Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da
matukar jarumtaka haka?
Duk sa'adda Sarki Labarazu ya gabza masa naushi
a kirji ko a fuska sai ka ga ya shanye dukan.
Amma da zarar shi tsohon ya gabzawa Sarki
Labarazu naushi daya sai ka ga har faduwa kasa yake.
Nan da nan cikin kankanin lokaci tsohon ya
hadawa Sarki Labarazu jini da majina.
AA Misau ke Magana
Koda Sarki Labarazu ya ga va fara jigata sai ya ci
gabu da anfani da karfin sihiri ya rinka watsawa tsohon
wula, kibbau da sauran mugayen abubuwa domin sun ki
su yi tasiri a jikin tsohon.
Ana cikin haka ne tsohon ya zage iya karfinsa ya
gabzawa Sarki Labarazu wawan naushi a fuska. Take
hakoran Sarki Labarazu guda biyu suka yi fitar burgu
daga cikin bakinsa ya sulale kasa daga tsaye ya yi
faduwar manya a sume.
Nan take Dakarun Sarki Labarazu suka ruga izuwa
kansa suak watsa masa ruwa.
Faruwar hakan ke da wuya sai Sarki Labarazu ya
farfado a lokacin da kansa ya kumbura yai suntum! Yana
bude idanunsa da kyar a lokacin da yake gani dishi-dishi
sai ya ga wannan Jarumin tsohon ya durfafoshi da nufin
ya karasa kashe shi.
Koda tahowar tsohon sai gaba dayan Dakarun Sarki
Labarazu suka watse suka gudu izuwa can gefe daya
suka zube kasa suna tsuma.
Shi kuwa Sarki Labarazu sai ya mike zaune zumbur
va kama rokon tsohon yana mai cewa, "Ya kai wannan
tsoho ka yi mini rai na yi alkawari yanzu zan bar wannan
gari kuma idan na tafi ba zan sakc dawowa ba."
Koda jin wannan batu sai tsohon ya dakawa Sarki
Iabarazu tsawa ya ce, "Kai tsohon azzalumi kuma
munafukin Allah, shin ka manta ne cewa sau biyu muna
fafatawa ni da kai kuma na yì maka kashcdi akan cewa
idan har baka tuba ba ka daina shayar da Dodonka jini
sai na hallakaka sa'adda muka yi karo na uku?
Tabbas ni mai cika alkawari nc domin rayuwarka
ba ta da wani amfani a wannan nahiya gaba daya.
Lallai yau Allah Ya kawo Rarshenka, don haka da
izinin Ubangijina yanzu za ka bar duniya".
Kafin Sarki Labarazu ya budc baki ya ce wani abu
sai tsokon ya daka tsallc sama tamkar an cilloshi daga
cikin baka.
A lokacin Sarki Labarazu ya. wangame bakinsa da
nufin ya ce wani abu, amma sai tsohon ya soka masa
wannan sanda tasa a cikin bakin.
Take sandar tá nutse a cikin bakin ta faso ta cikin
keyarsa sannan ya zare sandarsa.
Sarki Labarazu ya kana kakarin mutuwa, cikin
karfin hali ya zaro wani karanin kahon tsafi daga jikinsa
ya busashi.
gawa.
Yana gama busa kahon kansa ya langabe ya zama
A dai-dai wannan lokaci nc gaba dayan kauycn ya
kama girgiza kasa ta fara tsagcwa, mutane da gidaje suka
rinka ruftawa cikinta.
Nan take wannan tsohon Jarumi ya yiwa su
Gimbiya Suzaila inkiya da su biyoshi a baya.
Nan take kuwa dukkaninsu suka bishi a baya a
guje. Inda tsohon ya bi ne kadai baya tsagewa.
Haka dai su Suzaila suka ci gaba da bin Wannan
tsoho suna waigawa
haya suna ganin abin tausayi da abin
mamaki, domin kiri-kiri suka rinka iiyo ihun mutanc a
lokacin da suke nutsewa a cikin Kasa.
Gidaje kuwa suka rinka rugujewa suna bajcwa a
kasa. A takaice dai gaba davan mutanen wannan kauye
sai da suka hallaka, kuma babu gida daya wanda bai
dagargaje ba.
Sai da su Gimbiya Suzaila suka shafe sa'a guda
Suna gudu sannan suka tsira daga sharrin wannan
girgižar kasa kuma dawakansu ma gaba daya sai da suka
hallaka.
Lokacin da girgizar kasar ta daukc nc cif su
Gimbiya Suzaila suka waigo suka ga kauycn gaba daya
ya nutsc izuwa cikin karkashin kasa sai nan take suka
dawo cikin haiyacinsu suka tuno da sauran abokan
tafiyarsu wato Dakaru, bayi da kuyangi wadanda suka
barosu a gidan da Sarkin kasuwa ya saukesu.
Nan take hankalinsu ya dugunzuma suka fara
tunanin su koma da baya domin su jc su tona
gawarwakin su.
Ilar sun yunkura za su koma da baya sai wannan
Jarumin tsoho ya tsaida su ya dubi Suzaila da Sarkin
yakinta ya ce, "Ku kwantar da hankalinku da izinin
Ubangiji na za ku sadu da 'yan uwanku wadanda kuka
baro a cikin wancan kauye da ya baje.
Ina so ku gane cewa yanzu haka sauran yan
Uwanku mutum uku da kuka fito nema suna can kogon
Dodo da ke gabanmu tafiyar sa'a uku.
Tabbas rayuwarsu tana cikin hadari saboda haka su
va kamata mu je mu ccci rayuwarsu katin wannan Dodo
ya hallakasu".
Koda jin wannan batu sai Gimbiya Suzaila ta taho
gaban tsohon ta tsaya daf da shi ta dubeshi cikin
murmushi la ce "Ya kai wannan dattijo mai jarumtaka ta
ban al'ajabi kayí sani cewa ko a tarihi ban taba jin labarin
mutum mai irin jarumtakarka ba wanda ya kai
shekarunka haka.
Da farko dai ina mai mika godiya ta musamman a
gareka bisa ccton rayuwarmu da ka yi gaba dayanmu nan
domin in ba don kaiba da tuni yanzu wannan azzalumin
Sarki ya hallakamu tunda ya fimu karfin damtse da
karfin sihiri.
Alfarmar da nake nema a wajenka yanzu ita ce, ina
son ka bamu labarinka kuma ka sanar da mu irin addinin
da kake yi domin mun ji duk abinda za ka yi kana
ambaton Ubangijinka".
Lokacin da Suzaila ke wannan jawabi Gimbiya
Lushair ta fara matsowa gaba tana mai kurawa Dattijon
idanu saboda ta ga idanun nasa sun yi ma ta kama da na
almajiri Sarumi Imran.
Koda dattijon ya ga Lushaira tana matsowa kusa da
shi kuma ta kura masa idanu sai ya juyawa Suzaila baya
AA Misau ke Magana
ya ce, "Yanzu bamu da lokacin da zan tsaya baku wani
labari don haka sai ku z0 mu hanzarta tafiya iZUWa
kogon Dodo."
Yana gama fadin hakan ya juya ya ci gaba da taliya
yana mai dogara sandarsa.
Cikin hanzari Suzaila, Lushaira, Sarkin yaki suka
Kamar yadda tsoho ya fadi haka al'amarin ya
kasance, wato sai da suka shafe sa'a uku cur suna ratsa
daji sannan suka iso kofar kogon Dodo.
Abinda yai matukar baiwa su Gimbiya Suzaila
mamaki shi ne, tunda aka fara wannan tafiya tsohon bai
gaji ba kuma shi ne akan gaba yana ta tsala sauri kamar
zai tashi sama, duk da cewa sai ya dogara sanda yake
taliyar.
Su kuwa su Giimbiya Suzaila dukkaninsu babu
wảnda bai gaji ba har mna suna hada kafa suna sassarfa
kamar za su fadi kasa.
Shi dai wannan kogo wanda Dodo ke ciki ya
kasance mai girma da tsawo, sannan wani katon
gungumcn dutse ne ya rufe kofar kogon wanda koda
mutum dubu sun taru basu isa su iya matsar da shi ba.
Shi kansa Sarki Labarazu da karfin sihirin tsafi
yake daga dutsen sama, idan za a shigar da mutancn da
aka kamo ciki.
Da isowar su Gimbiya Suzaila bakin wannan kogo
sai suka yi cirk0-cirko aka zubawa dutsen idanu cikin
karayar zuciya.
Shi kuwa wannan tsohon Jarumi sai ya koma gefe
daya ya zauna yana kallon su domnin ya ga abinda Zả su
yi. Gimbiva Suzaila ta dubi Sarkin yaki sanann ta dubi
Lushaira da Hasnalu ta cc, 'Shin a cikinku akwai wanda
yake da dabarar da vake ganin zamu iya janye wannan
katon dutse mu shiga cikin wannan kogo?
Koda jin wannan batu sai Sarkin yaki ya ce, "Ya
Shugabata ai ina ganin cewa mu jarraba tureshi tukunna
ni da ke idan muka kasa sai kuma mu jarraba karlin
Lsafinmu".
Gimbiya Suzaila ta ce, "Tabbas ka z0 da shaw ara
mai kyau".
Ba tare da bata wani lokai ba gimbiya Suzaila da
Sarkin yaki suka je gaban katon dutsen suka dora
hatavensu bibbiyu akai suka tara karlinsu gaba daya
suha tura amma sai dutsen ya ki motsawa ko kadan.
Nan take duk su bivun suka fara amfani da kartin
sihirinsu don su ture dutscn.
Sai da suka jina suna lalatawa har ya 7amana cewa
Nn jike sharkal da gumi amma abu ya faskara.
Duk wannan abu da ke faruwa Gimbiva Lushaira
na tsaye a can gefe daya ta kurawa Jarumin tsohon nan
idanu tana ta kokarin ta kwatanta kamannin idanunsa da
Jarumi Imran, shi kuma tsohon duk sa'adda ya dago
kai ya hada idanu da ita sai ya yi sauri ya sunkui da
kansa kas.
Bayan su Suzaila sun yi iya yinsu sun kasa turc
wannan dutse sai suka koma gefe daya suka zauna. A
sannan nc Gimbiya Suzaila ta dubi wannan Jarumin
Isoho sannan ta dubi Sarkin yaki ta ce, "Ai kuwa mun yi
garaje.
Bai kamata mu jarraba kawar da wannan dutse ba
tun da farko tunda muna tare da wannan sadaukin
Sadaukai domin masu iya magana sun ce ta inda aka hau
ta nan ake sauka,'"
Hasnalu da ke tsaye daf da su sai ya dubi Gimbiya
Suzaila ya ce, "Ai shima wannan Jarumin tsoho yana
sane ya zuba muku ido domin ya ga iya gudun ruwanku
saboda na ga yana ta yi muku dariya a lokacin da kuke ta
kokarin kawar da dutscn".
Suzaila tayi ajiyar zuciya sannan ta dubi Hasnalu
cikin murmushi ta ce, "IHakika abinda ka fadi gaskiya
ne.
Ya kai Ilasnalu ka yi sani cewa ina godiya a garcka
bisa yunkurin ceton rayuwata a dazu sa'adda Sarki
Labarazu ke kokarin hallakani. Tabbas kauna ce tasa ka
yi ganguncin taimakona tunda ka san ccwa ba za ka iya
ba".
Sa'adda Hasnalu yaji wannan batu dapa bakin
Gimbiya Suzaila sai ya kamu da tsananin farın ciki
domin a zatonsa ta karaya ne ta sauya shawara akan
ka'idar da ta shimfida masa cewar sai ya kamo Jarumi
za ta karbi
mai kahon BSUA A MUTU sannan
soyayyarsa amma kuma sai kawai ya ga ta dauke kai ga
barin kallonsa ta juya ta nufi inda Jarumin tsohon yake.
Koda ta iso daf da shi sai ta risina a gareshi cikin
biyayya ta ce, "Ya kai wannan dattijo mai ban al'ajabi
ashe baka taimakcmu ba ka bude mana kofar wannan
kogo tunda mu mun kasa?"
Sa'adda dattijon yaji wannan batu sai
murmushi ga Gimbiya Suzaila ya ce, "Ai nima ba
ture wannan dutsc ba face da taimakon Ubangijina.
ya yi
iya
Zaman da kika ga na yi anan addu'a nake yi ina
rokon Ubangijin nawa domin Ya bamu sa'ar kawar da
dutscn.
A hálin yanzu bani da tababcin Ubangijin nawa Ya
amsa addu'ata amma kije ki sake jarraba ture dutsen mu
gani, wata kila Ubangijin nawa Ya amsa rokona bamu
sani ba,"
Ba tare da wata gardama ba kuwa Gimbiya Suzaila
ta durfafí bakin kogon cikin karayar zuciya domin ko
kadan bata sa ran cewa abin zai faru.
Tana zIwa gaban wannan dutse sai ta fara sa
hannunta gaba daya ta dafashi.
Ai kuwa kafin ma ta tura dutscn sai dutscn ya
mirgina da kansa sau uku ya bar bakin kogon sai ga kofa
Zururu izuwa cikin kogon ta baiyana.
Nima kuma AA Misau ganin wannan hanya zururu yasa zan dakata anan sai wani lokaci kuma idan Allah ya kaimu
Singn
Admin AA Misau ke Magana
BUSA A MUTU
Littafi Na Shida (6)
Part C
Na Abdulaziz Sani M Gini
Typing
AA Misau ke Magana
(Rashin Sakin Litattafan da muke kawo muku akan lokaci daga gareku ne domin muddin zaku dinga nuna kuna so a cigaba ta hanyar LIKES & COMMENTS bamuki kullum mu kawo muku cigaban ba)
Labari ya isowa Shagala cewa
Marubucin yaci gaba da cewa....
saboda tsananin mamaki Ginbrya Suzaila ba ta san
sa'adda ta bude baki ba kuma ta durkusa kusa bisa
guiwoyinta tana juyowa tana kallon wannan dattjo kyma
tana kallon kofar kogon dutsen wanda aka rataye fitilun
itatun wuta a cikinsa saboda duhunsa.
Suma su Sarkin yaki sai suka cika da tsananin
mamaki gaba dayansu. Nan take Jarurnin dattijon ya
Wuce gaba izuwa cikín kogon dutsen , sai Gimbiya
Suzaila ta bishí a baya sannan Sarkin yaki sai kuma
Hasnalu da Lushaira.
. Sai da suka yí doguwar tafiya a cikin kogon dutsen
basu hadu da komai ba kuma basu ga kowa ba amma
duk inda suka wuce suna ganin fitilun itatuwan wuta a
rataye a saman dutse.
Kwatsam! Ba zato ba tsammaní sai suka iso wani
babban fili a cikin kogon dutsen inda suka yí arba da
waní katon keji.
A cikin kejin akwai tagwaycn Sadaukai Shalaru da
Halaru da kuma kuyangar su Gimbiya Lushaira su uku
kacal
A gefe daya kuma gawarwaki ne na mutane
dubunnai ba adadi wata kan wata sn yi tsiri, wadansu
gawarwakin ma har sun rube, wari da doyi ya cika
kogon dutsen gaba daya.
Ba shiri su jaruma Suzaila suka toshe hancinsu da
rigunansu.
Su kuwa su Shalaru saboda warin gawar da ya cika
musu ciki ma tuni sun kama amai sun galabaita ainun har
suna kokarin sumewa.
Koda isowar su Jarumin tsoho daf da kejin da su
Shalaru ke ciki sai wani irin haske na musamman ya
baiyana ya haskake kogon gaba daya yadda ko allura ce
ta fadi a wajen za a iya ganinta.
Faruwar hakan ke da wuya kuma sai suka ji wani
irin gurnani mai matukar ban tsoro ya cika Dodon
kunnensu. Kafin wani daga cikinsu ya yi wani yunkuri
sai kawai suka ga wani gabjejen Dodo ya fito daga cikin
wani sako na kogon.
Girman wannan Dodo ya ninka girman Sarki
Labarazu sau bakwai.
Kai inda za a yanke kansa a ajiye shi a kasa da sai
yafi wannan dutse na kofar shigowa kogon girma da
nauyi.
Dodon yana da wawakcken baki tamkar rijiva
hakar mutanen da.
Wadansu irin manyan hakora ne da shi masu fika
kuma a wargatse suke ba kyan gani wadanda koda karfe
suka tauna sai sun ruburbusheshi. Girman idonsa guda
daya ya kai na katon tulun debo ruwa a rafi.
Lokacin da Dodon ya yi arba da su Gimbiya
Suzaila ncsa kadan da inda sukc sai ya takarkare ya
kwarara uban ihu har tartsatsin wuta ya rinka zuba daga
bakinsa ya haddasa karamar gobara a cikin kogon
dutsen, sautin ihun kuwa ya sa dutsen kogon ya kama
Sagewa, duwatsu suka rinka fadowa kasa suna fashewa.
Al'amarin da yasa kowa va firgita ke nan suka
dimauce amma banda Jarumin tsohon nan.
Ita kanta jaruma Suzaila ba ta san sa'adda ta koma
bayan Jarumin tsohon ba ta rakabe
Su Sarkin yaki kuwa rugawa suka yi da baya suna
neman ficewa daga cikin kogon.
Koda Jarumin tsohon ya ga wannan Dodo ya
durfafosu sai shima ya ruga gareshi da gudu yana mai
karanta wata addu'a a cikin zuciyarsa yana mai rike da
wannan sanda ta hannunsa wacce yake dogarawa ya yın
da yake tafiya.
Ai kuwa suna zuwa daf da juna sai Dodon ya kawo
masa wawan mangari da hannu daya.
Cikin bakin zafin nama ya gocewa mangarin.
Koda hannun Dodon ya bugi dutscn kogon sai inda
ya buga din ya rugurguje ya zube kasa.
Nan fa Dodon ya ci gaba da kaiwa tsohon mangari,
bugu da taku da hannayensa da kafafunsa, shi kuma ya
rinka gocewa cikin tsananin zafin nama yana tsalle Isalle
da shawagi akan sassan jikin Dodon yana dukansa da
wannan sanda ta hannunsa.
Duk inda ya doka a jikin Dodon sai ka ga wajen ya
dare jini na zuba tamkar da takobi ya sareshi sai dai kaji
Dodon ya kurma ihu amma saboda na ci, taurin rai. da
Karfin Allah Ya isa Dodon ya ki faduwa kasa sai daima
Al Amin Ahmed Misau
AA Misau ke Magana
ka ga ya dada haukacewa da kara, kaimi wajen kokarin
hallaka tsohon.
Sai da suka shafe sa'a biyu da rabi suna wannan
bakın gumurzu ya zamana cewa jikin Dodon yai fata-fata
da jini amma tsohon ya kasa kasheshi.
Ana cikin hakane tsohon ya fusata ainun ya daka
wawan tsalle sama ya shallake tsohon Dodon gaba daya
yana mai kwalla kabbara da karfi ya kwadawa Dodon
sanda a tsakiyar kansa.
Take kan Dodon ya 6are gida biyu tamkar an
bare gyada sai ga kwakwalwarsa tayi fallatsi ta
kwararo kasa.
Nan take Dodon ya sulale kasa ji kake tim!
Kamar giwa ta fadi.
Cikin tsananin farin ciki su Sarkin yaki suka ruga
suka 6alle wannan keji suka fito da su Jarumi Salaru.
A dia-dai wannan lokaci ne kogon dutsen gaba
daya ya kama girgiza ya ci gaba da rushewa yana
faduwa kasa.
Da kyar da sidin goshi suka samu suka fiice daga
cikin kogon dutsen ba tare da dayansu ya hallaka ba
ko ya raunana.
Suna gama fitowa daga cikin kogon ya baje gaba
daya ya nuke izuwa cikin karkashin kasa tamkar bai
taba wanzuwa ba a wajen.
Kamar a mafarki sai su Gimbiya Suzaila suka yi
arba da sauran 'yan uwansu da suka baro a cikin
Kauyen nan tsaitsaye a gabansu cikin koshin lafiya
kuma suna tare da wadansu tsirarun mutanan kauyen
maza da mata yara da tsofaffi wasunsu da yawa sun
sami raunika sakamakon wannan girgizar kasa da aka
yi musu.
Nan fa su jaruma Suzaila suka ske kamuwa da
matukar farin ciki.
Bayan kowa ya nutsu sai wannan Jarumin tsohon
ya dubi wadannan mutanen kauyeya ce "Ya ku
jama'ar wannan gari kun sani cewa shekara da shekaru
Sarkinku Labarazu yana zaluntarku yana yi muku
mulkin murdiya da danniya..
Ya debi iyayenku, 'ya'yanku, yayyenku da
kannanku ya bayar da jininsu ga Dodon da yakc
bautawa a matsayin Ubangijinsa. Yau gashi rana daya
na kashe wannan Sarki naku kuma na kashc Ubangijin nasa
Wannan ita ce shaidar cewa Sarkinku yana kan
addinin karya kuma yana bautawa Ubangijin da bai
cancanta a bauta masa ba tunda ya kasa kare kansa
daga mutuwa.
Ku saní cewa babu wani Ubangiji da ya cancanci
a bautawa facc Ubangijin Musulunci wanda Ya halicci
sammai da kassai da duk abinda ke cikinsu. Shi ne
Ubangijin da Ya bani karfi da sa'ar har na kashe
Sarkinku da abin bautarsa.
Shi ne Ubangijin da nake bautawa dare da rana.
Shin yanzu za ku bayar da gaskiya ga Ubangijin
Musulunci?"
Koda jin wannan tambaya sai gaba dayan
wadannan mutancn kauye suka hada baki suka ce mun
bayar da gaskiya ga Ubangijin Musulunci".
Cikin tsananin farinciki tsohon ya biyawa
mutanen kauyen kalmar shahada suka maimaita
sannan ya dubesu ya ce, "Yanzu zamu koma izuwa
tsobon kauyen naku mu sake rayashi.
Ma'ana mu sake gina gidajenku, kuma zan zauna
tare da ku har izuwa tsawon dan lokaci domin na
koyar da ku yadda ake bautar Ubangijina, "
Koda gama fadin hakan sai tsohon ya juya kuma
ya fuskanci su Gimbiya Suzaila ya ce, "Ya ku
wadannan baki shin kuma ba za ku bada gaskiya ga
Ubangijina ba tunda kun ga karfin Sa da ikonSa da
idanunku?"
Har Suzaila ta budi baki za ta ce wani abu sai
Lushaira ta tari numfashinta ta dubi tsohon ta ce,
Tabbas zamu iya karbar addininka yanzu take anan,
amma sai idan ka bani amsar tanbayar da zan yi maka
yanzu"
Koda jin wannan batu sai tsohon yadubi
Lushaira cikin mamaki ya ce, "Ke kuwa wacce irin
tambaya ce haka kike son a ki yi mini?"
Lushaira ta dubeshi cikin nutsuwa ta ce, "Ina son
ka dubi girman UbangijiniKa ka fada mini iyakar
gaskiya bisa abinda zan tambayeka.
Shin wanann kamanni da kake ciki a yanzu shi ne
kamanninka na gaskiya?
Me ka sani dangane da wani Almajiri wanda
muka hadu da shi a baya cikin wannan tafiya tamu
wanda ya zo mana a jigace cikin yunwa da kishirwa
har na taimakeshi, shi kuma ya bani labarin dokokin
da zamu kiyaye idan muka shigo wannan gari na Sarki
Labarazu?"
Lokacin da Jarumin tsohon yaji wadannan
tambayoyi guda biyu sai jikinsa ya yi sanyi ya sunkui
da kansa kas yana mai ajIyar zuciya sanann sai kawai
ya karanta wata addu'a ya tofa akan tafin hannaycnsa
biyu ya sha fa akan fuskarsa.
Nan take kamanninsa ya juye izuwa kyakkyawan
saurayi ma'abocin haiba da kwarjini.
Nan fa kowa ya kamu da tsananin mamaki aka
bude baki ana kallonsa. Ita kuwa Gimbiya Suzaila
yanke jiki tayi ta fadi kasa surmanmiya sai da aka
Zuba ma ta ruwa sannan ta farfado.
AA Misau ke Magana
Koda ta bude idanunta tayi arba da saurayin sai ta kura
kawai.
idanu.masa tana murmushi
A sannar ne dattijon ya dubi Lushaira ya ce, "Sunana
Jaruni lMRAN BIN HUZEIR.
Na kasance ma'abocin addinin Musulunci wanda
ya sallama rayuwarsa akan tafarkin yada addinin
Allah. Kaso tamanin na rayuwata ina gudanar da ita ne
a cikin daji don yin bautar Allah da kuma yin sana'ar
farauta.
Bani da wani abinci face dan itaciya. Bana shiga
cikin gari sai a lokacin sanyi ko zafi da damina. Babu
abinda na tsana sama da zalunći kuma bana taimakon
mutum face na jarrabashi na ga yana da gaskiya,
amana da jin kai'".
Imran ya dubi su Gimbiya Suzaila gaba dayansu
daya bayan daya, sannan ya ce, "Ya ku wadannan
matafiya ku yi sani cewa na taimakcku ne albarkacin
wannan yar uwa taku wacce ta taimakeni sa'ada na zo
gareku a galabaice.
In ba don ta tainakeni ba da ko kadan ba zan ceci
rayuwarku ba daga sharrin Sarki Labarazu da
Dodonsa.
Na kan batar da kamannina ta hanyar rokon
Ubangijina domin na shiga cikin mutane a kaskance
na jarraba halaycnsu. Ina mai sanar da ku cewa tun
kafin na hadu da ku Ubangijina Ya sanar da ni cewa
kun fito nemana ruwa
ruwa a jallo, ba don komai ba sai
domin na yi muku jagora izuwa dajin Kirzuta na
Kawar muku da Jarumi mai Gahon BUSA A MUTU.
Shin abinda na fada gaskiya ne?"
Cikin hanzari su jaruma Suzaila suka hada baki
suka ce, "Wannan gaskiya ne".
Jarumi Imras ya yi murmushi ya ce, "Tabbas na
amince zan yi muku jagora izuwa dajin Kirzufa amma
bisa sharadi biyu.
Sharadi na farko shi ne. za ku karbi addinina
gaba dayanku bayan na kama MURAISU DAN
MURAISU mai kahon BUSA A MUTU na dajin
KIRZUFA.
Sharadi na biyu kuma shi ne, ba zamu tafi izuwa
dajin Kirzufa ba sai bayan mun zauna da mutanen
wannan kauye tsawon kwana arba'in na koyar da su
yadda ake bautar Ubangijin Musulunci'.
Sa'adda Jarumi Imran yazo nan a zancensa sai
jikin su Gimbiya Suzaila yai sanyi suka shiga kallon
junansu aka rasa wanda zai ce kala.
Daga can sai jarụma ta dubi Jarumi Imran cikin
murmushi da wani irin kallo mai nuna tsantsar SO ta
ce, "Ya kai sadaukin Sadaukai, ka yi sani cewa kazo
mana da babban al'amari wanda ba zamu iya yanke
hukunci akansa ba kai tsaye don haka lallai muna da
bukatar đan lokaci da zamu yi shawara
saboda haka yanzu zamu zauna tare da kai a cikin
kauyen wadannan mutane na marigayi Sarki Labarazu.
Lallai kafin cikar kwanakin da za ka yi tare da su
muma zamu gama shawara mu sanar da kai hukuncin
da muka yanke."
Koda Gimbiya Suzaila tazo nan a zancenta sai
Jarumi Imran ya yi murmushi ya ce, "Shi ke nan ai
rana bata karya sai dai uwar 'ya taji kunya.
Yanzu sai ku zo mu koma da baya izuwa kauyen
wadannan mutane ."
Koda gama fadin hakan sai Jarumi Imran ya juya
da baya ya kama tafiya, take ragowar mutanen wannan
kauye suka bishi a baya duu!Tamkar kaza da
'ya'yanta, suka durfafi hanyar da za ta mayar da su
izuwa wannan rusasshen kauyce
Kawai sai Suzaila ta dubi su Sarkin yaki ta ce,
"Ai bamu da wani zabi wanda yafi mu bi bayan
mutancn wannan kauyc."
Babban abinda yafi daga musu hankali a yanzu
shi nc, sun san cewa sun rasa gaba dayan guzurinsu da
kayayyakin su wadanda suka nutse a cikin karkashin
kasa. Hatta dawakansu na hawa yanzu babu bare su ci
gaba da tafiya izuwa dajin Kirzufa cikin kwanciyar
hankali.
Wannan shi ne abinda ya faru ga su jaruma
Suzaila bayan sun dace sun hadu da Jarumi lmras,
Jarumin da suka fito nema ruwa a jallo.
AA Misau ke Magana
A CAN Birnin Lairuf kuwa, tunda aka tura su
jaruma Suzaila ncman Jarumi Imran, Sarki Imras bai
koma kasarsa ba kuma kullum yana cikin bincike a
cikin hallarar tsafi domin ya gano yadda karshen
tafiyar su Suzaila zai kasance walau akwai sa'a ko
rashinta.
Wata rana da rana tsaka Sarki Huraisu na zaune a
turakarsa tare da mahaifiyar Suzaila suna cin abinci
cikin nishadi sai kawai ya ga ta daina cin abincin ta
sunkui da kanta kas tana tunani.
Daga can sai idanunta suka ciko da kwallah har
hawaye ya zubo ma ta.
Al'amarin da ya dugunzuma hankalin Sarki
Huraisu ke nan ya dubcta cikin tsananin damuwa ya
ce, "Ya ke matata ina dalilin zubar wannan hawaye
naki?"
Koda jin wannan tambaya sai Sabirat ta dago kai
ta dubeshi ta ce, "Ya kai mijina ka yi sani cewa tun
daga ranar da 'yarmu Suzaila ta yi wannan tafiya
kullum sai na yi wani mugun mafarki a cikin barcina.
Abinda nake gani shi ne, mumnunan yaki ya
barke a tsakanin Birnin nan namu an kashe mutane
babu adadi, jini ya malala a ko ina ba kyan gani kuma
a gaban idanun 'yar tamu, wani Jarumin saurayi yake
sa takobinsa ya sare maka kai ba tar da ta ceci
rayuwarka ba."
Kafin Sabirat ta gama rufe bakinta tuni Sarki
Huraisu ya zabga ma ta mari.
Nan take bakinta ya fashe har jini ya fito, ta
zubawa Sarki Huraisu idanu kawai tana mamaki da
takaicin yadda yasa hannu ya mareta.
Cikin tsananin fishi Sarki Huraisu ya mikc tsaye
zumbur ya dakawa Sabirat tsawa yana mai cewa,
"Wannan mafarki na kì karya ne, har abada ba zai taba
faruwa ba.
Ni murucin kan dutse ne ban fito ba sai da na
shirya. Babu wani makiyina wanda ya isa ya sami
nasaraa kaina "
Koda Sarki Huraisu yazo nan a zancensa sai yaji
Sabirat ta bushe da dariya. Al'amarin da yai matukar
girgizashi ke nan ya zuba ma ta idanu kawai ya fara
zargin ko ta sami tabin hankali ne.
Daga can kuma sai ya ga ta murtuke fuskarta ta
dubeshi a fusace ta ce, "Ya kai mijina ka yi sani cewa
tun da ka kashe đan uwanka Muraisu ka kar6i karagar
mulki kake zalunci a Birnin nan naka.
Babu mai jin dadi a kasar nan face wanda ya
kasance azzalumi irinka kuma mai biyayya a gareka
Topa Nima kuma AA Misau zance sai wani jikon
Zamu dakata anan saikuma wani lokaci zamu cigaba
Admin
AA Misau ke Magana
Whatsp group
https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q
Facebook Fage
https://www.facebook.com/profile.php?id=100063661782295
Facebook page
https://www.facebook.com/AlaminGuyson?mibextid=3amO3DAFELuS4Abp
SaikunzoBUSA A MUTU 💕
Littafi Na Shida (6)🩸
Part D. 💎
Na Abdulaziz Sani M Gini 🤴
Typing
AA Misau ke Magana
✍️⭐⭐⭐
Labari ya isowa Shagala cewa
Marubucin yaci gaba da cewa....
(Kamar Yadda Mukayi Korafi Kan Kuna Son Litattafan Da Muke Dorawa Amma Bakwa Nuna Kuna So A Yanzu Nake Ga Kamar Kun Gyara Ta Hanyar Maida Hankali Akan Giya Mana Baya SABODA HAKA idan yau kun Samar mana da LIKES SOSAI gobe Ma Zamu Dora Cigabansa) 🥰
WANDA YA
KASANCE AZZALUMI IRINKA KUMA MAI BIYAYYA A GAREKA
sai da Gimbiya Suzaila ta girma ta tas0 da
gagarumar Jarumtaka sai mutane suka fara samun
Saukın zaluncinka domin sau da yawa ita ce take matsa
maka kake yiwa talakawanka adalci. yanzu
Gimbiya Suzaila bata nan ka dawo da mulkinka na
zalunci da cutar da talakawa.
To ka sani cewa mulki da zalunci baya dorewa,
komai daren dadđewa sai ka rasa wannan matsayı naka.
Bisa wannan dalili ne naji na yi imani da wannan
mugun mafarki

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment