Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idanun ta mutum tamkar shi yayi kan sa, kai kace wani balaraben Madinah ne idan yana magana, tsafta da wanka sun kama jikin sa radam.
Sai ta tuno alfarmar da take so yayi mata duk da ya bakanta mata rai yadda bata zato amma wannan ce dama ta karshe da zata iya rokon sa don ba haduwa suke yi ba, sai dai ta hange shi a harabar gidan daga balcony din ta yana shiga mota zai fita ko ya shigo gidan. Ko ya zo daukan Alhaji su fita.
Ta rasa ta ina zata fara don kwata kwata babu fuska daga Mukhy, yama kara daure fuska tamau da suka hada ido don kada ta kawo masa wargi, ya lura da kallon kurillar da ta ke masa wanda ya wuce shariah. Shikuma baya son ko kalma guda ta hada shi da Amani don kada raini ya shiga takanin su irin wanda takewa kowa da ke karkashin ta.
Ya Allah ya zata yi da wannan mutum mara sakin fuska? Sai kawai tayi kundumbala tace, Man, ina son fidda kudi ne daga corporate account dina? Mukhtar bai san cewa magana take da shi ba, ya dauka ma a wayar ta take magana da wani daban don haka ko juyowa bai yi ba.
Amani ta daga murya da dan amo tace na tabbata kai ba kurma bane, but you are acting kamar baka ji!
Sai yanzu ya san da shi ta ke, ya kuwa kara daure fuska yaci gaba da tukin sa. Amani sai ta fara hawaye don abun yayi mata ciwo mai yawa, baa saba yi mata irin haka ba, kowa na gidan girmama ta yake yi yana nan-nan da ita yana rawar jiki idan ta bada umarni, balle wanda ke matsayin yaron Baban ta ya yi mata irin wann funfurus din.
Kuka ta soma yi sosai har da sheshsheka da fyace hanci, tace tunda dai na san kana ji na, halin ka ne shariya da wulakaci, to bari in fadi sako na, ya rage naka ka yi min alfarmar ko kada ka yi.
Ina so zan cire kudi 5 million zan yi amfani da su bana son Daddy na ya tuhume ni, idan ka ga alert dinnan alfarma ce kada ka fada masa tunda dai kudi nawa ne, ba na wani ba.
Mukhtar ya rage gudun motar ya dan juyo kadan ya saci kallon ta, sai kuka take tana fyatar hanci kamar wadda aka yi ma wani mugun duka, kada ya je ta daura masa sharri, don ya ji an ce masa mata makirai ne. Ya kashe motar gaba daya a gefen titi ya ce.
Da ni kike?

Amani ta ce aa da sitiyarin motar ka nake. Karo na farko da Mukhtar ya yi wani miskilin murmushi, ya ce to kai sitiyarin mota ana maka magana!.
Amani ta kara rushewa da kuka tace Allah yasa ayi maka irin wulakancin da kake yi min. Allah ya hada ka da daidai kai, Allah ya sakawa mahaifina amana ta da ya baka kake ci don ka san ka asirce shi.
Mukhtar ya bugi sitiyarin sa ya ce ban da muguwar addua ga wanda baki sani ba Maam, you will never know what a man like me is going through, I hate hayaniya, ki gaya min wace alfarma ce kike so? Bana son koke-koken banza me na yi miki? Wane kudi kike magana a kai? Kuma me zaki yi da su? Ban fahimce ki ba anymore.
Amani ta dan ji dadi, at least hargagin ta ya sa ya kula ta, ta share hawayen ta da gefen mayafin ta, ta ce ba damuwar ka bane abun da zanyi da kudi na, kawai bana so Daddy ya ji ne, da ba zaka san ma na cire ba
to kin san ba damuwa ta bane kuma bai shafe ni ba don me zaki sako ni ciki? An gaya miki ina shiga abunda baa sa ni bane? Ai kawai ki yi abinda kika ga dama nima in yi aiki na na daukar zance in kai gaba, tunda shi aka sa ni, ba sai kin saka ni cikin shaanin ki ba, mind your own business and leave me alone.
Ya ja motar suka cigaba da tafiya Amani na gayawa kanta ta gara ta canza taku, tunda har kuka yana karya zuciyar sa ya saurare ta, ko baya so, ya bata amsa ko yaki Allah to zata rage izza tunda ta lura izzar ta ke tunzura shi ya ki sauraron ta.
Tabbas yau ta gamu da wani sabon mutum a cikin rayuwar ta, wanda bata taba ganin mai hali irin nasa ba.
Bawan Allah ko wa kake da suna? Na yi rantsuwa ba ta hanyar banza zan kashe kudin nan ba, kawai bana so Daddy na ya san da fitar su.
Ta sassauta murya ta ce kayi min wannan alfarmar, ba don ni ba ba don hali na ba.
Mukhtar ya yi mata kallon kin ishe ni haka kafin yace zan yi miki only in kin gaya min gaskiyar ko me zaki yi da kudin nan, bana backing munafurci da rashin gaskiya komai kankantar su, in kina da gaskiya ba zaki nemi a boyewa mahaifin ki wani abu da zaki aikata ba.
Amani ta share ido da bayan hannun ta ta marairaice, sai ta dan bashi tausayi, ta ce wallahi ina da gaskiya ta, trust me, kuma ta hanya mai kyau zan yi amfani da su yanda ba zai gane ba, don bai san irin ciwon da na ke ji in naga kowa a jikin uwar sa ba.
Ta cigaba da cewa Malam COO (Chief Operating Officer) ni din ban taba ganin uwa ta ba sai a hoto, ban rasa komai ba amma ina so in je gare ta, ba don kuma na raina kulawar Daddy na a kaina ba, sai don kowannen su matsayin sa daban a gare ni.
Zuciyar Mukhtar ta dan yi laushi, laushin da shi kan sa bai zaci tana da shi ba, yafi zaton zuciyar sa tafi dutse tauri amma ashe akwai sauran tausayi a cikin ta, akalla ya gamsu, tunda ba shaye-shaye zata yi da kudin ba don tafi masa kama da masu banka kwaya, yace I will think over it. But remember always zaman Alhaji nake ba zaman wata Amani ba!.
Maganar shi ta karshe bata yi mata dadi ba. Ta yi kuta ta ce kai a rayuwar ka baka da humanity ne? baka da concern? Baka da sabo da mutane kuma baka daukar kowa da muhimmanci sai Daddy?
Ya murmusa kadan, har beauty point din fuskar sa ya lotsa ciki sosai yace ban san ta ba humanity din, concern kuwa ko maanar ta ban sani ba, mai yuwuwa sanda ake rabon su ni ina Diffa. Kin san ni dan Diffa ne, Diffa region, ta kasar Nijar.
Amani ta kulu iya kuluwa, ta yaya ba zai dauki abinda ta gaya masa da muhimmanci ba bayan sirrin ta ne da bai kamata ma ta gaya masa ba? Zai bi ta da bakar magana bayan ta bude masa sirrin ta? Maganar mahaifiyar ta fa take masa, wadda bata taba gani ba, yana mata maganar wani garin su.
Daidai lokacin da suka iso tangamemen gate din gidan su Amani. Dama bata son zuwa dauko Hajiya Rabi. Ba tun yau ba ta fahimci matar zal wajahaini ce (mai fuska biyu) a gaban Daddy kawai take nuna kaunar ta, a bayan idon sa kuwa kashi ya fi ta daraja a gidan nan. Shi yasa itama ta kama kan ta, sam bata shiga shaanin Haj. Rabi ko hanyar sassanta bata bi, ta kuma yi wa kanta alkawarin bazata bari Daddy ya sake ta ko ya san halin ta a kan ta ba, don ta gaji da aure-auren sa da ake faman kirga masa akan ta.
Mace ta karshe da Alhaji ya saka wai ita Zaibi, ta fadi maganar data tsaya mata a rai har gobe ta kasa mantawa, kuma daga kanta ne ta kudiri aniyar hana Daddy kara sakin kowacce mata duk mugun halin ta. Gara ta bar su da halin su ta nemo tata mahaifiyar.
Cewa matar ta yi ga gidan nan ta bar mata, karshen soyayya Alhaji ya auri Amani ya maye gurbin ta da ita.
Don haka tun kafin ya gama daidaita parking ta soma kokarin bude kofar don ta fice kada ma ya ce suje dauko Hajiya Rabi tare, sai ta ji ta gadagau wato ya rufe ta automatically.
Kallon tambayar dalili Amani tayi masa. Idanun ta fal hawaye. Mukhy ya daure fuska sannan ya shafa sumar kan sa ya ce da ita as a brother, zan hore ki da abu daya, duk rintsi kada ki kasance mai munafuntar mahaifin ki, domin mahaifin ki extraordinary Uba ne, musamman a kan ki, ban taba ganin uban da ke son yar sa irin son da mahaifin ki ke yi miki ba. Don haka bai cancanci ki boye masa komai da ya shafe ki ba.
Mai zai hana ki same shi officially ki gaya masa damuwar ki, akan son ganin Maman naki? Im sure yadda Alhaji ke son ki da girmama lamarin ki ba zai ki kai ki ga mahaifiyar ki ba.
Wane irin bincike ne saboda Allah har miliyan biyar? A kasa ake hako kudin? In gaya miki gaskiya an doki hancin ki, don an ga baki da wayau, kuma you are desperate, a kan bukatar ki, ni ki bar ni zan lallaba Alhaji ya kai ki gun Maman naki on koboless (babu ko sisin ki) ba kuma don ke ba sai saboda Alhaji ne ya haife ki. Wani kwayan mutum guda daya da nake matukar kauna da girmamawa.
Alhaji da kan sa ya fi dacewa ya gaya miki inda take, ba sai kin bi ta karkashin kasa kin sha wahala ba
Amani ta yi ajiyar zuciya tana jin wani irin relief na zagayeta a zuciyar ta, yau Mukhy kamar ba shi ba, yana magana ne ta hanyar bata dukkan attention din sa da concern as a brother, duk da ba kallon ta yake ba wayar sa ya ke dannawa a duka maganar da yake yi, amma kuma ya dauki zancen yanzu da muhimmanci, ba don komai ba sai don ya tuno tasa UMMAMIn. Yadda yake son Ummami da yadda yake son zama kusa da ita bai samu ba, ba don komai ba sai dalilin norms, culture and traditions irin na gidan su. Ya yarda rashin kulawar ta a tare da shi ne duk yayi mujazar matsalolin sa a rayuwa da a yau suka saka shi garanranba a duniya. Amani na bukatar tallafin uwa da gaske. Musamman a kan dabiun ta da tarbiyyar ta, kai har addinin ta ma yana bukatar gyara, in yayi duba da irin dressing din da take fita da shi da rashin kunya ga na gaba da irin tabarar data ke yi wa mahaifin ta.
Amani ta ce I wish Daddy din zai saurare ni a kan damuwa ta irin yadda ka saurare ni yanzu, to ba zai saurare ni ba, ban san abinda ya raba su ba amma ko zancen ta baya so na yi masa, ya dauki gaba mai tsanani da mahaifiya ta yana fadin muddin na zabi zuwa gare ta to shikuma zai sallama mata ni ne.
Ta share hawayen ta tace and I love my Daddy more than everybody, saboda da shi kadai na taso, da kaunar sa gare ni na budi ido. Ban san kowa sama da shi ba ko yan uwan mu na Faskari sama-sama na san wasu daga cikin su, bani da wa bani da kanwa.
Cikin tausayi Mukhtar yace me yasa ba zaki neme su ba? Dangi da kike gani suna da matukar muhimmanci a rayuwar mutum, musamman ke da kike mace, daya tal a wurin iyayen ki, babu dan uwa babu yar uwa, it is your duty ki nemi dukkan su ki gyara gurbin rashin zumuncin dake tsakanin ku don hakika kina bukatar su, amma karkashin yardar mahaifin ki, dont ever try to hide anything from him no matter how bitter, ba abunda lallashi da ban baki ga iyaye bazai sa su yi maka ba.
Jikin Amani yayi sanyi kadan, don ta sani bata lallashin Baban ta sam kullum sai rigima da rikici in tana son ya yi mata abu dole ya yi, a kan zuwa gun maman ta ne kawai da korar Mukhy daga gareshi kawai ya taba turje mata, tace cikin murya mai ban tausayi,
ka ce zaka nemo min Mama na? Mukhtar ya ji wani iri a jikin sa da yadda tayi maganar murya na shaking, ya bude mata kofar yace cikin basarwa idan na lallashi Alhaji ya yarda ki je din, ni da kai na zan nemo ta, zan kuma kai ki duk inda take.
Amani ta fita tana dan murmushi, a ran ta tana fadin ashe dai yana da dan kirki ko yaya ne, ga taushin murya, ga jan class, fuskar ce dai bata taba canzawa daga yanayin ta na rashin annuri da bacin rai. Tamkar wanda kullum ake yi wa mummunar bushara ko ake yankan naman jikin sa.
Bai tsaya ta gama bacewa ba ya ja motar sa ya nufi airport don cika daya umarnin na Alhaji. Wato dauko matar sa.
Ya dauko Hajiya Rabi suka kamo hanyar gida, a hanya tana ta mitar an bar ta a shanye a filin jirgi, baa zo daukar ta da wuri ba, mota ba tasa ba amma ya tafi yawon banza da ita yana kwambo a cikin gari gurin yammata, idan yana ikon sa da jin kan sa ya dinga tsayawa iya kan Alhajin da ya kawo shi ya kuma daure masa gindi yana baza iko a gidan mutane, kada ya kuskura ya shiga gonar ta. Ita warki ce daidai kugun kowa yanzun nan zata yi maganin mutum, ko Amani bata isa ta shanyata ba balle shi wani banza a banza.
Mukhtar ya sunkuyar da kai yana jin ciwo a cikin ran sa, yau wata wadda bata ko kai matsayin mai gugar takalmin sa ba ke zagin sa haka, wai kwambo! Duk ba komi ya janyo masa ba sai zabar barin gida da independent life, an ce kuma a kowanne neman halal akwai challenges, ya cigaba da tuki bai ce mata komai ba.
Ba tun yau ba ba sa ga maciji da Hajiya Rabi, ta fannin ta ba don komai bane sai don son da ta lura Alhaji na masa. Daga Amani sai shi a wadanda bata so ta bude ido ta gani a gidan nan, amma fa bata taba nuna hakan a gaban Alhaji ba. Kullum nuna masa take tana kula da Amani irin kulawar da uwa take yi wa dan ta, tana kuma son wannan yaro nasa mai hankali da amana da kullum yake yabo a gaban kowa.
Shi kuwa Mukhtar ya san wacece Haj. Rabi sanin da ko Alhaji bai yi mata ba, shiyasa kawai ya ji baya son matar, wato ya san tana dan taba yawon barbada a waje don ba sau daya ba ba sau biyu ba ya taba ganin ta a hotels daban daban tare da wani mutum. Kuma har kofar gidan mutumin ya sha kawo ta. Duk da ba zai ce ga hakikanin abinda suke yi tare ba jikin sa yana bashi tarayyar banza ce don Alhaji yana da ciwon suga mai hana lafiyar auratayya.
Yana ajiye ta ya juya ya koma Company, akwai muhimmin aikin da zai yi wa Alhaji amma tun shigar sa office din sa sai ya kasa zaune ya kasa tsaye.
Mukhtar Diffa, ya hau safah da marwah, hannanyen sa biyu zube cikin aljihun farar shaddar da ke jikin sa. Ya rasa abinda ke tsaye a wuyan sa ya ki wucewa. Ya rasa meye ya tsaya masa a rai. Sai da yayi tsam da ran sa ya fafimci ba komai bane kukan Amani yake tunawa da shagwabar ta, da fyatar hanci cikin yanayin sakalcin ta.
Sai ya ji wasu sassa na jikin sa suna respoding. Zuciyar sa na vibrating. Ya tuna matsananciyar damuwar da ke kwance kan kyakkyawar fuskar ta a kan son ganin mahaifiyar ta, sai ta kwadaita masa son ganin tasa Ummamin shima, kwarai ya gane da gaske take son ganin Maman nata, wasu abubuwan data yi a yau sun tsaya masa a rai, sun kasa bacewa, musamman kukan shagwabar nan nata is arousing something in him komai dakewar sa don bai taba ganin wanda kuka ya yiwa kyau irin Amani ba.
Tsaki yayi cikin jin matsanancin mamakin kan sa, ya dauki kiran Alhaji da ya shigo masa a daidai lokacin. Ya ce Mukhy kana ina ne? Ina office Alhaji ya fada a kasalance. Alhaji ya ce to in ka kammala ka zo zamu yi wata muhimmiyar shawara. Kai bari kawai in gaya maka. Haka kawai ina zaune wani tunani ya zo min, ina son tsayawa takarar gwamnan jihar Katsina.

Mukhtar ya yi azamar rufe baki sannan ya bude, yana mai jinjina hadamar duniya irin ta uban gidan sa, me Alhaji yake nema kuma a siyasa da rayuwar sa bakidaya? A tunanin sa duk abinda dan adam ke nema a duniya Alhaji Usman ya gama samun sa, kamata yayi ya maida hankali ga kula da tarin dukiyar sa da neman lahira da aurar da wannan gansamemiyar sakaltacciyar diyar tasa, ba neman wani mukamin siyasa ba a yanzu, wand aba lallai yayi nasara ba, a fili ya ce Alhaji bari in zo kawai, wannan ba maganar waya bace.
Yana tafe a hanya yana tunanin ta hanyar da zai bi ya lallashi Alhaji kada ya tsaya takarar nan, ba don komai ba sai don ya san mawuyaci ne alummar Katsina su zabe shi yanzu, don duk wani mukami da ya rike a baya bisa magudi ake bashi ba don alummah na so ba, sai don kasancewar yana da iyaye a babbar jamiyyah masu karfi a gindin murhun, jamaa basa son Alhaji Faskari ne saboda kankamon sa, da rashin jan talakawa a jiki sai ka ce ba dan siyasa ba. Wasu yan jaridar ma kan ce, HON. USMAN FASKARI; dan siyasar da ya rasa dukkan attributes da qualities na yan siyasa amma yana da saa a siyasa.
Mukhy na tunanin karshen ta ya salwantar da dukiyar kamfanin sa a banza, wajen kamfen, kuma ya zo bai ci ba. Mukamin Sanata daban na gwamna daban. Mukamin gwamnatin jiha tabbas sai da soyayyar talakawa.
A sanin sa ko Zakkah Alhaji baya iya badawa, har sai bayan zuwan sa gare shi, shi Mukhtar din, da ya tsaya tsayin daka da lallashi da nasiha a kan Alhajin, bisa dole ya sa shi ya dinga fidda zakka don tsaftace dukiyar sa.
Sau tari, Mukhy kamar shine Ogan Alhaji subordinate, da wuya ya fadi abu Alhaji ya tsallake, don yayi amanna ba zai cuce shi ba, in Mukhy yayi magana akan abu, Alhaji baya iya tsallakewa saboda son da yake masa da yardarm da ya yi masa.
Sanda ya iso gida Alhaji na tare da baki. Ya yi sallama ya shiga falon, Alhaji ya bashi iznin zama, Mukhtar ya gaida hamshakin mutumin dake tare da Alhaji, cikin ladabi y ace da Alhajin yace zan jira a karamin falo kafin ku gama Allhaji no Mukhtar, zo zauna, gara a yi shawarar nan tare da kai, you are part of me, samu wuri ka zauna.
Mukhtar ya zauna bisa kilishi can gefen kafar Alhaji. Alhaji da bakon sa suna kan kujera, Alhaji yace Mukhy, wannan da kake gani shine aminina Alhaji Sadisu Talle, shugaban sabuwar jamiyyar data take tamu yanzu a farin jini wato PRC (Public Relation Congress) da ake wa lakabi da SAWUN GIWA. (ya take na Rakumi). Mun yi shawara da shi zan bar AC in koma PRC don AC bazasu yarda su bani takara ba. Sun riga sun tsayar cewa wannan karon yaro matashi mai jini a jika zasu baiwa takara.
Suna cikin wannan maganar kafin Mukhtar ya furta komai Amani ta sauko daga upstairs da zummar wucewa kitchen (madafi), yunwa take ji, ga mai aikin ta Rakiya ta je kasuwa, sai idanun Alhaji Sadi suka sauka akan kyakkyawa Amani.
Babu wanda ta gaisar a cikin su ta wuce zuwa kofar da zata kaita kicin, shi kan sa Alhajin yau sai da yaji kunyar wannan rashin tarbiyya ta Amani. Sabida matsayin Alhaji Sadi a wurin sa a ce yar sa ta wuce bata gaida shi ba, shi dama Mukhy baya layin ta. Data damo abinda zata sha wato quaker oat da madarar ruwa ta peak tazo zata wuce ta koma sama batare da tace musu uffan ba. Alhaji Usman ya yi jan wuya yace.
Shin Tafisu baki ga Alhaji Sadi Talle bane zaki wuce baki gaida shi ba? Ta zumburi baki, kafin ta ce da Alhaji Sadi din ina yini? Ba tare da ta juyo ko ta durkusa ba, ko jira ya amsa bata yi ba tayi wucewar ta sama.
Alhaji Sadi ya shiga yage baki duk sai ya dabarbarce ya rasa nutsuwar sa, sai mutsu-mutsu da baki yake yi ya kuma rasa abin cewa tun saukowar Amani falon ta tafi da imanin sa, yana tambayar kan sa ina Alhaji Usman ya samo wannan kyakkyawar diya haka? Babu kama ko ta farce shi da ita, ko adopting din ta yayi? Ya rasa yadda zai yi ya tambaya sabida Mukhy da ke zaune ya tsare shi da fusatattun idanun sa don ya gane canzawar sa da rudewar sa tun saukowar Amani. Shi Mukhtar takaici da haushin yadda dattijon ya kwalalo ido da baki yana bin Amani da wani mayataccen kallo har da hadiyar miyau yasa ya mike. Alhaji yace ya zaka tafi Mukhy bamu gama shawara ba? Yace Alhaji ban yi sallah ba ina zuwa. Nan kuwa ko zancen takarar Alhaji baya son ji, balle ya bar jamiyyar sa ta amana wato AC da ya dade a cikin ta ana damawa da shi. Kai shi bai ma yarda Alhaji Sadisu zai sa a bashi takara a PRC ba duk da matsayin sa na shugaban jamiyya, don ya san bashi da farin jini yafi yarda da cewa kudin sa zai ci ya wofintar da shi. Duk da cewa ba yau suke tare ba duk da banbancin jamiyya dake tsakanin su. Abota ce tsakanin su tun ta kuruciya.
Ai Alhaji Sadi kamar jira yake Mukhtar ya bar wurin ya muskuta cikin kujerar sa bakin sa nata motsi yace shin Hon. Usman wannan kyakkyawar diya taka ce ko yar riko ce? Hon yayi dariya yace Amani ce fa, Amani Faskari, ita kenan yar daya jallin jal dana mallaka duniya da lahira.
Sai a lokacin Alhaji Sadi ya hau tuna komai na Alhaji Usman yana bearing wannan sunan ne wato Amani Faskari, bai taba sanin sunan yar sa ne Amani din ba, don bai taba jin irin wannan sunan ba.
Alhaji Sadisu ya shafa gemun sa

1 Comments On AMANI
avatar
nafisa-adamu

8 months ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment