Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

8/9/20, 10:24 AM - Messages to this group are now secured with end-to-end encryption. Tap for more info.
8/9/20, 10:26 AM - Maman Baby: 🌹MARAICIN NAWAF🌹

STORY AND WRITING
BY
MAMAN BABY💝


*🌎MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM
________________________

*SHAFI NA DAYA DA NA BIYAR* ( 1️⃣↔️5️⃣)
________________________


.......📖Dan Allah yaya kirike min yarannan, nasan kobayan Raina zaki, kuladashi nidake bamuda kowa sai junanmu, nima gashi zanbarki, Dan Allah kirikemin *NAWAF* marayane ba uwa ba uba Dan Allah kirikeshi kamar yadda zaki rike naki yaran gawanan kibashi idan ya girma tamikomata wata yar akwati.

Sumaiyya kidena fadin haka ciwo bamutuwaba, Dan Allah kidena zakitashi kinji. Hmm yaya kemakinsan ciwan dakejikina banatashi bane, kide kirekiman yarona amana kicigaba dayimin addua.

Yaran dege gabansu yakama kuka yanacewa"mama Dan Allah kitashi karkitafi kibarni" wadda naji ankira da sumaiyya tajawoshi tace "kayuhakuri yarona kaddara tariga fata koda kaji abunda babanka yayimun Dan Allah karkarikeshi,kacigaba dayimamu addua ga yayata nan kariketa tamkar ni"tashafa kanshi tace Allah yayimaka Albarka in sha Allah saikazamo Abun Alfahari Aduniya.

Yaya lami dake gefe tatabe baki Amman bata Bari sunganiba.




Cincikin,dare sumaiyya raiyayi halinsa tana rungume da *NAWAF* yana bacci. Sai da safe yaya lami tazo Dan tadibata tatada *NAWAF* yatashi yamutsutsuke, ido yace mamana yaya lami tace "tashi katafi kaisallah" yatashi yafita itakuma tazo tanama sumaiyya manana Amman mai sumaiyya bako motsi tajijigata, Amman ina yaya lami ta fashe da kuka tanacewa"shikenan sumaiyya yanzu banida wani Dan uwa kimakintafi Allah yajikanki sumaiyya" *NAWAF* yasakai zefita kenan yajiyo Inna lami na sallallami, Tana kuka ai da gudu yadawo yace "menene inna"? Tace"sai hakuri mamanka, ta'amsa kiran rabbi"tafada Tana kara rushewa da kuka.

*NAWAF* dukda yana yaro Amman, yaji mutuwar Amman beyi kukaba yayi tawakkali, saboda, yaji malaminsu, yace ba'ama mamaci kuka.


haka akakai, sumaiyya gidan ta na gaskiya sai de muce Allah yasa mucika da kyau da imani.

_Bayan sati biyu da rasuwar sumaiya_

*Nawaf* yafara fuskantar matsi da takura, agurin Inna lami, da yaranta. Komi nagidan nakarfi, shikeyi Kai harma da aikin dayakamata, ace mace kayi, Amman komi anmedashi, kan *Nawaf*

Yanzu ma Inna lami ce keson yaje ya dokomata, jarkokin ruwa a mono,

Inna tace "kayi sauri kadokomin wlh katsaya, shiririta, hmmm kasan sauran".

*NAWAF* yace "to Inna baranaje Amman bana,iyadauka nikade, kimuje mujahid yatayani"? Inna tace "Eh,lalle gatsaranka, ko dalla kawuce, kadokomin kafin,nabatama,rai"

*NAWAF* yace "kiyi hakuri Inna banfadaba dan nafatamiki rai Dan Allah kiyihakuri,mamana tace namaki biyayya"


inna lami tace"naji jeka" *NAWAF* yatashi yafita yaname zubarda kwalla yanacewa azuciyarshi, mamana meyasa, kikatafi,kikabarni gurin Inna lami yaida fadin maganar abayyane, yanakara fashewa, Da kuka.

Bayan *NAWAF* yadawo daga daukar jarkokin, Inna lami yace "Inna Dan Allah kibani kosauran tuwan,jiya naci Allah yunwa nikeji" inna lami tace "innalilahi sokake acebana baka abinci, yo Duk wandayaji, kanacewa haka aisai,acebanabaka,abunci to wlh bazakadoramin mutanen unguwa suce banrike, Amanaba wlh kakiyayan"taja tsaki tabar *NAWAF* tsaye agun.

tanacewa"wlh ka isheni sumaiyya tatafi, tabarmin, jidali ni almajiranci zankaika, kowama yahuta.




Inna lami bayan tagama surutanta,juyowan dazatayi sukayi ido biyu da mijinta mijin Inna lami yace"lami kiji tsoran Allah wlh wanan yaran amanane agareki harma dani mijinki karfa kimanta Dan yar uwarkine, uwa daya uba daya nasan dake kikabarma sumaiyya amana wlh zatakula, dasu tamkar yaranta Amman kekinkasa duka, dauka yaushe sumaiyya tarasu Amman harkinfara muzgunama Dan da tabarmaki harkinacewa zakikaishi, almajiranci wlh lami kiji tsoran Allah" Inna lami taikasake tanajinshi tace "haba malam wasafa nike yaza,ainakaishi almajiranci wasanike"tafada tanawani murmushin yake. Mijin inna lami yace"komade dawasa kike koma da gasake baruwana inde inaraye bazaki kaishi ko,inaba zecigaba da zuwa makaranta kamar yadda yaranki sukezuwa"yafada yana shigewa daki. Inna lami tace kajimin malam dawani zance ko,ina ruwanshi da dan yar uwata mtsswww taja tsaki tace wlh sai de kayi komizakayi Amman saiyaje koda gadine gidan masukudi domin dashi yadace.

*NAWAF* netsaye shida wani yaro baze wuci sa,anshiba dan makoftansu ne mesuna umar umar bejin magana tunyana yaranshi yafara daukedauke,tun,agidansu yana daukar na mamanshi maman batawani kula haryakai yafara daukar nawaje.
*NAWAF* yana kuka yace"dan Allah abokina me,akayimaka dukda nasan kana shan wahala agun mamansu mujahid kadena kuka ni zandinga baka kudu kanasayan abinci inbatabakaba,zanbaka kaji *NAWAF* yace"nagode Abokina.

Amman kasani abunda kakeyi bashi da kyau kuma bazanci abunda banawaba.

Umar yace "in sha Allah zandena tunda babu kyau".

*Nawaf* yace "yauwa abokina" sukayi murmushi suduka.



Inna lami ce sai sababi takema, *Nawaf* harda duka kawai dan yace yanajin yinwa tabashi abinci, wai zejamata zagi a unguwa.



*Nawaf* Yabiyota, dagudu yana kuka yace"inna Dan Allah kiyi hakuri mamana tace nabiki nayinaki biyayya Dan Allah karki fishi dani" Inna lami tajuyo Afusace tace"kaidan Allah naji da anyi magana kace mamanka tace kabini yo kabuni sai kace wata zariya, mitssw Dan Allah karabu Dani naji nahakura tashi katafi.


Inna lami ce ita da wata kawarta Asabe, suna tattaunawa kan zatakai shi almajiran ci.

Asabe dama irin matannanne, masu safaran yara ta kaisu aikatau to shine Inna lami takes tabata nawaf dan tafiya dashi almajiranci, wai tagaji da rukon gwara yatafi yanemo ilimi acewarta.

Asabe tace "to yanzu wane gari kikeso akaishi"?

Inna lami tace"keni ko inama kaishi banida damuwa akai"

Asabe tace "to shike nan ba matsala zandawo bayan mako guda, dan lokacin zantafi"

Inna lami tace"to Allah ya kaimu sai najiki.


*BAYAN SATI DAYA*

Asabe tadawo Dan tafiya da *NAWAF* bayan sungama gaisawa da Inna lami Inna lami tace"to asabe yanzu in malam yatanbeyeni, ina yaron nan, mezance"?


Asabe tace"idan yadawo kicemasa kin aikeshi yasiyo itace za,ayi sanwa idan bedawoba sai kekuma kifara kukan karya yadda kowa ze tausaya maki"


hakade Asabe tayita kisama Inna lami yadda zatace yadda Kuwa zeji tausayinta.


Inna lami tace bara nayi sauri nakirawo shi kutafi karma wani yazo yaganku, tatafi dakin *NAWAF* Dan takirashi.


*NAWAF* kuwa yana labe yanajin duk abinda sukecewa.......🖊️

comment And
Share please🙏🏼

BY MAMAN BABY💝
8/9/20, 10:26 AM - Maman Baby: 🌹MARAICIN NAWAF🌹

STORY AND WRITING
BY
MAMAN BABY💝


*🌎MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

_______________________________
*SHAFI NA BIYAR DA NA GOMA*(5️⃣↔️🔟)
_______________________________


.......📖Inna lami tashigo dakin tace"kai nawaf tashi kahada kayanka zaku unguwa kaida Asabe,"

Nawaf yana kuka yace "Inna ina zamu"?

Inna lami tace "gidan uwarka zaku" tafada afusace.

Nawaf yace"yihakuri bara na shirya"

Yahada kayanshi komi da komi har wanan akwatin da maman shi Tabada, abashi saboda tunbayan rasuwanta, Inna lami tabashi.

Yafito yana share hawaye Inna lami dake tsaye itada asabe tace"wai nikam kukan mekakeyi"? Daga zakarakata, unguwa haba bansan shashanci,

Asabe tace "haba rabudashi yarone"

Anande, sukayi sallama dazummar zasudunga waya Dan taji ya nawaf din yake.

Shide bawan Allah nawaf lamarin innar yanabashi mamaki wai yanzu uwa daya uba daya da mamanshi, suke Amman tayime irin wanan Abu yace azuciyarshi Anya kuwa bakomi Allah yana tare dani.


Asabe taje tataho dayaran, Da zatakai gidan aiki sukusan goma suka dunguma sai tasha yan mata goma sai bawan Allah nawaf.


Asabe dasuka je Tasha basu zarce ko'inaba sai gurin motar Kano.

Sukashiga basu,wani dadeba mota tacika sai Kano tadabo.

Suna sauka nawaf kuwa yasha baccinshi, sai da Asabe tatashe, shi.

Bayan sunsauka takai kowace yarinya gidan aikin ta.

Sai nawaf kade yarage tamarasa yazatayi dashi itade ba wata makaran ta tasaniba bare takai shi nande suka ci abinci tasiya ta kuma siyamashi.

Bayan sungama, cikinta ya dauka sai tafara tunanin yazatayi da nawaf shuko yanata Kalle, Kalle.

Aikuwa sai dubara tafadomata nawaf yana ta Kalle kalle asabe tasabe, tagudu batare da nawaf ya ankaraba.

Nawaf yajuyo yacewa"aunty Asabe munkusa nafarajin bacci" Amman me ba Aunty asabe balabarinta.

Yakama waige waige yana dibata Amman begantaba. Aikuwa yafara kuka yanacewa"aunty asabe Dan Allah kina ina"?

Wani dake kusa da inda yake yace "Kai yaro mamanka ai tundazu Tasha wanan kwanar" yananuna masa wata kwana dake kusa da indda duke cin avincin,

Nawaf cikin kuka yace "to miyasa bakayimin maganaba dakaga zatatafi"?

Mutumin yakama dariya yace"to yaro niya zannasan, guduwa zatai tasako ruwa zata siyo maku"

Nawaf kuwa sai yakara fashewa da kuka wato dama shiryawa, sukayi insunzo a yaddashi, bisa hanya yafada cikin kuka.

Inna lami kinci amanar da mamana tabaki bazan yafeba Allah kasakamin yafada cikin kuka me suma zuciyar me sauraro.

```Waiwaye adon tafiya```

Alhaji mani da Alhaji saminu wa da kane ne, suna zaune acikin garin sokoto cukin tsakiyar birnin na sokoto.

Suntaso suna son junansu tunsuna yara dabi'ar da iyayansu sukadora, su akai kanan kafin su barduniya suso junansu karwani yashiga shakaninsu surike zuminci kobayan ransu suzama tsintsiya madaurinki daya.

Hakakuwa akayi sunrike wanan huduba ta iyayansu.

Alhaji mani yana aikin gomnati ne yana da mata daya wato maryam mami yaransu biyar kalisat itace babba sai umar sai mujahid sai sumaiyya sai auta sadeeq. Yaran suntaso, cikin kaunar Juna da ladabi da biyayya da girmama nagaba gaskiya sunsamu tarbiya sosai suna makaran tar Boko da isilama.

Alhaji saminu shikuwa yana kasuwancine, yanada mata daya Fatima wato ammi sunada yara uku naseer shine babba sai Habiba sai autarsu Mariya Amman sunace mata lami suma sunada tarbiya dede gorgodo.

Lami da sumaiyya tsaran junane Amman lami ta girmi saumaiyya da kusan shekara biyu.

Aiki yamedo babansu sumaiyya Katsina inda yatattaro, iyalansa sukadawo Katsina.

Shida Dan uwanshi basuso wanan cinjin gurin aikinba Amman yazasuyi, haka sukayi hakuri shiyana Katsina shikuma, sokoto.

Shakuwar da ke tsakanin lami da sumaiyya yasa da zasu taho suka taho tare da ita.

Halayan sumaiyya da lami ya sha banban dukda shakuwar da ke tsakaninsu, hakan besa lami jin zafin sumaiyyaba domin kuwa tunda suka taso sumaiyya Allah yayita da farinjini, Duk'intazuna guri to sai tayi masoya sumaiyya farace sosai doguwa Amman ba cinba tanada jiki dede misali ga fara'a ga habahaba da jama'a hakan Yana Kawa kesonta.

Hakankuma nafatama lami rai ta kudiri niyar kowama sai ya tsani sumaiyya dan sai de sutaru surasa masoyan acewar ta.

Ana haka sai sumaiyya tahadu dawani saurayi mesuna imran suna matukar son juna itada shi tana ganin zata iya barinkowa dominshi kuwa zata iya yinkomi, Dan taga takasance matarshi,

To haka yake abangaran shi yanason sumaiyya sosai.

Lami tunda ta kyalla, ido taga Imran takamu da wani irin mahaukacin, sonshi.

Tarasa yazatayi Dan itama tace sai inda karfinta ya Kare....... 🖊️







comment and
Share please🙏🏼
8/9/20, 10:27 AM - Maman Baby: 🌹MARAICIN NAWAF🌹

STORY AND WRITING
BY
MAMAN BABY💝


*🌎MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

_________________________
*SAHFI NA GOMA DANA SHABIYAR*(🔟↔️1️⃣5️⃣)
_______________________________

```Agaskiya masoya na na wannan book nagode sosai da fatan alherin ku da Adduoinku agareni in alfahari da ku wanan pg nakune kude kucigaba da min addua da comment nagode🥰```


......📖Lami sai tadingaba, sumaiyya mugayan shawara akan Imran bana kirkibane, hakan datakeyi, sukasamu sabani tsakaninsu, Da lami taga haka sai takoma tana bata hakuri har suka shirya. Sai takoma tana yabanshi, Amman Allah kade yasan meke zuciyarta.

Ana haka daddyn su lami ya bijiro da maganar hada yaransu aure Dan kara kulluwar zumincinsu.

Inda za ahada lami da umar sai kuma sumaiyya da naseer tofa nan akeyinta

Tunda wanan magana tazo kunnansu lami sukadin ga kuka akan su basaso kosama da kasa zata hade basaso aikuwa iyayan sukace basu yadda ba dole subi zabinsu.

Dafarko sumaiyya tafara yadda tafadama imran akan suhakura, gawanda iyayanta suka zabamata yayi ta shawo kanta,da kalamai da dadin baki haryashawo kanta.

Inda lami dama tanajin zata iyayun komi Dan ganin sumaiyya bata auri imranba, saboda tasan inde sumaiyya tace ma BABA gazabinta, to ze auramata.

Ganin haka yasa lami tafara hurema sumaiyya kunne kan su gudu tinda itama batason umar.

Dafarko sumaiyya takiyadda saboda tasan illar da yaya keshiga insuja bijere ma iyayansu, toma insun gudu ina zasu.?

Tanbayar dataima lami kenan lami tace"basai muje wani garinba sai mudibi gudi meyawa, yadda ze ishemu daga baya sai mudawo nasan zasu yafemana".

Hakade taita, turata hartayadda, aikuwa kwatsam akawayi gari su lami sun gudu.

Sukarubuta wasika cewa iyayansu, suyafe masu sukam sunshiga duniya dan bazasu bari aimasu auran doleba.

Ran iyayan su yayi matukar baci sunyi fushi dasu ainun sukace suje ga duniyar nan.


Sukuwa basu zarce ko inaba sai kaduna.

Inda suka je suka kama haya dasunan su marayau, ne.

Haka sukaci gaba da rayauwa inda sumaiyya tanacikin da muwan abunda suka aikata,

Lami kiwa datashigo kd kanta yakara wayewa inda tahadu da wata tantiriya wato Asabe in da suke kawance sosai, ita kekara tunzurata gurin ganin ta lalata rayauwan sumaiyya itakuwa sumaiyya bata ganewa tayi tunanin mesontace, bazata cutar da itaba.

Ana haka sumaiyya tahadu dawani saurayi Dan gidan manya, tunbata kulashi har tafara in da soyayya me karfi takulu tsakaninsu..... 🖊️




Comment and
Share please🙏🏼
8/9/20, 10:27 AM - Maman Baby: 🌹MARAICIN NAWAF🌹

STORY AND WRITING
BY
MAMAN BABY💝


*🌎MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

___________________________________
*SHAFI NA SHABIYAR DANA ISHIRIN*( 1️⃣5️⃣↔️2️⃣0️⃣)
___________________________________

.......📖soyayya suke sosai tamamanta, dawata soyayya datayi abaya, dan bakarya salman yahadu fari ne dogo in kaganshi kamar wani balarabe ya hadu ba karya gakuma masu gidan rana.

Salman salis shine sunanshi haddan gaye baban shi me kudin gaske ne dan har gidan mai gareshi yana da kudi sosai dan 9j Anajida shi bakadan ba.

salman yahadu da sumaiyya ne watarana, taje kasuwa Dan tayo masu cefane.

Shikuma sunshi go Don yin siyayya tofa anan yaga sumaiyya yarude, sai dayaga no unda take yasundunata, a login love dinshi, yasamu kwanciyar hankali.

Lami taji haushin wanan soyayya Amman sai asabe tabata shawara tabari ayi auran, zasusan yadda, zasuyi.

Ahaka sukayi aure inda sukace sumarayune, ita da lami uwarsu daya ubansu daya Dan balefi, tawani gurin suna Kama.

Amarya sumaiyya tatare dan kareran gidanta,

In dasuke shan love kamar bagobe.

Bayan auran sumaiyya lami matayi aure inda ta auri wani malamin makaranta bahaka tasoba, dan taso ta auri mijin da yaci uwar na sumaiyya, Amman Asabe tace ta aureshi Dan yan unguwa sunfara zarginsu tunda daga sama kawai sukashigo, unguwar shine yasa harta hakura ta auri malam mudassir.


Lami basuyi wata biyu ba Allah yabata ciki Amman sumaiyya shiru ita Allah bebataba.

Lami ta haifi Dan ta nafari Akasamasa suna mujahid balefi tana hutawa agidan malam Amman gidan sumaiyya ya tsone mata ido.


Abangaran Sumaiyya kuwa.......🖊️


Comment and
Share please🙏🏼
8/9/20, 4:24 PM - Maman Baby: 🌹🌹 *MARAICIN NAWAF*🌹🌹

*By maman baby* *AUTAR MARUBUTA*😊

*Bismillahir rahamanir rahim*


🌍 *MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION* 📚 🖊️

*M. W. A*

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoya ta.🤙🏻
https://www.facebook.com/107980080946102? referrer=whatsa
___________________________

*SHAFI NA ISHIRIN DANA ISHIRIN DA BIYAR*
_________________________

......📖Bangaran sumaiyya kuwa suna zuba soyayya sosai itada mijinta ta cannza Dan harwata kiba da haske Takara, saide wata matsala da tafara kunnomasu Kai itace, dangin mijinta sunfara yimata korafin bata haihuwa, su jikoki sukeso ga habaicin wai sunfarajin radedadin basuda dangi.

Aikuwa sumaiyya tasha kuka salman natabata, baki.

Sai alokacin tafara nadamar Abunda ta aikata itada lami gashi yanzu lamin kanta tadena kulata iyaka kotazo taitabata shawar, warin banza dana wofi.

Tayanke shawaran sanar da salman asalin susu waye, saide tana tsoran abunda zebiyo baya sumaiyya tayi matukar nadamar abunda ta aikata gashi tabison zuciya tagudu daga gida ga yanzu matsalar datafara, fuskanta.

Wata rana bayan salman yadawo daga aiki bayan yayi wanka yashirya sumaiyya takomishi abunci, yagamaci ya dago yaga tazabga tagumi

yace" my sweetheart meke damunki kwana biyu sai kitatunani, Dan Allah make damunki"?

Sumaiyya tafashe da kuka tace"wlh my dear wani kuskure nayi arayauwata, bansan yazan fadamaka wanan lamarinba"

Yace"wane irin abune wanan Dan Allah karkiji komi kifadaman"

Anan sumaiyya ta kwashe tarihinsu kaf tagaya mashi.

Aikuwa juyowan, dazatai Salman ya dauketa da mari sumaiyya tadago arazane.......🖊️



Comment
Share pls
8/10/20, 9:03 AM - Maman Baby: 🌹🌹 *MARAICIN NAWAF*🌹🌹

*By maman baby AUTAR MARUBUTA* 😊

*Bismillahir rahamanir rahim*
____________________________________
*SHAFI NA ISHIRIN DA BIYAR DANA TALATIN*
____________________________________

......📖 sumaiyya tayi wani malalacin murmushi, tace"banga lefinkaba saboda Nike dalefi, Dan Allah mijina kayi hakuri Abusa karyar danayimaka".

Aikuwa sai ma Salman yakaramata, wani marin yace"nizaki yaudara kigayaman karya wlh sai kinyi nadamar aurena, dama su hajiyata sunmin maganar ina iyayanki nace ke marainiyace, Ashe....yama kasa karasa abinda zece, yacigaba da bol da sumaiyya sai datagayama, jikinta kafin dankanshi, yagaji yakyaleta.

Tasha kukanta tanamecewa, "banga lefinshiba da ace ban baro gaban iyayenaba da hakan batafaruba Dana auri Dan uwana, nazuna gaban iyayena da yan uwana da banfuskanci wanan abunba..... Awanan rana sumaiyya tayi matukar nadamar abunda tayi arayauwarta datasani, batabiyo lamiba gashi yadda rayauwa takomamata.


Ana haka kwatsam wata rana sumaiyya taga mutane sai shigowa ake da kaya ana sawa adayan bangaran ginin dake, kusa da nata...wai Ashe Salman ne yakara aure, batasaniba.


Tana tanbayar mutanan lfy.?

Wata mata mesuffar yan danbe tataso tace "yakawo wadda zata haifamishi yarane Dan yagaya, manacewa bakya haihuwa Dan haka inma bakisaniba kisani yau aka daurama mijunki aure".

Sumaiyya wani shok ne yakamata takame agurin yanzu Salman ne yakara aure bata saniba.

Hakata wuce dakinta jiki ba lakka tana mekara, nadamar abunda ta aikata.

Wanan Amarya da Salman yayi takarasa sumaiyya cikin matsi datakura in da Salman yajuya mata baya....anahaka Allah yaba sumaiyya ciki cikin kuwa me danbanzan, laulayi Abu ,kadan zatayi Salman yabata karshin tsiya kai karshema yasaki sumaiyya Saki uku saboda watarana tashiga Kitchen din amarya tana wainar fulawa, itakuma sumaiyya cikinta nabukata daga tace dan Allah tasanmata, kawai sai takwasheta da mari wai ita tsarantace aikuwa itama tarama adede lokacin Salman yashigo Aikuwa shima yadaga hannu yasharara mata Mari, babincike bakomi yasaki sumaiyya.

Yace cikin datake dashi tatafi yabarmata beda bukata amarya ta haifamishi.

Haka sumaiyya tadawo gidan lami dazama Ammanfa zaman badadi kullun hantara da habaici. Harde Allah yasa ta haifi santalelan Danta. Bayan ta haifi *NAWAF* ne bakincin lami da na tsohon mijinta Salman ga tinanin gida yasa tasamu lalura tunbayan da tahaihu batasake tashiba ahaka tareni *NAWAF* harya dan fara girma Dan yanzu *NAWAF* bazewuce Dan shekara 12 ba Ahaka sumaiyya ta amsa kiran rabbi tabar Danta Nawaf ahannun lami galami takasa rike amanar shin yanzu ya rayauwar wanan yaron zatakasance.....?

*MUNDAWO LABARI*..........🖊️




Comment
Share pls
8/10/20, 9:03 AM - Maman Baby: 🌹🌹 *MARAICIN NAWAF*🌹🌹

*By maman baby AUTAR MARUBUTA* 😊

*Bismillahir rahamanir rahim*
_____________________________________
*SHAFI NA TALATIN DANA TALATIN DA BIYAR*
_____________________________________

.....📖 *MUNDAWO LABARI* haka nawaf yarika garari Agari Nashua indazeje, sai de dayaga lokacin sallah yayi sai yatafi masallaci yayi sallah.

Dadare yayi yarasa inda zeje yakwanta, yayita kuka sai de yasamu gurin wani shago yarabe yakwanta.

Dasafe meshagon yazo zebude yaga mutum akwance, shidafarkoma tsoro yabashi sai dayaduba yaga yarone yace"ikon Allah shikuma meyakeyi Anan"?

Yamatsa kusa dashi yatadashi yace "yaro mikakeyi anan inane gidanku"?

Nawaf yace"ni marayane watamata tataho dani zatakaini Almajiranci tagudu tabarni gashi bansan, kowaba anan garin"yafada yana hawaye.

Meshago yace "to Kai bakada kowa kuma awane gari kake"?

*Nawaf* yace "Ina da Tatar mama itakadenasani, itatabadani Akawoni"

Meshago yatausaya ma nawaf yace "bakomi Allah yasaka maka zandaukeka nakaika gidana zanrikeka harmuga abunda Allah zeyi"

Nisunan jameelu meshago ina da mata daya bamutaba haihuwaba, kaga munsamu yaro ko yana murmushi"

Nawaf yace "to Abbu nagode Allah ya sakamaka da alheri Allah yabiyaka kayimun abunda yar uwar mamana takasayi mun"

Jameelu yaji dadin da nawaf yakirashi dashi yace"karkadamu ai danakowane bakasan me temakonkaba yasunanka"?

*NAWAF* cewar, Nawaf...to Allah yayi marayauwarka, albarka.

Yanzu tashi mutafi gida nayima matata bayani ko.... To Abbu cewar nawaf.


Bayan sunje gidan jameelu yazaunar da matarshi mesuna jameela😊inye jameela da jameelu......yayi mata bayanin yadda yasamu Nawaf....yace"dan Allah jameena kirikeshi mukuladashi kinga marayane"

Jameela tace "haba sweet jameel yazakaga yaro kakama kadokoshi kakawo, mancikin gida hava Dan Allah nikam gaskiya badaniba, hakakawai kakawoman alkakai, to badaniba".


Jameelu yace "Dan Allah saurara jamee inaso komi zakiyi kisa Allah aranki mude temako zamuyi marayane dana kowane bakasan, waze temakekaba Arayauwa mude muyi tsakaninmu, da Allah kingane ko"?

Bakomi mijina in sha Allah zanyi kamar yadda kace zanri keshi Amana Allah yabamu ikon rikewa cewar jameela.

Jameelu yace Masha Allah nagode matata yana mesakar mata murmushi.

Rayauwa medadi nawaf keyi agidan Abbunshi da umminshi yanajin dadin zamadasu kamar sune suka haifeshi, Dan har makaranta sukasashi Boko da islamiya kuma yana ganewa sosai Dan balefi nawaf kanshi yanaja........🖊️

*BAYAN SHEKAR SHABIYAR*


Comment
Share pls
8/11/20, 9:07 AM - Maman Baby: 🌹 *MARAICIN NAWAF*🌹

STORY AND WRITING
BY
MAMAN BABY💝

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________

MARUBUCYAR

*MIJIN TACE*
*KATANGAR NERA*
*SAI KAMIN KISHIYA*
*DA*
👇🏻
*MARAICIN NAWAF*
______________________________________
*SHAFI NA TALATIN DABIYAR

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment