Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dai Uzair Ya miƙe rai a6ace yace"idan har ban tona masu asiri ba,tabbas zan ajiye aikina na ɗan jarida ne, domin ban cancance shi ba" yana kai ƙarshen maganar shi ya fuce, Taj dai yana a tsaye ya yi kasaƙe yana kallon bayan shi, har ya 6ace ma ganin shi,


Duk wannan surutun da su ke yi akan kunnan angel tun ɗazu ta farka daga bacci, duk da bata fahimci me suka tattaunawa ba,

"Daddy faɗa kuke da Daddy uzair?" a ɗan ruɗe Ya kalleta, da sauri yace"a'a, muna tattaunawa ne, game da zuwan Uncle abdallah, na faɗa mashi cewa Ya bari mu fara zuwa buzaye shi kuma yace dole mu jira su dawo Sai mu tafi atare"

Murmushi tasa ki"Nima nafi so mu tafi tare da su mommy adama"

"Me zaki Ci in kawo maki"?

"Komai zaka ci nima zanci" miƙewa ya yi tare da juyawa Ya nufi kitchen, don yau ba aikin safe gare shi, Sai wurin mare ce zai fita.


Zama tayi tana Jiran dawowar shi, almost 15 mins Ya fito hannun shi ɗauke da plate, indomie ce daga sama Kuma wainar ƙwaice, Asaman table ya ajiye masu,Kafin Ya koma kitchen ɗin Ya haɗo masu tea a cup biyu,Yazo ya ajiye gefen plate din

tare suka zauna Suna ci, still zuciyarshi a cunkushe take, Yana so ya taimaka ma uzair wurin fallasa asirin waɗannan mutanan ta wani 6angaren kuma Yana jin tsoran su jefa kan su Cikin masifa, tunda mutanannan sunfi karfinsu nesa ba kusa ba, Allah ne kaɗai zai Iya dasu, ga kuma angle din shi bayaso wani abu ya faru da ita ta sanadiyar shi gaskia yana cikin tsaka mai wuya


Ya yi zurfi cikin tunani, muryar Angel ce ta katse shi, "Daddy!"

Firgigit ya yi tare da kallon ta, "Na'am!"

Fuskarta da alamun damuwa ta ce, "Tun ɗazu ina ta kiran ka amma ba ka amsa mini ba. Daddy kamar kana cikin damuwa."

Girgiza mata kai ya yi, "Am ok, ba wani abu. Kawai ina tunanin rayuwar duniya ne mai ban al'ajabi, rashin tsoron Allah ya yi ƙaranci a zukatan wasu mutanen. ban sani ba neman duniya ne koko mene ne yake jan hankalin su har su manta cewa wata rana za su mutu? Kuma za su koma ga Allah, sannan duk wani abu da suka mallaka ba za a ta6a binne su da shi ba, a gidan duniya za su bar shi."

Tun da ya fara magana Angel ta ƙura masa ido tana kallon shi, sam ba ta fahimtar kan me yake magana. Shi kansa ya manta da wa yake magana? Abin ne ya dame shi yasa yake ta sambatu ko ya samu ya rage raɗaɗin dake cikin zuciyarsa.

Haɗa ido sukayi da ita, lokaci ɗaya yaja bakin shi ya yi shiru, da mamaki akan fuskarta take kallonshi, can dai tace"Daddy, Meya faru"?

Ƙaƙaro murmu shi ya yi"halan kinji inata zuba ko? wani programme ne da zamu gabatar a gidan radion mu shine nake tsara yadda zanyi shi"

Murmushi tasa ki"Allah ya taimaka daddy, I wish u all the best' ya amsa mata da ameen,

*ANEELER*

A zaune su ke ita da uzair saman dining chairs suna fuskantar Juna, gaba ɗaya hankalinta na akan fuskar Uxair tunda ya ruƙe spoon yake ta jujjuyashi Cikin abincin da ta zuba ma shi a plate sam ya kasa cin shi sai kacaccala shi yake yi kamar ƙaramin yaro, ta lura da canzawar da yayi daga daren jiya zuwa yau kamar wani abu na damun shi bama kama bace tabbas akwai abinda ke damun shi.

Gyaran murya ta ɗanyi ma shi, Ya ɗago suka haɗa ido tace"My man, kaƙi faɗamun abunda ke damunka, tun ɗazu nake kallon ka, sam ka kasa Cin abinci why pls"?

Daƙyar ya iya bude baki yace"don't worry ur self am ok, just bana jin daɗin zuciyata ne,"

"daka daure ka faɗamun may be in sama mana solution"

Murmu shi ya ɗansaki cikin zolaya yace"Matsalar bata asibiti bace balle kice za ki yi mun allura inji sauƙi"

Ta6e baki ta ɗanyi tare da mayar mashi da martanin murmushin "kana nufin matsalar data shafi asibiti kaɗai zan iya magani"?

Girgiza kai yayi"karfa ki dauka da zafi, It was a joke"
Kallon shi kawai tayi kafin ta mayar da eyes ɗinta akan abincin dake gabanta,

Wuraren ƙarfe shida na marece, taj, Yana daga kishingiɗe saman Sofa, jikin shi na sanye Cikin jeans da white shirt, a lokacin angel tana can cikin ɗakinta,

Ƙwanƙwasa ƙopar falon shi a kayi daga waje, A hakanlali ya ɗan buɗe i danuwans hi tare da tambayar wanene, Ba abashi amsa ba aka turo kopar ɗakin, uzair ya gani a tsaye Sanye da jallabiya, fuskar shi babu walwala, miƙewa zaune taj yayi yana kallonshi yace"Shigo ciki mana"

Ƙarasa shigowa Cikin falon yae tare da samun wuri saman Sofa ya zauna, batare da ya furta mashi komai ba,

"Meke damun ka ne aminina? naga sauyi sosai akan fuskarka"

harara ya dan jefa mashi tare da cewa"Kaine damuwata Taj, saboda kaƙi bani haɗin kai akan abunda nakeson Cimmawa"

Murmushin takaici taj yayi"cos You wanna get yourself into trouble shiyasa naƙi goya maka baya, Idan suka kama mu munayi masu leƙen asiri what do you think will happen next? They will kill us as soon as they find out that we are investigating them,"

Jinjina kai Uzair yayi"Yanzu haka zamu zuba ido ana aikata 6arna batare da Mun hana ba"?

"Ƙwarai kuwa, Saboda bamu da yadda zamuyi,illa iyaka Muyi addu'ar Allah ya kawo mana ƙarshen su, that's the only solution"

Jiki a sanyaye Uzair ya miƙe ya soma tafiya har yakai bakin fita daga Falon ya ɗan dakata
"Ka manta alƙawarin da mu ka yi ma juna tun kafin mu fara aiki'? shiru taj ya yi yana kallon bayansa,

Cigaba da magana uzair yayi" duk runtsi duk wuya zamu ƙarfafa ma juna gwiwa wurin ganin mun taimaki ƙasar mu, amma sai gashi kaine na farko daka fara sare mun gwiwata, Narasa goyon baya daga gareka, ji nake tamkar narasa wani sashe na jikina,"

Miƙewa tsaye taj yayi tare da nufar inda Uzair yake atsaye Ya soma magana"Ina jiye mana tsoron abunda zai biyo baya ne, akan idon mu suka kashe mutun da ƴa'ƴansa, a haka kuma ka ke so Mu yi bincike akansu?wannan fa ba aikin mu bane, shin wai kai baka tsoron asirin mu ya tonu su gane cewa muna bibiyar su?ko ba don saboda mu ba, ka tuna kana da mata ni kuma inada ƴa, So ka ke Mu jefa su cikin masifa ne? Yana kai ƙarshen maganar shi uzair yace"In sha Allah hakan bazata ta6a faruwa ba, Nidai inaso ka bani haɗin kai kawai"

Duk yadda Taj yaso ya fahimtar dashi amma Yaƙi ya gane, ba don yaso ba, Ya amince mashi akan suyi Bincike akansu, don su samu hujjojin da zasu fallasa su, har hukuma ta ɗauki mataki a kansu, Tun daga wannan Lokacin Suka soma tunanin ta ina zasu fara neman su, A ƙarshe Uzair ne ya ba shi shawarar su koma inda suka fara ganinsu acikin dajin nan, Cikin sa'a ranar da suka je again suka sake ganin miyagun mutanan nan sun kamo wani mutumin, kamar yadda suka kamo malamin nan, da alama Leƙen asiri shima Yayi masu, Akan idonsu suka koneshi, ranar Taj hankalin shi ya tashi matuƙa har yace ma Uzair shidai zai Cire hannun shi, kusan faɗa sukayi da uzair akan hakan, daƙyar suka sasanta kansu, kuma suka Cigaba da bibiyan Alhazawan nan, Sai dai duk wannan tsawon lokacin da suka ɗauka suna Bibiyarsu Allah bai basu damar sanin kosu wanene su ba, daidai da fuskokin su ba su sani ba, Abu ɗaya kawai suka sani inda suke yankewa mutum hukunci wato Cikin dajin nan a bakin ƙorama, Abunda su taj basu sani ba, duk wani motsinsu akan idanuwansu suke yin shi, Sunsan komai game da bibiyar su da su ke yi zuba masu ido kawai su kayi, yayin da su basu san da hakan ba, Lalube kawai su ke yi acikin duhu............


Ganin babu Riba a bindiddingin su da sukeyi ne yasa Taj ya cire hannun shi, uzair kuma yasa naci Akan binciken shi, duk yadda taj ya gargaɗeshi amma Ya sanya kafiya, ashe ajaline ke kiran shi.


*************************
A daren Ranar Alhamis ne Wannan mummunan ƙaddarar ta riskesu wadda tayi silar rasa rayukan su,

Wuraren ƙarfe 9 na dare, Taj na zaune tsakiyar gadon shi, ya tasa laptop ɗinshi agaba yana ta ƴan danne danne acikin, har ma ya yi shirin kwanciya singlet ce ajikin shi tare da short, wani aiki ne ya tsayar da shi, Allah Allah ya ke yi ya gama aikin ya je ya kwanta, sai hamma yake yi, ba zato ba tsammani yajiyo bugun ƙopar falo,

Agogo ya kalle, Cike da mamaki Ya sauko daga saman Gadon ya fito ɗakin ya nufi cikin falon, a baƙin ƙopar ɗakin ya tsaya tare da tambayar wanene? Daga waje yajiyo muryar aneeleerh,ka bude mun kopa nice" muryarta Cikin shessheƙar yaji sautinta, jiki na rawa ya buɗe mata ƙopar har saida gaban shi ya faɗi ganin Yadda fuskar ta tayi jawur saboda kukan da ta sha, kayan Bacci ne ajikinta riga da wando sai mayafin data yafa akanta, gefen goshinta kwantaccen gashin kanta,

Aruɗe yace"Aneelerh? Lafiya? me meya faru ne? Ya akai naganki acikin daren nan'?

Daƙyar take iya kallonshi, da runannun idanuwanta wadanda suka yi jawur da su,
"Uzair ya fita bansan inda yaje ba Cikin daren nan, na farka bangan shi ba, hankalina bai kwanta ba, na je wurin baba mai gadi don in tambaye shi ko sun yi magana da uzair kafin fitar shi, yace mun eh sunyi magana da shi kafin ya fita amma bai faɗa ma shi inda zaije ba,......" tunda ta soma magana hankalin taj ya ɗungunzuma, jikin shi ya soma kakarwa, fargabar shi kada ace uzair ya tafi Wurin mutanan nan, dama yace mashi bazai fasa bindiddiginsu ba, idan kuwa hakane to kuwa tabbas yaje yi masu leƙen asiri ne,

Jin yayi shiru bai ce mata komai ba yasa tace"ko kasan inda ya tafi ne"? girgiza mata kai yayi alamar a'a, saboda bai son ya tayar mata da hankalinta,
"Kin kira layin shi"? ya yi tambayar yana kallonta,
"Na kira shi har bansan adadi ba, Amma bai ɗaga ba, kuma kiran yana shiga"jinjina kai yayi" Bari na jaraba kiranshi, ki shigo Ciki ki zauna" yakai ƙarshen maganar yana nuna mata sofa,

Cikin sanyin murya tace"bazan Iya zama ba," tausayinta duk ya kamashi, bedroom dinshi ya koma a hanzarce Ya kai hannu ya ɗauki wayar shi dake a jiye gefen laptop ɗin shi, Ya shiga call logs, ya danna ma uzair kira, tana fara ringing, uzair yayi picking call ɗin,
Rufe shi da faɗa yayi ta inda ya ke shiga bata nan yake fita ba,
"Duk inda kake ka dawo gida yanzu yanzu, kasa baiwar Allah sai kuka take yi, Saboda rashin hankali, Ka kama hanya ƙarfe tara na dare ka tafi ka barta batare da ka sanar da ita inda kaje ba, Anya kuwa kasan me ka ke yi? wai shin ina kaje ne ma.......? duk wannan suratan da taj ke yi uzair baice mashi uffan ba, A ƙarshe ma saiya yan ke kiran gaba ɗaya, jikin taj ba ƙaramin sanyi ba, tunani ya shiga yi wai shin dawa ma yake waya? idan uzair ne meyasa bai yi ma shi magana ba? kuma ya ɗaga kiran Anya kuwa ba'a samu matsala ba, sake kiran Layin ya yi a switched off ya samu wayar, Nan fa jikin shi ya mutu, hankalinshi Ya tashi

Saman bedside drawer Ya ɗaura wayar, ya fito daga ɗakin ya koma falon, Cike da zullumin amsar da zai ba aneelerh,
Lokacin da ya shigo falon ya ƙaraso inda take tsaye, sai ya shiga Yin ƴan kame kame,
"Bai ɗaga kiran ba ko" ta yi tambayar a ƙagare,
Muryarshi na inda inda yace"Am..um..kingane..eh..muyi waya dashi, ki kwantar da hankalin ki, Yana kan hanyar dawowa gida, yanzu ki koma ki kwanta, kada ki takura kan ki,"
Wani irin kallo yaga tana yi ma shi kallon ban yadda dakai ba, da sauri yace"kiyi hakuri ki koma gida, nan badajimawa ba zai dawo"
Jiki asanyaye Ta juya ta fuce daga falon, Ko bayan tafiyarta saida ya kuma kiranta awaya, Ya ƙara kwantar mata da hankalinta,

Kasa zama ya yi, zarya ya shiga yi tsakanin ɗakin shi zuwa palour, ya rasa meke yi ma shi daɗi duniyar nan, duk bayan ƴan mintuna sai ya jaraba kiran Layin Uzair don yaji in ya bude wayar amma a kashe yake samun ta,

Bawan Allah ya rasa ta zama, duk ya shiga damuwar rashin amininsa, juyawa ya yi da sauri Ya haye upstairs ɗakin angel, ya tura ƙopar ɗakin a hankali, ko'ina duhu, ya lalauba jikin bangon ya kunna switch, tare dakai idanuwanshi kanta, Sai bacci take yi, ta ƙudundune Cikin bargo, murmushi ya ɗan saki kafin ya ɗauke i danuwan shi daga kanta, ya mayar dasu kan wall ɗin dakinta, Zanunnukan da tayi ne tare da kalaman da ta rubuta ma shi, a kullum ya kallesu sai yaji farin Ciki acikin zuciyar shi, duk mun baƙin Cikin da yake ciki,

A hankali Yake tafiya cikin ɗakin nata, ta 6angaren hagu ya zagaya saitin inda take kwance saman gadon, Kneel down Yayi tare dakai hannu Ya yaye blanket ɗin data rufa da shi, rigar bacci ce ajikinta,

Kyakkyawar fuskarta Ya ƙurawa ido yana kallonta, Hakanan ya dinga jin bugun zuciyar shi na ƙaruwa, wani irin matsanancin faduwar gaba, a cikin zuciyarshi ya shiga ambaton Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" ya ambaci hakan ba iyaka,

"Daddy" muryar ta ce ta katse shi, kallonta yayi ganin ta buɗe manyan idanuwanta a kan fuskar shi,

"Dama bakiyi bacci ba"? murmushi ta sakar mashi tare cewa"Nayi mana, yanzu na farka" hands ɗinshi ya sanya ya tallabo fuskarta"ƴar kyakkyawata, Allah yabar mun ke,"
"Ameen daddy, gobe uncle da aunty zasu dawo ko sai mu tafi buzaye ? tayi tambayar tana ƙoƙarin mikewa zaune,
Girgiza mata kai yayi"Till next week nake tsammani"

Ta6e baki ta ɗanyi"daddy ka kwana ɗakina yau"yatsina fuska yayi"Gadonki yayi mun ƙanƙanta" cikin zolaya ya yi mata maganar,
Turo mashi baki tayi"To muje ɗakin ka mu kwana" maƙe mata kafaɗa yayi"A'a, kowa ya kwana a ɗakinsa," shagwa6a ta soma yi mashi, sosai ta ba shi dariya, suna Cikin Yin fira, Ya tuna da uzair, Rass yaji gaban shi Ya faɗi, Da sauri ya kali agogo, Ƙarge goma da rabi mayar da idanuwanshi kan angel yayi" ki koma ki kwanta, Sai da safe" yana ƙoƙarin mikewa tayi saurin ruƙo hannunshi da sauri kallonta ya yi idanuwanshi sun taunta sosai, ƙaƙaro murmushi ya yi don ya gane me take nufi, Kiss ya mannata mata a saman forehead ɗinta, Yasa hannu ya kwantar da ita tare da lullu6e mata jikinta da bargo, addu'a ya yi mata, kafin ya kashe hasken ɗakin,

Lokacin daya fuce daga ɗakin yana jiyo sautin muryata tana faɗin"I love u so much daddy, Allah yabar mun kai, ina matuƙar ƙaunar ka habibi" murmushi yasaki A hanzarce Ya sauko down stairs, ya faɗa ɗakin shi, daga gefen gadon shi Ya zauna tare da ɗaukar wayar shi, ya ci gaba da jaraba layin Uzair, still a kashe yake samun ta, Zuciyar shi tajima da karaya, A sukwane ya ɗaura wayar saman bedside drawer, a wannan yanayin ne Bacci ya yi awon gaba da shi, sama sama yake yin baccin na shi, 🥺🥺🥺



Sannu a hankali agogon bangon ke harbawa, yana ba da sauti tik-tik-tik. Sakamakon dare da ya tsala don time din karfe ɗaya da rabi na dare, wayar da ke ajiye saman bed side drawer ƙirar Samsung Galaxy ta soma ruri da ƙarfi gaske. A lokacin ya yi nisa a cikin barcin nasa, kusan sau uku kiran na shigowa yana katsewa. A kira na huɗu ne, sautin ya daki dodon kunnansa, a firgice ya farka yana faman ambaton sunan Allah,

Kafin ya zame hannunsa daga kan fuskarsa wani kiran ya sake shigowa wayarsa a hanzarce ya mika hannu saman drawer ɗin ya ɗauki wayar,

Lokacin daya kalli screen ɗin wayar Sunan Aminina ne Ya bayyana, ajiyar zuciya ya ɗan sauke dama jiran kiran shi ya ke yi, A tunanin shi ya dawo gida ne, Shiyasa ya kira shi dan ya sanar ma shi game da dawowar shi, picking call ɗin yayi tare da manna wayar a kunnansa tun kafin ya yi sallama, kunnuwansa suka jiyo masa sautin harbin bindugu. A gigice ya furta, "Aminina!" Kafin Ya ƙarasa rufe bakinsa, muryar Aminin nasa ta katse masa hanzari, a ruɗe yake faɗin,"Na ba ni na lalace, shikenan tawa ta ƙare."

A firgice ya dakatar da shi, "Ka nutsu ka yi mini bayanin me yake faruwa ne?"

"Sun kama ni ina yi musu leƙen asiri, yanzu haka sun biyo motata, na san kashe ni za su yi, kai ma kuma ba za su ƙyale ka ba. ba zan so ka yi irin mutuwar wulakancin da zan yi ba, don Allah na roke ka, ka gudu kai da Angel, ba na fatan laifina ya shafe ka Abokina. Bayanan sirrin da na ɗauka a wurinsu, yana a cikin memory ɗina, ita kaɗai ce hujjar da asirinsu zai tonu..." Bai kai ƙarshen maganar ba, ɗif ya ji kiran ya katse.

A gigice yake kwaɗa masa kira na fitar hayyaci sam ya manta da cewar wayar ta katse, sake kiran layin nasa ya yi cikin sa'a aka ɗaga kiran, abin da bai ta6a tsammani ba, sautin kururuwa ya ji a cikin kunnansa mai matuƙar razanarwa, wata kausasshiyar murya ya jiyo tana magana ta cikin wayar, "Idan kana son sanin meke faruwa, ka kalli screen din wayarka." Jiki na rawa ya ɗago da wayar yana kallon screen ɗin yayin da suka canza kiran zuwa Video Call.

Saboda tsabar firgita, a ruɗe ya diro daga saman gadon, Idanuwansa sun firfiro waje tamkar ƙwayar idon za ta faɗo kasa. Ba komai ne yasa shi firgita ba, face motar Amininsa dake ci da wuta, akan idonsa suka zazzaga wa motar fetur, yana hango yatsun hannun amininsa ta tagar motar, wuta sai cin naman jikinsa take yi. Wata irin zufa ce ta wanke masa fuskarsa, a kiɗime ya shiga furta, "No, no!" Duk ya firgice, rejecting call din suka yi.

Wani irin matsanancin ciwon kai ne ya far masa, ba arziƙi ya zube gefen gadon a zaune yayin da jikinsa ke kyarma sosai, ku san minti goma shabiyar baya a cikin hayyacinsa, ya rasa ma me yake yi masa daɗi duniyar nan.

Yana cikin wannan halin ha'ula'in, muryar amininsa ta soma dawo masa a cikin kunnansa, "Ka gudu kai da Angel ba na so laifina ya shafe ku." Tabbas kuwa za su dawo kansa ne, domin su kashe shi kamar yarda suka kashe amininsa, ba komai ya fi ji ba face ƴarsa ɗaya tilo da ya mallaka wato Angel.

A matuƙar ruɗe ya miƙe, ko jallabiya bai zura a jikinsa ba, iya key ɗin motarsa ya ɗauko saboda tsabar ruɗu wardrobe ya dosa zai buɗe a matsayin kofar dakin, har sai da kansa ya bugu tukunna ya ankare, ya nufi ainihin ƙofar, da sauri-sauri ya fito daga bedroom ɗinsa da ke a downstairs ya nufi cikin babban falon, kai tsaye Upstairs Ya haye. A kiɗime yake tattaka staircases din benen, bai nufi ko'ina ba sai ɗakin Angel, bugu ɗaya ya yi ma ƙofar ta buɗe, ko'ina duhu, kunna hasken ɗakin ya yi, nan take haske ya gauraye ko'ina, wurga kwayar idonsa ya yi kan Angel da ke ƙunshe cikin lallausan bargo, a hanzarce ya ƙarasa shiga ɗakin, tare da hawa saman gadon yana kwala mata kira, "Angel, Angle my daughter!Azeezaty!" Babu alamun za ta farka, a hautsine ya cakume ta ya saba ta saman kafaɗarsa. Da sauri ya fito daga bedroom din nata, ya sauko downstairs, Sam baya a cikin hayyacin shi, balle ya iya tunawa da aneelerh dake a cikin mawuyacin halin na rashin dawowar mijin ta gida,

kai tsaye ya fito waje wurin da motocinsu suke, ɗaya daga cikinsu ya buɗe ƙirar Range Rover, back seat ya buɗe ya kwantar da Angel tukunna ya buɗe diver seat ya shige ciki, a gaggauce ya yi wa motar key, a daidai bakin gate ya tsayar da motar, a hanzarce ya fito ya buɗe gate ɗin, kafin ya koma cikin motar ya fusgeta da gudun gaske. Fitar motarsa ke da wuya, wasu danƙara-danƙaran motoci gudan shida suka nufo shantalelen titin da zai sada ka daga gidansa da alama sun hango motarsa hakan yasa suka bi bayan motar da wani irin matsiyacin gudu. Hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba, saboda ya hangi motocin da ke biye da motarsa ta cikin mirror ɗin motar, hakan yasa shi ƙara gudun motar. La66ansa na kyarma yake ambaton La'ila'ha'illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin! Shi kansa bai san inda zai dosa ba, driving kawai yake yi a makance, shessheƙar kukan Angel ce ta fara dawo dashi cikin hayyacinshi, da alama ta farka sakamakon gudun ceton ran da yake yi da su, yasa kanta ya dinga buguwa jikin motar, har hancinta ya fashe jini ya soma zuba.

A ruɗe take furta,"Daddy...What's happening, where are u going in this darkness night?"

Karamar yarinya ce da ba za ta wuce 11 years a duniya ba, maganarta ma daƙyar take fita saboda halin da take ciki, hawaye ne suka wanke masa fuska yana mai dana-sanin yin aikin jarida fiye da tunanin mai tunanin, saboda shi ne silar shigar shi cikin wannan tashin hankali.

"Angel am really sorry! Na cuci rayuwarki, a yau daddynki ba zai iya ceton ki ba, Angel ba zan jure rashin ki ba, ba zan so laifina ya shafe ki ba." Yana magana cikin kuka, tafin hannunta ta sanya ta dafe hancinta dake bleeding, jini duk ya 6ata fuskarta, cikin shassheƙar kuka ta kuma cewa, "Dad! My nose is bleeding, zan mutu, gabaɗaya ya rikice ya rasa inda zai tsoma rayuwarsa ya ji daɗi. Bai san amsar da zai ba ta ba, iya sorry kawai yake iya furta mata.

Har yanzu motocin nan na biye da motarsu, lokacin da ya fara jin saukar alburushin bindiga a bayan motar a gigice ya karya kwana ya faɗa wani kurmin daji, mai duhun gaske, shi kansa bai san ina zai dosa ba, ga manya-manyan bishiyoyi da suka cunkushe hanyar, a ruɗe ya yi parking ɗin motar ya zagaya ta back seat din motar jiki na kyarma ya zura hannu ya ɗauko Angel, daga ita sai rigar barci a jikinta, sumar kanta duk ta rufe fuskarta, da gudun gaske yavyi cikin dajin da ita yayin da take sa6e avsaman kafaɗarshi. Hasken motarsa ne da ya bari a kunne yake haskaka masa gabansa, yana cikin gudun nan ba tare davya ankara ba, ya ɗaura kafarsa saman wani ƙarfe mai tsatsa, wanda ke a tsire cikin ƙasa, kaifinsa tamkar na wuƙa, zuruf karfen ya shiga ta cikin tafin ƙafar ya 6ulo ta sama, wani irin raɗaɗin azaba ne ya kai masa ziyara, tsikar jikinsa duk ta tashi, tuni jini ya wanke ƙafarsa, sam ya kasa motsawa daga tsayen da yake a hankali ya shiga furta, "Innalallahi wa'inna ilaihir raji'un." Cikin kyarma yake ambaton hakan, muryar Angel ce ta katse shi, "Dad let's go home, nan fa daji ne, akwai kura da zagi za su cinye mu. Daddy ko dai mafarki muke yi ne?" Ta yi tambayar still tana shassheƙar kuka.

Cikin sanyin murya ya ba ta amsa, "Mafarki ne Angel, ba gaskiya ba ne." Hannayenta ta sanya tare da zagayo da su ta wuyansa, ta manna masa kiss a gefen fuskarsa, "Daddy, to mu tashi daga mafarkin, Angel tsoro take ji." Tamkar ya fashe mata da kuka haka yake ji,

A tsiyace suka kwararo da gudu cikin dajin da ya shigo da motar, ai ko da jin sautin shigowarsu, bai san lokacin davya fisgi ƙafarsa ba, ya ɗago da ita daga jikin ƙarfen, jini ya dinga kwaranya. A haka ya dinga jan ƙafar har ya karaso daidai wani uban rami mai zurfi wanda kasansa tafkeken ruwa ne ke gudana, tsayawa ya yi zuciyarsa na raya masa cewar ya jefar da Angel cikin ruwan, ya ƙwammace ta mutu a cikin ruwan dacta yi mutuwar wulakanta a hannun mutanen da suka biyo su, don babu ɗigon imani a kansu, in suka kama mutun fetur suke zazzaga masa su ƙona shi har lahira. Ya yi zurfi a cikin tunanin

Please Login or Register in order to submit comment