Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da shi).
Duk yadda yanayin halittar sa yake zan iya going da shi a haka, haka kema nake so ki fara, saboda babu mai iya yi min hidimar da yake yi min da jiki da kwakwalwa da lafiyar sa da zuciyar sa gabadaya hidimtawa dukiyata yake, haka Allah ya yi shi da rashin walwala, ba ke kadai yake yi mawa ba Tafisu. Kowa ma! Ki je office din mu ki gani, zan iya rantse miki ba wanda ya taba ganin dariyar sa.
Kuma banda abin ki Tafisu, ina ruwan ki da faraar sa ko rashin ta? Amfanin da yake yi min, da rikon amanar sa a kan dukiya ta zaki duba, kafin a samu mai amanar sa da gudun duniyar sa da rashin zalama akan KUDI, zaa jima Amani.
Na sha gwada Mukhtar ta hanyoyi masu tarin yawa da tawa hikimar da Allah ya bani ta testing mutane, amma ban taba kama shi da wani hali na son cuta min, ko yi min almundahana, ko munafurci ba. Hasalima amanar sa ce ta hada ni da shi ta hada wannan bond din mai karfi tsakani na da shi. Wanda ya wucde na ubangida da yaron sa nake masa kallon dan ciki na.
A baya in kin tuna maaikata nawa nayi kafun shi, cikin su babu wanda bai cuce ni ba in one way or the other.
Ban taba samun matashi nagartacce kamar sa ba, kuma kafin a samu yaro nagari irin wannan a zamanin nan abu ne mai wuya Tafisu. Inada dalilai na a kan son yaron nan, da bazaki fahimta ba.
Ai ba komai yasa kika ga na jure masa yana bata miki rai da halayen sa ba, sai don in muka sallame shi kamar yadda kike so ba zamu taba maida asarar rashin sa ba, akwai maaikatan da kai kake amfana da su, ba su suke amfana da kai ba, ko me zaka biya sub aka iya biyan su. Ki saka Moukhtar Diffa a cikin jerin irin su.
Saidai in ke zaki dinga yimin ayyukan da yake yi min din idan kika takura na sallame shi, which is impossible. A matsayin ki na mace ba zaki iya abinda Mukhtar yake yi min ba, irin su yawon kasashen ketare shigo da kaya da handling kamfani bakidaya, banda sauran wahalhalun da yake yi min (personally) a cikin gida, a kan dan albashin da bai taka kara ya karya ba, kuma cikin amana, girmamawa da tsantseni.
Ga ilmin kasuwancin Allah ya bashi, ga kwakwalwa kamar kwamfuta, duk wata hanya da kika sani da zata maida min kobo ya koma dari cikin shekarun nan da suka gabata ina tabbatar miki daga Mukhtar ne nake samun Theory, tun zuwan sa gare ni ban san faduwa ba sai dai riba.
Ya numfasa sannan ya dubi Amani wadda ke sauraron sa da kunne daya don kuwa hankalin ta na kan wayar hannun ta, bai damu ba don ya san tana jin sa, ya cigaba da fada mata cewa. Duk wata hanyar samun riba mai tsafta da kike gani yanzu a kamfanin nan shi ke kawo min ita.
One impressive thing about Mukhy, baya taba waiwaye da cewa ina kwarar sa da dan albashin dana ke bashi kowanne wata, amma wallahi bai taba korafi ba, dan kuwa albashin dana ke biyan sa ko kusa bai kai kimar yawan ayyukan da yake min ba, da abinda yake nemo min, in aka yi laakari da cewa, ya mallakawa dukiya ta lokutan rayuwar sa baki daya, da kuma tarin fasahar ilmin kasuwanci dake cikin kan sa. Ko iyayen sa bai taba ziyarta ba tun zuwan sa hannu na.
Kullum na yi masa maganar zuwa gida cewa yake Alhaji in na tafi wahala zaka sha, don ba lallai a bar ni in dawo ba.
Kin san akwai wasu jinsin mutane da sam-sam basu san wani abu wai shi jin dadin duniya da da shagaltuwa da kyale-kyalen ta ba, irin wadannan mutanen su sai dai su taimakawa wani ya ji dadin shi kadai, ko ya samu duniyar shi kadai ya ji dadin, ba tare da sun raina dan abinda zai basu ba, to ina tabbatar miki Moukhtar na cikin su.
Amani ta mike don zancen Mukhtar dinnan wanda ta laqabawa suna bare ka fi dan gida ya fara isar ta, ya gundure ta. Ta kuma san in ba ta bar wajen ba Daddy ba gajiya zai yi da bata labarin kirkin Mukhtar ba. Daddy ba zai sa comma ba bazai saka full stop ba kuma bazai gaji ba. Sai idan baka yi zancen Muktar Diffa a gaban Hon. Usman Faskari ba. Yanzun nan zaka soma jin nassi-nassi, maudhuI maudhui na kabakin alheri iri-iri daga bakin Alhajin a kan sa. Ta ce,
Daddy, zancen ka ya shiga ta hagu, ya fita ta dama, ko me zaka ce a kan wannan yaron ni kam bai yi min ba, na tsani mutum mai iko, mai fadin rai da jiji da kai, alhalin shi din ba kowan kowa ba.
Ta soma taka stairs don komawa dakin ta kada Daddy ya cigaba da gaya mata abinda ba shiga kan ta yake yi ba.
Alhaji Usman ya yi murmushi, ko yaushe Amani zata fahimci banbancin human personality? kowa yadda Allah ya halicce shi ta fuskar personality, gashi har digiri ta yi a kan International Relation amma har yau ta kasa gane personality na halittar dan adam baya taba zuwa daya, wanda bai da alaqa da facial expression nasu, yace zo nan Tafisu, ya zaki tafi baki duba takardun Boutique din ba? Amani ta ce ba tare da ta tsaya ba Daddy in komai yayi maka, nima ya yi min, zan dauki maaikata da zasu kula da shagon mutum uku cikin yayan dan uwan ka na Faskari, da wanda ka ce tare aka shayar damu Kamilu yake ko Kamalu? Ka bar su a kauye suna noma da kiwo cikin wahala ka kama bare ka rike da daraja.
Ni bani da lokacin zuwa wani boutique, ni dai in ji alert na shigowa kullum a ka yi ciniki, in sayi abubuwan da nake so shikenan.
Cikin sauri Alhaji ya katse ta.
Babu wasu yayan dangi da zaki dauka aiki a shagon nan kin ji na gaya miki, su zo su yi min rubdugu a kan dukiya ta da basu taya ni tarawa ba, in da na biye musu da hidimdumun su, da basa karewa, da yau ban tara abinda na tara miki ba.
Ki dauki inyamurai da suka karanci kasuwaci suka kware da kula da shago su kula miki da shagon karkashin kulawar Mukhtar ba gayyar yan kauye ba, ko ki bar shi ya kawo maaikatan da suka dace da kan sa, don na san ba zai kawo na banza ba, ko wadanda basu gogu da harkar ba, ko marasa amana da zasu yi miki almundahana.
Haushi da takaici ya kara kama Amani, na yadda komai na mahaifin ta sai ya dangana shi da wannan Mukhtar din yake samun aminci a zuciyar sa, wannan wane irin abu ne? Anya haka farin baabzinen nan ya bar mata Uban ta? Shi kadai ne mai amana a duniya a wurin Daddy, kamar wani dan sa na cikin sa, ga samari nan fal jinin sa yayan wan sa baya taimaka musu da komai, suna kauye suna gararramba, wau sun yi karatu babu aikin yi, kai bata taba jin tana kishin wani dake tare da mahaifin ta irin Mukhtar dinnan ba, wai har yafi yarda da shi a kan yayan dan uwan sa?
Wadanda lomar abinci kullum sai sun fita sun nemo a kasuwannin kauye, wasu cikin su da yawa sun yi karatu mai zurfi musamman Kamilu, amma babu aikin yi, alhalin suna da kanin Uba mai wadata da gwamnati a hannu irin sa a kasar nan, amma gashi yana fadin a nemo inyamurai wadanda ba lallai su kasance musulmai bane a basu aikin yi a karkashin sa, su yan uwan sa a bar su cikin wahala, karkashin kulawar wani bare, wanda yafi jinin sa matsayi a wurin sa da ko asalin sa bai sani ba.
Tana ganin tsayawa yi wa Daddy gyara a kan ire-iren kuskuren da yake tafkawa bata lokaci ne don ba dauka zai yi ba, ba kuma denawa zai yi ba tunda rowa, mammako, rashin yarda da wani ya amfana da shi, da rashin son nasa ya rabe shi halin sa ne zaunanne da ta dade da fahimta tunda ta soma hankali.
Ita kuma duk da halin ta na raina ajawalin kowa saboda iko da mukamin data rayu cikin sa, da ganin kowa bai isa ba, Allah ya yi ta mutum ce mai yawan kyauta, da matukar son yan uwan mahaifin ta na kauye duk da talaucin su, tunda bata san na mahaifiyar ta ba. Wani abu mai kyau da zaa iya cirewa a halayen Amani shi ne abin hannun ta baya rufe mata ido sam, ke dai bar ta da facaka da kudi wajen kwalliya mai tsada da gasar hawa motar yayi.
Ai kawai Daddy ka ce shi ka budewa boutique din ba ni ba, tunda shine mai ruwa da tsaki wajen gudanarwar sa gabadaya, bayan shi ya je Mexico ya shigo da komai, sai kawai a canzawa boutique din suna zuwa Mukhtar Collection.
Amani ta fada cikin bacin rai ko shagube zaa ce? Kamar ba da mahaifin ta take magana ba. Tana mai tattaka matattakala don komawa dakin ta.
Murmushi Alhajin ya yi, maimakon ran sa ya baci ya kwabeta a kan rashin kunyar da ta yi masa, amma sai ya buge da rubuta mata text message din lallashi da wayar hannun sa.
Zuwa shekaru kadan a gaba, idan Allah ya raya mu, Tafisu zaki zo ki gode min, for making MUKHTAR DIFFA your Business Mentor, ranar da kika ga Mukhtar ya maida dan Boutique din nan naki ya rubanya zuwa PLAZA guda.
Domin Allah SWA ya huwwace da ya halicce shi yayi masa hikimar maida taro ya koma sisi. Trust him my daughter, work with him for a while, give him a try as your business mentor!.
**** **** ****
Sai da Amani ta zo kwanciya ta ga wannan sakon na Daddy, zumburo baki tayi tana tunanin mutumin nan ba haka ya bar mahaifin ta ba. Yardar ta isa. Kaunar ta yi yawa. Ko shi ya haife shi sai haka. Iya shaidar arziki da zai iya masa kenan.
Daddyn ta da duk wanda ta nuna bata raayi nan take zai yanke alaqa da shi ko waye kuwa, ko da zai kasance jinin sa ne, amma banda MUKHTAR DIFFA. Farin baabzinen data taso ta gani tare da mahaifin ta, yana rayuwa karkashin sa matsayin mataimakin sa, kuma yana tare da shi kullum a gida ko ofis. Dan asalin garin Diffa, ta kasar Nijar, wanda ko asalin sa basu sani ba har shi Daddyn kuwa, banda sunan garin sa da yake amfani da shi a gaban sunan sa DIFFA.
Daddy dai ya dauke shi aiki ne da farko a dalilin haduwar jini kawai, ta sanadin wani halin amanar sa da ya bayyana gare shi, rashin zalama da rashin kwadayin abun duniya, in kana da wadannan halayen, tabbas zaka zauna lafiya da Hon. Usman Faskari tunda shi bay a so wani ya more shi ko yayi arziki da shi, sannan ga kyawawan kwalayen ilmi (educational qualifications) din sa masu nagarta, domin Mukhtar Diffa, ya fitar da kwalayen boko biyu masu darajar farko (B. Sc & M. Sc in Business Administration) daga jamiar Paris wato (Paris Saclay University).
***** ***** ****
FARKON HADUWAR HON. USMAN DA MUKHTAR DIFFA
Asalin haduwar su da Alh. Usman Faskari a wata tafiya da ya yi birnin Paris ne, lokacin da ya je shigo da wasu kayan assasa kamfanin sa na farko wasu shekaru kusan goma a baya.
Cikin tsautsayi Alhajin ya yarda wallet din sa a cikin jirgin kasa, wanda ke dauke da dukkan katunan sa na banki daban-daban (credit cards), fasfo, ID cards, da duk wasu muhimman abubuwa da ake sakawa a cikin wallet. Bayan ya sauka daga jirgin kasan, ya shiga motar da zata maida shi masaukin sa ne ya lura babu wallet din sa a tare da shi, wadda ba katunan bankin sa kadai ta kunsa ba, akwai kudade (Euros) masu yawan gaske a ciki.
Alhaji da kudi, ko sadakar dubu guda baya iya yi in ba ta hanyar siyasa ba. Yayi salati a gigice yana kara laluba aljihun sa yana gayawa direban da dauko shi su koma, ya yar da abubuwa masu muhimmanci su koma tashar jirgin kasa.
Komawar da bata haifar da komai ba sai bata lokaci, domin train din tuni ya dade da barin Paris, ya nausa wata jihar dake gaba da Paris wai ita Bourdeaux. Ya dai bar report a ofishin jirgin kasan da wajen yan sanda.
Hon. Ya shiga damuwa ba yar kadan ba a daren, domin a cikin wallet dinnan kusan duka sirrin rayuwar sa ne gabadaya. Ga tsabar kudaden da ke ciki wadanda ya fitar dasu daga banki ne da zummar zai yi amfani dasu wajen accommodation na tsayin zaman sa a kasar da cuku-cukun clearance na kayan sa har zuwa komawar sa gida.
Damuwar sa tana karuwa in ya tuna identity cards din sa daban-daban na siyasa da na kasuwanci duk a cikin wallet din sa.
Alhaji kamar ya zare. Amma ko minti goma bai yi da shiga masaukin sa ba ya samu kira a wayar sa, a lokacin yana kokarin revoking katunan sa na banki don kada a samu damar yashe shi. Duk da iya abinda ya mallaka ba wai a bankuna suka kare ba, yana da hannayen jari da kadarori masu yawa da kamfanin sa na FASKARI INVESTMENT LTD.
Yana dagawa ya ji an yi masa sallama da hausar da bata fita yadda ya kamata, ko dai Francaise ya rinjayeta ko harshen Espanol, ko kuma abzinanci. Cikin ukun dai. Duk da haka a kan gane hausar idan aka saurara, kasancewar cikin nutsuwa mai kiran yake yin ta.
Ina Magana da mai wannan layin ne? In sha Allahu kana tare da mai wannan layin Engnr. Othman Fass. Ya kasa furta sauran da accent din sa. Amma Alhajin ya gane yana son cewa Faskari ne.
Sai ya karasa masa da cewa Eh nine Engnr. Usman Faskari.
Alhmdulillah, ina zan sameka in baka wallet din ka yanzu? Na tsince ta a jirgin kasan da ya taho daga Bordeaux zuwa Paris. Na samu wannan lambar a jikin daya daga cikin identity cards din ka.
Alhaji a zaune yake amma bai san lokacin da ya mike tsaye ba yana hamdala, yana hailala, ya gaya masa sunan Hotel din da yake, yace ya kira shi in ya zo reception.
Cikin daren baa kwana ba saurayin ya zo hotel din, suka hadu da Alhajin. Ya dauko wallet din sa ya bashi. Ya tsaya har Alhajin ya bude ya duba sosai ya kuma kirga kudin sa ya ga suna nan cif, a jere yadda ya jera su, ko kwarzane basu yi ba, ya tabbatar ba abinda aka cire.
Babban abun mamakin Alhajin, kudin sa na nan yadda ya bar su ko guda daya baa cire ba.
Har yaron ya juya ya tafi, Alhaji Usman ya kasa daure mamakin sa. Sai ya bi bayan sa. Ganin cewa dan Afrika ne ga hausa kadan ya iya, duk da dai alamu sun nuna ba bahaushe bane Baabzine ko dai dan kasar Nijar ne, wato irin matasan nan na Nijar wadanda ke tahowa karatun boko kasar goyon su wato Faransa, daga Jamhuriyyar Nijar, kasancewar kasar Faransa ce ta goya kasar Nijar.
Amanar yaron, exceptional personality, da kuma bravity din sa kai har ma da character da attitude din sa sun yi matukar impressing din sa.
Alhaji Usman ya bi bayan sa da sauri yana fadin;
Ya ka Da na, dakata don Allah, yaya sunan ka?
Cikin halin sauri-sauri don kada ya rasa jirgin kasan komawainda ya fito, da koin kula irin nasa, kuma ba tare da ya juyo ba, cikin rashin sakin fuska da rashin annuri ya ce da Alhaji Usman,
suna na Mukhtar.
Daure ka tsaya ka ji Da na Mukhtar in maka godiya don Allah.
Amma bai tsaya din ba sai tafiya yake, Alhajin kuma bai fasa bin bayan sa ba, yana rokon sa Allah Annabi ya tsaya ya bashi tukuici.
Ya dan tsaya har Alhajin ya cimmasa, juyin duniya Hon. Usman yayi a kan ya karbi kudin dake cikin wallet din bakidaya don farin cikin taimakon da yayi masa, amma kyakkyawan matashin baabzinen ya ki, duk kuwa da cewa a lokacin neman kudin jirgin da zai koma Hong-Kong din China yake yi, saboda ya nemi wani aikin a can, kasancewar interview din da ya yi ta neman aiki da wani kamfanin turaruka a nan Paris din bayan kammala karatun sa, bai yi nasara ba.
To na ji bazaka karba ba, na kuma gode da karamcin ka, na kuma yabawa nagartar ka, samun irin ka a cikin matasa is a blessing. Ka cigaba da wannan halin na taimako da amana zai kai ka har inda baka taba zato ba.
Na sha gwada samari kamar ka, ban samu wanda ya san amana ba. Ni kuma mutum ne mai son mutane masu amana. Don ta yi karanci a wannan zamanin.
Still fuska ba walwala ya ce na gode.
Sannan ya juya da sassarfa ya bar reception din. Tafiyar sa kadai abin a bi da kallo ne, saboda taku yake da sassarfa, amma kamar na kasaita.
Yaron ya tsaya masa a rai har wayewar gari. Don haka washegari ya kira shi da layin da ya kira shi jiya, suka gaisa.
Alhaji Othman ne ko?
Ya fada da kakkaurar muryar sa bayan sun gaisa. Ni ne Da na Mukhtar, ya ka je gida? Alhamdulillah ya bashi amsa. In ba damuwa ina so in zo in gan ka kafin na wuce gida Nijeriya gobe. Yace babu mishkilah, Allah ya kaimu, amma ka bari ni zan zo in same ka kasancewar daga Clermont-Ferrand City zan taho, bana so ka sha wahala har nan Baba. Murmushi Alhajin yayi yace na gode Da na sai ka zo, don Allah ina jiran ka.
Lokacin da yayi masa waya yace ya taso a train daga Clermont Ferrand, Alhajin yasa aka shirya abinci na alfarma a dakin sa na hotel, dama kuma yayi sayayya ta sutturu masu tsada, agogon maza na (Swatch) da takalma da turaruka ga Mukhtar din, da niyyar ya je ya kai masa har gida a matsayin godiya, tunda ya ki karbar makudan kudin da ya barma shin.
Wannan ya nuna ba karamar alfarma da haduwar jini Mukhtar ya samu a gun Hon. Usman ba. Kasancewar shi mutum ne mai tsananin kankamo, bi maana, ba kowa ke cin arzikin sa ba bayan tilon yar sa AMANI sai wanda rabon sa ya rantse, mutum ne mai rowa kwarai. Tsakanin sa da duk wani maaikacin sa albashi kadai, babu ihsani. Amma shi wannan yaron ya nuna masa akwai sauran masu amana da rashin kwadayi a duniya, sabanin daukar da yake yiwa kowa, cewa mutanen yanzu duk kwadayayyu ne masu neman gasashshen tsuntsu daga sama, shi yasa yake so ko yaya ya gode masa.
Don yana yawan gaya wa Amani yanzu duk mutanen duniya makwadaita ne, shi yasa suke cewa ya fiya rowa, ya dauki kowa a irin dabiar da yake kai, wato son ci daga haram ko halak kamar sa.
Sannan a ganin sa mutaen yanzu basa ganin kudi su kyale balle irin wadannan Euros dake dankare cikin wallet din sa.
Ko a satin da wuce ya kori maaikata biyar daga kamfanin sa, da ya kama su da yi masa sama da fadi da wasu yan kalilan kudade. Bayan kuma kudaden ma bata suka yi cikin lissafi amma a hannun su.
Ya iso kofar dakin ya danna kararrawa, Alhajin ya bude masa yana lale marhabin da shi, sanye yake da farar shirt an rubuta Fred Perry da bakin wandon CK Jeans. Dogon matashi, kakkarfa, farin baabzinen usli, mai wani irin sassanyan kyau, hancin sa kamar an sa ruler an ja masa shi an saka masa shi a tsakanin idanun sa, komai na halittar sa ya zauna a inda Allah Subhana ya ajiye shi, kamar shi ya zaba wa kan sa zati da kamala, ga wata lallausar suma da ta taru a saman goshin sa ta abzinawan usli, har ta dan kalmaso a kan goshin sa, ta maida shi tamkar Baindiyen nan mai farin jini (Shahrukh Khan).
Alhaji ya bashi kujera ya zauna suka gaisa sannan ya nade hannun riga yace ya sauko kasa su ci abinci tare. Ko kadan rashin walwalar yaron da shan kamshin sa baya damun sa.
Kamar ba zai ci ba, amma ganin Alhajin da an sa yayi serving din su a plate guda, sai ya kasa tankwabe kulawar wannan dattijon, wanda ke ta haba-haba da shi cike da kauna, sai ya sauko kasa ya kalmashe kafafun sa, suka fara cin abincin a plate daya.
Suna ci, Alhaji Usman na hilatar shi da hira cikin dabara irin ta manya, har yaji abinda yake son ji, wato inda ya fito da kuma abinda ya kawo shi birnin Paris.
Nan yake gaya masa cewa daga wani yanki na jamhuriyyar Niger ya zo nan, ana kiran yankin nasu Diffa Region, yau watan sa uku da kammala karatun digirin sa na biyu a nan kasar, daga jamiar Paris Saclay University. Ya gayawa Alhajin tun baya kammala masters din sa ya nemi ayyuka na wucin gadi har uku bai samu ba, kasancewar shi ba dan kasa ba, don haka zai koma Hong-Kong yanzu ya nema a can. An ce suna bada ayyuka sosai ga yan Afrika, shi neman na kan sa ya fito, ba yanzu zai koma gida ba.
Kasancewar a lokacin kasar Nijar na fama da matsalar durkushewar tattalin arziki babu ayyukan yi ga matasa masu ilmi kamar sa a Nijar.
Alhaji Usman ya tambaye shi ko me ya karanta da level din karatun sa duk ya gaya masa, cewa daga digirin sa har master first class ne. Alhaji Usman became highly impressed da jin hakan, sai kawai Alhajin ya ce, ina ma za ka iya zaman kasar Najeriya, da mun tafi tare na baka ragamar kamfani na, in ya so sai ka dinga zuwa gida kana ganin iyayen ka lokaci-lokaci, saboda ni din bani

1 Comments On AMANI
avatar
nafisa-adamu

8 months ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment