Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ruɗe ta nufi gadon majnoon ganin daskararren jini asaman shimfiɗarsh, hannayenta biyu ta ɗaura saman bargon shi, yayin da zuciyarta ke tafarfasa.

Muryar Hannah na rawa ta furta"INA MAJNOON YA KE? JININ MENENE MU KE GANI A SAMAN SHIMFIƊAR SHI, DAN ALLAH KADA KU CE MANA YA MUTU SHI MA"!

Babu wanda ya iya buɗe baki ya basu amsa, hakan yasa su ka fahimci cewa Majnoon ya mutu babu shi, hawaye ne masu ɗumi su ka wanke fuskokinsu, A saman shimfiɗarshi Parveen ta kifa kanta da ke sara mata da ciwo, ta dinga kuka tamkar ranta zai fita, bakomai take tunawa ba face Irin rayuwar da su ka yi dashi, ta yi matuƙar tsaya mata arai, ta yi danasanin duk wani bugu da ta yi mashi, tun ranar farko daya fara kasancewa a cikinsu, Ya 6arar masu da Cake, Tana matuƙar son yaron tsanar da ta yi mashi a lokacin saboda 6arnar da ya ke yi masu ce, ɗago da hannayenta tayi tare da ɗaga su sama tana kallon fingers ɗin ta da ke kerma, Hawaye jaga jaga akan fuskarta, sautin kukanta ya cika ɗakin nasu, Muryarta da wani irin sauti ta ke faɗin"YA ALLAH KA ƊAUKI RAINA IN HUTA! BAZAN IYA JURAR TASHIN HANKALIN NAN BA! Bana fatan na sake yin tozali da gawar wani a cikin ƴan uwana, So nake na mutu in huta, Narasa Majnoon abokin Faɗa na ga Unaiza ma ta tafi tabar mu da kewarta, wayyo Allah nah! ' sosai ta rushe masu da kuka, kamar mahaukaciya haka ta cusa hannayenta cikin sumar kanta, ta dinga hargitsa gashin cikin ƙunar rai, kafin ta mayar da kanta saman mattress ɗin Majnoon.

Duk suna jin sautin kukanta, Jikin su duk ya yi sanyi, mutuwar mutun biyun nan ta raunata zukatan su, ta sagar masu da gwiwarsu, komai ya fita aran su, babu mai sauran walwala acikinsu, ba don zuciyar Imani ba da tuni wasu daga cikin su sun zauce, musamman Azeeza ta shiga halin ha'ula'u, tsoro da firgici sun hana ta sak, har zufa ke tsastsafo Mata saman goshinta, tun da ta farfaɗo daga suma ta zauna ko motsi ta gaza yi sai dai tabi su da ido.

Miƙewa tsaye Sarah Ta yi jikinta kamar zai 6alle, saboda rashin kuzari, fuskarta a bushe muryarta asanyaye ta soma magana"Idan har mu ka cigaba da zama ba tare da mun ɗauki mataki ba, za'a cigaba da yi mana ɗauki ɗai ɗai ne ana kashe mana rayuwa, Yakamata musan abun yi, wlh na tsorota Na firgita da ganin irin mutuwar da Unaiza ta yi, Tare da ita fa aka kawo mu cikin ku, bazan ta6a manta farkon gani na da ita ba, ban ta6a tunanin cewa zan shaida mutuwar ta ba, na girgiza sosai, please na roƙe ku, idan zaku iya ku kashe ni zaifi min kwanciyar hankali akan aƙara zuwa a ɗauki wani acikin mu, saboda na fahimci cewa rayuwar mu bata da amfani awurin su, mutuwa ta zamar mana dole yanzu ma aka fara yinta, bansan wanene next zai mutu ba, bana so na gani shiyasa nake so in mutu................" daƙyar ta ƙarasa maganar, saboda raɗaɗin da ta ke ji a cikin zuciyarta, miƙewa tsaye Hannah ta yi, idanuwanta jawur dasu ta soma magana tana fuskantar sauran ƴan uwan nasu da ke a zazzaune ƙasa

"Meyasa har yau Allah bai dube mu ba? Mu ma fa bayinsa ne kamar kowa, Angel ke da kan ki kika faɗa mana cewa wanda ya halicce mu yana sane damu, but why mu ke fuskantar irin wannan tashin hankalin? bawani mai taimakon mu, sau nawa muna hana idon mu bacci don mu kai kukan mu agare shi, amma shiru...!

Hankalin Angel ba ƙaramin tashi yai ba, jin maganganun da Hanna ke yi, duk da matsanancin halin da ta ke a ciki sai da ta girgiza, ganin sun soma ƙoƙarin kauce hanya, dama ba wadataccen ilmin addini gare su ba, ba lallai bane a yanzu da suka fara fuskantar tashin hankalin nan su iya jurewa ba, saboda suna da raunin imani da tawakkali, a haka ma sunyi ƙoƙari saboda basu ta6a ƙaryata maganar ba, sai dai awannan karan tana tsoron Su juye mata su canza ra'ayinsu.

Runtse idanuwanta ta yi sosai tare da cusa kanta a ƙirjin batul, ba ta yi tsammanin zata samu sauran hawaye a cikin idanuwanta ba, sai gasu sun soma tsastsafowa saman kuncin ta masu ɗumi.

zuciyar batul ba ƙaramin karaya tayi ba, Jin yadda Jikin Angel ya yi zafi sosai, tasan dole taji raɗaɗin a cikin zuciyarta,' ƙara ƙanƙameta ta yi a jikinta, hannayenta asaman sumar kanta, A hankali take shafa sumar Angel tana lallashinta, zuciyarta tamkar ta fashe saboda ƙunar da ta ke yi mata, gudun kada ta zauce ta rasa madafa, yasa ta soma furta duk wasu addu'o'i da tasan zasu kwantar mata da hankalinta.

A yayin da ta ke yin addu'o'in idanuwanta suna arufe, sosai ta matse su, tana jiyo muryar Yasmin tana faɗin

"Angel Kin yi shiru baki bamu amsa ba, har yaushe ne zamu tsara Jiran taimako daga wurin Allah! Kina ganin mun fara mutuwa, tsoro da firgici kaɗai kaɗai sun isa su sa mu zauce, Mun yi tunanin cewa idan muka kar6i addinin ki, Mu ka yi Imani da Allah, komai zaizo mana da sauƙi, Amma shiru sai ma ƙara shiga tashin hankali da mu ke yi, lokacin da kika zo cikin rayuwar mu Ba ki ji daɗin da mu ka ji ba, saboda alƙawarurrukan da kika ɗaukar mana na cewa Zaki taimaka mana wurin ganin mun ku6uta daga cikin kurkukun ƙaddarar nan, Ki ka sanya mana kwaɗayin son yin rayuwar ƴan ci kalar wadda ki ka yi awaje, Meyasa angel muke ganin ba dai dai ba? Idan da ace kinsan ba zaki iya taimakon mu ba, meyasa kika sanar damu hakan? Kuma kika bamu labarin rayuwarki har muka sanya rai da yin irinta........"

Yasmin bata ƙarasa maganar ba, ta rushe da kuka, Hankalin Angel idan yai dubu to ya tashi, Dama fa dole ta fuskanci wannan matsalar, cos itace mutun ta farko data fara sanar dasu komai agame da mahaliccin su, Nauyin komai ya rataya akan wuyanta! Duk idan su ka ji ba daɗi dole ita zasu tunkara, to ayanzu dai mutuwar Unaiza da Majnoon ta kwance notikan kawunansu, sun fara tsorota shiyasa su ke waɗannan maganganun.

"Angel idan har akwai abunda ya rage mana wanda ba mu yi ba dangane da addinin ki, to ki faɗa mana shi don muyi wata'ƙil Allah zai ji ƙanmu ya tausaya mana, ya dube mu da idon rahama ko mun samu mu tsira da ranmu!" Eve ce ta yi maganar, Duk sun mimmiƙe tsaitsaye Agaban Batul da ke a rungume da ita, sai ƙara tighting ɗinta ta ke yi a jikinta, ita kanta batul ɗin hawaye ne sharkaf akan fuskarta, cigaba da ambaton sunan Allah ta yi acikin zuciyarta, tana roƙonshi akan ya basu bafita kada yasa su ga gazawarta.

"Angel Mun san kina sauraron mu, kin yi shiru ba ki ce komai ba, kada ki sanya mana kokwanto A cikin zukatan mu, Mun yarda dake, Munsan kina ƙaunarmu, kuma kina son Farin Cikin mu, don haka Muna jiran amsar ki me ya rage mana wanda ba muyi ba a cikin addininmu wanda zaisa Allah ya jiƙan mu......" Cikin rauni na murya Hibba ta yi maganar, daga ganin fuskokin su a matuƙar tsorace suke.

Angel tana a cikin tsaka mai wuya, ta kasa ɗago da idonta ta dube su, saboda bata da ƙwarin gwiwar yi masu magana, to me zata ce masu? Itama fa A tsoroce take da abunda ya faru na mutuwarsu Unaiza.

Muryar Rubina a hargitse tace"Babban abunda nake jimawa, Ƴan uwan mu da aka kwashe Shin suna araye ko sun mutu, bamusan a wani hali su ke aciki ba, Tun da yanzu mun fahimci cewa kashe mu ake yi, Lalata rayuwarmu ake yi a kwashe wani sashe na jikin mu! Kamar yarda aka yi ma Unaiza, Da Majnoon......." Bugun zuciyar Angel ne ya ƙaru tunawa da Mazan su da aka kwashe, ba ita ba Hatta su Deeja damuwace ƙarara akan fuskokinsu, Tabbas Suna fuskantar barazana a cikin rayuwarsu.

"baƙin Cikin da mu ke ƙunsa da barazanar da muke fuskanta sun isa su sa zuciyoyin mu su buga mu mutu" Eve ce tayi maganar tana faman huci, idanuwanta a zazzare, ruwan hawaye ne kwance a cikinsu. Kowa Yana tofa albarkacin bakinsa, mutun biyar ne basu tanka ba, sai da su ka yi mai isar su tukunna Deeja ta miƙe cikin kakkausar murya ta soma magana tana duban kowan nan su.

"Na yi mamakin jin maganganun da harsunan ku su ke furtawa, saboda abun da ya faru ne yasa ku ke kokwanto Akan Addinin da Angel tazo mana dashi, Kun bani kunya duk da na fahimci cewa ba'a cikin hayyacin ku kuke ba, banaso mu yi abunda zamuyi danasani acikin rayuwar mu, Angel ba ita bace silar halin da muka shiga ba, Akan me za ku dinga ɗaura mata nauyin komai akanta! Yarinyar nan fa ƙanwar mu ce, babu wanda bai girmeta ba a cikin mu...."

Numfasawa Deeja ta yi a yayin da take bin fuskokin su da kallo.

"Ya ku ke so tayi da ranta ne? Kalaman ku zasu iya sanyawa ta zauce, itama fa tana jin raɗaɗin da mu ke ji, saboda ta ɗaurawa kanta nauyin kula da rayuwar mu, so ku ke ku ƙara sanya mata damuwa har zuciyarta ta buga mu rasa ta? Meyasa za ku yi kokwanto akan addinin da tazo mana dashi? Saboda kun ji shiru har yau Allah bai kawo mana ɗauki ba? Ƙaddarar mu ce tazo a haka, ba lallai bane mu moriya rayuwar duniyar nan ba, amma ku tuna abunda Angel ta faɗa mana, ko kun manta ne, zai iya yiwuwa namu jin daɗin ba anan yake ba, sai ranar da muka koma ga mahaliccin mu! Itafa wannan rayuwar duniyar ƙanƙanuwa ce jin daɗinta na wucin gadi ne, kowa zai mutu ne, damu da wanda ke rayuwa awajen kurkukun nan da waɗanda suka azabtar da rayuwar mu, kaf zamu koma agare shi ne, mutuwa dole ce, zamu mutu zamu koma ga Allah, za'ayi mana hisabi tsakanin mu dasu! Allah zai bi mana haƙƙin mu, zasu ɗanɗani kuɗarsu, Ai mu abun farin ciki ne agare mu, Haƙƙinmu ya rataya akan wuyan waɗanda suke sarrafa rayuwar mu, don haka daga yau bana son wani ya ƙara yin kukan mutuwa acikin mu, Mu sanya wa ranmu cewa dole mu rasa wani acikin mu, ko muna so ko ba mu so, dole mu mutu, Mu zama masu tawakkali kada mu butulce wa Ubangijinmu, Abun da na fahimta wanda ba lallai bane ku fahince shiba, Allah shine ya ƙaddara zuwan Angel a gidan kurkukun nan donta sanar damu komai agame dashi, yanzu mu musulmai ne, kuma munyi imani da Allah, don haka babu gudu babu ja da baya, Duk runtsi duk wuya kada mu kuskura Mu rasa ƙwarin giwar da mu ke da shi, tsakanin mu da Angel sai godiya, Allah ya saka mata alkhairi, Allah ya bata ikon cigaba da taimakon mu...."


Kalaman Deeja sun sanyaya zuciyar Angel, Jikin kowan nan su Ya yi sanyi, sun yi danasanin maganganun da suka soma gaya mata, kusan atare suka haɗa baki suna bata haƙuri haɗi da lallashinta, hakan ba ƙaramin kwantar mata da hankalinta yayi ba, har lokacin bata ɗago da kanta daga saman ƙirjin batul ba'

Deeja tace masu su share hawayensu, Su yi rayuwar su tamkar babu abunda ya faru dasu, suka masa mata da toh, Duk da sun san abune mai wuya su dawo kamar yarda suke ada, A ranar sun ɗan samu sunci abincin Da Jamimah ta ajiye masu a cikin kwando, Bayan sun kammala ci, Kowan nan su ya yi wanka, A saman gadajen su suka kwakkwanta, zuciyoyin su a ƙuntace.

Rayuwar prisoners ta zama abun tausayi Cikin kwanakin nan, jimamin rashin ƴan uwansu ya hanasu sakat, Babu wasa babu dariya, kullum fuskokin su a bushe su ke, abu ɗaya ne su ke yi su ji daɗin shi, su kuma samu natsuwa da kwanciyar Hankali, Karatun qur'ani da Angel ta ke yi masu tsakar dare, a lokacin da take samun damar yin shi murya abuɗe ba tare da ta samu targarɗa ba, tasha ware kanta ita kaɗai, Ta ke6e a sashen toilet ɗinsu, ta ɗaga hannayenta sama hawaye nabin fuskarta, ta dinga roƙon Allah akan ya taimaka mata, kada yasa taji kunya a idanuwansu, ya agaza masu yajiƙan su, Ya kawo masu mafita ko dan taci ka masu alƙawarin data ɗaukar masu na ku6utar dasu daga Cikin kurkukun ƙaddara!

Ta zama abun tausayi, ga duk mai imani idan yaga yadda ta ke roƙon Allah sai ya matse mata ƙwalla. dukkan wasu ladubban yin addu'a ta iyasu, Saboda an koyar da ita, mutun biyun nan sun bata gudummuwa a cikin rayuwarta, shiyasa bazata ta6a mantawa dasu ba, mutun na farko Mahaifinta Tajuddeen, nagartaccen uba wanda ya tsaya mata tsayin daka don ta nemi duniyarta da lahirarta, lokacin da Unaiza ta bata labarin nata uban daya tarwatsa rayuwarta, sai taji ta ƙara ƙaunar daddynta, kuma har aranta taji cewa Mahaifinta bazai ta6a iya sadaukar da ita ba, ɗan adam ba abun yarda bane, amma ita ta yarda dashi har cikin ranta, saboda tasan halin daddynta ita shaida ce akan shi, ko dabba bazai Iya sadaukar ba balle ita da ya ɗauke ta tamkar ranshi! Mutum na biyu da bazata ta6a mantawa ba, ANEELERH CE, matsayin da ta bata a cikin zuciyarta na mahaifiyarta ne data gudu tabarta, Aneelerh uwace ta gari agare ta, dayawa wasu abubuwan da Angel ta iya da suka shafi addini da rayuwar duniya, Aneelerh ce ta koyar da ita su, hatta karatun makaranta idan aka yi mata, Aneelerh ce ke ƙara koya mata shi idan daddynta bai nan, Tana matuƙar son aunty aneelerh, kuma bata zarginta cikin waɗanda su ka sadaukar da ita! bayan aunty aneelerh da daddynta babu wani shege da take tunanin zata ɗaga ma ƙafa, muddin ta fita daga cikin kurkukun nan sun shiga uku, Hatta hajiya Adama da uncle Abdallah, da Alhaji ubaid kakanta, da maigadin gidansu, da abokan dadynta na wurin aiki, da makwabtan dake a kusa da gidansu kaf ɗinsu abun zargine awurinta, Ba wanda ta cire a cikinsu, dama kawai take jira ta samu, duk wani mai hannu acikin sadaukar da su, sai ta binciko su, alwashine ta ɗaukarwa kanta, shiyasa bata son ta dawwama agidan kurkukun saboda idan har tana aciki bazata ta6a Iya gano su wanene shuwagabannin kurkukun ba, Dole sai tana awaje zata samu damar gano munafukan, ta ci buri akan su, musamman mahaifin Unaiza JAN WUYA, wannan ɗan tahalikin duk ranar daya bari Angel ta dira ƙafarta daga cikin kurkuku, sunanshi matacce, muddin ta gano shi.

Tuntuni Angel ta ɗauko Jotter ɗin unaiza da ta ajiye mata a cikin toilet ɗinsu, tare da pant ɗin data bata kyauta, tana matuƙar son pant ɗin musamman da ya fito daga hannun Unaiza, yanzu haka pant ɗin yana sanye a jikinta ko wanke shi ba ta yi ba, saboda ta shaida tsaftar da ke a jikin shi, daga gani ranar da za'a kawota kurkukun ta sanya shi a jikinta, saboda sabuntakar shi. a cikin backpact ɗin Unaiza ta sanya jotter ɗin tare da biro din duka ta tura su ciki ta zage zip ɗinta, tana fatan Allah ya bata damar isar da wasiyyarta.

Bayin Allah sun zubama sarautar Allah ido, almost two month Yau, babu labarin su Haris, Danish kuwa yafi kowa daɗewa don Yana acikin wata na uku da aka tafi dashi, tsakaninsu dasu addu'ace wadda ba fashi, kullum ne sai sunyi masu ita tare da waɗan da su ka rasu.


💔PRISONERS💔

Wuraren marece, Angel tana kwance saman gadonta, ta rungume pillow a ƙirjinta, ba zaka ta6a gane awani hali ta ke a ciki ba, ta lumshe idanuwanta tamkar mai yin bacci, Azeeza ce kwance a gefenta saman gadonta, Jamimah tana asaman bayanta ta haye ta ɗaura kanta, sun zamar mata alaƙaƙai, Kullum suna atare da ita, tana matuƙar son jinsu a tare da ita, babu mai yin magana a cikinsu, Parveen tana a kuɗundune cikin bargo saman gadon majnoon, kullum nan take kwana, da hannunta ta wanke jinin da ke abargon shi, ta gyara gadon taci gaba da kwana saman shi, saboda ƙaunar da ta ke yiwa majnoon ɗinta, wani lokacin har pillown shi ta ke yi ma wasa a matsayin majnoon kamar mai ta6in hankali.

Sarah na a zaune saman shimfiɗarta tare da Hibba da eve sai yasmin da rubina, babu mai magana acikin su duk sun yi zugudum, Deeja tana a kwance saman gadon Haris idonta na fuskantar ceilling, kowa dai da abunda ke damun shi, itama Hanna tana a naɗe saman gadonta.

Saukowa batul ta yi daga saman gadonta, Ta nufi sashen toilet ɗinsu, ba tare da kowa Ya ankara da ita ba, shigarta ke da wuya Angel ta buɗe idanuwanta muryarta asanyaye tace da jimamah ta sauka zata miƙe, zame jikinta ta yi daga na jamimah ta sauko daga saman gadon, Jikin ta duk ba ƙwari ga ramar da ta yi.

Sashen toilet ɗinsu ta nufa, tana shiga ta soma jin shessheƙar kukan batul, Hankalinta yai mugun tashi, bata zo da niyar tabi bayanta ba, tunawa da furennin dake a cikin tukunyar fulawar nan ne yasa ta zo sashen makewayin nasu, tun bayan rasuwar Unaiza babu wanda ke ba furennin ruwa saboda halin da su ka shiga, Cikin sanɗa ta nufi ƙopar toilet ɗin da batul ta shiga, A hankali ta tura ƙopar tare da Leƙa kanta ciki, karaf idanuwanta su ka sauka akan Batul da ke ta faman leƙa cikin wandonta da ta zame kamar wani abu ta ke dubawa,

Jin motsin shigowar mutun yasa ta firgice ta ɗago da idanuwanta fuskarta sharkaf da hawaye suna haɗa ido da Angel tasha jinin jikinta, da sauri ta gyara zaman wandon jikin ta.

"Batul me ya ke damun ki? Na jiyo shessheƙar kukan ki ne," wahalallan yawu ta haɗi, ba tare data furta mata komai ba.

Hakan ba ƙaramin ɗaga ma Angel hankali yai ba, fargabarta kar ace wani abu ne ya sami gabanta shiyasa ta ke kuka

"Ƴar uwata rabin raina, dan Allah ki faɗamin meke damun ki, Na yi maki alƙawarin bazan faɗama kowa ba, Hankalina ya tashi dana ga kina duba wandon Jikin ki, ina tsoron ace wani abu ne ke damun ki"

Ta ƙarasa maganar yayin da take nufar batul, girgiza mata kai ta dinga yi muryarta Ƙasa ƙasa take faɗin"Kada ki matso kusa dani Angel, babu abunda ke damuna, lafiyata qalau....." adabarbarce ta yi maganar.

"ƙarya ki ke yi min batul! Wai har ni zaki 6oye ma abunda ke damun ki? Me ki ka ɗauke ni ne? Nifa ƴar uwarkice, idan baki faɗamin ba wa zaki faɗa mawa, ni dama tun da aka dawo mana dake ban yarda dake ba, meyasa zaki 6oye min abunda su ka yi maki"? Fuskarta a ɗaure ta yi maganar, kafin taci gaba da cewa"Allah yajiƙan unaiza ba ta mutu ba sai da ta sanar dani komai daya faru da ita, don haka ki daina 6oye min, idan har kina son zaman lafiya to ki faɗamin me aka yi maki!! Cikin shessheƙar kuka batul tace"nifa ba abunda ya faru dani, ki daina tambayata bana so ki tafi kawai," Jinjina kai Angel tayi tare da sassauta muryarta"Its ok xan tafi batul tun da baki so in sani," Ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta nufi ƙopar fita, ajiyar zuciya batul ta sauke duk a tunaninta Angel tafiya zata yi tabar toilet ɗin ashe ƙopa ta je ta rufe don kada sauti Ya fita, jamlock Ta sanya ta datse ƙopar da kyau, fuskarta a ɗauke ta juyo ta kalli batul dake manne jikin bango, jikinta sai kerma yake yi

"Zaki Faɗamin meke damun ki ko kuwa kin fi so in bi ta ƙarfi"! Shiru batul bata tanka mata ba, sai faman zazzare mata idanuwanta take Yi, Cizon le6e Angel tayi tare da naɗe hannun rigarta, gadan gadan ta nufi batul, ganin tana tunkarota yasa batul ta bar jikin bangon ta watsa da gudu da niyar ta fuce, Cikin rashin sa'a Angel ta cafko Sumar kanta, ta janyota da ƙarfi ta maka ta jikin bango ta yadda bazata ji zafi ba, Faɗane ya kaure a tsakanin su, Sai nishi su ke yi sun cakumi juna, ga jikin nasu duk ba ƙwari, tuni sun haɗa uban gumi, ƙarfi Angel ta sanya wurin kada batul ƙasa, tare da sanya hannu ta damƙi wandon jikinta ta soma kiciniyar zame mata shi daga jikinta, duk don ta gane ma idonta abunda batul ke 6oye mata........."


💋PRISONERS💋




Ba ta kai ga ƙarasa cire wandon ba, sautin dariyar Batul ta janyo hankalin ta ga kallon fuskarta, tsabar mamaki ne yasa Angel ta sakar mata trouser ɗinta, ta tsaya tana kallon ikon Allah sai tiƙar dariya ta ke yi kamar ba ita bace ta ke ku ka.

"Batul bana son iya shege, menene haka? Dariyar me ki ke yi mini? Kin fara sanya mi kokwanto akan ki" ta yi maganar tana binta da kallon tuhuma yunƙurawa batul ta yi tare da miƙe wa ta zaune, Sumar kanta duk ta tarwaste har ta saman fuskarta, tana dariya ta sanya hannu tare da yaye sumar ta mayar da ita bayanta, A hankali ta ke bin fuskar Angel da kallo, ta haɗe rai har wani huci ta ke yi.

"Meyasa ki ke yi mini haka? Ko dan saboda kin ga na damu da ke ne? rai a6ace ta yi maganar, shiru batul taƙi magana sai kallonta ta ke yi,

Gyaɗa kai Angel ta yi"shikenan tunda na zama abun tsokana a wurin ki zan tashi in koma ɗaki, don't ever expect me to worry about you anymore."

Ƙoƙarin miƙewa ta yi da niyar ta fuce daga cikin toilet ɗin, muryar batul ce ta dakatar da ita.

"Ba za ki iya daina damuwa dani ba, that's why ki ka sanya mini ido, ko bacci nake yi idon ki a kaina, duk wani motsi idan na yi sai kin ji ba'asin shi, irin wannan ƙauna haka........" ta yi maganar da zolaya, hakan ba ƙaramin 6ata ran Angel yai ba.

"Nifa ba abunda ke damuna, lafiyata qalau, don kin ga ina bincikar trouser ɗina shiyasa ki ka ɗaga hankalin ki nasan me ki ke tunani nima abunda na ke tunani kenan, sai dai abun da mu ke hasashe bashi ba ne, It's just a rash
ya fito min a wurin, ya addabe ni da ƙaiƙayi, ɗazu dana kwanta bacci, nayi mafarkin Unaizah, hankalina na ya tashi, a lokacin bansan ƙurji bane nadai ji zafi a wurin, gani nake kamar zai yi irin na unaiza, kin ji dalilin dayasa na shigo toilet ina shessheƙar ku ka tare da bincika wandona don inga menene awurin daya haddasa min jin ƙaiƙayi, ban yi tsammanin za ki biyo ni ba, amma tunkafin ki shigo naji motsin mutun nan take raina ya bani cewar Ke ce, shiyasa na ƙara sautin kukan nawa don in firgitar da ke......." bata ƙarasa maganar ba, ta tuntsire da dariya ganin irin kallon rainin wayon da Angel ta ke Yi mata, tana a tsaye ta ruƙe qugu.

"Idan ba ki yarda da magana ta ba, zan nuna ma ki" ta yi maganar tare da sanya hannu tana ƙoƙarin zame wandon jikinta.

"Bana so ba sai na gani ba" ta faɗa tana harararta

"Idan ban nuna maki ba hankalin ki bazai kwanta dani ba, " bata jira jin me zata ƙara ce mata ba, ta yi saurin zame wandon kaɗan ta yadda tsiraicinta bazai baiyana ba, ƙaramin ƙurjine yayi jawur dashi daga gani ba ƙaramin zafi ya ke yi mata ba, Ajiyar zuciya Angel ta sauke hankalinta har ya kwanta, gyara wandon batul ta yi ba tare da ta ɗauke idon ta daga kan fuskar Angel.

Zuƙunnawa Angel ta yi agabanta"Idan har ba ki so raina ya 6aci to ki faɗamin me aka yi maki tsawon time da Giants su ka ɗauke ki," ganin irin kallon da batul ke yi mata ne yasa ta kuma cewa"Kada ki ce zaki 6oye mini komai batul, idan har baki so nima wata rana in 6oye maki wani abu dangane dani, "

A tsanake ta soma magana tana kallon cikin idonta

"Angel

Please Login or Register in order to submit comment