Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su, duk sun rame sun fita hayyacin su, sun zama mahaukatan ƙarfi da yaji, addu'ar da suke samu suyi yanzu sun daina saboda Rashin lafiyar da suke fama da ita, Kullum ne sai an samu wanda zai kwanta jinya acikin su, sun jigata sosai, kamar ba za su rayu ba, tun suna ci yana 6ata masu ciki har ta kai ga yanzu sun daina yin gudawa idan su ka ci ganyen, sun fara sabawa da cin shi, cikin nasu ya daina 6acewa, Idan aka kawo masu shi zama suke yi suci shi kamar dabbobi, ruwan kuma Basu iya shanshan shi da tsafi don zai iya yi masu illah, sai sun hura shi da bakunansu kafin su samu su kora shi ta cikin maƙoshin su, yaushe rabon da su wanke uniform ɗin jikin su yau tsawon wata ɗaya kenan, babu mai yin wanka a cikin su, damuwa da baƙin cikin halin da su ke aciki sakamakon canza masu abinci da akayi da kuma rashin dawo masu da ƴan uwansu yasa duk sun rasa kwanciyar hankali.

Sai da Angel ta yi dagaske wurin ƙoƙarin danne zuciyarta dake shirin bugawa ta hanyar dagewa dayi masu addu'a tukunna suka ɗan samu salama, natsuwa ta shiga jikinsu, yanzu suna samun damar runtsawa su yi bacci sosai, amma fa dukkan su bana tunanin za'a iya samun ɗaya wanda bai fama da depression, wani lokacin idan ƙirjinsu yayi masu zafi zuciyoyinsu suka yi masu nauyi, haka zasu zauna su dinga karanta duk wasu addu'o'i da su ka san zasu Sanyaya masu zukatansu, kuma cikin ikon Allah da zarar sun yi komai su ke samun sauƙi, harma su samu damar yin bacci, yanzu sun fidda rai da za'a dawo masu da ƴan uwan su duba da irin tsawon lokacin da aka ɗauka babu su, Danish Yana acikin wata na biyar a hannunsu, Su haris suna acikin wata na huɗu, basu san awani hali su ke aciki ba, Allah kaɗai yasan irin azabtarwar da ake yi masu, suna raye ko sun mutu basu da tabbacin hakan....................."

💔PRISONERS💔


Dare ya nutsa sosai, babu mai motsi acikinsu, Bacci su ke yi kamar matattu, numfashin Angel ne ya soma canzawa, zufa ta soma wanke fuskarta, bugun zuciyarta ya ƙarfafa, yatsun hannayenta dana ƙafarta suka soma Yin kerma, Ga dukkan alamu mafarki ta ke Yi, wanda yasa ta shiga wannan yanayin da take a ciki, su uku ne a kwance saman shimfiɗar da ta yi masu a ƙasa, Ita da Jamimah sai Azeeza.

Sai faman yin sambatu ta ke yi tana ambaton Sunan tsohuwa Tamira!

Wata irin firgita ta yi Sakamakon Ta6a jikinta da akayi, a hanzarce ta yi wuff ta miƙe zaune tana faman zazzare idanuwanta, gashin kanta duk ya tarwatse saman bayanta.

"Angel ni ce! Meyasa kike sambatu kina ambaton sunan tsohuwa Tamira? A tsananin tsorace ta ɗaura idanuwanta kan fuskar batul da ke yi mata magana, Farkawarta kenan daga bacci, fitsarine ya matse ta bayan taje toilet ta yi shi ne ta dawo ɗakin har zata kwanta sai taji muryar Angel tana sambatu acikin baccinta, wannan dalilin ne yasa ta nufi shinfiɗar su don taga meke faruwa da ita.

Bata amsa mata tambayarta ba, saboda bata a cikin natsuwarta, ganin ta miƙe tsaye ne yasa itama batul ɗin ta miƙe tana tambayarta lafiya meya faru? Babu alamun zata tanka mata, sai faman bin ɗakin su ta ke yi da kallo kamar ranar ta fara ganin shi.

"Angel dare ne fa, Me ki ke kallo? Magana fa na ke yi ma ki amma kin share ni....." tunkan batul ta ƙarasa maganar, Angel ta damƙi hannun batul tare da Janta da sauri ta nufi sashen toilet ɗin hannunsu aruƙe dana juna, bayan sun shiga sashen ne Angel ta saki hannunta, aruɗe batul ke kallon fuskarta gani take kamar angel tafara haukacewa ne shiyasa ta janyota a tsakar daren nan zuwa sashen toilet ɗinsu.

Fuskarta da alamun ruɗi tace"kiyi min magana mana, meyasa kika kawo ni nan"?

Sai da ta fara tattara natsuwarta guri guda kafin ta soma magana

"Batool na yi wani mafarki da ban ta6a yin irin shi ba, dangane da wani kalami da tsohuwa Tamira ta ta6a furta mana......" daƙyar tayi maganar tana faman haɗiyar yawu, batul duk ta gama ruɗewa
"Wani kalami kenan"!? Ta jefa mata tambayar.

"Zan faɗa maki amma kafin nan inaso ki sanar dani, Kafin zuwana gidan kurkukun nan, a ina ku ke yin rayuwa? Meyasa aka canza maku ɗaki daga asalin wanda ku ka baro"?

"Angel meyasa kika tambaye ni"? A tsiwace tace"nidai ki bani amsar tambayata"! Yawu batul ta haɗiya kafin tace"Ni kaina bansan dalilin dayasa aka dawo damu nan ba, kawai dai nasan tsohuwa Tamira tace zata sanya a canza mana ɗaki saboda asalin wanda muke aciki yayi mana ƙanƙanta, babu wadataccen filin da zamu sakata mu wala........" A dabarbarce take yin maganar saboda yadda Angel tayi mata rumfa kamar zata rufeta da bugu.

"Amma ranar da aka kawo ni kurkukun nan, Na tsinci kaina nikaɗai acikin ɗakin nan, sai daga bisani aka buɗe ƙopa sai gaku kun shigo Ciki, daga ina ku ke"!? girgiza mata kai Batul tayi"bazan iya tunawa ba Angel, bansan inda aka kaimu ba, " numfasawa Angel tayi tare da sanya hannunta biyu cikin sumar kanta, kamar akwai wani abu da take son ganowa, ganin yadda duk tabi ta ruɗe ne yasa Batul tambayarta"meke damun ki ne? meyasa ki ka tambayeni"?

"Saboda ina hasashen Akwai ƙopar da zamu Iya guduwa ta cikin ɗakin nan da muke rayuwa........." batul bata fahimci inda zancen nata ya dosa ba.

"Angel ƙopa fa kika ce a cikin ɗakin nan ta ina kenan? Anya kuwa kinsan me kike faɗa kuwa"?

Jinjina kai ta ɗanyi kafin ta soma magana" akwai wata magana da tsohuwa tamira ta ta6a furta mana, ban tashi tunawa ba sai Acikin mafarkin da na yi yau, abun tace mana shi ne tana so mu ɗauka cewa mu kamar

*MUKULLAI NE NA MABUƊIN WATA ƘOFA GUDA ƊAYA WADDA ZATA SAMA MANA FARIN CIKI ACIKIN RAYUWARMU, TABBAS MUNA DA DAMA*

Amma fa dole sai Mun yarda da kan mu, mun haɗa hannu, domin kuwa Ƙofar farin cikin nan tana atare mu Sa'annan

*MU NE MAKULLAN DA ZAMU BUƊE TA*

Numfashi Angel taja tare da cigaba da yin magana

"Kalamaine tayi mana cikin hikma, a hasashe na, dama tun fil azal tsohuwa tamira tana son taimakon ku, shiyasa tayi silar da aka canza maku ɗaki aka kawo ku nan, bayan haka tasan da zuwana gidan kurkukun nan........"

Ba ta kai ga ƙarasa maganar ba, Batul ta tari numfashin ta da cewa" kin manta wacece tsohuwa tamira, itama fa muguwace kamar sauran, banbancin kaɗan ne sannan ma'aikaciya ce ita agidan kurkukun nan, taya kike tunanin zata iya taimakon mu? ta yi mata tambayar tana bin da kallo.

"Mutun koda dutse ne a ƙirjin shi ba zuciyaba, idan Allah ya so ka da rahama sai kaga Ya rikiɗa daga mara tausayi zuwa mai tausayi, Zai iya yiwuwa tsohuwa tamira taji tausayin halin da ku ke acikine shiyasa ta nemi hanyar da zata ku6utar daku, Ita da kanta ta faɗa mana cewa tun da ta ke rainon prisoners bata ta6a samun waɗanda su ka kwanta mata aranta ba irin mu, da alama tun kafin zuwana kurkukun nan take so ta taimake ku sai dai tagaza gudun kada taja ma kanta, Shiyasa ta dakata har zuwa lokacin da aka kawo ni sai tayi amfani da kaifin basirar da nake dashi wurin sanar dani cikin hikma akan hanyar da zamu bi don mu gudu daga prison!"

Cike da ƙwarin gwiwa ta yi maganar, Nazari sosai batul tayi dangane da kalaman da Angel ta furta mata, Na ɗan wani lokaci babu wanda ya furta wani abu a cikinsu, can batul tace"Kamar fa akwai ƙamshin gaskiya a maganarki, Amma idan har ta tabbata dagaske ne tsohuwa tamira ta yi kalaman hikma donta fahimtar damu hanyar da zamu ku6uta, Tayaya zamu iya ganin ƙopar da zamu gudu? Sannan taya akai muka zama makullai


........................❓❗


Dai dai nan Na ajiye alƙalamina, Shin kuna ganin dagaske ne hasashen Angel akan kalaman tsohuwa tamira?



💋PRISONERS💋





Cike da ƙwarin gwiwa ta yi maganar, Nazari sosai batul tayi dangane da kalaman da Angel ta furta mata, Na ɗan wani lokaci babu wanda ya furta wani abu a cikinsu, can batul tace"Kamar fa akwai ƙamshin gaskiya a maganarki, Amma idan har ta tabbata dagaske ne tsohuwa tamira ta yi kalaman hikima don ta fahimtar damu hanyar da zamu ku6uta, Tayaya zamu iya ganin ƙopar da zamu gudu? Sannan taya akai muka zama makullai

Zama Angel ta yi dirshan a saman floor, ta jingina bayanta jikin bango, Hannayenta Biyu Dafe da kanta, Ganin ta zauna yasa itama batul ɗin ta zauna, Ya kasance suna fuskantar Juna ita da Angel, Kowa Da abunda Ya ke nazari a cikim kanshi duk a ƙoƙarinsu na su gano fassarar kalaman tsohuwa Tamira,

Sun ƙurawa Juna ido Kamar Malaman Duba, tsawon mintuna kafin Angel ta soma ƙoƙarin motsa bakinta wurin furta"idan ya kasance ƙopa ce, to kuwa mun rasa Makullin da zasu Iya buɗe ta ko da ace mun gano ta, saboda adadin makullin da zasu iya buɗe ta basu Cika ba, Babban makullin ma baya a cikin mu, idan mu ka gano ƙopar tayaya zamu iya tattara makullan da basa atare damu"? ta jefa ma batul tambayar, numfasawa batul ta yi kafin tace"Shi ne Abunda nima nake tunani amma anya kina ganin kalaman tsohuwa tamira suna nufin ƙofa ce ke akwai? Kodai kawai tana nufin mu zamu haɗa hannu don mu ku6utar da kan mu"? Fuskarta da alamun ruɗu ta yi maganar, Angel tace"Abin da zaki lura anan shine, Cewa ta yi mu ne makullan buɗe ƙofar, that mean ƙofar daban ta ke bamu bane ƙofar, sai dai mu zama makullan buɗe ta, ni dai a hasashe na kenan" kowa kanshi ya ɗauki zafi, Girgiza kai batul ta yi"A'a ni nafi hasashen Mu ne zamu sama ma kanmu ƙopar fita idan muka haɗa hannu, Ba wai tana nufin Akwai ƙopa a cikin ɗakin mu ba, kaina ya fara rikicewa, Ko dai inje in yi ma su Hannah magana Su zo mu haɗu Kowa ya faɗi nashi ra'ayin? Kinsan abokin shawara nada daɗi, wata'ƙil acikin su asamu wanda zai faɗi ainihin me ma'anar ta ke nufi tunda mu kan mu ya kulle, Amma idan aka kira su wanda su ka fi raja'a akan cewa ƙopa ce kin ga sai mu fara binciken inda zamu ganta, Idan Allah yasa muka gano ta sai mu yi ƙoƙarin tattara makullan da muka rasa!"

Angel ta gamsu da bayanin da batul ta yi mata.

"Kina ganin mu tayar da su daga bacci yanzu ko mu bari sai gobe da safe"? Batul ce ta jefa mata tambayar.

"Wani irin gobe? ai yanzun nan zamu farkar da su, Babu zancen 6ata lokaci, zuciyoyin mu da fargaba su ke buga wa, duk daƙiƙa ɗaya na rayuwar mu a tsorace mu ke yin shi don haka bamu da lokacin 6ata lokaci, wannan dama ce agare mu, ba zamu yi wasa da ita ba, dama tsohuwa tamira ta faɗa mana cewa Ba zamu fahimci me ta ke nufi ba sai nan da wani lokaci da muka fita hayyacin mu, wasu ma su ka rasa ransu, A yanzu mun rasa mutun biyu, bamu da tabbacin ma Ƴan uwan mu maza da aka ɗauka zasu dawo mana da su dukkan su ba tare da an samu wanda ya rasa ran shi ba acikin su, fita hayyaci kuma mun yi sau ba adadi, Yanzu ne yakamata mu nema wa kan mu mafita tun kafin su ƙarar da mu don inaji araina Bamu ga komai ba, domin kuwa har yanzu muna a TAKUN FARKO na kurkukun ƙaddara, Idan har muka kai TAKUN TSAKIYA a cikin Kurkukun nan ba tare da mun ku6uta ba, bana tunanin za'a samu rai ɗaya da zai rayu acikin mu In ba wani iko na Allah,' muryarta asanyaye ta ƙarasa maganar, Batul da ke sauraronta ganin ta ƙare maganarta yasa ta yunƙura ta miƙe tare da cewa"Ki taso muje mu tashe su daga baccin"! Miƙewa Angel tayi tare da kallonta.

"Batul duk wani motsi namu akan idon su! Dole sai mun yi takatsantsan idan ba haka ba Garin neman gira zamu rasa ido.

"Ya zamu Yi kenan"? Acewar batul
Angel tace"Ni aganina, mu kashe hasken ɗakin mu wata'ƙil idan mu ka yi hakan ba zasu Iya ganin mu ba, Sannan Ba kowa zamu tayar daga bacci ba, Mu za6i kamar mutun uku sun isa, Kinga mun cika mu biyar kenan, Sai mu ji ra'ayoyinsu."

"Ni nafi tunanin atada su duka saboda kowa da irin baiwar da Allah ya yi mashi, musamman Azeeza da Deeja ga kuma Parveen sannan Hannah bayan ita sai sarah zata taimaka mana Tunda tana da tsawo sosai wani abun da ba zamu Iya hangowa ba zata iya hango shi.

Girgiza kai Angel ta ɗanyi"Gaskiya baza a tada azeeza ba, kinmanta bata gani idan dare yayi? Ita kuma Jamimah tayi ƙaranta ba abunda ta sani"

"Shikenan, Zan je na kashe hasken ɗakin, Kafin mu dawo tare dasu Ki Buɗe ƙofofin kowani toilets saboda mu samu hasken Fitilun da ke a cikin su Ya haskaka sashen,'
Angel ta amsa mata da toh, Juyawa batul ta yi tare da fuce wa daga Cikin sashen.

Ajiyar zuciya Angel ta sauke tare da kifa kanta Jigin bango tana jiran dawowarsu, Ɗuff Taji hasken ɗakin su Ya ɗauke duhu ya gauraye ko'ina, A hanzarce ta lalubi ƙofofin Toilets ɗin ta buɗe su duka, Hasken Fitilun cikinsu Ya haskaka Sashen Duk da bai wadata sosai ba"

Jin motsin shigowar su Yasa ta yi saurin fuskantar su, sai faman murza idanuwansu su ke da yatsun hannayensu, Parveen sai hamma ta ke Yi bakinta hada miyan bacci.

"Sai da nace maki ban da Azeeza meyasa kika tado ta"? rai a6ace ta yi maganar idonta akan Azeeza, da Batul ta ruƙo hannunta

"Bani na tada ta ba, Ina cikin tada su Deeja ta farka tana Jin fitsari shi ne na ruƙo hannunta muka shigo atare" mayar da idanuwanta tayi akansu, Kusan su dukane banda Jamimah ita kaɗaice basu Tada ta ba, tana can ƙudundune Cikin bargo saman shimfiɗar su.

"Wai lafiya aka tayar da mu daga bacci? Ko an kawo abinci ne"? Parveen ce ta yi tambayar fuskarta a yamutse,

Harara Angel ta watsa mata"Halan mafarkin shi ki ke cikin Yi aka tada ki, shiyasa kike tambayar ko an kawo abinci" Kwa6e fuska ta yi ba tare da tace komai ba, Sai faman murza ido su ke yi, fuskokin su a tur6une.

"Hakanan muna yin baccin mu mai daɗi an tada mu," hannah ce ta yi maganar tana murgaɗa ƙaramin bakinta.

Jan hannun Azeeza Batul ta yi zuwa cikin toilet su ka shige.

"Ganin Yadda su ke ta kwa6a magana ransu a6ace saboda an katse masu bacci, har suna cewa ta tsare su da ido, idan ba abunda zata gaya masu zasu koma ɗaki su kwanta ne" Har sun yunƙura zasu Juya muryar batul ta katse masu hanzarinsu da cewa"AN SAMU ƘOPAR DA ZAMU GUDU" A ruɗe Suka dakata da yin tafiyar suna kallonta, tamkar saukar aradu Haka maganar ta dirar masu acikin kunnuwan su, wani irin kallon rainin wayau su ke binta da shi, ƙarasa fitowa ta yi daga Cikin toilet ɗin hannunta ruƙe dana Azeeza.

"Idan ku ka natsu zamu Yi maku bayanin komai" ga dukkan alamu sun shiga ruɗani duba da irin kallon da su ke yi mata.

"Wannan maganar daga jinta a cikin mafarki ake yinta ba'a gaske ba" Hibba ce ta yi maganar, idanuwanta kamar na mashayin giya.

Sarah tace"Nima nafi tunanin mafarki ne mu ke yi, idan har ta tabbata dagaske mu ke ganin batul da ta yi maganar to kuwa tabbas Ganyen da muke ci ya fara zautar da ita, shiyasa ta fara mana sambatu"
Sarah na rufe baki Hannah tace"ni bazan tsaya sauraron wannan shirmen ba, Kun ga tafiyata"

ta yi magnar tare da nufar ƙopa zata fuce da sauri batul ta saki hannun azeeza tai wuff ta ruƙo wuyan rigar Hannah ta janyo ta tare da dawo da ita ta jinginar jikin bango.

Angel ta kasa kunne tana sauraron su, gani ta ke kamar ba za su iya fahimtar su ba koda ace sun faɗa masu, saboda basu ɗauki abun serious ba.

"Kun tasa mu agaba kuna kallo kamar kun samu madubi, idan ba za ku buɗe baki ku yi magana ba, Ni zan koma ɗaki" acewar Rubina.

"Ki yi masu bayani mana ko ni zan yi masu"? Batul ce ta yi ma Angel magana.

Gyaran murya tayi Kafin ta sassauta muryarta ta yadda sautin ba zai fita sosai ba, kamar maiyin gulma, ta soma fayyace masu komai dangane da hasashen da su ke yi akan Kalaman tsohuwa tamira.

Sun natsu suna sauraronta, Yadda suka tattara hankulan su akanta sai ta yi tsammanin ko sun Fahimci inda zancen nata ya dosa ne, sai da ta kai ƙarshen Maganar, kusan atare suka haɗa baki wurin jan tsoki.

"Kawai don ta yi kalami sai asamu ƙofa, sai ka ce ba ku san wacece tsohuwa tamira ba, In banda ma rainin wayau taya za'ace mune makullan buɗe ƙopa? Ƙanzon kure ge ne wannan" Parveen ce ta yi maganar tana hura hanci ita ala dole an 6ata mata rai.

"Da nasan abunda zaku gaya mana kenan Allah da ban farka ba lokacin da batul taje tada ni daga bacci" acewar Eve

"Ni dama kwanakin nan ban yarda da ku ba, Ku biyun nan Batul da Angel, damuwa tasa kun fara zaucewa," Yasmince ta yi maganar , kamar zasu rufe su da duka Kowa Da abunda ya ke furtawa, Mutun Biyu ne a cikin su basu yi magana ba, Deeja da ta jingina kanta Jikin bango ta lumshe idanuwanta sai Azeeza da ke a tsaye bakin ƙofar toilet, Ta kasa kunne tana sauraronsu duk bata ganin su.

"Koda ace baku yarda da maganar mu ba, Inaso ku bamu dama, Mu fara neman ƙofar da ke a cikin ɗakin mu. Idan ba'a ganta ba ni na yarda Ku yi min duk abunda ya dace dani," cikin sanyin murya Angel tayi masu maganar.

"Deeja! Banji kince komai ba? Ke baki faɗi naki ra'ayin ba, dangane da kalaman tsohuwa Tamira,"

Daƙyar deeja ta iya buɗe idanuwanta masu ɗauke da bacci ta ɗaura su kan fuskar Batul da ke Yi mata magana, da buɗar bakin ta sai cewa ta yi"Oh wai da ba mafarki bane? Baki asake Take kallon su, Dafe kai batul tayi da hannu ɗaya"Wai meye haka? Idan har ba ku ɗauki maganar nan serious ba kun bamu haɗin kai tayaya zamu Iya ganin ƙofar...."

Tun kan ta ƙarasa maganar Rubina tace"Ae ba za ku ta6a ganin ƙofa ba, hasashen ku akan kalaman tsohuwa tamira Wasiƙar jaki ce wadda bazata ta6a zama gaskiya ba, in banda wahalar da kai ta ya tsohuwa Tamira zata Taimake mu? Ku yi amfani da kwakwalwarku mana, koda yake dama ba cikakken hankaline damu ba, " Murmushin takaici Angel tasaki Jin abunda Rubina tace, wato dama basu da cikakken hankali.

Muryar azeeza ce ta janyo hankalin su ga kallonta.

"Ni ina goyan bayan maganarsu Angel, tsohuwa tamira tana son taimakon mu, kafin tabar cikin mu, Ta yi mana abubuwan da zata faranta mana rai wanda ke nuni da za ta yi kewar mu sanna ta faɗa mana cewa tana so wata rana mu tuna da ita acikin rayuwar mu, duk mutumin da ya furta maka wannan kalami dole asamu ƙaunarka da tausayinka acikin zuciyarshi, yakamata muyi nazari sosai, Koda ace bazamu yarda da maganar su Angel ba dangane da hasashen su akan kalaman tsohuwa, Kada muƙi bin maganarsu Mu jaraba duba ko'ina na cikin ɗakin, kafin mu yanke hukunci, Sannan inaso na tuna mana wani abu, kamar yadda Angel ta faɗa mana ba'a ganin wanda ya halicce mu, That mean idan zamu samu taimako daga wurin shi ba kai tsaye zai bayyana ba don ya taimake mu, sai dai Ya haɗa mu da wanda zai taimaka mana, ko ya fahimtar damu ta wata hanyar Kamar dai yadda Angel tayi mafarki da kalaman tsohuwa tamira.........." tun da Azeeza ta soma Yin magana Hankalinsu ya dawo kanta, Ko ƙyafta idanuwan su basa yi, Sun natsu suna sauraronta, Musamman Angel tsabar mamaki yasa ta saki baki tana kallonta, Yarinyar Allah ya yi mata baiwa, Ita takasa fahimtar dasu yadda zasu gane sai gashi kalaman Azeeza sun yi ta'asiri acikin zukatan su.

Nauyayyiyar ajiyar Zuciya kowan nan su ya sauke, sarah tace"yanzu abunda za'ae mu fara neman ƙofar! idan Allah yasa aka same ta sai mu fara tunanin ta yadda zamu tattara makullan buɗeta,"

Atare suka haɗa baki wurin cewa"Haka Ya dace, "
"ita fa azeeza da bata gani? Ko dai in kai ta ɗaki ta kwanta"? Deeja ce ta yi maganar.

Tun kafin Wani ya bata amsa Azeeza ta bubbuga ƙafafuwanta Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"wlh ba in da zan je, dani za'ayi komai kawai don anga bana Iya gani shine za'a ware ni" ganin zata ja masu hayaniya yasa Angel yin saurin kai hannu ta janyota zuwa jikinta, ta rungumeta tana faɗin"Its okey azeezata, Ai dole ma ayi tafiyar nan da ke, kwantar da hankalin ki" ajiyar zuciya azeeza ta sauke tare da sanya hannayenta Biyu ta ƙanƙame Angel.

"Kafin Mu fara bincike, Yakamata Mu fara Yin addu'a akan Allah ya bamu Ikon ganota Cikin sauƙi," Angel ce ta basu shawarar Yin hakan, atare suka ɗaga hannayen su Sama ta dinga jera masu addu'o'i suna amsa mata da ameen, bayan sun kammala Hibba tace"Bafa lallai yakasance ƙofa ta ke nufi ba, A kalamanta, " Batul tace"ae shiyasa zamu fara dubawa, Kunga idan ba'a samu ƙofar ba, sai muyi wani tunanin na daban"


Gyaran Murya Angel ta yi Hankali ya dawo kanta.

"Zamu Raba kan mu wasu zasu shiga toilets, wasu ɗaki, Amma na ɗaki dole su ɗaga gadajen mu, don ina hasashen ƙofar ta sirri ce, ta in da bamu tsammani zamu Iya ganinta, don haka mu sanyawa ran mu cewa har cikin Tukunyar fulawa zamu Iya samunta, kota jikin bango, kota ƙarƙashin gado, kai harma ta inda ruwa ke bi ya wuce, amma fa Wanda zasu duba Ƙarƙashin gadajen mu dole su yi taka tsantsan saboda ana ganin duk wani motsin mu, don haka Na ɗaki mu bari sai gobe zan shirya mana wasan Ƴar 6uya, zamu dinga shigewa da sunan mun 6oye kunga zasu yi tsammanin wasa muke Yi, ba wani abu muke nema ba"

Murmushi su ka saki gaba ɗayan su, kafin daga bisani Batul ta rarrabasu zuwa gida uku, Nan fa suka baza cikin toilets ɗinsu suna neman ƙofar nan, Angel tana ruƙe da hannun Azeeza saboda makantarta, Uban gumi suka haɗa akan fuskokin su, Sun bada himma sosai, wurin neman ƙopar ba inda basu ɗaga ba, hatta tukunyar fulawar da ke a toilet ɗinsu saida batul da Deeja suka haɗa ƙarfi wurin ɗaɗɗagota amma basu ga komai ba, Bangon da aka jingine ta dashi ashafe Ya ke haka ƙasantama Ashafe Yake babu wata ƙofa, Kamar zasu fashe da kuka su ka sauke tunkunyar, furennin cikin ta ma duk sun bushe babu mai lafiya, Ko'ina Ciki da bai na sashen toilet ɗinsu saida suka bincika amma babu ƙopa, A ƙarshe sarah Ta hango masu Tagogin nan da ke a saman ceilling waɗanda tun farkon zuwan Angel ta yi tozali dasu a garƙame da kwaɗo, Kowani toilet akwai tagogin saman ceilling guda biyu, hankalin su gaba ɗaya ya karkata akan tagogin ransu ya gama basu cewar Za'a samu hanyar da zata 6ullar da su wajen kurkukun, Sai dai basu san ta yadda zasu Iya kaiwa gare su ba saboda basu da tsauni tsayin su kuma ba zai kai su ba, hatta Sarah Da tafi su tsawo bazata Iya koda ɗaga hannu ta ta6a jikin su ba, Bayan haka kuma basu da Makullin da zasu Iya buɗe tagogin, daga bisani tunani su ya canza akan Su nemo makullan buɗe tagar, A daren ranar basu koma bacci ba, Saboda Aikin neman makulli, Sunci baƙara wahala ga bacci a idonsu amma Sun nace akan neman makullai, wasa wasa har Gari Ya waye suna aikin neman makulli, A ƙarshe da su ka galabaita, don dole suka haƙura, Ga yunwa suna Ji ga bacci a idanuwansu.

A saman floor na sashen toilets ɗinsu, Kowan nan su Ya samu wuri ya zauna suka

Please Login or Register in order to submit comment