Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da nake yi akanka.
Bakin cikina shi ne, zan rasa mijina uban 'yata.
Ita kuwa 'yata za ta zamo marainiya. Ka je ka yi duk
irin shirin da za ka yi don fuskantar makiyanka amma
ina tabbatar maka da cewa abinda kake tsoron kada ya
faru sai ya tabbata".
Koda gama fadin hakan sai Sabirat ta fashe da
kuka sannan ta mike tsayc zumbur ta ruga wajc da
gudu. Nan fa Sarki Huraisu ya kama tsuma kuma ya
sake fusata ainun ya yi duru-duru ya rasa ma abinda
zai yi.
Daga can sai ya fita da sauri ya nufi bangaren
masaukin Sarki Imras, yana tafiya bugzum-buguzum
kamar zai tashi sama saboda sauri.
Duk inda ya gifta sai ka ga Dakaru sun tsorata
sun rakabe suna masu sunkuyar da kansu kas don kada
fishin Sarki ya hau kansu.
Kai tsaye Sarki Huraisu ya kunna kai izuwa cikin
turakar dakin da Sarki Imras yake. Yana shiga kuwa
ya iske Sarki Imras zaune a tsakiyar dakin ya harde
kafatu ya tankwashesu kuma idanunsa a rufe suke
yana karanta wadansu dalasimai na tsafi
Koda Sarki Huraisu ya durfafoshi kai tsaye sai
kawai ya daga masa hannu ya tsaida shi. Bisa dole
Sarki Huraisu ya tsaya cak yana huci kamar bakin
kumurci, har sai da Imras ya gama laziminsa na tsafi
sannan ya bude idanunsa ya mike tsaye fuskarsa cike
da alamar tsananin damuwa ya dubi Sarki Huraisu ya
ce, "Ya kai abokina ka yi sani cewa duk abinda
matarka ta gaya maka yanzu gaskiya ne kuma zai faru
a gaske muddin bamu dauki matakin gaggawa ba.
Nima a cikin bincikena na ga cewa 'yar uwata
Husnaila za ta kasheni da hannunta kai kuma Murisu
dan Muraisu zai kasheka, wato yaro mai kahon BUSA
A MUTU".
Lokacin da Sarki Imras ya zO nana zanccnsa sai
hankalin Sarki Huraisu ya dugunzurma ainun ya rasa
abinda ke masa dadi a duniya ya dubi Imras cikin
firgici ya ce, "Ya kai abokina yanzu wanne mataki ya
kamata mu dauka domin mu kubuta daga sharrin
wadannan makiya namu?
Sarki Imras yai ajiyar Zuciya sannan ya ce, "A
cikin binciken da na yi yanzu na ga cewa su Gimbiya
Suzaila sun sadu da Jarumi Imran kuma ya amince zai
yi musu jagora izuwa dajin Kirzula domin ya kamo
Muraisu a raye azo da shi har nan Birninka amma bisa
sharadin su Gimbiya za su karbi addinin Musulunci,
amma sai bayan sun shafe kwana arba'in a wani kauye
Ya zama dole yanzu mu yi shiri ni da kai mu bi
bayan su Gimbiya ya zamana cewa muna tare da su
amma basu sani ba har su shiga dajin Kirzufa su yi
yaki da su Muraisu bayan sun sami nasarar kama
Jarumi Muraisu da 'yar uwata Husnaila sun fito daga
cikin dajin Kirzufa mu kuma sai mu shammaccsu mu
sace Muraisu da Husnaila daga wajensu mu kaisu can
wani wajen mu kashesu.
Ka ga kenan Kura da shan bugu gardi da kwashe kudk
Ma'ana ba tare da mun sha wahalar komai ba
zamu kama makiyanmu a ruwan sanyi".
AA Misau ke Magana
Lokacin da Sarki Imras yazo nan a jawabinsa sai
Sarki Huraisu ya cika da tsananin farinciki ya rungume
Sarki Imnras yana mai cewa, "Ya kai abokina hakika ka
yí tunani mai kyau kuma ka z0 mana da shawara
wacce za ta fisshemu.
Daga can kuma sai ya janyc jikinsa daga cikin na
Imras ya dubeshi cikin tsananin damuwa da sanyin jiki
ya ce, "To yanzu ta ya ya zamu iya riskar su Gimbiya
Suzaila cikin kankanin loakci tunda na san cewa yanzu
suna nesa damu?"
Koda jin wannan tambaya sai Sarki Imras ya yi
murmushi ya ce, "Kada ka damu ya kai abokina, kai
dai kawai ka je ka yi shirin wannan tafiya gobe da
sassafe zamu tafi"
Cikin murna Sarki Huraisu ya juya da sauri ya
fice daga cikin turakar domin yaje ya fara shirin
wannan gagarumar tafiya.
Kashe gari kuwa tun da duku-dukun safiya Sarki
Huraisu ya gama kimtsawa ya yi gagarumar shigar
yaki.
Dama tun a daren jiya ya tara fadawansa ya sanar
da su cewa zai yi tafiya don haka ya bar musu ajiyar
gari a hannunsu kuma ba zai wuce wata biyu ba zai
dawo.
Bayan Sarki Huraisu ya gama kimtsawa sai ya
fito daga cikin turakarsa ya nufi kofar fita daga gidan
sarautar gaba daya.
Yana cikin tafiya ne ya yi kicibis da matarsa
Sabirat tsaye a gabansa, hawaye na zuba daga cikin
idanunta daki-daki.
Nan take jikin Sarki Huraisu ya yi sanyi kuma ya
Ji tausayinta ya shigeshi a karon farko a iya zamansa
da ita,
A haukali ya karasa daf da ita ya dubcta ya ce,
"Ya ke matata ina dalilin zubar wannan hawaye naki?"
Koda jin wannan tambaya sai Sabirat la rungume
Sarki Huraisu ta fashe da matsanaicin kuka ta ce, Ya
Kui mijina za ka yi tafiya amma ko yi mini sallama ba
ka yi ba
Menene tabbacinka cewar zamu sake saduwa?
Ka yi sani cewa a tarihin Sarakunan kasar nan gaba
dayansu suna bacewa ne su shude a lokacin da tafiya
ta riskesu, walau suna kan han yar tafiya ko ta dawowa.
Dan uwanka Muraisu ne kadai ya mutu a cikin
garin nan a kofar gari sa'adda ku ka yakeshi kai da su
Sarki Imras.
Yanzu shi ke nan haka duk za ku tafi ku barni ni
kadai a cikin gidan sarautar nan?
Suzaila ta tafi har yau ba ta dawo ba, kaima kuma
gashi yanzu za ka tafi ban san ranar daWowarka ba?
Na zama ni kadai babu 'ya, kuma babu miji".
Koda jin wannan batu sai Sarki Huraisu ya janye
jikinsa daga cikin na Sabirat suka fuskanci juna ya
dubeta cikin alanun tausayawa yà ce, "Ya ke matata ki
yI sani Cewa ba a san raina zan tafi na barki ba, kuma
in ba don wannan tafiya ta kasance mai hadari ba da
tare da ke zan tafi. Ina so ki sani cewar faduwar gaba
asarar namiji ce.
Da dai azo a cini da yaki har gida gwara na fita
na tari abokan gaba. Ina mnai tabbatar miki da cewa ni
da 'yarki zamu dawo gida a raye cikin koshiiin lafiya
nan da cikar wata biyu".
Koda gama fadin hakan sai ya sumbaci goshinta
sannan ya juya ya yi tafiyarsa ba tare da ya sake
waigowa ba amma tuni idanunsa sun ciko da kwallah
baya so ta gani ne, ita kuwa Sabirat sai ta bishi da
kallo kawia tana mai ci gaba da zubar da hawayc kurma
ta ji kamar ta
bishi.
ruga da gudu ta
Wannan shi ne abinda ya faru a Birnin Lairuftsakanin
Sarki Huraisu da matarsa Sabirat mahaifiyar Gimbiya
Suzaila.
A CAN bangaren su Jarumi Imran kuwa, lokacin
da suka iso wannan kauye tare da tsirarurn yan garin
wadanda suka rayu sai suka kama aikin gyaran garin
aka shiga kwaba kasa ana yin bululluka wasu kuma
suka rinka shiga daji suna saro itatuwa wadanda za
Yi rufin sama da su.
Haka dai aka wanzu ana ta yin wannan aiki har
Tsawon kwana goma sha tara, a sannan ne sabon Birnin
ya dawo sabo ya yi kyau matuka fiye da yadda yake a
da can.
A tsawon wadannan kwanaki kuma an fita bayan
gari an fitar da gonakai an vi shuka. Nan da nan
gonakin suka yi yabanya abin gwanin ban sha'awa.
Haka kuma kullum Jarumi Imran yana koyar da
mutanan garin yadda ake ibada, kai har ma sai da aka
gina masallaci a tsakiyar Birnin, Jarumi Imran ne yake
limanci.
Nan da nan mutanan garin suka sami ilimi mai
yawa kuma suka tsinci kansu a cikin rayuwa mafi dadi
gami da samun nutsuwa da kwanciyar hankali.
Duk abinda yake faruwa a Birnin su jaruma
Suzaila suna gani kuma abin yana matukar burgesu da
basu sha'awa amma kullum a cikin yin shawara suke
akan su karbi addinin Jarumi Imran ko kada su kar6a
sun kasa yanke hukunci.
A koda yaushe idan Suzaila ta ga Lushaira tana
kusanutar Jarumi Imran sai kishi ya kamata itamna ta
kusanceshi ya zamana cewa ta hanasu samin damar da
za su yi wata magana wacce ta shafi soyayya.
Al'amarin da ya rinka kona zuciyar Lushaira ke
nan ta inka kamuwa da tsananin bakin ciki kumna ta
rasa yzdda za ta yi ta shawo kan matsalar.
Ana cikin wannan hali ne wata rana Jarumi Imran
ya tara mutanan kauyen a tsakiyar gari ya hau
mumbari yana yi musu wa'azi ya sanar da su irin
abubuwan da Allah Ya tanada na azaba
ga wadanda
AA Misau ke Magana
suka bijire masa da kuma abubuwan da ya tanada na
jin dadi ga wadanda suka bishi sai ga su jaruma
Suzaila sun zo wucewa ta wajen domin su fita daji yin
farauta tamkar yadda suka saba yi kullum da safe.
Jaruma Suzaila ce mai jagorantar wannan farauta
kuma idan aka tafi farautar ba a dawowa sai yamma.
Sanadiyyar fatocin dabbobin da suke zuwa da su
ne aka kafa sabuwar kasuwa a kauyen ta cinikin fata.
Cikin kwanaki kadan kasuwar ta bunkasa ya
zamana cewa mutanan da ke zaune a sauran kauyukan
da ke makofataka suka rinka zuwa cin kasuwa, daga
nan kuma masu zuwa cin kasuwar suka rinka karbar
addinin Musulunci.
A kan wannan dalili ne Jarumi Imran yake
tsananin farinciki da wannan farauta ta su jaruma
Suzaila saboda ta kawo ci gaban Rauycn ta fannin
arziki da yaduwar addinin ALLAH.
Lokacin da su Suzaila suka zo giftawa ta gaban
Jarumi Imran a lokacin daya ke gabatar da wannan
wa'azi sai maganganunsa suka ratsa zuciyar Lushaira.
Nan take taji kaunar addinin Musulunci ta shiga
ranta, ba ta san sa'adda ta noke ba ta tsaya a inda ake
yin wa'azin. har su Suzaila suka nausa cikin daji suka
yi nisa basu ankara ba cewar babu ita a cikin zugar.
Sai da Jarumi Imran ya. shafe sa'a hudu yana
wa'azi sannan ya kammala.
A sannan ne mutane suka watse kowa ya kama
gabansa ya zamana cewa babu wanda ya rage a filin
wa'azin face Gimbiya Lushaira a tsayc, hawaye na
zuba a idanunta.
Ko kadan Jarumi Imran bai kula da cewar
Lushaira na tsaye a wajen ba sai da ya sauko daga kan
mumbari sannan kawai ya ganta a tsaye ita kadđai a
filin tana zubar da hawaye .
Cikin tsananin mamaki Imras ya matso kusa da
ita ya dubcta ya ce, "Ya ke Lushaira ina dalilin zubar
wannan hawaye a idanunki?"
Sa'adda Lushaira taji wannan tambaya daga bakin
jaruma Imran sai tayi ajiyar zuciya sannan ta dubcshi
cikin nutsuwa ta ce, "Ya kại wannan Jarumi ma'abocin
kyau da sadaukantaka ta ban mamaki ka yi sani cewa
ba wani abu bane ya sani zubar da wannan hawaye ba
facc tsananin jin dadin yadda kalmomin da na ji daga
bakinka a wannan wa'azi da ka gama yanzu.
Ka yi sani cewa tun da na zo duniya ban taba jin
irin wadannan kalmomi ba wadanda babu mahaluRin
la rai iya tsarasu komai iya zancensa. Babu wani
bil'adama ko aljani mai irin wannan basira da hikima.
Lallai wanda yai wannan zance shi ne mafificin
komaí da kowa don haka na yi imani da shi kuma na
gamsu cewa shi ne Ubangijin da ya fi cancanta a bauta
masa,"
Koda Lushaira tazo nan a zanccnta sai Jarumi
Imran ya kamu da tsananin farinciki mara misaltuwa
kuma yaji nan take a karon farko a rayuwarsa ya kamu
da soyayyar 'ya mace.
Cikin muraa ya dubeta ya ce, "Shin yanzu kina
nufin kin amince ki karbi addinin gaskiya?"
Lushaira ta yi murmushi mai taushi ta ce,
"Kwarai kuwa na amince da raina, zuciyata da gangar
jikina gaba daya.
Nan take Imran ya daga kansa sama ya yiwa
Allah godiya sannan ya dubi Gimbiya Suzaila ya biya
ma ta kalmar Shahada ta maimaita.
Lushaira ta ce, "Ya kai sadaukin Sadaukai, ina
rokonka alfarma guda daya.
Alfarmar kuwa ita ce, na boyewa sauran yan
uwana wannan addini da na karba kuma ina son ka
koyar da ni addinin a sirrance ba tare da sun sani ba."
Da jin wannan batu sai Jarumi Imran yai
murmushi sannan ya dubi Lushaira cikin nutsuwa ya
ce, "Ya ke wannan ma'abociyar kyau ki yi sani cewa
ba a yin addinin Allah da tsoro, sannan kuma bana son
na rinka koya miki wannan addini a sirrancc saboda
bai kamata mu rinka kebanta ba ni da ke tunda baki
kasance muharramata ba.
Koda jin wannan batu sai hankalin Lushaira ya
dugunzuma ta ce, "Ai kuwa in dai haka ne sai dai mu
yi abu da
daya, domin ka cetoni daga irin tsangwamar
yan uwana za su vi mini. Lallai za su ji haushina su
kyamaccni saboda na kar6i addininka ba tare da
shawararsu ba.
Abinda za ka yi ka kubutar da ni shi ne, kawai ka
aureni na zama matarka".
Koda jin wannan batu sai Jarumi Imran yaji
zuciyarsa ta buga da karfi ya yi shiru yana tunani, daga
can sai ya dubi Lushaira ya ce, "Ya ke ma'abociyar
kyawu ki yi sani cewa shi aure a Musulunci yana
bukatar walicci na dangi ko iyaye ko kuma wadanda
suka dace.
Anan garin ni da ke duk bamu da wanann
walacci, saboda haka ki ajiye wannan magana a gefe
daya. Ki tuna cewa fa akwai babban aiki a gabanmu na
zuwa dajin Kirzufa don gabatar da yaki da Jarumi mai
kahon BUSA A MUTU.
Abinda nake so da ke shi nc, ki saki jikinki kuma
ki kwantar da hankalinki domin zan zame miki
garkuwa mai kareki daga dukkan kyamatar abokan
tafiyarki.
Lallai ba zamu 6oye musu karbar addininki ba.
Yanzu ki je ki sami daya daga cikin matan garin nan
domin ta koyar da ke yadda ake wankan tsarki, alwala
da sallah, sannan sai ki ci gaba da daukar karatu na
samun ilimin wannan addini mai TSarki".
Koda gama wannan jawabi sai Jarumi Imran ya
juya ya nufi hanyar da za ta kaishi izuwa masallacin
garin,
Dama tunda aka gina garin, wannan masallaci shi
ne makwancinsa kuma shi ne makarantarsa inda yake
koyar da ilimin addini.
Ba tare da bata wani lokaci ba kuwa Lushaira ta
nufi daya daga cikin gidajcn garin domin ta koyar da
ita abubuwan da Jarumi Imran ya lissafa ma ta.
Al'amarin su Gimbiya Suzaila kuwa, lokacin da
suka yi nisa a cikin dajin don gabatar da farauta sai
kawai Suzaila ta tuno da Lushaira.
ta waigo baya ta dubi gaba dayan
abokan tafiyar,
Koda ta ga babu Lushaira a cikinsu sai hankalinta
ya dugunzuma ta ji wani irin bakin kishi ya turnuketa
tayi zargin cewa lallai Lushaira ta ki tahowa wannan
farauta nc domin ta sami damar da za ta gabatar da
soyayyarta ga Jarumi Imran,
Nan take Suvaila ta jí kamar ta bayar da umarnin
a koma da baya a fasa yin farautar amma da tayí
tunanin cewa sauran abokan tafryar Za su gano cewar
saboda kishi ne tayí hakan sai ta fasa, aka ci gaba da
kutsawa cikin daji.
Nima AA Misau ganin wannan kishin nata yasa zan dakata anan🥰
Zamu dakata anan saikuma wani lokaci zamu cigaba insha Allah
Admin
AA Misau ke Magana
WhatsApp group
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q

BUSA A MUTU!!! 💕
Littafi Na Shida (6)🩸
Part E. 💎
Takun Karshe😍
Na Abdulaziz Sani M Gini 🤴
Typing
AA Misau ke Magana✍️⭐⭐⭐
(HAKIKA KUN NUNA MANA KUNA SON LITTAFIN NAN SABODA HAKA GA ALKAWARI NA NAN NA CIKA 😎 kucigaba da nuna mana goyon baya kusha LABARAI)
Labari ya isowa Shagala cewa
Marubucin yaci gaba da cewa..
TUNANIN CEWA SAURAN ABOKAN TAFRYAR ZA SU GANO CEWAR
SABODA KISHI NE TAYÍ HAKAN SAI TA FASA, AKA CI GABA DA
KUTSAWA CIKIN DAJI.
Aikuwa ashe a sa a Suka fito domin sai da Suka
kama damisa guda ukü gamida manyan. Macizai guda bakwai
a lokacin ne rana ta fadi
Bayan sun yada zango an gasa maciji guda daya
kowa ya ci ya koshi sai suka tashi, suka kimtsa, aka
taho gida.
Suj auma Suzaila, basu shigo cikin gari, ba, sai daf
da magariba lokacin da ake yin sallah.
Koda su Suzaila suka zo giftawa ta gaban
Masallaci sai suka yi kicibis, da Gimbiya lushaira tayi
shigan fararen tufafii ta rufe jikinta ruf da mayafi za ta
shiga masallacin bangarèn mata
Nan take su duka suka tsaya cak suna kallonta
cikin tsananin takaici da mamaki. Saboda fishi ma, sai
su duká suka wuce basu ce da ita kala ba. Dan uwantai Yarima lHasnalu.ne kadai ya tsaya ya
dubeta cikin alamun tsananin darmuwa kamar zai yi
kaka yace, Yake yar,uwata mene ne dalilinda ya sa
kika kar6i wannan addini ba, tare da shawarar mu ba?"
koda jin Wannann tambaya sai:Lushaira tayi
rmurmushi taoe, Na karbi wannan addini ne saboda
shine na gaskiya kuma naga hujjoji a Zahiri da
idanuna;wadanda suka sä na gamsu da haka
Kuma kun ga wadannan hujjoji da idanunku
kawai dai kun tsaya yin taurin kai ne da yin
shawarwari na banza wadanda basu da wani amfani.
Koda gama fadin hakan sai Lushaira ta juya ta
shige izuwa cikin masallacin ta bar Yarima Hasnalu a
tsaye cikin tunani da wasi-wasi. Nan take shima yaji
zuciyarsa tayi na'am da addinin Musulunci.
Daga wannan rana Lushaira ta ci gaba da yin
addininta a fili a gaban su Suzaila ba tare da shakkar
komai ba har ta sami ilimi mai yawa na addini.
haka kuma ita da Jarumi Imran suka ci gaba da
soyayya a boye har ma soyayyar ta fito fili kowa ya
fahimta.
A sannan ne Suzaila taji ta tsani Lushaira ainun
kamar ta kasheshi ta huta saboda kishi amma ta
hakura ta danne abin a cikin ranta.
A ranar da suka cika kwanaki arba'in ne dai-dai a
wannan gari su Suzaila suka taru gaba dayansu suka
Z0 gaban Jarumi Imran suka durkusa kasa sannan
Swzaila ta dubeshi ta ce, "Ya kai sadaukin sadaukan
duniya ka yi sani cewa mun ZO ne mu sanar da kai
cewa wa'adin da ka dibar mana na Zama a wannan gari
ya cika, kuma yanzu mun amince da sharadin da ka
gindaya mana cewar za mu karbi addininka bayan mun
je dajin Kirzufa ka kamo mai kahon BUSA A
MUTU."
Koda jin wannan batu sai Jarumi Imran ya cika
da tsananin farinciki ya dubi Suzaita cikin murmushi
mai taushi ya ce, "Ai shi ke nan Sai ku je ku fara yı
mana shirye-shiryen tafiya. Kuma lallai a kammala
shirin kafin rana tayi domin mu sarni nutsuwar tafiyar.
Ba tare da gardamar komai ba kuwa su Suzaila
suka tashi suka ruga izuwa kasuwa suka sayi dawakai
da sauran kayan guzuri suka dawo cikin gari.
Sai da aka gama kimtsawa sannan aka je aka
sanar da Jarumi Imran cewa an gama shirin komai shi
ake jira. A wannan lokaci gaba daya mutanen garin
taru a masallacin domin su yi bankwana da shi.
Koda jama'a suka ji ccwar Jarumi Imran zai tafi
sai kowa ya fashe da kuka mazansu da matansu, yara
da manya saboda tsananin sabon da suka yi da shi da
kuma matukar kaunar da suke yi masa.
Kai ba ma shi ba, hatta L.ushaira da ta ja su a jiki
sa'adda ta kar6i addinin Musulunci sai sukai ta yin
kukan rabuwa da ita.
Nan fa zuciyar Imran da ta Lushaira ta karaya
suma suka kana kuka suka ji kamar su fasa yin tafiyar.
Da kyar su Yarima Hasnalu suka janyesu daga
cikin jama'a aka basu dawakai suka hau sanann suka
tafi suna waigen mutancn garin suna zubar da hawaye.
AA Misau ke Magana
Su kuwa jama'ar garin sai suka barke da kuka
wadansu manyan
tamkar wadanda
makusantansu.
suka
rasa
Komai taurin zuciyar mutum a wannan lokaci ne
dole ne tausayi ya kamashi domin su Gimbiya Suzaila
ma sai da suka rinka zubar da hawayensu.
Lokacin da wannan tawaga ta su Jarumi Imran
suka yi nisa da barin wannan kauye, suna cikin tafiya
sai suka ga wata inuwar wata katuwar halitta ta gifta ta
mansu cikin tsananin azababben gudu tamkar
tauraruwa mai wutsiya.
Kafin su daga kansu sama su ga ko mene ne tuni
halittar ta bace a cikin gajimare.
Kawai sai suka ga Jarumi Imran ya kalli sama yai
murmushi.
Cikin alamun mamaki jaruma Suzaila ta dubeshi
ta ce. "Ya kai sadaukin sadaukan duniya, menene
dalilin da ya sa ka kalli sama ka yi murmushi?"
Koda jin wannan tambaya sai Jarumi Imran ya yi
murmushi ya ce, "Kar ki damu nan gaba za ki san
dalilin yin wannan murmnushi nawa'".
Suzaila ta gyada kai sannan tayi dogon tunani ta
sake dubansu ta ce, "Ya kai Imran ka yi sani cewa
daga nan fa zuwa dajin Kirzufa tafiya ce ta a kalla
kwana arba'in da daya kuma akwai muggan aljanu da
muggan dabbobin daji da 'yan fashi wadanda za su iya
Keaa bata mana lokaci kuma za su zama sanadıyyar
ajalin wadansu daga cikinmu."
Imran ya numfasa ya ce, "Ai duk na san da
wadannan abubuwa amma da izinin Ubangijina babu
abinda zai taba lafiyar daya daga cikinmu har mu isa
dajin Kirzufa kurna wannan tafiya ta kwana arba'in da
daya Ailah zai gajarce mana ita ta koma ta kwana
goma sha daya".
Koda gama fadin hakan sai Jarumi Imran yai
shiru bai kara cewa uffan ba har aka yini ana tafiya.
Kamar yadda Jarumi Imran ya fada haka
al'amuran suka kasance wato duk dajin da suka ratsa
da zarar 'yan fashi ko muggan aljanu ko dabbobi sun
hangosu sai ka ga suni ratsawa suna basu hanya ko
matsowa ma kusa da su basa yi, kai ka ce ajalinsu suka
gani.
Ba komnai ne ya hadadsa hakan ba face karfin
addu'ar da Jarumin Imran ke ta karantawa a cikin
zuciyarsa ta neman tsarin Allah akan dukkan abu.
Wani abu da ya daurewa su Gimbiya Suzaila kai
shi ne, ganin yadda suka rinka shafe doguwar tafiya
mai nisan tsiya a cikin kankanin lokaci tamkar masu
daurin kasa.
A takaice dai a cikin kwana goma sha daya kacal
suka shafe tafiyar kwana arba'in da daya suka iso
bakin dajin Kirzufa suna isowa wajen ne Jarumi Imran
ya daga hannunsa sama kowa ya tsaya a bayansa
sannan sai ya karanta wadansu addu'o'i na musamman.
Kawai sai ya dubi su Gimbiya Suzaila ya ce,
"Kowa ya biyoni a baya kada wanda ya kuskura ya
wuce gabana".
Yana gama fadin hakan ya sakarwa dokinsa
linzami ya kunna kai cikin dajin. Lushaira ce ta fara
bin bayansa saboda tayi imani da Allah cewa babu
abinda zai sameta.
Suzaila, Sarkin yaki, tagwayen Sadaukai da
sauran bayi da kuyangi kuwa sai suka dan noke cikin
alamun tsoro-tsoro.
Sai da suka ga Imran da Lushaira sun yi dan nisa
a cikin dajin sannan Suzaila ta bi bayansu a guje suma
sauran tawagar suka bita.
A dai-dai wannan lokacin nc Muraisu ya kamata
ya busa kahon BUSA A MUTU, saboda haka tuni ya
dauko kahon ya zo tsakiyar dajin na Kirzufa ya tsaya.
Koda ya daga kahon sama ya busa sai yaji kahon
ya ki busuwa.
A zatonsa ya yi ne ya shiga cikin kofar kahon ya
tosheshi don haka sai ya zarzageshi a kasa amma bai
gu komai ya fado daga cikinsa ba.
Ya zura hannunsa cikin kahon nanma yaji babu
komai a cikinsa kawai sai ya sake daga kahon ya kafa
a bakinsa ya busa a karo na biyu.
Ai kuwa sai yaji dai kahon ya ki busuwa.
Al'amarin da yai matukar dugunzuma har alimsa Ke
nan ya rasa abinda ke masa dadi
Kawai sai ya sa6a kahon a bayansa ya juya da
nufin ya koma inda mahaifiyarsa take ya sanar da ita
abinda ke faruwa.
Yana juyawa sai yaji takun sawun dawakai a
bayansa.
Cikin hanzari ya juyo. Take ya yi arba da su
Jarumi Imran sun durfafo inda yake.
Koda Muraisu ya ga su Imran sai ya daga kansa
sama ya takarkare ya kwarara uban ihu. Faruwar
hakan ke da wuya sai ga dabbobin dajin suna fitowa
daga kowanne bangare suna falfalowa da gudun tsiya
suna taruwa a bayan Muraisu.
Ana cikin haka ne sai ga Husnaila ma rike da
mashinta ta falfalo da azababben gudu.
Tana isowa daf da Muraisu sai ta tsaya cak tayi
tirjiya tana haki.
A dai-dai lokacin ne su Imran suka kara
kusantosu ya zanmana cewa tsakaninsu bại wụce taku
goma ba. Kawai sai Imran ya ce da su Suzaila su
sauko daga kan dawakansu suka tsaya cak aka fara
kallon-kallon.
Koda Muraisu da Husnaila suka kyallara ido suka
ga Lashaira sai suka icka da tsananin mamaki saboda
AA Misau ke Magana
Lushaira da Husnaila kamanninsu iri daya ne sak
tamkar an tsaga kara.
Daga can sai HuSnaila ta dubi Lushaira ta daka
masa tawa ta ce, "Ya ke wannan budurwa mai kama da
ni, wace ce ke kuma mene ne ya kawoku nan cikin
dajin Kizufa?"
Har Lushaira ta budi baki za ta bata amsa sai
Jarumi lmran yai sauri ya numfashinta ya cc, "Wannan
ita ce Gimbiya Lushaira 'ya ga dan uwanki Sarki
Imras.
Ni kuam sunana Jarumi Imran ma'abocin addinin
Musulunci.
Wannan jaruma da ke bayanmu kuwa ita ce
Gimbiya Suzaila 'ya ga Sarki IHuraisu dan uwan
mijinki marigayi Sarki Muraisu.
Ku yi sani cewa bamu shigo nan dajin domin mu
yakcku ba mu kasheku sai domin mu tsaidaku akan
barnar da kuke yi ta salwantar da rayukan 'ya'yan
Sarakan duniya.
Kamar yadda danki Muraisu ya ga zahiri a yanzu,
wato a daga kahon domin ya busa amma sai kahon
ya ki busuwa.
To fa wannan ta faru ne da taimakon Ubangijin
Musulunci, ba wai taimakon tsafi ba.
Duk irin zaluncin da aka yi muku ke da danki aka
jefaku a cikin rayuwar kunci anan daji duk 'ubangijina
ya nuna mini a cikin barcina.
Abinda nake so da ku shi ne, ku ajiye
makamanku ku karbi addinina in yaso sai na tafi da ku izuwa Birhin Lairuf inda za a kirawo 'yan uwanku
Sarki Huraisu da Sarki Imras suma su kar6i addinin
gaskiya sannan mu yafi juna a fara sabuwar rayuwa ta
bin Allah".
Kafin Jarumi Inran ya gama rufe bakinsa tuni
Jarumi Muraisu ya daka masa tsawa yna mai cewa,
"Ya kai wannan ma'abocin addinin Musulunci ka yi
sani ccwa tunda ka Zo mana da batun yin sulhu
tsakanin mu da abokan gabainu ba zamu ta ba yarda da
kai ba don haka kaima kana sahun makiyanmu
tsakaninmu da kai sai yakı"
Muraisu na gama fadin hakan sai ya zare
takobinsa ya ruga izuwa kan Jarumi Imran yana
kururuwa irin ta manyan mazaje wacce ke firgita
dandazon mayaka.
Itama Iusnaila sai ta biyo bayansa a guje haka
ma gaba dayan sauran dabbobin dajin duk suka yiyo
kan Imran.
Har su jaruma Suzaila sun yunkura za su
taimakawa Jarumni Imran sai ya daka musu tsawa ya
hanasu.
Nan take yaja dogon layi a gaban su Suzaila ya
karta kasa da takobinsa sannan ya faifala da gudu ya
tari su Muraisu suka ruguntsume da azababbci yaki
Duk dabbar da ta iso dai-dai wannan layi wanda
Imran ya ja a gaban su Suzaila sai ta kasa ketare layin
ta kai nusu hari domin ji take tamkar ana huro ma ta
wuta mai mugun zafi.
Nan

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment