanzu ya fara hangawa ya auna ya gano ribar da zai samu a cikin sa.
Kaga in ya auri Amani zai taimakamin na zama gwamna, zai tsaya min kan duk mai son taka ni a jamiyya, abinda na tsara shine sai in nada ka mataimaki na amma ko shi ban gayawa hakan ba, ka nemo mata kayi aure kai ma mu tara dukiya iyakar tarawa, mu Mulki Katsina tare, mu ci duniyar mu da tsinke, amma na yi rantsuwa ba mijin da zai ci min dukiyar Amani, don ita na tara mawa, komai nata zai koma karkashin kulawar ka da amanar ka ko da ta auri Alhaji Sadi.
Hatta kayan daki ka ga ba sai mun yi mata ba gidan Alhaji Sadi duniya ne; babu abinda babu cikin sa. Kudin komai dana tanada don auren ta sai a kara jari dasu a boutique din ta ka ga dadin auren mai akwai kenan.
Gashi babu mace yanzu tare da shi tun rasuwar uwar yaran sa bai kara aure ba, yaran bakwai duk sun manyanta, biyar daga ciki sun yi aure. Don haka Amani bazata yi masa rainon yara ba. Ya ka gani?
Mukhtar Diffa dai ya zama mutum-mutumi a zaune. Tuki kawai yake ya rasa amsar da zai baiwa Alhaji. Bai san cewa ya bar hanyar da zata kai su company ba ya dauki wata daban da bai san inda zata kai su ba, har sai da Alhajin ya ankarar da shi, sannan ya koma da baya ya dauki hanya daidai.
Da Alhajin ya takura sai ya ji ta bakin sa sai ya ce ni me zan ce Alhaji? Banda Allah yayi zabi mafi alkhairi?. Tunda kun riga kun rubuta yarjejeniyar a rubuce ai bani da say. Kome zan ce is too late.
Sai dai naso ace Amani din da yardar ta aka zartar da komai. Saboda ina tsoron maka halin yaran zamani, kada ta baka kunya Alhaji. Yaran yau baa sha musu alwashi irin wannan.
Shima sai a lokacin yayi wannan tunanin na cewa ba lallai Amani ta yarda ta auri Alhaji Sadi ba in aka yi laakari da yawan shekarun sa.
A sanin da yayi wa Amani bata taba nuna tana shaawar a yi mata aure ba, tafi shaawar cigaba da rayuwar ta cikin hutu a gidan su, cigaba da tabara da wadaka da dukiyar mahaifin ta, ta hanyar yin kwalliya ta kece raini da sanya sitturu masu karshen tsada da hawa duk kalar motar data ke so wato yawan canza mota new mdel duk shekara, burin ta kenan.
Rana daya azo a ce an bada auren ta ga tsoho abokin baban ta don cimma wani kuduri na siyasa, abin zai zo mata banbarakwai, shima ya san ya daukowa kan sa Dala babu gammo. Dama Amanin ga ta nan ga kamar ta wajen hankali da tarbiyya.
Har suka iso ofishin Alhajin babu wanda ya kara magana a cikin su, Alhaji na cikin taraddadin yadda zai fuskanci Amani da maganar. Mukhtar da ke tuki na kokawa da numfashin sa dake faman kai kawo a tsakanin kirji da zuciyar sa.
Kwana biyu a tsakani Alhaji na ta nan nan da Amani, ya rasa ta inda zai bullo mata da zancen Alhaji Sadi, ya tuna lokacin canza motar ta yayi bari ya nemo motar da take mafarki in yaso yace mata Alhaji Sadi ne ya kawo mata a matsayin goron na gani ina so, ga Alhaji Sadin ya takura yana so ya bashi izni ya fara zuwa zance. Ya san in bay a yi da gake ba zai sha kunya idan Alhaji Sadi ya tare ta da zancen kafin shi. Don haka yau dai yayi kundumbala ya kira Mukhtar falon sa.
Suka zauna shi da Alhajin cikin dakin sirrin Alhaji, Alhaji Usman yace Mukhtar na yi abinda ya zo ya dame ni, har yanzu na kasa gaya mata zancen nan, jiya ta zo min da admission na son tafiya karatu a jamiar Queen Mary, ta ce tana so in yi mata iznin tafiya karatun digiri na biyu, ga Alhaji Sadi na maganar aure nan kurkusa, so yake in bashi izni ya fara zuwa ganin ta na rasa ta inda zan bullo mata.
Mukhtar kamar yayi dariya ya dai gintse ya ce Alhaji Amani yar ka ce, me yasa kake shayin ta? Hakan bai dace ba ko kadan Alhaji yace rikicin ta nake tsoro, baka san ta bane, wanizubin kamar sarka take fadi ki rikice ta fannin rikici, sau da dama in ta rikice min kamar mahaifiyar ta take komawa, bana sanin ta ina zan shawo kan ta. Mukhtar na so ya ce ita siyasar dole ce da zaa saida farin cikin ya domin ta? A fili kuma yace Alhaji kamata yayi ka kirawo ta ka zaunar da ita ka gaya mata hujjojin ka kamar yadda ka gaya mini, na tabbata bayan rikicin, zata zo ta fahimta tunda dai kana son takarar nan, in ya so daga baya in ta gama rikicin zata yi biyayya, zan taya ka tausar ta.
Da wannan shawarar ta Mukhtar ya dogara, washegari ya kira Amani, ya kawo takardar sabuwar mota da mukullin ta ya bata, ya ce Tafisu na ji kina korafin injin motar ki yana kara, nace bari kawai a sake wata, kafin ki zama Amarya. Amani ta karbe mukulli da murna tace My Daddy like no other, godiya nake, kamar ka san na dade ina son Lamborghini, Allah ya bar mini kai Baba na yace ai yau kyautar ba daga ni ta fito ba, daga Alhaji Sadi ne, ai kin san shi ko? Wannan abokin nawa da yazo satin da ya wuce?
Amani ta ce ni kuwa na san shi, wannan mai katon cikin kamar kwaryar kindirmo, da idanu kamar na soyayyar gyada, yana kallon mutane tamkar mage ta ga bera. Alhaji ya kama baki yace Amani ban san ki da cin zarafin na gaba ba, shi da ya gan ki ya yaba da ke ya nemi auren ki cikin girma da daraja a hannu na da alkawarin zai tsaya min sai inda karfin sa ya kare in samu takara. Idan na samu kujerar ai ke zaki fi kowa morewa da jin dadi.
Amani tayi sakale! Tana kallon bakin Alhaji tana cewa a ranta ko Daddy ya fara shaye-shaye ne? A fili tace Daddy ban gane komai cikin maganar ka ba, wace Amanin? Ni? Kuma takarar me ka ke magana? Alhaji ya sassauta murya cikin lallashi ya shiga yi mata bayanin yarjejeniyar su yadda zata fahimta. Sai Amani ta sunkuya ta rike ciki ta daddage ta hau zuba dariya tana cewa,
Daddy! Dariya ta ci karfin ta in ta tuno kamannin Alhaji Sadi, har ya fi Daddyn ta muni da tsufa, da kyar ta tsahirta dariyar ta ce wato Daddy kawai kace ka sayarwa da abokin ka yar ka Amani bisa yarjejeniyar siyasa, to wallahi ko shugaban kasa zai tsaya maka ka samu bazan aure shi ba.
Ai ba mijin aure na rasa a duniya ba, da sani na nake korar su, don lokacin aure na bai yi ba.
Duk duniya ban ga mijin da zan iya so ba Daddy, mai yiwuwa ma baa haife shi ba, saboda ba kowa zan iya aure ba sai wanda zuciya ta take matukar so.
Alhaji ya ce Amani kada ki yi min rashin kunya, tsakani na da Alhaji Sadi amana ce. abota ce ta kwarai, yafi karfin ya nemi alfarmar auren ki in hana shi.
Amani da yake kunyar ta ragagga ce sai cewa tayi Daddy ka rage son duniya, na rantse da Allah ba don abota ka amshi wannan maganar ba sai don son Mulki, ka manta cewa (power is transient), ammma farin cikin yar ka guda daya (has to be eternal), ban san me kake nema kuma a duniya ba, da zaka mayar da ni hajar siyasar ka.
Ta soma kukan ta na halitta na shagwaba kamar marainiyar da aka fadawa mutuwar iyayen ta, na yau har da sheshshekar kukan gaske. Kukan da ya fi komai dagawa Alhaji hankali. Cikin kukan ta ce wallahi Daddy bana so, bazan aura ba, ta yaya recently na gaya maka na samu admission ina so ka yi min izni in wuce Masters dina zaka kawo wannan maganar?
Alhaji ya soma fusata yace to in ke kika haifi kan ki sai ki tafi Masters din mu gani, magana na gama, na baiwa Alhaji Sadi auren ki, don kin ga ina sakar miki da yawa shi yasa kika raina ni, karatu kin gama shi daga kwalin digiri ba kari, dama ana ta cewa na barki babu aure. Amani ta mike tana cewa to Daddy sai ka zaba ko ni ko abokin ka, idan aka takura min kan maganar nan na rantse zan sha poison in mutu ka huta, da dai in auri wannan mummunan tsohon.
Gaban Alhaji ne yayi mummunar faduwa, exactly irin kalaman da mahaifiyar ta Jalan ta furtawa nata mahaifin a gaban sa, ranar da ya bashi auren ta. Kuma tabbas ta sha poison din bayan haihuwar Amani, bashi da tabbacin tana raye ko ta mutu, don tun ranar da ya kai ta asibiti ya damka wa mahaifin ta takardar sakin ta, bayan ya dauke jaririyar yar sa, bai kara waiwayar ta ba, a dalilin ta dade tana kunsa masa bakin ciki mai yawa saboda kawai ita kyakkyawa ce shi ba kyakkyawa ba.
Allah wadaran masu aure don kyau, Alhaji ya fada a fili cikin tuno dararen da suka shude tsakanin sa da Jal'an. Allah yasa kada Amani ta yo halin mahaifiyar ta tarihi ya maimaita kansa tsakanin ta da Alhaji Sadi Talle, don shi aure da Alhaji Sadi ya riga ya gama zartar da hukuncin yin sa ba zai fasa ba.
Amani ta wuce zuwa sama ba tare da ta san halin tunanin data jefa mahaifin ta a ciki ba.
Ya dade a zaune a wajen yana tunanin mafita ko ta inda zai bullo mata ta yarda da auren Alhaji Sadi, ba abinda yake hangowa kansa sai gashi a kan kujerar gwamna, ya tuna Mukhy ma yace zai taya shi lallashin ta, da wannan tunanin ya shiga bayan gida toilet na dakin sa domin ya yi wanka ya kwanta, yana sanya kafa cikin kwamin wankan ya zame ya fadi a ciki, wata irin muguwar faduwa da ta yi sanadin kai Alhaji Usman asibiti cikin daren, Allah ne ya kawo Haj. Rabi dakin taji karar da ya saki, ta fado bandakin tana salati.
Maigadi da mai ban ruwan shukoki ta kira suka kinkimi Alhaji suka sa a mota, Malam Tajuddeen ya tuka motar suka yi asibiti da shi. Sai da suka isa asibitin Malam Tajuddeen ya kira Mukhtar.
A gigice Mukhtar ya zo asibitin, shi yasa hannu ya biya komai likitoci suka soma baiwa Alhaji taimakon gaggawa.
Zuwa safe babban likitan da ke duba Alhajin ya tabbatar ma Mukhtar Alhaji ya samu stroke wato rabin jikin sa ya daina aiki. Kasancewar dama yana da hawan jini da suga masu tsanani.
Mukhtar ya saka fuskar sa cikin tafukan sa ya na ambaton innalillahi wainna ilaihi rajioun. Tabbas dan Adam ba a bakin komai yake ba. Jiya jiyan nan suna tare da Alhaji lafiyar Allah yana kasafta yadda zasu ci duniya da tsinke da kudin talakawa idan ya zama gwamna yau a ce rabin jikin sa ya mutu?
Amani tana gida bata san abinda ke faruwa ba, tun dare take waya da Hamidah tana kuka tana gaya mata Daddy ya daina son ta, zai aurar da ita auren dole ga tsoho, kuma saan sa saboda siyasa. Tace Hamida na tabbata ba zugar kowa bane wannan aikin annamimi Mukhtar ne, don ni Daddy bai taba yi min zancen aure ba, na tabbata shi ya zuga shi tunda yanzu baya jin maganar kowa sai tasa, kuma na tsole masa ido a gidan yana so a kawar da ni ya ji dadin cuta ma uba na. Ta fyace hanci ta ce Hamdy na shiga damuwa don ban ga alamar Daddy da wasa yake maganar nan ba, kamar auren da yake son yi min din is based on political aspiration din sa.
Hamidah yarinya mai hankali tace "wato Bestie ba zaki daina tsanar bawan Allan nan ba babu gaira babu dalili? Zato zunubi ne, how sure are you shi ya zuga Daddy? Ke da kan ki kin ce is based on his political aspirations sai ki cire Mukhtar a ciki tunda shi ba dan siyasa bane. Ba lallai ya zama Daddy bai da ra'ayi sai nasa ba, kamar kina exaggerating alaqar tasu. Sabida kin damu da shi, kuma ba kya son sa".
Amani ta saki tsaki tace "na damu da shi a gidan wa? Ai ni kawai so nake ya bar gidan mu" Hamida tace "ki ji da matsalar ki ta auren tsoho ki kyale bawan Allan nan ya sarara" "shawara zaki bani ko zagi na za ki yi Balewa?" Hamidah na dariya tace "duk wanda kika zaba shi zamu yi" ta ce "to shawara ta gaskiya nake so ki bani" "shawara ta itace ki yi wa mahaifin ki biyayya whatsoever hujjar sa na aurar da ke ga abokin sa, wanda yayiwa iyayensa biyayya baya taba tabewa.
A karshe ina so ni da ke duka muyi istikhara mu nemi dacewa da zabin Ubangiji ba abinda zuciyar mu tafi karkata ba".
"Menene istikhara!" Amani ta tambayi Hamidah. "Sallah ce ta nafila da Annabi SAW ya koyar ta neman zabin Allah kan kowanne al'amari da sulusin dare" Hamidah ta gaya mata yadda zata yi. Ta kuma daure ta yi din. Ita da kan ta tayi mamaki ganin cewa zuwa washegari data tashi sai taji ta wasai babu damuwa a dalilin istikharar data yi. Har jira take Alhaji Talle ya zo yayi mata bayanin dalilin sa na kutsowa rayuwar ta. Da abinda yake nufi da Baban ta, na cewa wani suyi yarjejeniya sai kace an gaya masa ita hajar sayarwa ce.
Mai aikin ta ce ta kwankwasa mata kofa. Tana budewa a fusace tace "lafiya da sassafe haka kike damuna da bugun kofa?"
Rakiya ta karya wuya ta langabe cikin lallashi ta ce "kiyi hakuri, Haj. Ce tace in gaya miki ki fito ku tafi asibiti Alhaji na can babu lafiya". Gaban Amani yayi mummunan faduwa, abinda ya zo ran ta shine irin rabuwar da suka yi ita da Daddy din daren jiya, kada dai shi ya saka a ran sa har ya kwantar da shi rashin lafiya?
In haka ne kuwa zata yi masa biyayya iyakar iyawar ta ba Alhaji Sadi ba, ko kuturu ya kawo ya aura mata zata yi biyayya da dai a ce wani abu ya faru da Daddyn ta a kan ta.
Sabida gigicewa a haka ta fito da kayan barci a jikin ta, sai Rakiya ce ta biyo ta da mayafi bakin mota.
A yadda ta ga Mukhtar zaune a reception din asibitin ya hada kai da gwiwa, yayi jajawur abun ki da farin mutum ainun, hatta idanun sa sun yi jawur ya tabbatar mata condition din na Alhaji ba mai dadin ji bane.
Ita ta sani ko Uban sa sai haka, a irin halin da ta gan shi a ciki.
Suna hada ido ya sunkuyar da kai, ta karasa da sauri tana tambayar sa me ya samu mahaifin ta?
Mukhtar ba baki sai ido ya bi ta da shi. Ta koma ga Haj Rabi tana tambaya. Babu wata damuwa a tare da ita tace "sun ce ya samu stroke ne, barin jikin sa ya shanye, Amma zasu dinga yi masa gashin kashi har ya samu lafiya".
Daidai lokacin da aka gangaro Alhajin a kan gadon marassa lafiya aka bashi daki na musamman.
Amani ta rasa inda zata tsoma ran ta, sai kuka take yi a dakin. Haushin ta ya ishi Mukhtar yace "ko ki yi shiru ki yi masa addu'a, ko ki koma gida" ta galla masa harara da jajayen idanun ta tace "Uban ka ko nawa?" Ya ce "to zage ni" ta yi tsaki ta ce "in aka zage ka din me za'a yi?" Kai tsaye yace "banida lokacin ki yanzu, amma ranar da kika kuskura kika zagenin, zaki ga me za'a yin".
Haj Rabi ta yi salati tace "Amma ku kuwa an yi sakarkaru, ta yaya mutun yana kwance rai kwakwai mutu kwakwai kuna neman dambe da juna a kan sa? Ku kuma irin naku hankalin kenan maimakon ku dukufa yi masa addu'a?"
Mukhtar ya juya ya fita daga dakin ya bar su. Amani ta nufi Alhajin da sauri ta kura masa ido yana barci kamar ba abinda ya faru da shi. Hawaye fal idonta ta soma magana.
"Daddy in dai a kan auren da kake son yi min ne ka saka kan ka a wannan yanayin na roke ka ka tashi mu tafi gida, na amince ka aura min duk wanda ka ga dama, don Allah Daddy". Kuka ya ci karfin ta.
Haj Rabi tace "toh? Ashe ke kika jawo masa? To ta Allah ba taki ba ban shirya yin takaba yanzu ba, in bai tashi nan da sati daya ba wallahi sai dai ku sallame ni don ban shirya yin takaba yanzu ba".
Amani ta juyo ta dube ta da fusatattun idanu ta ce "in kika kara shiga sha'ani na sai na karawa wannan katon bakin naki tsini, ina ruwan ki da ni? Ko ina shiga sabgar ki? In ni na jawo masa Uban ki ko nawa? Ko kin haifa masa ko gunduren kashi ne? Ba tumunin takabar kike jira ba me kike so in ba shi ba?"
Haji. Rabi ta kama baki, tace "ke mara kunya, wadda bata ganin mutuncin kowa, na fi karfin ki yimin diban albarka don uban ki nake aure, shashasha da bata san komai ba sai sangarta da rashin kunya".
Likita ya shigo dakin ya na cewa "haba! Haba bayin Allah. Yaya zaku tsaya kan mara lafiya kuna daga murya? To daga yau mun yafe zuwan ku. Mukhtar kawai muka yarda ya zo har sai ya dawo gida".
Amani da ta riga ta zo wuya, ga haushin Mukhtar ga na Haj Rabi ga kuma na wannan likitan yanzu. Ta ce "idan uban ka ne shi sai ka hana ni zuwa in gani" likita ya juya ya fita kafin yarinyar ta soma kai duka, ya fara tunanin tanada aljanu amma na rashin kunya da rashin tarbiyya.
Ta yi tsaki tana fadin "Daddy zan sa a dauke ka daga rubabben asibitin su ka ji? Jidda zan kai ka a duba ka sosai. Get well soon my Daddy". Ta sunkuya ta sumbaci goshin sa, ta gyara masa rufuwa da bargo duk Alhaji na barcin allurar barci bai san me suke yi ba.
Waje ta fito tana tunanin abun yi, tana neman mataimaki da zai taimaka mata wajen fidda Daddy saudiyyah. Amma Mukhtar shine yafi dacewa da ya taimaka mata din gashi ta gama caccakar sa ta masa gorin Uba. Da sanyin jiki ta hau neman sa a reception amma bata gan shi ba.
Bata san ma shi a lokacin yana can yana cuku_cukun samun visar tafiya da Alhaji kasar Faransa ba.
Ya gayawa Haj. Rabi niyyar sa ita kuma tace bazata jinya ba, saidai Amani ta je. Ko kwai bata ajiye masa ba bazata jinyar shanyewar jikin sa ba, alhalin ko tumunin takaba bai rubuta a bata ba komai na Amani ne. don haka ta karata da uban ta ita kadai.
Mamakinta ya kusa kashe Mukhtar a tsaye, to dama ya bata hakkinta ne a matsayin ta na matar Alhajin. Amma Shima baya so ta bi shi don baya jin zata yiwa Alhaji kulawar data kamata, wannan aikin sai namiji kakkarfa.
Yana tsaye a gate din gidan suna magana da Malam Tajudden yana gaya masa maganar zai tafi Abuja da Alhaji don Nemo visar tafiya asibiti a Paris. Amani ta shigo gidan tare da Malam Audi Mai baiwa shukoki ruwa wanda shi ya tuka su zuwa asibiti. Tajudden ya juya ya dan kalle ta sai yace da Mukhtar din ka sanar da Amani?" Yace "kaima ka san wannan yarinyar bata cikin 'yan shirgi na saboda rashin kunyar ta. Dazu har zagi na ta kusa yi fa Tajudden".
Malam

1 Comments On AMANI
avatar
nafisa-adamu

8 months ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment