Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hakan sai ya dauki ice daya daga cikin kiraren nan daya kunna wuta sannan ya nannadeshi da yankin nan na damararsa ya cinna wuta ya rikeshi a matsayin fitila dazata. Haska musu hanya ka wai sai ya nausa daji take dabira ta bishi a baya da sauri, sai da suka shafe kusan rabin sa'a suna neman ruwa basu samu ba sannan suka riski wata korama wacce ruwanta ke zubowa ta kan saman wadansu duwatsu. Ruwane garai-garai har wani irin kamshi yake mai dadi.
Cikin matukar farinciki Dabira da Uhaisu suka ruga izuwa bakin kooramar suka tsugunna suka sha sannan suka dawo gefe suka zauna.
A sannan ne wata irin iska mai tsananin sanyi ta fara kadawa wacce tasa jikinsu ya kama karkarwa kawai sai dabira ta dubi sarki Uhaisu a fusace tace, "Ya za a yi ka baroni da gidanmu inda na saba kwanciya a cikin daki kuma akan shimfida mai taushi kakawoni nan cikin daji inda sanyi ma zai iya lahantani?
Hakika ka zalunceni kuma ka cutar da ni. Haka ake yin SOYaYYA ka cutar da masoyinka?"
Koda jin wannan batu sai hankalin sarki Uhaisu ya dugunzuma ainun ya dubi dabira cikin alamun tsananin da muwa yace, "KI gafarceni ya masoyiyata yanzun nan zan magance miki wannan sanyi da ya dameki".
Yana gama fadin hakan ya mike tsaye yaje ya kama saran bishiya sai da ya karyo rassa dogaye da masu kauri da yawa sannan yazo ya shiga aikin gina daki. Har ya kammala ginin dakin da itatuwa ya lullubeshi da ganye Dabira na zaune tana kallonsa kawai tana mamaki.
A zuciyarta tana cewa, "yanzu kawai saboda ya kamu da soyayya yake ta wahala yake ta wahalar da kansa haka? Lallai kuwa ashe gaskiyar masu iya magana da suka ce "SOYAYYA dafice wacce in ta shiga jikin mutum bata fita har ajali"
Bayan sarki Uhaisu ya gama gina dakin ice har da kofarsa ta shiga sai kuma yaje ya nemo ganyaye masu fadi da taushi yazo ya yiwa Dabira shinfida dasu a cikin dakin sannan yace ta shiga cikin dakin ta kwanta shi zai tsaya. A waje yayi gadin ta don kada wata dabbar daji tazo ta cutar da ita".
Ba tare da gardamar komai ba kuwa dabira ta shiga cikin dakin ta turo kofa ta rufe tayi kwanciyarta ba tare da ta sake jin wani sanyi ba. A sannan ne fa taji tausayin sarki Uhaisu ya kamata domin ta san cewa ba karamar wuya zai shaba idan ya kwana a filin allah cikin wannan tsananin sanyin.
Saukinsa daya ya hura wuta wacce zai rinka jin dumi, kuma koda wutar barci dai bazai yiwuba a wajensa kuma wannan sanyin zai iya cutar dashi.dabira taji kamar ta tashi ta bude masa dakin tace ya shigo amma data tuna cewa abune mai hadarin gaske a addinance ta kwanta da. Wani da namiji a cikin dakin sai ta fasa.
A suba nayi Dabira ta farka daga barci ta bude dakin ta fito waje domin tayi alwala. Tana fitowa taga sarki Uhaisu zaune a gaban wuta yana jin dumi amma jikinsa na ta karkarwar dari kuma idanunsa sunyi jawur sakamakon rashin samun barci.
Nan take taji tausayinsa amma sai ta murtuke fuska ta kau da kai ga barin kallonsa taje bakin wannan korama ta tsugunna tayi alwala sannan ta mike tsaye ta fuskanci alkibla ta tayar da sallah.
Bayan ta idar da sallar ne ta shiga yin addu'o'I bata gushe ba tana yin addu'o'in har sai da alfijir ya keto gari ya fara haske sannan ta shafa addu'ar ta waigo ta dubi sarki Uhaisu tace, "Menene abin yi yanzu?
Zaka nemo mini abincin kalaci ne ko kuma zamu ci gaba da tafiya ne?"
Uhaisu ya dubeta cikin alamun damuwa yace, "Ki gafarceni ya masoyiyata bai kamata mu tsaya yin kalaciba anan domin ina zargin cewa mutanenku sun biyo sawummu, gwara mu kara gaba muyi nisa tukunna sai mu yada zango na nemo mana abincin kalaci".
Ba tare da gardamar komaiba Dabira tace, "Na amince da hakan".
Nan take suka hada nasu-inasu suka bar wannan daji suka kara gaba.
Babban kuskuren da sarki Uhaisu yayi shine da bai rushe wannan daki daya gina ba kuma bai batar da ragowar wutar daya kunna ba domin sun zamo alama ta cewar suna cikin wannan daji shida gimbiya Dabira.
Wannan shine abinda ya faru tsakanin sarki Uhaisu da gimbiya Dabira bayan ya satota daga gidan sarutar sarki Raihan a matsayin masoyiyarsa Jaruma YAZILA wacce ya kamu da tsananin kaunarta kuma yake son ta zamo abokiyar rayuwarsa ta har abada.
BASH I TKRW
08105808371{ BAKIN ARTABU TYPE C }
Tambayarki ta farko akan addini ce. Kana so
kasan dalilin dayasa bamu da addini?
Tambayarka ta biyu kuwa itace kana so ka san
dalilin da yasa naki yin aure, kuma kaima ban
taba nuna maka ina da ra'ayin kayi aure ba?
Kasaurara da kyau kaji amsar wadannan
tambayoyi naka kuma kayi amfani da basirarka
wajen amfani dasu domin idan baka nutsuba har
abada bazaka sami daraja da daukaka ba irin
wadanda na samu a rayuwata.
Dalilin dayasa bamu da addini shine, mahaifina
kafin yarasu nayi masa irin wannan tambaya,
domin yadda ka taso babu addini. Kuma babu
aure haka nataso amsar da yabani itace.
"Ya kai dana kayi tunani yanzu addinai sun yi
yawa a cikin wannan duniya, akwai masu bautar
rana, wata, ruwa, wuta, gumaka, dabbobi da
sauransu. Kai wasu ma aljanu suke bautawa.
Mahaifina yaga yamin cewa addini guda daya ne,
kuma ubangiji daya ne wanda shine na gaskiya
mai ikon komai da kowa.
A wannan zamani babu wannan addini kuma
kaima zaka riski wannan addininne a karshen
rayuwarka, abu ne mawuyaci kasan wannan
addini amma wata kila in ka sami haihuwa danka
yasan wannan addini.
To ka gaya masa cewa duk ranar da wani
gagarumin yaki ya taso ya halarceshi domin a
wannan tafarki ne zai san wannan addini na
gaskiya har ya fahimceshi kuma ya aminta da shi
"
Sa'adda mahaifina yazo nan azancensa sai na
cika da mamaki na dubeshi nace, "ya kai abbana
ashe baka gaya min cewa yaki ba zai taba zuwa
birnin tashwar ba? Ya kuma yanzu kake mini
batun yaki ?"
Koda jin haka sai mahaifina yaja numfashi
tamkar ransa zai fita, a sannan yace, "bana nufin
yaki zai zo har nan ya riskeka, ina nufin za'a
aikomaka da sakon gayyata. Lallai ka amsa
gayyatar, amma kafita yakin kai kadai, kada ka
kuskura ta tafi da kowa idan har kana son kasan
addinin gaskiya.
Dangane da tambaya ta biyu dake ranka kuwa ba
wani abubane face batun aure. Tun da
mahaifiyarka ta rasu ban sake yunkurin aureba.
Haka mahaifina ya kasance, shima mahaifina
haka rayuwarrsa ta wanzu har izuwa kan
kakanmu na arba'in da daya.
Abinda nake nufi anan shine duk wanda yai aure
acikinmu haihuwa daya yake samu kuma sai
matarsa ta mutu, shima sai yamutu yabar abinda
ya haifa.
Lokacinda aka haifeka sai naji babu abinda nake
so a duniya sama da kai, kuma naji ina son kayi
nisan kwana a duniya.
A cikin gidan sarautar nan akwai wani daki guda
daya wanda ba'a shigarshi kuma kai ma baka
taba ganin an shigeshi ba, haka ne?"
Kodajin wannan tambaya sai na jinjina kaina
nace, tabbas na san da wannan daki kuma na
dade ina mamaki da tunani akansa."
Mahaifina ya sake ajiyar zuciya yace, "Akwai wani
aljani bawanmu a cikin wannan daki wanda bama
bauta masa shima kuma baya bauta mana, amma
zaman amana ne da kauna tsakanin zuri'armu da
tasa. Duk abinda zai samemu a rayuwa shi
wannan aljani ne ke sanar damu. A iya tsawon
rayuwata ta duniya sau daya na taba. Ganawa da
wannan aljani kuma shine ya gaya mini cewa
kada na kuskura na kara yin aure a rayuwata.
Idan kuwa nayi sai an kawo harin yaki izuwa
kasata an kawar dani. Yakai dana kaima kayi
amfani da wannan nasiha wacce wannan aljani
yayi mini kuma kada ka kuskura ka shiga dakin
da wannan aljani yake domin ku gana sai ranar
daza ka fita wannan gagarumin yaki da aka
gaiyaceka. "
Har kullum sarki Uhaisu baya mancewa da
wannan jawabi na mahaifinsa don haka sai ya
hakura da batun aure gaba daya a rayuwarsa
saboda yana son yayi nisan kwana a cikin daular
mulki daya tsinci kansa a ciki.
A ranar da wasikar gaiyata izuwa yaki ta riski
sarki Uhaisu daga birnin kisra sai yacika da
tsananin farin ciki domin yasan cewa lokacine
yazo da zai cika babban burinsa na duniya domin
yasan mahaifinsa ya gaya masa cewa bayan anyi
wannan gagarumin yakinne zai iyayin aure har ya
sami magaji kuma lallai zai yi tsawon rai a
duniya.
Lokacin da maga-takarda ya gama karanta
wasikar gayyata a fadar sarki Uhaisu fadawansa
suka ga ya cika da farin ciki sai mamaki ya
kamasu domin su a saninsu babu sarki ya tsana
sama da yaki kuma babu abinda yafi so sama da
zaman lafiya.
Sarki Uhaisu ya kasance mutum mai adalci,
tausayi da jin kai, gashi da karrama mutane, wato
bai iya wulakanci ba bashi da izza da jin kai irin
na sarakai, duk da cewa allah ya bashi karfi,
kyawu da dukiya mai yawan gaske.
Bisa wannan baiwa da allah ya baiwa sarki
Uhaisune ya zama cewa 'yan mata, 'ya'yan
sarakai, attajirai da manyann matsafa suka kamu
da tsananin kaunarsa, wasu da yawansu a dalilin
kamuwa da sonsa ne ma suka kamu da cututtuka
saboda rashin samun kaunarsa. Wasu ma
sanadin ajalinsu kenan.
A duk sa'adda sarki uhaisu ya ci ado kuma yayi
hawa ya fito daga cikin gidansa sai dai kaga
mata suna fitowa da gudu domin kawai su
ganshi. Idan dakaru suna hanasu zuwa kusa
dashi sai kaga suna kuka kamar wadanda
akayiwa mutuwa.
Duk wacce ta sami nasarar koda taba dikin sa
ma kuwa sai kaga sauran mata na rungumeta
don su sami albarkaci. Idan kuwa maca tasami
nasarar koda taba hannun sarki Uhaisu ne sai dai
kaga ta yanke jiki ta fadi sumammiya saboda
tsananin farinciki.
Daga wannan rana kuwa mata sun dinga kai
mata ziyara kenan suna bata kyaututtuka ba
adadi.
Hakika a tarihin nashiyar kasar tashawar ba a
taba samun saurayi mai farin jini ba a wajen
mata kamar sarki Uhaisu, kuma labarinsa ya bazu
ko ina, har zuwa ake yi daga kasashe daban-
daban domin kawai aganshi.
Tabbas duk mutumin da yake shakka akansa da
zarar yazo ya ganshi dole yake gasgatawa.
Komai hassadar mutun da kushensa idan yayi
arba da sarki Uhaisu take yake sallamawa.
Sukansu maroka idan sarki Uhaisu ya fito suka
fara yi masa kirari sai masu rasa irin kalmomin
dazasu rinka fada wadanda suka dace da shi
akwai wani maroki wanda yafi kowa iya kodashi,
shine ya kance dashi:
Kaico! Ina gwanin wani ganawa? Ga saurayi uban
samari tauraron kyawawa mai magance yunwa
da kishirwar yan mata.
Gaka jarumi. Sarki sadauki mai ragargazar maza
yau fa ga mai tekun zinare mai shanye kogunan
attajirai. Ga ruwan sanyi mai sanyaya zuciya
talakawa kufara nan ga bargon kankara mai
kashe gobara daga kogi. Marhaban da babbar
gona nomanta sai shekara dubu ! Aduk sa adda
marokin ya haukace ya kama sambatu saboda
sai da dinare ya rufeshi ruf tamkar an nutsar da
shi a cikin yashi tun yana kirari. Ya koma yin
waka sannan ya fashe da kuka ya dinga mari da
cizon kansa har sai da aka tattarashi shi da
dukiyar daya samu aka kaisu gidansa lokacin da
sarki uhaisu yaga fadawansa sun cikada mamaki
bisa ganin yadda ya kamu da farin ciki don jin
sakon gaiyata izuwa yaki. Kuma ya fahim cewa
hankalinsu ya dugunzuma ainun sai ya dubesu
yayi murmushi sannan yace. ” Yaku yan majalista
ku kwantar da hankalinku. Ku sani cewa wannan
yaki bai shafi kowa ba awannan kasa tawa face
nikadai. Don haka nikadai zan shirya na tafi
wannan yaki. ”
Koda jin wannan batu sai mamaki da fargaba
suka dada kama yan majalistar wazirin sarki
uhaisu wanda ake mazwan ya dubishi cikin
tsananin damuwa yace. ” Haba ya shugaban
kasani cewa mu da sauran talakawanka muna.
Matukar kaunarka kuma tunda ka hau kan
karagar mulki bamu taba rabuwa da kaiba dai-dai
da rana daya.
Mun tabbatar da cewa idan babu kai babu wanda
zai iya yi mana mulki acikin adalci irin naka.
Tayaya kake tsammanin zamu iya barinka ka tafi
yaki kai kadai ? Katuna fa cewa baka da mai
gadonka bare idan muka rasaka musami
halifanka?"
Lokacin da waziri yazo nan a jawabinsa sai sarki
Uhaisu ya mike daga kan karagarsa yayi tafiya
izuwa tsakiyar fadar sannan ya tsaya ya dubi
jama'a gabas da yamma, kudu da arewa, kawai
sai hawaye ya zubomasa ya ce, "ya ku jama'ar
birnin tashwar kuyi sani cewa a iya rayuwata ta
duniya babu abinda nake kishinsa kuma nake
matukar kaunarsa sama da birnina da jama'ata.
Yau shekara a shirin da takwas a duniya amma
ban taba zuwa yakiba.
Duk wannan daukaka da ni'ima wacce nake da ita
a duniya bata gani ba sai jitake yi kawai.
Yau gashi dama tazo wacce za a sanni. Bugu da
kari. Ina mai sanar daku cewa wannan yaki da
zan fita ne zan cika babban burina na duniya
harna sami damar aure na sami wanda zai gajeni
yaci gaba da yi muku irin mulkin da nake muku
bayan babuni. "
Koda sarki UHAISU yazo nan a zancensa sai
fadar gaba daya ta rude da shewa, mutane suka
cika da farin ciki asannanne sarki Uhaisu ya
sallami kowa fadar ta watse nan labari ya bazu
ko ina a kasar cewa gobe sarki Uhaisu zai fita
yaki shi kadai kuma ga sakamakon da zai biyo
baya idan ya fita yakin.
Nan fa jama'a suka yi farin ciki da bakin ciki ba
face rabuwar daza a yi da sarki izuwa tsawon
kwanaki ko watanni ba a san ranar da wowarsa
ba. Haka kuma ba a san irin hadarin da sarki zai
gamu da shiba akan hanyarsa, babu tabbacin zai
iya tsira da rayuwar sa duk da an san irin
gagarumar jarumtakarsa amma kuma ai ba a taba
ganin kwazonsaba a filin yaki ba.
Dayawa daga cikin jama'ar gari kuwa basu yi
bacciba a wannan dare, musamman mata. Duk
gidan da kaje sai kaga ana koke-koke tamkar
mutuwa akayi.
Yayin da dare ya raba sai sarki Uhaisu ya shiga
cikin wannan daki na musamman wanda tunda
aka haifeshi bai taba shiga ba.
Kofar dakin a lullube take da yana gaba dayanta
alamar cewa an dade ba'a shigaba tsawon
shekara da shekaru.
Batare da fargabar komai ba sarki Uhaisu yasa
kwagirin sarauta ya share wannan yana sannan
yasa daya hannun nasa ya murza marikin kofar
dakin nan take kofar ta bude ya kunna kai ciki.
BASH I TKRW
08105808371{ BAKIN ARTABU»3 TYPE D }
Kasani cewa ni sunana Dabira, wacce ka kamu da tsananin sonta kuwa 'yar uwata ce gimbiya Yazila wacce da itane ka fafata yaki har ka kaita kasa da nufin ka hallakata amma sai hular karfe dake kanta ta cire kayi arba da fuskarta.
Na boye. Maka wannan sirri ne domin na jarrabaka na ga iyakar irin son da kake yiwa yar uwata, shiyasa nayi ta maka wulakanci iri-iri amma sai ka jure wulakancin ka ci gaba da nuna mini soyayya.
Tabbas ka cancanci ka auri 'yar uwta domin kaine irin namijin da kowacce 'ya mace ke fatansamu a rayuwarta. Baya ga wannan na auna halayenka gaba daya na gane cewa kai mutum ne mai hakuri, tausayi da amana kuma mai son gaskiya.
Bisa wannan daliline ma dakaga gaskiya a zahiri ka karbeta. Yanzu sai ka maimaita abin da zan karanta ma ka domin ka zama dan uwana musulmi. "
Nan take dabira ta biyawa sarki Uhaisu kalmar shahada shima ya maimaita.
*** *** ***
Koda su sarki daksur suka hango abin dake faruwa tsakanin sarki Uhaisu da dabira suka fahinci cewa addinin musulunci ya karba sai suka kamu da tsananin bakin ciki suka kama ihu har da kuka.
Kwatsam! Sai ga rundunar su sarki Raihan sun iso wajen a sukwane bisa dawakansu.
Koda. Hangosu sai dabira taruga garesu ta tsaida su kuma tayi musu albishir da cewat a halin yanzu fa sarki uhaisu ya karbi addinin musulunci.
Nan take farin ciki ya lullube sarki Raihan, yazila da Humaira suka sauko daga kan dawakansu suka rungume Dabira cikin tsananin murna bisa ganinta araye cikin koshin lafiya.
Nan take Dabira ta kama hannun jaruma Yazila taja ta takaita har gaban sarki Uhaisu ta dubeshi tace, "Wannan ita ce masoyiyarka ta kwarai wacce zuciyarka ta kamu da tsananin sonta".
Kawai sai yazila da Uhaisu suka kurawa juna idanu suna murmushi cikin farin ciki mara misaltuwa.
A dai-dai wannan lokaci ne sarki Raihan ma ya sauko daga kan dokinsa ya ruga wajen sarki Uhaisu. Yana riskarsa suka rungume juna.
Sarki Raihan ya kankame Uhaisu yana cewa, "Da ga yau kazama dan uwana na jini kuma na ba ka YAZILA"
Cikin tsananin murna sarki Uhaisu ya durkusa bisa gwuiwowinsa da nufin yayi godiya amma sai sarki Raihan ya kama kafadunsa ya tasoshi sama sannan ya dubeshi yace, "Yanzu ga abokan gabarmu can akofar birninka suna kuka da bakin ciki bisa karbar addininmu dakayi, yanzu wana irin hukunci kake ganin yakamata muyanke musu?".
Koda jin wannan tambaya sai sarki Uhaisu yayi murmushi yace, "kwantar da hankalinka ya kai sirikina kasani kura tasan gidan mai babban sanda, zabi biyu zanbasu yanzu, bani doki kagani"
Batare da gardamar komai ba sarki Raihan yasa akakawowa sarki Uhaisu wani ingarmar doki ya hau, ka wai sai ya zaburi dokin da gudu ya nufi kofar birninsa.
Saida ya rage bai fi tazarar kamu goma ba a tsakaninsa dasu sarki Daksur, kawai sai Uhaisu ya zare takobinsa sama ya daga murya yace, "Yaku wadannan sarakai kuyi sani cewa ni yanzu bana daga cikinku na karbi addininsu mai daraja wanda shine addinin gaskiya. Ina mai kira a gareku daku tuba ku daina bautar gumaka da aljanu kuzo ku rungumi addinin gaskiya, idan kuma kunki sai mu gwabza yakin karshe muda ku yanzu a ga wanda zai rinjayi wani.
Ni kam na tabbata da cewa ko yaushe gaskiya ce akan karya. "
Yana gama fadin hakan sai ya kada linzamin dokinsa ya juya da baya da gudu a sukwane ya koma can inda rundunar su sarki Raihan take ya juya yana kallon su sarki Daksur yana sauraron yaji hukuncin da suka yankewa kansu. Kawai sai sarki Daksur ya shiga cikin tsakiyar 'yan uwansa sarakai suka yi kus-kus suna gama tattaunawa ne suka zare makamansu suka sakarwa dawakansu linzami suka taho da gudun tsiya izuwa inda rundunar su sarki Raihan.
Koda ganin haka sai sarki Uhaisu ya daga takobinsa sama yana mai yiwa su sarki Raihan nuni da a tari abokan gaba. Nan take kowa ya zare takofinsa ya sakarwa dokinsa kaimi aka tari abokan gaba.
Musulmi suna kabbara, kafirai suna ihu aka hadu a tsakiya aka cakude. Nan fa aka ruguntsume da azababben yaki mai ban tsoro. Kura ta turnuke wajen gaba daya, ihun mazaje, haniniyar dawakai da karafkiyar karafa ta cika dodon kunne sai da rana ta fadi magariba ta doso kai ana ta yin wannan BAKIN ARTABU sannan aka karar da gaba dayan wadannan kafirai. Duk wanda ka duba a cikin musulmi sai kaga jikinsa ya rine gaba daya da jini, kuma kusan kowa ya sami rauni a jikinsa.
Tabbas allah ya Nuna ikonsa a wannan yaki tunda kafirai sun ninka musulman yawa sau kamar goma amma sai gashi musulman ne dai suka yi nasara.
Nan dai aka bude birnin, sarki Uhaisu ya yiwa su sarki raihan jagora suka shige ciki gaba daya.
Nan take. Wannan lokaci sarki Uhaisu ya kaddamar da ADDININ MUSULUNCI a birnin nasa kowa ya musulunta sannan aka yiwa mutane magani bisa raunikan jikinsu.
Kashe gari aka sake dunguma aka koma birnin misra inda acan ne aka daura auren sarki UHAISU da jaruma YAZILA ita kuma jaruma DABIRA ta auri wani sadaukin jarumi mai suna BASHER IBINI ISHAQ a she sun dade suna soyayya a boye batare da kowa ya saniba a garin.
Nan dai sarki Uhaisu yayi sallama gasu sarki raihan ya dauki amaryarsa JARUMA YAZILA ya tafi da ita izuwa birninsa cikin tsananin farin ciki.
Can birnin sarki Daksur kuwa da sauran biranen da aka ci sarakunansu da yaki duk sai da sarki Raihan ya taka da kafarsa tare da dumbin dakaru masu take masa baya suka je kowanne birni suka kafa tutar musulunci, kuma suka nada shugabanni masu adalci da tsoron ALLAH.
Har yau har gobe gaba dayan kasashen dake wannan nashiya sun zama birane na MUSULUNCI, kuma duk gumakan dake nahiyar sai da aka konesu gaba daya.
TAMMAT BIHAMBULLAH.
KARSHE.
Alhamdudila muna godiya ga allah madaukakin sarki da ya bani ikon kawo muku wannan littafi JARUMA YAZILA da cigabansa BAKIN ARTABU lafiya allah ya kara daukaka musulunci da musulmai.
TAMBAYA
ME KAFASHIMTA DANGANE DA WANNAN LITTAFIN?
Ga wanda bai sami karanta wannan littafin daga farko ba zai iya samun sa a wannan grp DUNIYAR LITTATTAFAI DA NISHADI tun daga jaruma yazila maza kuyi search din grp din sai kunzo
Naku a koda yaushe BASHEER ISHAQ TOKARAWA.
BASH I TKRW
08105808371
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment