Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta tashe su"

Tashi tayi tana kama dogon gashinta Mai shagen tsawo da cika ta daure a baya sai a lokacin ta fadawa inne abinda ya kawo ta

Sosai inne tayi Kuka Dan rayuwar nibras abin a tausaya mata ne tun a haihuwarta mahaifiyata ta rasu mahaifinta ya auri fatou domin ta raineta saidai ko kadan fatou Bata son nibras mugunta yau daban na gobe daba da yake Raye abin ya mafi sauki saboda yana sa musu Ido Amma tunda ya kwanta dama ta fidda mugun halinta a fili gashi Yan uwan mahaifinta sunki bari ta dawo guunta da zama bisa makircin fatou

Kallon nibras Dake Kuka tayi tace"yanzu ya zakiyi dan kin San halinta yanzu zata je ta kwaso min yan uwan mahaifinki Kuma kin San ba hankaline dasu ba tun ba kawunki mustafa ba kin San farkan fatou ne shiyasa take juyashi inda take so

. Ita dai kuka take nibras tace"ki taimakeni karki bari ayi min auren nan rabani da A'med zasuyi "

Inne ta zubawa A'med ido na wasu sakwani Saman ta maida kallonta kan nibras tace"ki fad'a min gaskiya Ina kika Sami wanan yaron?"


Cikin Kuka tace"ni ban tab'a Miki karya ba ranan dana tafi kauyen babana Ina dawowa na gan wani hatsari Wanda ya girgiza ni kin San inda hanya kauyen take ko hatsari akayi Babu Mai damuwa da hatsari saboda anguwa ne na yan ta'ada Nima har zan tafi sai naji kukan yaron nan na karasa na gan babu Wanda ya rayu cikinsu sai wanan yaron shine na daukesu na dawo dashi,shine fa ake ta zagina ana cewa ciki nayi
"Ta kare cikin kuka

Itadai inne Bata ce komai ba ta mike ta fita

Nibras ta rungume a'med da take jinsa har ranta yaron ma sai ya lafe jikinta

A haka inna ta kawo mata abinci me kama da gurasa ta fara ci tana hawaye

Kallonta inne tayi cikin nazari tace"ni ban San ya zanyi Dake ba yanzu kin San yan uwan mahaifinki inda suke nuna Iko a kanki kin fa San inda muka kare a wancan lokacin ni Kuma ban San kowa ba balle in turaki wani gari Kuma dole in suka gan baki nan nan bana zasu zo bana son damuwa gomma ki cinye abinci ki koma gida ga kudin mota

Cikin Kuka tace"karki min haka inne rayuwata zata lalace da ni kadai ne zan amince da auren baba Musa Amma rabani zaiyi da a'med kiyi wani Abu inne nifa jikar ki ce"ta kare magana cikin Kuka tana tura gurarsa Dan ji tayi Bata da energy cinsa

Shiru inne tayi tana kallonta cike da tausayawa tace"hanya daya ne shine in had'aki da aminiyata da take aiki a gidan sarki daga nan kila a sama Miki aiki a wani garin haka kadai shine maganin wanan matsifa da kike ciki"

Cikin farin ciki tace*na amince wallahi na amince"da wanan ta samu kwanciyar hankali ta mike ta Goya A'med ta fita ta fara aikin gida


----------

A lokacin da ma ta fargab ba nibras a gidan hankali ta ba karamin tashi yayi ba tayi ta hauka ta kira Yan uwan mahaifin nibras su ma suka Goya mata baya domin tana da Farka cikinsu shiyasa kome tayi dai-dai ne kawu mustafa na Goya mata baya

Kwana uku suna niman nibras Amma shiru

Yau ko da asuba baba Musa ya zo da wasu katti yasa aka dauke mata inji markad'a da tv tare da Bata tabbacin in har bayan kwana uku Bata biyasa kudinsa ba toh wallahi zata gan ba dai-dai ba

Wanan abin ya d'aga mata hankali sosai kamar wacce ta tuna wani Abu ta mike daga zaunen da take ta kira mustafa Wanda kanine ga tsohon mijinta Yana dagawa tace"ka zo da mashin muje gun kakar yariyar nan mu duba ta Kai na masan tana gidan meyasa banyi tunani tun farko ba*

Yace"gashi nan zuwa "
____________________

Kawu ne tare da abokinsa a babban falonsa Dake masarautar Sudan

Yarima Ahmed na kishingid'e a kujera Yana latse wayarsa kamar baya Jin hiransu

Kawu yace"nifa ban Saba zama wuri daya ba ka kaini mu zaga gari please

Aminin nasa Wanda Shima halinsu daya da kawun Kuma za a bashi sarauta ne nan da kwana uku shiyasa su kawu suka zo zai Kuma Kara aure ta hudu a ranan

Yace"toh mike muje nan bayan akwai gidan wata tsohowa da Nike zuwa the woman is great bari muje,but we are going in disguess bana son a gane ni

Kawu yace"Hakan ma zaifi ai "

Yarima Bashir yace"Kaifa bazaka ba"yatmusa fuska yarima Ahmed yayi yace"nahhhh sai kun dawo"

Kawu yace"ai ba zuwa zaiyi ba da fatan dai ana tuwon shinkafa a gari nan"fita sukayi yarima ya bisu da Kallo Yana girgiza Kai Yana mamakin hallayensu sai yanzu yake Dana sanin biyo kawu kasar nan....

Gidan inne driver yayi dasu straight tun daga Nisa suka tarar da tashin hankali domin kuwa Ma ce ke Jan nibrass a dole sai ta tafi da ita inne na Janta da goyon a'med dake tsala ihu kamar cire me Rai za ai

Shikuwa mustafa Yana gefe Yana ta zuba yare Yana zagin inne akan Bata isa ba ya' ta su ne sai inda sukayi da ita

Sosai nibras ke ihu Hakan ya Tara jama'a Amma Babu Wanda ya iya taimakonta

Pakawa driver gidan sarki yayi...kawu ya fito Kai ka ce shine d'an gari saidai duk inda ya so ya fahimci abinda ke faruwa rudewa yayi saboda yare suke Dan ma Yana ta tsinta wasu saboda larabci ne ma yake ta fahimta

Yarima Bashir ya karaso ya rungume hanun,but babu Wanda ya ganesa

Cikin izza ya koma mota ya zauna ya kira kawun nibras yaje,dukda be ganesa ba Amma yayiwa mustafa kwarjini

Tambayarshi yayi sai ya fara in Ina Hakan yasa ya tambayi nibras

Cikin Kuka nibras ta karasa ta fara fad'a me tana Kuka itama inne nayi

Kawu yace"ku fad'amin meke faruwa take Kuka haka"kawu na da tausayi baya son ya gan mutum a kunci

Cikin turanci yarima Bashir ya fad'a me

Kawu ya bisu da Kallo yace"nawa ne kudin da ake binta bashi"
Yarima Bashir ya fad'a me

Haka kawai kawu yaji nibras tayi me yayi shiru

Cikin Kuka inne ta fara cewa su tafi da ita su taimaka ko aikin ne su Bata

Yarima Bashir ya dube kawun nata sai Kuma ya kalle kawu idi da ya fahimci abinda inne tace yace"kina son a Bata aiki Dan a rabata da miyagun mutane nan Amma duk inda akayi ai Yan uwanta ne Bata da kowa sama dasu Kuma in ba aure tayi ba bazasu Daina hanttaranta ba sai ma suyi Wanda yafi nan a gaba,in tana da manimi ta fito dashi a daura musu aure a huta kawai Amma aiki tayi kankata ai"yayi magana cikin ko in kula saboda su aure yarenta is common a gunsu

Kawu ya Kalli yariyar da mamaki yace"aure fah ??"

Yace"yes ba wani Abu bane shine kadai masalaha a wanan case din "

Kawu ya gyara tsayuwa Yace"ok what do you intend doing now"

Yace"in Bata dashi ai ga driver na ya Kara a na biyu nasan Yana da Amana zai riketa

Inne ta saki Kuka tana godiya kawu yace"kawai sai ayiwa yariya aure kamar kaza Kuma yariya ce fa"

Yarima Bashir yace"toh in ba haka akayi ba Kai zaka aureta ne"

Washe baki kawun mustafa yayi yace"Daman ni bawai Ina kin ta bane but nauyi ne ya rataya a Kaina ga nawa yaran in zai aureta ga massalaci yanzu za a kira sallah la'asar sai a daura a mikan sadaki na "

Haka ko akayi yarima Bashir ya kama hanyar mosque,ana gab da daurin auren bayan an idda da sallah kawu yace"a dakata"

Kallonshi akayi.ya goge zufa yace

Yarima Ahmed na kudine for payment:πŸ‘‰300 for regular group 500 vip via Aisha Mohammed
2378022567
Zenith bnk,in Kuma MTN card ne Zaki turo sai ki min magana via watsaap number na 09090112846

Maman nur
[8/21, 11:28 PM] MAMAN NOORUL HUDAH Writer: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*_YARIMA AHMED_*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
_By maman noorul_
_Hudah_

_Paid book_

πŸ…Ώ9️⃣&1️⃣0️⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Yarima Bashir yace"kaifa muke jira kana b'ata Mana lokaci"

Kawu ya mike yace"mu gan juna a waje minti uku"

Yarima Bashir ya mike ba a Jima ba suka dawo Suka zauna

Yarima Bashir ya sake kallon kawu yace"are you sure of this??"

Ji yayi kamar yace"ah'ah but in ya tuna fuskar that innocent young girl sai yaji tausayinta na overtaking emotion dinsa "

Murya a dan shake yace"eh kawai a d'aura "

Ba shi da kudi a aljihu sai wani zoben yarima da yake matukar so ramar da yayi lokacin b'atar d'ansa *Azhan* yasa ya cire ya ajiye gaban mirrow dinsa da yike a lokacin yayi rashin lafiya aka kawo sa Nigeria shine me kula dashi ya d'auke yasa,gold ne me nauyi Wanda darajarsa Bata misaltuwa yarima na son wanan zoben sosai

Kawu yayi ta juyawa sai Kuma ya Mika a matsayin sadaki

Kawu Mustafa jiki na rawa ya Kai hanun zai d'auka kawu Bashir ya Riga shi da cewa"hakkin yariya ne"

Kwarjini da ya masa ya hanashi magana

Babu b'ata lokaci aka daura auren

Yarima Ahmed Khalifa wali

Da

Fatima Ahmed (nibras)

Ana gamawa duk suka fito sai a lokacin kawu yaji wani sanyi ya lullub'eshi,Dan yasan ya had'a bomb ko hauka ake yasan yarima bazai tab'a accepting yariyar ba thinking of nafeesat sai duk yaji zazzab'i

Toh shi a wa,yayi wa yarima aure??ya tambayi kasan hmmm this decision is wrong Taya zai Fara kallon Mai martaba mahaifinsa yace"shi yayiwa yarima aure balle a Zo ga mahaifin yarima shi kansa,hmmm karma a tab'o sultana Bintu daga ina zai Fara fad'a musu Kai gaskiya wanan abu ne da bazai yiwu ba sai yanzu idanunshi ya bude yasan ya had'a kwamacala da dole ya warwareta toh Taya??shi da igiyar auren ba a hanunsa yake ba dole dai in za ayi maganar saki sai ya sanar da yarima auren kafin maganar saki ya biyo baya

Lura da ya daburce yasa yarima Bashir cewa ya na ganka a haka?"

Yace"fin haka ma zaka ganni my ass is on fire my friend, Wai Ni bazan iya sakin yariyar bane,sai yanzu nake tunanin da kawai tafiya da ita mukayi na Bata aiki a can har allah ya Bata mijin aure...Bashir ko Karen hauka ya cije ni bazan iya fidda maganar auren Nan ba shifa miskilin pimmm bazai ce ba Amma kallon da zai min Zan gommace yace pimmmm din,mahaukaciyar matarsa ko bazata nuna abin ya dameta ba ta bayan fage zata fito tasa a saceni ayi ta cin ubana sai na gane bani da wayau,karma a Zo Kan mahaifinsa "

Bashir yayi hanya gidan inne yace"daga baya kenan ko, Bari dai a Kai mata zoben "

Yace"Kai bani zoben,sai fa yarima ya b'ata min rai akan wanan zoben'

Bashir da yike shima daidai yake dashi yace"ai wallahi baza ayi wa yariya kwalele ba wallahi "Yana fadin Haka yayi cikin gida kawu ya fad'a mota yayi tagumi

Ba karamin Dadi inne taji ba sai Kuma da tuna ance yarima ne sai ta ji jikinta duk yayi sanyi,Taya nimbras zata iya rayuwar gidan sarauta,itama sai ji tayi kamar tace a raba auren
Amma sai Bashir ya kwantar Mata da hankali tare da tabbacin shi zai Zama mata uban gida

Goge hawayenta tayi ta roki alfarma a bata kwanaki kafin a tafi da ita

Mika mata zobe Bashir yayi yace"ga sadakinta "ta amsa tana juyawa a take ta gane Yana da daraja,har hakan ya Bata mamaki da tsoro Dan tasan gold

Sallamarta yarima Bashir yayi ya fito ya


Maman Nur
[8/21, 11:28 PM] MAMAN NOORUL HUDAH Writer: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*_YARIMA AHMED_*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
_By maman noorul_
_Hudah_

_Paid book_

πŸ…Ώ1️⃣1️⃣&1️⃣2️⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Kawu Mustafa da be fahimci dawa aka d'aurawa nimbras aure yayi ba ya d'au da wani matsiyaci ne but idanunshi na kan zoben tunda ya gan manyan mota yasan kila su Suka biyawa driver sadakin danshi bawai ya wani gane Bashir bane

Bashir ya lura da idanunsa na kan zoben hakan yasa ya bashi sound warning akan karya kuskura ya Bari ya samu labarin sun Shiga lamarin yariyar nan in ba Haka ba sai ya dau mataki,,,ai kamar kiftawar Ido kawu Mustafa ya bar wurin dama karshen matsoracine

Ko da ya karasa mota da gaske zazzabi ya lullube kawu Idris har abin ya so bashi mamaki yasa driver ya ja mota

Kawu idi na fita masaukinsu yayi ya tarar da yarima Ahmed yasa laptop a gaba Yana latsewa

Zama yayi a kasa Yana kallonshi ya rasa ta inda zai fito ya fada Masa

Can dai yace"son"da dai kamar yarima bazai d'ago ba sai Kuma ya d'ago bayan wasu second ya sauke idanunsa a kansa yayi me kallon minti uku cafff ya d'auke Kai

Idanunsa na kan laptop yace"what have you done this time??"

Kai tsaye kawu yace"aure nayi maka kasan ni da taimako gari na shiga na gan za a cirewa wata yariya Yar mitsisiya zani toh a lokacin na samu b'acewar basira sai nace a d'aura maka aure sai daga baya ka saketa "

Tunda ya Fara magana yarima Ahmed ya zuba Masa Ido Yana karantarsa a sanin da yayiwa kawu yasan zai iya kasancewar gaskiya yake fad'a Dan Haka yake magana kamar Wasa ya Zo ya Zama gaskiya

Tunda ya zubawa kawu Ido kawu ya daburce

Cikin maganarsa kamar Wanda akayiwa dole yace"me ka ce??"

Kawu ya kirkiri dariya hahhhhhhh ya Kai me bugu a cinya yace"Kai wasa fa nike maka Ni a wa zan maka aure?Ni din banza ai tsakanina da Kai shine ka rakani wuri "

Yarima dai kallonsa yake can dai ya mike yace"anyways in ma gaskiya ne Kai ka sani dan wallahi Saida ka zauna da ita ni matata ta isheni tun wuri ka koma ka warware kullin'

Kawu yace"Kai dai ba a Wasa da Kai,nifa kawun kane,kawai dai Yar aiki na sama Mana za a kaita Mali yariya marainiya na gan ana ci Mata mutunci zatayi Sha uku zuwa hud'u sunanta lambras so Nike tayi ta kula da harkokinka tunda matarka malalaciya c......"

Kira ya shigo wayar kawu ya Ciro waya ya duba yace"ita Kuma kullum sai ana tsaka da gulmarta take kira,Dan girman ka tausaya ka dinga daukar wayarta ta barni in sarara haba ko matana Basa kirana irin inda take kirana ta fasan halinka da kin d'aukar waya Amma sai ta nace kamar kaskar Kare in Kana Mali toh ubanwa take Kira?_

Shidai Ahmed be ce komai ba ya cigaba da aikinsa har Kira na biyu ya shigo kawu ya d'auka yace"uwargida nafeesa kamar ko kin San yanzu Nike maganarki na alkhairi sabar alkhairin da kike min muna Sudan na gan wata yariya nace na samo Miki special maid shine fa yace be so"

Nafeesat na dariya tace"a toh gaskiya in baby baya so a barta nifa ma Bata min ba kana fad'a gabana ya Fadi gaskiya ah'ah "

Yace"hmmm ku dai ba a muku arziki sai ka ce Zan cutar daku "

Tace"ni ba wanan ba Ina baby?"

Yace"ai babyn nan bacci yake ai "

Yarima ya kalleshi ya d'auke Kai

Zatayi magana ya yanke yace"ta Bari inji da abinda ke damuna kamar da ita nayi shawara Randa zan sai waya"

A bazata yaji yarima yace"me ke damunka"

Yace"toilet zani"

Yana fadin haka ya bar falon yarima ya bishi da kallo yasan halin kawu something is fishy,but shi ya sani"

Koda kawu ya fito ya tarar baya falon,kawu ya zube kujera Yana maida numfashi sai ga Bashir ya shigo

Yace"ya yayi accepting auren??"

Kawu yace"ni a wa Zan fad'a Masa Kai dai ka Bari a bi komai tsetse tsetse tunda ma yariyar Bata da shekaru Kuma kasan mu Nigeria bamu irin auren Nan a Bari Nan da Dan shekaru sai in sanar me lokacin ta koyi al'adamu "

Bashir yace"nidai Yar Amana ce a gunka kasan hakkin marainiya ya kamata a sanar dasu sun San akwai hakkin juna a kansu "

Kawu yace"ai tausayin ya jefa Ni a halin da Nike ciki......."

Be karasa ba ya gan yarima tsaye a kofar daki ,,,tsorata yayi Allah yasa be ji maganar ba

Cikin in Ina yace"is not what you thin......"be karasa ba yarima ya cire Bluetooth dake kunninsa ya nuna masa yayi cikin d'aki

Kawu ya sauke ajiyar zuciya,ba a Jima ba sai ga yarima ya fito da karamin jakka

Kawu ya mike yace"Ina zuwa??"

Yace"Mali"

Kawu yace"ya zamu Zo tare ka ce zaka wuce ba shawara"yarima be ce komai ba yayi tafiyarsa

Kawu yace"Anya yaron Nan be ji mu ba??_

Bashir ya tab'e Baki yace hakan zaifi

Da gaske yarima tafiyarsa yayi ya bar kawu,

BΓ yan kwana uku da tafiyarsa kawu ya shirya komawa Suka tafi d'aukar nimbras da har yau be iya Kiran sunanta ba saidai yace"labaras

Da yike an San da zuwansu inne ta shiryarta sai dai tashin hankali da ba a sa Mata rana ta rako su mota kawu yace"sallame su mu wuce ki Basu d'ansu

Itadai ba hausa take ji ba ta zuba me Ido

Ya kalli Bashir yace"ce Mata ta bawa me Dan danta mu tafi"

Yarima Bashir ya kalli inne yace"ki amshi Dan toh",cikin yare yayi magana

Tace"ai d'anta ne Bata rabuwa dashi Nima naso ta barminshi Amma taki shima dan ba Zama zaiyi ba

Yarima Bashir ya zaro Ido yace"what '

Kawu yace"Yaya Yaya???"ku fad'an me ke faruwa

Bashir yace"Ashe Wai d'anta ne dashi zaku tafi

Ai wani dammm kawu yaji kanshi ya bada duuuummmm yace"me???,,,ban fahimta ba dama bazawara ce???"

Ganin ya rude yasa inne girgiza Kai ta Fara korawa Bashir bayani Yana fassarawa kawu

Duk sai kawu ya gan dai kamar dan nata ne da gaske karya ake musu mussaman inda yaron yaki bari jikinta Sam yau yaron naji da kiwuya yaki barin jikinta sai tsala ihu yake nimbras nayi

Badan kawu ya so ba Bashir yace"su tafi dashi tunda bada zuwa zata tare ba,ba wani Abu for now

Kawu ya


Maman Nur
[8/21, 11:28 PM] MAMAN NOORUL HUDAH Writer: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*_YARIMA AHMED_*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
_By maman noorul_
_Hudah_

_Paid book_

πŸ…Ώ1️⃣5️⃣-1️⃣6️⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Tace"saidai wani hazari ba gudu ba ai sultana tasan Yan uwana wanan Kuma na gan balarabiya ce ai zata gane bamu da alaka "

Yace"cewa zakiyi an marainiya ce aka Baki Amana wasu Wanda kukayi Zama dasu be"

Mama ladi tace"toh,Amma yariyar zata wahala a gidan Nan na lura Bata Jin hausa balle Kuma yarensu ta Nan kasan fa kalilan ke hausa anan Kai sai ka wata baka ji Wanda zaiyi hausa ba fulfude suke "

Kawu yace"tunda Kika iya itama zata iya ki dai rike ta Amana in akwai matsala ki kirani ban amince tayiwa kowa aiki ba sai yarima,shi kadai ya cancanta ta dukawa ko nafeesat karta mata aiki kafin in samo mafita Amma ba yanzu ba sai ta fi Nan girma

Mama ladi ta kalli nimbras sai ta ji tausayinta tace"shi Kuma d'an fa??"

Yace"ai kamar gum suke basa rabuwa sunce ba d'anta bane Amma ban yarda ba wanan shakuwar tayi yawa "

Mama ta mike zata amshi A'med aikuwa ya lafe jikin nimbras Yana b'ata fuska itama nimbras ta Kara rungumeshi Lura da Mama na son ta amshi yaron yasa ta maidashi baya

Sai abin ya bawa mama dariya a ranta tace"ikon Allah rowar yaro "

Kawu yace"nidai Zan tafi Nan da minti biyar sai ki Zo ki fad'a Mata"

Mama tace"toh "

Fitowa yayi Yana tafiya Yana bin gidan da kallo fitowar shi yayi dai'dai da dirowar uwargida zainabu tana ganinshi ta washe Baki tana lale marhaba lale Idris ne yau a gidan namu yaushe rabo"

A ranshi yace"li'ilafi"a fili ko murmushinsa Mai kyau yayi yace"yanzu na shigo ranki ya dade ya su aliyu kwana biyu ban gansa ba"

Tace"yarima Aliyu ai Yana U K kasan shi baya Zama kila dai in ya amshi sarauta ya zauna ai"

Kawu yayi murmushi yace"ikon Allah Ashe shi zai gaje sarauta"

Tana murmushi tace"ai a yaran shine mafi cancanta ai gashi da Yara maza har uku "

Kawu yace"na gan alama Amma ki dage kuyi tawa Mai martaba addu'a tsawon rai, bawai zanjen magaji ba "

Fuska ta b'ata sai Kuma tace"zaka leka Binta kenan"

Yayi murmushi yace"sultanan Bintu dai Kar a jiki a yanke Miki halshe"Yana fadin haka ya Kara gaba ya Barta Baki sake"murmushi tayi bΓ yan ya b'ace daga ganinta tace"zamu gan inda Ahmed din zai hau kujerar sarauta"

B'angaren sultanan yayi straight Yana zuwa ya tarar da ita a zaune a kasar laulausan carpet tana Shan fruits sai glowing take

Ya karasa ya gaidata Aiko ta d'au minti kusan uku Bata amsa ba kafin daga baya tace"ya ka baro gida"

Shima shareta yayi har ta kallesa sai ta cigaba da abinda take

Can tace"yanzu Kai Idris baka da aiki saidai ka dau Ahmed kuyi ta zaga duniya babu abinda kuke tsinanawa shima da yike yanzu ya gane yawon baya son zaman Mali mutum da gidan ubansa saidai ya tafi can Nigeria kana zuga sa"

In kuka gan inda kawu ya kankance Ido kwace mummunan sako aka fad'a Masa yace"Sannu uwargida a gun sarkin mali,Sannu Yar sarki jikar sarki matan sarki,binta Ni kike zagewa saboda kawai Ina kula d'anki in Banda so gamo na jinine ga dangi a gari me zanyi da wani Ahmed Wanda ba dadin Zama ne dashi ba,,da kike maganar muna zaga duniya da karuwai muke yawon,??karki sa na wanke ki yanzu Nan dan wallahi kallo Yar uwa Zan Miki ba matar sarki ba ku jimin rashin mutunci da dibar albarka ni na hanasa aiki toh da kike maganar Ina zuga sa in yaki zaman gidan ubansa ai Yana Zama gidan kakarsa Wanda ubanki ne ko....wallahi Kika Kara min irin wanan maganar za a Jim......."

Be karasa ba mama ladi ta shigo da sallama nimbras na binta a baya

Ganin mama ladi yasa ummi rufe Baki

Mama ladi ta karasa tace"ki gafarceni uwargida in babu damuwa zamuyi magana"

Tace"ok ok ba damuwa"

Tace"Bakuwa ce aka kawo min daga Sudan nace Bari in kawo ta ku gaisa"

Ummi ta zubawa mama ladi da kanta ke kasa tace"bakuwa Kuma??"

Kawu yayiwa ummi kallon kasa sai mama ladidi tace"jikar wata kawata ce toh ta dade da rasuwa Ashe Wai d'anta yayi aure a Sudan sai Allah yayi me rasuwa aka rasa Wanda zai riketa shine jiya jibrin ya kirani kiyi hakuri ban nimi izini ba Kan a kawo ta Amma Wai aiki ake so tayi "

Kawu ya kalli

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment